Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Ayla za'a barta, dan ciwon ƴa mace ta ƴa macece, dan haka Akila zata kuka da Ayla. Kuka sosai Aseef ɗin ya rinƙa zuba masu, amma suka ki kula shi. Daga karshe dai sai ya hakura ya wuce bedroom nasu shi da Areef ɗin.

Lion yana shiga cikin bedroom nasa, wanka ya sake yi, saboda tsananin zafi da rana da ake narkawa. Bayan ya shirya cikin ɗaya daga cikin kayan da ya saya, sai ya ɗebi baya kala biyu ya kaiwa su Aseef ɗakinsu, sannan ya wuce ya fita daga hotel ɗin.

Su kuwa, wanka suka yi, kowa ya tsabtace jikinsa, suka sanya kayan da Lion ɗin ya kawo masu. Suna gama shiri sai ga masu karɓar order abinci sun shigo. Kasancewar su sun saba cin abincin Naija, sun ci shi a wajen Rimsha, sai suka bada order fried rice, and pepper chickens, sai ruwa da Maltina.

Mai karɓar order ya amsa da okey sannan ya fita, yana fita ya faɗa ɗakinsu Mark, bayin Allah su basu taɓa cin abincin Naija ba, amma a yau basu da zaɓin da ya wuce dole su ci, kada yuwa ta illatar da su, haka suka bada order pepper cikin, dan suka ganin kamar shi ne zai fi masu.

A ɓangaren Akila kuwa, order jolof rice and chips ta bada. Haka mai karɓar order ya tattara kan order tasu ya koma abinsa.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya kawo masu duk abin da suka saka order. Dukkansu babu daɗi bakunasu, amma haka suka daure suka tsakuri abincin, dan kada yunwa ta kayar da su.

After some minutes, Areef ne ya fito daga bedroom nasu, ɗakinsu Akila ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, da yake shi ya fisu tausayi, Ayla tana a cikin ransa, yana ta tunanin halin da take a ciki, ya kasa samun sukuni, burinsa kawai ya zo ya dubata, ya kuma sa Lion ya nemo likitar da zai bata taimakon gaggawa da zai taimaki rayuwarta kada ta mutu kafin su karisa gida.

Kamar yanda ya kwantar da ita, haka ya shigo ya sameta. Yana shigowa bai kai ga karisawa cikin bedroom ɗin ba, Aseef ya shigo shima bakinsa ɗauke da sallama, hannunsa ruke da wata jibgegiyar leda da Lion ya sayowa su Akilar kayan sakawa a ciki.

A bakin bed ɗin dukkansu biyu suka zauna, Areef ya kai hannu ya taɓa Ayla, dan ya ji har yanzu akwai sauran rai a jikinta ne. Shi kuma Aseef ya miƙawa Akila ledar kayan yana faɗin "Yanzu Lion ya dawo ya kawo maku, ya ce ku shirya da wuri, helicopter zata zo ta ɗauke mu zuwa gida". Ya kai karshen maganar tare da miƙa mata ledar.

Karɓa ta yi tare da fara buɗe kayan, Abays ne a ciki, sai takalma. "Heartbeat zaki iya yi wa matar uncle wanka idan na kai maki ita cikin toilet?". Cewar Areef.

Da sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e zata iya, dan tun ɗazun take yi wa Ayalar kuka, Allah sarki, ba shakka Akila tana da tsananin tausayi kamar Areef ɗin, halinsu kusan ɗaya, dukkansu, kuma babu in da suka baro daddyn Rimsha a kamannin hali, kunga shi ma duk abin da ƴan uwansa suka yi mashi a duniyar nan bai sa ya ji cewa ba zai iya taimaka masu ba, to haka Areef da Akilar ma suke, shi Aseef yana da zuciya gaskiya, idan ka yi mashi abu ya taɓa mashi zuciya, to yana wahala ya mance da wannan abin, kuma shi ruwa biyu ne, wani lokaci yana da zafi sosai, wani lokaci kuma yana da sanyi, kun tuna time da suke Washington? Har su Uncle T bai kyale ba, to haka yake, idan ka yi mashi laifi, to ba zai yafe ba sai ya rama, ko kuma ya fita harkarka, ya zubaka a kwandon shara, shi kuma Lion ai ba wata zancen fita harka, hukunci zai baka mai kyau, daga nan kuma shikenan komai zai wuce, bashi da riko kamar Aseef.

