Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake son bawa matar tasa baby.

Hasbunallahu. Kasa juyowa gwaggo ta yi bare ta haɗa idanu da shi, a hakan ma bata san cewa ya yi mata raɗan ne dan kada Akilar ta ji ba, ba dan Akilar tana wajen ba, ai da afili zai faɗi maganarsa, yo su ina ruwansu? Ina suka san me kunya? Ai sam basu san shi ba. Turawa ma da suke wasu abubuwa marasa ɗa'a a kan tsakiyar hanya, ai su nasu ma mai sauki ne, turawa ai iskancinsu a bayyane yake.

Kawar da zancen gwaggon ta yi da cewa "To gaskiya wannan aure dai bai ɗauru ba, dan ni ban bada Jehan da Rimsha ba!".

Areef zai yi magana daddyn Rimsha ya katse shi da cewa "A'a ni ai na bawa ɗana, kuma aure ya ɗauru, dan haka ba wani sharhi, Jehan matar Areef ne".

Kafewa gwaggo ta yi a kan ita sam bata bayar ba, dole a zo a tsugunna a gabata a nemi aure Rimsha da Jehan, kuma sai ta tantance masu neman auren zata ba su, sai ta yi musu jarabawa masu tsanani tsauri, idan sun ci, sai a basu mata, idan ba su ci ba, shikenan ta rike ƴaƴanta, ta nema masu miji na gari.

Ganin Lion yana ƙoƙarin mikewa ya bar wajen ne yasa gwaggon ta ce "Saif zauna mu yi magana ko?".

Ba musu ya koma ya zauna yana faɗin "Mummy my head is penning me to much, bana son hayaniya, idan kuna yawan magana bazan iya zama a wajen ba, that's why nake son baku waje!".

Hannu ta kai ta shafa kan nasa tana faɗin "Tom shikenan zamu yi maganar anjuma, je ka huta yanzu ga ji?". Ba tare da ya amsa ba ya miƙe ya fuce daga ɗakin abinsa.

Shi kuwa Areef raɗa ya fara yi wa Jehan a kunne bayan ya matseta a jikinsa. Babu kunya a gaban gabaɗaya iyayenta. Ita kuwa ko kallo bai samu ta ɗago ta yi mashi ba, haushinsa ma take ji, burinta kawai ya saketa, shi kuma yaki, ya kankameta gam kamar wani ya ce zai kwace mashi ita.

Nan fa hira ya ɓarke a cikin bedroom ɗin, ga Brr Naurat a wajen, ai sai ta fara basu labarin rayuwarta a Russia, su kuma suka gaya mata bayan tafiyarta Dr Salman ya rasu. Nan take ƴar tsohuwa ta fara kuka. Taruwa suka yi a kanta suna bata hakuri. Jikokin nata kuma sai dariya suke yi mata, wai ta tuna da tsohon zuwa, Imran da Irfan sai tsiya suke yi mata.

Lallaɓawa Anaya ta yi ta fice daga cikin bedroom ɗin. Tamkar wata ɓarauniya haka take sanɗo. Palon kasa ta sauko, sai waige waige take yi tana neman Mark, dan ɗazun da suka shigo da daddynta, ta gan shi a palon kasan, ba halin ta yi mashi magana ne saboda daddynta. Shi kuma bai ganta ba, yana latsa waya, ba sai na sake gaya maku ba, irin halin Lion ne da Mark, abin da yake gabansu kawai suke yi, so ko mutun zai wuce ta kusa da su, sam basu ɗago kai bare su kalle shi, hakan tasa har su Anaya suka haura sama bai ɗago kai ba.

Ta zo zata nufi waje ta hango shi a cikin kitchen yana aiki, wani irin tsantsar farinciki ne ya rufeta, sai sakin cool murmushi take yi. Cikin sanɗo ta lallaɓa izuwa cikin kitchen ɗin.

Sarai ya ji alamar mutun, dan su suna amfani ne da sautin numfashi mutun, dan sun iya yakin sunkuru. Amma bai kawo cewa ita ba ce, ya yi tunanin Rimsha ce ko Jehan or Akila, dan sune kawai masu shigowa cikin kitchen ɗin.

Hatta kariso kusa da shi bai juyo ya kalli wacece bane. Hannu ta sa ta tsaƙalo wuyarsa tare da ɗale jikinsa ta baya tana murmushi. A tsananin fusace ya juyo tare da damko wuyarta, ya dawo da ita ta gaban fuskarsa.

Ta yi matukar razana na ganin yanda ya shaketa ɗin, nan take idanunta suka firfito waje, ta tsorata ainun, kirjinta sai dukan uku uku yake yi.

Yana kawota saitin face nasa ya ga ashe ita ce, ga shi ta zaro mashi idanu tamkar za su faɗo kasa. Ai a dubu ya sake wuyar tata yana ɗan sunkuyar da kai kasa. Sam bai taɓa tunanin ita ɗin ba ce.

Ganin tana ƙoƙarin zubawa kasa ne yasa a hanzarce ya rikota tare da jawowata jikinsa yana faɗin sorry. Ya yi maganar tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, wani irin sanyi ya ji na jinta a jikinsa.

"Haba my shi ne kake son kashe ni? Dan kawai nazo ganinka ko?". Ta yi maganar tamkar zata saka mashi kuka, tana yi tana turo baki.

Cikin sanyin murya bawan Allah kasa kasa ya ce "Sorry my Queen, ban san ke ba ce ai, am so sorry". "Ni gaskiya ba zan hakura ba".

Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin daga bisani ya matso da face nasa daf da tata, kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "Zaki fara ko? Wai har yanzu ba zaki dai'na wahalar da ni ba? Haba mana, kullum fa a waya sai kin yi ta yi mani kuka, kuma kin san bana son hakan, sai ki yi ta bani wahala, yanzu a zahiri ma ba zaki barni na huta ba?".

(My peoples yau ga Mark ma da cewa mace sorry 🤔 duniya kenan😂 kai waye ya taɓa tunanin Mark da Lion za su furta wannan kalma ta sorry ga wani ma ba wata ba?🤔 Lallai mata mun ciri tuta, mu ɗin duniya ne, duk giman namiji da karfi izza da isarsa, muna iya juya shi son ranmu😂 dan haka dole a bimu 😂)

Turo ɗan bakinta ta yi har sai da ta taɓa nasa, kasa kasa ita ma ta ce "Ai kai ne, sai ka yi ta yiwa mutun wani irin hali na basawa da bana ganewa". "Am so sorry zan dai'na duk abin da baki so kin ji ko? Amma a dai'na yi mani fushi da kuka please".

Tana ƙoƙarin sake yin magana suka ji motsi a bayansu. Da sauri ya saketa, suna juyowa a tare, dan su ga wanene.

Brady ne ya zo taya Mark ɗin aiki. Ajiyar zuciya Anayar ta sauke tare da wucewa da sauri, dan ta fice daga kitchen ɗin kada ma daddynta ko wani daga cikin family ya ganta.

A hanzarce ya riko hannunta yana faɗin "Haba mana, ina kuma zaki je?". A takaice ta ce mashi cikin ɗaki zata koma, dan kada ma a nemeta, dama ta zo ganin shi ne kawai, tana tsananin kewarsa.

Sake jawota jikinsa ya yi yana faɗin "Haba my Queen, bari na ɗan ganki tukun nan mana, kin san yanda nake kewarki kuwa? Please ki bari na ganki ko da na 1 hour ne".

Sakalo wuyarsa ta fara kokarin yi, amma ina bata kai shi tsawo ba, ko ta sakalo ba zata iya tsayuwa a hakan ba, dan ko ta ɗaga kafa ba zai yi mata dai'dai ba.

Ganin hakan yasa shi ya ɗan rankwafo mata da kansa kaɗan yana faɗin "Ƴar karama da ita a wajen, ba tsawo". Turo baki ta yi tare da jan gashin kansa ta wajen bayan wuyarsa.

Wash ya ɗan furta kafin ya matseta a jikinsa da karfi. A can cikin bedroom ɗin Lion kuwa, sai hira ake yi, tamkar za su cinye junansu saboda tsantsar so da kauna, sai dai ko kaɗan basu taɓo hirar abin da ya faru a baya na dan gane da rayuwarsu Abba, ma'ana rayuwar gidan Dr Salman na baya, sam basu taɓo wannan hiran ba, saboda yau suna cikin tsantsar farinciki, ba su son tuna abin bakinciki. Shi dai Aseef ya makale a jikin mommansa abinsa yana ta zuba mata shagwaɓa, shi kuma Areef sai tsokanar Jehan yake yi bayan gwaggo ta gama gabatar masu da gabaɗaya uncles nasu. Shi kuma daddyn Rimsha da daddyn Anaya tamkar za su haɗiye juna, saboda kauna.

Haka suka kasance har tsawo good 2 hours, kiraye kirayen sallar mangariba ne ya tashe su daga hirar ta su.

Mazan suka wuce masallaci, matan kuma suka nufi bedrooms na su Rimsha. Ƴan matan kuma wato su Rimsha, suka wuce bedroom na daddynta dan su yi alwala a can. Gwaggo dai a nan ɗakin Lion ɗin ta yi alwala. Shi kuwa Lion tun da ya bar ɗakin, basu sake jin ɗuriyarsa ba.

Rimsha tana shiga cikin toilet dan ta yi alwala, ta samu waje a saman chair, ta zauna ta fara tikar kuka kamar wadda aka yi wa sakon daddynta ya mutu.......... To fa kukan me kuma take yi hakan? Mu je dai zuwa.

Ita ma Akila lokacin da ta shiga toilet ɗin da nufin tayi alwala bayan Rimsha ta fito, sai da ta yi kuka kamar ba gobe. Ita dai Jehan ko a jikinta, alwalarta ta yi ta fito. Umaisha ciki ya fara girma sosai, sai tura abinta take yi.

Bayan sun yi sallah sun dawo ne aka haɗu gabaɗaya a palon sama. Nan fa su Abba suka ce za su wuce gida, kuma za su wuce da Brr Naurat. Suna cikin yin magana sai ga Lion ya shigo. Kusa da gwaggon ya zauna, kasa kasa ya tambayeta ya ta wuni?. Da fara'a ta amsa mashi da lafiya. Dawo da kallonsa a kan Areef ya yi kafin ya ce "Where is dad?".

Yana bedroom nasa Areef ɗin ya bashi amsa. Jinjina kai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba.

Gwaggo ce ta gaya Lion ɗin uncles nasu za su koma, amma tare da ita za su tafi, kuma za su tafi da Brr Naurat. Girgiza kai ya yi yana faɗin "No momma, ke kina nan, kuma ita ma grandma a barta a nan!".

Abban Imran ne ya karɓi zancen da cewa "A'a ita A'isha ta zauna a nan ɗin, dan kuna da bukatarta fiye damu, amma ita Brr zamu tafi da ita, dan mun fiku bukatarta muma, muna da bukatar mu zauna da ita, akwai abubuwa da dama da zamu tattauna da ita".

Shiru ya yi bai sake cewa komai ba, gwaggon ce ta sake cewa, to shikenan hukuncin da Abba ya yanke ya yi. Miƙewa Lion ɗin ya yi tare da wucewa bedroom nasa abinsa. Cikin hanzari Areef ya bi bayansa, shi kuwa Aseef har wa yau yana kwance ya tada kai da cinyar gwaggon abinsa.

Shiryawa su Abba suka yi, gabaɗayansu suka wuce izuwa gidan Abba, Jehan, Rimsha, Akila, duk sun bisu, sun bisu ba tare da su Abba sun sani ba, dan a motar Imran suka shiga, shi kansa Imran ɗin bai lura ba, dan familyn dukka sun haɗu, kuma shap ya mance da cewa su fa matan TRIPLETS ne.........

Bayan anyi sallar isha, gwaggo ta idar da sallah a bedroom ɗin Lion, tana zaune a saman dadduma, su kuma sun tafi masallaci.

Tana zaune a wajen har suka dawo, bakinsu ɗauke da sallama suka shigo cikin ɗakin. Su ukun dukka gwanin ban sha'awa. Fuska ɗauke da murmushi ta amsa masu sallamar tana mai binsu da kallo. Wani irin tsantsar farinciki na wuce misali take ji a tattare da ita, har wani ji take yi kamar ta mayar da su cikin cikinta, dan so da kauna.

A bakin bed Areef da Lion suka zauna, shi kuwa Aseef saman bed ɗin bakiɗaya ya haye ya kwanta. Zubawa mahaifiyar tasu idanu suka yi suna ta kallonta. Sai zuba adduo'i take yi tare da askar har tsawon good 30 mins. Sannan ta shafa tare da mikewa ta dawo kusa da su.

Suna ƙoƙarin matsa mata, dan ta zauna a tsakiyarsu, sai ta wuce ta zauna a saman bedside drawer.

"Momma ki dawo saman bed mana?". Cewar Areef. Girgiza kai ta yi tana faɗin "Bari na zauna a nan, zan fi jin daɗin ganin fuskokinku da kyau". "To shikenan ai muma a wajen zamu fi jin daɗin ganinki our pleasure".

Murmushi ta ɗan yi kafin ta ce "Son lafiya kuwa?". Ta yi maganar tana kallon Lion.

Shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci da ba su biyu ba, kafin ya amsa mata da "Nothing mum".

Dawo da kallonta a kan Areef ta yi, girgiza mata kai ya yi yana nuna mata alamar shi fa Lion haka yake da rashin magana, dan haka kada ta wahalar da kanta ma wajen yin tunanin ko dai wani abin ne yake damunsa, haka Allah ya yi shi. Jinjina kai ta yi alamar gansuwa.

"Son ya daddyn naku yake? Kun duba shi kuwa?". Ta sake tambayarsu

Sai a lokacin ya ɗago da dara daran idanuwansa a kanta. Allah sarki soyayya, hakika Gwaggo tana tsananin son Dr har gobe, duk wannan abin da ya yi mata a baya, amma ta kasa samun natsuwa a yanzu dan yana cikin wani hali, ba zata iya sharesa yana cikin ciwo ba.

Sam bata bawa Lion mamaki ba, dan dama a yanayin tarihin soyayyarsu, ya san fin hakan ma Gwaggo zata aikata, hakan ce ma tasa ya kula da lafiyar Daddyn nasu, ashe fitar da ya yi ɗazun, zuwa ya yi ya bashi kula tare da allurai, dan yasan confirm sai gwaggon ta tambayesu, ga shi kuwa ta kasa hakuri sai da ta tambaya.

Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Yeah mum, na kula da shi". "Kai Dr ne?" Ta tambaya tana dawo da kallonta a kan Areef. "No mum, but na yi karatun a wajen daddyn".

Ji ta yi tamkar ta ce musu zata je ta duba shi da kanta, zata bashi kulawa a matsayinta na Dr, sai kuma ta share, ta danne tare da kawar da zancen da cewa. "To shikenan ya kamata ku ci abinci ku kwanta ku huta ko?".

Jinjina mata kai ya yi tare da faɗin "Where is Meesha?".

Sai a lokacin ma ta tuna ashe babu kowa a gidan sai ita kaɗai, su Rimshan duk sun bi iyayensu, sai a lokacin kuma ta tuna ashe a labarin da Jehan ta bata, Rimsha matar Lion ɗin ne, ashe auren ta zo rabawa zancen ta sauya, sai yanzu ta tuna komai, lallau kuwa.

"Son dama kai ne mijin Siha na ko?". Ta tambayi tana kallon shi.

Bai amsa mata ba, kuma bai sake ɗagowa ya kalleta ba. Areef ne ya amsa mata da e.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ban ji motsinsu ba, kila sun bi su yaya babba ?".

Nan ma shiru Lion ya yi yana kallon kasa, bai sake yin magana ba.

Areef yana ƙoƙarin sake yin magana Aseef ya katse su da cewa "Kai momma har da Heartbeat ta bi su?".

Jinjina mashi kai ta yi tana faɗa mashi ai dukka suka tafi. Mikewa zaune ya yi yana faɗin "Wlh i can't believe it! A kan me zata je wani waje kuma bata gaya mani ba? Ni wlh ba zai yi wu ba, gaskiya dole na je na ɗaukota!".

Murmushi gwaggon ta yi tana faɗin "Yau dai sai ka hakura ka barta da iyayenta, murna take yi na ganin kakanta da sauran ƴan uwa, nima ba dan murnar ganinku ta fi yawa ba, ai da ba zan zauna a nan ba!".

Kuka ya saka mata yana faɗin "Allah momma ni ba zan yarda ba, dole sai ta dawo yau, kuma sai na yi punishing nata, dama da safe ta yi mani laifi".

Dariya kaɗan gwaggon ta yi dan ta ɗauka wasa yake yi, bata san halin ɗan nata ba, bata san rigimarsa ba, ai yau idan ba dawo mashi da Akila aka yi ba, to ba zaman lafiya, wannan kuka ya rinƙa yinta kenan har washegari.

Waya Lion ya ɗauka ya fara kiran number Mark. Bugu ɗaya ya ɗauka. A takaice ya ce ya kawo masu abinci cikin ɗaki, sosai Mark ɗin ya yi mamaki, dan ya jima rabonsa da ya kawowa Lion ɗin abinci, sai dai ya girka kawai.

After some minutes Mark ya shigo masu da abinci kala kala, a saman carpet ya jere masu.

"Momma let's eat". Cewar Lion ɗin, ya yi maganar tare da miƙewa ya isa ga abincin.

Make kafaɗa Aseef ya yi yana faɗin shi wlh ba zai ci ba, dole sai Akila ta dawo. Da kyar gwaggo ta rarrasheshi ya sauko, shi ko Lion ko a jikinsa, Areef ma dai bai wani kula shi ba, dan suma dukkansu kusan hakan suke ji. Shi Areef baya jin zai iya barci ba tare da ya kalli face ɗin Jehan ba, shi kuwa Lion barcin ne ma kwata kwata ba zai iya ba idan ba tare da Meesha ba, dan sun saba kwana gado guda da ita a cikin jirgin ruwa, Areef dai Allah ya taimaka dama bai taɓa kwana da ita ɗaki ɗaya ba. Shi kam Aseef na shi ai kun sani dama na daban ne, yanda suke kashe juna da love da shagwaɓa ko wani dare shi da Heartbeat nasa, yau kawai ta gudu ta barshi, ai ba zata saku ba........... E KAM BA ZATA SAKU BA, AMMA KUMA TA TAFI ƊIN😂YO ME RUWA NA NI? KO YA KUKACE MASU KARATU? ME RUWANMU? AI NAMU IDO.

A tare suka fara cin abincin suna hira sama sama, Areef ya fi sakewa ya biyewa gwaggo suna zuba hira, shi kuma Aseef sai wani kumbure kumbure yake yi, shi a dole ran maza ya ɓaci, Akila ta bijire umarnin miji. Lion kuwa ba sai na faɗa ba, kun sani, magana ce baya so.

A ɓangaren su Rimsha kuwa. Bayan sun isa gidan Abba ne daddynta ya ganta, faɗa sosai ya fara yi masu akan me za su baro mazajensu, su biyo su?. Kuka ta sakawa daddyn nata sosai, kuka ta gaske mai sauti da iya karfinta.

Nan take kowa ya fara tambayarta lafiya kuwa? Me ya sameta take kuka?.

Cikin kuka ta fara magana da iya gaskiyarta, tana yi tana kara sautin kukan nata. "Daddy wlh bana son yaya Saif, ni ba zan zauna da shi ba, ba zan sake zuwa in da yake ba, ba ruwana da shi, ba zan sake zuwa gidansa ba, dan girman Allah daddy kada kace na koma can, wlh zan mutu, ni bana son shi....." BABBAR MAGANA.

Bata gama rufe baki ba Akila ta karɓi zancen da cewa "Wlh nima daddy bana son heartbeat, ni kawai na dawo gidanmu, wlh ba zan koma ba".

Yau ga ikon Allah su daddy suna gani, sun ma rasa abin faɗe.

Jehan ce ta katse su da cewa "Ku da dama kuke sonsu kenan, ai ni dama tun ainahi bana son shi, daddy ne kawai ya wani kakaba mani shi, kuma wlh yanzu ba ni babu shi, ya san in da dare ya yi mashi". To fa, yau ga ikon god.

Ɗaure fuska sosai daddyn ya yi zai fara magana kenan Brr Naurat ta riga shi da cewa "To shikenan tun da baku son su, ku je ciki ku ku ci abinci, sai ku kwanta ku yi barci, da safe sai mu yi maganar ko". Brr Naurat akwai saurin gane abubuwa, ta gane me matsalarsu, dama ita da kanta ta yi danasanin labarin da gwaggon ta bayar a gabansu, ta san dama hakan zata iya biyowa baya, ta zan za su guji mazan nasu, dan za su yi tunanin irin abin da ya faru da gwaggon, abin da Dr William ya yi mata na cin amanar soyayyarsu, za su yi tunanin suma haka su Lion ɗin za su yi masu, tun da duk Turawan ne. TO FA BABBAR MAGANA, E DAMA DOLE ZA SU JI HAKAN AI, SABODA YANDA DR WILLIAM YA NUNAWA GWAGGON TSANTSAR SO DA KAUNA, DAGA BAYA YA CI AMANARTA, AI DOLE SU RIMSHA SU KARAYA, BARE MA ITA RIMSHA DA DAMA LION BAI TAƁA CEWA YANA SONTA BA, KUNGA KUWA AI DOLE TA GUDU DAN TA RUFAWA KANTA ASIRI, KADA TA FAƊA IRIN TARKON GWAGGO, SUN MANTA LAIFIN WANI BAYA SHAFAN WANI, SUN MANTA KOWA DA IRIN HALINSA, AMMA BA ZA KU GA LAIFINSU BA, SUNA A KAN GASKIYARSU NE❤️

Daddyn Rimsha ne ya ce "Mum zamu wuce dasu gidana na nan Kd, dama a gyare yake, nan gidan ya yi mana kaɗan, gobe da safe zamu zo". To Brr Naurat ɗin ta amsa mashi da shi, sannan ta kira shi gefe a in da ta gaya mashi kada ya yi wa su Rimsha tsawa ko faɗa a kan cewa da suka yi ba su son mazajensu, ya kyalesu zuwa gobe idan sun zo, ita zata yi magana da su. Okey ya amsa tare da yi wa su Abba sallama ya kwashesu, Rimsha, Jehan, da kuma Akilar, sai mum, suka wuce gidan nasa.

Daddyn Anaya ma, ya koma gidansa da iyalansa, saura su Abbi, daddyn jelly sai Abban, Aunty ma tana nan, ita kuma Hjy Hadiza tana gida. Sune suka kwana a gidan Abba tare da Brr Naurat, kwana suka yi suna ta zuba hira.

Su daddyn Rimsha kuwa, bayan sun isa gida, abinci daddy ya fita ya sawo musu, suka ci suka kammala, ko wacce ta yi wanka ta yi shirin kwanciya, da yake gidan yana da matuƙar girma, ga yelwar ɗakuna da abubuwan more rayuwa, sai kowacce ta wuce daɗinta daban, ita kuma mum ta bi daddy abinta, dan suna bala'in kewar juna.

Duniya dukka sun yi barci Rimsha da Akila sun kasa yin barci, kuka yarannan suke yi tamkar za su mutu, tun hawaye na fita, har ya dai'na fita, yanda suka ga rana, haka suka ga dare, ba barci, amma duk da haka sun ki yarda ko kiran mazan nasu a waya su yi, kashe wayar tasu ma suka yi, Lion ya nemi number Rimsha a kashe, shi ma Aseef ya kira Akila a kashe, ga shi gwaggo ta hanasu zuwa su ɗauki matan nasu, ta ce yau su hakura, haka suma suka kwanta cikin kaɗaici da kewar matan nasu.

Ita kuwa Jehan wlh ko a jikinta, barci ta yi har da manta a wani duniyar take, shar zuciyarta, ta bar Areef da kwana kallon hotonta bawan Allah.

KAI JAMA'A YARANNAN SU RIMSHA SUNA SHA'ANINSU WLH, WAI YAU RIMSHA CE ZATA CE BATA SON LION?🤔😂 A LALLAI KUWA, AKWAI KALLO GOBE, GA SHI DAI KWANA ƊAYA KAWAI TA KASA HAKURA, SAI KUKA TAKE YI, INA GA KUMA ANYI SATI? INA GA SAI GADON ASIBITI ZA'A WUCE DA ITA😂AMMA KUMA SUNA DA GASKIYA, SU TSARE KANSU, KADA ABIN DA YA FARU DA GWAGGO YA FARU DA SU, INA GEFE NI DAI!!! JEHAN KUMA ƳAR DUNIYA, KO A JIKINTA😂 KAI LITTAFIN TRIPLETS AKWAI ƳAN AIR WLH😂 SU HEARTBEAT MA DAI AN KASA BARCI😂 KO YA ZA SU YI GOBE IDAN SUKA FITO DADDYNSU YA KALLI IDANUNSU A KUMBURE SABODA KUKA? ME ZA SU CE IDAN AKA TAMBAYESU A KAN HAKAN?😂!!!.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E6




Washegari, kasancewar mum ta san babu kayan abinci a gidan, sai bata yi ƙoƙarin tashi ta haɗa masu breakfast ba, ta bari su je gidan Abba or restaurant su karya, kwata kwata ma bata fito daga daɗin daddyn ba, suna a tare manne da juna abinsu, su kuwa su Rimsha, sun ci uban kuka tamkar ransu zai fita, idanu sun kunbura luhu luhu, har wani ja suka yi ta kasar fatar idanun, Jehan ƴar gwaggo kuwa, ko a jikinta, bayan ta tashi ta yi sallar asuba, sake mayar da barcinta ta yi, hankalinta a kwance.

A ɓangaren Lion kuwa, kwana ya yi bai yi

Please Login or Register in order to submit comment