Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo kujerar da take kusa da wacce sameemah tah zauna"
"Kallonsa tayi cikin yahtsina fuska irin ta tattatun shu'uman matannan kafin tayi masa magana tana yin bubble da dank'on cingam din da yake bakinta,
"Alhaji ka damu akan nazo nazo,toh gashi nazo saika fadamin menene dalilinka na kirana,kana ta zancen shakatawa gidan rawa zamuje koh gidan shaye shaye"
"Ah kina zuwa gidan rawane da dakuma shaye shaye?"
Yah tambayeta da mamaki,
"Hmm lallai kai karamin dan akuyane a cikin awakin,ai inaga nafi sabuwar bishiyah lokacin damina rausaya,sannan fidda hayaki kuwa,koh itacen murhu bazai nuna mini fitarda hayaki ba"
Maganar da sameemah tayi masa ta bashi haushi amma haka yah murkushe ta yah hadiye kaman wanda tayi masa asiri.
"Toh shikenan barina kira idi tun baiyi nisa ba yah had'o miki da taba"
"Ahah mai kake nufi banasha cigarettes,wannan kayan saka mutum baki,saidai dulah,itama karka wahalar da kanka dan ba kowacce nakeso ba "
"Toh shikenan ranki yah dade,yanzu dai mekike bukata"
"Kai me make bukata dai?saboda kai ka damu nazo ba nice na ce zanzo ba,yanzudai ina bukatar shiga bandaki nuna min dakinnaka zan shiryah tukunna"
AI kuwa cikin rawar jiki har murmushi yake ya nuna masa dakinnasa,dan shi a ganinsa koh irin dabarunnan irin na mata zatayi kafin azo kan harka.
Wuceshi kwas kwas tayi ta nufi dakin,har tazo bude klfar zata shiga sai kuma tazuyo tana kallon alhaji bala,
"Am yawwa nace ba,karka kuskura ka biyoni ka jirani na fito dan ba dad'ewa zanyi ba"
Saida yayi dariya irin ta yan duniya kafin yace,
"Ahhhhh karki damu wane irin shigowa kuma,ai ki gama shirinki tsaff yanda zakiyi zam zam najini a sama tah bakwai"
Wani Murmushin gefen baki tayi masa kafin ta bude dakin ta shiga,tana jijjiga kai,alamun zaka ci ubanka.
Tah dan dad'e a d'akin saiga ta tafito,tana gyara zaman rigarta wadda ta tattare saboda matseta da tayi,cire gyalen kafad'arta tayi ta ajiyeshi a kusa da itah,Alhaji bala sai binta yakeyi da wani mayen kallo yana lashe baki.
Duk abinda yake tana kula dashi har yah bude soyayyar kazar da aka nannadeta a takadda,cirewa tsokar yayi daban dakuma kashin yah ware a gefensa sannan yah tura gabanta yana cewa,
"Bisimillah hajiyata kici iyah cinki"
Kiran sallah akeyi a cikin anguwar na azahar,sameemah ceh tah kalli alhaji bala bayan tah cika bakinta da naman kazar ta cinye,
"Alhaji bala bala zuwa masallacine naga kana zaune ana ta sallah"
"U hmm na'am oh wai sallah zanje,ke kuma idan kin gama saiki shiga ciki kiyi sallahr"
"Karka damu ni banayi ai"
"Eh me kike nufi yanzun dama kinsan kina cikin rashin sallah kuma baki fad'amin ba har kika zo?"
"Ba wannan nake nufiba sallahr ce dama banayi ,daga azumi sai azumi nake sallah a rayuwata saidai kuma idan ansakani dole,wanda ita ma idan inayi bana cewa komai,amma idan akan ra'ayin kaina ne bana yin sallah"
Cikin jin dad'in zancenta alhaji bala yah tuntsire da dariyah harda buga kafa yace,
"Kai kefah kin had'a abinda nakeso,kuma dama ke bakyayin sallahr kike cewa ni naje nayi,toh nima yau kam sallah nayi mata yajin aiki,kinga idan muka shiga daga ciki bazamu fitoba har sai duhu yakawo kai ,koya kikace?"
Bata kulashi ba duk surun dayake yi saima antaya naman kazarta da take tayi ,saida taci tayi nak kafin tace masa,
"Zuba min lemon na Kora da sanyinsa kar yah huce"
"Hooo Bari a zuba miki lemo kisha kam,saboda kiji dad'in hawa service,nima ai na koshi da naman tunda kin koshi"
Kofi biyu yah fitar masu glass sabi fill a leda kafin yah zuba lemon a ciki,wasu kwayoyi ya d'akko da niyyar zubawa a cikin lemu kan,sameemah ceh tayi saurin dakatar dashi tah hanyar cewa,
"Ahah karka sakamin kwayoyin karin sha'awa"
"Ah ashe kin sansu kenan?"
"Me ka daukeni karamar yar iska?"
"Ahah nibance haka na,tunda bakya so shikenan,da alama yanda kike da karfinnan haka kike idan an hau gado"
"Eh ina ga kam,kai idan kanaso ma zaka iyah juye nawa kwayoyin ma akan naka,nafijin energy idan banyi amfani dasu ba"
"Hahaha ayi haka,kice nakara duk akan nawa danna
jini a sama kenan,ku ai yarane nikuwa saida su kwayar idan inason yin dogon aiki wanda zai d'auki lokaci,toh bari najuye su ma dukka kawai"
Aikuwa yana gama magana yajuye dukka kwayoyin sameemah acikin nasa lemon.
Yana dagawa saida ya shanye tas kafin yah ajiye kofin yana karewa SAMEEMAh kallo kaman zai cinyeta d'anya.
Saida tasha lemon ta tabbatar tah koshi sosai kafin ta dan kishingide akan cushion din kujerar,alhaji bala ne yayi saurin cewa,
"Haba madam da girmanki ki kwanta akan kujera,ai muje daki ki baje sosai ,amma kya kwanta akan kujera"
Batayi masa musu ba sai tashi kawai da tayi ta nufi cikin dakin,kaman jira kuwa yake da sauri yah bita yana had'a hanya kaman dan maye.
Tana zama a bakin gadon shima yah zauna yana narai narai da ido kaman anyiwa yaro kwacen alewa,ga idonsa yayi ja da alamun kwayar da yayiwa over dose ce tah fara tambayar sa.
"Menene yasa ka kirani nan wajen ,har yanzu baka ban amsata ba bayan tun dazu nake tambayarka?"
Ransa ne yah fara b'aci da tambayar ta ganin yanda tah ma raina masa hankali,cikin bacin rai yace,
"Bai kamata kina min haka ba seemah dan kinga ina binki ina lallabaki,ke kanki ba buk'uwace ba a wannan harkar kin fi kowa sanin abinda nake bukata daga wajen ki,tunda a gabanki na sha kwayoyin karin kuzari "
"Toh Idan kuma naki baka abinda kake nema kuma yah zakayi?"
"Hakanma bazai faruba dan nasan bazaki taba fadan hakan ba tunda kema da amincewarki za'ayi"
"Haka nace maka da amimcewata ?"
"Kee yakamata kima daina batamin lokaci dan baki isa kicemin kin fasaba saboda yanda na bata lokacina wajen lallamarki da kuma naman dana sayo,sannan kuma idan baki shirya ba saiki fadamin yunda farko ,amma kina ganin na sha kwaya a gabanki amma bakice komai ba sai yanzu kicemin wai idan kika ki yarda mezai faru?"
"Eh Toh mezai faru idan naki amincewar,ai tambaya ce nayi maka"
"Matseki zanyi nayi miki dole dan in kinki ta dad'i saka miki karfin maza zanyi tunda yan dabar taki basanan bare su kwaceki,Sannan kuma bazan baki koh sisi ba haka zan koreki a gidannan,inaga yarinyah bakisan halina ba ne,toh bari kiji na fadamiki a gidanna bansan iyah adadin yara nawa nayiwa fyade ba ,ko kuma na lalata,dukkansu kuma babu wanda nayi mata a san ranta,ke kadaice nake binki dan nayi miki da yardarki saboda bakaramin sonki nake ba,in kikayi sa'a ma harka ta goge dake zan dunga zuwa abuja"
"Duk naji bayanin ka amma ban amince ba"
"AI kuwa baki isaba yarinyah"
Yana gama fadar haka yayi sauri yah riko kunkuminta yah jawota kusa da shi. Bai ankara ba kuwa saijin mari yayi tasss a kumatunsa saida yah fad'a kan gadon tah baya yana kikkifta ido,saboda hasken ganinsa daya d'auke na wucin gadi.
Tashi tayi daga kan gadon tah koma jikin madubin dakin tah tsaya wanda yake kallon gadon,tsura masa ido tayi har yah gama juyinsa akan gadon yah tashi ya zauna,yana had'a ido da ita ya hadiye wani yawu tareda cewa,
"Kai kai dutsin guga kika manna min a fuska ko me"
"Au tambaya ma kake,zaka kuwa san me na manna mama,kuma kayi kuskure tabbas ka tsokano rina a gidanta,dan kayi min abinda tunda nake babu wanda yah taba gigin yinsa ,shine tab'a gangar jikina,duk duniyah babu wanda zanyiwa amincewar taba jikina,ba miji ba koh mai martaba ne bai isaba,saboda jikina ne nikadai kuma nikadai ce mallakinsa.
Kai kuma ka sab'a dokata dan haka a hukuncin danayi niyyar zartarwa akanka na rainani dakayi ta hanyar gayyatoni wannan matsiyacin gidan,saina k'ara maka da tab'a jikina ma dakayi,yau mai hanani hukuntaka a gidannan banganshiba a fad'in duniyar nan"
Tana magana muryarta tana fita da amo kamar muryah guda biyu ga kuma annurin fuskarta daya d'auke tass.
Tun kafin aje ko ina alhaji bala ya sau fitsari akan gadonnasa,ga jaraba tana cinsa na maganin daya antaya a cikinsa.
😄😄😄😄😄
Tab kashigesun ka (su alhazawa anji manyan mata).

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
  Kasuwar  Rimi  Kano
Tel:📞 *07038339244*

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤12❤

Nufoshi tayi yana matsawa har sukaje karshen gadon,a lokacin jikinsa har karkarwa yake saboda tsoronta daya d'arsu a cikin zuciyarsa,dan a sannan koh qur'ani aka bashi zai iyah rantsewa akan ba sameemah daya sani wacce yah saka aka kawota bace a gabansa,duk da suna kama da itah saidai kamanninta sunsha banban da itah.
Wani marin tasake kifah masa ,saidah tah jerah masa kusan biyar,kan kace me kumatun alhaji bala sunyi luhu luhu kaman fanke sai shek'i sukeyi saboda kumbura da sukayi.
Tun yana daurewa har yah fara kuka wiwiwi harda majina shab'e shab'e. Komawa tayi inda take tsaye saidai sannan tah koma ainihin kalar ta,wani Murmushin tayi masa irin na muguntar nan kafin tace,
"Karka damu mucigaba daga inda muka tsaya a maganarmu,wannan hukuncin tab'a jikina dakayine na maka"
"Yanzu menene sunan abinda kikamin ina nemanki da arziki kina nemana da tsiya?"
"Yawwa gwanda da kace kana nemana da arziki ai haka nakeso Alhaji,kai ne shugaban kungiyar vigilantee na garinnan koh?"
"Eh nine amma bazan had'aki dasuba ai"
"Oh kana nufin cewa zanyi karka saka su su kamani?,lallai baka sanniba ina ga so kake na k'ara maka wani marin"
"Ahah kiyi hakuri na tuba ki yafeni"
"Kai Dallah ni kadaina wani rokona haka,sai kace wani sarki da bafade,so na ke shugaban kungiyar ka d'orani akai,zan baka nan da wata d'ayah daga nan bazan k'ara koh kwana d'aya ba,sannan yarana ma zan nad'aasu mufara aiki tare,dan garinnan yana bukatar gyara sosai,kuma na duba naga babu mai gyarashi sai ni nan jar wuyah"
Watstsakewa yayi daga marin da tayi masa yah yah gyara zama kafin yace,
"Lallai na yarda ke yarinya ce,yanzu marin dakika yimin ne kike tunanin zai sa na sauke yarona dayake kan shugaban kungiya na baki,kinsan irin wuyar dana sha kafin na kafa wannan kungiyar zuwa yanzu,lallai da sauran ki"
"Babu saurana alhaji kungiya kuma dole saika bani idan kuma ba hakaba zaka ga aikin yarinta kaman yanda kafad'a"
Tana gama fadar hakan ta matsa wajen television dinsa tah ciro wata y'ar karamar camera wanda duk nacin mutum bazai san da ita ba inba yasan sanda aka saka ba.
Zuwa tayi gaban alhaji bala tah tsugunna,
"Nasan kasan menene wannan ba sai nayi maka karin bayani ba ,kuma kasan wacece hajiyah kulu,(matarsa) dakuma wannan saurayin umaruje(babban d'ansa wanda yake karatu a UK),toh cikin minti talatin sakon dayake cikin nan zaije ga kunnensu ,sannan bayan sun gama ji sun more,saikuma mutanene garinnan suma su shaida wanene alhaji bala,ko ban tuna maka ba ,kasan wane irin fad'e fad'e kayi a dakinnan koh?,toh maza saka hannu a cikin takardar nan"
Tafad'a tana mika masa wata takarda,tsilli tsilli yayi da ido,ganin irin ruwan daya d'ebowa Kansas babu damar kuma fita daga ciki.
Mika hannu yayi yah karb'i takardar hannunta amma daga nan ko motsi bai sake yi ba kaman wanda aka sankare shi.
"Oh Ashe ban baka biro ba,bari nabaka"
Tafad'a tana mika masa biro,ya dad'e kafin yah karbi biron yah fara rubutawa kaman mai koyon rubutun,
Yana gamawa yah mika mata takarda fuskarsa d'auke da dana sani,fisgewa tayi tareda sake dubawa,
"Yawwa yaron kirki ashe kana jin warning,yanzu kuma saikayi shirye-shiryen d'orani saboda jama'ar gari su shaida,ko baka jiba?"
"Eh naji"
"Yawwa mutumina,ashe kasan abinda kakeyi,kuma yawwa bari na fadamaka,motar da aka kawoni d'azu gaskiya akwai dadi,kuma ta birgeni,dan haka da itah zan tafi ina sonta"
Alhaji bala bai san sanda hawayen takaici yah zubo masa a fuska,saboda tsabar irin fashin da sameemah tayi masa tunda yake a duniyah ba'a taba yimasa ba,ga kuma babu damar yayi magana.
Itah kuwa gogar key d'in motar ta d'auka akan kujera a palour,tah fita tana kakkad'ashi tana fed'uwa har ta bawa motar wuta tayi gaba abinda kaman babu abinda ta aikata.
Bayan fitar sameemah Alhaji bala ya dade a zaune bai motsaba ,can kuma yah kokarta yah tashi yana tafe yana had'a hanya gakuma rashin arzikin da sameemah tayi masa.
Itah kuwa gogar daga wajen gidan shakatawa ta wuce(club)inda kowane d'an iska yake baje nasa bidirin.
Tun a hanyah tah fad'awa su burgu akan su sameta acan,da murnar su suka isa wajen kuwa dan sunsan baza'a tashi banzaba.
A tare suka iso wajen su da itah,saidai sai waigawa suke koh zasu ganta amma babu wanda yah hangota,ita kuwa a nata bangaren tana kallon su daga cikin motar da take zaune,saida taga alamar bazasu gantaba kafin tah bud'e motar tah fito,da mamaki suke kallonta bakinsu a bud'e,burgu ne yayi karfin halin cewa,
"Shugaba jar wuyah wannan motarfah daga ina kika samotah,ta wayeh haka?"
"Tawa ce"
Daga nan bata sake cewa komaiba sai wucewa da tayi cikin club d'in suma suka bita a baya.
Shirya musu table akayi ita da yaranta kafin aka tambayi order,kowa shiru yayi yana jiran shugabar ta fad'i abinda takeso,d'aga yatsunta tayi sama tai kyass dasu kafin tace,
"Ki kawomin ruwa mai sanyi kawai,su kuma kowa ki kawo masa abinda ransa yake so"
"Sai ogahhhh suka fad'a cikin jin dad'i"
Kafin kowa yah fadi wane irin kayan maye yakeso.
Bayan an kawone kowa yah fara hawa caji,kafin sameemah ta kallesu d'aya bayna d'aya tana wani linshe ido kaman wanda akewa tausa,ajiye kofin ruwan sanyin tayi kafin tace,
"Kusha iyah shanku,daga yau duk kun daina shaye shaye"
Kallonta sukayi a zabure cike da Mamakin abinda ta ce,
"Eh Ai nasan kunjini,shaye shaye is enough from now,do you hear me"
"Kowa kallonta yayi kamar ba itah ba,jin yanda take turanci kaman wata yar gidan mongopark,
"Daga yau duk gyaraku zanyi na d'ora ku a hanyar gaskiya,saboda iyayenku basa son abinda kukeyi,kuma nayi tunanin dan inaso nayi iskancina bai kamata nasaka ku acikiba,bayan wannan shaye shayen dakuke zai iyah tab'a hankalinku dan na kula ni kuke biyewa bayan nidaku ba d'ayah bane.
Saboda haka wani watan zan zama shugabar kungiyar vigilantee na garinan,dukkan ku zan d'aukeku aiki,saidai bazan hana kowa yin muguntar daya ga dama na,amma shaye shaye na hanaku daga yau,ni kadai zan dungayi banda ku,saboda zai iyah yimuku illah.
Dan haka kowa yaje yah shirya kafin zuwa nan da wani watan,zaku tayani fara aikin rashin mutunci a garinnan,dan nakula kowa yah rainani,tun daga kan yan gidanmu har kan yan gari saina saita su na gyarawa kowa zamansa.
Da fari sun ji babu dad'i data hanasu shaye shaye,amma daga baya da sukaji zasu sami aikin vigilantee kuma kowa zai yi tsiyarsa yanda yaga dama ba mai hanashi,ai suka fara ihu,kowa yana tunanin wace irin mugunta zai shuka a garin saboda ya kafa tarihi.(Allah dai yah kaimu lokacin)
Suna cikin ihunsu ne,itakuma sameemah tana zaune kaman wata mai hankali tana jinsu,wasu y'an matane suka zo wajen table dinnasu guda biyu,sunyi shiga irin ta bariki amma daga ganinsu kasan bakaraman gogaggu bane a harka tsiyah,wani rausaya sukayi tareda sauke muryah kafin sukace,
"Uhm idan bazaki damuba seemah jar wuyah muna san muyi magana dake"
"Ku fad'i miye ina jinku"
"Am da mundan fita waje saboda yanayin hayaniyar wajennan da kuma gamu a gaban maza,sannan maganar mai muhimmanci ce"
Har su burgu sun hayyak'o zasu fara masifa ,sameemah tah dakatar dasu tareda cewa,
"Ahah ban as on hayaniyah,ku kuma ina kukeson muje muyi maganar?"
"Akwai wani lungu ta bayan gurinnan inaga muje can,saboda nan babu kowa"
Burgune ya hararesu kafin yace,
"Gaskiya shugaba bai kamata ki bisu ba ,ni kawai daga ganinsi naji ban yadda dasuba gaskiya"
"Kai ne gaba dani koh nice shugaba?"
"Kece shugaba"
"Toh bance kasake shiga maganar nan ba,sannan kar kowa yah biyoni ku gama abinda kuke ku tafi gidanku"
Tana gama fadin hakan ta tashi ta bi bayan matan suka bar wajen.
Saida sukayi tafiya mai nisa amma babu wanda yah ce komai daga itah harsu,dan a yanzu sun bar wajen hasken club d'in sun fara shiga cikin duhu,tsayawa tayi tana karemusu kallo,yayinda suma itah suke kallon ganin ta tsayah,murmushi tayi tareda kama kunkumi ta gyara tsayuwarta,
"Wai har yanzu bamu iso gun wanda suka aiko kun ba,koh suna tsorone basu fitoba,yanzu kam ai munfita a cikin haske,kafar mutane ta d'auke a wajen ,duk abinda zasumin ma babu wanda zaiji su"
Zaro ido matan sukayi da Mamakin yah akayi tasan abinda suke niyyar aikatawa,kallon kanannan yara tsyimusu kafin tak'ara da cewa,
"Lallai Ku yarane,a tunanin ku bansan me kuke nufi ba,toh tun a hanya nakulada ku kuna bibiyata,har na shiga club din kuma kuka kama table,bayan kunyi waya da wanda yasakaku kafin kuka nufo inda nake".
Fezar da iska tayi daga bakinta irin na takaicinnan sannan ta d'ora da cewa,
"Lallai wanda yah aikoku bai sanni ba har yanzu,ku kuma ba laifinku bane,amma idan muka gama da wannan cakwakiyar ku tabbatar kunnemi inda nake kunzo ,domin inason yin magana daku"
Bata gama maganar ba tajiyo karar fed'uwa a bayanta anabin kid'an wakar *naira maley*,koh kuyawa batayiba har me wakar yah zo ta gaban ta,da wata wuk'a a hannunsa ya sak'alata a wuyansa.
"Yau wata tazo hannu babu yaranta,ina dasu kike takama har kika aikatawa shugaba haka(buba jini).Toh yau saidai uwarki ta haifi wata,dan saimun farke cikinki mun cikashi da kasa,mun jefar a hanyar dabbobi"
Duk maganar cikin larabci yakeyi irin na sudan,dan shikansa mutumin baiyi kama da mutanen nijeria ba.
Farine sol yahsha rawani ,amma koh a duhu mutum yah ganshi yasan ba karamin tantiri bane.
Wani ne daga cikin mutanensa yah matso kusa da itah tareda fassara mata abinda ogannasa yace,saidai har yah gama fassarar babu alamar tsoro a fuskar sameemah,dan ko motsawa batayiba daga inda take.
Mutumin ne yah kalli yaronnasa tareda tambayar,
"Ka fassara mata duk abinda nace kuwa?(yah kara fa'da cikin harshen larabcin)"
"Eh shugaba dukka na fassara mata"
Fusata yayi da yanda tah wani tsaya babu alamar tsoronsa,bayan duk kasar dayaje kowa tsoronsa yake,cikin zafin nama yah d'aga wukar hannunsa yah shaftawa sameemah a hannunta na hagun inda rigarta bai rufeba,wanda kuma yayi dadai da isowar su burgu wajen da gudu.
Ihuu suka fasa dukkansu ganin abinda akayiwa shigabar tasu,burgune yah isa wajenta da sauri,saidai tsayawa yayi cakk a gabanta yana karewa wajen da'aka yanketa ido,jijjiga kansa yayi tareda murza idonsa,anya kuwa yah gani dadai,saidai lokacin daya d'ago idonsa yah kalli Mamakin dayake kan fuskar kowa har shikansa wanda yayi aika aikar sai hakan ya tabbatar masa da abinda yah gani gaskiyah ne ba gizo idonsa yayi masa ba.
Wajen da aka yanki sameemah ne yake komawa yana had'ewa dakansa,kaman yankan wuk'a bai tab'a wanzuwa a wajen ba,shikansa jinin daya fito a wajen k'onewa yayi ya b'ace b'atttt.😲😲😲.

*+______________________+*
*ABIN YABO BOOKSHOP*
  Kasuwar  Rimi  Kano
Tel:📞 *07038339244*


❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

#comment
#share
#like
#follow.

____** *GIDAN GANDU* **____
❤❤By sadi-sakhana❤❤


Wattpad username:SAKHNA03


❤13❤

Ganin kallon da burgu yake mata yah isheta ne yasa ta tureshi daga kusa da itah kafin tace,
"Kai miye kazo kusadani har haka kaman zan maida ka cikina,wato dana ce karkuzo saida kuka biyoni koh,banzaye taron matsorata,ji idonku kaman kunga aljani da tsakar dare"
Har tagama masifarta bayan ta tureshi bai ko motsaba,saima kallonta yakeyi kaman yah samu hoto.
Wuceshi tayi taje har gaban shugaban,wiwi din da take hannunsa tah karb'a saida tayi masa zuk'a mai kyau kafin ta fesar tah hanci da baki,jefarta tayi take a kasa kafin ta mayar masa da martanin maganar da yayi mata cikin harshen larabcin da babu inda akeyinsa sai ainihin cikin kasashen larabawa.
"Oh da kana tunanin banajinka d'azu koh,hmmm lallai kana cikin duhu a gameda sanin koh ni wacece,saidai yanzu zan nuna maka wani misali"
Tana gama fad'ar hakan tayi masa ruk'o tareda kafa hakoranta a akan wuyansa,babu wanda yasan mai yah faru sai ganin sa sukayi dukka yah fad'i a kasa kaman wanda yah mutu.
Kare masa kallo tayi tana goge jinin dayake bakinta,tana kuma tofar da yawu,
"Ka tursasani yin abinda banida niyyah,ku kaishi asibiti aka ra masa jini yah mori lokacin sa kafin su biyo nemansa kwanan sa yak'are"
Juyawa tayi ta bar wajen,har ta yi nisa amma su burgu basu biyota ba kamar wanda suke jin tsoron ta a yanzu,kallonsu tayi harda matan da aka aikosu gurinta,kafin tace,
"Duk wanda yake wajennan yaga abinda yah faru inason gobe da safe yah sameni a office din kungiyata ,wanda bai san wajenba yah samu yarana su rakashi,kunji ina?"
"Eh munji muka zamu dole"
Kowa a wajen yah amsa jikinsa har rawa yakeyi tun daga kan yarannasa har yarannata.
Tana komawa gida ta shige dakinsu kan gadonta tareda rike kanta wanda yake barazanar fashewa dan azabar ciwo,da haka har bacci barawo yah saceta.
Da safe gidan da shirye shirye aka tashi na zuwan major sameer wanda zasuzo shida matarsa da kuma d'ansa,zuwan gobene amma tun yau ake shiryawa saboda cewar matar tasa yar shugabansu ce.
A bangaren sameemah kuwa da ta tashi ma batasan wace wainar ake toyawa ba saboda wankan ta tayi ta fice babu wanda tayi wa magana.
Motarta ta nufa wanda ta ajiye a kofar gidan,abin mamaki babu yaro ko d'aya a kusa da motar,saboda da wanine koh mashin ya ajiye sai an jefar dashi barekuma sabuwar motah

Direct gidan kungiyar tasu ta nufa inda take kiransa da office dinta,saboda a makare ta zo ,gidan a cike yake kowa yah hallara ana jiran isowarta.
Tana shigowa kowa yayi tsitt kaman ruwa yah cinyeshi saboda ganin fuskarta a murtuke kaman ta boss din y'an indiyah.
Zama tayi akan kujerarta yayin da kowa yah zube akasan wajen yah zauna kaman wanda akayi musu wahayin su zauna a lokaci d'aya,kallonsu tayi da mamaki ganin harda su burgu ake mata kallon dodanniya ko mayyah,wanda ko kadan bata ga laifinsu ba saboda ita kanta tasan ta dace a kirata da dodanniyar,domin tun tashinta lokacin data fara maida martanin abinda ake mata ,yazamana kowane halitta yah rabeta sai yaji tsoronta,"lallai akwai aiki"ta fad'a a ranta.
Gyaran muryah tayi kafin daga baya tace,
"Kowa yah ga abinda yah faru jiya daddare ko?"
"Eh kwarai kuwa mun gani sosai"
"Toh inaso daga nan wajen kar kowa yah tuna cewa yah ga abinda ya faru barekuma yabawa wani labari,idan kuma ba haka ba,............"
"Baza akai ga hakaba babu wanda yah tuna abinda yah faru ,koba haka ba yan uwa"
Burgu yah fad'a yana kallon kowa a wajen,cikin sauri kuwa suma suka amsa da cewa,
"Hakane babu wanda zai tuna da abinda yah faru"
"Shikenan naji abinda kukace,saidai nasan a yanzu kunsan koni wacece,kowa a cikinku zai dunga kallona a matsayin dodanniya,kaman sauran mutanen dana yi rsyuwa dasu a baya,saidai bazan ga lafinkuba saboda nasan dagaske hakan nake"
Sukunyar dakai tayi alamun hakan yah tabata,saidai cikin sauri tamayar da fuskarta wanda babu wanda yasan mai yake cikin zuciyarta.
Burgune yah d'ago kaman zayyi magana sai kuma yayi shiru,kallonsa tayi ganin yanda magana ma yanzu yakasa yi mata,ganin yanda a lokacin baya har kyaleshi take idan yah isheta da surutu,
"Karamin shigaba wace magana kake da itah?
"Eh dama shugaba,mun ji kinyi yaren larabci kaman wata balarabiyah,ga kuma abinda yah faru wanda gaskiya yah shige mana duhu,toh kafin kizo kowa yah ce na taimaka na tambayeki ,idan bazaki damuba munason jin tarihinki"
"Shine bukatarku jin labarina"
"Eh Ranki yah dade"
"Toh shikenan bari naga koh bazai d'auki lokaciba,saidai inaso kusani bawai zan fad'amuku saboda ku kai wa wasu labariba,saidan inason yin aiki daku,kuma naga yakamata kusan ni danjin da wa kuke zaune"
*** *** *** ***

Da farko kaman yanda kukaji sunana SAMEEMAH,saboda tunda nayi wayo haka na tashi naji ana kirana,abinda yha faru kuma kafin nayi hankali toh banida masaniyah akai.
Mahaifiya ta hajara batada lafiyah,kullum tana daki kafafunta suna ciwo,ko yau she nice nake gyara kaya idan tah bat'a sannan na kai mata abinci idan kuma taci na fito dashi,shikuma yayanah wanda shima muke uwa d'aya dashi wato yah sameer,shine yake wanke kaya idan tah b'ata saboda ni sannan ban yi wayon yi mata hakanba.
Watarana da safe na tashi daga bacci da safe lokacin banfi shekara shida ba,saboda tun bankai shekarun yin wasu abubuwan ba nake koyah,duba da halin da muka tsinci kanmu nida ummah tah,shikuma yah sameer namijine kuma yayi girma koyaushe suna gona shida baba umaru ,don su manjo ko me za'ayi bazasu jeba,kuma haka inna ramatu take d'aure music gindi suyi abinda suka ga dama.
Bayan na yi shara da kuma gyarah dakin da muke,inna ramatuce tah shigo d'akin tana ta zage zage wai ummah tah bata iyah aiki kuma ta hanani ni na gunga tayasu aiki,ummah ceh takalleni bayan ta d'auke idonta daga kallon inna ramatu wadda tah kama labulen kofar ta rike tana ta masifa kaman tanayi da y'arta ba kishiyarta ba,
"Seematu tashi kije ki tayasu wanke wanken kinji keda su sameerah kuyi"
Inna ramatuce tayi saurin cewa,
"Su sameerah bazasuyi ba itah kad'ai zatayi ,ai su jiyah su sukayi lokacin da kika aiketa karb'o maganin munafurci,yanzu haka ma na cutar damune mu da y'ay'anmu"
Ummah bata kulataba saini ce,da abin yah k'ona min rai nayi magana,saboda maganin da take magana akai,manjo fah ummah tah aika a wani kauye kusa damu amma yak'i zuwa,saboda

Please Login or Register in order to submit comment