Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ita ma Sapnan ba wata kwalliya ta yi ba amma kallo daya za ka yi mata ka kirata da sunaye uku; ‘yar gata, ‘yar hutu, yar gayu.
Shadda ce getzner dinkin Senegal a jikinta dark pink wadda ba a cika zare da yawa wajen yin sirfaninta ba, wanda aka yi shi da zare light pink, haka dan shara-shara gyalen da ta zarga a wuyanta shima light pink din ne, sai babbar jaka ta mata baka mahadin takalmi flat baki da ke kafarta samfurin (gucci).

Haka suka ci gaba da kallon juna kowacce ba ta yi magana ba, amma ta soma huci, hancina sun bubbude kowanne tsiron gashi ya mike sai Allah ya jeho Ibrahim gabanin a fara baiwa hammata iska.

Mara gaskiya an ce ko a ruwa jibi yake, Ibrahim rikicewa ya yi. Amma da yake namiji ne lab-coat din jikinshi ya soma kokarin cirewa yana fadin
“A’a, Sapna, wata sabon gani”.
Ta mai da budadden hancin nata a kansa kamar ta feso shi daga cikin hancin don takaici.
Me wannan bakar yarinyar ta fita da har ya zabeta a kanta? Tsakaninta da Ibraheem sai ALLAH YA ISA! Domin ya gama wulakantata……
Rahane ta mike tsaye wanda ya baiwa Sapna damar ganin matashin cikin dake jikinta har ya soma turowa gaba sosai. Sai Sapna ta cire takalminta ta rufe Ibrahim da duka da hannu da kuma takalmanta…..
“Mugu….. azzalumi…. maci amana, tsakanina da kai sai ALLAH YA ISA! Na gode Allah da ban taba baka budurcina ba balle in yi nadamar haduwa da kai….. I hate you Ibraheem….!!!”
Ta zubar da takalman ta fashe da kuka ta durkushe a gabansa tana ta yi. Daga karshe ta mike ta yi kofa da gudu ta fita, ga mamakin Rayhanah sai Ibrahim ya bita, amma ba da gudu ba sai sassarfa.
Rayhanah ba ta iya tukin mota ba, wannan dalilin ne yasa ta tsimayen Ibrahim, banda haka da tuni ta ja motar ta tafi in ya so ya debo da sayyadarsa ko masoyiyar tashi ta kai shi gida.
Daga inda take tsaye jikin motar mijin nata tana hangosu ta cikin gilashinta, Sapna ta bude mota ta shige shi kuma ya zauna a gefen mai zaman banza ya danne totur din motar da kafafunsa yadda ba za ta iya jan motar ba, ya kuma dafe sitiyarin da hannayensa yana yi mata magana, da alama cikin lallashi.
Sai ta ji wani bakin ciki ya turnike mata zuciya ba ta ankara ba sai da hawaye suka zubo. Sai kawai ta hau tafiya ta fita daga harabar Illinois TH tana bin gefen titi a hankali ba ta san inda take jefa kafarta ba.
Da gudu motar Sapna ta zo ta wuce ta, tabbas ba don a kasar da ba’a laifi a kwana lafiya bane da ta kwasheta da motar.
Jin tahowar motar Ibraheem ta yi a bayanta yana ta horn yana binta sannu-sannu, amma ko kallon shi ta ki yi, ba ta ko son ganinsa ya yi duhu a zuciyarta, ya yi muni a idanunta.
Maimakon ta tsaya ma hanzari ta kara yi, dole ya kashe motar a gefen titi ya kara da gudu ya cimmata ya rike hannunta a lokacin da ita kuma ta rufe idonta gam, sai kawai ya daddage ya sureta tana fiffizgewa tana komai ya sata a motar ya rufe kofofinta da lock, glasan motar dama ko guduma aka rotsa musu ba za su fashe ba saboda ingancinta.
A haka ya ja motar suka nufi gida.

*****


Lallashin duniya Ibrahim ya yi, ban bakin duniya ya yi shi, Rayhanah ta ki saukowa. Ta yanke duk wata kyakkyawar mu’amala dake tsakaninsu, ta kaurace masa a shimfida, ta kaurace masa a ido biyu. Ko falo ta daina fitowa balle ta rakashi wani wuri.
Cikin ma dake like jikinta da za ta iya da ta ciro masa abinsa ta bashi, in yaso ya kaiwa Sapnar. To ba ta da ikon wannan, wanda take da iko da shi, ta hana.
Duk da ta san cewa zai iya jure komai amma ban da wannan Hausar (a raba daki). Ba ta yi karya ba, idan ta ce Ibraheem ya rame, ya rage fita.
Wani sashi na zuciyar da soyayya ta mamaya na neman fizgarta su sako mata tausayi, musamman da ta soma saukowa. Ba ta da saurin fushi amma idan ta yin, ba ta sauka da wuri. Ibrahim a falo yake kwana tsayin kwanaki goma sha hudu (sati biyu).
Ba rufe daki take yi ba, cewa ta yi muddin ya shigo mata daki wallahi zai nemeta ya rasa a Chicago.

“Idan wannan shine kishi Rayhanah, ashe kuwa dole a cika jahannama da mata. To ni wannan ai lasisi kika bani idan ni dan iskan ne ma in je in ci gaba da iskanci na. Kina tunanin wannan rashin hankali da rashin zurfafa tunanin naki, shi zai raba namiji mai kuruciya kamana da mata a America? Kin yi kuskure.
Idan kin manta ne bari in tuna miki, ba ni kika fara so ba, Khalipha ne. Kaddarar Allah ce ta wanzar da aurenmu ba tare da mun san juna ba.
Ni kuwa Rayhanah na so ki ne tun kina RAHANE.....Na so ki ba tare da na ganki a fili ba, na so ki again daga jin muryarki zuciyata ta gaya min uwar ‘ya’yana ce wannan duk da ban ganta ba.
Da na ganki a fili a matsayin matata babu abin da ya canza daga soyayyar da nake yimiki, sai ma abin da ya karu. Duk da nasan ke din ba ni kika fara so ba. Rayhanah duk baki duba wannan ba, sai don wata ta ce tana sona, alhalin na barta ne saboda ke?
Ai idan baki gode min ba, to a kalla ki cire takunkumin da kika sanya a tsakaninmu. Hakurina ya gaza ba zan iya jurewa ba….!!!”

Tsaye yake a bakin kofarta a sanda yake yi mata wannan maganar. Ya tokare hannunsa da kofar. Tana kwance ta yi shiru tana jinsa amma ba ta ce komai ba, ba ta juyo ba ma balle ya ga fuskarta. Har ya san cewa maganganun sa sunyi tasiri a gareta ko basu yi ba. Sai ya girgiza kai, ya fita ya bar mata dakin.
Abu daya yake tattali yanzu a duniyar nan (cikin Rayhanah). Wannan ne dalilin da yasa bai fiya takura mata ba, don sau biyu tana yin barin ciki dan sati uku. Wannan ne aka samu ya zauna da taimako da dabarun likitoci.

Ibraheem ya rasa yadda zai yi da ita ta birkice ta hautsine masa gaba daya. Bai taba ganin kishi irin na Rayhanah ba. Tun yana binta yana lallami har ya gaji ya rabu da ita, ya kuma koma zagayawa wajen Sapna ta bayan fage.
A sabuwar tarbar da Sapna ta yiwa Ibraheem cikin rayuwarta, a shirye take da ta mallaka masa kanta in dai zai aure ta. Bai yi hakan ba, cewa yake da ita a yawancin lokuta.

“Idan kin bani kan naki yanzun Sapna, idan muka yi auren kuma me za ki bani???”

Rayhanah da kanta ta soma noticing Ibraheem ya canza, ya daina zama a gidan sam-sam, in kuma da dare ne to cinye daren yake yana waya, kamar yadda ya ce ta ba shi lasisin iskanci, iskancin sa kuwa yake ta yi abinsa har a office kullum suna tare da Sapna kamar tip da taya.
Idan ta saurari hirar da yake yi da dare duka da Sapna ne. Wata irin hira marar dadin ji da tada hankali agareta.
Sai fushin ya sauka, hankalinta ya yi mugun tashi, ta soma kokarin repenting gundumemen kuskurenta.
Amma duk ta inda tayi tunanin bullowa Ibraheem baya bata fuska. Mata da yawa muna wannan kuskuren, a lokacinda miji yake binmu da lallashi da kokarin amsa laifinsa, a lokacin ne shekarar girman kanmu ke kamawa.
*****
[12/30/2019, 14:40] Takori: BAYAN WATA DAYA
1/Sha’aban
Wannan rana bakar rana ce ga Sapna da shi kansa Ibraheem din watakila. A yau ne za su bar kasar Amurka a dalilin sauyin aiki da aka yiwa mahaifinta Ambasada Kabiru Abubakar Dogon-Daji zuwa kasar Djibouti. Kuma da yake ta kammala karatunta mahaifinta ya sata a gaba suka tafi yana gaya mata wannan Dr. Ibrahim din da ta likewa ba karamin raina mata wayo ya yi ba, dan taking advantage ne ba aurenta zai yi ba.
So ba hauka bane, ko lambarta ta kasar Djibouti ta ba shi sai ya tsine mata albarka.

Addu’ar Rayhanah ce kawai Allah ya amsa amma ba isarta ba. Tashi take cikin dare ta yi sallar nafila raka’a biyu, cikin sujjadarta ta karanta
“Ya hibbu na hum ka-hibbullahi (kafa bakwai). Qad shagafahaa hubbah (sau bakwai). Sai ta ce,
“Yaa Allah ka mallaka min soyayyar Ibrahim dan Mansur da Asma’u. Ka kare min shi daga zina da neman maza, da duk ayyukan sabo dake da alaka dasu. Ka juyo da hankalinsa gareni ka ragemin kishin da nake da shi a kansa.
Yaa Allah ka bani soyayya da kaunar dake cikin zuciyarsa baki dayanta, ka dora shi a kan hanya madaidaiciya ta neman halali, ka cire haramun daga aljihunsa.
Yaa Allah ka ba shi ikon ciyar damu (ni da abin da ke cikina) da tufatar damu da shayar damu da halal. Ya Allah ka zama jagoran sa, ka rabani da abinda ke ciki na lafiya.”
Wannan ita ce adduar da Rayhanah ta dukufa tana yi dare da rana a cikin satittika hudun da suka biyo baya, wadanda suka yi dai-dai da cikar cikin jikinta watanni shida.
Kasancewarta doguwa kuma cikin fari, kallon farko ba za ka ga cikin ba, musamman in riga da zani ne a jikinta, sai in ta sanya doguwar riga.
Yau kwanan su Sapna uku da barin America. Idan ya ce bai yi kewarta ba ya yi karya. Ya rage gantalin, dama wuraren shakatawa suke zuwa, ko bakin ruwa (beaches) su ci su sha, suyi kazamiyar soyayyarsu.
Don haka yau da ya kasance a gida wuni guda zur, ko kofar gida bai leka ba, ita kanta Rayhanah haushinta yake ji. Yana ta tsimayen wayar Sapna amma har ta cika sati da komawa Djibouti ba ta kira shi ko sau daya ba.
Ita kuma wannan muguwar ta cikin gida ga yadda take, ba ta da niyyar ko ranar daina muguntar ta.
Iyaka tunanin da ta yi na hanyar da za ta bi ta nuna ta karbi laifinta ba ta samu ba. Sai ta hau zirga-zirga daga kicin zuwa bed room, ta yi kyau cikin (Layered-mini-Dress) duk da cikin ya turo sosai, amma ko kallon ta ya ki yi.
Ya yi rigingine da waya a hannu yana faman hira da wata daban, tunda ba Sapna.

Rayhanah ta ga idan ta bari Ibraheem ya ci gaba da cusa mata bakin ciki a kan ‘yammatan kan titi ta fadi babu nauyi, kuma zuciyarta za ta buga. Sai ta yi zaman ‘yan bori a gabansa ta daddage ta fasa masa kuka mai gigitarwa.
Iyakar tsorata Ibraheem ya tsorata, wayar hannunsa bai san inda ya jefa ta ba. Don ya dauka nakuda ce ta zo mata da ciki wata shida. Ya kama ta ya kankame yana kira.
“Mene ne Rayhanah? Haihuwar ce?”
Ture shi ta dinga yi da iya karfinta..
“Ka rabu dani, in ma mutuwa zan yi in mutum mana ina ruwanka? Tunda ‘yan iska sun sa ka juya min baya, to ka mai dani inda ka dauko ni…..”
Dariya ce sosai ta kama Ibraheem da ya fahimci musabbabin wannan ihun da ya kada masa ‘ya’yan hanji, yasa shi cikin tashin hankalin, kada a haife masa bakwaini a tsakar daki.
Ya ce, “To ga bayan na dawo miki da shi, zo ki hau!”
Ya juyo mata bayan, ya yi durkuso a gabanta…..
“Zo ki hau Rayhanah, na daina juya miki shi. Zo ki hau ki riga baby hawa, don ban tashi juya miki baya ba ma sai ranar da Allah ya fito da Da na ko ‘yata duniya Rayhanah, muddin baki daina kokarin azabtar dani da kishinki na shirme ba, wanda ba irin na su Nana Aisha ba.
Kishi ne na halaka da daukar hakki Rayhanah, duk abinda zai munana lahirar ki bana sonki da shi Rayhanah, kuma ba zan zama sanadi ba.
A da, na san Rahane mai yiwa mutane uziri ce, uzri sau saba’in, kafin ta kama su da yi mata laifi, tunda ‘no body is perfect, except our Almighty…..!!!”

Jikin Rahane ya yi matukar nauyi, idonta ta dago a hankali ta kalli mijin nata, shima idonsa a kanta. Sai dai gab yake da ya fidda hawaye.
“Zo ki hau…..”
Ya zube a kasa ya bata bayan. Da gudu ta runtuma ta rungume shi ta bayan, tana fadi cikin kuka,
“Ka yafe min Yaa Himu? Zan kasance cikin tababbu, butulu masu manta alkhairi da rashin godiyar Ubangiji idan baka yafe min ba IBRAHEEM…....”
Juyowa ya yi ya kama ta, fuskar mai cike da kwarjini da kamala, kunshe da murmushi mai kayatarwa yana kada kai.

“Zan yafe miki only in kin hau bayan nan na goya ki, kafin na goya ‘ya’yan Ibrahim!!!”.

Sai ta dane shi, ya mike kamar bai dauki komai ba sabida rashin nauyinta, ya nufi master bedroom dinsu.
Tana tuno kalaman Daddy ne a wannan lokacin…..

“Ibraheem is a nice person… Allah ba kwarzantashi nake yi ba Rayhanatu… wata rana ke da kanki za ki gaya min hakan….
Lokacin da zai sunkuya yana yi muku doki sukutum ke da yaranku…..”

“Ba ka yi karya ba Daddy… bayan kasancewarsa nice, honest ne, kind ne, brave ne, sweet ne, jarumi ne kuma sadauki a fannin nuna soyayyah!!!”

*****









Tun daga wannan ranar da Ibrahim ya nunawa Rayhanah, ita wani bangare ce na rayuwarsa da ba zai iya rayuwa ba ita ba, fushinta a kansa zai iya gurbata rayuwarsa. Rayhanah ba ta sake yin irin wautar da ta yi a baya ba, ba ta sake takurawa Ibrahim a kan ‘yammata ko wayarsa da mutane ba.
Ita duk mai son Ibrahim ma duk kyanta da matsayin da take takama da shi ko na iyayenta tausayi take ba ta. Annabi (S.A.W) ya ce,
“Imanin dayan ku baya cika har sai ya sowa dan’uwansa Musulmi abin da yake sowa kansa”.
Ta yarda ta amince Ibraheem abin so ne, ba kowacce mace mara aure ce za ta iya dauke ido a kansa ba, don haka ta kama addu’a ta kama Ibrahim, ta kuma hada da kau da kai daga mu’amalarsa da kowa.
Illa kullum tunaninta shine hanyoyin da za ta bi ta kara kyautata aurenta, ta kara martabarta a idanunsa. Tunda ita din dai da ba kyakkyawar ba, ba ‘yar kowan-kowa ba, ita Allah ya kashe ya baiwa.

Already Ibrahim ya gama duk abin da zai yi a Chicago, amma ganin cikin Rayhanah ya shiga wata tara sai ya bari sai ta haihu don su jewa Daddy da tsarabar da za ta gigita shi, don ko kusa bai taba gaya masa Rayhanah na da ciki ba.
Shi Daddyn ne dai yake faman tambaya sai ya yi dariya ya ce,
“A ci gaba da addu’a Daddy”.

A dai-dai lokacin EDD dinta ya cika, don haka bai cika yin nisa da gida ba, haka ko tafiya yake on the street waya suke, sai idan driving yake. Shima din earpiece na jikinsa, da ta yi kira zai sauka gefen titi ya amsa.
Ranar litinin, bayan gajeruwar nakuda ta haifi diyarta mace mai kyau, abin mamaki mai matukar kama da Mami, duk da cewa kalar iyayenta ce (choculate) har sun fi ta haske. A labour - room na asibitin (Illinois).
Ibrahim da shi aka karbi haihuwar, kuma sai da aka sake dinketa kamar kwarya (kamar yadda yake fadi).
Shi da kansa ya goge jaririyar da olive oil (Zaitun), ya nadeta cikin shawul ya rungume yana yi mata huduba da kalmar shahada cikin kunnuwanta, ya dura mata zam-zam, ya tauna dabino (ajwa) ya sa mata a baki, sannan ne ya bari Nurses suka karbeta suka yi ta wanke ta.
Ashe har da dattin ciki ya kara mata baki, da aka gama wanke ta sai ta koma kamar Abida. Rayhanah da ta dubi yarinyar da Ibrahim ya dora mata a kan cinyarta sai da ta tsorata…..
Yarinya kamar Abida ce ta haife ta, cleft din Ibrahim a kasan habarta, ga beauty point din Mami.
Sai ta ji hawaye na diga daga idanunta suna sauka a fuskar jaririyar da ta tabbatar Mami da Abida ba za su karbeta a matsayin jininsu ba, duk da cewa dasu take kama, saboda daga jikinta da suke gani kaskantacciya sauran cuta ta fito. Sai ta yi wani tunanin da ya sanyaya mata zuciya, tunanin cewa,
“ Jawahir za ta goya ta, Aziza za ta dauke ta.”

Rayhanah ji ta yi hankalinta ya dugunzuma ya yi gida Nigeria, gara ayi wacce za ayi tsakaninta da Mami wannan boyayyen aure ya isheta, ba za ta yarda Mami ta sheganta mata ‘ya ba, tunda ba ta san da auren ba.
Babban takaicinta a kullum idan ta tuno tozarcin da Mami ta yi mata sanda take zargin Daddy da nemanta.
A wancan lokacin ba ta dau al’amarin da zafi ba saboda rayuwarta dake reto a gidan iyayen rikon nata, amma yanzu da ta samu nutsuwa da karin hankali ta yadda ba karamin tozarci da wulakanci Mami ta yi mata ba. Mutumin da yake makwafin mahaifi agareta.
Ta dauki ‘yar sosai a jikinta, tana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta ji hanci da ido, da dan bakinta mai kyau kamar Dr. Asma’u Mansur Takai….
Sai ji ta yi Ibraheem ya rungumesu ta baya.
Dukkansu rufe idanunsu suka yi ruf, daga su har jaririyar, a sakamakon shigowar wata sabuwar kauna da soyayya mai girman da baya misaltuwa da ta kara shigewa cikin zukatan kowannensu.
Tsayin minti biyar sannan Ibrahim ya karbi Babyn daga hannunta yana kallo yana murmushi, ya ce,
“Mami na ce….. sunanta NANA ASMA’U!’
Cikin karaji Rayhanah ta ce,

“Ban yarda ba, sai in ita da kanta ta amince a kira ta Asma’un…..”

Idanun Ibrahim suka yi mici-mici yana kallon ta da mamakin dalilin wannan ANGER haka a kan sunan mahaifiyarsa. To sunan Mamin ne ba ta so ko Mamin ce ba ta so?
Ko kuma me take nufi da sai idan ita da kanta ta yarda a kira yarinyar Asma’u?
Bai gama tunanin da yake yi ba sai gani ya yi Rayhanah ta goye ‘yarta da tawul din da take kunshe ciki, ta yi lullubinta yadda ta saba ba tare da tunanin cewa a asibiti take ba, kuma likitanta bai sallameta ba ta doshi kofa.
Ibraheem tsayawa ya yi yana kallon ta ya daskare a tsaye kamar statue (mutum-mutumi). Bai ankara ba har ta kai kofa, sai ya yi azama da sassarfa ya cimmata ya damko hannunta.
A rikice ya ce, “Rayhanah ina za ki je? Tafiya za ki yi ki barni Rayhanah? Me na yi miki? Ko ko ba ki yi farin ciki da kyautar da Allah ya bamu bane? Ko don na ce zan sawa ‘yata sunan mahaifiyata? Above all ma ina za ki je ne?”
Hawaye na kwarara a kan fuskarta ta ce,
‘TAKAI!”
“Takai???”
Ya fada cikin sigar tambaya.
“To wajen wa?”
Ya sake fadi a gigice. Ba tareda ya jira amsar farko ba. Ta kai tafukanta ta rufe fuskarta ta soma shesshekar kuka kafin ta ce,
“Wajen Inna Juma da Inna Zinaru”.
Wannan lokacin Ibrahim ya fara fusata.
“Saboda na ce zan sawa ‘yata suna Asma’u? Ko don tsuntsun soyayyata ya tashi don kin haihu dani?”
Ba ta ce komai ba, sai girgiza kai take tana kuka.
“Zinarun ta ci uwata….. ta ci ubanta! Ke idan kina da hankali har za ki sakota cikin wadanda za ki yi tinkaho da su? To amma ba da wannan jaririyar da ke bayan ki ba ko?”
Ta fiddo ido jike da hawaye ta ce,
“Ai ita zan kai can, sai ni in dawo”.
“........Da yake kutumar uban Zinaru ne ya yi cikinta ko? Sakko min ‘yata!”
Ya mika mata hannu. Shi kansa baisan sanda wannan ashariyar da bai taba yi ba koda wasa ta sulmiyo

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment