Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsafin nata a tsakkiyar wasu irin bakaken bukkokin bamboo da ke a jajejin. Firgitaccen ihunta da gumzar azabar da take yasa dajin amsawa, kamar busa kaho wasu irin mutane marasa kyawun gani da mummunar suffa irrin tata suka fara tururuwar fitowa. Duk dinsu babu mai kaya a cikinsu, tsirara suke yara da manya maza da mata, sai dan ganyen da suke rufe iya al'aurarsu kawai. Matan ko da ga samansu ma duk a bude yake tun daga yammata har tsoffi. Cikin kankanin lokaci duk suka zagayeta, yayinda wasu tsoffi da bazasu kaita shekaru ba suka rufu a kanta su kusan biyar maza biyu mata uku. Dagata sukai gaba dayanta ita da kujerar, daya da ga ciki kuma yay saurin yafa mata jan kyalle a saman fuskar datai kaca-kaca da jini. Daya da ga cikin dakunan Bamboo din suka shiga da ita, shikam da yar sabuntarsa kuma babba ne, sai dai cike yake da da was irin tarkacen bakaken gumaka da akaima ado da ja. Kujerar suka ajiye tare da fara zagayata suna was irin surutai da dukawa da tashi kamar wanda zasuyi ruku'u. Tuni nacan waje ma sun tattaru a kofar dakin yara da manya a layi, idan wadan can suka fadi surkullen sai su kuma su amsa musu da ga waje suma suna dukawa da mikewa. Gaba daya jajejin babu wani sauti da kakeji sai wanna surkullen nasu. Haka suka dingayi tsahon lokaci kafin a ciki su fara dibo was ruwa dake a manya-manyan randunan kasa na cikin akin suna zubama Uwa da cigaba da zagayeta cikin surkullen. A haka suka wanke mata jinin fuskarta tsaf, hancin dai ya fita babu kyawun gani sai fuskar ta kara munancewa fiye da da can. Amma jinin ya tsaya. Magunguna suka sassaka mata a ciwukan dan duk ta yayyanke dan ba hancin kawai ba. Bayan sun nutsa itama ta daina mummunan nishin da takeyi sai dai har lokacin a wajige take. Cikin mummunar muryar nan tata ta shiga kwala kiran wasu irin sunaye, jif!! jif!! jif!!! Kakejin abubuwa na fadowa cikin dakin, babu alamar toro a tattare da su, sai dai duk suna gabanta a tsaye kawunansu a kasa alamar girmamawa a gareta, Da wani irin zafin rai ta shiga nuni da bakaken hallitun dake ta fadowa. Ta nuna na farko cikin karaji da fadin, "Keje jajjal, da ga yau na baka umarnin, karka sake barin ta-kurya barci lafiya, a zagaye jikinta da kuraje masu warin da babu wanda zai iya rabarta koda danta ne, a dinga firgitata a ido biyu da cikin barcinta".

"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".

Ya fada yana mai zabura a guje kamar iska ya bace bat. Na kusa da shi ta nuna, shima cikin bada umarnin, "Zurnini kaje ga dan da muka samar mata(Shahan-shan 😱), da ga yau karya sake tunani irin na mutane, a maidashi majanuni, yayta dariya da soshe-soshe. Ya tsani shegiyar matarnan tasa fiye da komai a duniya, nanda kwanaki kadan jininsa halattacene garemu".

"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".

Shima ya fada yana bacewa. Ta sake nuna na kusa da shi shima "Rudde! Kaje ga tsohuwar can (Malikat Haseenat 52 ), ka taya Banou aikinta, da ga nan zuwa kwana uku jininta halattacce ne agaremu".

"Fadi naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".

"Zambo kaje ga karsugumar shegiyar yarinyar can,ka zukemin gudan jinin da ke jikinta, ka ringa
firgitamin ita da wajiga rayuwarta, har saita san wacece Uwa kafin masana nayi gareta".

"Fadi naki, Cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".

"Gamberu! Ina bukatar jinin shegun iyayen da suka haifi yarinyar nan da umarnin mu (Wa'iyazubillah)".

"Fad naki, cikawa tawa Uwa magajiyar Uwa".

Wani irin mahaukaciyar dariya ta shiga babbagawa da fadin, "Sai na ga bayansu, sai na haukata rayuwarsu, saina gigitasu. Yanda suka hanamu zama cikin alkaryar kasarmu suma basu isa su rayuwuba. Sai na mulki ruman, sai na mulki duniya, zan zama mafi girma a karfin iko. Matsiyacin tsoho (Kaka) gani nan gareka, nice da kaina zan tsireka a tsakkiyar kasar ruman. Hahahahaha!

Gaba daya na wajen suma suka dauki dariya. Dandanan dajin ya dauki amsa kuwwa. Tako ina dariyarsu amsawa take a cikin dajin..




*****






"Akia, an taba ciwo babu cin abinci, ki daure ko kadan kisha madarar nan sai kisha magani". Jasrah da dawowarta kenan da ga gidansu tun bayan tashi a kotu data tafi sai yanzu take dawowa, ta sanar ma babban yayansu komai yay mata alkawarin zuwa kuma duk da dama Shahan-shan ya tura masa sako, dan yana daya daga cikin mashawartansa ma akan yankema su Miran Jasim hukunci, kasancewarsa babban malami masani. Kai tsaye dakin Malikat Bushirat ta nufi, shine ta iske ta farka. Ganin jikin nata duk babu karfi tai zaman fara bata madara mai dumi akan tasha kafin ta watsa ruwa sai tai sallolin azhar da la'asar da suka wuceta. Amma Malikat Bushirat din taki amsa sam, gaba daya ta gama fita a hayyacinta. Lallashinta Jasrah ta cigaba da yi har ta samu ta dan sha madarar kadan. Magungunan ma da kyar tasha. Mikewa tai zuwa bayi ta hada mata ruwan wanka sannan tazo ta kamata ta kaita. Fitowa tai ta barta da rokon tayi wanka koda ruwanne kawai ta zubama jikinta kozai danyi karfi.


Kamar jira ake Jasrah ta fita aka fara kyalkyala dariya. A firgice ta fara waige-waige sai dai bataga komai ba. Kuka aka fashe dashi kuma. Nama duk ta kidime tuni ta mike zumbur kamar ba itace aka kawo bayin da kyar ba. Sake kwashewa akai da dariya. Sosai jikinta ke wani irin rawar mazari kamar zata amayo zuciyarta ta baki. Tako ina waigawa take amma babu komai sai ita kadai a bayin. Da mugun sassarfa ta nufi kofa da nufin ficewa. Amma ina kofar ta rufe gam-gam babu alamar zata bude, Tanata kiciniyar budewa akai mata wani irin harrrrr!!! Daga jikin kofar sal ga mummunar suffa ta bayyana, baya taja a razane ta kwalla wata irin kara mai tsananin firgitarwa data saka Jasrah dake gyara mata gadon kafin ta fito zabura itama tayo bathroom din a razane….✍️


DAUDAR GORA....!!
Book 2
Chapter: 82

..A guje Jasrah ta fado toilet din da tunanin ko faduwa tayine tunda taga jikinta babu kwari. Wanwar ta sameta a tsakkiyar bayi sume harta farke hannu da wani dan karfe da akaima bayin ado da shi. Ai batama san ta fasa razananninayar kara ba tai kanta itama a kidime. Jijjigata ta shigayi amma babu alamar rai tare da ita. Sai kawai ta sake fashewa da kuka, dan a rayuwa tana matukar kaunar yar uwar tata, itace ta zame mata uwa a lokacin da suka rasa mahaifiya. Ta mata gata irin na Va da uwa bata taba banbantata da dan data haifa ba. Zama ta iya cewa ta fishi samun gata dan shi an dauke sa a gabanta.Itako tunda tasan kanta a gabanta take,duk abinda tace tana so shi take yimata.Idan tashin hankali yay tashin hankali baka tuna-mai ma ya dace kayi, kuka kawai take faman rusawa tama manta a bayi suke.

Diwa da ke tsaye a bakin kofar dauke da kayan lunch da ta kawo ma Malikat Bushirat din ce ALLAH ya jiyar kukan Jasrahn. Dama kuma itace tace ta hado abinci mara nauyi ta biyota da shi. Bata da hurumin shiga dakin sai da izini, ga kuma kukan tashin hankalin da takeji Jasrah nayi. Tray din ta ajiye cikin dan rawar jiki ta fice zuwa sashen Malikat Haseenat. Suna zaune a falo Daneen Ammarah na faman lallaba Ummu ta sake kwana itako ta ce yau sai gida zataje suyi shirin tarbar amarya gobe insha ALLAHU sai ga Diwa ta shigo a firgice. Kallon mamaki gaba daya suka bita dashi, Daneen Waheeda Sarkin masifa ta daka mata tsawa dan abinda Diwar tayi babban tsaurin ido ne. Malikat Haseenat ce ta katseta da fadin, "'a Waheeda wannan ba dai lafiya ba bita a hankali. K! Miya faru ne?". Kuka Diwa ta fashe da shi tana nuna bayanta bayan ta zube a kasa. "Ku gafarceni ranki ya dade, babu lafiya ne gaskiya. Ga Aunty Jasrah can nata kuka a dakin Malikat, da alama akwai matsala ne why, tabbas akwai matsala, dan dama likita nata zaryar dubata tsakanin jiya da yau"

Babu wanda gabansa bai fadiba
a cikinsu, dan dama basu jima dayin maganar rashin ganinta a kotu ba. Daneen Waheeda ce make cewa kila bata da ra'ayin zuwan ne yau tunda sun san halinta. Gudun kar maganar tai tsaho ga Ummu da take bakuwa a tare da su yasa Daneen Ammarah kauda zancen ta dako wani.



Gaba dayansu suka kunduma sashen Malikat Bushirat, Ummu kawai aka bari. A gaban idon Banou da ke tsaye da wata bakuwar fuska a jikin fulawoyi suka wuce.Da wani mummunan kallo suka bisu, sai dai babu wanda yace komai. Su Malikat Haseenat da basu san sunayi ba ko mota suka shiga zuwa sashen Malikat Bushirat din. Sun sami Hadiman sashen Jigum-jigum, dan zuwa yanzu kusan duk sunji irin kukan da Jasrahn keyi. Babu wanda ya saurari gaisuwar hadiman sukai ciki da hanzari, dan suma dai suna shigowa da kukan Jasrahn suka fara cin karo. A bathroom din suka sameta har yanzu, da kyar Daneen Ammarah ta dagata, rungumeta tai cikin jikinta dan ta sami nutsuwa, Malikat Haseenat kuwa inda Malikat Bushirat ke kwance wanwar ta nufa, tattabata ta shigayi. Daneen Waheeda dai na tsaye babu alamar damuwa tattare da ita. Sai ma bin toilet din take da kallo baki a labe. Da kyar Daneen Ammarah ta lallashi Jasrah har ta dan musu bayani a takaice. Dole aka kara kiran Doctor sannan aka saka hadimai shigowa suka kakkamata aka fiddota aka kwantar saman gado.

Zuwan doctor ya tabbatar musu ba mutuwa tai ba, ta dai suma ne. Ajiyar zuciya suka dinga saukewa, shi kuma ya shiga kokarin ganin ta farfado, yayinda Malikat Haseenat ke faman tofa mata addu'oi. Wani irin numfashi ta kawo tare da zabura mai karfi, wadda har doctor dole ya kai hannu a kanta domin maidata amma ya gagara shi kadai. Dole Jasrah da Daneen Ammarah suka matso domin taimaka masa. Amma fa sun kasa dan wani karfi na masifa ta musu, ga fisge-fisge tanayi na tashin hankali.

(Tofa al'amarin fa babbane) cewar Daneen Waheeda a cikin zuciya tana dan tabe baki. Suko da basu san tanayi ba sunata kici-kicin son gain ta lafa, Malikat Haseenat kuma na tofa mata addu'a. Da kyar suka iya tankwarata, har sun hada zufa sharban kamar yanda itama tayi.Numfashi suka shiga saukewa na jigata. Doctor kuma ya shiga aikinsa. ya sake maidata barci sai dai fa barcin yaki yiwuwa. Dan da ya dan figeta sai ta zabura sai sun sake dannata ta
koma kwance. Al'amari fa tun anayi da marmari harya fara gundurar kowa aka karo doctors da was alluran masu karfi sosai da sukafi na farko da akai mata..


Cikin kankanin lokaci zancen rashin lafiyar ya zagaye masarautar. Masu tausaya mata nayi masu farin ciki nayi. Masu kuma fassara al'amarin da wani abu daban nayi. Dan danan labarin ciwon nata ya zama latest topic à cikin masarautar. Dama ga nã hukuncin su Miran Jasim da bai gama disashewa ba.




***





Duk wanna al'amarin Iffah nacan kwance tana shan barcinta bata san bikin da ake ba. Dan sai la'asar ta tashi. Wanka tai tayi salla. Bayan ta kammala kimtsawa ta fito neman abinci dan yunwa takeji. Hadimanta da ke dan kus-kus din su suma akan al'amurin Malikat Bushirat din sukai saurin mikewa. Kallo daya ta musu ta dauke kanta, dan har yanzu zuciyarta babu dadi. Zama tai tare da bada umarnin a kawo mata abinci anan. Cikin ko kankanin lokaci amintacciyarta ta jere komai. Ta bude zata zuba mata ta dakatar da ita idanunta kur akan abincin. "Waya dafa wannan abincin?"Ta fada tana kallonsu. Cikin rawar jiki amintacciyar tata ta sanar mata itace da mai girki. Ta nuna mai abincin. Shiru Iffah tana duban wadda aka nuna matan sai faman sinkuy da kai take. Ai bama tasan ta daka mata tsawa ba tace ta dago. Ba ita da taima tsawar ba hatta sauran hadiman sun matukar razana. Dan abu ne da bata taba musu ba. Wani irin kallo Iffah take ma matar rai bace. Jikinta har tsuma yake ga idanunta sunyi jazur na tashin hankali. Duk wanda ya dubeta sai ya razana, idan ma irin su Bily ne fitsari zamu saki a zani😝Dan gaba daya ta juye tabbacin ba Iffah bace.

Wani irin shakota Iffahir tayi ta dauke ta da bahagon marin da ya idasa tsurar da sauran hadiman jikunansu suka fara rawar mazari. Marin matar nan Iffah take tamkar ALLAH ya aikota. Gashi ta shaketa da iya karfi. "Ubanwa ya aikoki nan?". Ta fada da wata irin gigitacciyar murya mai matukar razanarwa da amsa kuwwa. Cikin kakarin azaba matar da gaba daya ta gama jiyo kamshin mutuwa da kyar ta ce, "Uwa."

"Uwa. uwa. Iffah ta fada kamar mai bitar sunan, sai kuma ta kyalkyale da dariya ta kuma hade fuska. Cikin dage gira da zuba jajayen idanunta a tsakiyar na matar da ke a shake har yanzu a hanunta ta ce, "Ohhhyyyyo ita bata gane karatun kurma kenan. Bakuma ta gane gargadin makawo sai ya doka sandarsa. Shin wai dolene sai ta fusatani ne?!!!!!. Nace sai ta ga ainahina sannan zata tabbatar nafi Karfinta?!!". Ta sake fada cikin karaji tana gwara kan matar da centre table. Wata iriyar wahalalliyar kara ta sake illahirin jikinta na rawa dan fa ta bugu matuka duk da katako ne. Tuni hadiman sun fara sakin fitsari a wandunansu. Yayinda Iffah da bata san sunayi ba tana cigaba da maka kan matar nan jikin centre table. Sai da tai mata ligi-ligi har numfashinta na fita da kyar ga jini yay mata faca-faca sannan ta dagata tsaye, cikin daka tsawa ta dubi amintacciyarta tace a kira mata Ghazi guda biyu. Cikin kankanin lokaci suka iso kuwa. Jefa musu matar tayi taki zube yaraf a gabansu. Rai bace ta ce, "Ku dauketa, a dauremin ita a tsakkiyar masarautar nan". Cikin rawar jiki suka amsa mata da "Umarninki shine abin jiranmu ranki ya dade". Kota kansu batabi ba ta nufi dining, wajen wanke hannu ta nufa ta wanke hanunta da jini ya dan bata, har yanzu a birkicenta take. Bedroom dinta ta koma, babu jimawa ta sake fitowa cikin sabuwar shiga. Har yanzu hadimanta na lafe jikin bango a tsorace. "Ku biyoni da wannan abincin". A zabure duk suka mike, Itako tuni ta ma fice abinta. Kamar yanda ta saba tafiya duk inda take so a kafa yanzun ma hakane. Sai dai yau ko sau daya bata kula gaisuwar kowanne hadimi ba. Koma kallo basu isheta ba har ta isa sashen Malikat Haseenat. Anan din ma babu hadimin data kula Sai dai tana binsu da kallo daya bayan daya. Ganin babu wadda take nema cikin wata irin razananninayar murya ta kwala
kiran sunan "Banouuuu!!!"

Ba Banou din da taima kiran mafarautan ba, hatta Ummu da Iftihal a dari suka fito, hakama duk wani hadimi dake sashen dama wanda basu san da zuwanta ba har tuntube suke wajen fitowa. Banou da jikinta ke wani kakkarwa ta zube a gabanta, wani irin mari ta kai mata itama tare da shakota ta mikar da ita tsaye. Cikin murya mai razanarwa ta furta, "Ina bakuwar takini?!!!!"

Ba Banou din kawai ba, kowa ma a wajen jikinsa rawa yake yi, hatta Ummu data raineta yau ji tai Iffahn na bata toro. Iftihal kam ai tuni ta jike dogon wandon jeans din jikinta da fitsari, jikinta ko tsabar rawa da yake tuni har wayarta taje kasa bata sani ba

Banou dake watsal-watsal din kakarin mutuwa ta nuna matar da suke tare dazun lokacin da su Malikat Haseenat ke fita zuwa sashen Malikat Bushirat. Sakin Banou din tai, sai gata a kasa rikica. Tako kwalla karar azaba. Da hannu taima waccan nuni da tazo. Zatai mata wani noke-noke tai wani irin fisgota ta buga da bango. Gaba daya falon ya sake ridewa, Iftihal ta shige jikin Ummu ta fashe da kuka. Cikin karaji Iffah ta ce, "Ku nawa ne?!!". Jikin matar na rawa ta ce, "Karki kasheni, nayi alkawarin zan fada miki duk abinda kike bukata, na rokeki.

'"'Na ce dan uban ubanka ku nawa ne?!!".

"Mummu biyar ne?"

"Kai mi aka aikoka yi? Da har ka koma suffar mata?"

"'Z.z zan taimakawa Banou ne mu karasa uwar masu gida, d. d. Dan ta dade anan din tare da ita…✍️


DAUDAR GORA....!!
Book2
Chapter: 83


…Babu wanda bai zaro ido ba a falon. Cikin bacin rai Iffah ta ce, "Na fika sanin wannan"Jikin matar na rawa ta cigaba da zayyano mata sauran. Yayinda tuni Ummu dake rude Iftihal mamuke da ita ta yunkura da niyyar zuwa ta nemi Kaka a waya, dan dazun da sukazo sun kawo mata wayarta shima Babiy yana amfani da nashi. Kin sakinta Iftihal tayi, dole sai tare suka tafi. Iffah kam juyawa tai ta dubi hadimanta da ke dauke da abincin data bada umarnin a biyota da shi, ta nuna na hannun amintacciyarta. "Ajiye musu shi suci"

Da ga Banou har abokiyar aikin nata kuka suka sanya, dan su suka san abinda suka gani a abincin. Ko kallo basu ishi Iffar ba, tana tsaye a kansu fuskarta kawai abar firgitarwa ce. Haka suka fara cin suna kuka da rokon tayi hakuri, a haka su Malikat Haseenat da akeje aka sanarmawa suka shigo hankali tashe. Dan can sun samu Malikat Bushirat tayi barcin da kyar bayan an rufu kanta da addu'oi. Kallon Iffah da su Banou din kawai suka tsaya yi cirko-cirko. Daneen Waheeda kam tuni ta koma bayan Mammah ta makale, yayinda Daneen Ammarah itama nata kamanin suka fara canjawa dan idanunta sun kada sunyi jazur. Ture abincin Iffah tai da ga gabansu, ta wani irin hankada Banou gaban Malikat Haseenat. "Jeki sakar mata kafafu!!". Cikin madaukakin mamaki Malikat Haseenat ke duban Banou da Iffah. Sai dai razananniyar tsawar da Iffahr taima Banou din ita kanta sai da zuciyarta ta shiga tsitstsinkewa. Banou dake kuka cikin rawar jiki ta kama kafafun Malikat Haseenat, wani fushin kumburi da kafafun sukai tsahon shekaru an kasa gane kansa sai gashi yau yana bajewa, Kusan minti biyu tace mata ta mike, mikewar tai jikinta sai kakkarwa yake, du da girman jikin nan nata ga tsaho amma Iffah dake yar digila gabanta ta zame mata dodo. "Na baki minti hudu, ki dakko tukunyar da kika ajiye a cikin flowers".

"Umarninki shine abin jirana ranki ya dade".

Banou din ta fada cikin sake gurfana. Suna tsaitsaye har yanzu babu wanda ya iya cewa komai sai ga Banou ta dawo da tukunyarta, A gaban Iffah ta zube, ta bude tukunyar ta shiga fiddo abubuwan da ke ciki. Abinne kamar tsokar nama, duk ta daure. Kwancewa ta shigayi tana sakinsu, firrrr suke tashi kamar tsuntsaye, wasu ko da kyar zakiga sun tashin saboda ta jima tana wahalar da su. Cikin
bada umarni ta dubi sauran hadiman ta ce, "Aje a duba duk wanda yake a halin ciwo ya mike a yanzu a kaimun shi tsakkiyar masarautar nan. Ina bukatar Ghazi guda biyu anan".

Cikin kankanin lokaci Ghazin data bukata suka shigo, su tasa suka tasa mata keyar su Banou.




*Tun fito da Hadimar da ta jibga a sashenta al'amarin ya fara zagaye masarautar. Abin mamaki sanda take fitowa su Malikat Haseenat biye da ita masarautar ta gama cika. Dan sashe-sashe an fito kamar busar kaho. Cikin kankanin lokaci duk wani mara lafiya dake gidan aka fito da shi, harma wanda ba Banou din ce ta tabasu ba. Tana kuka da faman rufe fuska ta tsatstsallakasu. Tana gamawa suma sawa tai aka daure mata su tare data farkon. Dai-dai nan su Baby suke isowa cikin masarautar. Hakama Tajwar Eshaan a rikice Malikat Haseenat tai kiransa ta sanar masa babufa lafiya a gidan da ya kamata ya
fito. Dama shirin fitowa yake, dan amintaccensa yazo masa a kidime babu dadewar nan, hakama Sayeed Fayzul-haq ya kirasa shima.


Lokaci daya wajen ya dauki shiru sakamakon fitowar tasa, dan abunne da babu wanda yay zato. Kowa a wajen sai da yay kasa da kansa har Iffah, dan a zahirinsa yake kyakykyawar fuskar nan a bayyane, sai dai fa cinkus take babu alamar wasa ko sassauci. Amintaccensa ya ajiye wata yar kujera mai kyau dake a ninke aka budeta. Sai kuma katuwar umbrella da aka bude masa duk da bawani ranar nada zafi bane dan ta la'asar ce ma dake neman faduwa. Sai dai kuma a mamakin kowa ma bai zauna ba. Sai duban Iffah da yay na kusan mintuna biyu. A hankali ya furta, "Mike faruwa". Cike da irin girmamawar dake nuni da ba ita bace ba ta kai kasa gurfane gabansa. Gaisuwa ta fara mikawa,kafin dukkan abinda ke faruwa ta zayyane masa. Idanu ya dan lumshe da sake budewa. Kamar bazaice komai ba sai kuma yay mata nuni da ta tashi, tare da fadin,"Duk da ba itace a tare da gangar jikinta ba kuskurene kai Zawjata-almilk kuma * Malikat * kasa a kowane irin yanayi a gaban al'ummar kasar ta"

Wanna furici nasa ne yasa kowa fahimtar ba ainahin Iffah'r bace iskokinta ne yau suka bayyana kansu abinda basu taba yi ba, sannan kuma maganar cikin jikinta tabbataccene tunda har shi da kansa ya kirata (MALIKAT). Neman afuwa suka shiga yi, da tsayawa tsaye akan kafafun Iffah'r. Alokacinne Sayeed Fayzul-haq ya yafito Kaka dake tsaye kawai yana murmushi. Sai da ya fara mika qaisuwa ga Shahan-shan shima sannan ya duba Iffah, kamar yanda sukaima Tajwar Eshaan bayani haka shima kakan sukai masa. Kansa kawai ya jinjina da cire jakar hannunsa ya ajiye. Ruwa ya bukata, cikin kankanin lokaci aka kawo masa. Magunguna ya fiddo da yawa ya shiga zubawa a ruwan nan. Wani irin ihu su Banou suka dingayi da rokon yayi hakuri, bama su ishesa kallo ba ya fara dibar ruwan maganin yana watsa musu. Ihu na gaske suka dinga kwallawa da surutai suna girgiza da gunji. Sai da yay musu ligif sannan ya basu umarnin bayani da bakunansu. Biyun sun tabbatar da su ba mutane bane sun rikidane kawai. Kuma a yau din nan suka shigo cikin masarautar bisa umarnin uwa da Iffah ta raunata a dazun. Banou kam mutum ce ita, sai dai akwai aljanun maita tare da ita, irin kusan duk zuri'arsu ke da shi, dan itama cikin zuri'ar uwa take. Cikin galabaita ta shiga fadin tun sanda take tare da su.

"Ni shekarata goma sha tara anan, tun bayan korar uwa da akayi da ga wannan masarauta. Ina daya daga cikin zuriarta da aka kora shekaru masu yawa da ga cikin wannan alkaryar, a da kakanninmu wannan filin masarautar shine garinsu. Amma sanda za'a kafata sai aka tashesu aka canja musu waje. Ransu ya baci matuka da wannan al'amari, dan tunda suka taso anan suka samu iyayensu da kakanni suma, nan kadai suka sani matsayin kasarsu kuma gari, ga abubuwan bautarsu masu tsahon tarihi tsahon shekaru duk an ruguza musu. Dan haka sukaji zafin tashinsu da akai da bata musu wajen bauta da abubuwan bautarsu saboda gina masarauta bayan akwai filaye da yawa da babu kowa a cikinsu miyasa baza ai acan ba. Wannan haushin yasa sukaki zama inda aka basu sukai hijira zuwa cikin jeji. A haka suka cigaba da sabuwar rayuwarsu wadda da kyar suka saba da wajen, sai ya zam duk wanda aka haifa a cikin zuri'ar mu wannan
shine labarin da za'a raineka a kansa, da kuma kiyayyar wannan gida. A haka duk muka rayu da burin daukar fansa. Mun dade da shiga jikinku muna muku illa da suffar bokanci, hatta lokacin da kuka samu ambaliyar ruwa a kusan kasar baki daya zuri 'armu ne suka balle wani yanki na kogin da ke zagaye da ku. Mu bamu taba jingina da ku domin mu taimakeku ba sai dan mu ruguzaku, a haka iyayenmu da kakanninmu suka dinga shudewa. Uwa ta kasance mafi girman hatsabibanci da yin tasiri a al'amuranku a cikin duk wanda suka zo da nufin masu taimako a gareku a cikinmu. Duk da dai akaf zuri'armu daga maye sai matsafi, kuma kowannenmu nada abinda yake yi domin ku. Jajircewar uwa da zamowarta mafi iyawa a kan iyawar kowa cikinmu yasa ta zama shugaba a garemu, kuma ita muke fata da gain ta

Please Login or Register in order to submit comment