Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasar da ita saman titi. kinga bazata san kosu waye suka Aikata mata hakan ba"iyaka kawai kiyi k'ok'arin sanin wad'anda zaki saka su bibiyenta bazasu fallasama kowa ba"ah ah yaya basuda matsala course mate d'ina, kuma mayun kud'i ne"ta fad'a tana d'an murmushi sbd k'arya ta zabga masa"k'ananun y'an dabane ,kuma y'an shaye shaye wajensu take siyan kayan maye"Adalilin hakan ta sansu"shi kuwa Mr mahuta beyi zaton komai ba ya Amince...

*****************
tun lokacin da Ahyaan ta sanarwa Abdallah Mashi tayi Accepting d'in soyayyar sa "gaba d'aya wajen Aikin nasu Akasan suna son juna"sbd yadda yake nuna mata soyayya k'arara da tsantsar kulawa"Ayanzun duk Friday yake zuwa kai mata ziyara"su daddy da Abba sunsan dashi"sbd sun saka Ayi bincike game dashi da iyayensa da halayyarsa"kuma Alhamdulillah harma yaturo iyayen nasa sun kawo kud'in gaisuwa"rana kawai za'a saka yanzun" duk Abinda ke faruwa Dr darma yasani saidai be saka kansa cikin hidimar ba"ko wajen bincike da Akace zasuje da khaleel uzurin Aikinsa yakawo shiyasa beje ba"saidai duk yana Ankare da hidimar da Akeyi "sarai ya fahimci Ahyaan naso ta masa zancen Amma bataga fuska ba Awajensa.....tun lokacin da yaga haka jikinsa yayi mugun sanyi"Ada yana ganin kamar wasa zuciyarsa keyi masa ba son Ahyaan yake ba"Amma yanzun data kasance tana gab da zama rabon wani ya fahimci zuciyarsa ta jima da mutuwa a soyayyar yarinyar"wacce sai bayan yadawo Nigeria ne yafara jin Alamar soyayyar ta da zafin kishinta Aransa Amma Ada baya jin hakan"ya kuma fahimci bata sonsa"idan tana sonsa bazata kula wani ba"shi kuma Ayanzun baya jin zaima iya furta mata"gara kawai ya bari daga shi sai zuciyarsa....da wannan tunanin yaci gaba da rayuwa"duk yayi rama ga Azumi duk litinin da Alhamis sai yayi"ga wani irin shiru shiru yak'arayi ,ba sosai yake kula kowa ba"dukda dama ya kasance bame yawan surutu ba"dama yawan firan tasa da ita ne"saidai sarai halin damuwar daya saka kansa Aciki mamy na lura"kuma jikinta yayi sanyi itama"saidai dukda haka tana Addu'ar Allah ya musu zab'in Alkhairi gaba d'aya "garama Ahyaan d'in ita tanada samari"shi kuwa baya kula mata.....Acikin gidan kuwa har yanzun tsakanin zaman luba da Abba babu Abinda ya sauya zane"saidai tanama shirin zuwa k'asar nijar itada wata k'awarta da zata rakata ,sbd suje Akarya sihirin daya koma kanta na warin jab'a datakeyi"sbd har yanzun bata dena warin ba"kuma tana so Ayima Ahyaan Aikin da za'a koreta daga wajen Aiki.sai kwatsam Aka kawo kud'in gaisuwar Ahyaan d'in"hakan yakoma dagula ma ummah luba lissafi"Ayanzun ta yanke shawaran siyar da gadonta da tumakai 3 datake kiwo gidan mahaifiyarta sbd ta tafi nijar...Allah ya tsare mana imaninmu yasa mudace duniya da lahira....
Ayau yakama week end ba office "kuma Ajiya Ahyaan ta d'auki Albashin farko nera 200f...."Ayau kuma taje ta cire duka kud'in da safe ta bama mamy"sai ta kama dariya tace"Ahyaan Ai kud'inki ne ko?"zan d'auki 2k na saka Albarka"saina kaima Alh ya gani"kuma suma su mama zaki kai su gani su d'auki Abinda zasu d'auka "itama Ammah da musty yaka mata ki basu wani su saka Albarka"dato ta Amsa"mamy ta d'auki kud'in ta samu daddy har d'aki takai masa"sai yakama murmushi yace"toni meye sai An kamun na d'auka ?"na gani Allah yasa Albarka"Ameen Amma Alh ka d'auki wani Abin"shima 2k ya d'auka"mamy kuma da kanta taje ta kaima su mamah kud'in "saidai kason ya canza"dubu ishirin ishirin Abba yace su d'auka itada daddy"suma shida mama haka zasu d'auka, sai Abata sauran ta bama y'an uwanta Abokan haihuwa wani Abu"sannan kuma da kanta ta bama Ammah"badan daddy yasoba ya Amince suka Amshi kud'in sai dan sbd Abba yanuna beji dad'i ba"lokacin da sauran kud'in suka zo hannun Ahyaan biyu ta raba ta kalli mamy tace"gashi ki Ajiye ma broth"haba Ahyaan! wannan wane irin Abune? Ina Aka tab'a haka?ah ah mamy dan Allah nidai ki barshi nida broth duk d'aya ne"Abinsa nawane ,Abuna nasa ne ko?"mamy na k'ok'arin mgn shi kuma ya shigo cikin parlourn "wanda sarai yaji kalamanta"Atake zuciyarsa tayi wani irin rauni"yabita da kallo itama shine take kallo"Atake ta fahimci yayi rama"saidai suna had'a Ido ta janye idanuwanta"ya zauna kan kujerah yana fad'in mamy da y'arta sannunku! yauwa sai yanzun ka tashi ?"cewar mamy"uhmm" kawai yafad'a "ita kuma saita bar musu parlourn"Ahyaan ta saci kallonsa yana sanye da k'ananun kaya yayi kyau sosai da haske"Ashe ita yake kallo"wai broth baka lafiya ne?"me kika gani?"ba naga ka rame ba"shiru kawai yayi yana dannah waya"gashi tunda baza kayi mgn ba"ta fad'a tana Ajiye masa 50k saman jikinsa"ya kalleta ya kalli kud'in"tamkar baya so yace na meye?"naka ne jiya na d'auki Albashin farko"Masha Allah! Allah yasa Albarka "Amma sunyi yawa ki bani 5k ma sunyi nagode"nidai Allah ah ah ka d'auka duka indai nida su khaleel d'aya ne Awajenka"shiru kawai yayi sbd shine kawai yasan me yakeji sbd shagwab'ar datakeyi"shi yaushe rabonma daya zauna har suyi mgn irin haka da ita?"kaji broth?"girgiza kansa yayi ya mik'e tsaye rik'e da kud'in ya zare 5k"saiya kalleta da rinannun idanunsa da har sun fara sauya kala"sosai yayi mamakin ganin Idanunta sun ciko da k'wallah....indai bazaka Amsa duka ba toka bani"ta k'are maganar hawaye na ziraro mata saman kyakykyawar fuskarta"yana k'ok'arin mgn kira ya shigo wayarsa"dukda yau week end ne yayi mamakin ganin kiran daga Asibiti ne"sallama kawai yayi"Dr Marwan ya Amasa tare da cewa" pls doctor idan kana kusa kazo ka taimaka mana An kawo patient emergency wlh"ko numfashi batayi"ni kuma ba irin wannan matsalar na sani ba"gashi likitoci basufi 5 bane A Asibitin sbd yau week end "wlh Akwai matsala huhun yarinyar ne keda matsalar"kamar yanda Dr John ya fad'a"kayi hak'uri pls kazo ko zaka iya dubata mugani...okay kawai yafad'a yana yanke wayar "ya duba gefensa yaga wayam babu Ahyaan"saiya saka kud'in cikin Aljihu ya fita daga cikin parlourn da sauri.....
Tsaye yake gaban emergency room d'in da farar jallabiya Ajikinsa "yayi uban gumi sbd tashin hankali da mamakin yaushe yarinyar nan ta fara shaye shaye har ya fara yimata irin wannan illar haka Ajiki?"kansa ya d'ago yana furzan da huci daga bakinsa yabi Dr Marwan da kallo daya gama wayar zai wuce....pls doctor ya kukayi dashi ne?"kodai mu canza wani Asibitin ne tunda babu doctors Anan"kasan yau weeks ends dama Ana samun irin wannan matsalar ta rashin doctors da yawa "sannan yanzun kafin kuje da ita wani Asibitin Adubata An samu matsala"gara kayi hak'uri nanda 10 minit zai iso"shima Alfarma muka nema gunsa, dukda tsarin Asibiti nan idan lokacin da bana Aiki bane bai zama dole likitah yatsaya ya duba patient ba"Amma da yake shi babban likitah ne koda