Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake ƙoƙarin gyara gashi karaf sukayi ido huɗu da juna a tare suka zaro ido a tsorace suka haɗa baki gurin cewa!!!!!!!





Vote and Comments



_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_


# Real eeshow



_*Paidbook ,Amount Nml grp 300,Vip 800, pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 2


5️⃣5️⃣➡️5️⃣6️⃣



Nuna juna sukayi a tare suka haɗa baki gurin cewa"kece? kaine?".
suka nuna juna lalubar hijab ɗinta tashigayi bazato taji ya fisgota tafaɗa faffaɗan ƙirjinsa numfashinsu na sarƙewa cikin na juna a harzuƙe yace"ke wacce irin mayyace tace da duk inda nayi sekinbini".
"kai zancewa ma mekakeyi a gidanmu Allah ya kyauta inrasa mayyar wanda zanzama setaka kaima zancewa mayena da duk inda nayi seka bini goto-goto ko kunya bakaji".
binta yashigayi da kallon mamaki gani yayi babu alamun zuwa tayi lokacin sema lura dayayi kamar anan ta kwana kallon tamfatsetsen agogon dake falon yayi yaga a lokacin seven daidai ƙuramata sexy eyes ɗinsa yayi yanamata kallon mamaki karaf idanunsu ya sargafe cikin na juna kallon kallo suka shigayi na wani lokaci bazato sejin muryar Rahama sukayi akusa dasu tace"Sweetheart barka da asuba My Aunt barka da asuba".
saurin sakinta yayi yana sosa ƙeya alamun kunya ya wani ƙara haɗe rai kamar bashine ke rungume da itaba yawani ɗauke idanunsa akanta a zuciyarsa yace"tome wannan futsarariyar yarinyar kuma takeyi a gidannan bayan anɗauramata aure jiya anyako ita nagani kuwa ba gizon data saba yimun bane kuwa to kuma meyasa Rahama takirata da Aunty har kuma take gaisheta".
ɓangaren Inteesar ko a zuciyarta tace"me wannan mara mutuncin yakeyi a gidannan iwannan lokacin kuma da jallabiya tomeyasa Rahama takirashi da Sweetheart kuma".
wata zuciyarce tabata amsa da"kika sani ko saurayinta ne".
sauke ajiyar zuciya tayi tana tinanin yadda zasu ƙare da Namijin duniya
sakejin muryar Rahama yayi tana cewa Inteesar data lula duniyar tinani"Aunty memakon nima ki tasheni infara course ɗin girki gurinki shine kikaƙi tashina ko".
taƙarasa zancenta cikin shagwaɓa saurin danne tsananin mamakin ganinsa a wannam lokacin Inteesar tayi tare da yin sansanyan murmushi cikin zazzaƙar muryata meƙara tafiya da zuwar duk wani ɗa namiji tace"sorry My Sis gani nayi bekamata na tadaki kina bacci ba saboda wasu in antadasu suna bacci suna iya tashi da ciwon kai shiyasa ban tasheki ba amma gobe insha Allahu zan tasheki kinga nima seki riƙa koyamun girkin dama nima karan bani nakeyi
"kinji wai Aunty wai na riƙa koyamiki kefa nikeson ki koyamun domin ba abinda na iya".
"toh zan koyamiki".
sosai Abdallah ke mamakin yadda Rahama take magana da Inteesar abinka da miskilin mutum seya make abunsa kamar ba mamaki yskeyi ba ya wuce ya nufi bedroom ɗin Granny da kallon mamaki Inteesar tabishi har ya ɓacewa ganinsu sauke nannauyar ajiyar zuciya tayi suka cigaba da aikinsu ita da Rahama.





Abdallah na zama akan sofa Granny tafito daga toilet tana ganinshi tayi murmushi tare da zama gefan gado suna fuskantar juna tace"Mesunan Manya ba haƙuri wato amaryar taka kabiyo da sassafenan saboda rashin haƙuri irin naka yaushe rabon danaganka da sassafe se yau kamar mejiran kaɗan".
ƙara haɗe rai yayi tare da cewa"Ammih ina kwana".
"lafiya ƙlau ".
miƙewa yayi da niyyar tafiya yayinda a zuciyarsa yaketa tinanin ta yadda ze fara tambayarta kan Inteesar ƙara haɗe girar sama data ƙasa yayi tare da cewa"Ammih sabuwar ƴar aiki kikayine?".
"meka gani ".
"wata yarinya nagani a kitchen ɗinki".
"ƙila takwarata ce Aishatu matarka ce ai wannan yarinya akwai tarbiyya jiya daddare muna gama cin abinci ita ta kwashe kayan ta gyara gurin gaskiya anyi sa'ar samunta komai na yarinyar nan abun birgewa ne anyako ba shuwa arab bace kuwa kai kaga kyau ko a gurin yarinyar nan kamar ita tayi kanta".
a zuciyarsa ya maimaita cewa"matata kuma".
ashe a fili yafaɗa ba'ah zuciba yana cikin maimaitawa yaji Granny tace"kwarai kuwa ɗan iya nasan yanzu zakace batayimaka ba uban sanabe todai kaji abinda mahaifinka yafaɗamaka atoh nasan yanzu zaka kusheta inkyau kake nema Aishatu kyakyawa ce ajin farko ga tarbiyya ga nutsuwa da hankali ga girmama nagaba da ita mekuma kake nema inama laifi data rufamaka asiri ta yadda kamar yadda bakasan da aurennanba haka itama batasan dashi ba dahar kake wani taɓe baki".
jin tahowar Inteesar ne yasashi taɓe baki yace"ina wani kyau yake anan gurin aba single bawani diri kamar one yazanyi tunda anliƙamun alaƙaƙai dole na haƙura na ansheta ammafa sede intemakamata amma ba ajina bace".
yaƙarasa zancensa yana sakin murmushin mugunta.




Jitayi wani iri luu jiri na ɗibarta sakamakon jin abinda Namijin duniya ke cewa dafa bango tayi sakamakon jindatayi tana niyyar yanke jiki zata faɗi lokaci ɗaya zufa tashiga ketomata a zuciyarta tace"Innalillahi wa'innah ilaihi raji'un nashiga ukuna ni Aishatu idan naji daidai ana nufin wannan mugunne mijina meke shirin faruwa dani ne daka wannan masifar se wannan wannan wacce irin rayuwa ce ya Allah kabani ikon cinye duk jarabawar dake bibiyar rayuwata".
taƙarasa zancenta wasu hawaye ne masu zafi suka zubomata saurin sharewa tayi sakamakon jin sautin tahowar Rahama ta ƙaƙali murmushi a fuskarta jiki sanyaye tashiga cikin sanyin murya tace"salamu alaikum".
washe baki Granny tayi tare da cewa"wa'alaiki salam takwarata ashe kitchen kika shiga dasassafennan aida baki wahalar da kanki ba ga Haire ai duk zatayi komai aida kin huta".
ƙarasa zama tayi tare da yin ƙasa da kanta tayi kamar batasan dashi a gurinba taɗanyi dariya tace"ai bakomai Ammih bawata wahala sema lada dazan samu na farantawa Ammih na rai danayi".
"aikuwa dai ɗiyata Allah yayimiki albarka".
"Ameen ya Allah Ammih na".
a wutsiyar ido tasaci kallonsa karaf suka haɗa ido saurin ɗauke ido tayi daga kallonsa turo ɗan ƙaramin pinky lips ɗinta tana ƙunƙunai ta juyar da fuskarta tace"ina kwana Yayah Abdallah".
shiru yayi kamar bejita ba harta fidda ran ze amsa sannan ya taɓe baki tare da cewa"lafiya ".
aninda kawai ya ce da ita kenan shigowa Rahama tayi tare da cewa"Ammih bakiji ƙanshin da falonki keyiba harna ƙagu danaci abincinnan da Aunty ta girka dakajin yadda yake ƙamshi nasan zehaɗu wallahi".
dariya Ammih tayi tare da cewa"kema hakanan zaki dena wannan banzan baccin naki na ƙaddara ki fara koya".
"ai yau ma Ammih seda nace meyasa bata tasheni ba aida munyi tare nima na koya Auntyna dan Allah gobe ki tasheni muyi tare".
taƙarasa zancenta a shagwaɓe ɗaga idonnan da Inteesar taga Namijin duniya ya taɓe baki tare da cewa"amma dai Rahama kinji kunya wallahi kirasa wadda zakiyiwa shagwaɓa se wannan ƴar abar wadda a girme kin girmeta ".
murmushi Inteesar tayi dantasan danya ƙularda ita yayi wannan maganar tace"ki kwantar da hankalinki Sis insha Allah gobe zan tasheki".
"yauwa Auntyna nagode".
fakaitar idanun mutane tayi ganin bame kallonta tayiwa Namijin duniya gwalo aiko sukayi ido huɗu dashi jinjina kai kawai yayi alamun zekamata ya miƙe yana duba agogon wayarsa yace"Granny nizan wuce Sweetheart anjuma kije ki wanken toilet".
turo baki Rahama tayi tare da yin ƙasa da murya tana ƙunƙunai tana cewa"waikai Yayah koda yaushe bazaka bari masu yima aiki suyima aikin bedroom ɗinka ba sede kasa mutum to daban dawo ba kumafa yanzu aiga matarka nan setayimaka".
ƙara haɗe rai Namijin duniya yayi kamar betaɓa dariya ba yadakamata tsawa tare cewa"kee yaushe nafara wasa dake dahar kika rainani haka to bazansa masu aikinba kenaga damar sawa".
"a'ah Malam dakata bazakazo har ɗakin kace zaka takurawa ɗiyata ba ai gaskiya tafaɗa ko ƙarya tayimaka meyasa bazakasa masu yima aiki suyima ba kokuma matarka tunda sune yazama dole suyima da dabatanan yaya kakeyi ".
"Ammih ke kikeja yara suna rainani wallahi".
yaƙarasa zancensa yana yin kwafa yafice fuuu yana fita ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya dariya Rahama tayi tare da cewa"tofa munfa kinsawa Sweetheart baƙin ciki se Allah ya zuciya".
murmushi yaƙe kawai Inteesar ta yiwa Rahama domin hamkalinta duk baya jikinta tanacan tana tunanin rayuwar dazatayi da Abdallahnta ɗan zafin kai hira kawai sukeyi amma ita hankalinta kaf baya kan hirar tasu dariya Ammih tayi sosai tace"ai gwara daya fusata haka kurum yaro se baƙin miskilancin tsiya da faɗin ran tsiya ga matarka seka dami yarinya da mugun sa aiki idan matarshi batasan cikinsa ba wa yakeso yasani anjuma Aishatu ki shirya kije ɓangarensa ki gyaramasa".
gaban Inteesar ne yabada dammm sakamakon jin zataje gurinsa lokaci ɗaya yanayinta ya canza zuwa kalar tausayi tace"Ammih da anbarshi tunda yafison na Rahama".




Salati Ammih tayi ta sanar da ubangiji gami da tafa hannayenta duka biyub tace"yau ninaga ja'irar yarinya ni Indo ana ƙoƙarin kwatarmata ƴanci tanaiwa mutane shashanci amma gaskiya albasa batayi halin ruwa ba anyako sunanki Aisha ba Sarai ba kuwa ƴar nan domin nidai a iya sanina dame suna Aisha jaruma ce batada tsoro keko daka cewa kije ɓangaren mijinki duk kinbi kintashi hankalinki kamar wadda akace taje gurin mutuwarta hadda wani marairaice murya Ammih kibarshi tunda yafison na Rahama".
taƙarasa zancenta tana kwaikwayon muryar Inteesar ganin yadda taƙara ruɗewa ne yasa Ammih kamo hannunta Granny tayi ta zaunar da ita gefanta ta kama hannunta tace"karki bani kunyaman takwara ta kizama jaruma kidena jin tsoronsa mijinkine a tafin hannunki yake duk wani hura hanci dakikaga yanayi yadena baki tsoro ki tsaya ki natsu ki gyara mijinki aida ba haka yakeba kinada damar da zaki canzashi daga wannan murɗaɗen halin nasa yadawo normal kefa macece kiyi amfani da kisisinarmu ta ƴaƴa mata ki canzamanashi kinji ɗiyata nasan abu ne me matuƙar wahala amma ki daure nasan zaki iya kinji ɗiyata watarana se labari kiyimun alƙawarin zakiyimun wannan aikin danasaki Aishatu domin rabonda muga haƙuri Abdallah a waje da sunan dariya tun kafin mahaifiyarshi ta rasu dan Allah ki temakeni ki dawomasa da walwalarsa kamar da yazama mutum kamar kowa dan Allah ƴata".
jiki a sanyaye Inteesar tace"insha Allah Ammih zanyi iya bakin ƙoƙarina".
murmushi Ammih tayi tare da cewa"nagode ɗiyata Allah yayimiki albarka yabaku zaman lafiya da zuri'ah tagari kuje ku shirya saboda Abbih ɗinku yace idan angama cin abinci akwai meeting.
ƙasa Inteesar tayi alamun jin kunya a zuciyarta ta amsa da Ameen dukan wasa Ammih takaiwa Inteesar saurin gocewa Inteesar tayi tana dariya .




Dariya gabaki ɗaya sukayi Ammih tace"kinibabba kinason mijinki kina kaiwa kasuwa Allah ya shiryamunku kutashi kuje ku shirya muci abinci".
"Ameen dai Amminmu toh".
cewar Rahama daketa dariya nansuka tafi suna shiga bedroom Rahama tayi sauri ta shige toilet tanaiwa Inteesar dariya tayimata wayo taɓe baki Inteesar tayi haɗe da cewa"kedai kika sani yarinya tunda dai bakwana zakiyi a toilet ɗinba aida sauƙi bawani haushi dazanji".
nan tashiga tazar dogon gashinta Rahama batawani jima tafito nan Inteesar itama tashiga batawani daɗe ba tafito ɗaure da towel kama haɓa tayi alamun mamaki ganin yadda Rahama tasha uwar kwalliya kamar wadda zata gasar kyau tasha abaya ƴar ubansu se walwali takeyi tasha stone tace"Sis irin wannan kyau haka kamar wadda zata gasar kyau ai wannan inkika fita waje seki haddass accident ɗin motoci a gari".
murmushin daya ƙaramata kyau tayi tare da cewa"kai Aunty banda sharri duk kyauna aiban kaiki ba kefa ko bakiyi kwalliyaba kyau gareki bare kinyi".
"Allah ba sharri bane gaskiya na faɗamiki idan nayi kyauwunki ai a kalleni".
"bawani nan kawaidai tsokanata kikeyi dan kinga kinfini shiyasa kawai kike ƙoƙarin zagina".
"wlh ba zaginki nake ba gaskiyata nake faɗamiki ƙaraso kiyi ki shirya nasan ƙila yanzu kowa ya hallara a dining mukaɗai ƙila ake jira ".
"toh ai yanzu zan shirya ni ai shirina bashi da wuya mai kawai zan shafa".
"wanne irin mai Aunty aiko dai kwalliya zan tsaramiki saboda so nike ki gigita Yayah ta yadda zeƙara faɗawa a kogin sonki ".
murmushi tayi kawai tare da cewa"Allah shiryeki Sis".
"ameen dai matar babban Yayah".
murmushin yaƙe kawai tayi domin baƙaramin faɗuwa gabanta yakeyi ba idanta tino da wai wannan mutumin me girman kan tsiyar ne mijinta tana wannan tinanin har Rahama tagama tsaramata kwalliya tana gamawa ta tsaya ƙaremata kallo tas sannan tace"amma Aunty kin haɗu tsarki ya tabbata ga Allah subhanahu wata'ala gaskiya bazaki kalli kanki a mirrior ba sekin saka kaya nayimiki rolling kinga muna gama cin abinci semu wuce shopping ɗinda Ammih tace basemun dawo ɗaki ba".
"toh nagode Sis dan Allah idan mundawo ki aramun wayarki nakirasu Besty".
"toh ai se a haɗo da wayarma ".
"toh".
nanta saka inner wears ɗinda ta fitomata dasu sababbi masu colour ɗin coffee sannan ta ɗora wata haɗaɗiyar abaya coffee wadda tasha adon stone se walwali takeyi da ɗaukar ido ɗauremata dogon gashinta dayasha gyara Rahama tayi da coffee ɗin rebom sannan tayi rolling ɗin kanta da ɗankwalin abayar lokaci ɗaya ta rikiɗe tazama tamkar balarabiya kama hannunta Rahama tayi takaita gaban mirrior tare da cewa"Aunty kallarki kiganki".
kallon madubi Inteesar tayi taga lokaci ɗaya tacanza tayi kyau murmushin dayaƙara fito da kyawunta tayi tare da cewa"nagode Sis amma wannan kwalliyar kamar tayi yawa gakuma gashi dakika fitomun dashi dukya dameni".
"bawani yawa da kwalliyarki datayi Aunty light make-up fa nayimiki shikuma ai gashi baze rife bane shiyasa amma dan Allah karki lalata kwalliyarki mutafi nasan mu ake jira ".
"toh muje".
nan kowacce tasa plate shoe ɗinta da hand bag ɗinta kalar kayanta suka fita sunata baza ƙamshi.





Ɓangaren Namijin duniya ko yana gama rai ɓace ya isa part ɗinsa yana shiga falonsa ya zube kan kujera tare da sauke wani nannauyar ajiyar zuciya harya lunshe idanunsa yaji verbrating ɗin wayarsa tsaki yayi tare da duba mekiran yakara a kunne tare da yin shiru daga ɗaya ɓangaren Ahmad yace"mutumina inaka shigane inata kiranka baka ɗauka ba".
wani guntun tsaki yayi tare da cewa"wannan yarinyar ce taɓatamun rai wai kamata za'ayiwa auren dole batare danasani ba kuma Abbih ya rasa yarinyar daze auremun se fitsarrar yarinyar nan mara tarbiyya".
"aure kuma My Man wacce yarinya kenan".
"wacce yarinyace banda Inteesar take kowa oho mata".
a zabure Ahmad yace"wacce Inteesar kake nufi badai ta office ɗinka ba".
"itaman".
wani farinciki ne ya lulluɓe Ahmad yashiga godiya ga Allah nunawa Abdallah yayi yana tayashi alhini daga ƙarshe yacemasa zasu shigo shida Adam daddare nan sukayi sallama Ahmad ba abinda yakeyi se murna tsaki Abdallah yayi tare da miƙewa yashiga bedroom ɗinsa ya ɗaura towel yashiga bathroom dan watsa ruwa bewani jimaba yafito towel ƙarami yana tsane kwantacciyar sumar kansa hand drayer ya jona yashiga busar da gashin yashiga gyarashi da mayamayan gyaran gashinsa lokaci ɗaya suma taɗau sheƙi
yana gamawa yayi shafa ys shirya cikin wata haɗaɗiyar black arman suit yasaka komai baƙi yafeshe jikinsa turarukansa masu daɗin ƙamshi ya gyara jikinsa tsaf ko ina yaɗau gayu cikin takun ƙasaita ya nufi ɓangaren Granny dan amsa kiran Abbih.




Yana isa falon Granny ya nufi dining dan yagasu Ammih nacan cikin girmamawa ya gaidasu Mummy suka amsa tashi Meemah tayi daga kujerar datake zaune takoma kusa data Abdallah shiko ɗan gogan yi yayi kamar besan tazauna kusa dashi ba ya maze ta ƙasan ido yashiga kallon kowa na gurin yaga Rahama amma beganta ba kai hannu yayi ya tsiyayi ruwa a glass cup yakai bakinsa a zuciyarsa yace"ko ina kuma wannan fitsararriyar yarinyar tashiga oho".
yana cikin wannan zancen zucin yaji ƙamshin wani daddaɗan turare ya daki hancinsa saurin maida glass ɗinsa yayi a idonsa ya kalli direction ɗin dayaji wannan ƙamshin tozali yayi da Inteesar dataci uban gayu kamar ka saceta ka gudu dan kyau hannunta riƙe da wani babban ball tari yashigayi!!!!!!!!!





Votes and Comments





_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_




# Real eeshow



_*Paidbook,Amount Nml grp 300,Vip 800,pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 2



5️⃣7️⃣➡️5️⃣8️⃣




Saurin shanye ruwa dake hannunsa yayi yayinda yake binta da idanu ta cikin baƙin glass ɗinsa kamar wanda yaga sabuwar halitta har ta aje ball ɗin dake hannunta kallon chairs ɗin gurin tayi taga ɗaya ce kawai ta rage wadda ke facing ɗin Abdallah jiki a suluɓe ta nufi kujerar yayinda kanta ke ƙasa gabanta ke tsananin faɗuwa saboda jin idanunshi na yawo a jikinta ta zauna tare da sauke wata boyayyar a jiyar zuciya kanta a ƙasa tace"sannunku da hutawa kuyi haƙuri nabarku kuna jirana".
murmushi Ammih tayi yayinda takejin wata ƙaunar Inteesar dake ƙara ninkuwa a zuciyarta tace"bakomai daughter ke za'aiwa sannu irin wa'innan abinci haka Allah dai yayi albarka ɗiyata kema Allah yabaki masu yimiki".
murmushi tayi tare da yin ƙasa da kanta alamun kunya tace"ameen".
taɓe baki Namijin duniya yayi tare da
# Real eeshow



_*Paidbook,Amount Nml grp 300,Vip 800,pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 2



5️⃣7️⃣➡️5️⃣8️⃣




Saurin shanye ruwan dake hannunsa yayi yayinda yake binta da idanu ta cikin baƙin glass ɗinsa kamar wanda yaga sabuwar halitta har ta aje ball ɗin dake hannunta kallon chairs ɗin gurin tayi taga gabaki ɗaya da mutane kai saura guda ɗaya ce kawaita rage wadda ke facing ɗin Abdallah jiki a suluɓe ta nufi kujerar yayinda ƙirjinta ke dukan tara-tara kanta a ƙasa gabanta na tsananin faɗuwa saboda jin idanunshi na yawo a jikinta batason yakuma tsiromata da wani salon masifar tashi ta zauna ganin bemata wata muguntar bane yasata sakin wata ɓoyayyar ajiyar kanta a ƙasa tace"sannunku da hutawa kuyi haƙuri nabarku kunata jirana".
murmushi Ammih tayi yayinda takejin wata sabuwar ƙaunar Inteesar na ƙara ninkuwa a zuciyarta tace"bakomai daughter ke za'aiwa sannu irin wannan abinci haka Allah dai yayimuku albarka ɗiyata kema Allah yabaki masu yimiki".
murmushi tayi tare da yin ƙasa da kanta alamun jin kunya tace"ameen".
taɓe baki Namijin duniya yayi tare da yin magana a ƙasan maƙoshinsa ta yarda ba wanda zeji se ita yace " a haka kamar wata mutuniyar kirki hadda wani ƙasa dakai kamar gaske nanko ba abinda ke cikinta se ƴar banzar rashin kunya kamar kuɗin cizo".
karaf sukayi ido huɗu da Inteesar kashemata ido ɗaya yayi tare da sakin wani shu'umin murmushi ya ɗagamata gira alamar yadai saurin ɗauke kanta tayi daka gareshi dankar wani yagansu.



Karaf akan idon Meemah waddata tashi cikin yauƙi zatayi serving ɗinsu tinani tashiga yi itako a ina tasan wannan fuskar ganin tashiga tinani ne yasa Abbih cewa"Daughter ƙarasa ladanki mana kiyi serving ɗinmu".
cikin girmamawa ta miƙe tare da cewa"toh Abbih".
nanta shiga serving ɗin kowa cike da nutsuwa gefe guda kuma ba abinda Meemah keyi se aikin kallon Inteesar tana son tino inda tasanta a haka takoma ta zauna har Inteesar tagama serving ɗinsu tana tinani nan kowa yafara cin abincinsa cikin kwanciyar hankali a zabure ta miƙe tare da cewa"bura uba kece..........?".
ta faɗa tare da nuna Inteesar dake ƙoƙarin kai spoon ɗin shayi bakinta kowa na gurin ne yajuya yana kallon Inteesar saurin maida spoon ɗinta tayi tare da shiga dube-dube alamun nema wanda Meemah ta nuna gani tayi kowa na gurin na kallonta saurin yin ƙasa da kanta tayi gabanta na dukan tara-tara domin tin shigowarta tagane Meemah sarai a zuciyarta tashiga addu'ar Allah yasa karta faɗi inda ta taɓa ganinta domin batason kowa yasan ta taɓa ganin Namijin duniya.




Tana cikin wannan zancen zucin taji muryar Abbih yace"A uzubillahi mina shaɗanirrajim anan gidan ake kutuntuma wannan ashar ɗin sekace gidan maguzawa".
saurin zungurarta Mummy tayi ta ƙasan dining ba tare da angansu ba tayimata alamun a cikin mutane suke ganin tayi shiru ne tana jifan Inteesar da wani kallon ƙasƙanci ne yasa Mummy yin gyaran murya cikin ƙissa tace"nifa banson shashanci kinsanta ne?".
"wallahi da naɗauka wata ƴar class ɗinmu ce da mukayi karatu a England Zainab se yanzu nagane ashe ba ita bace amma ko suna tsananin kama sorry fa".
taƙarasa zancenta tana mai jifan Inteesar da wani kallon wulaƙanci murmushin gefan baki Abdallah yayi domin shima yagane inda Meemah ta taɓa ganin Inteesar.



ɓangaren Inteesar ko sauke wata uwar ajiyar zuciya tayi me ƙarfi wadda ta ja hankalin kowa na gurin yayo kanta ganin ana kallonta ne yasata yin ƙasa da kanta muryar Abbih taji yace"Daughter lafiya kuwa ?".
murya na rawa tace"lafiya ƙlau Abbih".
"kodai wanine yayimiki wani abune".
"ko ɗaya Abbih ba abinda akayimun kawai dai nima naji nayi ajiyar zuciya ne amma bansan dalilin yinta ba".
"toh Allah yayimuku albarka ".
"ameen ya Allah".
nan kowa na gurin ya cigaba da cin abincinsa yayinda Rahama keta faman santi .




ɗaukar pork ɗin dake gabansa yayi tare da ɗaukar doya ɗaya yakai bakinsa da sauri ya miƙe ya nufi toilet ɗin dake manne a falo yashiga kakarin amai kamar gaske bewani daɗe ba yafito yana wani yamutsa fuska ya nufi dining har yaja kujerarsa ze zauna yaji muryar Abbih a ruɗe yace"lafiya kuwa son kake amai ".
ƙara yamutsa fuskarsa yayi tare da sakin murmushin ƙeta ya kalli Inteesar da itama shi take kallo kashemata ido ɗaya yayi haɗe da yimata alamar one-zero buɗe bakinsa yayi da niyyar yin magana sukayi ido huɗu da Meemah data kafeshi da ido tanason jin mezece ɗauke kansa yayi daka garesu tare da shafa kwantaccen sumar kansa datasha gyara cikin nuna yanayin rashin lafiya yace"bakomai Abbih jikinane banajin daɗinsa tunda na tashi Sweetheart haɗomun coffee ko zan iya sha".
yaƙarasa zancensa yana kallon Rahama dake cin abincinta hankali kwance turo baki Rahama tayi tare da yin ƙasa da murya tana ƙunƙunai tace"kaidai Yah Abdallah kana baƙincikin ka ganni ina hutawa seka tasheni duk ga mutane nan inbakason na masu aiki aiga matarka nan basekasa ta haɗamaka ba ai duk a cikin dutyn tane".
ƙara haɗe rai yayi kamar wanda be taɓa dariyaba rai ɓace ya dakamata tsawa yace"ke yaushe nafara wasa dake dahar kika rainani haka to bazansa masu aikinba kenaga damar sawa".
yaƙarasa zancensa yana huci kamar wani mayunwacin zaki dakatar dashi Ammih tayi ta hanyar cewa"a'ah Malam dakata bazaka zo har ɗaki saboda baka da lafiya ka takurawa ɗiyata ba ai gaskiya tafaɗa tunda bakason masu aiki su haɗamaka aiga matarka nan itace kake tilashinta ba itaba to da batanan yazakayi ke Aishatu tashi ki haɗowa mijinki coffee".
dammm gaban Inteesar yabayar tayi saurin ɗagowa ta saci kallon Namijin duniya ta wutsiyar ido karaf suka haɗa ido saurin ɗauke kanta tayi daga kallonsa lokaci ɗaya gumi yashiga ketomata domin batason duk wani abu dazesa tashiga sabgarshi tana cikin wannan zancen zucin taji muryar Ammih na cewa"ko bakiji bane".
"naji Ammih bara na haɗo".
nanta miƙe jiki a saluɓe ta nufi kitchen yayinda Mummy da Meemah suka rakata da uwar harara haɗa ido Mummy tayi da Namijin duniya hakan yasata saurin ƙaƙalo murmushin ƙissa tace"sannu ko Son Allah yaƙara lafiya ka kira family Doctor yazo ya dubaka".
fuska a haɗe yace"yauwa Mummy dama so nake idan naɗansha coffee ɗin sena kirashi".
"toh wai nikam ina muka samu yarinya haka me hankali da nutsuwa haka ko ƙawar Rahama ce ta kawomana ziyara".
taƙarasa zancenta cikin ƙissa irinta riƙaƙƙun ƴan bariki murmushi Abbih yayi tare da cewa"surukarki ce ai".
a razane Mummy da Meemah suka kalli Abbih danson tabbatar da abinda kunnuwansu yajiyemusu dakyar Mummy ta iya saita nutsuwarta tace"Dadyn yara bangane surukata ba matar waye".
"matar Abdallah ce jiya aka ɗauramusu aure dama abinda zanfaɗamuku kenan bayan mun gama cin abinci".
dakyar Mummy tasaita nutsuwarta ta ƙaƙalo murmushin da iyakacinsa leɓe tace"masha Allah ,Allah ya sanya alkhairi yabasu zaman lafiya da zuri'ah tagari".
"Ameen ya Allah".





Ɓangaren Inteesar ko tana shiga tafara haɗamasa harta ɗakko sugar zata zuba ɗaga idonnan da zatayi tayi tozali da abun gishiri murmushin ƙeta tayi tare dakai hannu ta ɗakko salt ɗin ta makashi a cikin coffeen ta motsa tashiga dariyar ƙeta seda tayi me isarta sannan tace"badai ni kacewa one zero ba to yanzu za'ai one-one mara tarbiyya kawai maga tasa aikin tsiya kawai zanyi maganinka yau".
dariya taƙarayi sosai sannan ta ɗauƙi cup ɗin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment