Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai kaga andace gaskiya kam ..


Bawani tsoro babu komai yanufi gidan marayu yayi musu bayani sunkuma yadda da komai dan yanzu sundaina yadda da kowa sai anyi gwaji kafun siyama ta,amince ta yadda daman Rafi,atu sundade suna jan ra,ayin ta shiyasa mama Salamatu batasha wahala wajen nuna mata wannan abun akwai Alkairi a ciki ba ba,adau lokacin mai tsayiba aka tsaida ranan aure wata d'aya babu yawa.




Siyama tanada girman jiki tafi, su Rafi,atu komai shiyasa mutane sukanyi mata kallon babba ce ma.




BAYAN WATA D'AYA


A wani ranan jumma,a ne aka d'aura auren siyama da Abba Faruq babu hidima dayawa dan yace shiba yaro bane babu Wanda Ummi Aisha tagayawa sai Mabaruka, itan mayazama dole shiyasa tafad'a dan zirga zirganta ,a kai akai tanaganin tunda auren ta yamutu ko Abba Faruq zai amince ya aure ta in zatazo da kwalliya take suwa Sosai in Ummi Aisha ta kalleta sai tayi dariya


Tunda ,a kayi bikin Sayyada babu wani tashin hankali da kad'an kad'an Malam Sulaiman yake siyan wasu kayan ,a duk lokacin da yatina ,ina zainemi dangin shi sai yaji wani iri a ranshi "yazama dole ya nemi hanyar da zai sadashi da y'an uwanshi babu abunda yarage na shedan samun yan uwanshi
I
[25/05, 07:36] Maman Khairat: 🅿️9️⃣1️⃣⏭️9️⃣2️⃣


Alhaji musa ne yakira Nura "kaje gida kacewa Maryam tashirya kakawo ta tsamiyan lilo"lafiya kuwa? E batun dangin natanne ,nikuma ina office " ganinan zuwa.


"Anty Maryam ina wuni"kadai nacemun Anty "yazama dole in gayamiki kefa matar Babana ne taya bazan gayamiki Anty ba" Baba ne yace in daukeki ,in kaiki Anguwar tsamiyan lilo zai samoki a wajen "bari nashirya sai mutafi " ina Rukayya ?tana gida lafiyanta


A nutse yakejan motar, har suka, iso sunsamu Alhaji Faruq yana jiransu, zulfa,u itama tazo Nura yana,ajiye su yawuce gi da Alhaji Faruq yatsaya "sannun Ku kushigo mana duk an zauna " munaso muji labari akan maimuna da Yusuf"


"Kamar yadda mukayi zaman mutunci " tacemun ita yar Bauchi ne an hanasu ance bazasu yi aure ba shine suka gudo dan iyayen su basusan in dasuke ba sunzo nan damaturu wani babban malami malam Ibrahim ya daura musu aure ,akan wata budurwar shi tabiyo shi shima ,sannan tayi mishi fariya muddin bai aureta ba zata,iya had'a gobara duk su mutu ,da sunzauna a pamfamari ,daga baya suka dawo da tsamiyan lilo,tacemun sun rabu akan wancen budurwar tasa .suka rabu a lokacin tanada ciki amma suna zaune daga baya suka dawo da auren su tayimun kwatancen anguwan su a bauchi.


Har address d'in gidan tabani lokacin danaje, bauchi naje har gidansu naje sannan nace musu tarasu bamusan waye tazo tasaka wuta a d'akin ba "dan haka ke y'ar halak ne bata hanyar banza ,aka sameki ba ko yau zanbaku number wayan da suka bani",


Kowa nawajen hamdala yayi ,babu wanda yakai Maryam murna zataga kakanun ta da dangin mahaifin ta,basu number tayi sukayi mata in sani sosai.




*Washe gari*


Da safe suka shirya dan zuwa bauchi,tayi mamaki da yadda taga kakanun ta sunada ilimin addini taya suka bada k'ofa wajen ruguza rayuwar Yaransu sunyi madama bak'adan ba sunsha kuka kukan da babu amfani


Hak'uri suka bayar tare da had'asu da mutum d'aya dan yaga inda suke zaune har wani jiki maryam tayi ranan Rukayya da Rafu,atu sunje tayata murna " kinji dad'inki yanzu kam Allah dai yasa mudace"kekam rayuwarki da Sauk'i "banaso kunasa kanku damuwa duk Allah ne ya halicce mu bakuga yadda Allah yatsara abun shiba.


BAYAN SATI BIYU




A cikin satin ,aka d'aura auren Sayyada da malam sulaiman babu wani hidima da,akayi dan mutum ne mara sakewa da jama,a shiyasa bashida Abokai nai Sosai sai nagun aikin su.


Ansha hidima Inna bata gayyaci mutane dayawa ba, dan auren ma,a masallacin jumma,a aka d'aura auren .


Maryam da Rukayya sunhaihu a satin da suka haihu a satin sukafara jarabawar gama makaranta Exam sukeyi sun maida hankalin su suna karatu dangin Maryam sunzo dayawa dan Ranan sunan duk kansu suna Exam


Matan Baban Rukayya susuka zo dan zauna mata a satin Ummi Aisha tayi rawan gani wajen taimakawa Rukayya da shawarwari Sosai
[25/05, 07:36] Maman Khairat: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


STORY AND WRITING BY AMINA. MA,AJI (MAMAN KHAIRAT )


TRUE LIFE STORY


PAID BOOK 200


9️⃣5️⃣⏭️9️⃣6️⃣


Inna cikin kwanciyan hankali take babu wani sauran damuwa a tattare da,ita dan yanzu itama har taimakawa Almajirai takeyi in sunshigo bara kowani wata Malam Sulaiman yakan siyamusu shinkafa rabin buhu da wasu abubuwa daya sauwak'a .


Watansu hudu zakace sunyi shek'ara da aure " maman sadiya yanzu rayuwar tayi musu dad'i Sosai babu wani sauran damuwa, inda Sulaiman yanuna yanason Sadiya da aure haka, akaturashi k'auye wajen nema mishi auren ,anyi sa,a anbashi yayi murna saboda hankalin sadiya yanuna ra,ayin shi a kanta..


Alhaji Kyari"Rukayya yanzu nasan dukkanku kungama nasama muku duka aiki kuci gaba da tafiyar da rayuwar Ku,wannan aikin zaitaimake ki keda yaranki koda bayan babu raina.


Dan shi duniyan nan y'ar hak'uri ce nasan nawadata ki da komai banrageki da komai ba "naso mutanan da suka rayu dake, basu barki kinyi kukan rashin ,asali ba..


Baba kadai na fad'an haka rubuceccen Al,amari ne munaso bamaso namu k'addaran kenan " Allah yamuku Albarka Amin naji dadi da kukasawa Gwaggo Maisuna dan tasanadiyan Ku nasan darajanta gashi y'ar uwata ce tajini kuwa Allah yayi Albarka Amin




Babu wani sauran kunya yanzu da Rukayya mahaifinta yake shawara bayayin shawara da wani dan yafijin shawaranta a kan nakowa yana son y'arshi Sosai .




Mama Salamatu tana tafiya tafad'i take aka kaita Asibiti numfashi yak'i tsayawa ,ansanar a gidan marayu take Rafi,atu Rukayya Maryam Siyama duk sunji duk suzo banda kuka babu abunda sukeyi ga Siyama da k'aram ciki har kusan tara ,na dare duk suntaru babu Wanda ya,iya magana juyata,anata yumata fifita "Rafi,atu bani ruwa zansha " toh bari na d'agaki duk Kansu suka d'agata tasha Ruwan suka juyamata kai shikenan tafiyan kenan Allah yajik'anta yamata rahama .


"Tayi bacci kuduba babu abunda ke motsi fa," shikenan mama salamatu tabarmu ,babu Wanda baya kukan rashin mama Salamatu ,mata mai kirki ko haihuwa bata tab'ayi ba kowa sai yatausaya musu ,irin kukan datasukeyi koni naji mutuwar ,duk Wanda aka tambaya sai ace yaranta ne dan kowa sai katausaya mata, lalle gidan marayu anyi babban rashi bana kad'an ba...✍




Maman Khairat ce




🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


🅿️9️⃣7️⃣⏭️9️⃣8️⃣


🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


Haka ,aka shirya ta mutane dayawa suntaru kowa Alkairin ta yake fad'a babu Wanda bai fad'i Alkairin mama salamatu ba "Su Rafi,atu duk sunrame babu Wanda mutuwan bai shigeshi ba Yadda suka damu da mama Salamatu basudamu da iyayen Su hakaba Suwaiba tazo gai suwa tare da jajanta musu .




Malam Sulaiman yatafi memo dangin Su cikin sa,a yasamesu da kwatance Allah yahad'ashi da yan uwanshi yayi murna da hakan satin sa biyu yadawo Nigeria tare da musu Alkawari duk ranan da Allah ya Sauk'i Sayyada zai kawota tasaba da yan uwanshi dan suma suna cikin Farin ciki zasu koma Nigeria da zama


Wani kulawa da Abba Faruq yakebawa Siyama kaman bai tab'a aure ba sai a kan Siyama ganin hakan ne yasa Rafi,atu bata yawan zuwa gidan ,badan komai ba sai dan har yanzu kunyan Abba Faruq takeji taki sabawa da shine yahaifeta..




,A wani ranan ,alamis Siyama tahaihu tasamu beby girl yaranya kamar ba jaririya ba zakace tayi wata da haihuwa ,lafiyayya da ita gonin sha,awa.






Anyi Auren Sadiya cikin ikon Allah komai anyishi cikin rufin asiri Garbati shiyazama kaman uba dan duk abunda ,a,kenema babu Wanda yagaza ,yayi wa wani magani yad'auki yarshi yabashi ,Sadiq shikam karatu yakeyi yana polytechnic malam Sulaiman shike d'aukan d'awainiyan shi .




Sayyada taje wuni gidan Inna kafun kace miye tahaihu tasamu yaranta guda biyu duka maza ,sai kiran shi ,a kayi yazo yakaisu gida babu Wanda yasan zata haihu daga shi sai ita.


Garbati karatu ,duk da ya girma amma yasaka Ibrahim karatu dan ya ,dogara da kanshi.,sai dai muyi fatan Alkairi a Inna dan gidan ta yazama gidan Alkairi tarik'e Wanda bajinin taba ta .




Ansha suna y'an uwan Inna duk sunzo tare da na Janbo Anyi abu cikin kwanciyan hanhali.






A hanyar kaduna Abba Faruq sukayi hatsari take ya amsa kiran ubangiji babu Wanda baiyi kukan rashin Abba Faruq ba musamman Siyama ,bayan rasuwan da sati d'aya Ummi Aisha tarasu jama,a sai surutu sukeyi tsakanin Ummi Aisha da Siyama wata shida Allah yamusu rahama,anraba gado


*Tammat Tammat*


Anan Nakawi k'arshen gidan marayu kuskuren dake cikinta Allah ya yafemana Fad'akarwar Allah yabamu ikon amfani dashi


Sai munsake haduwa a littafi nagaba mai abun Al,ajabi Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment