Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙoƙarin shiga dressing room na ɗakin ya bata amsa da cewa yana jinta.

"Na ji gwaggo ta ce yaranta masu blue eyes irin naka su biyu ne, amma kuma naga kai kaɗai ne a cikinku mai blue eyes".

Cak ya tsaya, ya fasa shiga cikin room ɗin, a dubu ya juyo da kallonsa a kanta.

Zaro idanu ta yi, jikinta har ya fara kerma, dan tana tunanin ta faɗi abin da ya ɓata mashi rai ne. Shi kuma mamakin ta yake, ya sani a gabaɗaya cikin palon, gabaɗaya waɗan da suke wajen time da gwaggon ta bada labarin, babu wanda ya lura da zancen da gwaggon ta ce na cewa masu blue eyes biyu, dan da sun lura, dole zasu tambaya, amma saboda kaifin ƙwaƙwalwa irin na Rimsha, ita har ta rike cewa su biyu ne masu blue eyes, lallai akwaita da basira, wato tun jiya ma abin yana cikin ranta, ta rasa waye zata gayawa ne kawai.

"Kayi hakuri Noorish, ban ɗauka maganar zata saka ka ji babu daɗi ba". Girgiza mata kai ya yi yana faɗin "No baki ɓata mani rai ba, you are special My Meesha". Ya kai karshen maganar tare da karisa shiga cikin room ɗin.

Shiru ta yi tana tunani, har ya fito sanye da jallabiya fara kal a jikinsa. "Let's go". Ya faɗa tare da miƙa mata hannu alamar ta zo gare shi.

Da sauri ta diro kasa daga saman bed ɗin, a hanzarce ta tafi ta faɗa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. "Meesha pray for me more kin ji ko?". Yana magana yana shafa kanta izuwa bayanta.

Gyaɗa mashi kai ta yi tana faɗin "In Sha Allah mijina, addu'a sosai zan yi maka". Hannunta ya riko tare da ɗan raba jikinsu, har lokacin idanuwansa suna nan jajir da su, yau ya so ya yi romancing nata over, amma kuma tasa ya tuna da wani abin, dole ya je ya aiwatar da abin da wuri, dan dama tun jiya abin da yake ta tunani a kansa kenan, yanzu tasa ya samu kaso talatin cikin ɗari na abin da yake nema.

Da sauri ya nufi hanyar fita daga ɗakin hannunsa na ruke da nata. Mamaki take yi a kan meya faru yake sauri haka.

Bai zame ko'ina ba sai ɗakin gwaggo. Zaune ya iskota ita da Aseef, sai kukan shagwaɓa yake zuba mata, ya haye mata gado tare da tada kai da cinyarta, shi dole sai an ɗauko mashi matarsa, ta ce ya yi hakuri tun da sun kira Areef a waya ya ce zai zo da ita, to ya dai'na kuka zata dawo, kwafa ya yi tare da gayawa gwaggon Allah yau ba zai kyale Heartbeat ɗin nan ba, sai ya bata wahala fiye da tunanin kowa, ita dai gwaggon, sai rarrashi kawai take yi.

A gefenta ya zauna, tare da zaunar da Rimshar a gefensa. Cikin sanyin murya ya ce "Momman i want to ask you something!".

Dawo da kallonta a kansa ta yi tana faɗa mashi tana jinsa.

"Momma a wani gidan kaka ɗaya kika kaiwa daddy mu time ɗin? And them a wani gida kuka zauna da Josephine?".

Ba tare da ɓata lokaci ko wani dogon tunani ba ta bashi amsa kai tsaye, dan bata manta komai ba, komai yana nan a cikin brain nata.

Wayarsa ya ɗauko, cikin sauri ya kira Tyrone, dan dama already Tyrone ɗin ya koma shi kam. Bugu ɗaya ya ɗaga, ba tare da ɓata lokaci ba ya ce mashi ya je gidan da su Dr William ɗin suka zauna, dan gidan yana nan yanda yake, babu abin da aka taɓa a ciki tsawon shekarun nan, sai ma zuwa da ake yi ana gyara shi kowani sati, so komai yana nan normal, dan haka Tyrone ya je gidan da akwai camera a palon gidan, ya ciro mashi camerar yanzun nan, ba tare da ɓata lokaci ba, sannan ya shiga ainahin computers room da yake cikin gidan, ya duba stories, ya ɗauko mashi memory na shakaru 31 zuwa 32 baya.

Okey Tyrone ya amsa da shi. Katse kiran ya yi tare da miƙewa ya nufi waje, bin shi da kallo dukkansu suka yi, harda Rimshar.

Sai bayan ya fita ne Rimshar ta ce "Yaya Aseef ni ka tashi mani a saman cinyar gwaggona zan kwanta".

Kin kulata ya yi, sai aikin tura baki yake yi abinsa. Gwaggon ce ta ce mata ta zo ta kwanta a gefe, ta rabu da Aseef ɗin nan, rigima yake ji dashi, yanzu ya tashi barci, ko breakfast bai yi ba, ya tsayar masu da rigimar sai an ɗauko mashi Akila.

Tuna cewa Lion bai ci komai bane yasa ta miƙe tare da cewa Gwaggon a'a tana zuwa dai.

Ɗakin da suka fito ta koma, abinsa ta ɗauko mashi, sannan ta dawo cikin bedroom nasa. Zauna a saman bed ta iskosa, ya sanya laptop a gaba yana ƙoƙarin kunnata. A saman carpet ta ajiye abincin, sannan ta dawo kusa da shi ta zauna.

A tsananin shagwaɓe ta ce "Noorish, idan baka jin yunwa, Meeshan ka fa tana jin yunwa, ban fa ci komai ba, kuma ni da kai nake son muci abinci".

Yanda ta yi maganar tasa bai san time da ya juyo gateta ba. Yana juyowa ta faɗa jikinsa tana zuba mashi shagwaɓa.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, wani irin sanyi ya ji a ransa, hannu ya kai ya shafi kanta, ƴar karama da ita, amma ta samu tarbiya sosai, ta kuma iya soyayya sosai, duk fushi da halin mara daɗi da mutun zai shiga, ta san ta yanda take kwantar mashi da hankali, yanzu ga shi dai a kage yake da ya fara binciken nan, har ya mance da cewa yana jin yunwa, amma daga zuwanta, ta zuba mashi shagwaɓa, har ya ji yunwar ta dawo sabuwa, sai ya ji hankalinsa ya kwanta sosai.

"Muje to na baki abincin a baki ko?". Ya faɗa a sanyaye. Da sauri ta ɗago kanta, tana ƙoƙarin ta yi magana, sai ga Brady ya shigo ɗakin da gudu. Kai tsaye ta kanta ya bi ya haye jikin Lion ɗin, da alama bai ma lura da ita ba.

Ihu ta zunduma tana ƙoƙarin ta gudu, rikota da sauri ya yi, sannan ya dakawa Bradyn tsawa a kan ya sauka mashi a jikinsa, zai haukata mashi ƙwaƙwalwar Meeshansa, yasa tana zunduma ihu haka.

Haushi Bradyn ya daka masu, irin ya ji haushin nan shi ma. Hannu Lion ɗin ya ɗaga zai mare shi, ai a dubu ya diro kasa, da gudu ya nufi waje, dan ya san marin Lion fa ba wasa ba, ya taɓa marinsa sau ɗaya, a lokacin ya yi mashi ɓarna, ya kuwa wanke shi da mari, to shi ne har yanzu bai mance da marin ba, da Lion ɗin ya kara marinsa, gara ya gudu abinsa.

"Kin cika tsoro Meesha, Brady is your friend, ki dai'na tsoronsa, babu abin da zai yi maki, kuma shi ba zai dai'na shigowa nan at anytime ba, yakamata ki saba". Ya kai karshen maganar tare da ruko hannunta suka mike tsaye.

Wajen abincin suka nufa. Ita ta zuba masu abincin a plate. Spoon ya ɗauka tare da ɗebo abincin, yana ƙoƙarin kaiwa bakinsa, ta yi maza ta kwace tare da fara tauna. Ko sannu bai ce mata ba, ya sake ɗebo wani ya kai bakinsa. Haka suka cigaba da cin abincin cikin nishaɗi da tsantsar farinciki.

A ɓangaren gidan Abba kuwa, bayan sun tashi da safe, su daddyn Anaya sun zo, haɗuwa suka yi a palon gidan Abba, sai hira suke yi, suna jiran gwaggo da TRIPLETS nata, sai daddyn Rimsha, zasu yi magana ne a kan abubuwan da suka faru a baya.

Sai hira suke zubawa kamar ba gobe. Can wuraren karfe 12, daddyn Rimsha, mummy, Areef da kuma Jehan da Akila suka zo gidan. Nan fa hira ta kara armashi, abin ba kama hannun yaro.

Brr Naurat ce ta dakatar da su ta hanyar gabatar masu da Alex duk da cewa baya wajen, yana gidan Lion, a kage suke da son ganinsa, amma bai zo ba, yana tare da Mark.

"Zahradeen ina matanka da ƴaƴanka?". Cewar Brr Naurat, ta tambayi Abbi kenan. Cikin girmamawa ya nuna mata, Aunty, Irfan, da kuma Umaisha da take a wajen, sai ya rufe da cewa Aafia tana gidan mijinta.

Murmushi Brr ta yi tare da zuba masu addu'a da ruwan albarka, sannan ta tambayi Abba ma, shi ma haka ya gabatar da nasa matar da ƴaƴan, haka shi ma ta zuba masu addu'a, sai da ta bi gabaɗaya ƴaƴan nata ta tambayesu, daddyn jelly shi ne na karshen da ta tambaya.

Kallon Jelly dake zaune kusa da Ammie ta yi shiru kamar wata mara lafiya ya yi, cikin sanyin murya ya ce "Wannan ita ce kaɗai ƴata, Allah ya yi wa mahaifiyarta rasuwa, sai matar da na aura a yanzu". Ya kai karshen maganar yana juye juye dan neman Ayla, bata a wajen sam.

Fuska ɗauke da mamaki ya ce "Sadiya ina Ayla take?". Da sauri Aunty ta ɗago kai tana ƴan waige waige, sam babu ita a cikin palon. Tambayar juna suka fara yi, kowa yace tun safe shi bai ganta ba. Abba ne ya ce jelly da Akila su tashi su je su dubata a ɗakunan gidan, wata kila tana can tana barci ne saboda ciki.

A hanzarce suka miƙe suka haura sama. Suna tafiya Abbi ya ce "Hossain me ya sami Akila a idanunta kuma?".

Girgiza kai daddyn Rimsha ya yi yana faɗin "Kuka ta yi mana". "Kukan me kuma?". Daddyn jelly ya tambaya da sauri. Zai sake yin magana su Akilar suka sauko suna gaya masu bata cikin ɗakun dukka sun duba, har a cikin toilet dukka sun duba bata ciki. Nan fa hankulan kowa ya tashi, wannan ya kalli wannan, wannan ma ya kalli wannan.

Kasancewar da turanci suke magana, sai Areef ma ya saka masu baki, dan ya ji komai da suka ce, da turanci suke yin magana, saboda Brr Naurat bata wani iya hausa ba, Hausan nata a kwaɓe yake, dama bata iya shi sosai ba, sai kuma ta sake komawa ƙasar Russia tsawon shekaru, hakan tasa ɗan Hausar da ta iya ma shaf ta gudu daga bakinta, shi ne yasa suke magana da English.

Mikewa suka yi gabaɗayansu, harabar gidan suka fito, duk suka rarrabu aka fara nemanta. Amma ina, shiru, babu ita babu alamarta, nan take mamanta ta fara kuka, dan ita ma tana wajen, daddyn Jelly tamkar zuciyarsa zata fashe, amma ya daure suka cigaba da nemanta.