wane lokaci zamu iya kiransa"it's okay"mr mahuta ya fad'a cikin gamsuwa yaci gaba da safa da marwa Awajen"ba'a fi cikakken minti 10 ba Dr darma ya iso wajen"daddad'an k'amshin turarensa ya fara kawowa Mr mahuta ziyara"ya juyo da sauri sbd yaji kamar yasan me wannan k'amshin....Ido hud'u sukayi dashi"k'irjin Mr mahuta ya buga! musammun daya san shi likitah ne"fatansa Allah yasa ba shine aka kira yanzun ba..... doctor ka k'araso ne?"cewar Dr Marwan daya fito shida wasu nurses guda biyu daga cikin wani office "Anutse ya juyo fuska Ahad'e yace"uhmm Ina patient d'in?"tana nan ciki su Dr John na'a kanta"gama yayanta nan daya kawota yadamu sosai"pls Dr Abata taimakon daya dace"Cike da shan k'amshi Mr mahuta yace"Eh ka dubata ko nawane zamu biya indai Akanta ne"nasoma mu tafi private hospital da tafi nan to kuma time ya k'ure"Dr darma beyi mgn ba saidai wani shegen murmushi kawai daya keyi yatura k'ofar emergency room d'in ya shiga"Mr mahuta ya sauke Ajiyar zuciya "saidai befi 5minit da shiga ba yafito"dama ya shiga sbd yaga fuskar patient d'in da kuma duba file nata"dan yaga mak'asudin ciwon nata....yaya ka fito kuma?"cewar Mr mahuta yana shan gabansa"cike da jinkai Dr darma yabishi da kallo fuska Asake yace"nuna dukiya ko Mulki da isah basu sakawa nayi Aiki nah! saidai na kanyi Aikin sbd tausayi ko Alfarma! saidai kashhhhh"kai baka daga cikin wad'anda zanji tausayi balle har nayima Alfarma"sbd Aganina duk me tunanin kud'i suna iya maganin duk wata damuwa ta duniya"to kamata yayi duk sadda ya tashi yin wani Abu to yayi Amfani da kud'in wajen neman abun yaga ko zai iya samu"ya k'are maganar cikin gadarah yana sakin wani makirin murmushi ya rab'a ta gefen Mr mahuta ya fara tafiyarsa cikin k'asaita yana basarwa" tamkar tauraron dake haskawa haka kowa ya bishi da kallo"wasu nurses d'in najin inama inama....cikin tsananin b'acin rai da damuwa Mr mahuta ya fara masifa da cewa waye kai?"yaushe kayi karatun harka zama likitan balle ka gayan mgn?"Ayanzun ko k'asar waje ne Ake da buk'atar Akaita zamu kaita"kuma yanzun zamu bar wannan banzar Asibitin "saidai inaso kasani wlh wlh !! sai kayi nadamar Abinda kamun"kuma daga yau kadena Aiki Anan "Dr darma beko kalli gefen dayake ba ya Ida yin gaba yabar wajen"dama burunsa ya bashi haushi ya gaya masa mgn "ya kuma gaya masa bashida matsala"batun kurarin da yakeyi da maganga nunsa na burga basu damesa ba"saidai yayi mamakin ganin bilkisu ce k'anwar mr mahuta"sannan beyi zaton kamarta duka 25 yrs tana irin wannan shaye shayen "da yake neman yima lafiyarta lahani ba...da wannan tunanin ya wuce chemist"sai bayan sallar la'asar yanufo gidan sbd yunwar daya kwaso... Ada sashen su mamah yayi niyar tafiya saiya tuna ba itace keda girki ba"hakan yasa ya wuce wajen su mamy"tsakar gidan ya kallah yaga ledar biscuits dasu chiweengum dasu sweet"ga kuma abun goro"haka nan yaji fad'uwar gaba "saiya dake ya shigo cikin parlourn da sallama.....katan d'in biscuits kusan guda 12 dana ruwa da lemo dasu sweets ya samu tsume gefen bango Ajiye"mamy na zaune da wasu gabanta tana d'aurawa Afaran leda"ta bishi da kallo tana Amsa sallamarsa"saida ya zauna kafin yac"e wai goro da Alawan meye ?"na saka ranar Auren Ahyaan ne"gama naka nan"wata 5 aka saka ranar"ta kare maganar tana mik'a masa k'ulli me d'an girma dake d'aure cikin bak'ar leda......âœï¸

sharhi 😎
pls bana son k'orafi kunl zubaðŸ‘ï¸ðŸ‘ï¸
wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251

dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba

Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn

Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba

#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: ðŸ§â€â™€ï¸? *AGE MATES* ðŸ§

*39&40*




*Littafin kud'i ne!*

.......tamkar saukar Aradu ! haka Dr darma yaji kalaman mamy cikin kunnuwansa"ga wani irin mahaukacin bugu da k'irjinsa keyi fat fat fat!!!....cike da dauriya had'e da b'oye yanayin daya tsintsi kansa Aciki ya had'a haruffan guda ukku wajen furta"Allah yasa Alkhairi! yafad'a da k'yar ba tare daya Amshi ledar da mamyn ke mik'o masaba"yadai girgiza kansa Alamar baya buk'ata"daga haka ya mik'e tsaye yabar parlourn "Abincin da baiciba kenan ya wuce d'aki ya kwanta ciwon kai me tsanani ya masa sallama"sai gab da sallar magrib ya watsa ruwa ya fito sbd ya tafi masjeed"idanunsa sunyi wani irin jaa"inda da yawan mutanan dake a *gida biyu* sun gansa Alokacin da sun tabbatar da babu lafiya"gaba d'aya jinsa yakeyi wani iri kamar bamai rai ba"Ahaka ya tursasa zuciyarsa yayi sallar magrib ya zauna yafara karanta Alkur'ani me girma sannan ya jira Aka gabatar da sallar isha'i"ba laifi yaji zuciyarsa tayi sanyi"saidai tunanin Abin na'a ransa daram"ji yakeyi yanzun daya Ida tabbata ita ba tashi bace yake jin wani sonta na fusgarsa"sunan Allah kawai yake Ambata Azuciyarsa yana jin tausayin kansa"sbd yasan Abanza yake damuwa sbd wacce yakeyi Akan ta ita ba tasan yana yiba..... Awannan dare Dr darma yayi shi cikin wani irin yanayi.
mamy kuwa bata ji haushin k'in Amsar kayan saka ranar da baiyiba"hasalima tausayinsa taji"saidai tasan matar mutum kabarinsa"kuma idan har Ahyaan na sonshi da bazata kula kowa ba"iyaka zata cigaba da yimasa Addu'ar dangana da samun wacce ta fita"sbd ta jima da fahimtar matsalar yaron nata shiyasa yake yawaita Azumi "kasancewar sa me jin nauyinsu yasaka ya kasa fitowa zahiri ya nuna musu matsalarsa"Amma tana lura da komai"tasan da dalili da yasa yake yawaita yin Azumin nafilah"ta kuma tabbatar da kafaffiyar zuciyarsa ta hanashi ya bayyanah soyayyar sa ga Ahyaan"gashi ta sub'uce masa "wanda tanada yak'inin k'ilan sbd kar tace bata sonsa dan suna AGE MATE ita dashi shiyasa yak'i sanar mata da soyayyarsa...tana cikin wannan tunanin Ahyaan ta fito daga cikin d'akin ta zauna tana fad'in mamy broth be shigo bane?"ya shigo ya fita Amarya"nama bashi nasa kason yayi murna ya tafi"sai tayi d'an murmushi bata ce komai ba"Ahaka kiran Abdallah Mashi ya shigo cikin wayarta"ta harari wayar tak'i d'auka "ki d'auka mana Ahyaan" ko Ammah ce?"ah ah"ba wannan Abdallah d'in bane kullum zafin waya baya gajiya shi"Ammah kuma Ai tuni ta hak'urah mamy ta dena fushi dani"musammun data san waye Abdallah da family nasa"shiru mamy tayi Aranta tace" Anya koda Nura yace" yanama son yarinyar nan kakarta zata Amince kuwa?"ta Ayyah Aranta sbd tasan halin Ammah burinta Ahyaan ta Auri me hali"dukda tasan babu wanda zai kushe nurah Amma gani takeyi da kamar wuya Ammah ta Amince.....kallonta ta maida Akan Ahyaan fuska Ad'aure tace meye haka Ahyaan?"ki d'auka mana yanata kira ba dad'i "kamar zatayi kuka ta d'auka ta wuce bed room d'insu.....
washe gari misalin k'arfe 12:11 pm Dr darma ne zaune a office nasa yana d'an hutawa be jima da gama ganin patient's ba"yadi ne coffee brown Ajikinsa,rigar me gajeran hannu "kansa babu hula"idanunsa na b'oye cikin eye glass bak'i sbd Jan da sukayi "har yanzun beci Abinci ba"ko yau da Asuba yaje ya gaida mamy be koma komawa gidan ba sbd beson ganin Ahyaan "ji yakeyi yadda zuciyarsa tayi rauni har rungumeta zai iyayi kodan ya sami sauk'in rad'ad'in daya keji Azuciyarsa"dukda idanunsa nason ganinta,kunnuwansa nason jin sautin zazzak'ar muryarta. Amma Aganinsa yin baya da ita shine Mafi Alkhairi Agaresa "tun ruwan Lipton daya sha da safe be koma cin wani Abu ba"duk yayi zuru zuru..laptop yake dannawa Amma hankalinsa ba'a kanta yake ba"har mu'az ya shigo yayi sallama sau biyu bejiba"saida ya daki k'ofar shigowa cikin office d'in "sannan Dr darma ya Ankara dashi"ya sauke wani zazzafan huci daga bakinsa yana lumshe sexy eyes nasa yana koma bud'ewa.Abokina lafiyarka dai ko?"yafad'a yana zama kan kujera"Alhamdulillah! kawai Dr darma yafad'a Atak'aice "mu'az yace"bakada kirki tun bayan kunzo cin girkin Amarya shikenan baka koma lek'o muba?"na d'auka ma ko Ahyaan zaka kawo mana ta mana wuni " yayi shiru yak'i mgn"hakan ya k'ara tabbatar masa ba y'an k'yaliyar kawai bane Akwai damuwa Atare dashi"dama yazo yamasa k'orafi wai An sakama Ahyaan ranah itada Abdallah Mashi Amma be sani ba sai yau da safe yaga Ana fad'in saka ranar tasu Agidan TV d'in da suke Aiki"A lokacin da yaji sai yake ganin hasashen sa Akan Dr darma nason Ahyaan yakeyi ba gaskiya bane"tunda gashi zatayi Aure"saidai kuma damuwar daya zo ya samesa Aciki yanzun ya tabbatar da cewa Abinda yake zato ba haka bane....Nurah! Nurah!! ya zare eye glass d'in ya kallesa bece komai ba "wai dan Allah bazaka mun mgn ba, ka sanar mun da damuwarka ba darma?"shin ko ban Isa nasan damuwarka bane?"Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kansa Ahankali yace"damuwata *Ahyaan ce*! Ita kad'ai ce damuwata Abokinah" sai yanzun na tabbatar da zuciyata tayi shishshigi,ta kuma saka nayi kuskuren Abari ya huce"gashi Allah ya kawo rabon wani"tun bayan nadawo daga London nafara jin sauye sauyen daban tab'a jiba game da ita"sai na dinga k'aryata zuciyata musammun idan Ina jin kishinta"ban Amince yes Ina son Ahyaan ba saida nafara ganin Abubakar Ibrahim mahuta yafara sonta har yasaka Aka saceni sbd ita"(ya labarta masa komai)"kafin yaci gaba da cewa" daga nan kuma sai muka dinga yawan samun matsala da ita tana neman ta rainani"Ahaka har wannan mutumin ya bayyanah Aka saka musu rana jiya dashi"ban tabbatar da nayi sake ba saida na samu labarin hakan"kuma Ashe mahutan ma yarinyar nan bilkisu dake bibiyata Ashe k'anwarsa ce sai jiya daya kawota nan babu lafiya na fahimci hakan"yaya zanyi da Raina mu'az? Ina ganin zan Amshi tayin zuwa k'asar India da Akamun last week "naje nayi course d'in wata shidda Acan"kafin na dawo nasan sunyi Aurensu"yak'are maganar cikin wani yanayi yana cije baki....Ajiyar zuciya mu'az ya saki yace"ko yanzun bazaka fidda rai ba sai An d'aura tukum"Ina maka jaje Abokinah"sbd najima da fahimtar ka mace a soyayya Ahyaan "ta kishinta da kake nunawa da kuma k'wayar idonka ta nan nagane"Amma duk idan na maka zancenta saika basar ka canza topic d'in "na jima Ina hasaso ku Amatsayin couples sbd kunyi masifar dacewa da juna"na kuma tabbatar da cewa Ahyaan kawai ce zata iya da fitinarka....dogon tsaki Dr darma yaja yana wurgo masa harara"saidai kayi hak'uri my man gaskiya na fad'a maka"Amma jin kanka yasaka ka b'oye mun"da tuni kasanar mun kana sonta da wlh munsan yadda zamuyi koda bata sonka har ka cusa soyayyar ka Azuciyarta"to san girmanka ya hanaka"saidai Ayanzun Addu'ar zab'in Alkhairi da dangana zakayi tayi"idan har Ahyaan rabonkace in sha Allah zaka sameta duk rintsi "haka idanma ba rabonka bace kome zakayi bazaka same taba "dama tunda naga suna yawan shirye shirye da Abdallah Mashi Raina yabani sonta yakeyi....pls mu'az kaje kawai "taya zaka k'aramun da wani zafin?"ya katse sa cikin zafin rai....kayi hak'uri Abokinah"Amma ka kwantar da hankalinka"yanda nasanka da jure Abu to haka zakayi karka bari Ahyaan ta fahimci ka damu ko kuma baka son tayi Aure"tunda dai ita bata san sonta kakeyi ba, zata d'auka da wani Abu"kansa kawai ya gyad'a masa bece komai ba.duk yadda mu'az yaso ya sake masa suyi y'ar fira k'iyawa yayi"hakan yasa ya barsa yatafi kawai cike da tausayinsa.....

*************
Hahahahahahahahaha!!sautin wata iriyar murya marar dad'i ke tashi cikin jejin"yayinda suke zaune su biyu gaban wani shed'anin boka Acikin wani bak'in daji"wanda kafin su iso saida suka hau kwalo kwalo"kafin suzo inda bokan yake kowace tayi sartse sama da guda goma ga hannu da kuma k'afa"tunma kafin suyi masa bayani yasanar musu yasan komai. bayan ya gama dariyar tasa kafin yace "zamu karya sihirin da likitah yasaka Amayar kanki"baki washe ummah tace"yauwa boka"sannan ka taimaka ka hana faruwar Auren nan da shegiyar yarinyar nan zatayi"kuma inaso Akoreta daga wajen Aiki "idan buk'atata ta biya zan dawo kan uwar tata...hahahahaha! kin cika marar Imani "to ki sani mu Aikinmu yasha banban dana wasu"kuma Ahankali muke Abinmu ba farar d'aya ba"koke sai kin kai kusan sati d'aya ko kwana biyar kafin ki dena warin jab'a"Aure kuma zamu lalatashi"Eh boka Asa mata tsanarsa da k'insa Azuciyarta ita yarinyar...bazai yuyuba! ta zaro Ido "ya kece da dariya kafin yaci gaba da cewa"yanzun yarinyar jikinta Ashirye yake da Addu'oin tsari"kuma tana Azkhar "saidai zamuyi Aikin Akan shi yaron dazai Aureta"batun Aiki shima zamuyi Abinda za'a koreta"saidai komai daki daki zaizo. Amma boka...ku Ajiye sadaka ku tafi , Akwai masu son isowa nan suma suna hanya"ya fad'a yana gimtse fuska"hannunta na kirma ta Ajiye masa kud'i kusan dubu 50" K! kud'inki nera dubu d'ari ne"kuma kinzo dasu"haka zaki Ajiye ki wuce"Aiki ukku za'a maki"sbd haka idan baki shirya ba tafi ki bani waje"uwale tace haba luba ki Ajiye muje mana"ummah hannu na kirma ta zaro cikon ta Ajiye"Atake hayak'i yacika wajen,suka kama tari"ku rintse Ido sannan ku bud'e"da sauri suka rintse,suka kuma koma bud'ewa ,sai gasu gaban kwalo kwalo "ba k'aramin tsorata ummah tayiba"yayinda uwale ta kama dariya sbd batayi mamaki ba"zuwanta Anan na ukku ne Ayau"na farko zuwan kanta ne,na biyu wata ta rako,yanzun ma ta koma rakowar Akaro na ukku.sai zuzuta Aikin malamin uwale keyi har suka shiga cikin kwalo kwalo ya tsallake ruwan dasu"yayinda luba kejinta cikin farin ciki"dama burunta shine rayuwar Ahyaan ta k'untata"so takeyi Ab'ata komai Akanta sannan tadawo kan mama"sbd itama ba k'yaleta zata yiba.....
misalin k'arfe 10:11 am na safiyar yau Asabar "garin yayi lullumi sbd hadarin dake A sararin samaniya"ga iska me dad'i na ratsa jiki"Ahyaan ta fito rik'e da wata k'aramar leda fara ta shopping Ahannunta"tana sanye da doguwar riga ta Atamfa red& white,sai mini hijab red colour"wacce tayi masifar yi mata kyau"ta k'awata kyakykyawar Choco face nata"yayinda plate shoes ne sanye Ak'afarta.sai sauri takeyi da k'yar mamy ta barta zataje gun saloon.....tana k'ok'arin fitowa daga k'ofar shiga shashen nasu shi kuma yana k'ok'arin shigowa! kusan fad'a masa Ajiki tayi"cikin hanzari tayi baya kamar zata fad'i "Dr darma yayi saurin rok'o hannayenta"Atake idanuwansu suka sark'e "Ahyaan dake jin wani iri Ajikinta sbd hannayenta daya rik'e"saita janye idanuwanta daga cikin nasa ta fara k'ok'arin zare hannayenta daya rik'e....ya kafeta da Ido tamkar yau ne ya fara ganinta"yana sanye da wondo 3 quarter da t shirt me gajeran hannu wacce ta fidda shape d'in body building d'insa"ya k'ara haske da frash saidai fuskarsa da rama har yanzun "ga k'asumba ta cika masa fuska"be jima ba da tashi daga bacci ba ya watso ruwa ya shigo cikin gidan sbd yayi break fast"yana kuma fatan Allah yasa karya ganta"gashi Addu'ar tasa bata karb'uba.....pls ka cika ni naje broth "ta fad'a tana b'ata fuska"cikata d'in yayi sbd shima wani irin Abu yaji yana fusgarsa daya rik'e hannuwan nata"zuciyarsa na ingizashi daya rungumeta koya sami sassauci, Amma saiya dake....Ina zakije?"ya fad'a tamkar bayaso"kallonsa ta komayi saita turo baki tace"wai broth tamkar baka duniyar"kamar ya?"hmm ! rabon dana ganka harna manta ni"ta k'are maganar cikin mamaki tana d'auke Idanunta daga kansa"sbd ganin kusan 2 weeks rabonta dashi"wanda yayi daidai da wata biyu cif kenan da saka ranar su itada Abdallah Mashi "yawanci duk sadda zai shigo gidan da Asuba"ko bacci takeyi ko tana sallah"be kuma sake shigowa sai k'arfe 2:30 pm "lokacin kuma tadawo daga office tana bacci"sbd data dawo tayi sallah kwanciya takeyi sai la'asar take tashi"shiyasa sai tayi har sati biyu ko d'aya bata gansaba....uhmmm !idan kin damu da son ganin nawa Ai kinsan inda nake kwana ko?"sai tayi shiru,tarama rab'a gefensa ta wuce"ya d'age kafad'a irin ko Ajikinsa d'in nan "yama d'auka koda motarta zata fita"da wannan tunanin yayi gaba Abinsa"saidai hoton fuskarta na'a cikin zuciyarsa "gaba d'aya yau ta masa wani irin kyau"ga wata k'uruciya daya gani Atare da ita "sai ta masa kamar y'ar 20yrs.... Ahyaan na fitowa ta wuce bakin titi ta tari nafef"kai tsaye zainab beauty saloon Aka Ajiyeta "suna isowa ta sallami me nafef d'in ta wuce ciki.saida ta d'auki kusan Awa guda Aciki sannan ta fito sbd ta samu layi"daga gaban shagon taga me nafef ya kara gefe"har zata wuce taji yace Hjy tafiya zakiyi?"Eh "Ina zakije?"*baya jidda road*"to shikenan shigo muje kud'inki 500 ne"okay ta fad'a tana shigowa"basufi mintina 5 suna tafiya ba wata mace ta tsaidasu"tana sanye da face mask da eye glass bak'i"haka nan Ahyaan taji fad'uwar gaba da suka tsaya "saita dake kawai tana kallon matar da sauraren inda tace za'a kaita"wansa kusa da Anguwar sune"bayan sun gama mgn dame nafef saita shigo"da sauri Ahyaan ta kalleta sbd k'amshin turarenta yamata kama da wani k'amshi data tab'a ji"sai kawai ta basar taci gaba da kallon waje suna tafiya....can kawai taji an dafa kafad'arta "ta waigo da sauri"Ikkhee dake zaune gefenta ta watso mata wata powder fara"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! ta furta tana tari"kasancewar jininta me k'arfi ne sai hodar batayi saurin gusar mata da numfashi ba"tana jin dariyar Ikkhee da ganinta bibbiyu"saita lumshe lulu eyes d'inta, Adaidai lokacin kuma Ikkhee ta kira Mr mahuta yana d'auka tace"yaya Abubakar gata nan mun kamota muna hanya ne...iya nan Ahyaan taji daga haka bata koma sanin inda kanta yake ba.......âœï¸

🫣🤫🤔 Sharhi kawai🤓

wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251

dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba

Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn

Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba

#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
7/21/24, 11:01 - Buhainat: 🧠*AGE MATES* ðŸ§â€â™€ï¸?

*41&42*





*Littafin kud'i ne!*

.......tafiya suka cigaba dayi me Nisa, wacce Ak'allah sun

Please Login or Register in order to submit comment