Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alhaji ko wani dake waje ɓatar Abdul, a cewar ta bata so a ɗaga masa hankali alhali ya na gun kasuwancinsa, hakan ya saka kowa ya ja bakinsa ya tsuke suka zubawa sarautar Allah ido.

Can zuwa sha biyu na rana Hajiya Hasina ta fito da shirin fita unguwa, sai dai ba ta yi wata kwalliya ba, duk da cewa mayafi ta saka, amma kallo ɗaya zaka mata ka gane bata cikin walwala.

Da fitowar ta kai tsaye gun motarta ta nufa, Direbanta ne ya zo da sauri don karɓar makulli, domin a zatonsa shi zai fitar da ita, ga mamakinsa sai ya ji ta ce "A'ah! Hamisu komawakka ka huta, yau da kaina zan hita, dan yawo zan yi da yawa a garin."

Da mamaki ya kalle ta ya ce "Amma hajiyya baki cikin yanayi mai daɗi, kuma kahin Alhaji ya tahi sai da yammin umurnin cewa in tabbatar duk inda za ki na na kai ki, kat in bari ki hita da kanki."

Ɗago kanta ta yi da alama zancensa ya ɓata mata rai, cikin alamun fushi ta ce "Yau kuma sai nicce ma ban buƙatat tuƙinka, ka banni in ji da damuwata, so ni kai in kai rahoton ɓacewar ɗana wurin 'yan sanda da kahwahen yaɗa labarai kahin Alhaji ya dawo."

Har ya buɗi baki zai kuma cewa wani abu, ta ɗaga masa hannu ta na cewa "Ban son jin komi dagga gareka, in kakƙara yi min gardama wallahi a bakin aikinka."

Ta na gama faɗa ta shige motar tare da mata key ta juyo hancin motar da ƙarfi, har ta na yunƙurin bige Hamisu direba, da ba don ya janye da sauri ba, da ɓarna ta auku.

Jiki a sanyaye Hamisu ya isa teburin da Baba direba ke zaune yana kallon duk abinda ke faruwa a gun, ya zauna kawai bai ce komai ba.

Haka ma Baba Direba bai ce komai ba, amma yana ji aransa cewa Uwar ɗakinsu tana da sa hannu a ɓatan yaron nan, yanzu ma wata munaƙisar za ta je ƙullowa wata ƙila, duk kuwa da an ce zato zunubi ko ya kasance gaskiya.

¥¥¥¥¥¥¥

Hajiya Hasina na barin gidan ta miƙi hanya sosai, maimakon ta nufi station ko gidan rediyo sai ta durfafi cikin gari, gidan ƙawarta Kulu mai adashen sharri, da yake awa biyu baya kenan da suka yi waya da ita, ta shaida mata cewa sha biyu na rana su Gumush za su zo karɓar kuɗin aikinsu, don kuwa sun dawo daga aikin da ta saka su.

Mintuna ashirin ne suka kai ta cikin ƙofar Atiku, da yake a unguwar gidan Kulun yake, sai da ta shiga da motarta har cikin lungunsu, sannan ta faka nesa kaɗan da gidan.

Ta fito cike da nishaɗi hannunta riƙe da ƙatuwar jakarta, ta ƙarasa gidan a ƙafa.

"Assalamu alaikum!"

Ta yi sallama a ƙofar gidan, ba tare da ta jira an amsa ba ta faɗa ciki kai tsaye ta na faɗar "Ina kike mai adashen sheri?"

Da murna Kulu ta fito daga ɗakin tana cewa "Gani nan Hajjiyata! Aiki ga mai ƙare ka, mu shiga ciki."

Murmushi ne kwance a fuskar hajiyar ta nufin ɗakin tana yiwa Kulu mita.

"Gaskiya Kulu ki canza wanga baƙin gida, haba! Dan Allah duk kuɗɗin da kika samu a ce kina zaune cikin wagga baƙar shiya? Wai don bala'i ko mota bata shigowa lungun ga sai dai a aje ta garkat wani? habah!"

Mitarta take har suka isa cikin ɗakin Kulu bata ce komai ba sai dariya da ta yi.

Maimakon ta tamka Hasina a waccan maganar sai cewa ta yi "Hajjiya ga sunan ga ki."
Ta nuna su Gumush da suka bararraje akan ya galgalallun kujerin falon.

Daƙyar Hasina ta iya zama a kan kujerar, sai da Kulu ta ɗauko mata filo ta ɗora sannan ta zauna a kai, ta na kallon su Gumush da murmushi a fuskarta.

Gumush ne ya ce "An gaida Hajjiya mai yawo da kuɗɗi, nerori basu wuya ga hannunki ga mu mun taho an ce kina biɗar mu."

"Ƙwarai da gaske, kun yi min aikin da nijji daɗi nai sosai, tun shiga ta gidan Alhaji ba a taɓa ranar da niyyi hwarinciki ƙwarai ba irin na yau, don ko kun kawas min da dodon da nit tsani gani a duniya, yanzu ku hwaɗamin nawa at ladar aikinku?"

Wata uwar Shewa Gumush da yaransa uku suka buga, sannan ogan na su ya ce "Ai Hajjiya ki ɗai kwatanta, mun san zaki yi muna adalci."

Murmushi kawai Hasina ta yi, ta buɗe jakarta ta ciro bandir ɗin 'yan dubu guda huɗu ta ajiye masu a gabansu.

Ihu suka hau yi suna godiya, Gumush ya yi saurin kwashe kuɗin ya miƙe ya na faɗar "Ku taso mu tahi, sai mu shaggun madatsa, yau duk sai mun addabi kowane ƙaramin ɗan iska da at madatsa."

Su na gama faɗa suka yi gaba har sauran sun fice, Gumush ya dawo daga baya ya ce "Hajjiya mun gode, ko gobe an ka samu wani aiki irin wanga ko ma wanda yat hishi karki ji komi ki kira mu, zamu miki shi sussettifully." Ya faɗa wai shi a dole ya ji turanci.

Da gama faɗa ya juya ya bar ɗakin.

Kulu kuwa har jikinta ke ɓari ta ga an ajiye mata nata kuɗin, gajin haƙuri ta yi, ta ce "Hajjiya nihwa? Ina nawwa?"

Dariya Hasina ta yi ta ce "Matsalata dake kenan Abbukiyata gajin haƙuri, to ga na ki."

Ta faɗa a lokacin da ta zura hannu jaka ta ɗauko dubu ɗari biyu ta bata.

A raine ta kalli kuɗin ta ce "Haba dai Hasinata! Waɗanga ai ke san sun min kaɗan, ko su sun hini samu hwa?"

"To ai sun hiki shan wahalar aikin." Ta mayar mata da zance.

Ita kuwa ta ce "A'ah hwa Hajjiya! Ni ke san hat inda nissamo su? Sai da hwa nittahi har tsakiyar madatsa, nit lalubo tataccin 'yan daba sannan ni sasu aikinki."

Gyaɗa Kai Hasina ta yi da murmushi a labbanta ta ce "Ina motata sun kawo miki?"

Maƙullan ta miƙo mata ba tare da ta yi magana ba.

"Riƙe su can hannunki, ki ɗauki motar ki ƙara na baki ita halak malak, sai dai in aikina ya tashi zaki bashe ta amin."

Ihun murna Kulu ta saka, sai da ta gama murnarta da godiya, sannan ta ce "Ni kam Hajjiya Alhaji Munir hwa? Ya san shegen ɗan nan ya ɓace?"

Wata Shewa Hasina ta yi ta ce "Ina hwa yassani? Ai na hana kowa ya hwaɗa mai, kuma nima ban hwaɗa mai ba, don ban son ya taho ya ɓata min ranar hwarincikina, ke san yau dole in yi kwanan hwarin ciki."

Ta ƙarashe zancen cike da fara'a.

Kulu ta ce "Kai! Gaskiya sai yanzu nika ganin ba mu kyauta ba, don yadda Alhaji ka son ɗan nan ya na iya haukacewa dan rashi nai."

Miƙewa Hasina ta yi ta na jan wani uban tsaki tare da faɗar "Ke shi at matsalakki wallahi, to ni ke ga tahiyata, in kina jin tausai nai ki tai ki dawo da shi."

