Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

share gidan nan ba kitchen ma gashi nan kaca kaca..dakin duk wari yake


wallahi Allah bani na ɓata kitchen ba su Maryam ne da sara suka dafa mana indomi zancen kuma kace daki na wari to ai da sauki tun da bani nake ba dazu da safe na saka turaren wuta


Rufaida ta faɗa tana ɗaga hammatar ta tana shin shi nawa..


wata kan idan kana da rai zaka sha kallo bin ta yayi da ido ya ma kasa magana dole ya nema wa kansa mafita yace


'' kafin na dawo wallahi Allah ki gyara gun nan idan kuma ba haka ba zaki ga abin da zai faru..,


zama tayi a kan gado tana cire daurin ta ashe a jiyan hular gashi ta saka tamanta da yanzu ma bata saka ba ta ture daurin kanta sai gashi yan mutsi mutsin kalba irin wacce ake wa yara da sabulu ta fito kasa tantance me yake gani, kamar fa kan jariri yake gani jar uban can haka ya ambata a zuciyar sa zuciya da hange hange sai ta hango mai dazu lokacin da suke tara da nasreen a lambo da sauri ya kawar da tunanin nan daman ya dade da shafe wannan babun a ransa duk da shi kansa yasan karya yake wa kansa ba zai iya ba..,


afusa ce ya fice domin a halin da yake ciki idan yayi magana to kalma mara dadi ce zata fito daga bakin sa da harara ta bi bayansa da ita sai a lokacin ta lura da kanta tsaki ta ja tace


'' koma mene ai an riga da an daura kome zai biyu da baya me sauki ne..,


kwanciya tayi a binta a nan bacci ya ɗauke ta tayi rashi rashe bakin nan a buɗe miyun bacci na zuba har akai sallar isha tana wannan baccin na asara kamar da ga sama taji an buga mata pillow a gigice ta tashi tana zab ga ihu ganin shi ne ta mustsuka idanuwanta tace


'' kai innalillahi ashe daman haka auren sojan yake haba altab abin da kake ba baya kyautawa ka dena cin zali wallahi..,


wata uwar harara ya gallamata yace


'' idan na rantsai bazan yi kaffara ba akai magariba kina kwance akai isha kina kwance duk baki tashi kin yi ba sannan aikin da nasaka ki baki ba...,


wani uban salati ta saki tana tashi tace


'' haba sweet na ga addinin nan dan sauki ne dan girman Allah idan kai kake amsar sallar nan idan nayi dawo min da a bata naga tun da kata shi da safe baka irin tarairaye ni ba haka kayi sauri ka tafi kayi sallar asuba sai wani cewa kayi,


beb tashi kiyi wanka kiyi sallah tsakani da Allah ya dace ban taɓa shan azaba irin ta yau ba kuma da ace mazan waje ne har toilet suke raka mace


da sauri ya kalleta yace


'' ke ina kika san ana yin haka..,


da sauri ta rufe bakin ta tace


'' kar ka ne mi ga zarge ni nima faɗa min ake yadda yake yi shi ya saka na kwanta ina jiran ka dawo to shiru shiru baka dawo ba kuma ga yanayin sanyi na shigowa garin nan gudun mura sai kawai nayi kwaskwarima idan rana ta danyi na yi wanka na haɗa sallar nayi to da rana tayi na duba zan kunna heater switch din yaƙi kunnuwa kawai sai na hakura idan ka dawo ka haɗa min ruwan wankan nayi


tamkar wani mata laka haka ya zauna dafe da kai yace


'' yanzu dai asuba ahazar la'asar magariba isha duk baki ba..?,


cikin da confidence ta ɗaga mai kai domin ita bata ga abin laifi ba addnin nan dan sauki ne kuma Ubangiji yaga zuciyar ta


tsawa ya daka mata da sauri ta takure guri ɗaya tana zare idanuwa yace


'' wallahi rana ɗaya nasan na gamu da ƙaddara domin ke wallahi kaddara ce da ranki da lafiyar ki har ki dinga haɗa sallar saboda baki da tunani wallahi idan zaki ci gaba da haka wata ran bazan san lokacin da zan karkaryaki ba kin san kuwa mece sallah kinsan kuwa wanne mahimmanci Ubangiji ya bata...itace fa marabar arne da musulmi sannan kuma itace idan mutum ya tsayar da ita zata zo ta dinga tash zaman kabari..,


zunburo baki tayi ta tashi tana karka da mai zani ta shiga toilet fita yayi dakinsa ya kwanta wayarsa ya ɗago duk ƙarfin zuciya irin tasa a yanzu zuciyar sa tayi rauni yasan ba zai taɓa samun muradin sa limshe ido yayi ya buɗe a lokaci ɗaya ka ƙurawa screen din wayar sa ido itama kamar shi din take kallo ajiye wayar yayi..


ya kurawa suspender ido yawa me shirin gano wani abu idan ya furta zai zama barazana da farin cikin wasu har da nasa idan ya furta yasan baƙin cikin da mahaifiyar sa zata shiga ba ƙarami bane gwara ya bar shi a ransa idan ya mutu ajalinsa ne wayar sace tayi ringing da sauri ya ɗaga ganin me kiran cikin girmamawa ya yi mai sallama tare da gaishe shi


amsawa me kiran yayi yace


'' ya kowa da kowa dafatan kowa yana lafiya..?,


Altab yace


'' lafiya qalau alhamdulilah ya su ni'ima..?,


Suna lafiya qalau alhamdulilah kowa lafiya dan Allah ka ƙara riƙe min amanata ina gab da dawowa


tashi zaune yayi yace


'' Allah ya dawo da kai lafiya...insha Allahu baka da wata matsala.,


godiya yayi mai sukai sallama ya kashe wayar sa


_______________ BOMPAI




jazz ka tabbatar wannan zancen gaskiya kake faɗa min cewar nasreen da ta dora kafa ɗaya kan ɗaya acikin mota shi kuma jazz yana tsaye da kan sa yawa abarba saboda tara gashin da ya yi yayi tsaibebe a ka yace


'' na taɓa kawo miki rawo tan karya ne..?, da kunnuwana naji suna maganar..,


cije lips dinta tayi ta duki staring wheel tace


'' kasan me jazz wallahi tara matar nan nake akwai ranar da zan kamata naci ubanta..,


Sai wacce rana kenan kawao hajiya ta ki baza yanayin ki kema


ɗagowa tayi tace


'' ban gane ba nayi mai kaga duk wata harkar haram kai ne a sahun gaba nidai barni a nan rabon bawa da arziki mutuwa baruna yanzu ba wannan ce a gabana ba da sauri ta ɗago jin karar parking din mota baffa ne driver sa ya fito ta buɗe mai idanuwansa ne lokaci ɗaya suka canza launi tun daga sama har ƙasa ya kalli...


jazz shi kansa wandon sa yawa an kwato shi daga bakin kura ga wani Ban zan aski sai kace kan abarba kai ya jin jina ya wuce a yau zai zartar da hukunci ko ya yiwa kowa dad'i ko karya yiwa amma dole ya ɗauki mataki akan yarinyar nan tun kafin ta fara ajiye musu shegu a gida..


idan na waje yaƙi zama da ita dole ya tursasa wanda yake ganin ko bayan ransa ba zai iya hufuntar da ita ba wanda zai tsaya tsayin daka gurin tarbiyyar ta ta dawo yadda take a baya kafin ta haɗu da shedanun mutane wayar sa ciro bugu ɗaya aka dauka cikin girmamawa alhaji Usman yake kokarin gaishe shi katsai shi yayi yace


'' ka buwa yan uwanka su duk inda suke suzo ina son ganin ku...,


yana kaiwa wannan be jira me zai ce ba ya katsai wayar kafin kace mai kowa ya hallara gyara zama yayi sannan ya karato addu'ar buɗe taro yace


'' ba komai ne yasa ka na tara ku ba sai akan dalili Babba na lura ina gab da shiga cikin wani yanayi da al'ummar gari zasu fara zagina na gama hukunta masu laifi amma me laifi dake rayuwa a cikin gidana na kasa wani ɗaukan mataki akan abin da ke faruwa bayan dogon nazari da nayi yau kuma idanuwana sun gane min abin da ya kamata tun farko na yiwa tubkar hanci duk masu gadin gidan nan da security din dake cikin gidan nan da raina da lafiya ta a matsayina na babban alkali wanda ya rike mukamai da dama ni za a dinga tara yan iska a cikin gida to yau zan zartar da hukunci duk wanda yaga an mai rashin adalci ba haka naso ba amma ba yarda zanyi da nayi fushi sai kuma na gane hannunka baya taɓa rubewa ka yanke ka yar


gyatsuna fuska Hajiya tayi duk wannan kwana kwanar ya fito fili ya fada musu me ke faruwa amma sai zance yake cikin zance kallon ta mamy tayi tayi ƙasa da murya tace


'' yaya me kika fahimta a cikin wannan zancen na tsoho..?,


kallon ta tayi ta take mata kafa tace '' sai an lura damu koma mene ai zai fada...,


dan jim baffa yayi ya kalli altab yace


'' jeka ka kirawo min wannan yarinyar Khadijah..,


tashi altab yayi da sauri ya fita har yanzu tana inda take kallon ta yayi yace


'' baffa yace ki zo...,


fitowa tayi daga motar jazz tana cewa hukuma tayi kira muyi magana ta waya


okay ni yanzu akwai inda zani komin dare dai ki bar wayar ki a kunne


Okay ba damuwa ta faɗa tana bin bayan altab har suka isa parlour cire takalminta tayi ta shiga zama tayi ba tare da ta kalli kowa ba tace


'' baffa gani..,


wani kallo yayi mata sannan yace


'' KHADIJATOU ABDULRASHEED HUSSAIN MAI TANGARAN.. wannan sunan shi kike amsa wa ko..?,


kai ta ɗaga mai mayafinta ya cire yar stair din dake huyanta ya gani ta tattoo ya girgiza kai yace


'' dabi'un ki da halayyar ki sunyi kama da ta musulmin kwarai..,


da sauri ta kallesa baza ta iya ci gaba da kallon cikin idanuwansa ba maida kallon tayi kan hannayen ta da jiya taje ta cire farcen hannunta tattoo ne kawai a jikinta kasa magana tayi,


murmushi takaici yayi tace


'' ke kanki kinsa gaskiya jibi wuyan ki kamar ba yar musulma ba kai Khalil..,


da sauri yace


'' na'am baffa..,


Na baka nasreen a yau zan daura muku aure ka amince


kai khalil ya ɗaga alamar eh


da sauri ta ɗago altab ya dago zuciyar sa na tafasa Abba kuwa yace


'' gaskiya baffa ban amince ba wata kila ba za a rasa ta da cutar kanjamau ba haka kurum na rasa ɗana altab ne ya ɗago be yi zaton haka daga gurin Abba ba ya buda baki yace.....


turƙashi me hakan ke nufi me altab zai ce tab da sauran rina akaba wacce nasreen wane zai aure ta saboda duk mazan da yayi yunkurin aurenta sai a fasa wai shin ina mahaifinta


ɓangaren mazan gidan har guda uku ko wannensu akwai kudirin sa akan ta shin idan altab yace shi yaji ya gani rufaida fa ita zata ji ta gani yanzu auren ma kuwa zai yiwu...?,


domin jin wannan amsosin wa'yannan tambayar ku biyo ni a littafi na gama book 2,3,4,5


duk akan farashi me sauki 500


Idan na gama ya zama 1000


Alhamdulilah Allah nayi maka godiya da ka bani ikon gaba book 1 lafiya kamar yadda na gama lafiya Allah ka bani ikon gamawa sauran lafiya.


ni fatahiyya Muhammad yakasai (oumyasmeen) nake cewa ku huta lafiya


kar ku manta masu son a tallata musu hajojin su kofa a buɗe take muyi magana ta wannan number 09061890481 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment