Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan munafukar Ina suke zuwa ne da Abbin su Fadila?Mama Tace su suka sani Idan tayi tsami zamuji,Amma su Khaleesat sunce zuwansu gidan Fu'ad sau biyu Amma gidan a kulle sai Mai gadi da me kula da Compound,Amma da suka tambayi me Gadi Ina masu gidan Suma munafukan sai cewa sukayi Wai sun tafi Lagos Honey Moon,Momy Tace Wai su masu Aiki na Amana baza su tonawa Ogan su asiri ba,duk sai sunci Ubansu da kaina zanje gidan Anjima,Mama Tace muje Kai tare,5pm suka shirya Mama itace ke Driving har gidan Fu'ad suka je ko motar Basu shigar ciki ba a waje suka Yi parking ,suna kwankwasawa me Gadi ya taso tare da lekowa ta Yar wata kafa a jikin gate din Wanda dama anyi ta Dan ganin waye yazo,Ta ciki Yace basa Nan sun tafi Lagos,Momy ta galla Masa Harara Tace Kai karka Raina Mana hankali idan ma zaka fada Mana gaskiya ka fada kudi zamu biyaka,Me gadi yace Hajiya baza ki Iya biyana kudin da Oga ke bani ba,Kuma sunce sun tafi Lagos sai nayi Miki karya,gwara ku tafi sabo da Ina da bindiga ta sai na dakko ta na fasa muku kafafu,Momy Tace da kuwa ka Kare rayuwarka a fursuna,to sai ki hauro katanga ki bude gidan mu gani,Mama Tace muje zamu dawo Next time sai kaci Ubanka,Me gadi ya rufe Yar kafarsa ya koma ciki abinsa ya barsu Nan suka gaji tare da tafiya.

Sai da Iya ta Gama Yi Mana Tuwon shinkafa miyar taushe Tasha nama sannan na daukar Mana,dama tunda yazo har Iya ruwan Roba muke Sha,Iya tana Sha Tace Typhoid Karyarki ta kare,sai dai na dauka a Salat Amma ta hanyar ruwa kuwa na Gama da ke,Iya taji Dadi suna ta cin dadinsu tunda Fu'ad yazo shi yasa Bata so ya tafi,shima wani dadin garin yake ji,Muna cin Abinci Wayarsa tayi Kara,Umma ce ke kiransa ,kin dagawa yayi har ta Kira sau biyu Bai daga ba,Nace ka daga Mana yace sai Mun Gama ci sannan Zan kirata,Da Hunnu muka ci Tuwon mu yace tsotse min yatsu na,Daya Bayan daya na tsotse yatsunsa tas,Nima ya tsotse min Nawa tas,Fitowa Mukayi tare da wanke Hannu da baki,Mukayi Alwala yaje masallaci,Ni kuwa da Iya munyi Sallah a gida na gyara dakinmu Dana Iya har tsakar Gidan,Ina wanke wanke Fu'ad ya dawo ya tayani Yana min dauraya,Sai da muka Gama sannan ya Kira Umma,Bayan sun gaisa yace Iya...da Sauri yace au Umma,Umma Tace Iya kuma? Nice Iya yau Kuma? Sai kace Wanda ka Dade a gidan Su Rumaila ka rike sunan Iya sosai har mantawa kakeyi kana kirana da Iya Kai ga me suruka ko,Dariya Fu'ad yayi yace ba Haka bane Umma, kinji shuru ko Meeting ne ya rike Ni sai yanzu na fito,Umma Tace ai nayi tunanin Haka,gobe zaka dawo ko? Fu'ad yace Aikin ne Umma yayi yawa da kyar ne Idan Zan dawo goben ma sai dai ko jibi ko Kuma Nan da kwana Uku Ma,Umma Tace ai kafin ka dawo an karbo maganin Rumaila idan ka dawo sai kaje ka Kai Mata tayi amfani da shi mu gani ko za a Dace, Fu'ad Yana Murna yace to Inshaallah za a Dace Iya...Au sorry Umma zance,Umma ta girgiza Kai Tace zaka zo ka sameni.

Yamma na Yi yace zai tafi Iya Tace Sam bazai tafi ba sai gobe dama shi ba Niyyar tafiya yayi ba shi yasa yace to Allah ya kaimu goben,Iya Tace goben ma sai yamma yace Inshaallah,sai murna yakeyi,Yau ma Haka Mukayi bacci makale da juna Aljani Bai zo ba,Lokacin tafiyar Fu'ad yayi Amma sai ya kwanta yace Kansa ne ke ciwo,Iya duk ta gigice tana Sannu kaji, tafiyar Nan ka fasa ta sai kaji sauki, Fu'ad ya kwanta yayi wani ranga ranga kace mutuwa zaiyi har da kuka na,Iya Tace Bari a samo maka Yar Fura kasha naga tun safe ka kasa cin komai,dama Fu'ad Yunwa yake ji Dan kar ace cutar ba me zafi bace sai yaki cin komai,Iya tana jikin Kofa Tace furar za a kawo maka ko ayi maka kunun gyada,Ko Kuma Taliya da Miya za a kawo maka? Fu'ad yayi wani Ranga Ranga da kyar yake magana kasa Kasa yace a hada duka Ukun,ba Iya ba har Ni Rumaila sai da Mukayi mamaki,maralafiya Amma duk zaici Abu Haka,Iya tunaninta Bata ji dai dai ba Tace me kace? Ya sake cewa a hada duka Ukun a hankali Yana nishi.












Masu Sharhi a ci gaba Dan Allah
Ina godiya Kuma.
















AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈









NA KUDI NE

DUK WACCE TA CI AMANA TA FITAR DA NOVEL DIN NAN MUSAMMAN MASU TURAWA A GPS DAN A BIRGE FANS BAZAN YAFE BA.








DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM













76-80












Official















By
AsmaBaffa














Page naku ne

Mmn Saddeeq
Nafee

















Iya tace gaskiya yau babu tafiya jiki yayi zafi da yawa, Dan Nan ko ruwan garin Nan da kake wanka Bai karbeka ba?Fu'ad yace ae Ina Jin da shi dinma,Iya Tace Bari to a samo maka magani,Fu'ad yace nasha dazu ai zaiyi sauki Iya,Iya Tace to Bari na hada maka Furar sai a kawo ke Rumaila ki taimaka Masa ya canja kayan jikinsa sunyi nauyi wannan uban Jus (Jean) dake jikinsa kafin mutum ya cire ai yayi fitsari a wandonsa,Kinga Idan Sallah zaiyi kafin ma yayi Alwala an Idar da Sallah da wannan wandon nasa, Yana ji Yana ta Dariya a ransa,Iya tana tafiya na karasa saman katifar Ina tattaba wuyansa da Bayan Hannu na nace naji ba zafi? Yana numfarfashi yace ai...aini Haka nake zazzabi na jikina baya zafi Watarana ma sanyi Zaki ji,Doctor Dina yace zaman da nayi ne a turai shi yasa,Kuma abinci ma Ina Iya ci sabo da Albarkacin turai na samota a cikin jinina,Ni ban taba Shiga ko jirgi ba nace Allah ya taimakeka,Kayan na Taya shi cirewa yasa jallabiya fara,Harda cewa na Miko Masa turarensa,na dakko Masa tare da fesa Masa wani dadin kamshi abinka da Abu me tsada,Rufe Kofar ya Furta,naje na rufe ta yace sa key,na saka Key na dawo yace to kwanta haka na kwanta a gabansa,Kansa ya daura a dogin wuyana Yana sinsinar kamshi na,gashi na ya shafa yace yau an wanke min gashin Nan kuwa? Nace ae ban sharce shi sosai bane baka da lafiya shi yasa,yace min cumb,Mamaki ya kamani wannan wacce rashin lafiya ce Haka,Na Miko Masa Cumb ,ya wani Mike da kyar kamar zai Fadi har Ina rikeshi Ina cewa Karfa ka Fadi a hakura da taje gashin Nan zanyi da kaina,No Ni Namiji ne ya kamata na dinga yin kokari a Abu Zan Iya,Can muka matsa jikin Miro ya zage tare da taje min gashin kaina Shar,ya shafa min Mai me kamshi,jana yayi muka sake Kwanciya ya juyo Dani Muna kallon juna,Nace harka Dan Rame kuwa na Furta a hankali,a ransa yace kaji karyar Mata,dama Mata Haka sukeyi Haka Kawai sai ma idan suka ga Dan uwanka sai suce ya fika kyau,ko kana cewa baka da lfy sai suce shi yasa naga ka rame aikin su kenan kakale kakale da sa Ido.

Hancinsa na Danja kadan nace Hancin naka Ina sonshi da yawa ko Kai ka zanawa kanka baza kayi kamar wannan ba,yace ke kuma naki fa?fari nayi da Ido,yace Dan Kara Yi na gani,Dariya nayi Ina Jin kunya na sake Yi yace kin ci kyautar sarkar Gold nayi tunanin Wasa yake yi nayi Dariya kawai tare da yin Wani Wal Wal da idanuwa na yace kin cinye harda dankunnenta,gashin girarsa na shafa me yawa,Ina ta Masa tabe tabe a fuska yace na fara Jin Dan sauki, Alhmdllh na furta,Rungumeni yayi sosai a jikinsa bacci ya fara kwashe Ni Iya ta Kira Ni,Zan tashi ya sake makalkaleni Yana wani Shagwaba harda cewa karki tashi jikinki Dadi,Nace Iya ce fa ke Kira kasan Halinta ba ruwana,da sauri yace tashi ki tafi kar Iya tace sai na bar gidan Nan,Kofa na Bude na fito naje kitchen Tace gashi Nan ki Kai masa,Ni banga kina chasa kwalliya ba Rumaila Haka akeyi? Iya Bata San Fu'ad ko nayi kwalliyar ba Indai zamu kwanta sai ya cire min kayan idan Zan fito ne Kawai nake maida kayan jikina,nace Iya ko banyi kwalliya ba ai Ina da kyau,ke ki kiyayi maza wallahi ba ruwansu da kyanwunki Kawai ki Zama Me Maggi da gishiri har da Onga,Ashe Iya ba kwalliyar Kaya take nufi ba gyara jiki na matan aure,Nace to Iya ai Ina Sha,Ni dai Ina gaya Miki karki Bari ki warke bakya cikin shiri,Abincin na dauka na tafi Dakinmu,Ko da na ajiye a katon Tire nace ga Abincin yace sai dai ki bani bana Jin karfi,Sai da na fara bashi taliyarsa Yana ta ci muka ji sallamar su Saude,Iya ce ta tare su Tace a Miko ishirin ishirin su Uku ne Suka bawa Iya Naira Sittin,Iya Tace ki zauna can gefe sai sun fito sai ku kalle su,Kamar Wanda suka je gidan lalle da Sallah Haka Suka zauna Saude Ana ta tauna chewgum Ana kas kas,Hajara Itama Haka Ashe Har da Rabi ta dawo daga birni jiya Kuma Gulma tazo daukarwa Su Momy sune Suka turo ta tazo ta gani Ina gida ko an Kore ni,sai akace ai Angon ma yau kwanansa Uku a kauyen shine tazo ganin Zahiri.

Iya kuwa Shiryawa tayi Tace na tafi gidan Suna daga can Zan wuce taron siyasa sai dare Zan dawo Amma daga can gidan Kawunki Haruna Zan wuce na kwana sai Kuma gobe idan Allah ya kaimu, Fu'ad harda cewa Iya a dawo lafiya ki gaida kawun Yana ta murna a ransa,Iya tana tafiya yace je ki kulle Mana gidan Nan,Ina fitowa naga su Rabi a zaune suna ta surutu,nace au kune dama kuka zo? Saude Tace muka biya kudi dai gida idan za a shugo Dan son abin duniya sai an biya Ishirin, Fu'ad ne ya fito yaga su Rabi Kamar yaga Kashi ko kallon su baiyi ba yazo ya daukeni cak tare da Saba Ni a kafadarsa,nace Sweety ga mutane fa yace matata ce fa Ni Nace su zo,Su Rabi ya kalla tunda yazo garin ko Kofar gidan su Rabi Bai taka ba,Suka gaida shi,lfy Kawai yace sannan yace idan kun Gama zamu rufe gida,Tsoron Fu'ad da kwarjininsa yasa su Saude suka Mike tare da ficewa sum sum,suna fita Saude Tace a Dirka mata ciki,a shekara biyu ta Haifo Yara Uku suka gudu, Fu'ad yace lallai Yaran Nan Allah ya kawo su Gidanmu tun daga gate Zan sa a maido su Kauye zasu ci ubansu,Allah yasa naga Rabi a gidan Abbi zata ga yanda Zan koreta,kamar Ni su fada min magana wannan Sauden me kafa Kamar tsinken Tsintsiya sai naci Ubanta tunda Bata da kunya,Ni tafiya ma zanyi wannan Yan kauyen naku jahilai wlh.

Dariya ya dinga bani yanda yake ta faman masifa yace Iya ce Kawai wayayya,Iya tafi Yan Birni ma wayewa,Affa Kuma fa? Yace ai yanzu Affa baya layin mutane bare ayi lissafin.....bakinsa na rufe masa da sauri nace Kai Affan nawa? Shine fa ya Haife ni,Ni Ina son Abina,akansa zamu Bata wallahi,Hakuri ya bani ya Gane yayi subutar Baki,Fushi nayi na kwace jikina Zan tafi ya riko Ni da Sauri yace I'm sorry, Hawaye ne ya shararo min,Yace cikin sigar lallashi kiyi Hakuri kuskure nayi bazan sake ba, Hawaye na ya dinga lashewa Daya Bayan daya,Yana ta lallashi na,nace na hakura ai ya wuce,Yace to Smile for me,nayi murmushi yace Dan kadan kika Yi ai na sake bangale Baki yace to na yarda kin hakura,nace sai munje ka gaishe shi yau ma, Fu'ad yace ba komai ko Baki fada ba ai Affa ya cancanci gaisuwata kullum,ai Affa shima wayayye ne ga fara'a ya fara Yabon Affa Dan naji dadi,yace ai duk kauyen Nan Bamu da kamar Affa,nace to waye ma ya Isa ya Kai Affa matsayi a garin Nan,Yana ta min wayo Dan na hakura Ni ban Gane ba sai murna nakeyi Ina Kara zuzuta Affana.

Kallo na yayi yace Baby Ina tausayinki kin shiga jarabawa kala kala Amma Baki da zuciyar fushi da wata ce yanda take Laulayin Nan da kika Yi da bakin ciki bazai Bari ma ta iya komai ba a duniya,nace ai Ni ba komai ke shiga zuciyata ba ya dameni,Yace kice Kawai Idan Zan Kara aure bani da matsala? Dukansa nayi a kirji cikin Wasa nace Wai Ina cutarka ne? Yace dauriya Kawai nake Yi Amma Ina jinta a jikina kadan kadan,Tsabar samun sake yau a tsakar gida Mukayi wanka, Fu'ad yace wannan gidan akwai Albarka Salahu tsoron Iya yake ji,da acan ne ko Hannunki ban Isa na taba ba, nice na shafa Masa Mai sama sama na saka Masa wata arniyar shaddarsa Sky blue yayi kyau dinkin dai dai shi,hularsa Kalar kayan ya saka irin na matasan zamani an wani coka ta,sumarsa me uban yawa ta baya,Kai ba karamin kyau yayi ba,Nima na shirya na sa wata doguwar rigar material me tsada cikin na Lefe na,zanyi kwalliya ya kwace kayan yace powder ma ta Isa,Nace lipgloss din fa? Da Kansa yace kawo na shafa Miki kadan,Haka ya Dan zizara min kadan Wai kar maza su gani su yaba.

Yawon mu Muka fice ta cikin gonakin Mutane muke bi gaba daya garin Kore Shar gwanin birgewa,Ta Kan Yar hanyar da mutane ke wucewa muka bi muna tafiya dake Yamma ce ba mutane a gonakin,Hannu na ya rike muna tafiya muna hira,Rikeni yayi Muna tafiya muka tsaya,Hannayensa ya ware tare da furta Ayi Mana muma,Mu Kashi muka Miki a gado da baza ki Mana ba,Dariya na kyalkyale da ita sabo da na tuna farkon zuwan mu gidansu,Nace Ashe kaji me nace Amma ka share mu Kamar baka San Ina Yi ba,yace har tarihin pics dinki ne Dani sabo da kinfi kowa chaske gayu,Dariya nakeyi kamar ba gobe sabo da nasan irin Haukar da Mukayi,Yace gayun Habuja,Abujar ma sai dai kuce Habuja,Tunda kika zo gidan Nan kin fiye takura min sai da na soki ta dole,Dariya nayi na rike kugu Ina kallonsa,Ina ta fama da zuciya ta Akan lallai karta so ki Amma Ina,Sanda nace ban shirya aurenki Abbi yace ya Bawa Islam ke a lokacin Hada Kaya na nayi na koma Lagos,ciwon so yasa ko kwana daya banyi ba na dawo,nace mu muka San kayi wani yaji ma ka bar gida,yace ko Umma Bata sani ba,kar kuma mu koma gida ki fadawa Umma Watarana na San Halinki da shegen surutu,Hoto na ya nuna kwalliyar mu ta Fulani har da Radio a rataye ga Dan glass Dina irin na yara Baki na kwama a fuskata, Tsalle nakeyi sai ya goge yace ai Baki Isa ba Yaran mu Zan ajiyewa suga mamansu ranar da muka taba fara haduwa,Har pics Dina Ina zaune a palon Nene na saki Baki da Ido Ina kallon TV,Duk ban San ya dauka ba,Wai yaushe ka dauka?yace Islam ne yake ta daukanki Dana gani a wayarsa na tura a wayata na goge na wayarsa Baki daya,Wani Hoto na ya nuna min Ina Exercise shima na famfara da gudu,Kukan Shagwaba na saki nace Allah sai ka goge,Hannun sa ya daga sama nayi nayi na kwace Amma na kasa,nace muje to tunda baza ka goge ba,Tafiya muka ci gaba da Yi sai Hotuna yake daukan mu,Harda bani Wayar na Masa shi daya,Nima yayi min kala kala,nace Ni hoton Yan karya zaka min a motarka Ina tukawa Ina bin waka yanda Naga anayi Ana sawa a Instagram,Yace Amma da Mayafi Zaki Yi nace na hajiyoyi zaka min.

Komawa muka Yi muka Shiga motar nice ke Dan tukawa a tsorace sabo da ban wani Iya ba,Kida ya kunna na zabi ta Hausa wacce nasan na Iya, a wajen yayi Downloading wakar ya kunna min ita ta Garzali Miko (So Halitta ne)

Nayi daurin manyan Hajiyoyi ture kaga tsiya harda saka Glass din Fu'ad me tsada yayi min masifar kyau Yana ta Dariya nace ka daina dariyar Nan kayi min Video Kuma ka tabbata nayi kyau,Yace Kin shirya,Yes na Furta,Yace action...na wani fuske Ina ta tuka mota da kyar Ina bin wakar har wani nunawa nakeyi da Hannu Ina gwadawa kamar ana shooting film,Yayi aka gama,yace saura mu biyu ,ya canja wakar turanci Yana bi Ni Kuma Ina Driving Yana Mana har wani Yar rawa nakeyi Ina tuki,Muka sake pics,Ya tura min Nima a wayata,Sannan yace muje garin Yan uwanki duk Inda Iya tayi aure na San Yan Uwanki,Nace ka Bari sai gobe,ai gobe Zan tafi,no idan muka je sai mu koma Jigawa mu kwana a Hotel da safe sai ka ajiyeni a gida ka wuce abinka ko? Fu'ad yaji za a sake kwana a Hotel yace Masha'Allah harda wani kalkala yayi,Dariya nayi nace Lallai shayi ya ratsa ka wannan Irin fidda tajweed Haka,Hannu ya Mika min muka tafa.

Iya kuwa Tana gidan Suna Yamma tana Yi Tace ke mejego Zan tafi taron Siyasa Allah ya raya,Wata cikin Yan suna Iya ta taba auren mijinta har an rabu ma Mata basa hakura da kishi,gulmar Iya tayi ita da wata Baki ta tabe Tace a Haka dai za a Kare a neman kudi son abin duniya, Dan Abin kunya surukinta yazo ta bar musu gidanta sabo da Yana da kudi ko kunya Babu Yara suna ta tambadewa a gabanta,Ni Wallahi na tsani matar Nan gaba daya haushi take bani yanzu kaga Iyayi yarta ta auri me kudi sai yashe shi sukeyi komai shi yake musu,Karaf a kunnen Iya.
Iya Tace to Algunguma Ina jinki,Mene abin Jin haushi na idan kudin Dadi ne ke kiyi Mana ko kema yarki Mariya ta auri me kudin mana,Ni ban Hana ki Zama Mista miliniya ba a garin nan (Mrs Millionaire),ko na Hana kiyi kudi? duk bakin cikin tanda sai munci waina,Kuma kune jahilai bani da lokacin ku,kwarto yar tawa ta kawo ko dadironta ne? Halak malak mijinta ne babu Wani tantama,tsarkakarken Aure ne, yaro me tsarki Rumsilata me tsarki aka daura Aure tsarkakarke.

Matar tayi mukus tasan Halin Iya, Iya Tace ke auren yarki da akayi ba ingantacce bane sabo da lilamin Kauye ne yayi hudubar Auren bakinsa dagajaja da goro ko fatiharsa Bata Inganta ba,ita kuwa 'yata tsarkakakkun malamai ne Suka Daura shi,kace Balarabe ne sabo da Ilimin Addini, ke kuwa Auren Yar Taki Haka muka ji Ana daura Aure,Kun Bamu mun karba,Kun Bamu mun karba ita ake ta maimaitawa har sau Uku sannan Ana cewa Fatiha da Kursiyyu,An bada Sadaki dubu Bakwai da dari biyar Kamar kudin Yar budurwar Akuya ta kiwo,Hassada a kanku zata Kare,kuma Surikina shima Dana ne su sakata su Wala,kema idan kin koma gidan mijinki Dan Iska fakirin banza ki baje ku kwashi soyayya,ko na hanaki kiyiwa mijinki kema? Wannan jaririn da yake Hannunki uban me kikayi kika haife shi Algunguma ke Kuma a bokiyar gulmar kema a gidanki Mijinki baya murkushe ki? Kinibabba an kwantar da Yara a Palo suna yin bacci Zaki zare jiki ki fada dakin Miji aje Ana fyarfyadiyar Dadi shegiya me suffar Yan bori,Iya ta dinga masifa da kyar aka Bata Hakuri ta tafi matan Suka Yi mukus sabo da akwai kunya a kamaka kana gulmar mutum
Mejego Tace gaskiya baku kyauta ba kune baku da gaskiya Kuma kun San Halin Iya ba kyaleku zata Yi ba,Ina ruwanku da harkarsu,kishiyar Iya a da Tace jarababba ai ban San zata ji ba,na manta kunnenta kamar na miciji Haka yake.

Mu kuwa sai dare Muka je wajen Affa a wajen suyarsa Yana ta Yi,Gaida shi Mukayi yace to Yan bana bakwai daga Ina Haka fatan dai ba kyauta kuka zo na baku suya ta ba,Affa Tarwadar zaka bani,Daurin zaninsa ya gyara a kirjinsa saman Riga t-shirt,tsohuwar Rigata ce Dana taba mantata a gidan Affa sai gata yau a jikinsa duk ta jeme,Ni tausayin Abbi ma nake ji wannan sai Addua,yace ke uban me kike gani a jikina? Cire min shi ya Furta Yana gyara daurin zaninsa tare da bankaro min kirjinsa,Nace Affa Wai mu kuwa me muka yiwa Allah na laifi Haka ya jarrabce mu,Dan Ubanki Yi sabo a daina Yi Mana ruwan sama,maza kici gaba da sabo Dan Iskanci maimakon ki godewa Allah yayi Mana Baiwa gani Ina sana'a ta ci gaba kudi nake Tarawa Amma kina wani cewa kaddara,Abin farin ciki ya samu kice kaddara Dan Gyatimar Taki Iya ko bakin ciki kike min ne,Baki na turo nace Ni Wallahi ka daina abin Nan abin kunya ne,Affa ya rike Haba sannan yace Ayyiriri nanaye Ashe kina da Aiki,nace Affa Kawayena da surikinka a gabansu fa Affa kake Haka yace ki fadawa Surikin Nawa da kawayen naki anjima da dare suzo muyi gada da Wasan Buya buya,Nace Affa Surikin naka? Yace ae ya kalli Fu'ad yace kai taho muyi Tafa tafa,Allah baza mu sake zuwa gaishe ka ba na Furta,yace har Mahdi ya bayyana kar kuzo ko ance Neman ku nakeyi, Fu'ad ya kalla yace Kai mene kayi min wani kerere Haka a kaina ku tafi ku bani waje, Fu'ad ya juya shi Dariya ma Affan ke bashi,a ransa yace maybe ciwon hauka ne zai shige shi ta Haka.

Ko da muka koma gida Fu'ad yaga na Dan Shiga damuwa,Sai ya hada Mana game wayarsa da wayata yayi joining,Tabarma ya shimfida Mana a gindin Bishiyar gidanmu katuwa,Fresh Air tana ratsa mu nayi matashi da cinyarsa Yana Zaune Ni Ina kwance muna ta game sai na ware Muna ta nishadi,sai cinye Ni yake Yi ban Iya ba,Shagwaba na saki Ina bubbuga kafafu daga kwance nace Allah wayo kake min na daina,Kwanciya yayi Yana dariya na haye saman cikinsa Ina tsalle,Yace Zaki karasa Ni kin fiye Wasa Kamar wani Yar biri,Tashi ki dafa min Indomie Yunwa nake ji,Sharp sharp na dafa Masa Indomie da kwai dafaffe Guda biyar mu biyu Muka ci tayi dadi sosai.
Bayan ya dawo daga masallaci yayi Sallar Isha yace Zan fita majalisa nayi Abokai a garin Nan,ban so ya fita ba sabo da Ni nafi so Muna tare,Yana fita na kulle gidan nace idan ka dawo Ka Kwankwasa,Yace to ya tafi.

Fu'ad Bai San Su Jauro bane tsofaffin samarin Rumaila ne gaba daya a majalisar,Jauro anzo daga Lagos an Zama Dan Sanda,dabara yayi kudin da yake samu a can ya shiga makaranta yayi Yar Diploma dinsa Allah ya taimake shi ya samu Aiki.
Sauran Kuma duk cirani suke zuwa sun Dan waye sunfi Wanda basa fita a garin,wannan majalisar itace ta manyan Yaran garin samari masu tashe, Fu'ad ya zauna a cikinsu bayan ya Basu Hannu sun gaisa,wani aciki Iro yace Oga kafa jefa ka cafke,Rumaila Sarkin kyau da Yanga Kaine ka same ta,Jauro yace Kai Kamar saukar Aradu Haka naji Dana ji an Mata aure har na fara Tara kudin lefe,Sai da nayi sati Ina kuka, Allah na tuba Iya ta Sha zagi a wajena nayi tunanin Iya ce ta Mata aure da me kudi Ashe sai Naga Handsome ne Irinka,Iro yace samari da dama sunga Iftila'i a garin nan,Gashi tayi aure ta bar kawayenta Basu Yi ba,Jauro yace ai na tsani Rabin Nan Bata da hankali ko kadan da Yar Iskar Sauden Nan me Kama da Agwagwa, Fu'ad yaji wani kishi ya soke shi Ana ta Yabon matarsa,su Kuma mutan Kauye ba hankali,Wani Sabo yace Gaskiya Oga ka Dace Murmushin Rumaila Kawai ya Isa kaji kanka Yana wani juyawa,Ibrahim yace tafiyarta Kawai Jauro tafi birgeni,da Sauri Fu'ad ya kalli Jauro ransa a bace ya karewa Jauro kallo Dan matashi kyakyawa Caras dashi duk da Bai Kama ko kafar Fu'ad a kyau ba Amma shi Fu'ad yaga Jauro fa yayi shima

Please Login or Register in order to submit comment