Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gidanshi, bayan Abdul ya gama shigo da kaya Salem ya kalli affan,
"Little bros...excuse us..." Ya fadawa affan,
"Ok sir... But remember my promise.." Ya fada yana hawa stairs, dariya Salem yayi
"Don't worry.. Am a man of my word..." Ya fada, bayan affan ya tafi ya kalli mom don itace main concern dinshi, as for dad he can goto hell,
"Hajiya da akwai maganan da zanso fada maku amma ina ganin is late already..." Bai idaba dad ya katseshi dacewa
"Ai in baka takuraba shikenan..." Salem murtuke fuska yayi Sannan ya fara basu labarin abinda ya faru tsakanin shi da ameera har izuwa yanzu daya kawota gidan, ya kara dacewa
"So ina Neman yafiyanki amatsayin ki na mom dinta...nasan na shiga hakkinki...ki yafemin...kuma Allah ya bata mijin da dayafini...." Tunda ya fara magana dad ya sadda kai kasa, sai lokacin yafara danasanin tarbiyan da ya bawa ameera, hawaye ne ya gangarowa mom, Ahankali ta goge Sannan ta fara cewa
"Alhamdulillah... Allah na ganin I tried my best in bata tarbiya na gari..amma inayi dad dinta na rushewa...nagode wa Allah dayasa ka zama sanadin shiryanta...ko kadan raina bai baci ba..Allah ya saka maka da alkhairi... Don nasan inda aljani ko wani mugun mutum tayiwa haka bazata kai labari ba...so once again thank you.." Tafada tana kuka, itama ameera kuka ta dingayi sosai, kneeling tayi tafara cewa
"Mommy am so sorry... I promise to be a good a girl..." Da sauri mom ta rungume ta, Salem sai ya tsinci kanshi da tausayi da kuma jindadi, dad kam hawaye ya farayi amma babu Wanda ya gani cos kanshi na kasa,Salem yakara cewa
"Babu idda akanta..." Duk sun gane abinda yake nufi,
"Samun irin ka a mazan zamani zaiyi wuya... Mungode..." Mom tayi adding, mikewa yayi
To nima nagode for your understanding...zan wuce sai na sake zagayowa.. " ya fada yana takawa ahankali, ameera mikewa tayi tabi bayan shi, har bakin kofan motan ta rakashi, juyawa yayi ya tsaya yana kallon ta, itama tsayawa tayi kanta kasa, hannu ya bude mata, Ahankali ta taka ta fada jikin shi rungume ta yayi casually Sannan ya saketa,
"I will miss you..." Yafada mata cikin whisper, shuru tayi batace komaiba, cikin mota ya shiga Sannan yace
"Yauwa na mance wannan iPad din is for affan.. And kibani number ki..so that mu dinga gaisawa, " pin dinta ta bashi Sannan ta matsa kusa da motan
"Sir please take care of Tawakaltu.. She's a good person..." Dariya Salem yayi
"I will insha Allah.." Yafada waving dinta yayi itama tayi waving dinshi Sannan suka bar gidan.
๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’š


ยฎzuwairat( ummu Maryam)


7โƒฃ0โƒฃ


Salem relaxing yayi cikin mota duk jikin shi ba dadi don sai yanzu yasan ko baka son mutum rabuwa bata da dadi. Har suka koma gida bai ce komaiba. Suna zuwa yayi wanka ya rama sallolin da ake binshi Sannan ya hau gado yayi ya cire number Khalid daga blacklist Sai lokacin yake ganin messages din Khalid, sunfi talatin, dariya kawai yayi ya fara waya da matarshi.

Itama ameera sam jikinta ba dadi don tasan yanzu babu ita babu Salem,
"Hmmm...I will definitely miss you..." Ta fada cikin ranta daidai lokacin da ta shiga parlour, jikin mom ta kara fadawa dad kam har lokacin yana zaune kanshi kasa,
"Habibty kinga riban wulakanta mutane ko?... Na fada maki amma Sam bakiji.... Ko alhakin maaikatan gidan nan ya isheki...yanzu look what happens..." Mom ta fada tana shafa kanta, ajiyan zuciya tayi
"Mom am sorry... Zan nemi yafiyansu duka...." Tafada cikin sanyin murya,
"Duk baki da laifi...laifi nane.. Duk ni da ja maki..,am sorry daughter..." Inji dad, da sauri mom da duk jikinta yayi sanyi tace
"Alhaji.. Allah ya kaddara hakan zai faru..."
"Dad ka bar daurawa kanka laifi...it was destined to happen" inji ameera data koma wurin dad. Mom mikewa tayi ameera ta mike ta bi bayanta suka hau upstairs,aranan basuyi bacci ba din hira suka dingayi har da affan, shi kanshi affan yaji dadi yanda anty ta chanza don a da bai isa ya tsaya kusa daita ba balle suyi hira.

First thing in the morning ya kama hanyan yola, gidan Khalid ya sauka, Khalid na ganin shi, ya hade gabas da yamma,
"Daman kai haka kake bansani ba?.... Allah yaisa tsakanina dakai..." Salem dariya kawai yayi ya samu wuri ya zauna yana kallon Khalid dake huci, Khalid yacigaba dacewa
"Wallahi Allah ya taimakeka...I intended to take this later to Umma and Abba...."
"Kace masu me?..." Salem ya tambayeshi atakaice
"Kasan sauran..." Baki Salem ya tabe
"Ai is your word against mine....banza Mara hankali..." Salem ya fada yana dariya, tsaki Khalid yaja
"Dalla ina yar mutane?..."
"Tana gidansu...." Afusace Khalid yace
"Haka mukayi da kai?..lallai ka isa dan bakin ciki...don kaji nace inason ta shine ka tashi ka kaita gidansu ko?...no problem.. I will find my way..." Yafada cikin fada, Salem tabe baki yayi
"See dalla relax let's talk like two matured men..." Salem ya fada mashi, Khalid baice komaiba ya dinga girgiza kafa, Salem ya cigaba dacewa
"Please in kasan ba auren yarinyan nan zakayi ba kawai just let her be..." Hararanshi Khalid yayi
"Look who is talking... Kai da ka aureta ka ajiye ta cikin sambiza fa?... Ai kasan ni na fi karfin wannan..." Dariya Salem yayi don shi ko kadan bai daukan abun da zafi kaman yanda Khalid ke ta tada jijiyoyin wuya,
"Ni dai rokonka nake...if you know you are lusting after her then just forget about her..don wallahi if you tries anything stupid zan manta da friendship dinmu in ci burouban ka.."
"Sannu dad..." Khalid ya fada mashi
"Wallahi ba da wasa nake ba...ba dan ban sonta na rabu daita ba...don ko makaho yasan da ameera..." Tsaki Khalid yaja
"Kana sonta ubanwa yasaka rubuta mata saki...kawai in kana bani address dinta kabani and stop all this Bullshits..." Salem bai kara cewa komaiba ya mike
"Ni zanje gaida su Umma kafin in koma..." Yafada yana nufan bakin kofa, da sauri Khalid ya tari gabanshi
"Haba guy...why are you doing this to me...wallahi yarinyan nan son ta nakanyi..." Salem dariya yayi don yanda Khalid yayi maganan,
"Wallahi am serious... Please just give me her address... I promise to take good care of her...kaji daddy..." Salem dariya ya karayi
"Please help me.." Khalid ya kara cewa, kallon manyan idanuwanshi Salem yayi
"In ba karya ba ka taba ganin inda mutum yayi falling in love da wacce bai taba ganin koda pic dintaba?..."
"AI kullum cikin imagining face dinta nake, yanda kayi describing dinta ma ya isheni..."
"Naji...tell Abdul guard dina ya rakaka gidansu..." Da sauri Khalid ya dan rutsuna
"Thank you Abba..." Salem banza yayi dashi ya fita
"Abba kajira in saka kaya muje gaida su Umma mana..." Banza yayi dashi yayi tafiyan shi.

Salem family house dinshi yaje inda Umma da Abba suka nemi jin actual reason dinshi na zuwa Nigeria yayi masu karya da wani emergency meeting ne ya kawo shi, zama yayi ya cika cikin shi Sannan yayi masu ban kwana, karfe twelve ya bar Nigeria.

Ameera kam gari na wayewa ta shirya ta sauka downstairs ta shiga kitchen da masu aiki tare sua dafa abinci, Sai mamaki suke, kallon su tayi Sannan tace
"Sahura" wacce ta kira ta amsa mata tana kallon ta,
"Talatu..." Ta kira daya itama amsa mata tayi Sannan ameera ta fara cewa
"Dan Allah, ina neman yafiyanku kan abinda nayi maku abaya...Dan Allah Ku yafemin..." Dukkan su biyu shuru sukayi suna kallon juna,
"Dan Allah fa nace...ba kaman ke talatu nasha marinki batare da kin yimin komaiba... Dan Allah Ku yafeni..." Da sauri sukace
"Mun yafe maki...Allah ya yafemana..." Cikin jin dadi ameera tace
"Ameen nagode..." Tafada tana rungume su biyu lokaci daya, Allah yasa ba mafarki suke ba, don sun San ko cup din ameera babu wacce ta isa ta taba cikin su ba tare da tacin uwarsu ba. Bayan sun gama jera breakfast kan dinning ameera ta fita waje taje wurin masu wankin mototaci da sauran maaikanta maza ta nemi yafiyansu, suma duk yafe mata sukayi, tambayan tsohon data fesawa pepper spray tayi daya daga cikin su yace
"Ai tunda wani yabashi kudi ya bar gidan nan..." Inji daya cikin su
"To Dan Allah kunsan inda yake yanzu?..." Ta tambayesu cikin sanyin murya
"Eh...yana sabuwar gandu...."
"To Dan Allah zuwa gobe zaka rakani wajen shi...."
"To Hajiya karama..." Suka amsa mata Sannan ta bar wajen, duk abinda take yi a idon mom dake tsaye bakin window upstairs, kara godewa Salem tayi tana yi mashi adua. Sama ta hau ta kira mom da dad su sauko breakfast.
Suna kan dinning take basu labarin su hinde da yaranta, ba karamin dariya dukkan su suke ba ba kaman mom dake kallon ameera With adoration
"Wallahi mom sanda na fara ganinta nayi tunanin zombie ce..." Tafada tana dariya
"Sai gashi ta zama the most important person in my life at that time... Ashe mom mutum Rahama ne?...I was willing to give all the money sir Salem gave kawai don a barta ta shigo..." Tafada tana dariya sosai, dukkan su dariya suke, mom bata taba jinta cikin kwanciyan hankali ba kaman yanzu, don bata da matsala kaman rashin respect din ameera ga mutane
"Ai ina fada maki... Ko trillion zaa baki a hanaki zama da mutane an gama da kai...don mutane are very important in our lives... No matter how dirty... Poor...ugly they are..." Inji mom
"Hakane wallahi...." Ameera tayi adding, hira suka cigaba dayi har suka gama breakfast. Ameera ta tattare plates ta kai kitchen, ta dawo ta tadda mom dake zaune falo looking very relaxed, kusa daita ta zauna
"Yanzu mom inason inje gidan su zeenat..."
"No baby...ki je kiyi wanka ki kwanta... Just call her...nafison ki maida jikin ki sosai kafin kifara fita..."
"Ok..amma mom in fada mata gaskiya abinda ya faru tsakanina da sir Salem ko...." Ta tambayi mom, shuru mom tayi for a while Sannan tace
"If you trust her...don banason mutane suji ainahin reasons din daya maido ki gida...kawai a fada masu rabuwa kukayi is better than a fada masu komai...don bakasan mai farinciki kan problems dinka ba..."
"Mom I trust zeenat... Bazata fadawa kowaba...she's the only friend I trust... Ai ranar da muka fara haduwa da sir Salem muna tare daita..."
"Ok..." Kawai mom ta fada mata Sannan ta mike ta hau upstairs.
Kayan da sir ya saya mata ta jera cikin wardrobe dinta ta fiddo wasu da yawa don ta badasu, wayanta ta dauka ta saka sim card dinta, tana kun nawa taga message kaman haka,
_"The ugly taxi driver is saying good morning... Ki gaida mutanen gidan...na tafi..."_ dariya tayi Sannan tayi saving number Salem.
Zeenat ta kira, in one word tace
"Babe am home..." Wani irin ihu zeenat tayi
"Am flying over right now..." Zeenat ta fada Sannan ta katse wayan ta.
Wanka tashiga tafito ta shirya cikin daya daga kayan da Salem ya saya mata, ba karamin kyau tayiba, tana komawa down stairs taji an bude gate, da sauri ta fita don tasan zeenat ce, ko parking lot zeenat bata kai motan ba ta fito da gudu itama ameera da gudu suka rungume juna, kaman yara suka dinga ihu suna jumping, kallon ta zeenat tayi
"Amma babe kin Dan rame..."
"Hmmm..sis kedai bari...naga rayuwa"
"Kodai ciki ne?...." Dariya ameera tayi,
"I have gist for you... Amma muje ciki in baki ruwa ki sha..." Wani irin dariya zeenat tayi
"Shegiya ke zaki bawa mutum ruwan sha?...wonder shall never end..." Dukanta ameera tayi
"Sis ki bar ruwa...just give me the gist...." Zeenat tayi adding. Wuri suka samu nan waje suka zauna ameera ta fara bata labarin komai, zeenat baki kawai ta bude tana sauraron ta, saida ta kai karshe Sannan zeenat tace
"Ikon Allah... Am I dreaming..."
"No dear... Its real..." Ameera tayi assuring dinta
"Daman na dade ina warning dinki amma bakiji...nasha fada maki duk abinda kike takama dashi da akwai Wanda yayi doubling dinka...in kudi ne..motan da wani yake hawa ya sayi komai naka... In kyau ne.....ko kafan wani baka kamaba...in ilimi inda naka ya kare nan na wani yayi starting... Look now for instance jet din Salem ya sayi duk abinda dad ya mallaka..."
"Kedai bari...now I know better....sis da akwai dukiya inda take... Kar kiso ki ga gidanshi na abuja...estate guda
..."
"Ai kinyi loosing... Wait ya matanshi?.." Zeenat ta tambayeta
"Wallahi Matan is very nice... Har kuka take wai kar in tafi..."
"You mean tanason Ku zauna tare?..."
"Seriously.. I was surprised.. Yanzu we're friends..."
"Hmmm...sis anya har yanzu ke ba matar Salem bace?..tunda kince kina period lokacin da yayi sakin?..."
"Ai babu abinda ya taba shiga tsakanina dashi...so babu aure.." Hira suka cigaba dayi kaman sun shekara basu haduba,
"Sis enough about me...ya zancen auren ki da Mahmud..." Ameera ta tambayeta
"Sauran two months wedding... Yanzu tunda Allah ya kawo ki Sai mufara choosing wears din da zamuyi amfani dashi..." Tsalle ameera tayi don jindadi, zeenat ta fiddo wayanta, tana cewa
"Bari kiga kayan da yaya sultan ya yimin order..." Tafada tana bude gallery din wayan ta, kusa daita ameera ta dawo tana cewa
"Yaya sultan ya dawo daga Madrid ne?..."
"Aa..Sai next week... Shima don Abba yaci ubanshi..." Dariya sukayi, zeenat nuna mata wasu elegant kujeru da gado tayi, baki ameera ta bude
"Wooowwww...babe na kasa rufe bakina.... Please ki tayani rufeta..." Tafada tana daria, dukkansu Dariya sukayi
"Amma yaya sultan ya iya choosing... Gaskiya yayi kokari..." Inji ameera,
"Yo sis baki San wani abu ba...set uku yace zaiyi Abba ya hanashi..."
"Kam...Ashe daman yan kwallo suna da kudi haka?..." Inji ameera
"AI weekly aka basu kudi kuma ba kadan ba....amma abun haushi wai baturiya zai aura... Abba ya hana..."
"Tofah...amma da sun barshi ya auri wacce yakeso...." Bata idaba zeenat ta galla mata harara
"Haba sis...Sai kice babban wanmu ya auri kafira?...Aa wallahi..."
"Allah ya zaba mashi wacce tafi alkhairi..."
"Yanzu kikayi magana...".
Haka suka cigaba da labartawa. Sai bayan magrub zeenat ta koma gida.
๐Ÿ’œโค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’™๐Ÿ’šโค๐Ÿ’œ๐Ÿ’›

ยฎzuwairat(ummu Maryam)


7โƒฃ1โƒฃ


_One week later_

Ameera ta maida jikin ta sosai don har haskenta ya dawo, Sai gulma ake wai Salem ya saki ameera daga auren beyerabiya, su kam ko ajikinsu tunda sun san gaskiyan maganan, kawayen ameera datake wulakantawa Sai Allah shi kara suke yimata, wasu har kiran number ta suke su zolayeta, amma ko uffan bata ce masu, itadai alhamdulillah she's a changed person.
Ameera da zeenat tare da daya daga cikin masu aikin su sunje gidan wannan tsohon da ta taba fesawa pepper spray, har yau tsohon bai gani sosai saida glass, shikuma mako ya hanashi ya dauki kudi daga cikin kudinda Salem ya bashi ya kai kanshi hospital, yanzu shago ya bude shi da babban danshi suna zama, ranar da sukaje sauran kadan babban danshi ya doki ameera wai tayi sanadiyan mutuwan idanuwan ubanshi, hakuri ta dinga basu don har kneeling tayi tana kuka, tsohon ya yafemata, hospital tace zata kaishi tsohon yace ta barshi. Babu irin rokonshi da batayi ba amma tsohon yace ta tafi ya yafe mata, haka suka bar gidan jiki ba kwari, kan hanyan su ta dawowa zeenat tace
"Babe ko alhakin wannan tsohon ya isheki rayuwa..Allah ya taimaka bai mutu ba kafin ki tuba..." Ameera dai batace kala ba sai tukin mota take.

Bangaren Khalid kam da kyar Salem ya shawo kanshi kan ya bari ameera tayi at least sati two a gida kafin yaje, don babu dadi daga dawowanta ya kama hanya gidansu donshi ko kadan bayason ameera yasan da akwai wata dangantaka tsakanin shi da Khalid.

Salem da matarshi kam honeymoon suke don yanzu sun bar Malibu sun koma Hawaii, Salem dai kejin dadi honeymoon amma tawa duniya ta isheta, don tun ranar first night dinsu bata huta ba har yau. Har ga Allah tasan Salem is every woman's dream don he's caring, loving, romantic, giver don har company ya bata kyauta for keeping herself intact until marriage amma he's rough and mean in bed.
Har fargaban dare take ,gashida rana he's gentle and nice amma in dare yayi duk kukan da zatayi bai sashi ya raga mata, duk Wanda yaga yanda take tafiya kasan da akwai matsala.
Shi kanshi abun yana damunshi don har personal doc dinshi ya kira ya fada mashi bai samun natsuwa da wuri inda doctor ya shaida mashi side effects din drugs da ya dinga sha for years ne. Har tausayin tawa yake amma he can control himself.

A Hawaii resort mai suna Waikiki resort hotel suka sauka, fadin haduwan wurin is a waste of time, don ga beach Sannan da akwai babban restaurants, a bayan hotel din da akwai designer show room zaka zabi duk kayan da ka ga ya burgeka ajikin model.
Suna zaune da safe a waje suna breakfast ga wasu sunata houla dance, Salem kallon tawa da duk ta shiga duniya tunani yayi, hannun yasa cikin pocket dinshi ya dauko wata sarkan diamond daga company muai divers jewelry, Wanda akalla zaiyi 15000$ ya ajiye kan hannun ta dake kan table, bata Sani ba cos duk tunanin rayuwan masu kudi take, suna son komai perfect, kaya neat, makeup, perfect,
"I love normal life..." Ta fada cikin ranta, Salem mamakin tunanin da take yayi don har yanzu bata ga abinda ya ajiye mata ba, hannun ta ya taba, Ahankali ta daga idanuwanta ta kalleshi, batace komaiba, nuna mata sarkan yayi, Sai lokacin ta ganshi, kallon sarkan tayi tadan saki murmushi amma da gani bai kai cikin ranta ba,
"Thanks..." Ta fada atakaice.
A ranan suka je submarine don ganin sea life, tawa kankame Salem tayi don tsoro don wasu abubuwa ko a film bata taba ganin su ba.
Yawo suka dingayi cikin gari Hawaii amma Salem ya lura da tawa don't look excited. Sai dare suka dawo resort.
Sallan ishai sukayi room service ya kawo dinner yaci itakam tawa banda faduwa babu abinda gabanta yake,
"Habibty please eat..." Kallon shi kawai tayi ta kauda kanta, mikewa yayi ya dawo kusa daita,
"Please baby what's wrong with you... Why are you moody?.." Ya tambayeta
"As if he's not the cause of my problem..." Ta fada cikin ranta, daga ta tsaye yayi ya rungume ta ya farayi kaman yana rawa ahankali
"Please tell me what your problem is and I will solve it this instance..." Yafada cikin whisper, shuru tayi batace komaiba cause yana cikin shawaran da Haj kudirat ta bata kan she should not complain about such things,
"Baby..kinyi shuru..." Ya sake fada yana moving da ita ahankali,
"Ba...komai..." Ta fada cikin sanyin murya.
"Ok..seat here..." Yafada yana zaunar daita kan wani sofa dake kusa da fire place, bathroom ya shiga tawa ta bi bayan shi da kallo don tasan abinda zaiyi, bayan kaman 15 minutes ya dawo, daga ta yayi
"Muje muyi wanka mu kwanta mu huta..." Bai idaba ta girgiza mashi kai
"Why?..." ya tambayeta
"Ba yanzu zan kwanta ba.." Ta amsa mashi atakaice,
"I insist.." Ya fada yana rike da hannun ta ba don ta soba suka fara wanka, mugun wasan shi ya fara yi mata, aikam Sai ta fashe da kuka
"Am tired... Ni wallahi na gaji..." Ta fada tana Dan tureshi, bai saurareta ba ya cigaba da abinda yayi niyya, kuka sosai ta fara tana cewa
"Am tired... Duk jikinta ciwo yake min...marata ciwo yake min...wallahi am tired..." Salem daka tawa yayi ya tsaya yana kallon ta, yana tausayin ta amma he can't help it,
"Nagaji...nagaji...nagaji...!" Ta fada cikin kuka, still kallon ta kawai yake, yasan she's not the type of woman you will beside without anything,
"Baby am sorry... I can't help it...very you will get use to it..." Da sauri ta girgiza mashi kai
"I will never get use to this suffering... Wahalan is too much for me alone... Shiyasa na ce ka maida sis Aisha amma kaki...ni wallahi nagaji..." Tafada tana kuka kaman ranta zai fita, tsaya kallon ta yayi shi kanshi yana Dana sanin sakin ameera, he remembered lokaci da yaje wurin ta, when he played with her she was willing to allow him go to any length..
"Kiyi hakuri...yanzu let me give you a bath...saikije ki kwanta..." Ya fada yana kara taba ta, da sauri ta dan matsa baya
"Zanyi wankan da kaina..." Tafada tana watsawa kanta ruwa, kowa yayi wanka suka fito daure da towel, kwantawa yayi kan gado, ita kuma ta koma cikin closet don saka kayan bacci dukda tasan bai yarda ta kwanta da kaya, kallon ta yayi
"Princess me zakiyi?..." Ya tambayeta
"Kaya zan saka...." Ta amsa mashi atakaice
"Princess kinfa San banason kina kwantawa da kaya...kawai zo ki kwanta..." Kuka tafarayi
"Haka ka fadamin shekaranjiya....amma still..." Sai tayi shuru, Salem Dariya yayi ya mike daga kan gado, wurin ta yaje ya riketa
"Just come and sleep... Ba abinda zanyi maki..." Yafada dajin maganan kasan karya yake, harara ta galla mashi ta cigaba da kuka
"Nasan karya kake..." Ta fada cikin kuka, Dariya ya sakeyi yana rike daita
"Princess nike karya?...remember am 17 years older than you... Nidai zo ki kwanta..."
"To kabari in saka kayan..." Girgiza mata kai yayi
"I said I will be a gentle man.,"
"Ba wani gentle man... That's what you always say..." Tafada tana kuka kaman ranta zai fita, hannun ta ya kama ya kaita bakin wani hadedden Italian bed
"Kin kwanta kinji..." Girgiza kai tayi
"Banji bacci..." Tafada tana kuka, Dariya yayi yaje ya kwanta yana tunanin yarinya ta maidani dodo.

Aranan duk yanda taso kaurace mashi abanza don bai kyaletaba kuka ta kwana tanayi, babu irin rarrashin da baiyi bataba amma taki yin shuru cewa take
"Ya maidata gida..ita bata Iya wannan wahalan.

A week later babu abinda ya chanza ga halin Salem, ita kuma tawa babu alaman sabo da halin shi, yanzu go tour bata binshi honeymoon yazame mata honey wahala, kullum cikin bata gift yake amma bata amsa ita kawai ya maidata gida. Duk ta rame amma skin dinta yayi kyau da haske, amma kullum idanuwanta kumbure saboda yawan kuka gani take kaman ba sonta yakeba ya aureta ne don yayi molesting dinta, and the most annoying part shine kaman its getting worst than ever, ita da bacci Sai da rana at times ma da ranan hanata yake, she hate him and also hate herself for accepting him.

Salem kam kaman yayi hauka saboda irin wahalan da Tawakaltu take sha hannun shi, da yayi niyyan cigaba dashan drugs dinshi amma doc yace it will only worsen it, kallon yanda take ta faman kuka yake
" baby am sorry... " yafada yana rike hannun ta, da karfi ta buge mashi hannu
"Stop it...kawai bring Aisha back...in ba hakaba ka auro wata...nidai Allah nagaji..."
"Yanzu princess zaki amince inyo maki kishiya?..." Harara ta galla mashi da red eyes dinta,
"Ko uku ka karo...I don't care..." Tafada tana kuka,
"Ok naji..I will think about it..."
"Think f kace?...I don't think there is time to think... Just act before you kill me..." Dariya yayi
"Naji...taso inyi maki wanka..."


Tun jiya da yamma Khalid ya sauka garin Kano saboda zuwa wurin ameera, bayan sunyi breakfast tare da Abdul ya shiga wanka kasancewan a gidan Salem na Kano ya sauka, yana fitowa ya shirya cikin manyan kaya looking so breathtaking.


" mom zanje gidansu zeenat... " ameera dake kyalli saboda haske ta fadawa mom,
"Habibty kibari...." Mom bata idaba ta katseta dacewa
"Please sweet mom..."
"Ok..." Mom ta amsa mata, da sauri ta saki ihu Sannan ta hau upstairs.
Bayan hour daya ta sauko cikin English wears, black Tommy Hilfiger skirt Sai white simple top.gyara gashin ta tayi sosai ta yafa Vail Dan karami kanta, batayi kwalliya ba amma ba karamin kyau tayiba, yanzu bata da damuwan komai cikin ranta,
"Mom na tafi..." Tafadawa mom dake zaune falo, mom kallon ta tayi ta yimata alaman OK da hannu Sannan tace
"Baby na kinyi kyau..." Tafada tana shaawan yarta har cikin ranta
"Thanks mom..." Tafada Sannan ta nufi waje hannu ta daya rike da car keys dinta Sai dayan hannun ta rike da pause.

*Please zakujini shuru for a while, commitment sunyi min yawa, thanks.* ๐Ÿ‘‹๐Ÿป๐Ÿ‘‹๐Ÿป๐Ÿ‘‹๐Ÿป
๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™๐Ÿ’š
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›

ยฎzuwairat( ummu Maryam)


7โƒฃ2โƒฃ



Ahankali ta dinga tuki har takai gidansu zeenat, horn tayi maigadi ya bude gate, tana shigowa ta hangi zeenat tsaye da swiss lace dinkin riga da skirt kanta babu head, tayi mugun kyau don yanzu an fara mata gyaran amare, ameera na packing ta karaso kusa da motanta ta bude mata kofan ameera ta fito,
"Da girman kujeran ki..." Inji zeenat,
"Kedai keda girman kujeran.. Tunda kece amarya.." Ameera ta amsa mata tana dariya. Zolayan juna suka fara Sannan suka shiga ciki, wurin umma sukaje ameera ta gaidata Sannan suka koma dakin zeenat, labarin duniya suka fara har zuhr basu fitaba suna dakin, saida suka gama sallah Sannan suka fito cin lunch kasancewan mai aiki tazo kiransu, a kan dinning Umma ce zaune Sai wani cute

Please Login or Register in order to submit comment