Ɗaukar Aylar Areef ɗin ya yi ya kaita cikin toilet ɗin, already Akila ta haɗa ruwa mai zafi a cikin jacuzzi, yana zuwa ya sanyata a cikin jacuzzin, sannan ya fito ya fice daga ɗakinma gabaɗaya.

Yana fita wajen Lion ya nufa. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga bedroom ɗin, Lion ɗin yana zaune a bakin bed nasa yana aikin latsa waya.

Kusa da shi ya zo ya zauna yana faɗin "Ka yi magana da su momma ne?". Bai amsa ba, kuma bai ɗago ba, ya cigaba da abin da yake yi na tsawon lokaci, kafin nan ya ɗago kansa tare da kai kallonsa a kan Areef ɗin. "Where is your phone?". Yana gida ya bashi amsa.

Shiru ya ɗan sake shi kafin ya ce "A wajen waye wayar take? Momma or your wife?". Girgiza kai ya yi yana faɗin "In my room, kuma switch off nata ma na yi".

Okey ya amsa mashi da shi, sannan ya mayar da hankalinsa a kan wayar tasa, tun ɗazun number Rimsha yake kira, amma taki ɗauka, hasalima wayar tana a cikin bedroom nasa, ita kuma tana tare da Brr Naurat, dan taki yarda kowa a gidan ya taɓata sai Brr Naurat, ƙwaƙwalwarta sai kara birkice masu yake yi, abu kamar wasa yana neman ya zama babbar case, sam yanzu ta dai'na magana ma, idan ka tambayeta abu, sai dai ta zuba maka idanu kawai taka kallonka, Allah mai iko yau harta daddynta da mummynta bata sansu ba, abin ya yi mugun ɗaga masu hankali ba kaɗan ba, sun shiga damuwa na wuce misali, dan ma Brr Naurat tana kwanta masu da hankali ne, da abin sai ya fi haka, a takaice dai Rimsha bata leƙawa ko palo, ko da yaushe tana kwance a saman bed ɗin Brr Naurat, wanka ma Brr Naurat ɗin ce take yi mata, yanzu ta zama tamkar jaririya, wanka ma bata iya ba, in short ba wani abin da Rimsha ta iya a yanzu, common abinci Brr Naurat ce take bata a baki, duk taurin zuciya irin ta Jehan, sai da ta zubarwa da kanwar tata kwallah ba kaɗan ba, ta sha kuka sosai, saboda Rimsha dai ita kaɗai ke gareta, ita ce kawai kanwarta, duk wannan dirama da suke yi suna tsananin kaunar junansu na wuce misali, kawai Jehan ɗin ce dama da shegen iya tsare gida yasa Rimshar bata kusantar ta sosai, amma suna kaunar juna over.

Lion ya kira wayarta har ya gaji ya hakura. Hakika yana son yin magana da ita, saboda a jikinsa yana jin cewa bata da lafiya, ba lafiya take ba, dan duk lokacin da ya tuna sunanta, sai zuciyarsa ta harba, abin ya ɗan ɗaga mashi hankali, hakance ma tasa ya ce da His excellence ya sanya a turo masu jirgin helicopter kawai su koma gida da wuri, sannan da akwai abubuwansu da suka bari a airport na Enugu state, dan haka his excellence yasa ya mayar masu da shi gida. Burinsa kawai ya koma gida, da gwaggo da Rimsha sun tsaya mashi a cikin tunaninsa fiye da tunanin mai tunani.

A ɓangaren su Akila kuwa, Areef yana fita daga toilet ɗin Aylar ta farfaɗo, saboda ruwa da aka sanyata a ciki. Tana farfaɗowa ta fara zuba kuka babu kakkautawa, rarrashinta Akilar ta rinƙa yi, amma taki ta yi shiru, hakan tasa Akilar ta kyaleta ta yi mata wankar kawai, bayan ta gama ta tallafa mata ta fito, sannan ta ɗaura mata towel daga kirjinta, da kyar Aylar take iya jan kafarta har suka fito izuwa cikin bedroom ɗin. Ko da suka fito basu sami Aseef a ɗakin ba, ya fice abinsa. A bakin bed ta zaunar da Aylar, ta ciro kayan da Lion ya saya masu, tare da tallafa mata ta sanya a jikinta, sannan ita ma ta wuce toilet ɗin dan ta je ta yi nata wankar. Baiwar Allah Ayla, har kumbura face nata ya yi, ta yi wani iri da ita, gwanin ban tausayi.

A takaice dai sai misalin karfe 3 na yamma, sannan jirgin helicopter ya iso, basu ɓata lokaci ba wajen tafiya, Ayla dai sai ruwan hawaye take yi, cikinta tsananin ciwo yake yi mata, baiwar Allah bata taɓa jin azaba irin haka ba, dan cikin nata ba ƙaramin ciwo yake yi mata ba, shiyasa ma ta kasa daurewa har take kuka. Areef bawan Allah shi ya yi ta fama da ita, ya yi ta rarrashinta har suka dira a cikin Kaduna.

Already su Imran suna airport suna jiransu. Basu ɓata lokaci ba suka fito suka nufi gida, dan akwai majinyata sosai a tattare da su, shi kansa Lion ɗin kamata ya yi ace yana kwance a gadon asibiti, amma saboda dakiya da taurin zuciya tare da karfin imani, yasa ya dake, ya ki yarda ma kowa ya duba shi, ya ce sai ya dawo gida kawai.

Gabaɗaya family suna tsaye a harabar gidan suna jiran isowarsu, Rimsha, Jehan, Anaya, su ne kawai basu a cikinsu, suna ɗaki suna barci, Jehan da Anaya sun ci kuka sun ƙoshi ne har barci ya yi awon gaba da su, ita kuma Rimsha already kun san matsalar da take a ciki, an yi mata ruƙiya ma, amma shiru, farko sun ɗauka aljanu ne suka shafeta, sai da aka yi ta yin ruƙiya aka ji shirune yasa suka fahimci ba aljanu bane, wata matsala ce dai ta daban, dan haka sai suka kyaleta sai Lion ɗin ya dawo, dan sun san halinsa, kada su kira malami ko a kaita wajen magani ya dawo ya sauke masu kwandon aradu a kansu, dan ba ƙaramin aikinsa bane ya ce uban waye ya ce a taɓa mashi matarsa? Waye ya ce wani ko wata ya zo ya dubata? To gudun kwandon bala'insa ne yasa suka bar mashi kayarsa, ya zo ya san yanda zai yi da ita.

Suna dira a gida, Lion ne farkon da ya fara fita daga cikin motar, tun motar bata gama tsayawa a parking space bama ya fice abinsa. Sam bai bi ta kan kowa dake tsaye a wajen ba, cikin gida ya wuce abinsa, kai tsaye bedroom nasa ya wuce. Yana shiga ya nufi toilet, wanka ya yi a gurguje, sannan ya fito ya shirya cikin three cuter sky blue da singlet, singlet ɗin fara ce tas, tamkar yanzu ya cirota daga ledarta, abin da ya sanya ya saka singlet ɗin kuma, saboda ciwukan dake a kirjinsa.

A box ya ɗauko tare da zama a gefen bed nasa, dan hannunsa in da wuka ta yankar nan ba ƙaramar ciwo take yi mashi ba, hannun ta kumbura, kun san wuka da akwai dafi a jikinta, hakance tasa hannun ta kumbura sosai.

Family kuwa, cikin tsananin murna suka fara rungumar juna, kowa baki ya ki rufuwa, saboda tsantsar farinciki. Areef yana ɗauke da Ayla a saman kafaɗarsa, bai wani tsaya a wajensu ba, sai ya wuce izuwa cikin gida kawai, dan ya kwantar da ita, ta huta.

Gabaɗaya family sun sha matukar mamakin ganin Aseef a tare da su, sai dai kuma sun kasa iya tambayarsa ya aka yi hakan? Ga tambayar a cikin ransu, amma ta kasa fitowa fili, abin ya ɗaure masu kai, amma haka suka hakura suka daure.

Sai rungumar Dr Salman suke yi tamkar za su mayar da shi cikinsu, Brr Naurat har da ruwan hawaye, sai tsiya su Imran suke yi mata.

Shi ma Dr Salman ɗin ya sha kuka ba kaɗan ba, dan bai taɓa tunanin familynsa suna a raye ba, ya yi zaton komai ya kare ya lalace masu, ashe dai sunanan, sun zama taurari zakarun gwajin dafi ma a cikin al'umma, wannan abin ya yi mugun sanya shi farinciki wanda baki ba zai iya furtata ba. Haƙiƙa farincikin da wannan family suke ciki a yau, sam baki ba zai iya furtata ba, ya wuce misali.

Haka Dr Salman ya rinƙa yin kuka yana faɗin kowa ya yafe mashi, ina Nawazuddeen ɗinsa? Dan Allah Nawazuddeen ya yafe mashi. Anyi anyi ya yi shiru yaki yi, ya ce har sai Nawazuddeen ya yafe mashi. Haka daddyn Rimsha ya rungume shi yana faɗin. "Daddy ni baka yi mani laifin komai ba, idan ma kayi, to ni na yafe maka, ban taɓa ji a ra'ina kamar ka taɓa yi mani laifi ba, kullum cikin yi maka addu'a da fatan alkhairi nake yi, dan Allah ka dai'na kukannan kada ka saka muma muyi kukan".

Sosai Dr Salman ɗin ya rubgume shi yana mai cigaba da matsar kwallah. Da kyar suka samu suka lallaɓa shi ya yi shiru, a tare suka rankaya izuwa cikin gida, kai tsaye bedroom na Lion suka nufa, while shi kuma Areef ya kai Ayla ɗakin gwaggo ya kwantar da ita a kusa da Rimsha, sannan shi ma ya fito izuwa bedroom ɗin na Lion ɗin.

Lion yana zama a bakin bed ɗin nasa yana ƙoƙarin fara duba hannunsa, sai ga family gabaɗaya sun shigo cikin ɗakin, duk sun biyoshi, gabaɗaya fuskokinsu ɗauke yake da tsantsan annuri da farinciki, yau Dr Salman ya dawo cikinsu, ga shi ba su rasa ko mutun ɗaya ba a cikin ƴaƴan nasu, abin ba karamar daɗi ta yi masu ba. Sun shigo ne dan su duba lafiyar Lion ɗin, dan kunga shi bai tsaya a wajen nasu ba, suna sauka ya wucu bedroom nasa kawai.

Kallo ɗaya Lion ɗin ya yi masu ya kawar da kallonsa gefe guda, ya cigaba da aikin da yake yi.

Ganin abin da yake ƙoƙarin yi na yiwa kansa magani ne yasa gwaggo da Areef suka kariso kusa da shi da sauri. A tare suka zauna a gefe da fefensa, suka sanya shi a tsakiya kenan.

Gwaggo ce ta fara karɓar A box ɗin tare da kama hannunsan tana dubawa, ba shakka ya ji ciwo sosai. A hankali ta ɗago da kallonta a kansa, hannu ta kai ta shafa lallausan kumatunsa kafin ta ce "Let me do something". Shiru ya yi bai yi mata magana ba, ya dai zuba mata idanu, shi ya mance da cewa ita ma babbar likita ce kamar daddynsu, sai da ta ce bari ta yi mashi wani abin ne yasa ya tuna ashe ita ma babbar likita ce sosai, dan haka sai ya miƙa mata hannun ya bita da idanu kawai.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara yi mashi aiki, duk wani magani da zata zuba mashi sai ta ɗago kai ta ce mashi sannu, dan tasan da akwai bala'in zafi ba kaɗan ba, bare kuma yanda hannun ta ɗauki lokaci, ta jiƙa sosai ciwon, dole zai sha zafi, sai dai kuma shi wayarsa ma ya ɗauko yana latsawa da hannu ɗaya, a cewarsa duk zafinta bata kai harbin bullet zafi ba, dan haka shi bai ga abin cewa da zafi a nan ba.

Haka gwaggo ta yi mashi treatment na wajen da kyau da kyau, sannan ta ce ya kwanta bari ta duba lafiyar jikinsa gabaɗaya. Sai sannu family suke yi mashi, sam bai ɗaga idanu ya kalli ko mutun ɗaya daga cikinsu ba, dan yana cikin wani irin yanayi wanda shi kaɗai yasan me yake ji bawan Allah, da yake shi kullum a siffa ɗaya yake ne yasa sam sam ba wanda ya gane cewa yana cikin tsananin damuwa, kullum face nasa a haɗe take, baka gane farincikinsa bare bakin ciki, harta TRIPLETS nasa ma basu iya rabe yana cikin farinciki ko bakin ciki, saboda kullum dai yanda yake a haka yake babu canji.

Bai yi wa gwaggo musu ba, ya miƙe ya kwanta a saman bed ɗin da kyau, dan a agajiye sosai yake. Duba lafiyar jikinsa ta fara yi ita da Areef, ya rufe idanuwansa yana tunanin duniya.

"Momma where is Meesha?". Kamar daga sama su gwaggo suka ji sanyayyar muryarsa ya gefo masu wannan tambayar, ya yita kuma idanuwansa a lumshe.

Kallon kallo jama'ar cikin bedroom ɗin suka fara yi, ita kanta gwaggon sai da gabanta ya faɗi na jin tambayar nan tasa. Ganin yanda suke kallon kallo a tsakaninsu ne yasa Aseef da Areef har suna haɗa baki wajen cewa "What is happening? Where is our Rimsha? Ya naga kuna ta kallon juna, is there any problem?". Kamar abin haɗin baki suka jera masu tambayoyin, Areef kam har da mikewa tsaye yana binsu da kallo, dan wlh idan wani abin ne ya sameta yau za'ayi yaki ba kaɗan ba, saboda ita ɗin tamkar bugawar zuciyar TRIPLETS ɗin take, dukkansu ukun suna tsananin sonta fiye da tunanin mai tunani, akwaita da mugu mugun shiga rai na wuce misali ne.

Kara datse idanuwansa gam Lion ɗin ya yi, kansa na yi mashi ciwo sosai, yana jin duk abin da suke faɗa, amma ya kasa buɗe idanuwansa, dan ƙwaƙwalwarsa ba zata iya ɗaukar wani abin ya sami Rimsha ba, shiyasa ma ba zai buɗe idanu ba bare ya ga fuskokin family su kara jefa shi cikin wani raɗaɗin.

"Areef nothing happened to her, just she is not feeling well, tana ma cikin bedroomna tana kwance, she is sleeping now". Cewar gwaggon kenan.

Kusan a tare Aseef da Areef ɗin suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da sauri Aseef ya ce bari ya je ya ganta ya tabbatar. A tare suka fita da Areef ɗin dan su je su dubata. Ita kuma gwaggo, sai ta cigaba da duba ɗan nata, Dr Salman ne ya ce su fita su bar Lion ɗin ya huta, dan ya gaji matuƙa. Haka kuwa aka yi, duk suka fita, ita ma gwaggon da ta gama yi mashi duk abin da ya dace, sai ta fita ta kyale shi, yana jin fitarta, amma bai ce mata komai ba, saboda yana da bukatar ya huta ɗin ne, ga salloli na la'asar da mangariba a kansa bai samu ya yi ba. Ransa cike da tunani barci ya yi awon gaba da shi, bawan Allah ya yi matuƙar gajiya na wuce misali, dole ne ma barci ta ɗauke shi.

A ɓangaren Aseef da Areef kuwa, da suka je suka tabbatar yes Rimsha tana nan tana zuba barci, sai suka ji wani irin sanyi da salama ya lulluɓesu. Hakan tasa suka zauna a bakin bed ɗin na gwaggon suna ɗan tattaunawa a tsakaninsu. A gabaɗaya cikin family an rasa wanda zai iya tambayar Aseef ya aka yi ya je shi Daular Mutuwa? Ga dai tambayar a cikin ran kowa, amma sun kasa fito da ita fili. To meye dalili? Alƙalamin PRINCESS TEEMA ce kawai zai iya rubuta maku dalilai, dan haka ku biyoni!!

A nan family suka shigo suka samesu. Da mamaki ɗauke a fuskar gwaggo take tambayar Areef ɗin me ya sami Ayla kuma?.

Kallon daddyn Jelly Areef ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye, cike da tausayi ya ce "Sorry uncle, ta yi loosing pregnant nata ne, momma ki bata taimakon gaggawa, dan babu abin da muka yi mata, babu wani drugs or injection da yake a tare da mu, so tana cikin mawuyacin halin, help her". Ya kai karshen maganar tare da sa kai ya fice daga ɗakin, a lokacin ita ma Jehan ita da Anaya duk suna bedroom nasu suna barci, sun ci kuka ne sun ƙoshi, har barcin wahala ta yi awon gaba da su bayin Allah.

Haƙiƙa gwaggo ta tausayawa Aylar na ganin halin da take a ciki, dan haka sai ta ce Aseef ya kawo mata kayan aikinsu bari ta dubata, daga nan kuma ta yi wa daddyn Jelly ban hakuri. Kowa daga cikinsu Abba sai da ya bashi hakuri. Ba shakka ya ji zafin fitar cikin na Ayla, dan yana tsananin son yara, Jelly kaɗai gare shi, ita ma ta yi aure, so yana tsananin kaunar yaga ya sake samun yara, amma kuma farincikin dawowar Aylar ta fi yawa a cikin zuciyarsa sama da zubewar cikin, kuma shi dama mutun ne mai yarda da ƙaddara, dan haka ya yarda da ƙaddararsa, ya kuma rungumeta hannu bibbiyu, ya ce babu komai, haka Allah ya ƙaddara, dama ai ba su suka bawa kansu cikin ba, Allah ne ya basu, dan ya karɓi abinsa ba zasu ji babu dadi ba, shi ya godewa Allah ma da yasa ta dawo gida da ranta, iya wannan ma ya ishe shi murna, kuma dole ya godewa Allah da yadawo mashi da ita da ranta.

Da haka Brr Naurat ta ce kowa ya je ya yi sallar issha, tun ɗazun aka yi sallah su suna nan suna zaune. Haka suka watse kowa ya nufi bedroom nasa, dan su je su yi sallah, Dr Salman kuma suka tafi tare da Akil, ita kuma gwaggo Aseef ya kawo mata kayan aiki ta fara duba lafiyar Aylar, dan ta lura sai anyi mata wankin ciki ma.

Bayan ta gama sai ta yi mata alluran barci dan ta sami hutu. Daga nan ita ma ta mike ta fita izuwa bedroom nasu Jehan dan ta yi sallah, ta bar Brr Naurat tare da Aylar da Rimshar.

Tana shiga bedroom ɗin ta tarar da Areef zaune a saman bedside drawer kusa da Jehan, ya zuba mata idanu yana ta kallonta, ita kuma tana zuba barci, ya yi wanka ya canza kayan jikinsa izuwa na barci, da alama ya yi sallah ya ci abinci.

"In tasan maka ita ne Areef?." Cewar gwaggon, ta yi maganar tana nufar hanyar toilet dan ta yi alwala. "A'a momma ki barta, i want to see her ne ma kawai yasa na zo dubata, na yi missed nata over, yau ina gajiye sosai, ba zan iya da rigimarta ba, dan haka kyaleta sai da safe". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa, ko kunyar gwaggon bai ji ba ya ɗan duka ya sumbaci Jehan ɗin a kumatu, sannan ya juya ya fice, ita ma gwaggon ko a jikinta ta shige cikin toilet abinta.

After some hours, gabaɗayansu sun yi barci, dan a tsananin gajiye suke, family kowa yana cikin bedroom nasa yana zuba barci, masu aikin dare suna yi, yau suma family za su yi barci a cikin salama, dan tun da TRIPLETS suka tafi basu samun barci mai kyau, a kaikaice suke yin barcin, to yau za su sami barci mai cike da daɗi.

Misalin karfe biyu yunwa ta farkar da Jehan, dan bata ci abincin dare ba ta yi barci, fitowa ta yi izuwa palon kasa, abinci ta ɗebo a plate, sam bata da labarin mijin nata ya dawo, komawa palon sama ta yi ta zauna a saman sofa, cikin nutsuwa ta fara cin abincinta tana yamutse fuska tamkar mai cin magani, ita kuwa Anaya sai zuba barci take yi, ita bata farka ba. Kamar daga sama ta ga Lion ya fito daga cikin bedroom nasa sanye da farar jallabiya a jikinsa, sai yanzu ya samu ya biya bashin sallolin dake a kansa, tun da ya yi barci sai karfe 1 ya farka, wanka ya yi tare da ɗauro alwala ya zo ya fara biyan bashin sallolin dake a kansa, bayan ya kammala ne ya fito dan ya je ɗakin gwaggo wajen Meesha.

Ba karamar tsorata Jehan ɗin ta yi da ganinsa ba, da farko ma ta ɗauka aljani ne, saboda dare ne kuma ga shi da farar jallabiya, bugu da kari bata san sun dawo suna gidanba, sannan ya saki dark black cuirly hair nan nasa bai ɗaure ba, ga shi da tsawo sosai dama, ai dole ya bata tsoro.

A dubu ɗari ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin kurma ihu, sai gani ta yi ya shige ɗakin gwaggo bai ko kalli in da take bama, hakan yasa ta fahimci lallai sune suka dawo, dan haka sai ta ajiye plate ɗin abincin nata, da sauri ta sauka kasa izuwa bedroom na Areef.

Babu ko sallama ta faɗa cikin ɗakin, wani irin duhu ne a cikin ɗakin, kun san shi baya shiri da haske dama, idan zai yi barci a duhu yake yi, hakan tasa bata iya ganin komai, lallaɓawa ta yi a hankali ta nufi wajen switch, da kyar ta gano switch ɗin ta kunna wutar, nan take haske ya gauraye ko'ina a cikin bedroom ɗin.

Cike da tsohon abin da zata iya cin karo da shi a saman gadon ta ɗago kanta, a hankali ta kai kallonta wajen. Yana kwance cikin kyawawan kayan barcinsa yana zuba barci abinsa, ya rungumi pillow a kirjinsa, ya kuma ɗaura kafafunsa a saman pillow ɗaya. Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, ta kasa motsawa daga wajen, ta zuba mashi idanu sai kallonsa take yi.

Saboda wannan haske da ta kunna mashi ne yasa ya ɗan fara motsawa yana son farkawa, ganin hakan yasa ta yi maza ta kashe wutar tare da juyawa

Please Login or Register in order to submit comment