Ta na gama faɗa ta yi fuu! Ta wuce, Kulu na lallashinta bata ko saurare ta ba, ta faɗa motarta ta wuce station ta kai report don kare kanta daga zargi, daga nan ta je gidan rediyon vision fm sokoto da garkuwa FM da sauran kafafen yaɗa labarai ta kai rahoto, sannan ta wuce gida.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Bawan Allah Abdul kuwa, a haka ya wanzu ya na tafiya a cikin jeji har shuɗewar wasu sa'o'i ba tare da ya haɗu da kowa ba.

Zuwa lokacin yunwa ta gama cinsa ya rasa abinda zai ci, don haka ya shiga zince-zince a ƙasa, duk wani abun da ya gani a ƙasa mai kama da abinci ɗauka yake ya kai baki, haka ma daƙyar ya samu wasu ruwan kududdufi ya ɗiba ya sha.

Tafe yake a hanya tun ya na kuka har hawayensa suka ƙafe, ya rasa wanene ya masa wannan ɗanyen aikin, duk da cewa shi ƙaramin yaro ne amma ba wanda ya fara zargi a ransa inba Mamansa ba, ya na ji a ransa da saka hannunta a jefar da shi da aka yi.

In ba ita ba, waya isa ya shiga ɗakinsa har kan gadonsa ya dauƙo shi ya fito da shi daga gidansu?

Haka ya ci gaba har dare ya riske shi, ya yasu a nan cikin tsakuwoyi ya kwanta ya na tunani kala-kala.

A ransa yake cewa "Allah sarki ni! Yau ina haɗaɗɗen gadona? Ga ni kwance babu ko shimfiɗa."

Abbunsa ne ya faɗo masa a rai, a take ya shiga tuno ran da suka rabu na ƙarshe a daren ranar da zai yi tafiya zuwa kwatano, ya zaunar da shi su na hira, a cikin hirarsu yake cewa "Abdul ɗina gobe tun da sahe zan yin tahiya, ka kula da kanka, ga mamakka nan na san zata kula da kai sosai, ka mata biyayya, ka maida hankali ga karatu, in zan dawowa ina kawo maka kayan daɗi, sannan bayan na dawo muna komawa asibiti a duba ma ƙahwakka ka ji? Yanzu dai mi kaka son in kawo ma?."

Gyaɗa Kai ya yi ya ce "Abu dai mai daɗi da kyau."

Abdul na zuwa nan a zancen zucinsa ya share hawayen da ya gangaro masa, ya rufe idonsa, nan take barcin wahala ya yi gaba da shi...

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Bayan kwana biyu da ɓatar Abdul Alhaji Munir ya dawo gida cike da farin ciki da sa ran zai ɗora idonsa a kan tilon ɗansa, don ko ya jibgo masa tsaraba mai yawa, sai dai me? Ya dawo gida ya tarar da mummunan labari wanda ya tarwatsa tunaninsa da farincikinsa gaba ɗaya.

Ya shiga tsananin tashin hankali da damuwa da ruɗewar ƙwaƙwalwa, a ranar bai samu runtsawa ba, zuciyarsa cike da zargi.

Washegari ya tara dukkan mazauna gidansa ya shiga tuhumar su a kan ya a ka yi ɗansa ya ɓata?, sannan me suka yi bayan ɓatarsa? me yasa ba'a gaya masa ba?"

Baba Direba ne ya yi karaf ya ce "Tun shekaranjiya da yat ɓace munka so hwaɗa maka, amma Hajjiya ta hana mu sanar maka ta ce za ta biɗo shi kahin ka dawo."

Juyawa ya yi zuwa ga Hasina ya na tambayar ta cike da tuhuma.?

"Missa kin ka min haka Hajjiya?"

Nan take idonta suka kawo ruwa, ta yi rau-rau da ido, cike da damuwa ta ce "Da ma ni ban son a ɗaga maka hankali, shiyasa nicce kat a hwaɗa ma, amma ai na kai rahoto a...."

Bata samu damar ƙarasawa ba saboda saukar wani gigitaccen mari da ta ji a kuncinta, cike da mamaki ta ɗago idonta da take gani disishi ta sauke su a fuskar Alhaji, da yake tsaye cikin ficewar hayyaci.

Mamaki ne ya rufe ta, yayinda Alhajin ke tsaye cikin ficewar hayyaci, shi kan shi bai san ya aka yi ya mare ta ba....

Sai dai bai damu da hakan ba ya hau ta da masifa a gaban 'yan aikinta, faɗar ya ke "Ke san abinda kinka aikata min kuwa? Ina hankalinki da wayonki sun ka tahi? Ta a'a tilon ɗana kuma amanata ka ɓacewa baki hwaɗamin ba? Ya ma anka yi har kuka bari masu garkuwa da mutane suka shigo har cikin gida sun ka ɗauke min gudan jinina?"

Ganin Alhaji ya rufe ido ya na ta surfawa matarsa masifa, cikin wani irin yanayi da ba su taɓa ganinsa a ciki ba, ya saka duka ma'aikatan suka sulale daga wajen kafin ya juyo kansu, don ko da ɗai basu taɓa gani ko jin ya yiwa matarsa ko da tsawa ba sai ga shi yau har da mari, dole abin ya bawa mutum tsoro.

¥¥¥¥¥¥¥¥

Lokacin da labarin ɓatar Abdul ya riski 'yan'uwan Alhaji da Mamansu kuwa, Mizbahu da Hajiya Inna sun shiga damuwa matuƙa yayin da su yaya Bilya,Sani da Sunusi suka ji tamkar su zuba ruwa a ƙasa su sha, labarin ya musu daɗi sosai don ko abin nema ne ya samu matar falke ta haifi jaki.

Sai dai sun ɓoye wannan murna a ƙasan ransu, don ko duk ƙwanƙwantonka baka isa ka gano wannan ɓoyayyiyar murnar tasu ba, inka gan su zaka rantse da Allah sun fi Alhaji Munir ɗin shiga damuwa.

Har gida suka je masa jaje, sannan su kansu mutane kan zo har gidajensu don masu jajen ɓatan yaron ɗan'uwansu........


More comment
More typing.........


Follow me on wattpad @ Ruky_i_lawal.






RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*


*DEDICATED TO: YAYA MUKTAR MUSA ƘARAMI (ABU HISHAM)*

MILIYOYIN GODIYA ZUWA GAREKA, RABBI YA BAR ZUMUNCI, ALLAH YA RAYA MANA YARANMU;

HISHAM MUKTAR MUSA ƘARAMI
AISHA MUKTAR MUSA ƘARAMI (MIMIE).

ALLAH YA RAYA SU CIKIN AMINCI, SU TA SO DA ƘAUNAR JUNANSU, SU ZAMA MASU AMFANAR DA AL'UMMA, AMEEN YA RABBI🥰🥰





________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*


PAGE 23-24

Mutane basu sani ba cewa murna ya kamata a taya su ba jaje ba, don kuwa murna ce fal ransu, yanzu abu ɗaya ya rage masu shi ne; su kawar da ƙaninsu don su mallake dukiyarsu, sai dai fa har yanzu da sauran rina a kaba, kuma har yanzu tsugunne bata ƙare ba wai an sai da akuya an sayi kura, domin ko da sun kashe shi za'a raba gado kuma dole za'a ajiyewa yaron dukiyarsa har a gansa, tunda ba a da tabbacin ya mutu ko yana raye.

Suna cikin wannan damuwar ne suka hau teburin shawara bayan sun haɗu a gidan Hajiya inna....

Yaya Bilya duk yafi su ɗaukar zafi, don haka ya kada baki ya ce "Ba abinda yafi kyau sai mu maida hankali mu nemo yaronga mu kashe shi tun kahin wankin hulla ya kai mu dare, don ko wanga aikin namu, shi aka kira da tufkar makaho ta gaba ta baya na warware wa."

Sani ya saki ajiyar zuciya ya ce "Gaskiyakka yaya, dole sai mun yi da gaske, tunda aikin namu a sirrance muka yinai, yanzu dai a ganina mu hanƙura mu ci gaba da biɗat yaron, tun da yanzu Munir ɗin a hannunmu yake sai yadda muka so mu yi da shi."

Sunusi ya gyaɗa kai yana faɗar "Hakane, sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba."

Da haka suka ci gaba da tattaunawarsu har zuwa wani tsawon lokaci, Mizbahu na daga gefe yana kallonsu, duk da ba ya jin me suke tattaunawa, ya san ba alkhairi suke ƙullawa ba.
Bai ce da su komai ba, sai fatan shiriya da ya bisu da ita.

¥¥¥¥¥^¥^¥^^¥¥¥

A can gidan Alhaji Munir kuwa bayan saɓanin da suka samu shi da matarsa, ta bi shi har ɗakinsa ta lallaɓa shi tare da ba shi haƙuri, kuma ta nuna masa bata damu da marin da ya mata ba, da haka ta shawo kansa ya yarda da ita, sannan ta sanar mishi ta kai report ɗin ɓatan Abdul a Marna police station ne.

Ya bata haƙurin marin da ya mata, ta kuma yafe masa cike da sakin Fuska ta ce "Bakomai mijina, na sani ka mare ni ne a cikin zafin zuciya da kuma kiɗima, ɓatan ɗa ai ba wasa ba ne, musamman mai lalura irinta Abdul."

"Nagode sosai Hasina matar albarka!." Ya faɗa cike da sakin Fuska, duk da cewa ba walwala ƙwata-ƙwata a tattare da shi tun lokacin ɓatan yaronsa.

Abinda bai sani ba shine; Hasina fa bata yafe masa da zuciya ɗaya ba, ta ƙudurce a ranta sai ta ɗau fansar wannan marin da ya mata, ko da za ta yi yawo tsirara.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Abdul kuwa tun a ranar da ya tabbatar ba shi da wani mai ceto ko majiɓinci al'amarinsa, duniya ta masa ƙunci, ya rasa inda zai fake ya ji daɗi, shi kaɗai a dokar daji ba ruwa ba abinci, sai dai ya yi 'yan tsince-tsincensa a ƙasa yana ci, ko kuwa ya kakkabo kunnuwan fure ya ci, ruwa kuwa sai Sa'a yake haɗuwa da ruwan kududdufi ya sha, ga shi lokacin ƙarshen bazara ne, ba a fara ruwan sama ba, don haka ne ba wata inuwa mai daɗi ko wani damshin laima da zai zauna ya fake ya ji daɗi, a haka ya ci gaba da tafiya in ya gaji ya zauna ya huta, tunani kala-kala yake har tunanin da ya girmi ƙwaƙwalwarsa a wannan yanayin sai da ya yi shi, bai haɗu da kowa ba bare a samu mai taimaka masa ya maida shi gida gun Abbunsa...

Wani lokacin haka zai zauna yana kuka yana kiran "Abbuna! ka taho ka taimake ni, yunwa zata kashe ni, ga shi bansan hanyar komawa gida ba."

¥¥¥¥¥¥^^

Ranar wuni na uku, Hasina ta nemi izinin mijinta, a kan cewa zata je duba wani ƙanin mahaifiyarta dake kwance a asibiti.

Kai tsaye ya amince mata don ba ya zaton ƙarya daga gare ta.

Tana fita bata zarce ko'ina ba sai gidan abokiyar cin mushenta, da yake a ranar ma ta ƙi yarda Direba ya kai ta.

Ɗaukar Kulu ta yi suka wuce can wani ƙauye dake gaban bafarawa estate domin a can gidan bokan Kulu ya ke.

Isar su ƙauyen Dundume ke da wuya, suka kutsa can ƙarshen garin inda gidan bokan yake, daga nesa da gidan suka yi fakin motar sannan suka ƙarasa ciki da ƙafa.

Layi suka tarar mata ne birjik waɗanda suka kauce hanya, kowacce jira take layi ya zo kanta.

Nan suka hau layi, har bayan shuɗewar awa layi bai zo kansu ba.

Hasina ta kalli Kulu da damuwa a fuskarta ta ce "Ni hwa na hwara gajiya, ke san hwa ƙarya niwwa Alhaji cewa zan je duba Kawu Basiru a asibiti, yanzu dana daɗe an samu matsala, yana iya kiran inna, ita ko ke san kwafsamin zata yi, bata iya ruhin asiri ba."

Kallonta Kulu ta yi da ɗan murmushi a fuskarta ta ce "Abukkiyata ki kwantat da hankalinki, saura kaɗan ai mu kai ga layi, ke san dama shi aski in yattaho gaban goshi ya hi zahi."

Tsagaitawa ta yi tana kallon Hasina don ta ga yanda ta karɓi zancen, jin ba ta ce komai ba kuma har yanzu da alamun damuwa a fuskarta, yasa ta ci gaba da cewa "Habah Hajjiyata! Ki ƙara hanƙuri, yanzu so kikai mu koma ya ci gaba da tuhumarki ɗanai har ya gano ke kinka ɓatar da shi? Ko so kikai Abdul ya samu mai maisai gida?"

Jin tambayoyin da Kulu ta watso mata yasa hankalinta ya yi mugun tashi, haƙiƙa ta yi ragon azanci da bata saka an kashe mata shi ba; ga shi yana son zame mata alaƙaƙai ƙadangaren bakin tulu.

Don haka dole ta haƙura har zuwa lokacin da layi zai zo kanta.

Bayan shuɗewar mintuna sha biyar, layi ya zo kansu, suka faɗa bukkar bokan..

"Salamu alaikum."
Hasina ta faɗa cikin ɓarin baki, domin ta tsorata da yanayin gurin.

"Ke la'ananna!" Boka ya daka mata tsawa ya na faɗar "Ba a min sallama a nan, don ko ba aminci kinka zo nema ba.."

Jikin Hasina ne ya fara rawa da ta yi arba da mummunan mutumin dake zaune a gabanta, kasa yin magana ta yi, sai Kulu ce ta yi magana cikin ƙarfin hali ta ce "A yi hanƙuri boka bata sani ba ne."

"A kiyaye gaba, in ba haka ba, in maida mutum kiyashi..."

Cikin ɓarin jiki Kulu ta ja hannun Hasina ta danƙwafar da ita suka zauna tare a gabansa..

"Meke tafe daku."
Ya faɗa cikin sauti mara daɗin sauraro.

"Dama Abukkiyata ce na rako don ta kawo kukanta gare ka, tana so a mallake mata mijinta, kuma a......"

(Wa'iyazu billahi! mata mu ji tsoron Allah, idan kina da wata damuwa a zuci, ki miƙa ƙoƙon bararki zuwa ga mahaliccin wannan zuciyar, haƙiƙa ya fi ki sanin damuwarki, kuma shine kaɗai zai magance miki, zuwa gun boka ba zai amfanar dake komai ba, face ya saka ki a halaka da taɓewa, ya maidaki mushrika.)

Hannu bokan ya ɗaga mata alamun ta dakata, sannan ya tada kansa sama kamar mai nazarin wani abu, can ya dawo da fuskarsa ya zubawa Hasina jajayen idanunsa ya ce "Na sani, ki na son a mallake miki mijinki ne, ya bar damunki game da ɓacewar ɗa nai, shi ko ɗan a nisanta shi daga gida kuma a shahe mai tunanin gida da kowa da ya sani a ƙwaƙwalwarsa koh?"

Cikin alamun mamaki ta gyaɗa kanta sama alamar tabbatarwa.

Bayansa ya juya, ya ɗauko sauran tarkacensa sannan ya kuma juyowa kamar yanda yake da.

Bukkar ce ta yi shiru baka jin komai, sai 'yan surutan da bokan ke yi ƙasa-ƙasa, yana yiwa kansa kirari.

Wasu ƙullukan gyallaye ya ciro guda biyu, ya miƙa mata ya ce "Wannan na jan ƙyalen ki saka masa a ruwan wanka, ki tabbatar ya yi wanka da su, sannan garin maganin ya bushe a jikinsa, na shuɗin ƙyallen kuwa ki tabbatar kin saka masa a abinci ya ci, yana ci magana ta ƙare."

Cike da murna ta karɓi ƙullukan ta saka a jaka tana godiya, a ranta ta ce "Alhaji ƙaryarka ta ƙare, sai na nuna maka ba a taɓa Hasina a zauna lafiya, don ko kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Ja da ni tamkar ka yi kashi gonar fara ne, ka san kuwa zata rama."