JAMA'A INA AYLA TA SHIGA⁉️

Shiru shiru fa babu ita, Areef ne ya tambayi daddyn Jelly a kan ko ta ce mashi zata je wani waje ne ya hanata, shi ne ta yi tafiyarta, nan fa ya yi masu bayani, ita Ayla bata da kowa, bata san kowa ba face su Abbi, sai su Rimsha, kuma ko harabar gidansu bata taɓa fita ba tare da shi ba, kullum tana ɗaki abinta, idan kunganta a waje, to a tare suke za su fita unguwa, ita ko waya ma yanzu bata da shi, saboda cikin nata ma ya tsani ana latsa waya a kusa da ita, dan haka in dai Ayala bata gidan nan, to wlh hannu ne ya ɗauketa, tabbas ɗaukarta aka yi!!. Tashin hankali!!!

Shiru Areef ɗin ya yi kafin ya sake cewa "To waye kake tunanin zai ɗauketa? Shin kana da abokin gaba na bayyane ne?".

Jinjina masu kai ya yi yana faɗin "Baban Muneer, shi ne kawai abokin gaba na wanda ya yi niyar ɗauke Jelly ya haɗata aure da Muneer a lokacin baya, to bayan shi kuma, ni bani da wani abokin faɗa".

"Waye baban Muneer ɗin? Kuma a ina yake?". Areef ya sake tambaya.

Kasancewar daddyn bashi da burin da ya wuce yaga matarsa ta dawo, sai ya basu labarin tsamar da take a tsakaninsu da baban Muneer ɗin, bai ɓoye masu ba, harda videon da ya yi mashi na sharri duk ya gaya masu.

"Aina yake to yanzu?". Areef ne ya sake tambayarsa, nan ma basu amsa ya yi da shi dai a Kano ya barosa, so bai san a ina yake ba yanzu.

Kallon Imran Areef ɗin ya yi yana faɗin "Zamu je wajen yanzu ko prof?". Jinjina mashi kai Imran ɗin ya yi.

Nan take hankulan kowa ya kara tashi, ganin da gaske Ayla fa ta ɓata ne, babbar magana.

Areef, Imran, da kuma Irfan ne suka nufi Kanon tare da tallafawan daddyn Jelly da ya basu number wayar babban yaronsa, wato engr Muhammad Imam, a kan idan sun je Kanon su nemesa, zai yi masu karin bayani a kan wanene Baban Muneer, zai ma kaisu har companynsa. Da farko daddyn Jelly ya ce da wuya idan baban Muneer ɗin ne ya ɗauketa, dan shi a Kano yake, sai da Areef ya gaya mashi cewa, ai zai iya turowa a ɗauko mashi ita, dan wlh mai son abinka, ya fi ka sanin hanyar kula da shi, dan ya ɗauka, shi ne sai hankalinsa ya yarda a kan hakan.

Da kyar Abba ya lallaɓa matan suka koma cikin palo, su kuma mazan, wato su Abbi, sai suka fita gari nemanta, ko Allah zai sanya a ganta, daga nan su kai report station da sauransu........NIMA PRINCESS TEEMA INA TAYAKU DA ADDU'AR ALLAH YASA A GANTA ƊIN, AMMA ƁATAR AYLA BA KARAMIN ABU BANE, DAN DOLE DAI HANNU NE YA ƊAUKETA, SABODA BAIWAR ALLAH NAN KO HARABAR GIDA BATA FITA, TO WAYE YA ƊAUKETA? ALLAH SARKI, GA KARAMIN CIKI, GA UBAN LAULAYI.

A ɓangaren Lion kuwa. Bayan sun kammala cin abinci, Rimsha ta kwash kayan abincin ta fitar, ta gyara wajen tsab, sai ta dawo ta haye saman bed nasa, a kusa da shi ta kwanta, tare da lumshe idanu, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita, saboda daren jiya bata samu damar runtsawa ba.

Shi kuma Lion, yana can yana aikin latsa laptop nasa, Tyrone ya ɗauko mashi wannan memory da camera ta naɗi komai, sai dai, da kyar aka samu memoryn, dan ma dai babu nai shiga gidan nan, kuma dama ana ajiye storyn camera irin haka sosai, so suna nan a ɗakin computers ɗin, an dai ci kwakwa ne kafin a nemosu.

Miƙewa Lion ɗin ya yi tare da ficewa daga bedroom ɗin. Ɗakin gwaggo ya koma, tambayarta ya je ya yi a kan zata iya tuna ranar da abin ya faru a tsakaninta da Dr William, ma'ana ranar da ta kai mashi TRIPLETS ɗin gidansa. Cikin sauri ta ce ai bazata taɓa manta wannan rana ba, biyu ga watan biyu ne.

Jinjina mata ya yi da ƙoƙarinta na ruke komai na tsawon shekaru a kanta, sannan ya juya ya koma bedroom nasa. Cewa Tyrone ɗin ya yi da ya saka memoryn a laptop, ya duba mashi videon biyu ga watan biyu a shekaru 32 baya.

Okey ya amsa mashi tare da fara aikin babu kama hannun yaro. Cikin ƙanƙanin lokaci ya samo video ya turowa da Lion ɗin.

A hanzarce ya buɗe video, dan dama jira kawai yake yi. Shiru ya yi ya zubawa video idanu yana ganin komai kamar a gaske a gabansa ake yin komai. Tun daga shigowar gwaggon gida, tun wayewar garin ranar, har shigowar gwaggon da TRIPLETS ɗin, yanda ta faɗa, ga yanda ta kwantar da su a saman sofa, komai da komai yana gani kamar a zahiri.

Dai'dai lokacin da Dr William ya bugawa jariri ɗaya santa, sai da Lion ɗin ya datse idanunsa, saboda har cikin ransa ya ji saukar wannan sandar, babu irin azabar kalolin kisa da Lion bai gani ba, amma ba zai iya jure gani ko ɗan ƙaramin bulala ne ya taɓa TRIPLETS nasa ba, shiyasa lokacin da ya ga Dr ya kwalawa ɗaya ɗaga cikinsu sandar, sai da zuciyarsa ta amsa, ji ya yi tamkar shi aka bugawa.

A hankali ya waro idanunsa ya cigaba da kallon video, yana ganin gwaggo ta fice waje da gudu, shi kuma Dr William ya yi kan yaran da gudu bayan ya jefar da sandar, ita ma Josephine da gudu ta kariso cikin palon.

Ɗaukar jaririn Dr ya yi, da gudun gaske ya nufi waje da shi, sai zubar da jini kansa yake yi, kai tsaye asibiti ya nufa shi da Uncle Herry, ita kuma Josephine, kan sauran jarirai biyun ta nufa, da sauri ta ɗauko ɗaya ta ruke a hannunta tana shafa ɗayan da yake kwance a saman sofar da hannunta, dan ta tabbatar da lafiyarsu.

Sai ruwan hawaye take yi. Kamar daga sama wani mutun ya faɗo cikin palon, wani dogo da shi, yana sanye da bakaken kaya, long cut ce baka a jikinsa, daga ta cikin kuma T-shirt ce mai karamar hannu, ita ma baka, ya sanya wata hula mai gashi a kansa, fuskansa na a sanye da black mask, hannayensa dukka biyu suna sanye a cikin hands gloves bakake kirin suma, kafarsa na'a sanye cikin Booth baka kirin, baka iya ganin komai na daga jikin mutumin nan fa ce idanunsa da suke ashe color masu tsananin haske kamar glass, tamkar ba na mutun ba.

Hannunsa na ruke da jariri sabon haihuwa cikin towel baka kirin, ga jaririn fari kal da shi, kasancewar yana jikin bakar towel ga shi fari kal, sai ya haska sosai.

Kai tsaye Josephine mutumin ya nufa, yana zuwa ya miƙa mata jaririn da yake a hannunsa, karɓa ta yi, ita kuma sai ta miƙa mashi ainahin cikon TRIPLETS da yake a hannunta, tana yi tana shafa kan baby ɗaya da yake kwance. Juyawa mutumin ya yi da ainahin cikon TRIPLETS ɗin a hannunsa, ta kofar da ya shigo, ta nan ya fita, ita kuma Josephine, sai ta cirewa jaririn da mutumin ya kawo waɗan nan bakaken kayan da suke jikinsa, sai ta ɗauko wani towel fari daga cikin ɗaki ta rufe shi da shi, sannan ta kwashi bakaken kayan ta nufi waje da su.

Jim kaɗan ta dawo, kusa da jariran ta dawo ta zauna tana kare masu kallo, babu wanda zai iya banbanta su, babu wanda zai iya cewa su ba TRIPLETS bane, wancan ɗin ya saje da ɗayan.

Wani irin datse idanuwansa gam Lion ya yi da karfin gaske, tamkar zai fashe idanun nasu, karo na farko a rayuwarsa da ya fara danasanin gani abu, da ya sani, da bai kalli video nan ba, dan wlh ba zai taɓa yarda ace ɗaya daga cikinsu ba cikon TRIPLETS nasa bane, da bai kalla ba, da ya rufe maganar sun tafi a haka har su mutu, ba zai iya taɓa rabuwa da ko ɗaya daga cikin TRIPLETS nasa na yanzu ba, yau an zo gaɓar da ya kasa, ba zai iya ba. Toma a cikinsu wanenen jaririn da mutumin nan ya kawo? Kuma ina shi wanda aka ɗauka? Me aka yi da shi? Meyake faruwa ne? Josephine ta sadaukar da shi kenan? Ko yaya ne? Wanne ma wannan mutumin? Meyasa dukka hakan ta faru?. Wannan shi ne tashin hankali.

Cikin tsananin zafin rai Lion ɗin ya ɗauki laptop ɗin ya makata da jikin bangon ɗakin, ji kake yi war, ta tarwatse, dafe kansa dake yi mashi barazanar tarwatsewa ya yi, cikin fitar hayyaci ya miƙe tsaye, wani irin azababben jiri yake gani, duniya juya mashi take yi, gara ace mashi mutuwa ɗaya daga cikinsu ya yi da wannan bakin abin da ya gani, wlh sai dai ya rufe maganar nan, amma ba zai taɓa iya rabuwa da Areef ko Aseef, su ne bugawar zuciyarsa, shi kam ya yarda sune TRIPLETS na sa, a bar mashi su kawai........ Ba shakka da akwai ciwo na wuce misali a cikin rayuwar TRIPLETS tamkar yanda Malika ta gayawa Rimsha a baya, to a hankali dai ga shi abubuwa sai bayyana suke yi, mu je zuwa dai, ku kasance da PRINCESS TEEMA, dan ni kaɗai ce zan iya warware maku wannan babbar al'amari, kun dai ga abin da Dr William ya karyata na cewa bai san gwaggo ba, to ga gaskiya ta fito, ga komai kamar yanda gwaggon ta faɗa!! Lallai akwai wani abu wai shi ruɗanin kwakwalwa a cikin TRIPLETS!!.

Waje ya nufa, sam baya ganin gabansa, dan wani irin jiri da uban duhu da yake gani, ji yake tamkar zai haɗiye zuciya ya mutu kawai ya huta. Ɗakin gwaggo ya nufa, da hannu biyu dukka ya dafe kan nasa da ƙarfin gaske, yana tafiya yana huci tamkar ransa zai fita, iska mai tsananin zafi ce take fitowa daga bakinsa, ya ilahi ya lillahi!!.

Da sauri gwaggo ta mike tana tambayarsa lafiya. Ina ai bai kai ga karisowa in da take ba, ya zube kasa wanwar, baya numfashi!.

A dubu gwaggon ta kariso wajen da yake kwance, shi ma Aseef da yake kwance yana aikin zuba shagwaɓa, a ɗari ya sauko daga saman bed ɗin, bai ma san time ɗin da ya iso wajen ɗan uwan nasa ba.

Sunansa suka fara kira babu kama hannun yaro, ina ko motsawa bai yi ba, tamkar rai ne ya yi halinsa. Fridge Aseef ya nufa da sauri.

Ruwa mai bala'in sanyi ya ɗauko, tsabar shiga tashin hankali har kerma jikinsa yake yi, da kyar ya iya ɓalle bakin robar ruwan. Tashin hankali ya hana shi ma ya iya tarbo ruwan a hannunsa, da bakin rofar ya fara zazzagawa ɗan uwan nasa, ita kuma gwaggo, sai ambatar sunansa SAIF!! SAIF!! SAIF! take yi.

Tas Aseef ɗin ya zazzaga mashi ruwan, amma ina ko motsawa bai yi ba.

Ganin duk wannan uban ruwa mai bala'in sanyi da ya zuba mashi bai farka bane yasa ya zunduma uban ihu tare da fara jijjiga shi da karfi yana kiran sunansa da ya tashi, kada ya mutu ya barsu, ba zai iya rayuwa babu shi ba, dan Allah ya tashi.

Wannan ihun da ya zunduma ne yasa Uncle T ya shigo ɗakin a guje. Ganin abin da yake faruwa ne yasa ya kariso ciki da sauri. Sai kuka Aseef yake yi tamkar ransa zai fita, bawan Allah!.

Babu ɓata lokacin TGA ya naɗe hannun rigar jikinsa tare da sanya karfi ya saɓi Lion ɗin a kafaɗarsa, kai tsaye sai waje ya nufa. Da sauri suka rufa mashi baya.

Bai tsaya tambayarsu me ya faru ba, kawai ya sanya shi a cikin mota tare da bawa Mark umarnin a kan ya ja su zuwa asibiti. Kafin su gwaggon ma su iso harabar gidan, har Mark ya tashi motar. Gabaɗaya sojojin da suke gidan, kowa ya nufi sauran motocin dake cikin gidan dan su rufa masu baya.

Donal Aseef ya kira cikin kuka, ya ce mashi ya ɗauko mota su bi su TGA, sai ringin wayar Aseef ɗin take yi, amma ina hankalinsa baya a tattare da shi, kuma Areef ne yake kiransa, dan ya kira wayar Lion yafi sau a kirga, amma bai ɗauka ba, shi ne ya kira Aseef ɗin dan ya ji ko lafiya, saboda a jikinsa yana jin tamkar basu lafiya, kamar akwai wani abin. Amma ina Aseef ɗin ma yaki ɗaukar kiran, shi burinsa kawai Lion ya tashi....... MASU KARATU, WANNAN SHI NE ASALIN CAKWAKIYA, LITTAFIN TRIPLETS YANZU ZAI ƊAUKI ZAFI JAU KAMAR WUTA, KADA KU MANTA BOOK 4 MUKE, KUMA SHI NE LAST IN SHA ALLAH, TO MUNA FATAN AYI KOMAI A NAN A GAMA, HAR KULLUM PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA.💋

Gwaggo babu ko mayafi a kanta, daga ɗankwalin doguwar rigar jikinta, shikenan, haka ta bi su a motar Donal ɗin. Bayansu TGA suka bi, Uncle Herry kuwa, yana can yana kula da Dr William, bai ma san abin da yake faruwa ba, John da Jay kuwa basu ma a gidan gabaɗaya, sun tafi yawonsu!. Rimsha sarkin rigima, tana can tana barci ga Noorish nata tamkar rai ya yi halinsa!

WANNAN KENAN, ABIN DA YAKE FARUWA A GIDAN LION, BARI MU LEƘA GIDAN ABBO, WATO WAJENSU DR NAWID, WATA KILA KAFIN MU DAWO, ABUBUWA SUN ƊAN YI SANYI, GIDAN ABBA BA SAUKI, AYLA TA ƁATA, GIDAN LION KUMA YA MA KAMA DA WUTA BAL, BAL NE MA GABAƊAYA, SABODA BALA'IN TASHIN HANKALI DA SUKE A CIKI, TO BARI MU JI GIDAN ABBO KUMA KO DA ƊAN SAUKI SAUKI.

GIDAN ABBO.

Gabaɗaya familyn Abbo, wato Ummi, Dr Nawid da Aafia, suna a cikin tsananin tashin hankali, suna tsaka mai wuya, yau tsawon kwana uku kenan Dr Nawid yana kwance rai a hannun Allah, ko motsawa baya yi, ga idanuwansa a buɗe garau, amma baya iya ko motsawa, likitoci daban daban Ummi ta kira, amma kowa ya zo, sai ya ce babu wani abin da yake da

Please Login or Register in order to submit comment