Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce ma malam " amma uncle ya za ayi ta manta rayuwar ta, amma ta san rayuwar wasu ko kuma amnesia ce ? "

Girgiza mishi kai Malam ya yi kafin ya ce " Zayd abun guda na sani , duk ranar da ku ka zama abu guda , ita da kan ta za ta ba ka wannan amsar , ni da kai na na jima ina neman wannan amsar amma na rasa , Ina ji a jiki na , Inaya kamar ba ita daya ba ce a cikin gangar jikin ta , amma zuciya ta ta kassa yarda da hakan , idan ma aljanu ne gare ta ko ma minene ita kadai za ta iya ba mu wannan amsar "


dan karamin tsaki Zayd ya yi ya na kauda kai gefe kafin ya juyo ya kali malam ya ce " uncle ku na son ku saka rayuwar ta cikin hatsari ne , ba ku san wanene ni ba , ba ku san da ga ina na fito ba , ba ku yi tunanin ko bibiya ta a ke ye ni ma , ba ku san irin hatsarin da ke cikin rayuwa ta ba ku na neman ku saka ta ta a cikin wannan kangin "

murmushi mai dan sauti Malam ya yi kafin ya kai hannun shi saitin zuciyar Zayd ya ce " ni wannan na duba , ban duba kyawon ka , ko arzikin ka , wannan kadai na duba , saboda na San sai wanda ke da zuciyar maza zai iya ba wa autar tawa kariyar da ta dace , Zuciyar ka mai kyau ce Zayd dalilin da ya sa na yarda da kai kennan " ya kai karshen ya na janye hannun shi


a hankali Zayd ya motsa lips din shi ya ce " Heart ?????? "

yar karamar Dariya malam ya yi kafin ya ce " yo malam Zayd kai ka san minene hakan dan ni ban yi boko ba, yanzu dai mu tafi lokacin sallat ya yi kar mu rasa jam'i "

Malam na shirin tafiya Zayd ya yi saurin cewa " uncle ina son nayi magana da Nesrine kafin mu tafi "

Juyowa malam ya yi ya na kallon cike da tambaya, ko dalilin mi ya ke son magana da Nesrine ? Ya tambayi kan shi

Shi kuma Zayd ya tsaya ya zuba mishi idanu ta cikin glass din shi ya kassa yi mishi magana fada mishi dalilin da ya ke son magana da ita , yau dai zai kawo karshen komai

TO FA NESRINE YAU ZA KI GA FUSHIN ZAYD 🤣🤣🤣
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment