Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabawa diyar hinde dubu 60 tace ta sayo small plasma TV Sai startime.
Ita da ta tafi tun 8am bata dawoba Sai 11:30am. Tana shigowa duka suka dauki tsalle banda ameera dake kallon yanda suke jin dadi, kuma jindadinsu na sata farin ciki ba kadanba.
Da kyar ta roki masu gadi sukayi masu fixging don saida suka amshi 5k hannun ta Sannan.
Suna fara kallon ameera ta saki ajiyan zuciya don yanda hinde da yaranta suke shewa, yanzu ji take tamkar suna na wani alaka. Lokacin zuhr nayi ta kalli babban diyar hinde
"muje muyi alwallah.." Mikewa tayi amma badan ta soba don tashar dadin kowa suke kallo. Suna fita waje ta suna ruwa cikin kettle biyu ta dauki daya ta mikawa ameera daya, Tsugunnawa tayi tafara alwallah, kusa daita ameera ta dawo Sannan ta fara cewa
"Yar uwa har yanzu baki fadamin abinda ya taba auren ki da mijinki ba..." Diyar hinde ta ajiye butanta Sannan ta kalli ameera
"Wallahi ba komai bane illa bai daga kafa..." Sam ameera bata gane inda ta dosaba, dan dariya tayi sannan tace
"Ban ganeba?... Bai daga kafa kiyi me?" Shuru tayi ta sunkuyar da kanta kasa don kunya takeji tayi mata dalla2
"Ki fadamin mana.." Ameera ta tambayeta, shuru tayi kaman bazatace komai ba Sannan tace
"Bai Bari na hutawa...kullum cikin auratayya muke..." Dan kallon tuhuma ameera tayi mata
"Aurat...oho..." Ta fada da Dan karfi don Sai lokacin ta gane inda ta dosa, Dan dariyan rainin hankali tayi tana cewa
"Don wannan Sai ki rabu da mijin ki?.." Ido diyar hinde ta kwalo tana kallon ta
"Haka kikace?..hmmm..kiyi adua Allah ya rabaki Dana mijin da baya daga kafa... Basu da tausayi..." Har lokacin ameera bata bar dariya ba, cewa tayi
"Amma ina ganin wannan bai isa yasaki rabuwa da mijinki ba..saidai in baki sonshi..." Dan baki diyar hinde ta tabe Sannan tace
"Wasa ki ganin abun...misali kina Iya zama da mijin da kullum babu ranar banza?...Sannan ko da rana wani lokacin bukata yake...sau hudu ina bari..har hakuri likita ya bashi yadan dinga ragamin...amma baiyiba..." Shuru ameera tayi tana cewa
"This is serious..."
"Kedai kiyi adua Allah yabaki namijin da bashi da jaraba..." Ameera batace komaiba ta don ita tunani take me zatayi da 1 minute man, she need a hard guy, cikin zolaya tace
"Kilan flowern ki nayi mashi sugar.. Shiyasa yakasa daga maki kafa..."
"Kedai raba kanki da jarababben namiji"

