Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su ya shiga tare dasu da Daddy, d'akin su Husnah ne ya gani a bud'e yace, "Husnah kiyiwa Allah ki ajiye komai kibar ni na shigo cikin d'akin nan, wanda rabon da na shige sa tun kafin mutuwar mahaifiyar ku".


Anty Zarah ce ta shiga cikin d'akin da gudu, Husnah ce ta isko ri'ke da sarka da yan kunnen da maman su take so sai har take sheda masu irin son da take yiwa yan kunnen, ai kuwa Anty Zarah da sauri itama ta d'auki kayan ta fashe da kuka kamar yan zun ne mutuwar mahaifiyar tasu, Daddy dake tsaye a waje duk mu shiga ciki ganin halin da suke ciki ne ya baiwa Yaya Yusuf da su Husain tausayin su, gurin su suka 'karasa Baban su Husnah ya matsa shima ya anshi kayan yace, "tunda ba addu'a zakuyi mata ba, ku kawo kayan na zubar" da sauri suka share hawayen idon su Husnah tace, bayan kayi farin cikin mutuwar mama na kwana d'aya akayi jimamin rashin ta, a gidan nan amman kuma, kuka ci gaba da jin dad'in ku, kuci abinci mu kuwa mu zauna da yunwa, kokon da mune muke damashi amman mune ake baiwa wanda kudaje suka bi wanda yayi datti dan dai kawai lokacin mutuwar tamu ba yi bane, shine yan zun kake cewa zaka rabamu da abu mai muhimmanci a rayuwar mu, baka zama damu baka sauraren mu, naira biyar taka baka bamu, zagi da duka ne tsakanin mu da kai, haba dai".



Baban yace, "Husnah ki fad'i duk abunda yazo bakin ki nasan duk na aika ta shi amman dan Allah kiyi hakuri bada son raina na aikata maku hakan ba kuma kullum cikin kukan rashin matata nakeyi mace ta kwarai mai afuwa shin miya sa Husnah ba zaki gado da ita ba ne? ".


Da sauri Husnah taje ta fad'a jikin sa tana kuka wanda kowa ya tausaya masu.


Haka dai su Husnah suka yafi mahaifin su shima ya yafe masu, matar sa kamar itace ta haife su, da zasu tafi kamar kar su rabu.



Koda suka koma garin su akayi bikin su Anisah aka kaisu gidajen su lafiya su Husnah kwana biyu suka dawo gidan su ba tare da sun sanar da dawowa war suba, sukayi mugun gani, dan Zee ce ta kwarto kwance a saman kujerar falo, zigidir haihuwar uwar su.


Wani irin tsanar su Husain yaji a take ya d'auko wayar cabur yaci uban su ya saki Zee a gurin kuma yace ko tsinke bazata d'auka ba, a haka tabar gidan.


Cikin kunci yake da ket Husnah ta samu ya sauka, tun daga wannan ranar ne suka dawo da soyayar su, watan Husnah d'aya da dawowa ta fara ciwo, sukaje asibiti aka sheda masu cikin Husnah boye, wa yayi yan zun ne ya fito watan sa hud'u, murna da farin ciki gurin su ba a magana, koda aka sanar dasu Ummey sunyi farin ciki sosai tare da fatan Allah ya raba lafiya.


Bayan wasu watanni Husnah ce ke lebour, Husain duk ya rud'e kamar ba Doctor ba indai akan Husnah ne, mancewa ma yakeyi da cewar shi likitane.


Nurse, ce ta fito tayi masu albishir da an samu baby boy, farin ciki harda sujada Husain yayi, da take lafiya ta haihu aka sallamesu suka dawo gida Ummey Zubaidah anyi Aure anyi hakali da ita ake Komai su Anisah kuwa ba 'acewa komai.

Su Baban Husnah da matar sa sun zo anan ne matar Baban Husnah wadda suke kira da mama tace, "wai kun san kuwa a ranar da kuka baro garin a ranar ne Marka ta haukace tabi daji, a she yaran nan nata "ya'yan bokan tane yazo ya kwashe yaran tare da sanar da ita cewar ai tunda ta bari su Husnah suka zo garin ita kuwa sai bar garin kuma bada yaran sa ba, kuma fa a gaban kowa hakan ta faru, kowa Allah waddai da masu irin halin ta suke yi"

Ai kuwa Husnah da Zarah suka ce Allah ya 'kara karemu da son zuciya"

Atake kowa ya amsa da amin.


Anyi biki lafiya Husnah kam an samu gudumawa a gurin yan uwa da abokan arziki, biki yayi biki, sai sam barka anyi taro lafiya an watse lafiya an samu Hanif

Su Baban Husnah sun koma garin su tare da sha tara na arziki.

Zubaidah ma tazo tayi barka ta zauna har akayi biki, mijin ta ya zo ya d'auke ta suka wuce.



kwanan su sitting aka maida Husnah d'akin ta, suna kwance sun saka Hanif a tsakiyar su, Husain yace har dai na tuno da Husnah lokacin da kike cewa, suka had'a baki gurin fad'ar *A GIDANTA NA GIRMA* .


*TO ALHAMDULILLAH NA GODEWA ALLAH DA YABANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN WANDA YA D'AUKI DOGON LOKACI BAN 'KARASA SABA SABODA RASHIN LAFIYAR MAHAIFIYAR FIYATA HAR ZUWA RASUWAR TA YA ALLAH KAJIKAN TA RAHMA KASA ALJANNA CE MAKOMAR TA ITA DA MAHAIFINA DA DUK KANNIN MUSULMI BAKI D'AYA* AMIN


INA GODIYA DA HA'DIN KAN DA KUKA BANI MASOYA NA ALLAH YABAR 'KAUNA. AMIN



*COMMENT AND SHARE*


Sai mun had'u a wani sabon novel d'ina mai suna...


*UMMU IHSAN CE*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment