Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga ya ya cire brown jallabiya dake jikinshi ya kwanta daga shi sai boxer ya rufe kanshi da bargo.
Yana fita tawa ta dawo falo, nan ta tsaya har gari ya ida wayewa, gani tayi babu kowa compound din, gani tayi wani kusa da gate kuma shine Wanda ya bude masu gate jiya, daukan bag dinta tayi, ta fita tana kokarin sakin fuskanta, tan zuwa daidai bakin gate ta gaida shi, shima cikin murmushi ya amsa yana cewa
"Har zaki wuce?"
"Eh...tafiya ta na gaba"
"To Allah ya saukeki lafiya" yafada yana bude mata kofa,
"Ameen nagode" tafada tana kara yiwa gidan kallon bankwana.

Daga nesa wasu guys dake cikin black Prada suka hangi wata ta fito daga cikin gidan Salem, daya nunata yayi
"Guy ko wancan ce yarinyan?" Dayan kallon yarinyan data taho tana waige2 yayi tare da Jan tsoki
"Uban me sir Salem zaiyi da wancan?" Yafada yana dauke kanshi daga kan tawa. Still daya cewa yayi
"Da akwai hanyan dazamu gane in itace" dayan bai amsa mashi ba yace
"Nufa na gashi da wannan zaman...nasan da kyar ace yarinyan tana gidan.... Sannan in tana gidan bazata fitoba sai dashi..."
"Ka fadawa Hajiya hakan Mana?" Dayan ya amsa mashi, shuru sukayi har tawa ta zo wucewa, daya ya fito daga cikin mota yace
"Tawakaltu.. Ki tsaya mana" nan take gabanta ya fadi ta juyo tana kallon shi
"Tawa ina zaki haka da safe?" Ahankali tace
"Gidan yan uwan zani..." Bata idaba dayan guy din dake sauraron hiransu ya fito tare da nuna mata pistol
"Enter this car before I blow your brain off" habawa nan take jikinta ya fara rawa
"Dan Allah kuyi...hakuri..bani da komai.." Bata idaba wani daga cikin su ya turata cikin mota. Suka shiga sukayi gaba. Abinka da unguwan manya babu kowa waje..sai CCTV cameras dake gidan Salem dake ta daukan su.

Thanks so much my sawwama...Allah ya bar Mani ke..
Note this: your are also a super star, keep your good attitude up..


๐Ÿ’™๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’™

ยฎzuwairat(ummu maryam)

3โƒฃ6โƒฃ

Gari na wayewa, diyar hinde ta tashi da wuri tayi yan wanke2 tare da shara, ameera fitowa tayi
(Yan mata a rage shafe2,inke bakace maintain your colour ) ameera ta fara duhu sosai ga kuma rama datayi, gefen fuskanta yafi duhu, duk sai ta koma kaman ba itaba,
"Dan Allah kina da kudi ki sayo min Maganin malaria?" Ta tambayi yar hinde
"Eh..amma mai chemist bai kaiga budewa ba" ahankali tana dafa bango tace
"To..please in kin gama ki dora min ruwan wanka..sanyi nakeji"
"To shikenan" ta amsa mata tacigaba da abinda take.

Around 8:30 hinde ta shigo still sanye da kayan da ameera ta bata, bayan sin gaisa ameera ta dauko bangle bracelet dinta guda daya ta mikawa hinde
"Gashi ki saidomin" da sauri hinde ta amsa sannan ameera tacigaba dacewa
"Ki boyeshi sosai dan Allah..110k yake..in kinje shagon zaa auna sai abaki kudin...ki nemi inda ake saida waya ki sayo min ko wacce iri ce sai ki sayomin layi Mtn da kati na dubu daya..sai ki biya shago ki sayomin kayan shayi manya tin ..." Ameera sai lissafa mata take itakuma sai
"To" kawai take cewa, bayan ta gama yimata bayani ta fito da shirin tafiya, ameera kiran tayi
"Gashi ki yafa..kar ace satoshi kikayi" ta fada tana mika mata expensive Vail dinta, hinde wace hakora tayi ta masa
"Kuma dan Allah karkije kina wace hakora haka..it looks disgusting"
"To shikenan" ta fito ta kalli yarta
"Ko me take so kidafa mata"
"To Inna..ki dawo lafiya"
"Allah yasa" ta fada sannan ta fita daga cikin gidan.

Tasha taje ta hau motan dazai kaita gwagwalada, bayan ta sauka chan, ta dinga tambayan mutane ina akesiyan zinari, kasancewan yawan cinsu ba hausawa bane, basu gane abinda take cewa ba, wasu samari guda biyu ta gani zaune suna shantaba,wurin su ta nufa ta gaida su aka cin saa irin hausawa nan ne masu fita nenan kudi ,
"dan Allah shagon da ake sayan zinari nake nema" ta fada masu, samarun kallon junansu sukayi, daya yace
"Muga irin zinarin" hinde ta fidoshi daga karkashin zaninta..ko cikin pant dinta ta sanyoshi Oho, samarin Kara kallon juna sukayi, da suka ga abu na kyalli, mikewa sukayi bayan sun yiwa junansu sign
"Kizo mu nuna maki wurin" daya ya fada, hinde binsu tayi, daya baya daya gaba sai Hajiya hinde tsakiya, sunyi tafiya kaman na minti ashirin, saida sukaje inda babu mai ganin su suka tsaya, na bayan wawan mari ya ballewa keyan hinde sannan ya mika mata hannu, agigice hinde ta juyo, sai shafa inda aka mareta take,
"Miko.

" mutumin yacewa hinde,
"Haba Dan nan..ban haifekaba?.. Sai kace in baka basai ka taba min lafiyan jikiba..amshi" tafada tana mika mashi zinarin, suna amsa suka bar wajen aguje, sai lokacin hinde ta gane sata akayi mata, hannu ta dora bisa kai tafara kuka
"Wannan yarinyan Mara mutunci za a hadani da ita..wayyo na shiga uku na mutu" ta dinga maimaitawa har inda zata shiga motan komawa gida.

๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›

Tawa kuka ta dinga yi kaman ranta zai fita, dama ga gajiyan Wanda tayi jiya, sai shessheka kawai take, mutanen ko kallon inda take basuyiba suka cigaba da driving abinsu, daya waya ya dauko yayi dailing wani number, few seconds later akayi picking, gaisuwa sukayi sannan yace
"Hajiya mun ganta...yanzu yolan zamu wuce daita?" Shuru yayi yana sauraron abinda ake ce mashi
"To shikenan.." Yafada tare da katse wayan. Tawa najin ance yola ta fara kuka sosai tana yarfa hannuwa
"Dan Allah kuyi hakuri Ku maidani...bani bace tawa..sunana maryam" ko kallon ta basuyiba Wanda yayi waya ya kalli Wanda ke tuki
"Ka kara gudu muna da tafiya.." Dayan baice komaiba ya kara gudu sosai, tawa kuka ta dinga yi,aikam sai wayanta ya fara ringing, abinka da China phone, nan take tayi saurin dauka zatayi picking Wanda baya tukin yayi saurin fixgewa daga hannunta ya wurgar dashi waje, sabon kuka ta fara, kallonta yayi
"Kinsan Allah saanki daya anbamu strict instructions kar mu tabaki amma wallahi na lahira sai yafiki jin dadi.." Tawa karawa kukanta volume tayi
"Dan uwarki bazaki yimana shuru ba?".. Mutumin ya daka mata tsawa, da sauri ta kama bakinta ta rikeda hannu, amma hakan bai hana hawaye zubowa ba, haka suka cigaba da tafiya tawa sai tunani take, tana Allah yasa ba kasheta zasuyiba

๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›๐Ÿ’š

Salem bai tashi ba sai 10am, mikewa yayi zaune ya dauki wayanshi ya kira majed
" alh..ka je wurin mai fashion dress na Sheraton hotel ya baka designer dress sai shoes da jewelry da zai hau kayan..daga nan ka wuce chan gidan da muka kai wata Shaidaniyan yarinya ka dauko min CCTV record din gidan"
"Yes sir" yafara cewa sannan yace
"Sir ina CCTV recorder din yake?.."
"Call my agent"
"OK.." Katse wayan yayi sannan ya mike yana rawa da filo kaman baby, da sauri ya wurgar da pillow ya kira cook yayi mashi umarnin ya jera mashi abinci a part din da tawa take.

Wanka ya shiga ya fito daure da towel, mai ya shafa tare da body perfume sannan ya shiga cikin closet ya dauko wasu three quarter Jordan da t shirt mai kyau da tsada, red sneaker ya saka cos riganshi red ne. Gaman mirror ya koma ya wanke kanshi da perfume kala2 sannan ya fito yana wani annashuwa ko na meye, oho, fita yayi ya nufi mansion din da tawa take, sallama yayi ya shiga falo yaga an jera abinci kala2, bedroom yashiga ya tare da sallama, shuru yaji ya zauna bakin gado yana jiranta don a tunanin shi bathroom ta shiga.
Bayan minti goma yace
"Habibty.. Am waiting..." Ya fada yana kallon agogon hannunshi, shuru yaji ya kara tsayawa for 5 more minutes, bakin kofan ya je yayi knocking
"Habibty ki fito haka nan mana..lokacin breakfast is going.." Still shuru no response, kara knocking yayi still no answer, Ahankali ya bude ya shiga, gani yayi wayam ba kowa, wani irin shar ya saki tare da fito waje da gudu, da gudu ya isa bakin gate,
"Umar!" Ya kira mai gadi da karfi kaman muryan shi zai tsage, da gudu ya fito daga BQ
"Sir gani" cikin fada yace
"Ka budewa kowa gate?"
"Yes s...."
"Kan burouban nan...ubanwa yasaka bude mata gate.." Ya fada lokacin daya nufi mai gadin gadan2, wani wawan mari ya wanka mashi sannan ya shakeshi
"Ubanwa yace ka bude mata gate" yafada yana girgiza shi,
"Wallahi in ban ganta ba..consider your self fired!" Wulla dashi yayi
"Abdul!..Idris!..isa!..." Haka ya dinga kwalawa guards dinshi kira dayan bayan daya kaman mahaukaci da gudu su biyar suka fito banda majed.
"Where is tawa!...?" Yafada da karfi har jijiyoyin wuyanshi na tashi, kallon juna suka tsayayi,
"Sir bamu ganta ba..."
"Fuck all of you...meye aikinku..kun tsaya bacci har ta fita daga gidan nan ko.." Dukkan su shuru sukayi suna mamakin irin fadanshi don basu taba ganin shi haka ba
"Now listen..in baku nemota in the next one hour ba...consider all yourself jobless.." Yana kaiwa nan ya shiga wurin shi da gudu.
Guys din komawa sukayi cikin part dinsu suka dauko makulla motansu suka rarraba Kansu suka shiga cikin garin tare da zuwa motor park.

Salem na zuwa ya dauki wayanshi ya kira number tawa, ji yayi not reachable, kara dailing yayi still not reachable, wurgar da wayan yayi tare da dafa kanshi,
"Tawa..why did you do this.." Yafada Ahankali
"Why are fucking with my heart!" Ya fada afusace, nan take fuskanshi yayi ja, yana zaune ya ji kara saukan jet dinshi, da sauri ya fito ya shiga ciki
"Take me to Kano" ya fadawa pilot, nan take a juya jet, cikin 40 minutes suka isa kano, har kofan gidansu tawa aka saukeshi, duk mutanen unguwan taruwa sukayi suna mamakin abinda ya kawo Salem Yusuf sulaiman unguwansu, don mutane da yawa sin san fuskanshi, da sauri ya sauka ya shiga gidansu tawa, gani yayi kofansu kulle, wani neighbors dinsu ya tambaya
"Da safe mami ta koma garinsu...amma tace zata sa a kwace masu kayansu" inji mutumin
"Please ya sunan garin su
" garin yarubawa"
"please garin Yoruba na da yawa..wanne daga ciki?"
"Gaskiya bansan sunan garinba..."
"Dan Allah kasan gidan wani danuwan su?" Mutumin girgiza mashi kai yayi, nan Salem yaji kafanshi bata daukan shi, Dan durkusawa yayi wajen for more than five minutes sannan ya mike ahankali ya koma waje tare da shiga cikin jet dinshi ya bar wajen,
"I regret falling in love with you.." Yafa cikin zuciyanshi
๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
โค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’š

ยฎzuwairat(ummu maryam).

3โƒฃ7โƒฃ

Wajen karfe one suka isa yola,har lokacin hawaye bai bar zubowa tawaba, nadaman abinda ya fidota kawai take, wani makeken gida suka shiga sukayi parking, waya taji sunayi
"Mun iso..." Shuru yayi for a moment sannan yace
"OK ma" fita sukayi suka bude mata, kin fitowa tayi, daya mai bakin fuska ya fixgota, ya rike mata hannu
"Dan Allah kar kuyimin komai.. Narokeku...ni kadaice wurin mamina... Please kuyi hakuri.." Ta dinga fada cikin muryan ta Mara fita don kuka, cikin wani katon falo suka wulla ta sannan suma suka shigo, falon ta fara kallo, gabanta ne yayi mugun faduwa data ga makeken hoton Salem, sanye yake da red fitted suit hannunshi cikin aljihunshi.. Fuskanshi kaman da models, kara kara juyawa tayi ta ga wani yana tsaye bayan wata beautiful mata da wani cool looking man, nan tasan gidansu Salem aka kawota, sabon kuka tafarayi, sun fi minti ashirin da zuwa sannan Umma ta fito, tafiyanta na kasaita tamkar ka tabata jini ya fito, tawa daga kumburarrun idanuwanta tayi ta kalleta, gani tayi da ita da Salem kaman an tsaga kara, tsawo kawai zai nuna mata, da sauri tawa tayi kneeling down kanta kasa hawaye na zuba tana fargaban abinda zai faru, Umma tsayawa tayi tana kallon tawa, mamaki ne kwance kan fuskanta don atunaninta wata gingimemeyin Yoruba zata gani, sannan kuma Sam babu alaman yarbancin jikin ta, kallon fuskanta tayi taga she is beyond wonderful.
"Please sit" ta fadawa tawa, Ahankali tawa ta girgiza kanta, gaidata tayi dukda muryan ta bata fita,amsawa tayi tana kara mamaki don Sam hausanta babu alaman yare cikin shi..kallon guys din tayi
"Are sure she's the one?"
"Yes ma..daga gidanshi muka daukota" daya daga cikin guys din ya amsa mata, kallon yanda tawa take shessheka tayi
"Kunyi mata wani abune?" Ta sake tambayan su, da sauri suka girgiza mata kai.
"Excuse us" ta fada masu, da sauri suka fita, kallon tawa tayi
"Come closer" ta umarceta, tawa bata mike ba tayi rarrafa zuwa gabanta, Umma kura mata ido tayi ta rasa abinda zata ce mata, Ahankali tace
"What is your name?" Cikin shessheka tace
"Tawakaltu Lukman"
"Wace yare ce ke?"
"Yoruba" ta amsa mata Ahankali,
"Koma ki zauna muyi wata magana" tawa kara girgiza mata kai tayi,
"Bari insa akawo maki abinci kafin muyi magana" tawa still girgiza kai tayi, Umma tsaya kallon ta tayi sai taga sam yarinyan ba irin yarinya marasa jin maganan nan bane...cikin zuciyanta sai tafara nadama daukota dayawa akayi,
"You can't let your only son marry Yoruba" wata zuciya ta fada mata,
"Kinsan Salem Yusuf sulaiman?" Umma ta tambayeta, Ahankali tawa ta gyada mata kai
"Meke tsakanin Ku?" Ta sake tambayan ta, shuru tawa tayi bata ce komaiba, Umma tacigaba dacewa
"Nice mahaifiyan Salem...kuma banason ki dauka cewa don inci maki mutunci yasa nasa adauko Mani ke...me kikeyi gidan ?" Gaban tawa faduwa ya farayi,still bata ce komaiba
"Zina kukeyi?" Da sauri tawa ta girgiza mata kai sabon hawaye na zubo mata,
"Then me ya mace kamanki takeyi gidan namiji mara aure?.." Tawa bata ce komaiba sai goge hawayenta take, Ahankali Umma tacigaba dacewa
" anyway.. Kome ke tsakanin Ku inason ta tsinke from this moment... Badan baki yimin ba..Aa..saidon aladan mu da naku ba daya bane ...but if you want...you can name your price... From 1m to 20m zan iya baki indai kin yimin alkawarin zaki rabu da Salem" tawa girgiza kanta tayi tafara cewa
"Please I don't want anything.. I want to go to my mami...kuma bazan kara kula Salem ba" tafada cikin muryan ta Mara fita, Umma duk sai taji haushin kanta
"Please kar ki kirani da muguwar mace...am just a woman that loves her son.." Ahankali tawa tace
"You are not ma..." Umma Dan murmushi tayi, tawa kuma goge hawayenta tayi,
"Yanzu ina baki shawaran kar ki Kara zuwa gidan saurayi..baa haka a aladanmu" Umma ta fada mata, Ahankali tawa tace
"First love wallahi bansan gidanshi bane..." Umma dadin sunan taji.. Don babu mai kiranta hakasai Salem
"Hope babu abinda yayi maki" da sauri tawa ta girgiza mata kai
"Ki gayamin in yayi maki wani abu.. Am he's mother..I know how to deal with him"
"Baiyi min komaiba "
"That's good to hear..hope baki ji haushin abinda na fada maki ba?"
"No ma" ta amsa mata Ahankali
"Tashi daga kneeling kici abinci sai insa a maida ki gida" bata tashi daga kan gwuiwowinta tace
"Thanks ma..na koshi"
"To shikenan.. Yanzu are we friends?" Da sauri tawa ta daga mata kai
"Then ki bani number ki..sai mu dinga gaisawa time to time" Ahankali tawa taba labarin yanda guys din suka yarda mata waya, mikewa Umma tayi ta shiga bedroom dinta, baa dadeba ta fito dauke da wani waya gionee m6 amma ba sabuwa ba, sai wata Leda mai dauke da kudi, tana zuwa ta mika mata wayan, kememe tawa taki mika hannu
"Ikon Allah.. Ki amsa mana" girgiza kai tayi
"To..kina fushi kan maganan danayi maki kenan"
"Aa..nagode" ledan ta mikewa tawa
"Gashi ki sayi duk abinda kike so.." Shima tawa girgiza mata kai tayi
"Gaskiya we are not friends.. Ya zaayi kiyi refusing dina..to amsa" ta kara mika mata wayan, Ahankali tawa ta amsa
"Thanks ma" Umma kara miko mata kudin tayi amma taki amsa, duk magiyan da Umma tayi bata amshi kudin ba
"Shikenan.. Amma ki huta zuwa yanma sai a tafi dake gida" kanta kasa tace
"Zan tafi yanzu"
"To shikenan.. Bari insa driver na ya maidaki gida" girgiza mata kai tayi
"Kawai su kaini park" Umma sawa tayi aka dauketa tana tunanin anya ta kyauta abinda tayi..don yarinyan ta kwanta mata
"She's Yoruba" tafada cikin ranta.
Tawa mancewa tayi bata dauki bag dinta daga cikin motan guys din da suka kawotaba, wani hummer ya kaita park. Kuka kawai take in ta tuna daga yanzu babu ita ba Salem.ji take kaman yau yafi kowane rana bakin ciki da muni a rayuwanta,.Ana sauketa ta duba taga babu bag dinta, wani shagon da ake saida waya ta shiga ta mika masu wayan da Umma ta bata, abanza suka sai wayan a 18k, bata tsaya ciniki dasuba ta amshi kudin, cikin shagon ta amshi wayan ta kira mami tayi mata karya cewa motan su ta lalace sannan kuma an dauke mata waya a park.
Cikin park ta shiga ta hau motan Ilorin , duk Wanda ya ganta yasan bata cikin hayyacinta.

๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค๐Ÿ’š

Tun cikin kauye ake tambayan hinde abinda ya faru cos kuka take kaman anyi mata albishir da jahannama, bata cewa kowa kala ba ta isa gidan ameera, da kuka ta iso Wanda hakan yayi sanadiyan mikewa ameera dake kudundune cikin zaninta,
"Wayyo sun kashe ni " tafada tana kuka
"Inna meyasameki?" Yarta ta tambayeta, hinde zama tayi nan kasa
"Zinarin da ameera ta bani aka amshe../" bata idaba ameera dake tsaye bakin kofa ta saki ashar
"Wallahi kinyi kadan...kawai ki kawo min zinari na..don wallahi sai ya sayi dukkanku.." Tafada tana rike kugunta
"Wallahi Aisha..wasune suka amshe..."
"Tell that to the birds..sai kin biyani kayana...kawai daga nace Dan saki da ku shine zaki cuceni?.. Aikam ban yarda sai kin biyani..." Hinde bata ce komai ba tacigaba da kuka
"Ki fidomin kayana..barauniya..." Gaskiya ki bar zaganmin uwar..." Inji diyar hinde, tafa hannu ameera tayi sannan ta nuna diyar
"Look at this creepy zombie.. Har kin isa kiyi magana inda nake magana?..ki gayawa barauniyan nan ta bani kayana..in ba hakaba in na fita daga gidan nan...sai na kulle duk zuriyanku..banza karamar bazawara..." Yarinya tsaka taja ta mikar da uwarta, aikam da sauri ameera ta karasa inda suke ta rike hinde da hannu daya sannan ta mika mata dayan hannunta
"Yanzu mikomin zinari na..." Bata karasa ba aka bude gate majed yashigo, ko kallonshi batayiba tacigaba da girgiza hinde tana cewa
"Ki bani yanzu ba sai gobe ba..." hinde sai kuka take ita kuma banzan diyarta sai kokarin kwace hinde take,
"Meke faruwa nan?" Majed ya tambayesu, cikin kuka hinde ta gaya mashi, ameera kam ko kallo bai isheta ba ,nace ko kin mance abinda ya taba yi maki
"Dalla malama ki saketa..."
"Ka biyamin zinari na mana..."
"Baki sakinta?..." Yafada yana karasowa inda suke, ameera na ganin ya karaso wajen su tayi saurin sakin hinde, Hinde najinta free ta bar gidan da gudu diyarta ta bi bayanta, ameera nuna majed tayi da dan yatsa
"Ban manta abinda ka yimin ba..kuma when the time is right zan rama..."" Tsaki ya ja zai shiga ciki ya dauki abinda akace ya dauko wayanshi yafara ringing, nan Abdul ke fada mashi tawa ta gudu, da sauri majed yaje ya dauki CCTV recorder ya kara gaba.

๐Ÿ’™๐Ÿ’œโค๐Ÿ’›๐Ÿ’š

Salem ya dawo abuja duk Ahankali shi tace, baisan ta inda zai fara Neman ta ba...baisan wane garin Yoruba zai fara zuwa ba, kaman ya hadiye zuciya ya mutu yakeji don zuciyanshi baki wulik take, yana sauka daga jet ya nufi inda ya sauke ameera, dakunan yadinga dubawa daya bayan daya kilan Allah yasa ya ganta ciki, amma nothing. Gaban wani kujera ya zauna ya hada kai da gwaiwa, gani yake in zai ganta yanzu babu abinda zai hanashi cin uwarta for playing with his heart
"Tawa..you can't run from me...Nigeria is too small for you to run.. Wallahi sonki bazai hanani maganinki ba..." Ya fadawa kanshi.

Around 2pm su Abdul suka dawo amma babu courage din da zasu shiga ciki, tsakar gidan Salem ya fito yana kale2, ajiyan zuciya kawai yake, baisan ana guduwa daga mutum don yawan arzikin shi ba. Tun safe baisha ko ruwaba, tap da bawa flowaer ruwa yaje yayi alwallah sannan ta ya fita waje don zuwa masjid, nan yaga su Abdul tsaye waje, ko kallonsu bai yiba ya wuce su, kan hanyan da zaibi ya hangi wani abu kaman waya tarwase a kasa, Ahankali ya karasa wajen, yana zuwa ya tsaya yana kallon wayan, nan take yaga kaman wayan tawa, Dan dukawa yayi ya dauki wayan yaga confirm wayan tawa ne, juyawa yayi yaga CCTV na kallon wurin, daukan sim card din yayi ya saka cikin aljihunshi ya kara gaba.

Yana dawowa yaje dakin da wasu mutane uku ke duba mai shiga da fita suke, yana shiga CCTV monitor takwas nagani, yana shiga yace
"I want to see what happened since in the morning"
โค๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’œโค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’š

ยฎzuwairat (ummu maryam)

3โƒฃ8โƒฃ


Kan daya daga cikin kujeran wajen Salem ya zauna, fara maido recording din baya sukayi, Salem kurawa monitor din ido yayi, ana zuwa inda tawa ta fita, da farko ya saidasu, fara playing dinta akayi, har inda gate ya wulla ta saida ya gani, idanuwanshi cikowa yayi da kwalla, kallon su yayi
"Kuna ina wannan lokacin?" Ya tambayesu
"Sir muna masjid cos 5:20am ne" daya ya amsa mashi, cigaba da playing yayi har inda tawa ta fita tana kallon gidan tana goge hawaye, kan Wanda ke waje ya maida kanshi , nan yaga sannan wasu suka saida tawa..da sauri Salem ya mike tsaye, gani yayi suna yi mata magana kuma the next minute suka fara nuna mata bindiga, hannu Salem ya dora bisa kai, yana kallo suka tafi daita.. Komawa yayi kasa ya fashe da kuka kaman Dan yaro, don gani yake tamkar an kashe ta, dayan daga cikin guys din yadan dafa mashi kafada, da karfi Salem ya tureshi sannan ya mike tsaye,
"Kuna ina sanda aka dauketa!" Yafada da karfi, dukkan su shuru sukayi suna kallon juna
"I said kuna ina!?..." Still shuru sukayi.. Ahankali Salem ya fara cewa
"What have I done to deserve this From you guys... Na baku free food.. Free shelter...the best cloth...and you can't do your job...saboda in wani ya gaji ya huta sai wani ya hau aiki, shiyasa na dauki Ku uku aiki..amma hakan bai da amfani... Nasan you guys are incompetent.. All of you are fired!!!" Ya fada sannan ya fice daga dakin yana kuka...yasan in ba Umma ba babu wacce zatasan yana abj balle ayi kidnapping tawa..
"Umma..why..." Kuka ne yaci karfinshi, kasa ya zauna gaban jet yana kuka kaman yaro, pilot ne yazo ya dinga rarrashin shi, saida yayi mai isanshi sannan ya mike ya kalli pilot din
"Call me those fools outside" yafada cikin husky voice, da sauri pilot ya kirawo su Abdul, cikin jet ya shiga da sauri su Abdul suka yi parking motan su suka shiga cikin jet sannan pilot ya kalleshi
"Sir ina zamu?"
"Yola" yafada yana kafa speck a fuskanshi.

Around 3:45pm suka isa yola, personal house dinshi suka sauka sannan suka dau motan sukayi family home, agaban masjid dake gidansu sukayi sallah sannan Salem yayi trekking zuwa gidansu, yana daf da shiga gidan yadan juya aikam sai ya hangi bag din tawa cikin flowers din kofan gidansu, da sauri ya karasa wurin ya dauki bag din ya bude gani yayi har kudinta na cikin bag din...wani sabon kuka yafarayi
"What did Umma do to you...you caused it..why do you have to run from me?.....is it a crime to love you?..." Kan ya dora da bangon gate dinsu yana kuka, yafi minti goma wurin sannan ya shiga ciki. Already guards suna jiranshi, yana zuwa yav kalle su
"Don't let anybody into this falo..except Abba.. Kun gane?" Yafada yana nuna masu side din Umma
"Yes sir" suka amsa mashi sannan yashiga ciki.

Afalo ya tardata tana zaune ita kadai tayi tagumi, ko tunanin me take? Oho. Takalmin kafanshi ya cire, ya karasa inda take, kwantawa yayi kasa flat tare da rike kafan Umma, sai lokacin Umma tasan da mutum cikin falon, kuka sosai Salem ya farayi
"Umma na rokeki da sunan Allah.. Ki bani yar mutane in maida masu..." Umma kallon mamaki tafara yi mashi
"Kai ..kana haukane?.." Kai ya fara daga mata
"Umma am mad in love with tawa..kin dauketa..please tell me where she is..." Umma kokarin kwace kafanta tayi amma Salem yakara rike ankle dinta kaman his life depends on it..
"Umma please tell me inda kika kai tawa...nasan baki sonta amma bansan you can go this length ba..." Kuka ya dingayi har da shessheka.. Umma tsaya kallon ikon rabbi tayi..
"Son..please free my leg.." Girgiza kai yayi
"No Umma.. Na rokeki..kifadamim inda kika kai Tawakaltu.. Menayi?..meye laifina?..is it my fault that I feel in love with the wrong person?... Ba laifi na bane...bani na sa zuciya ta ta kamu da son wacce baki soba... Umma please tell me inda kika sa aka kai taw..." Kuka yaci karfinshi , yana kuka yana

Please Login or Register in order to submit comment