Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata ™asar ba gwara na yi bara ba, Allah ya kiyaye."

Safeera ta ce, "Amin Islaha. bara na wuce, sai mun haWu gobe."

"Kamar kin san Chairman ya kira ni, wai yana so gobe na je da wuri zamu tattauna akan wata magana."

Ta yi ´ar dariya ta ce, "Chairman dai yana ciki, amma na san bashi da space, wajan Hamma Saheer ne."

Ta yi murmuahi ta ce, "gaskiya ne, bana iya kallon ko wanne namiji da fuskar soyayya sai Hammana, ina sonsa sosai Safeera."

Ta yi dariya ta ce, "ya cancanta ki so shi ai Bestie, ya yi miki komai a rayuwar nan."

Safeera ta mi™e ta ce, "sai mun haWu, don Allah ki samu ki shiga ciki."

Islaha ta ce, "To bestie, ki kwana lafiya." Daga haka suka yi sallama ta fita.

Wainar fulawar take son ci amma baza ta iya ba, sanyin ratsa ta yake yi, ga sauro da ya fara kawo mata hari. Duk da wajan akwai haske amma sauro ya dame ta sosai.

Ta mi™e ta ™arasa ™ofar sai ta tarar an kulle ™ofar,  ta Wan yi knocking aka yi mata banza, kuma tana jin motsinsu. Ajiyar zuciya ta yi ta zauna a wajan tana tunani kala-kala.


     "Islaha!"

Ya faWa yana ™arasowa wajan da sauri. Ta kalle sa, bata yi magana ba har ya ™araso. Ya bita da kallo ya ce, "me ki ke yi a wajan nan a zaune ga sanyi? In ki ka samu attack fa?."

Islaha ta karyar da kai, cikin shagwaSa ta ce, "Mama ce ta ce in fito."

Da mamaki ya ce, "ki fito kuma, to akan me?."
Ta girgiza masa kai alamun bata sani ba.

Ya Wan yi tsaki ya ™arasa yana buga ™ofar falon Mama amma aka ™i buWewa. Ya kira Maman a waya bata Wauka ba, ya kira ™annensa duk suka ™i Wauka. Ya dawo kusa da ita ya ce. "Taso."

Ta mi™ewa tsaye, ya ri™e mata pack Win ya ce, "mu je Wakina ki zauna, in wannan sanyin ya yi miki illa fa, mai lafiya ma ya cika balle ke?."

Islaha ta bi bayansa, a hankali dan gaskiya bata son sanyi, tana da wani irin ciwo kamar asthma, duk da Hamma ya ce asthma ce, dan alamominta gabaWaya ya bayyana a kanta, amma an je ayi test an ce babu. Hamma dai ya ce ™arya suke yi, asthma ce da ita.

Šaki ne babba mai Wauke da gado da komai na kayan gado, gashi a gyare babu tarkace sai takalmansa da laptop Win da yake aiki da ita.

Ya nuna mata gefen gadon ya ce, "ki zauna."

Ba musu ta zauna ya ce, "me zaki ci?."

Ta fara sosa kunnenta da sanyim ya shiga ta ce, "Zan ci wainar fulawa, Bestie ce ta kawo....." ta kasa faWa saboda atishawar da ta zo mata.

Saheer ya fusata, cikin faWa ya ce, "meyasa ba ki zo nan kin zauna ba za ki bari sanyi ya yi mili illa? Gashi nan har kin fara atishawa, kin manta kina da asthma ne?. Haba Islaha, meyasa baza ki faWa min ba?."

Cikin sanyin murya ta ce, "ka yi ha™uri. Kuma har yanzu ba a tabbatar asthma ba ce."

"Ni na tabbatar. ˜arya likitocin suke yi, duk wanda ya ga yadda ki ke yi ya san itace."

Ya sake yin tsaki ya ce, "ki ci wainar, zan fita na samo miki magani. Akwai ruwa a fridge ki Wauka ki sha. Akwai abinda ki ke so in kawo miki?." Ta girgiza kai alamun babu sannan ya fita.

Tashi ta yi ta buWe fridge ta Wauki ruwan da babu sanyi sosai. Ta dawo a hankali ta zauna ta fara cin wainar ta hankali a kwance.

Bayan ta gama ta wanke hannunta ta goge da tissue ta sha ruwa.

Tana zaune ta yi shiru sai ta ji wayarsa da ya bari tana ™ara, ta duba gefenta ta ganta ajjiye, sunan boss yana yawo a kai. Bata Wauka ba ta Wauke kai, ta saka hannu ta jawo bedside drawer ba tare da zata yi wani abun ba.

Har zata rufe sai ta sake buWewa ganin abinda yake ciki, ta saka hannu ta takadar tana kallo. Copy visa ne na mata da yawa, ta dinga bi tana karantawa wasu an tura su ™asar larabawa, wasu ta turawa. Amma ´an Saudia duk sun fi yawa.

Ta girgiza kai ta ce, "Hajiya Mama, ashe abin ya bun™asa haka."

A lokacin ya buWe ™ofar ya shigo, ta kalli ™ofar shima ya kalle ta, ya ™araso ya ce, "har kin gama ci?."

Ba tare sa ta mayar da abinda ta Wauko ta ce, "na gama."

Ya bata magani ya ce, "ki sha." Ba musu ta sha maganin, takardun suna cinyarta.

Ya kalli abinda ta ajjiye a jikinga ya ce, "kina kallon copy visa ne?."

Islaha ta ce, "uhum, kawai na gansu ne. Na ce ashe Mama har kai take bawa ajiya."

Ya yi murmushi ya ce, "Hajiya Mama kenan."

Ta yi murmushi ta ce, "Chairman ne ya kira ni dazu, wai gobe yana son ya yi magana dani."

Ya kalle ta ya ce, "wacce magana kenan?."

"Ban sani ba, amma na san baza ta wuce akan Rehaan Yola ba."

"Rehaan Yola da na sani, nake jin sunansa a gari?."

Ta Waga kai ta ce, "Shi fa, ya matsa yana so mu yi hira dashi a channel Winmu. Ya dame ni akan ni zan kai invitation card Winsa, ko ta ya zai amsa gayyararmu ma oho."

"Daman ba mail ku ke turawa guest Win ba?."

"Mail ne mana. Shi sau nawa ana yi masa mail? An yi ya fi a irga, bayan shi har wani Jafar ake yiwa duk a banza. Shine za a je a kai masa Iv."

Ya bita da kallo ya ce, "To Ray Win ya dawo Nigeria ne? Ba fa a nan yake rayuwa ba, ance a Uk ne ko Us ban sani ba."

Ta taSe baki ta ce, "waye ya sani? Tunda ka ji yace nazo maybe ya ji magana akan zuwan nasa. Yana son yin hira dashi, ni kuma nasan bazai amince ba."

Saheer ya yi murmushi ya ce, "ke kin san waye Ray kuwa? Daga ranar da ya je tv ku, ko ya gayyace ku ai kun gama Waukaka Islaha. Har yanzu bai taSa hira da wata channel a Nigeria ba, shiyasa ko wacce channel take marmarin ta fara hira dashi."

Cikin ko in kula ta ce, "Ni fa wallahi ban taSa ganin hotonsa ba, ko maganarsa na ji ana yi zan wuce bazan kalla ba. Ba wai dan ba™in ciki ko hassada ba, ni bai yi ba Hamma. Bana son mutumin da ya cika Waukaka da yawa, kuma yana banzatar da mutane. Kuma ance yana da abubuwan cigaban da in ya kawo Yola, zamu zama na farko a Nigeria da aka fara samu. Amma ya tare a ™asar turai."

Ya yi dariya ya ce, "ke waye ya faWa miki?."

Ta turo baki ta ce, "haka na ji an ce."

"Haka ki ka ji, dan haka baza ki Worar ba. Ban taSa ganinsa, ba amma ana faWa halayyarsa masu kyau. Kuma ya kawo babban asibitin da babu kamarsa a nigeria, kuma ga kasuwar zamanin da in ki ka shiga zaki ce a dubai ki ke. Ai mun je dake kin ga yadda take, zan Wauke ki mu je asibitin ki yi kallo."

"Ni fa ba wani burge ni yake yi ba, in na je ma bazan gani ba."

"A'a matar Hamma. Ki faWi gaskiya."

Ta yi dariya ta ce, "shiyasa ake so na kai masa  invintation da kaina. Tunda sun ce ina da sa a, ban taSa gayyatar wani ya yi denying ba. To ni kasan bana son raini ka sani, in ya yi min wula™anci wallahi ba ™yalesa zan yi ba. Ka san halina, bana Waukar raini. Tsaf zan yi tsalle na gaggaura masa mari."

"In ya saka aka zane masa ke babu ruwana."

"Ina da kai, zaka rama min."

"Gaskiya ne, babu mai taSa ki ya kwana lafiya."

Ta yi dariya. Saheer ya ce, "Ba dan kar na rantse ba, da na rantse da Allah sai ya yi accepting Winki, kin san meyasa?."

Ta girgiza kai tana murmushi, ya kalli idanunta ya ce, "saboda daga jininki abin ya ke, Allah ne ya baki ba wani ba, matar Hamma."

Murmushi ta yi tana rufe fuskarta cikin jin daWin abinda ya ce. Shima murmushi ya yi yana kallon ta cikin soyayya, kafin ya mi™e ya ce, "zan fita, zan koma wajan Sadik mu kwana tare."

Ta mi™e tsaye tana kallonsa ta ce, "fita zaka yi?." Ya Waga mata kai yana kallon idonta.

Ta shagwaSe fuska ta ce, "ni kaWai zan kwana? Allah tsoro nake ji."

Ya Wan matso kusa da ita ya ce, "to ya ki ke so ayi, Debbo am?."

"Ka zo mu kwana, sai in kwanta a kan floor."

"Sai ni na kwanta akan gadon ke kina ™asa?" Ya faWa yana bin fuskarta da kallo. Ta Waga masa kai kamar ™aramar yarinya.

Ya yi murmushi, tare da jan hancinta ya ce, "A'a Debbo am, zan je mu kwana da Sadik, ke ki kwana a nan."

Cikin shagwaSar da ta saba yi masa ta ce, "ni dai A'a, Allah bazan iya bacci ba."

Ya sake yin murmushi ya ce, "tsoro ki ke ji?."

Ta Waga kai alamun eh. Ya ce, "babu abinda zai same ki, ki kwanta kin ji."

"Ni dai a'a, don Allah ka kwanta kawai."

"islaha bazan kwana a nan ba."

"Meyasa?."

"Akwai shaiWan Matar Hamma, gwara na baki space, zan dawo da asuba in sha Allah."

"Ni ba ™anwarka ba ce? Ai babu komai."

Ya yi dariya ya ce, "™anwar Hamma. Na san ke ™anwata ce, kar ki damu babu abinda zai same ki."

Ta yi shiru bata ce komai ba, ya san bata yarda ba kenan. Ya sake yin dariya ya ce, "za mu kwana tare wata rana, ranar ba sai kin ce min in zo mu kwanta ba, da kaina zan ri™o hannunki mu kwana tare. Na yi miki wannan al™awarin, indai ranar nan ta zo zan tuna miki. Kin san me zan yi?.

Ta girgiz kai tana Wan murmushi, kanta yana ™asa saboda kunya.

Saheer ya ce, "bazan bari ki kwanta akan komai ba, ni zan zamar gadonki kuma pillow ki. Al™awari na Waukar miki, kuma zan tabbatar miki dashi, Debbo am!."

Islaha ta ji kunya mai tsanani, ta juya masa baya harda rufe fuska da hannunta.

Ya yi dariya ya ce, "kina da aiki gobe matar Hamma, ki kwanta sai da safe. Ki kulle ™ofar kin ji? Sannan kar ki yi alwala da ruwan sanyi." Ta Waga masa kai ba tare da ta juyo ba.

Ya ce, "to ki juyo na ga fuskarki sai in tafi."

Ta no™e kafaWa ta ™i, ya ce, "ki juyo na ganki."

A hankali ta juyo kanta yana ™asa, ya yi dariya kaWan ya ce, "ki kwana lafiya."

Ta Waga ido tana kallon kyakyawar fuskarsa, mai cike da kwarjini ta ce, "Allah ya tashe mu lafiya."

"Amin matar hamma" ya faWa yana niyar fita.

Sai ta ce, "Hamma!." Ya tsaya cak yana kallon ta, ta juya ta Wauki wayarsa ta ™arasa kusa dashi ta mi™a masa, ta ce, "ka manta wayarka."

Kafin ya karSa sai da ya bi hannunta da kallo sannan ya sake kallon fuskarta, ya murmusa ya ce, "Thank you matar Hamma." Murmushi ta yi ya ja ™ofar ya fita.

Islaha da murmushi ta zauna a akan gadon tana kallon Wakin. Tana jin daWin yadda ba ya za™ewa akanta, soyayya yake yi mata mai tsafta ba ya za™ewa irinta zamani.

Yadda ya ce saboda shaiWan Win nan ba ™aramin daWi ta ji a ranta ba, dan sai mai hankali ne zai tuna da hakan har ya faWa.

Shiyasa a kullum take ™ara ™aunarsa har zuciyarta, domin bata da kowa sai shi, kuma yana yi mata so na tsakani da Allah, ba ya tunawa da ita Win a gidan marayu ta tashi. Yana yi mata so mai tsafta, wanda zata bugi ™irji ta ce ita matar so ce a ko ina. Da wannan tunanin ta Wan kwanta, tana sake kallon Wakin dan bata taSa jimawa haka a ciki ba.

Nana Haleema
'<Øûß

*RAGAYAR DUTSE.*

            ©þ *Nana Haleema.*

More pages on Arewapen@nanahaleema11.

*Book 1*
*Page 005.*


Saheer yana fita ya shiga motar da take ajjiye a ™ofar gidansu. Yana shiga wanda yake cikin a zaune a motar ya ce, "ka kirani a daren nan, ga sanyi."

Ya Wan yi tsaki ya ce, "ka cika mita wallahi, Islaha ce a Wakina shiyasa zamu tafi tare."

Sadik ya buWe ido ya ce, "Wow, ka ga masoya, har kwana take a Wakinka ashe. Kana nunawa yarinyar nan soyayya, ko da yake itama tana sonka. To meyasa baza ka kwana tare da ita ba?."

"Sai aurena ya hau kanta, sannan hakan zai faru."

Sadik ya bi sa da harara ya ce, "Kamar wani mutumin kirki, mtsww. Meye dan kun kwana tare? Ai normal ne."

Saherr ya ce, "babu ra'ayin yin hakan" ya faWa yana duba wayarsa.

Sai ya ce, "kai boss ya kira ni, mu je duk yadda aka yi akwai wani abun."

Sadik ya fara jan motar sannan ya ce, "wai meyasa baza ka shigo da Ishala cikinmu ba?."

Saheer ya yi masa banza kallo ya ce, "Matar da zan aura ce fa."

"So what dan zaka aure ta? Mata nawa ne a cikin mu suke da auren?."

"Baka da hankali."

"Na san daman haka zaka ce, amma da zata shigo zata kawo haske sosai."

"Ka daina wannan tunanin, domin kuwa har abada!."

Sadik ya yi dariya ya ce, "Allah ya sa kar boss ya gano ta, kuma ka san in ya gano ta ko wacece ita  sai ta shigo."

Saheer ya wani kalle sa, sannan ya ce, "ta ya zai ganta?."

"Itace take gabatar da shirin Rayuwarmu talkshow, ko Wazu na ji wani yana kallon shirin har yana yabonta, fuskarta ba Soyayyiya ba ce, tsaf zai iya ganinta."

Saheer ya ce, "Don Allah ka bar maganar nan, bana so wallahi. Harka kasuwancina daban, matata daman, ka daina haWa min ita dashi."

Sadik ya ce, "Allah sarki, ashe mu duk bamu san abinda mu ke yi ba" ya faWa yana hararasa shi dai bai ce masa komai ba suka cigaba da tafiya.

                 Washe gari.

Slowly take tafiya zuwa cikin falon, bata so ta ga wani daga cikin gidan a zaune, bata shiryawa tashin hankali ba.

Tana zuwa tsakiya ta ji muryar Mama, cikin Waga murya ta ce, "dawo nan!."

Islaha ta runtse ido, ta dawo a sanyaye ta zauna a akan carpet ta ce, "Ina kwana."

A fusace ta ce, "da ban kwana ba zaki ganni? Shegiyar yarinya ™aramar karuwa, ni za ki kawowa bariki har cikin gida? Kuma ki rasa da wanda za ki yi barikin sai da Wan cikina?. Kina cikin hankalinki kuwa?."

Islaha ta kalle ta ta ce, "Wallahi Mama ba abinda ki ke tunani ba ne, kawai....."

Bata ™arasa ba, Mama ta tsinke ta da marin da ya saka ta yin shiru tana dafe fuskarta. Ta dinga bin Mama da kallo cikin mamaki, ba dan matsayin mahaifiyar Saheer da take dashi ba, wallahi sai ta rama. Amma baza ta iya ba, ko babu komai Mamansa ce.

Mama ta sake fusata ta ce, "in ki ka kuma yi min magana wallahi sai na yi miki dukan tsiya a gidan nan...." Islaha ta yi shiru hawaye ya cika mata ido, suka fara sauka akan fuskarta.

"Ni za ki kawowa iskaci har gida? Ki shiga Wakin Wana ku kwana tare, sannan ki dawo min yanzu ki shigo min falo, dan ba ki da kunya ba ki da mutumci? Uban me Saheer Win ya yi miki?."

Bata amsa ba sai kukan da take yi a hankali cikin ™unar rai da ba™in ciki. Ta so ace wata ce ba Mama ba, da ta faWa mata abinda kunnenta zai toshe gabaWaya.

Hanan da hayaniyar Mama ta tashe ta daga bacci, ta fito tana kallonsu ta ce, "To Mama sai kin tambaya? Me ta yi masa za ki ce, ba me ya yi mata ba. Da yawan wanda suka tashi a wani waje inda ba gaban iyayensu ba meye basa yi? Balle Islaha, yarinyar da kowa ya san halinta. Ai kawai ki saka a ranki ta gama lalube miki Wa, daga ganin yanayinta kin san ta gama dashi wallahi."

Mama ta sake fusata, ta kalli Islaha ta ce, "za ki faWa min abinda ki ka yi masa ko sai na ci uban ki a gidan nan?."

Islaha ta goge ido, tana ji ko Maman ce fa sai ta mi™e ta Wauki mataki, in ba haka ba rainin zai yi yawa. Ta haWe rai ta ce, "ni babu abinda ya faru, kuma ba a Wakin ma ya kwana ba."

Hanan ta ce, "™arya ki ke munafuka, wanne halinki ne ban sani ba? Babu irin abinda bakya aikatawa a wajan aikin ku."

Islaha ta Waga ido, ta harari Hanan cikin fusata ta ce, "ba da ke nake magana ba, ki ™yale wacce ta isa da ni ta yi min magana amma ba ke ba. Kar ki ga Mama ta faWa na yi shiru, ki yi tunanin ke in kin faWa zan yi shiru. Duk abinda mu ka yi ina ruwanki? Ai mun kai mu yi Win ne."

Mama ta fara tafa hannu tana salati. Sai da ta gama salatin sannan ta ce, "shikenan komai ya ™are, tunda har ki ka iya buWe baki haka a gabana, kina faWawa mai bin mijinki magana abinda nake zargi ya tabbata, babu abinda ya rage wanda baki sani ba. Islaha kin san maza, kin cuce ni, kin lalata min Wa."

"Ko ya lalata ni ba" ta faWa ™asa-™asa tana goge idonta.

Hannan ta buWe ido ta ce, "Mama kin ji me ta ce? Wai ko ya lalata ba."

Mama ta mi™e tsaye ta ™arasa wajan Islaha, tana zuwa kusa da ita ™hamshin turaren Saheer ya mamaye ta, ta ce, "Ke Wago ki kalle ni."

Islaha ta sauke kai ™asa bata Wago ba, ba dan bazata iya ba sai dan tana Wan girmama Maman kaWan.

Mama ta ce, "yau sai kin bar gidan nan dan ubanki, ai ba a gidan nan aka haife ki ba ko? Ba a nan aka haifi uwarki ba. Aure kuma tsakaninki da Saheer babu shi, na soke shi!. Bazan bari ki zauna kina cigaba da lalata min yaro ba, dole ki bar gidan ko bakya so. Karuwar banza karuwar wofi, daman daga ganinki ni na san ba mutuniyar kirki ba ce."

Islaha ta ji Waci ya mamaye mata zuciya, ta kalli Mama ta ce, "Mama ki daina kirana da wannanan sunan, ni ba karuwa ba ce. Kuma in lalatawa ne sai dai shi ya lalata ni, ba ni zan lalata sa ba. Ban taSa jin tarihin da aka ce mace ta lalata namiji ba, sai dai shi."

Labiba da ta fito a lokacin ta ce, "ke Islaha! Maman ki ke faWawa haka? Wacece ke in ba karuwar ba, wacece take kwana a Wakin wanda ba mijinta ba, faWa min sunan sunanta?."

Islaha ta kalli Labiba, ta bita da banzan kallo ta ce, "ke za a tambaya, wannan harka ki ce ba tawa....."

Maganar ta katse saboda marinta da Mama ta sake yi mata cikin fusata. Islaha ta fashe da kuka mai tsananin sauti, zuciyarta tana zugata akan kawai ta rama.

Mama ta ce, "ita ce karuwar ki ke nufi?. TabWijam! Lallai yau mai raba ni dake a gidan nan sai Allah, sai na nuna miki banbancin tsakanina dake, sai na nuna miki na dame ki a iskanci na shanye. Lokacin da na yi nawa ba a haife ki ba, ba ki san komai akaina ba. Shegiya ´ar gaba da fatiha, wacce iyayenki suka yi cikin ki suka cillar dake. To daman ta ya za a samu tarbiyya a wajanki? Ta ya tarbiyya zata wanzu a wajanki?."

Islaha ™unci ya mamaye mata zuciya, ta tafi tunanin kenan waWanda suka girma a gidan marayu dukkansu ba ta hanyar aure aka same su ba? Mutane basa tunanin akwai ™addarar da zata iya kawo mutum ciki?. Meyasa ake yi musu kallon waWanda iyayensu suka haifa suka cillar?.

    "Mama me ya faru.?"

Saheer ya shigo yana tambaya, yana kallon Islaha da take dur™ushe a ™asa tana kuka.

Mama ta bisa da harata ta ce, "ka je ka baje jiki, yarinya ™arama kamar wananan ta gama lalata min kai. Sai da ta san yadda ta yi maka wayo ta bi ka Wakinka ko?."

Saheer takaici ya kamasa, ya ce, "Mama ni na ce mata mu je ta kwana a ciki saboda bata yanayin jikinta, kuma ni ba a gidan nan na kwana ba, yanzu na shigo gidan."

"Yi min shiru, daman ai baza ka faWa min gaskiya ba, Soye min zaka yi saboda ita ´ar gwal ce a wajanka bata laifi. Kowa ya ga idon yarinyar nan ya san ta jima da sanin maza, kaima gashi ta lalata min kai ban ji ba ban gani ba. Shegen tausayinka na tsiya shine ya saka ka jajubo min ita da sunan amana, har ka ke zancen aurenta ubanka ya goya maka baya...."

"To yanzu na soke, dole ta bar gidan nan dan baza ta lalata min yara ba. Tunda har ta san ta kwana a Wakin Waya da namiji, gwara ta tattara ta bar min gidana."

Hanan ta ce, "ta je can ta ™arata da gajojin samarinta."

Saheer ya fusata ya yi kan Hanan zai dake ta, ya Waga hannu sama ya ce, "sai na fasa miki baki, dake ake magana?."

Mama ta ce, "ni zaka daka ba ita ba Saheer, ni zaka juyo ka daka, a nan zan tabbatar da wuyanka ya isa yanka. Ka ga sai fahimci Islaha ta fi ni daraja a wajanka."

Ya girgiza kai yana harararsu Labiba, ya kalli Mama ya ce, "Wallahi Mama ni ba a gidan nan na kwana ba, kuma koda na kwana Waki Waya da ita babu abinda zai faru a tsakaninmu, domin dukka mu mun san daidai, kuma muna da ilimi, mun san abinda mu ke yi. Dalilina na kai ta Wakina na san yanayinta, zata iya samun attack. A haka ma sai da na siya mata magani ta sha, saboda sanyin ya shige ta. Don Allah Mama ki bar wannan maganar, ki ™yale ta ta je ta yi abinda yake gabanta."

Mama ta ce, "Saheer! Yarinyar nan baza ta sake kwana a gidan nan ba, dole ta bar sa tunda ba na ubanta bane!."

Saheer ya ce, "Don Allah Mama ki daina wannan maganar, ki yi ha™uri. Kin san amana ce a hannuna, ki bari ya sauke nauyin da na Waukarwa kaina."

Ta kalli Islaha da kanta yake ™asa har lokacin bata Wago ba, ta ce, "in dai nan gidan mijina ne, wallahi sai ta barshi. Ta shiga ta Wauko tarkacenta tazo ta bar min gida. Ri™on amanar an fasa, aure tsakaninka da ita an fasa, daman ba so nake yi ba. Yanzu na samu gaSar da zan kafa hujja da ita, bazan bawa Wana mace irinta ba."

Islaha ta mi™e ta shiga Wakinta, ba jimawa ta fito da handbag ko kaya bata canja ba ta fita daga falon tana kuka sosai.

Mama ta bita da kallo baki buWe, sai ta girgiza kai ta ce, "kutumeleci, ka ga shegiyar yarinya. To kar ki dawo min gida, ki je can Allah ya raka ta ki gona!" Ta faWa cikin Waga murya dan Islaha ta jiyo ta.

Saheer kamar zai yi kuka ya ce, "Mama meyasa ki ke yiwa Islaha haka? Amana ce a hannuna, meyasa baza ki ta ya ni ri™e amanar ba?. Lokaci kaWan ne ya rage ta bar gidan gabaWaya."

"Da kai da amanar zan haWa na zaga Saheer. Kai! ka fita daga idona na rufe, daman can ba son zamanta nake yi ba, yanzu kuma ta nuna so take ta tafi, sai a ™yale ta."

Saheer ya ce, "Haba Mama, itama ´a ce kamar kowa, baza ki so a yiwa su Labiba abinda ki ke yi mata ba."

Mama ta ce, "su Labiba marayu ne? Ko a gidan marayu suka tashi?. Kar ka sake haWa min yara da ita, ta ko ina sun fita, baza su haWu ba ko a hanya." Ya sauke numfashi bai ce komai ba, ya bi bayan islaha da sauri.

Labiba ta bisa da harara ta ce, "tabWijam, gaskiya da sake wallahi. Tun kafin ta auresa ta mallake sa haka? Kalli yadda ya bar ki a

Please Login or Register in order to submit comment