Mintsinar da Kulu ta mata, ita ta dawo da ita hayyacinta.

Kallon bokan ta yi ta ce "To boka yaron fa?"

Dariya sosai ya bushe da ita, can kuma ya gimtse kamar bai taɓa dariya ba, ya ce; "Maganar yaron nan ki bar ta, asiri baya tasiri a kansa sosai, sai dai yanzun nan zan miki aikin da zai mantar da shi kowa nasa, kuma zamu saka tsanar gida a ransa, ta yanda ba zai waiwayo ba, ke ko labarin jihar nan ba zai kuma son ji ba bale ya dawo."

Murna ce ta gama kashe Hasina.

Wani ɗan kasko ya janyo mai kama da tukunya na ƙasa, wanda ya kusan cika da wasu ruwan asiri, ya ajiye shi a gabansa.

Wasu surkulle ya karanta sannan ya shafi saman ruwan da hannunsa, sai ga hoton taswirar Abdul ta bayyana a saman ruwan.

"Ku matso ku ga ni."

Ba musu suka matsa ya nuna masu ruwan ya ce "Ko ba wannan ba ne yaron?"

Gyaɗa kai ta yi bata ma samu damar yin magana ba, ganin Abdul zaune cikin rana ƙwayam, yana sharar ƙwalla duk ya lalace a cikin kwana biyun nan.

"Madallah!" Ya faɗa sannan ya ciro wata tsabga dake kusa da shi, ya kuma karanta wasu surkulle sannan ya shauɗa tsabgar a kan hoton Abdul ɗin.

Take yaron ya yi wata uwar zabura daga zaunen da yake ya miƙe kamar zarararre...

Kallonsa su Kulu suka yi da alamun rashin fahimta.

Shi ko gogan ya taƙarƙare ya kwarara wata uwar dariya dake barazanar tsaga masu kunne.

Sai da ya yi mai isar sa sannan ya gimtse ya ce "Aiki ya kammala, wannan zaburar da kika ga ya yi ta tabbatar da cewa aikin ya tafi yanda ake so."

Cike da tsananin murna Hasina ta zaro kuɗi daga jakarta masu ɗan dama ta ajiye masa, sannan suka miƙe suka bar cikin bukkar zuwa waje; inda har yanzu akwai layi na wasu ɓatattu daga cikin mutane dake jiran fitowar su.


Takawa suka yi har gun da Hasina ta faka mota suka shiga.

Sai kuma a lokacin ne ta duba agogon hannunta, zazzaro ido ta yi ganin agogon ya buga ƙarfe biyu da rabi na rana, ita da ta baro gida sha biyu da rabi, ga shi yanzu awar ta biyu a waje bata ma je asibitin ba.

Cikin hanzari ta ja motar ta nufi cikin gari, a nan ƙofar asibitin specialist sokoto ta sauke Kulu, tare da bata kuɗin napep ta ce ta ƙarasa gida, ita tana sauri ne, zata shiga asibitin a gurguje ta dubo shi ta juya, gudun kada asirinta ya tonu.

Ba musu Kulu ta sauka ta hau napep zuwa gida; da yake ita tana girmama duk wani aiki na mugunta da kuma kare kai daga zargi.

A gurguje Hasina ta dubo kawo Basiru, sannan ta juya zuwa gidanta, domin ta san Alhaji na nan bai fita ba.

Ko da ta isa gidan ta tarar da 'yan sanda suna bincike, don haka cikinta ya ɗuri ruwa, fargaba ta kamata, kamar ta juya ta bar gidan ta ji, amma bata da mafita face ta tsaya ayi duk ya ce za'a yi; ta sani dai kushewar baɗi sai baɗi, mai rabon ganin baɗi kuwa sai ya kai, don haka ta shige cikin gidan kai tsaye.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

A ranar wuni na uku Abdul ne tafe a galabaice, ɗan idonsa ɗayan ma ya fara gani disishi, saboda yunwa da ta masa mugun illa, ga shi tun jiya yake cikin tsanani, ya yi-ya yi ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa wani abu game da shi amma ta kasa.

Jin ƙafarsa ta yi tsami, yasa ya nemi guri ya kwanta,

Please Login or Register in order to submit comment