Tawa na tashi Matan ta maidata bayan tayi sallan subhi, for the first time ta kara bacci cos ta saba da aiki bayan sallah asuba. Haj kitchen ta shiga ta hada mata nice ugwu soup Sai Sai hot tea. Tana farkawa ta shiga wanka cos already ta hada mata ruwan wanka. Kan gado ta tadda wani mini skirt da shimi, daga skirt din tayi taga in ta saka bata Iya bending cos pant dinta zai bayyana. Badan ta so ba ta dauka ta saka ta fito tana tafiya tana rangwada kaman Salem din na zaune. Kan dinning ta zauna tayi breakfast da miyan ugwu da tea. Saida ta gama Haj kudirat ta kalleta
"Now give me that sexy look and smile.." Tawa mikewa tayi ta fara tafiya kaman wata model Sannan ta zauna tana yiwa kudirat wani irin shuumin murmushi kaman yanda ta koya mata,
"Excellent..now yau zamuyi rawa" tawa kallon ta tayi tana tunanin
"Here comes the problem.." Tafada cikin ranta
"As a woman.. Ba Sai lokaci wedding ko wani shagali zakiyi rawa ba, turawa sunawa hubby dinsu pole dancing amma tunda mu bamu da pole Sai muyi lap dance...Yakama a matsiyin ki na yarinyan dazatayi aure ta koyi sexy dance steps da zakayiwa hubby.. Lap dance shine kiyi rawa kina Dan shaking jikin ki Sannan ki zauna kan laps din hubby ki..make sure kinyi sexy dress kaman yanda kikayi yanzu Sannan make sure you don't break eye contact with him..." Tawa dai jinta kawai take don tasan da akwai matsala.
"The most shameful thing shine na miji yaga nakedness dinki..so the moment haka ya faru tsakanin ki da mijinki then babu sauran kunya..so zaki fidda kunya..." Ta fada tana kunna wakan Beyonce cikin MP3 dake kan dinning. Wakan am a diva ya fara tashi, mikewa Haj tayi ta umarce tawa da ta juyo da kujeran dinning ta kalleta, ahankali ta fara rawa tana Dan juya jikin ta ahankali tana shafa jikin ta da kaman tana shafa kwai, Sai girgiza jikinta take tana Dan bin wakan Ahankali, duk abinda take eye balls dinta cikin na tawa, itakam tawa baki ta bude tana kallon ikon Allah
"Close your mouth.. I know am incredible.." Tafada tana karasowa wajen tawa, Sai lokacin tawa tasan bakinta bude take . tana zuwa wurin tawa ta bude kafanta ta Dan zauna kan cinyan ta tana kada hips dinta, Dan dukawa tayi boobs dinta na shafa fuskan tawa. Duk abubuwa da take idanuwanta cikin na tawa. Mikewa tayi sannan tace
"Your turn.." Tafada tana zama. Ahankali tawa ta girgiza kanta
"Ma'am.. I can't.."
"No...babu word impossible.. Saidai I'm possible.. So stand up and give it a try.. Banason gardama.." Tafada tana maida wakan farko. Jiki ba kwari ta mike tafara takawa amma duk step din da zatayi Sai ta kushe ta, sunfi hour biyu suna Abu daya amma still she's not getting it right, Idayat ta shigo da ATM da Salem ya aiko dashi, dariya tayi dataga yanda tawa ke rawa.
"Kina da aiki.." Ta fada tana mikawa Haj ATM din ta fita.
"Yanzu zanshiga Dubai market in sayo maki abubuwan da zaki bukata.. Kiyi ta practicing kafin in dawo.." Ta fada mata sannan ta fita, tawa zama tayi ta rafka uban tagumi.
Sai lokacin tawa ta tuna da wayanta, da sauri ta dauko nan ta cikaro da miss calls din Salem har dana Daren jiya, nan take tayi calling dinshi.

Sai bayan zuhr Haj tadawo da uban kaya kala2, perfumes kaman a shop ga Arabian Sannan American, ga expensive cosmetic Sai mayukan shafa complete set daga company dass.

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œ
Pls kuyi hakuri, commitment ne sukayi min yawa, so har yanzu zaku dinga kina shuru so zaku Dan ji ni quite for a while, hope you will bear with me...thanks๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’›โค๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat(ummu Maryam)

5โƒฃ5โƒฃ

Tafi kwana uku tana practicing rawa kafin ta iya, acikin kwana ukun kullum Haj kudirat Sai tayi mata spa treatment, Sannan ga special gyaran gashi banda wankan turaren da takeyi mata kuma tana bata abinci mai rai da lafiya tana ci, kullum cikin waya suke da Salem

A week later Salem ya shigo kwara for the pre wedding pics, adakin baki aka saukeshi, abinci mai kyau kala2 aka jera mashi, yaci ya koshi amma kawai idanuwanshi a hanya ko zai ga Tawakaltu, har lokacin zuhr bai ganta ba.
Abangaren tawa kam jet din Salem na landing taso tarenshi amma Haj ta hana ta, wai dole shi zaizo gareta that it is called dignity.
Kwalliya ta sansara mata ta zauna kaman wata sarauniya tana jiran zuwanshi.
Shikuma Salem yana dawowa daga masjid ya rasa sukuni, wayanshi ya dauka yayi dailing number ta, ringing yafara daga chan bangaren tawa ta dauka tare dacewa
"Hello sugar..." Tafada ahankali kaman yanda Haj ta umarceta, Salem daga wayan yayi daga kunnenshi ya kalleta Sannan ya maida wayan kunnenshi
"Habibty.. What did you call me?.." Ya tambayeta, cikin sanyin murya takara cewa
"Sugar.." Dariya Salem yayi yana biting bottom lip dinshi
"Habibty.. You sound naughty..."
"Meye naughy kuma?..." Ta tafada kaman wacce tayi aiki ta gaji, Salem shuru yayi yana lumshe idanuwa don yanda muryanta ke shiga har cikin ranshi.
"Habibty.. Kusan hour uku ina cikin palace amma you don't seem to want to see me..." Dan murmushi tayi
"Am a little bit busy ne...amma kana Iya zuwa ganina yanzu.." Dariya Salem yayi
"Habibty are serious?... I fly all the way to see you... Kuma bazaki Iya zuwa ganina ba?... Its not fair..."
"Sorry sugar...but please come to me..." Salem ji yayi kafafunshi na sayi don yanda take magana
"Habibty.. Who is corrupting you?.. Who ever..thank the person.. Cos am loving it.." Yafada cikin whisper, tawa Dan dariya tayi, Salem yacigaba dacewa
"Now my princess.. Gayamin inda kike cos I can't wait to lay my eyes on you" ahankali tawa ta fada mashi inda take, bai bhata lokaci ba ya katse wayan Sannan ya fito ya nufi discription din data bashi, palace din babu hayaniya haka yabashi daman zuwa bakin kofan data kwatanta mashi yayi knocking, Haj kudirat ta bude, gaisawa sukayi Sannan tace
"Daman inason ganinka.." Salem na dan waige2 yace
"OK...am here.." Nan Haj kudirat ta fada mashi da akwai Dan abubuwan daya kamata yasani game da traditions dinsu Sannan ta fada mashi da akwai training dasuyi da tawa, duk bayanin da takeyi sam baijinta Sai neman ta inda tawa zata bullo yake,
"Kayi shuru.." Ta fada mashi, da sauri yace
"Is OK ma'am..." Dan girgiza kanta tayi sannan ta shiga tayiwa tawa magana, fitowa tayi ta shiga bedroom dinta.
Tawa kama tana jira ta saka Vail din jallabiya dake jikin ta bude kofa tafito, gaban ta Sai faduwa take, Salem na ganin ta ya kwalo idanuwa cos ko kadan bai ganeta, ahankali ta karaso wurin shi tana girgiza ta durkusa ta gaidashi, kasa amsawa yayi Sai kura mata ido kawai yayi, ahankali ta daga kanta ta kalleshi tana yi mashi murmushi, muryan shi na rawa yace
"Habibty kece?... " cikin zolaya tace
"Yes of course..." Tafada tana zama gaban shi anan kasa.
"You are my own rihanna" dariya kawai tayi
"Bari in kawo maka abun sha..." San bata fuska yayi
"Just sit let me watch you" ya umarceta,irin zaman da aka koya mata tayi Salem banda kallon ta babu abinda yake, kallon kafanta yayi yaga sunyi sumul
"Hmmm.." Kawai yace under his breath, kallon shi tayi eye balls to eye balls Sannan tace
"Meye..." Yanda take magana tamkar ba yarinyan daya ganin last few months tana saida abinci gefen hanyaba
"Don't underestimate people.." Ya fada cikin ranshi
"I missed you..." Ya fada cikin whisper kara dacewa
"I can't wait for the next 4 weeks..." Gaban tawa Dan faduwa yayi amma sai ta sakar mashi wani shuumin murmushi, Dan dukar da kanshi yayi kusa daita
"Princess.. Are you flirting with me?..." Dan kallon shi tayi ya kashe mata ido daya, Dan kauda kanta tayi
"Yasu first love da Abba?"
"Suna lafiya.."
"Habibty.. Me kike ci?.. You look ravishing..."
"Thank you.."
"Princess..." Ya kirata sounding so lustrous
"Naam.." Ta amsa batare data kalleshi ba
"Me kika kirani dazun?..." Dasauri ta rufe fuskanta kaman wata mai jin kunya
"Am waiting.. Call me that in front of me..." Ya kara fada mata, fuskanta rufe tace
"My...sugar..." Salem Dan dariya yayi
"Habibty.. Wait until you have tasted me..." Tawa Dan turo baki tayi
"Zaka farako?..."
"Kedai kika fara..." Dan hira suka cigaba dayi, kaman an chunkuleta tace
"Baby...da akwai abinda ban Sani game da kaiba?.." Salem tsaya kallon yanda take fidda magana kaman bataso yayi for a moment Sannan yace
"Why are asking love?.." Ahankali tace
"naji ana cewa da kyar mutum yasan 10 to 30% na halin maza..ni kuma am thinking I know you..." Kura mata ido yayi yana tunanin abinda tace, shidai yasan bashi da wani secret saidai case dinshi da Aisha, kuma yana ganin ko ta Sani nan gaba bazai zama case ba
"Honey kayi shuru.. Ko da akwai abinda ya kamata in Sani..." Tafada tana kama mashi hannu, da sauri ya dawo hayyacin shi, rike hannun ta yayi da two hands dinshi, kaman ya fada mata gaskiyan abinda ke faruwa yayi kuma ya fada mata ko yau yana iya sakinta kuma ya tabbatar mata bai taba komai da itaba amma this moment is precious, he don't want to ruin it, kallon eye balls dinta data maida kaman na maijin bacci yayi Sannan ya saki murmushi
"Habibty.. Bani da secret.. You know komai about me...sai dai ina Abu guda daya..." Da sauri ta zaro idanuwa Sannan tace
"Please what?.." Tafada gaban ta na Dan faduwa don, yatsan shi yasa yafara shafa tafin hannun in a circular form Sannan yace
"I think I can last 4 to 5 hours in bed.. " zare hannun ta tayi tadan kauda kanta gefe tana Dan murmushi,
"I don't want you to be surprise.. So prepare well for me..." Tawa shuru tayi don tasan karyake, amma cikin ranta tasan yana hiding wani secret,
"Hmmm...I just want to know everything about you... Banason Sai bayan aure in gane wani Abu Mara kyau game da kai..."
"Haba habibty saikace ina yankan kanu?... To tell me abinda kike gani zai tada maki hankali.."
"Nidai I don't know.. Amma am telling you..it won't be okay..." Sai kuma tayi shuru don tasan irin tempern ta..tasan she's respective amma she don't take bullshit
"Habibty relax.." Yafada in reassuring tune don yasan zai saki ameera batare datasan anyiba.
"Habibty.. Wacce zatayi planning traditional wedding zata zo nan around 5pm yau...zata kawo pictures Sai ki zabi irin kayan da kike bukata" Dan turo baki tayi
"Is it necessary?.. Kawai duk abinda ka zaba is OK by me..." Dan bakinta ya rike
"No...just choose.. Kinsan its your time.. Inason komai yazama yanda kike so..." Dan rike hannun shi tayi daga bakinta
"OK.." Hannun ta ya cigaba da murzawa kaman yana shafa kwai
"An kawo kayan da ladies zasu saka?.." Ya tambayeta
"Eh..naji su dija nata kiran friends dinsu suzo su amshi ashobi..kasan ni bani da friends" Dan dariya yayi
"Daman banason mata mai tarin kawaye..suna leading ko misleading mutum..amma akano baki da friend ko daya..." Shuru tayi kaman tana tunani
"Sai guda daya itama wurin aiki muke haduwa..mami bata yarda inje gidansu..."
"Sai ki bada address dinta a tura mata invitation.."
"OK..." Shuru yadan biyo baya Sannan yace
"Habibty mu shiga cikin gari mana?..." Ido ta kwalo
"Bansan koina ba..besides wannan Matan bata barina fita ko ina.."
"No..problem...da karfe nawa zaayi pics din?" Ya tambayeta har lokacin hannun ta cikin nashi
"Wai dole ne?.."
"Yes love... I want to show you to the world.. I want people to know some delay is a blessings.." Daga kai tayi takara sakar mashi wani lustful smile
"This smile is killing me.." Yafada kasan makoshinshi, wani takara sakar mashi Sannan ta mike
"Where to.." Ya tambayeta yana lumshe idanuwa
"Ruwa zan kawo maka...maganan da mukayi yanzu ya isa ya saka jin dry throat.." Dan Jan hannun ta yayi ta kusa fadawa kanshi, da sauri ta zari hannun ta ta taka cikin kasaita ta duka ta bude fridge, Salem gyara zama yayi yana kallon yanda take tafiya komai nata na shaking, juice ta dauko ta saka kan tray dake kan fridge Sannan ta shiga kitchen ta dauko cup ta kawo mashi, tamkar mirror ya maidata don ko blinking baiyi.

Around six sukaje Emirates garden sukayi pics, na farko suka English waer jean da t shirt agaban na Salem an rubuta her prince, agaban nata an rubuta his princess, ta tsaya gabanshi ya saka hannun shi cikin aljihun wandonta suna kallon juna,ba karamin kyau sukayi ba.
Nabiyu sun saka kayan Fulani Salem ya rike sanda itakuma rike da kwarya nan ma ba karamin kyau sukayi ba, na uku ya saka shadda fari kal dinkin babban riga amma ba mai zurfi ba, na hudu ta saka gown blue Sai shi yasha blue suit Sai na karshe sun saka kayan Yoruba, Sai around 8 aka gama pics don duk chanzawa da zasuyi Sai an gyara mata fuska suna kan hanyan dawowa ta kalleshi
"Wai kai kayi hiring wayan nan mutanen dasuka dauke mu photo?" Dan girgiza mata kai yayi
"No.. Wani abokina ne...har kayan da muka saka da directors dinshi shi ya dau nauyi.."
"He's nice.." Murmushi kawai yayi Sannan ya kalli drive dake driving dinsu yace
"Take us to the best restaurant in town.."

Atakaice basu dawo gidaba Sai around 10pm har bakin kofan part da take ya rakata saida ya juya yaga babu kowa Sannan yayi saurin hugging dinta , kafin tayi wani Abu har ya hada bakinshi da naya, passionate kiss yayi mata sannan yace
"Good night...make sure you dream of me.."

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

Ameera kam count down kawai take, don har ranar auren Salem tasani kuma yanzu alhamdulillah ta fidda shi daga cikin ranta kawai gurinta kawai gida, yanzu suna shiri sosai da babban yar hinde zainabu don har hiran da bata taba yi da aminiyar zeenat ba tanayi da Zainabu don har yanzu bata fada mata gaskiya alamarin ba, kullum cikin kallon film suke wani lokacin har yar gala2 suke, yanzu ameera ba rabuwa da Salem ne matsalan taba Sai rabuwa da hinde da mutane ta don har cikin jininta take jinsu, adua take Allah ya bata ikon kula dasu in ta bar gidan, kuma har Allah 2 take ta koma gida don ta nemi yafiyan mutanen data zalunta especially masu yimasu aiki. Tasan Salem yashiga hakkinta amma she can't give him all the blame,
"Ni abinda ke daure min kai shine dalilin dayasa yaki sallama ta tunda ya sami Matan aure.." Tafadawa Zainabu da ke zaune kusa daita tana wanke2 itakuma tana dauraya
"Hmmm..wayasani...kilan so yake ya barki Ku zauna tare.." Bata idaba ameera ta ja tsaki
"Wa zai hada miji da mayu?... Ai ko yace in zauna dashi bazan zauna..kawai Allah ya hadani da mai sona...."
"Yarinyan dazai aura mayyace?"
"Yo yarbawa ai masafane...ko a lahira bana fatan Allah ya hadani ni dasu wani harka balle miji..."
"Hmmm da gaskiyanki..amma in da akwai rabo tsakanin Ku fa?"
โค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’›โค๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat(ummu Maryam)



5โƒฃ6โƒฃ


"Rabo!.. Tab Allah ya rabumu da mummunar kaddara..." Tafada tana Dan mikewa tsaye,
"Daman bakison shi..amma in kana son mutum duk yanda yake zaka zauna tare dashi.."
"Ni gaskiya ya fita raina.. Kinga ranar dana kirashi..zagi ya dingayi...gaskiya mutumin bashi da kirki..."
"Aike kika yarda damanki tun farko..." Ameera dai shuru tayi batace komaiba don tasan gaskiya Zainabu ta fada
"Amma kin San me?" Ahankali ameera ta girgiza mata kai
"Allah zsai saka maki..saboda ya wulakanta aure..kuma aure ba abun wasa bane..don haka nasan tabbas Allah bazai barshi hakaba..." Still ameera batace komaiba ta tsaya tana goge ruwan hannunta ga zanin dake jikin ta
"Allah yasa Matan taci mashi uwar..." Dariya ameera tafarayi tana cewa
"Kai na ji dadin wannan aduan.. Inama ina kusa inga yanda zatayi mashi..."
"Kikasan ikon Allah?... Kedai Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi.."
"Ameen.. Amma da kika ce banason shi..ke ba kinason mijinki ba amma kika rabu dashi saboda extra banana da yake baki?" Zainabu tattara plates din tayi tana cewa
"Inason shi mana.. Amma ban Iya zama dashi.." Dan shuumin murmushi ameera tayi kafin tace
"Amma tsakanin ki da Allah da akwai lokacin da kike jin dadin abinda yake yi maki.."
"Ina dadi kullum ana cikin fama maki ciwo.. Wallahi Sam babu dadi..." Ameera dariya tayi
"Ni shiyasa hankali na kwance don ina cikin Leda ta.." Dariya Zainabu tayi
"Ai kinji dadi..in wani na mijin ne bai kyaleki haka nan..." Tafada tana kai plates cikin kitchen, su hinde kam anachan an kurawa TV ido kaman her life depends on it.

๐Ÿ’›โค๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

Sai the following day Salem yabar kwara inda kudirat ta zauna dashi ta bashi advice sosai kan in take fada mashi ya fidda zancen sex gabanshi cos karamin abune cikin aure, alokacin da take bashi wannan shawaran cikin ranshi kam cewa yake
"Ashe?" Kamar kar su rabu da Tawakaltu don har kukan gulma tayi mashi. Salem kaman ya dawo kwara da zama har agama wedding din yakeji don wani irin sonta da kaunarta ke ratsa shi. Alokacin ya Riga ya baza pics dinsu a social media.

Yana cikin jet kan hanyan shi na dawowa Khalid ya kirashi yana picking yaji yana cewa
"Nima wallahi Sai ka samomin irin wannan a gidansu..." Dariya Salem yayi
"To ni wani ya samomin?..."
"To nima zanje taxi driving.." Yafada yana dariya
"Allah ya hadaka da irin wannan shaidaniyan yarinyan ta gurguri buroubanka..." Yafada yana dariya, Khalid ma dariya yayi
"Na ma mance da ita...ka rabu daita?"
"Aa..."
"What are you waiting for..."
"Time.. So nake insa akai mata wedding video dina ta kalla taga abinda tayi missing..."
"Ka kyaleta haka nan... Komai ya wuce.. Haba"
"Ai komai ya wuce.. Da ban yafe mataba zan bata enough money for her up keep?.. Kawai dai.." Da sauri Khalid yace
"Kodai ka fara sonta..."
"No way...am in love already.. No free space a zuciyata..ni kama tuna min in nayi aure da maganan sakinta cos ina Iya mancewa saboda abubuwa..."
"Da gaske dai sakinta zakayi...ni kama bani takardar sakin in kai mata ko Allah yasa tayi min Sai in aureta cos the devil you know is better than the angel you don't know..." Dariya Salem yayi
"Ai yarinyan tayi...she's beyond beautiful amma she's nothing compared to my baby.." Shima Khalid dariya yayi
"Gaskiya ai your madam karshe ce..." Ahankali Salem yace
"In fada maka gaskiya wannan shekiyar yarinyan tafita kyau.. Kaman aljana take don kyau amma Sam bata da kyau hali..." Ihu Khalid yayi Sannan yace
"Guy...tayi min kawai... Kawai ka saketa yanzu....please kasan I always have something for beautiful ladies..." Dariya Salem ya karayi
"Wannan balarabiyar fa?...ko ka fasa..."
"Manta da wannan.. Kawai ka saketa yanzu..."
"Nayi alkawarin Sai nayi aure zan saketa...kuma am a man of my word" Shuru yadan biyo baya kafin Salem yace
"Har yanzu bansan irin party da zaayi ba..." Shuumin dariya Khalid yayi farayi Sannan yace
"Zan hada mana cool party har da bikini party zaayi..." Dariya sosai Salem ya dingayi har da rike ciki
"Su waye zasu saka bikini?.." Ya tambayeshi yana dariya
"Ladies.. Har da matanka..." Yanda yayi maganan yasa Salem kara fashewa da dariya
"Amma baka da hankali..."
Kunji min Dan iska...bakasan ana bikini party ba?...kawai ayi bikini party a Lagos beach Sai kuwuce... "
"Duk iskanci na ai ban kaikaba...tunda ni har yanzu ina cikin Leda..." Dariya raina hankali Khalid yakarayi
"Weirdo...Virginia..virgin at 37...nima virgin ne..." Shima Salem daria ya dingayi yana cewa
"Dalla get out of my phone" yafada yana girgiza kai Sannan ya kashe wayan shi yana dariya.

Bangaren su Abba komai yayi ready, sun sayi kayan list din a aka basu kuma komai saida suka linkashi.
Ana sauran sati biyu traditional wedding Umma da su ilham da shuwa da yanuwan Umma Sai tareda kawayenta uku sukaje kwara, wani irinhospitality suka bawa su Umma, su shuwa kam kaman su maida Tawakaltu ciki saboda yanda suka nuna so da kauna kanta, tasha kyautan kayan mussanman wajen shuwa, don katon bag ta bata cike da perfumes da kayan shafa, Umma hakuri tabawa Tawakaltu kan maganan data fada mata kuma ta nuna just n dadinta da son gaskiya da Tawakaltu ta nunawa Salem dukda batasan koshi WAYE ba
"He tells me everything" tafada sannan tayi bata alkawarin bazata samu matsala a gidan Salem ba muddin ta zama mai biyayya, Sai a wannan lokacin mami ta Dan samu kwanciyan hankali amma har lokacin hankalin ta bai kwanta dukaba cos ta lura da irin kallon da ammi takewa Tawakaltu. Shuwa ido tayiwa tawa alaman mukebe, ahankali tawa ta mike ta bi bayanta tafada mata da akwai magani cikin kayan data kawo mata, ta dinga sha da madara. Bayan asar suka tashi tafiya kasancewan da jet din salem sukazo Yaran ilham cewa sukayi su abarsu wajen antyn uncle Salem.

Bakin jet su mami da mutanen gidan suka rakasu, ammi Dan matsawa tayi kusa da Tawakaltu Sannan ta kwantar da murya tace
"Munji Ku baayi maku kishiya ..to mu danmu Sai ya jera Matan nan hudu..babu gudu babu ja da baya don wannan yayiwa mace daya yawa..." Tafada yanda babu mai jinta Sai tawa, nan fa jikin tawa yayi sanyi.
Mami ta lura da tana fadawa tawa magana same with Umma saida suka hau jet Sannan Umma ta tambayeta abinda ta fadawa tawa maimaita mata abinda tace tayi, Umma batace komaiba Sai daya daga cikin friends din Umma tace
"Maganan ki gaskiya ce...don su basu yarda da akara masu kishiya...kaman ba musulumai ba" still Umma shuru tayi don har cikin ranta tanason danta ya auri cikakkan bafulatana. ilham kam cewa tayi
"Yanda bana fatan ayimin kishiya bazan yiwa ko wacce mace fatan kishiya ba...." Bata idaba ammi tace
"Wai Nafisa meyasa yaran ki basu rufe baki in manya suna magana?... Ko Dan Allah bai bakisuba da yawa yasa baki basu tarbiya ba?...to wallahi duk yar kutumar burouban data kara sakamin baki cikin magana Sai na cire mata hakora...mussanman ke mai kama da aljanu" tafada tana nuna shuwa da yatsa, Umma dai batace komaiba don abinda ke damunta daman. Shuwa kallon ilham tayi sannan tace
"Anty wallahi Matan yaya kaman rihanna..don tafi kyau a kasa kan cikin waya.." Daria ilham tayi don tsaki ammi ya hanata cewa kala cos cikin yaran Umma tafisu tsoro cos bata da rikici kaman Salem da shuwa.

Su tawa na komawa gida mami ta tambayeta abinda wannan Matan ta fada mata amma tace bakomai, duk juyin duniya taki fada mata, mami part

Please Login or Register in order to submit comment