Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli Hasina dake tsumayen amsarta ta ce "Ke dai bari Hajjiya wanda ya yi nisa ai bai jin kira, kuma shi ɓatacce bai gane kan ɓata yake sai ya hwaɗa cikin kwatamin nadama."
Dariya sosai Hasina ta dinga yi na tare da ta lura cewa yaɓa mata magana ne Kulu ta yi ba.

Sai can ta tsagaita da dariyar ta ce "Wallahi ko Kulu da gaskiyakki, basu ganewa da sun bar wahalar da kansu."

Kulu ta mata wani irin kallo mai nuni da shashantar da mutum ta ce "To ke gani ba?, don haka mance da su hito mu bi layi kahin wasu su muna rigaye."

Da wannan maganar suka rufe babin hirar tasu tare da fitowa daga motar, Hasina ta rufe motar suka nufi gun layin, sai wani takun ƙasaita Hasina ke yi tana shan ƙamshi Kulu na take mata baya.

Kulu ta ce a ranta " ki gama iskancinki Akwai ranar ƙindillacin tana zuwa, ranar da haƙƙin ɗan talikin yaron nan Abdul ya tashi kama ki zaki yabawa aya zaƙinta."

Sun jima a layin sai bayan shuɗewar awanni biyu sa'annan suka samu ganin bokan, a nan Hasina ta bayyana masa buƙatar ta son ganin ta samu haihuwa da alhajin.
Boka Barkuza ya ƙyalkyace da wata mahaukaciyar dariya data firgita su sannan ya gimtse fuska, ya karanto wasu surƙulle tare da shauɗa gezar hannunsa a ƙasa sannan ya ɗago da gwala-gwalan idanunsa ya kalli Hasina ya ce "Aiki ja, ki aje maganar haihuwa yanzu don akwai wani tarnaƙi da ke tunkaro ki a yanzu, mu mai da hankali kan binciko matsalar dake tunkaro ki tana son shiga tsakaninki da burinki kahin ayi maganar haihu, don ko zaki haihu da Alhaji ba yanzu ba..."

Jin wannan batun ya saka hankalin Hasina ya yi mummunan tashi.
A haka suka yi bankwana da boka bisa alƙawarin zai binciko mata tarnaƙin dake fuskanto burin rayuwarta.

@@@@@@@@@@

Bayan Mahmud ya rufo part ɗinsa ya ɗauko plate ya zubawa Abdul abinci yana ci, kamar wanda ya tuna wani abu sai ya miƙe ya nufi uwar ɗakansa ya ɗauki wayarsa ya kira Likitansu don ya zo ya duba Abdul yagaya masa matsalar yaron da kuma halin da yake ciki.

Jiyo ihun Abdul ɗin daga falo ya saka shi katse wayar ba shiri ya yo waje don ganin meke faruwa.

Tarar dashi ya yi ya yada cokalin ƙasa sai faman ihu yake yana riƙe baki.
Dasauri ya yi kansa yana duddubawa jikin yaron don har cikin ransa yake jin kukan yaron.
A ɗan firgice yace "Abdul Menene?"

"Halshena, na taune halshena." Ya faɗa cikin ƙarfin hali.
Tallabo shi ya yi ya duba har gun ya fashe kaɗan, haka ya cigaba da rarrashinsa.

Bayan mintuna sha biyar sai ga Likita ya iso, nan take ya shiga yiwa Abdul gwaje-gwaje.
Bayan ya kammala Mahmud ya kwaso magungunan da Yasir ya bawa Abdul a Kano ya nuna masa.

Nan ya ware waɗanda za'a yi amfani dasu ya nunawa Mahmud tare da rubuta mashi ƙarin waɗanda ake buƙata.

A nan ya mishi bayanin lalurar yaron ya nemi da a sama masa sanduna.
Dr Amir ya kalli Mahmud yace "Kasan ni ba ɓangaren ƙashi nake ba, amma zan bincika maka gun aminina dake ɓangaren, duk yanda muka yi zaka ji insha'allah."

"To madallah Nagode sosai, sai na ji ka." Cewar Mahmud.
Daga haka suka yi sallama, Dr Amir ya fito takawa ya yi zuwa inda ya ajiye motarsa.
Yana zuwa dai-dai part ɗin Hajiya suka haɗu da Hajiyar lokacin ta fito don Sallamar bakonta lokacin kusan ƙarfe tara na dare.

"Barka da dare Hajiya." Cewar Dr.
Cike da sakin fuska ta kalle shi, "A'ah! Dr kai ne a gidan? Yaushe ka zo?" Ta tambaya da mamaki a fuskarta.

Da murmushi a fuskarsa yace "Ban jima da zuwa ba, bros Mahmud ya kira ni, ina cikin uzuri ne shiyasa ban leƙo mun gaisa ba."

Cikin alamun kaɗuwa ta zaro ido "Meke damunsa ne?"
"Kwantar da hankalinki Hajiya bashi ne mara lafiyan ba yaron dake tare dashi ne." Ya faɗa.
Wani irin ɓacin rai ne ya taso mata, amma don bata son Mahmud ya gane ta saki fuska ta ce "Ok yana part ɗinsa ko?"
"Eh." kawai yace mata ya mata sallama ya ƙarasa bakin motarsa a hanzarce, ya shige yabar gidan.

Cike da ɓacin rai mara misaltuwa ta juya ba tare da tayi abunda ya fito da ita daga sashenta ba, ta nufi sacen Mahmud tana zancen zuci.
Lallai Son ya raina ni, da nace yaron nan ba zai kwana a gidan nan ba shine zai nuna mun ban isa ba koh?"

Ƙwanƙwasar ƙofar sashen take tun ƙarfinta, tsabar ɓacin rai ta manta da bell ɗin ƙofar bare ta matsa.

Jin irin wannan bugun ƙofar da ake cikin rikitaccen yanayi, ya saka shi tsurewa, bako shakka ya san wannan aikin Hajiya ne, wataƙil ta samu labarin yaron yana tare da shi, to waya gaya mata?.........





RUKY I LAWAL CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*


DEDICATED TO: ALL MEMBERS OF AREWA WRITERS ASSOCIATION, SON SO FISABILLAHI NAKE MUKU❤️🥰❤️


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_



PAGE 51-52

Cike da ruɗewa ya ja hannun Abdul ya nufi uwar ɗakansa ya saka yaron a banɗaki ya rufe tare da masa umurnin duk abinda za'ayi ko kyakkyawan motsi kada ya yi har sai in shi ya bashi dama.

Rufo ƙofar banɗakin ya yi da makulli tare da jefa makulin saman walldrob ɗinsa.

A gigice ya fito jin ƙarar bugun ƙofar na daɗuwa har yana ƙoƙarin fasa masa dodon kunne.

Cikin dakiya da nuna kamar bai san komai ba, ya zo ƙofar ɗakin aro Muryar masu barci ya ce "Waye ne?"

Jin muryarsa yasa ta daga murya tace "Ni ce buɗe."

Ba musu ya buɗe tare da janye wa ya bata hanya.

Bata yi wata-wata ba, ta shiga dube-dube a falon, kamar wacce aka bawa ajiyar rai ya ɓata.

Bin bayanta Mahmud ya yi yana cewa "Hajiyata me kike nema ne da dare haka?"

Harara ta aika masa wacce ta saka shi ƙara kiɗimewa ta ce "Ba dai ka raina ni ba ko Son? Ince bana buƙatar zaman yaron nan a gidan nan shine zaka nuna mun ban isa da kai ba koh?"

Tana maganar ne cikin masifa da ɗaga murya.

"Wane yaron kuma Hajiya? Ina ce ke da kanki kika saka a fitar da shi, taya zan gan shi, har ki yi tunanin ko na ɓoye shi?"

Kallonsa ta yi taga ba alamun tsoro a tare da shi, hakan yasa wani sashe na zuciyarta ya bijiro mata da tambaya, "Idan har yana nan to ina ya ɓoye shi? kamar ma daga barci ya tashi fa."

Kamar yasan me take tunani ya hau mitsitsika ido yana hamma......

Duk da hakan bai saka ta haƙura ba, sai da ta shiga har uwar ɗakansa ta duba ba Abdul ba dalilinsa.

Ganin haka ya saka ta tsaya ta ce "Yanzun nan fa na haɗu da Dr yace ya zo duba wani yaro anan sashenka, amma yanzu kace baya nan?"

"Hajiya da yana nan ai da kin ganshi, kawai na tausaya masa ne, ganin baya da lafiya na kira likita ya duba shi, yana gama aikinsa na haɗa masa maganin a leda na fitar da shi ta ƙofar baya, ki yarda da ni."

Da wannan kalaman ya yaudare ta ta yarda da zancensa. Kawai sai ta juya tana faɗar "Shikenan Allah ya maka albarka je ka ƙarasa barcinka, amma da farko hankalina ya tashi ganin zaka bijire mun, sai na yi tunanin kodan yana gidan gadonka ne kake ganin ka isa ka yi abunda ka ga dama..."

Tana gama faɗa ta juya ba tare da ta jira cewarsa ba, ta fice daga sashen zuwa nata.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke ganin ya sha daƙyar, ya bi bayanta tare da rufo kofar sashensa, ya bar makullin jikin ƙofa, gudun kada ta shammace shi ta dawo ta buɗe ƙofar da spare key dake hannunta.

@@@@@#

Haka ya ci gaba da ɓoye Abdul a sashensa har na tsawon mako ɗaya, ba tare da wani daga cikin mutanen dake rayuwa a gidan sun sani ba.

Domin in zai fita sai ya kulle yaron a daki, ya bashi ɗaya makulin ya ja masa kunne da kada ya sake ya koda leƙo waje ne, idan ya dawo shi zai buɗe ƙofar da makullin hannunsa.


A wata ranar Litinin Bayan fitar Mahmud gun aiki, da misalin ƙarfe 11:30 na safe Abdul na kwance kan gadon Mahmud yana shaƙar barcinsa cikin kwanciyar hankali, juyawar da zai yi haka, ya ji ya rungume wani abu mai gashi ga santsi, kafin ya gama tattance miye magen dake kwance daf da shi ta zabura tana neman guduwa, cikin rashin Sa'a tabi takan fuskarsa.

Saukar daginta akan fuskarsa ke da wuya ya buɗe ido tare da kwarara wani uban ihu mai firgitarwa, gashi shi ba ƙafafu ba bare ya gudu don haka ya silmiyo ƙasa cikin kiɗima.

Ita kuwa mager ta fara zagaye ɗakin tana neman fita..
Ko da Abdul ya gama gane mage ce a gabansa, abinda yake tsananin tsoro a duniyarsa, kawai sai ya hau rarrafe ya nufi ƙofar falon yana kwarara ihu.

Har ya kusa fita, ya tuna da makullin kofar dake ajiye a bedsite durowa, a kiɗime ya juyo da rarrafe ya ɗauka ya fice da sauri itama mager ta biyo bayansa kowa na gudun wani, wannan fa shi ake kira banza ta kori wofi.

Ashe daidai lokacin da Abdul ya ratsa ihu a karon farko, Hanne mai'aiki ta zo wucewa ta kusa da part ɗin Mahmud.

Jiyo ihun yaro kuma ga part ɗin a rufe, ya sakata ƙara sauri don kai gulma da zafinta, don bata raba ɗayan biyu, kodai shegen yaron nan ne Boss ya ɓoye a ɗakinsa ko wani abun dabam ke faruwa.

Cikin mintuna da basu wuce uku ba sai ga Hajiya ta fito cikin sauri, kallo ɗaya zaka mata kasan cike take fal da Masifa.

Hanne ta biyo ta abaya don bawa idonta abinci.

Isowarsu ƙofar part ɗin ya yi dai-dai da lokacin da Abdul ya buɗe ɗakin da makulli yafito da rarrafe cikin sauri, da alama iya ƙarfin gudun gwuiwoyinsa kenan.

Ganinsa ya ɓatawa Hajiya rai ba kaɗan ba, domin da za'a bata aron rai a ranar da har shi sai ya ɓaci saboda wannan abun da ɗan cikinta ya mata.

"Chabɗijam! Lallai Mahmud ka gama raina ni, amma bakomai Allah ya dawo da kai lafiya zamu gamu ne..."

Ta yi ƙwafa cikr da haushi ta ci-gaba da bambaminta kamar Mahmud ɗin na tsaye gabanta, ta ce "Bari na ɓatar da kai kafin ya dawo sai mu ga abinda zai iya yi."

Tana kai nan ta kira ma'aikatan gidan maza ta masu umurni su fitar mata da wannan mummunar halittar...

Ba musu suka yi kan Abdul don cika umurnin uwar gidan tasu.

Abdul yana kuka shaɓe-shaɓe ya fara magana kamar haka "Don Allah Mama ki yi hanƙuri, ki taimake ni wallahi in kit kore ni bansan inda zanna ba..."

Katse shi ta yi da faɗar "Yi mun shiru, Ni na tsani Musakai ba zan zauna da kai ba wallahi."

Cikin kuka Abdul ya ce "Meyasa Mama? Me yasa Mutane suka tsane mu mu Musakai? shin laifin waye ya sa muka zama musakai?. Malaminmu na islamiyya ya ce ba kyau wulaƙanta ɗan adam, sa'annan ba wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda ya fi jin tsoronsa..."

Ranta ne ya yi ƙololuwar ɓaci wai ita ɗan wannan talikin yaron zai ma wa'azi?

Cikin ɓacin rai ta nufe shi gadan-gadan har ta daga hannu zata......





Hmmm! Kome Hajiya zata ma Abdul?
Mahmud zai dawo gida ya tarar da Abdul kuwa?

Miye makomar rayuwar Abdul in har hajiya ta kore shi?


Don jin wadannan amsoshin ku biyo NI a pages na gaba.




Kada ku manta More comment more typing, in na ji tsit kunsan sauran masoya🥰



Alƙamin:✍🏻✍🏻✍🏻UMMU INTEESAR NE❤️❤️🥰


*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*


*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*

DEDICATED TO ALL MEMBERS OF HALITTAR ALLAH CE FANS GROUP.

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR_RAHMANIR_RAHIM*


PAGE 53-54

Cikin ɓacin rai ta nufe shi gadan-gadan, har ta daga hannu zata mare shi, suka jiyo sautin shigowar mota cikin hanzari.

Waigayawa suka yi gabaki ɗayansu don ganin waye.
Mahmud ne ya fito daga motar a sukwane ya nufi inda Abdul ke sunkuye yana kuka.

Dama shi tun lokacin da agogon hannunsa ya buga ƙarfe sha ɗaya na safe yake jin matsananciyar faɗuwar gaba, da yaga abun bana ƙare ba ne shine ya ɗebo mota ya dawo gida domin tunawa da ya yi da ajiyar sirrin dake ɗakinsa. Shigowarsa gate ɗin gidan ke da wuya ya hango tashin hankalin dake faruwa.
"Shi ke nan yau kashina ya bushe, tabbas yau nasan daƙyar nasha a hannun Hajiya."
Ya faɗa a ransa.

Sai dai wannan fargabar bata hana shi tunkarar matsalarsa don magance ta ba.

Yana isa gun ya tsaya a gaban Abdul tare da kare shi, ya haɗa hannayensa biyu guri ɗaya tare da zubewa akan gwuiwoyinsa yana magiya.

Ganin hakan ya saka su Hanne da sauran ma'aikatan 'yan ganin ƙwaf suka watse, don sun san waye Boss sarai, baya ɗaukar raini, idan suka yi wasa wannan kallon da zasu tsaya zai zame masu silar kubcewar ayyukan da suka dogara da su.

Ita ko Hajiya tana nan tsaye sai huci take, har yanzu bata sauke hannayenta ƙasa ba, sai cika da batsewa take.

Magiya ya fara mata kamar haka:
"Don girman Allah Hajiya ki yi haƙuri, ki tausayawa yaron nan, ki dubi maraicinsa da halin da yake ciki na ƙunci da kuma larurar dake tare da shi, ina tsoron abinda zai biyo baya bayan kin kore shi daga gidan nan, ba mamaki zai koma faɗawa rayuwar jeji cikin tsuntsaye Da dabbobi, sa'annan ina tsoron Allah ya kama mu da laifin ƙin taimakawa wannan rayuwar dake buƙatar taimakon gaggawa.."

Yana maganar yana marairaicewa kamar zai saka kuka.
Sai a lokacin Hajiya ta sauke hannunta, da alama zuciyarta ta fara sanyaya.
Ba tace masa komai ba kuma bata bar wajen ba.

Ganin wannan nasarar da ya fara samu ya saka shi cigaba da cewa "Hajiya a ganina da kin haƙura mu taimaki rayuwar wannan talikin yaron, wataƙila hakan ya zama silar rabautarmu duniya da Lahira, sannan na maki alƙawarin zan nemo iyayensa a duk inda suke a faɗin duniya don maida shi ga tsatsonsa kuma mahaifarsa."

Yana kai nan a zancensa ya ga Hajiyarsa ta juya fuu ta yi gaba abinta ba tare da ta sake tamka shi ba.

Zahiri Hanne mai'aiki da Ƙasimu mai gadi basu ji daɗin wannan al'amari ba, don kuwa akan idonsu komai ya faru. Saboda bayan watsewar ma'aikatan ashe su basu tafi gaba ɗaya ba, wata kusurwa suka samu suka maƙe don ganin ya zata kaya, duk da basa jiyo sautinsu Mahmud ɗin.

Ganin juyowar Hajiya a sanyaye ya sagar masu da gwuiwa don da alama ta haƙura, cikin hanzari suka gudu daga malaɓarsu.

Shi kuwa Abdul har zuwa lokacin kuka yake ba ƙaƙƙautawa.

Miƙewa kawai Mahmud ya yi ya ja hannunsa ba tare da ya ce ƙala ba, ya shige da shi ɗakinsa ya rufo ƙofa.

Zama ya yi gefen gado yana dafe kansa da ya fara sara masa, zahiri baya son hayaniya, ga kukan Abdul da yake ji har cikin ƙoƙon zuciyarsa.

Don haka ya shiga rarrashin Abdul har sai da ya yi shiru sannan ya ce "Ka kwantar da hankalinka Abdul insha'allah ba inda zaka kana nan gidan tare damu."

"Don Allah yaya ka taimake ni, wallahi in tak-kore ni bansan inda zanina ba, sai dai in koma daji."
Abdul ya faɗa cikin dasasshiyar murya.


Sosai yake jin tausayin yaron a ransa, ya rasa inda zai saka ransa ya ji sanyi. Nan take ya tuna da zancen abokinsa Dr Yasir inda ya ke masa tuni da yanda Hajiya ta tsani nakasasshi da talakawa kuma ya nuna masa kada ya je gidan da yaron ya bar masa shi, amma fafur yaƙi.

Nan take yaji nadamar bijirewa shawarar amininsa.

Nan ya fara tunanin ko dai zai kira Dr Yasir ne ya nemi shawara? Sai kuma ya ji kunyar abinda ya masa. "Kai ina! Ba zan iya ba, ai abin da kunya." Ya faɗa a ɗan bayyane.

Da yamma Mahmud ya shiga sashen Hajiya don gaidata anan ya tada maganar zaman Abdul a gidan, yana ƙara bata haƙuri ya ce "Ki ƙara haƙuri Hajiya na bawa Dr cigiyar sanduna, kafin nan zan nemo masa iyayensa na maida shi gida, bana son ya kuma shiga garari tausayi yake ban matuƙa."

Hajiya ta nisa ta ce "Shi ke nan na fahimta kuma na amince, amma ka ci gaba da ajiye shi a sashenka, bana son ganin wulgawarsa ta gaban idona, tsoron fuskarsa nake."

Murna ce ta bayyana a saman fuskarsa ya ce "Na gode sosai Hajiyata Allah ya ƙara girma."
Tashi ya yi ya fice da murna. Raka shi ta yi da ido a ranta ta yi wani zance wanda ita kaɗai tasan me ta ƙissima, ta yi murmushi itama ta tashi ta haye sama.

Bayan kamar kwana huɗu Maganar komawa ƙaro karatun da Mahmud zai yi ƙasar Spain ta tashi.

Dama tuni ya yi applying lokaci kawai yake jira, tsintar Abdul da ya yi shi ya mantar masa da tafiyar, sai gashi ƙwatsam abokinsa ya yo masa waya yana tunatar da shi wajibinsu ne su yiwa ƙasar zobe a wannan satin.

Sosai ya yi murna dama ya jima yana jiran lokacin amma tunawa da Abdul da ya yi ya ji kamar ya fasa tafiyar.

Sai kuma ya tuna ai Hajiya ta amince da zaman yaron a gidan don haka ya ci gaba da shirye-shiryensa a gaggauce ba tare da ya sanar da yaron tafiyar ba gudun kada ya tayar masa da hankali.

A daren ranar da zai wuce ya samu Hajiya a sashenta ya ƙara tuna mata da Abdul tare da damƙa amanar yaron a hannunta ya ce "Na yi waya da Dr ya ce ana kan bincike da zaran an samu sanduna zai zo ya sanar miki, sai ki bada kuɗin kawai ki karɓa masa pls Hajiyata ki mun wannan taimakon."

Da farko ta so ta nuna masa rashin amincewarta amma sanin halin tilon ɗan nata ya saka ta bar abun a zuciyarta.
"Shi ke nan insha'allah! Allah ya bashi lfy."

Sosai ya ji daɗin amincewarta da haka suka ci gaba da hirar bankwana domin ya sani gobe iwar haka baya ƙasar...


Hmmm! Yaya zata kaya bayan tafiyar Mahmud?

Anyah kuna ganin Hajiya zata bar Abdul ya zauna a gidan kuwa?🤔

To mu je zuwa dai don jin yanda zata kaya.


More comment more typing🥰












Ummu inteesar ce❤️❤️❤️❤


️*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*


*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*

DEDICATED TO: Yar malam member ta halittar Allah ce fans group ina jin daɗin comment ɗinki sosai Allah bar ƙauna
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 55-56

Bayan ya koma sashensa ya tarar da Abdul zaune ya buga tagumi da duka hannayensa guda biyu ga hawaye dake bin kuncinsa.

Tsayawa ya yi ya kafe shi da ido, sai dai da alama Abdul ɗin ya yi zurfi a kogin tunani.

Girgiza kai Mahmud ya yi alamun tausayawa, ƙarasawa ya yi gunshi ya zauna daf dashi amma duk yaron bai ɗago ba, alamun ma bai san da zamansa a gun ba.

Sai da Mahmud ɗin ya dafa kafaɗarsa sannan ya yi firgigit kamar wanda aka tayar daga barci.

"Me ya faru Abdul?" Mahmud ya tambaya da damuwa a fuskarsa.
Don har a zuciyarsa baya son ganin damuwar yaron, jinsa yake tamkar ɗansa ko wani jininsa.

"Yaya missa kowa yat-tsani ganin huskata na? Missa kowa bai son in zauna kusa garai?
Saboda banda lahiyar ƙahwa ko don ina da rabin huska? Abin na damuna....."

Yana kai nan a zancensa ya fashe da kuka kamar an kunna shi.

Duk da bakomai Mahmud yake fahimta a Hausar yaron ba, amma ya fara jin wani abu saboda zama da Abdul ɗin.

Nan fa ya shiga rarrashin yaron yana bashi baki "Ka yi haƙuri Abdul, shi komai da ka gani muƙaddari ne daga Allah shi ke jarabtar bayinsa don ya gwada ƙarfin imaninsu. Insha'allah zaka warke watarana kamar ma baka taɓa yin ciwon ƙafa ba..."

"To ita huskata hwa tana gyaruwa?" Abdul ya jefo masa tambaya yana nuna bangaren dake shafe a fuskarsa da yatsa.

Sosai ya ƙara bawa Mahmud tausayi.

A ransa ya ce "Sai dai ka yi haƙuri Abdul wannan halitta ce ba zata taɓa sauyawa ba, haka Allah ya so ya nufe ka da zama, ba wanda zai iya canza maka halitta sai...."

Yana tsaka da zancen zucin Muryar Abdul ta daki dodon kunnensa in da yake cewa "Yaya huskata hwa? Bata gyaruwa koh?" Ya fada kamar zai yi kuka.

"A'a Abdul zata iya gyaruwa watarana kai dai ka ci gaba da addu'a kawai ka ji."

Girgiza kai Abdu ya yi alamun "Eh"

Har Mahmud ya miƙe zai wuce ciki ya tuna abinda ya shigo da ƙudurin yi.

Nan ya ji damuwa ta lulluɓe shi. Amma bashi da wata mafita da ya wuce ya sanar da yaron tafiyarsa don ta yiwu ko da zai wuce da safe yaron na barci ba kuma zai iya tashinsa ba.

Dawowa ya yi ya zauna.
"Abdul!" Ya kira sunan yaron.

Yaron ya ɗago ya kalle shi.

Sai da ya yi jim, sannan ya ce "Gobe zan yi tafiya, zan je ƙasar Spain Amma ba jimawa zan dawo..."

Ai tun bai gama rufe bakinsa ba, Abdul ya rungume shi ƙam-ƙam yana faɗar "Don Allah yaya kat ka tahi ka banni Mama bata sona kora ta zata yi."

"Ba zata kore ka ba mun yi magana da ita ka kwantar da hankalinka." Da haka ya ci gaba da lalaɓa shi har ya samu ya masa wayo ya yarda.

A haka suka kwanta rungume da juna, sosai Abdul ya ƙanƙame shi don ganin yake kamar guduwar zai yi ya bar shi.

A wannan daren Abdul kasa barci ya yi sai wuraren uku na dare barci ɓarawo ya yi awon gaba da shi.

Wannan dalilin ne ya saka da safe ya kasa tashi da wuri sai ƙarfe 9 na safe ya farka.

A hankali ya buɗe idon shi ya sauke su kan katifar sai dai me? Wayam ba Mahmud ba dalilinsa.

Nan ya shiga ƙwalawa Mahmud ɗin kira "Yaya! Yaya!!" Jin shiru ya yi tunanin ko yana banɗaki ne, can kuma ya tuna da maganar tafiyarsa ta jiya kenan bai haƙura ba?

Hankalin Abdul ya yi ƙololuwar tashi. Dabara ya yi ya sako daga kan gadon yana rarrafe tare da duba ko wane lungu da saƙo a part ɗin ba Mahmud ba dalilinsa sai kayan break fast da ya ajiye masa, hakan ya tabbatar masa da Mahmud ya yi nisa da shi ya tafi ya bar shi.

Don haka ya fashe da kuka tare da zama guri ɗaya yana raira waƙa cikin kuka "Yayana ka tahi ka banni, nii Abdul ya zan yi da raina.... Hajiya bata hwa sona ya zata zauna da ni kuma... Don Allah yaya ka dawo ni Abdul na ga ta kaina, kai kaɗai ke sona a duniyata yanzu."

Haka ya cigaba da rera kukansa tare da waƙa har ya gaji amma ko mai kama da Mahmud bai koma gani ba.

Zuwa lokacin tuni jirginsu Mahmud ya lula cikin gajimare sai dai fatan Allah ya sauke su lafiya.

Tun bayan dawowar Hajiya daga rakiyar yaronta a airport take zaune a falonta tana shaƙatawa tuni ta manta da wata amana da ya bar mata har wajajen azahar sannan ta tashi ta shiga ciki domin ta shirya ta fita.

Sai bayan ta shirya ta fito zata fita ne da ta ga sashen Mahmud ta tuna ajiyarsa.

Ya mutsa fuska ta yi tana faɗar "Na manta da ajiyarka son."

Hanne ta ƙwalawa kira da gudu ta ƙaraso ta ce "Gani rankiya daɗe."

Cikin ya mutsa fuska ta ce "Ki ɗebo abinci ki kaiwa waccan halittar dake rayuwa a can sashen." Ta faɗa tana nuna sashen Mahmud da hannu.

"To ranki ya dade." Hanne ta faɗa tare da juyawa ciki don cika umurnin uwargijiyarta.

Ita kuwa Hajiya ɗauke kai ta yi tare da wuce parking space ba tare da ta kuma kallon sashen ba ma bare ta je duba halin da amanarta ke ciki.

Ko da Hanne ta je kicin sai da ta tsaya ta ciji yatsa sannan ta fara zuba masa abincin, irin ƙanzon nan na ƙasa

Please Login or Register in order to submit comment