Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar kakata ki ke."

Daada ta yi dariyar jin daWi, tana kallon Islaha ta ce, "Gaki nan ba™ar bafulatana, kyakyakawa ma sha Allah. Ga kyau ga kirki, ga tarbiyya da sanin darajar tsoho. Islaha ta sake yin murmushi bata ce komai ba.

Daada ta ce,  Kina da aure?."

Ta girgiza kai tana murmushi ta ce, "bani dashi Mama."

"ai kuwa na samarwa jikana mata, daman yarinya mai hankali da tarbiyya nake nemar masa, kuma gaki na samu. Shikenan sai a yi bikin a huta.

Islaha ta kuma yin dariya sosai ta ce, "Hajiya Mama kenan."


"Da gaske nake jikata, daman ina so na samar masa yarinya jinin fulani mai tarbiyya, kuma ga ki na samu."

"Mama ni an kusa bikina."

"Sai a fasa auren da wancan, jikana Muhammad zaki aura ba wani ba."

Islaha ta sake yin dariya bata ce komai ba, dan bata Wauki maganar da gaske ba, ta san irin wasan tsofaffi ne da suka saba.

Mai napep ya ce, "mun shigo unguwar."

Islaha ta ce, "Mama mun shiga unguwar, a ina za a ajjiye ki?."

Ta kalle ta ta ce, "gidan Wana AbdulAziz."

"Ina kenan?."

"A nan unguwar ya ke, kawai gidan Wana."

Islaha ta girgiza kai ta kalli mai Napep ta ce, "ka san gidan?."

Ya girgiza kai ya ce, "wallahi ban sani ba."

Ta ce, "ka Wan tambaya, ba za a rasa sani ba."

Ya fita ya je wajan wani mai gadin wani gida ya tambaye sa yana nuna masa Hajiya, yana ganinta ya gane ta ya kuma yi masa kwantance estate Win.

Ya dawo ya shiga ya ce, "ai mun kusa, gashi layin gidan can."

Yana karya kwana zai shiga estate Win aka hanasu ™arasawa saboda security da yake wajan.

Islaha ta kalli Daada ta ce, "Maman hana mu wucewa, wai sai dai mu wuce da ™afa."

Sai a lokacin Daada ta kalli wajan ta ce, "in ji ubanwa? Matsa na fita ki gani."

Islaha ta ce, "A'a Mama ki zauna, bara na yi musu magana."

Daada ta ce, "ke dai bani hanya." Islaha ta fita itama ta fito.


Daada ta kalli Waya daga cikin masu tsaron ta ce, "waye ya ce bazan wuce ba? Na ce waye ya ce bazan wuce na shiga ba?."

Ya kalle ta ya ce, "Kaka ba a shiga da napep wajan nan, sai dai ku wuce da ™afa."

"In ji wa? Wallahi da babur Win zan shiga har gidan nan, sai naga wanda ya isa ya hana ni."

Islaha ta bita da kallon mamaki, ganin tsohuwa da ita faWa da neman rigima kamar bata girma ba.

Islaha ta ri™e ta ta ce, "Mama ki tsaya, ba a wasa da irin wajan nan, zasu iya harbin ki. Mu je sai in raka ki har cikin gidan."

Daada ta kalle ta ta ce, "nida gidan Wana a ace bazan shiga ba? Sun isa su hana ni wuce?."

Ta kalli mai Napep Win ta ce, "Mai babur mu je, sai na ga wanda ya isa ya hana ni shigewa ciki."

Šaya daga cikinsu ya ™araso yana Waga bindinga sama ya ce, "Mama ki koma, ba a wucewa da keke, sai dai a ™asa."

Daada ta tsuguna ta buga ™asa ta ce, "wallahi sai na shiga da babur Win nan, in ban shiga dashi ba ku ce ban haifu ba..."

Ta kalli Waya daga cikinsu ta ce, "Kai shiga gidan nan, ka ce AbdulAziz ya zo in ji ni."

Shugaban masu gadin gidan ya ™araso da sauri ya du™a mata ya ce, "Daada barka da zuwa."

Ta kalle shi ta ce, "yauwa Sulaimanu, shiga gida ka kira min AbdulAziz, ka ce yazo ina nemansa."

Ya du™a da girmamawa ya ce, "Ba ya nan Daada."

Ta ™arasa kan wani tudu na dutse ta zauna ta ce, "zan jira sa a nan, babu inda zan je sai na nuna musu matsayin da nake dashi. Duk sai na saka an kore su, zasu san sun wula™anta ni, har suna nuna ni da bindiga."

Islaha ta dafe kai, tana mamakin wannan faWa na tsohuwa kamar ba babba ba. Ga rigima da Worawa kai, in banda rigima ina ita ina faWa da masu tsaron hanya.

Islaha ta duba agogo ta ga lokacin sallah har ya wuce bata yi sallah ba, ta kalli Daada ta ce, "Mama ni zan wuce, sauri nake yi."

Ta ta ri™o ta ta ce, "babu inda zaki je, sai kin shiga cikin gidan nan a wannan babur Win."

Mai gadin ne ya yi musu bayanin wacece a gidan, duk sai suka rikice, suka ruWe, gashi ta ce sai ta saka an kore su.

Cikin taushin murya guda Waya ya ce, "Ki yi ha™uri Hajiya, ba mu san ke bace, duk muna wannan abun ne saboda tsaoron lafiyar ku."

Ta hararesa sannan ta kalli mai gadi ta ce, "jinin indiyawa ya dawo ko?."

"eh ya dawo Hajiya."

"Ai na san sai shi, zuwansa ne kawai zai saka a tsayar daku a wajan nan kamar wani zuwan shugaban ™asa. Ku je gidan ku kira min Muhammadun, ya zo ya shiga cikin babur Win da kansa, mu shiga gidan a tare."

"Ki yi ha™uri Hajiya."

A fusace ta nuna su ta ce, "kuma duk sai na saka ya kore ku wallahi."

Suka haWa baki wajan faWin, "Ki yi ha™uri Hajiya, shiga babur Win sai ku wuce."

Ta harare su ta ce, "Sai da ku ka wula™anta ni? Nima sai na wula™anta ku sannan zan shiga."

Suka dinga bata ha™uri tana shan ™hamshi, da™yar aka samu Daada ta shiga Napep Win nan, Islaha ma ta shiga aka buWe musu suka wuce aka shiga da Napep Win har cikin gidan.

Islaha tunda suka shiga take kallon gidan saboda girma da kyau, duk da ta taSa shiga government house, ta shiga manyan gidaje sosai, amma wannan ya fi burge ta akan ko wanne gida. Ga motoci a zube kamar ba a so, ko ina mota ce babba da ™arama.

Lokaci kaWan jikokinta suka baibaye wajan, suna haWa baki suna cewa, "Daada ina ki ka tafi ke kaWai? Abba yana ta neman ki."

Islaha ta fito tana kallonsu, musamman Banisha da take ta dariya kanta babu Wankwali.

Sai ta ji yarinyar ta burge ta, kana kallon ta ka san ruwa biyu ce, iya gashinta ya gwada hakan, dan bai yi kama da na fulani ba. Islaha ta zuba mata ido tana kallonta, gata yar duma-duma, irin yaran masu kuWin nan.

Bashisha ta kalle ta ganin tana kallon ta, sai ta ce, "Sannu."

Islaha ta yi murmushi ta ce, "yauwa."

Sai kuma ta kalli Islaha ta ce, "kamar na san ki, Islaha ko?."

Islaha ta yi murmsuhi ta ce, "haka ne.

Ta Wan buWe ido ta ce, "Wow, na ji daWin ganinki. Ina ganin programs Winki a tiktok" ta faWa tana bata hannu alamun su gaisa.

Islaha ta saka hannunts a cikin na Banisha tana murmushi.

_Kai, ka ji hannun yarinya da shegen laushi._

Islaha ta furta tana sake kallon Banisha tana ayyana Allah ya yi mana arzu™i a ranta.

Banisha ta ce, "Sunana Banisha" kafin ta bata amsa ta tafi a guje ta yi cikin gidan tana kwalla ihu kamar ™aramar yarinya.

Ta bita da kallo tana murmushi, tana sake maimaita sunan Banisha, tana aiyana su fa ´a´a masu kuWin nan gudu ba komai ne a wajansu ba, duk shekarun mace dan ta yi gudu abu ne mai sau™i a wajansu.

Islaha ganin Daada ta yi gaba ita da jikokinta, sai ta koma cikin Napep Win ta ce, "Yi ha™uri Malam, juya mu koma kawai bana son Sata lokaci."

Ya ce, "Hajiya ai da kin shiga, baki san alkhairi da zata yi miki ba."

"In rabona ne zai kira ni, mu je kawai." Bai musa ba ya ja napep Win ya juya suka fita daga gidan.

Daada tana shiga Sangarenta Abba ya shigo, sai da ta samu waje ta zauna sannan ya ce, "Daada ina ki ka je ke kaWai? Hankalina ya tashi, tun Wazu na fita ina neman ki, na rasa inda ki ka nufa."

Ta yi shiru bata ce komai ba, sai ta kalli ™ofa ta ce, "ina yarinyar da ta dawo dani ta ke?."

Ya kalli ™ofa shima ya ce, "babu kowa a nan."

"Akwai yarinya da mu ka dawo tare, tana ina?."

Kafin ya yi magana aka shigo da sallaama, ta amsa ta ce, "Ke ina yarinyar da muka shigo da ita a babur?."

Ta ce, "Daada ai sun tafi, tun kafin ki ™araso suka hau babur Win suka tafi."

Daada ta ce, "Sun tafi fa ki ka ce, ta tafi ba tare da mun yi sallama ba? A yi maza a bi bayanta a nemo min ita yanzun nan."

Janan ta ce, "Daada a ina za a ganta? Ai kawai ki ™yaleta."

"Bazan ™yale ta ba, aje a nemo min ita,
ko ni na tashi naje na nemo ta" ta faWa tana mi™ewa.

Abba ya ce, "A'a, baza a yi haka ba. Janan je ki ki faWawa drivern Daada, ya bi bayansu ko zai gansu."

Janan ta juya ta fita tana ™un™uni, banda rigima irin ta Daada ko a ina za a gansu oho.

Abba ya ce, "Sannu Daada." Ta Waga masa kai tana shan ruwa.

Abba ya ce, "Don girman Allah ki daina fita ke kaWai, ban san kin fita ba, sai da na tambaya masu gadi suke ce min wai kin fita a keke. Don Allah ki daina fita ke kaWai, tunda an girma."

Daada ta ce, "na tashi ina son na yi ziyara, na tashi ina son na je dubiya matanka duk sun aiki direbobin. Ita waccan ishahshiyar da yake tafi kowa mutum biyu ta aika, Waya ma ta aiki wani. To ya ka ke so nayi? Ina da mai kai ni ne?."

Abba ya ce, "sai a buga min waya Daada, ko a tura cikin gida, in da wani yaron sai ya kai ki. Amma fitar ki ke kaWai bai kamata ba."

"Ni fa dan na fita ni kaWai babu abinda zai ci ni, kawai wannan juyewar kan da nake fama dashi ne matsalata. Šazun ma juyewa kaina ya yi da zan dawo, sai wannan yarinya ce, meye ma sunanta...." Ta faWa tana tafiya tunani.

Sai kuma ta ce, "Ishlaya. Yarinya ´ar albarka, itace ta sako ni a babur har gidan nan. Amma da yake wancan yaron ya dawo, muna zuwa wai aka hanani shigowa gidan nan."

Abba ya Wan sauke numfashi ya ce, "ki yi ha™uri, duk akan tsaron lafiyarku ne ya saka aka ajjiye jami'an."

"Tsaron lafiyarsa dai, dan sai ya dawo ake wannan dafifin a ™ofar gidan nan."

"Ki yi ha™uri, zan samar miki da driver da zai dinga kai ki duk inda ki ke so. Na ki ne ke kaWai, duk wacce ta aike sa bazai je ba."

Daada ta taSe baki ta ce, "ban yi sallah ba, zan shiga in yi sallah. Kafin na fito a nemo Ishlaya, sannan in an idar da sallar i'sha ka kira min ba™on da ya dawo yau, ka tattaro min kan kowa ina da magana.."

Abba ya mi™e kamar yadda ta mi™e ya ce, "in sha Allah." Shi ya ri™e ta har Wakinta, ta shiga ta yi alwala ta fito ta tayar da sallah sannan ya fita.

Yana komawa part Winsa Rehaan ya shiga part da sallama. Abba ya amsa yana kallonsa ganin fuskarsa ta yi ja, kana ganinsa ka san bashi da lafiya. Abba ya girgiza kai, dan ya san daman sai anyi haka, da wahala Rehaan ya dawo bai yi ciwo ba.

Ya taka a hankali ya zauna a kan carpet ya ce, "Abba barka da dare" ya faWa cikin yaren fulani, dan Abba ya fi so ya yi masa magana da yaren.

Abba ya amsa yana kallonsa ya ce, "Rehaan an dawo lafiya?."

Ya Wan dafe kansa sananan ya Waga kai ya ce, "Lafiya lau Abba."

"Ya dai, Lafiya ka ke?."

"Kaina yana ciwo Abba" ya faWa yana dafe kansa da hannu Waya yana sauke numfashi a hankali.

Abba ya bi sa da kallo tausayi ya ce, "sannu, ka je ka sha magani sai ka kwanta. Sannan ka tabbatar da ka yi addu'a."

A sanyaye ya ce, "To."

Abba ya bishi da kallo, a sanyaye ya ce, "Rehaan kasan za a yi faWa da Daada akan gashin nan naka ko? Meyasa baka rage ba?."

Ya kalli mahaifin nasa ya ce, "Abba ai ba laifi bane dan na bari."

"Na san babu laifi Rehaan, sunnah ce ta annabin mu. Amma ita baza ta gani ba."

Ya Wan lumshe ido ya buWe bai ce komai ba, yana mamakin wannan ™arfa-™arfar da Daada take yi masa.

Abba ya ce, "ka yi sallar i'sha?."

Ya Waga kai alamun eh. Abba ya ce, "mu je wajan Daada, ta ce na tattaro kowa, kuma ka san saboda kai zata haWa taron."

Ya kalle sa a sanyaye ya ce, "bani da lafiya Abba."

"Yi ha™uri mu je Win."

A hankali ya mi™e suka fita shiga mahaifinsa zuwa wajan Daada kamar yadda ta ce.

Kusan kowa na gidan yana falon, kasancewar falo ne mai girma sosai, ya Wauke kowa da kowa harda space.

Abba ya shiga Rehaan yana bayansa ya nemi waje can nesa ya zauna, inda ya saba zama inda za a yi meeting yana ™asar, a nan ya zauna ya kawar da kai baya kallon kowa. Kowa ya san haka yake yi, zai yi shiru bazai yi magana ba, sai wani lokacin in abin maganar ya tashi zai ce.

Daada ta bi sa da harara ta ce, "Ka fi ™arfin ka ce min ina yini ko Muhammad?."

Rehaan yana ji ya san dashi take, dan itace mai ce masa Muhammad. A faWar ta baza ta ce Rehaan ba, sunan indiyawa ne. Amma wani lokacin tana faWa, tunda yau da gobe sai Allah.

Ya Wago jajayen idanunsa saboda azabar ciwo, cikin muryarsa mai sanyi da daWin saurare ya ce, "na zo bakya nan. Ina yini?."

"Ka ri™e gaisuwar ka bana bu™ata, tunda ba ta ™asar india bace dole ka ™i gaishe ni."

Ta kalli Abb ta ce, "An samo yarinyar?."

Abba ya ce, "wallahi ba a gansu ba Daada."

"Yarinya ta yi min wannan alkhairin kuma na bari ta fita ba tare da na saka mata ba. Gaskiya ban kyauta ba, amma duk inda take zan nemo ta, zan yi mata tukwici mai girma."

Babu wanda ya amsa mata, ta bi Rehaan da kallo ta ce, "kalli wani gashi a kanka kamar wani kafiri, baza ka taSa ganin muslimi ya ajjige dogon gashi haka ba sai kafurai. Kuma iyayenka suna gani suka zuba maka ido, kai ga Wan gayu mai kuWi, kuma Wan ™asar waje."

Shi dai bai ce mata komai ba ya yi mata shiru yana jinyar kansa.

Ta buga ™wafa ta ce, "Yauwa, bazan lamunci yawan barin ™asar nan da ka ke yi ba Muhammad, ™ananun jikokin gidan nan wasu basu san ka ba saboda baka zama. Kai likita ne, kuma kana da babban asibiti a nan, ka dawo ka cigaba da harkokinka a nan, kasuwancin ma duk k tattaro ka dawo nan, dan baza ka sake komawa ba. Aure zan yi maka, ka tare na ga jikoki."

Sai a lokacin ya Wago ya kalle ta, suka haWa ido jin tana batun aure.

Daada ta buWe idanunta ganin yana kallon ta ta ce, "Eh aure! Ko ban isa bane?."

Ya Wan Wauke kansa daga kanta ya kalli Mamy da kanta yake ™asa, ya kalli Abba da yake kallonsa sai ya sake kallon ta ya ce, "Daada na ce miki ina son aure ne?."


"Sai ka faWa min kana so? Yadda ka ke cuWanya da fararen fata ko ba a faWa ba kowa ya san kana son aure. Za a yi maka aure kafin ka jawo mana abin kunya. Dan haka za a haWa aurenku dasu Juwairiyya, kowa ya huta."

Ya girgiza kai ya ce, "bani da bu™ata, in lokacin yin ya yi zanyi."

"Wallahi sai ka yi, indai har na isa da ubanka to na isa da kai, dole ka auri wacce na zaSa maka."

Ya Wan sauke numfashi  ya ce, "Okay zan yi, a jira in kawo wacce nake so in aura."

Ta harare sa ta ce, "baka isa ba, wannan yarinyar da nake magana a kanta ita zaka aura, tukwicin taimakona da ta yi aurenka zan bata. Ta yi min Wari bisa Wari, jinin fulani ce gaba da baya, mai tarbiyya da kyau, ga za™in murya ta ™arasa faWa tana murmushi tunawa da muryar Islaha.

Ya Wan sake kallon ta, kallon ™asan ido ya yi mata ya ce, "ke ce ni?."

Ta nuna Abba ta ce, "ni ce ubanka, mara kunyar yaro fitsararre. Kana so ka nuna min ban isa da kai ba kenan ko?."

Ya Wan dafe kansa ya yi shiru kawai bai ce komai ba, sai da ta gama faWanta sannan ya ce, "ban ga dalilin da zai saka ace za a yi min aure yanzu ba, kuma auren ma da wacce ban santa ba."

Daada ta fusata ta ce, "Ni ka ke mayarwa da magana, Ina faWa kana faWa?..."

Ta girgiza kai cikin takaici ta kalli ta ce, "AbdulAziz ka ga abinda ka Wauko mana ko? Ka ga abinda ka kawo mana har cikin gida ko?. In ban da shi waye a gidan nan faWa yana faWa? da yake shi ruwa biyu ne, ba cikakken batulatani ba, ina faWa yana cewa bazai yi b.

Abba bai yi magana ba, dan bai san ya zai yi da rigimarta ba, shi kansa ya san ba daidai take yi ba. Haka kawai ta ce zata yi masa aure, kaf samarin da suka yi aure babu wanda ta zaSawa mata, kowa da kansa yake nemo mata ya kawo kuma a amince. Haka kawai shi ta ce ita zata zaSar masa, ai hakan ba adalci bane.

"Ko da yake ta ya za ka yi kunya? Ta ya ya zaka san kunya bayan ba nonon bafulatana ka sha ba?. Sauran yaran da suka sha nonon fulani ai ba zasu aikata abinda ka yi ba, duk abinda nace shi suke yi saboda jinin fulani ne."

"Kalle ni Muhammad, na rantse da Allah in ka ga ba a yi auren nan ba, to yarinyar ce bata amince ba."

Ya buWe baki zai yi magana suka haWa ido da Abba ya yi masa alama da ya yi shiru, ya sauke ido ™asa, amma yana so ya faWa mata shima indai har anyi auren to tabbas sai dai wani bashi ba, dan zai iya amincewa da komai amma ban da auren wacce bai santa ba, kuma baya so. Mamy ce kaWai zata yi masa haka ya amince, in Mamy ce zai yarda ayi auren kuma a zauna lafiya. Amma Daada kam bata isa ba.

Daada ta ce, "gwara ka ji da kyau, zan saka a nemo min ita a Waura auren ko baka so, sai dai in aka aura maka ita ka sake ta."

˜asa-™asa ya ce, "ashe akwai mafita."

Bai san Daada ta ji ba, sai da ya ji ta rafka salati taba tafa hannaye, sai kuma ta fashe da kukan da ya saka Abba ™arasa kusa da ita.

Daada ta ce, "Kaga abinda ka jawo mana ko? Ka ga irin da ka je ka auro mana daga wata ™asar ko?. Kamar ni ina magana yaron nan yana magana, Ina cewa a yi yana cewa baza a yi ba?. Kaf gidan nan babu wanda na taSa saka abu ya tsallake ko ya musa min, amma shi ina faWa yana faWa, da yake idonsa ya buWe ko?."

Abba ya ™arasa ya ce, "ki yi ha™uri Daada, ki daina kuka."

Bata daina kukan ba ta ce, "babu wanda na taSa cewa ya yi yace bazai yi ba, amma shi na saka shi ya ce bazai yi ba."

"Shima zai yi duk abinda ki ke so, bazai sake yi miki musu ba. Tunda auren ki ke so ya yi dole zai yi, duk wacce ki ka zaSa masa ita zai aura ya zauna da ita a matsayin matarsa."

Abba ya kalli Rehaan da ya sunkuyar da kansa ya ce, "Rehaan faWa mata zaka yi abinda ta ke so, ka faWa mata zaka auri duk wacce ka ke so."

Ya Wan Wago idonsa ya kalli Abban, kansa yana juyawa sosai, ya Wan sauke numfashi kaWan ya ce, "Amma Abba...." Abb ya dakatar dashi ya ce, "Yi min shiru, ka amsa abinda nace kawai Rehaan."

Ya Wan cize bakinsa cike da takaici, ta ya zai yi abinda bazai iya ba? Ta ya zai amince da auren da ba ya so? Ta ya ake tunanin zai amince da wannan auren da ba Mamy ce ta zaSa masa ba?.

Abba ya bi sa da kallo ganin ya yi shiru bai ce komai ba.

Daada ta sake fashewa da kuka ta ce, "ya raina ni ya raina ubansa, babansa yana yi masa magana ya share shi kamar bai ji ba. Daman an ce matasan masu kuWi basa jin maganar iyayensu, ga yaro ™arami Wan mitsisi ya raina babansa."

Abba ya ce, "Rehaan!."

Slowly Rehaan ya ce, "zan yi."

Abba ya ce, "kin ji abinda ya ce, zai yi duk abinda ki ke so."

Ta share hawayenta, daman na rigima ne ba na wani abu ba, daman so take kawai ya amsa ta ce, "ina so a haWa aurensa da na Juwairiyya."

"An gama."

"Ina so ka nemo min gidansu Ishlaya a ko ina take, ko da an yi mata miji ka bi duk yadda zaka yi a warware auren a aura mata shi. Ta shiga raina sosai, kyakykyawa ce jinin fulani, mai kirki da tarbiyya. Ita nake so ya aura, ko dan saboda ta koya masa kaWan daga cikin tarbiyyar fulani, wacce ba a koya masa da yana yaro ba. An bar shi cikin turawa, ana koya masa yaren matsafa."

Abba da ya ke ya san rigimar kayyasa sai ya ce, "shikenan, in sha Allah za a yi duk abinda ki ka ce."

Daada ta ce, "hakan shine kwanciyar hankalina, akasin hakan kuma an nuna min ban isa ba, an nuna min ni Win ba kowa ba ce a gare ku."

Abba ya ce, "za a yi in Allah ya yarda, ki kwantar da hankalin ki Daada."

Daada ta kalli Mama ta ce, "Batun nemo masa mata da nace ki yi na soke, na samo yarinya daidai dashi."

Mama cike da ba™in ciki da takaici ta ce, "Shikenan Hajiya" ta faWa tana kawar da kai gefe, domin wallahi bazata bar auren nan ya yu ba, yadda ta ce mai tarbiyya da hankali ita akasin hakan take so ya aura, sai ta san yadda ta yi ta kifar da batun auren ko ta wanne hali.

Daada ta ce, "kowa ya tashi ya bani waje, saura na ji wata magana ta sake Sullowa."

Rehaan ne ya fara mi™ewa yana yamutsa fuska saboda ciwon kai.

Yana jinta tana magana akan gashin kansa ko kallonta bai yi ba ya yi ficewarsa, yana aiyyana ko ta wanne hali bazai auri yarinyar ba, sai dai duk abinda za a yi ayi. Ya ga ji da jure abubuwan da baya so a gidan, a wannan lokacin sai dai ran kowa ya Saci, amma bazai yi aure ba. In kuwa ya yi auren, sai dai in Mamy ta zaSa masa ita.


Topa, ya abin yake ne? Saheer ne ko Rehaan?.


Nana Haleema
'<Øûßd'þ


*RAGAYAR DUTSE.*

            ©þ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 015.*

SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah.
Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su suna nan kamar haka.

Kabbasa spray
Dufr khumrah
Mahlab khumra
Body milk
Kuleccam
Matan Maiduguri
Ready to use dilka
Halawa
Shuwa Arab hair mist
Cotton incense
Dorut after period
Dukhaan stool
Gabgab
Sandal flex
Sandal sukkaria
Kajiji
Halud
Arabian oud
Oil perfume
Room fresh
Multi purpose sprays
Curtains incense
Kabbasa
Farce
Marshoosh
Senegalese Kajiji
Dilka soap
Dilka cream

Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168
08164570032

       -

Daada ta bisa shi da harara ta ce, "Wan laSuSu mai zubin mata kawai."

A lokacin Mamy

Please Login or Register in order to submit comment