Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ

Telegram : https://t.me/NovelsHQ

✨✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨✨


*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA* *ADAM IDRIS*
( _Shalelen_ _kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN MAHAIFANA👩‍❤️‍👨*


*AND NOW*

✨✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abunda zai amfani Alummar musulmai.



*Sadaukarwa*


Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu idris* Allah kara lafiya da nisan kwana
Amin.


_2nd January 2021_


1~2


Kano ta dabo tumbin giwa ko da mai kazo an fika gari mai tarin albarka tu mai dala da goron dutse.



Unguwar dorayi wasu Yan Mata ne gudu biyu su na tafe su na hira dayar ta dubi yar uwarta ta ce “khadeejatu wallahi yanayin sanyi nan da karfin shi ya shigo wanna karan , muyi sauri muje mu yiwa Umma cefa nen nan, yau mu je islamiya da wuri.



Wanda aka Kira da Khadeejatu ta dan harare ta tayi murmushi ta ce “Ai Hafsa ke kike makarar da mu a sanyin na a zane mu su ma malaman sam ba imani".



Haka suka karasa gurin mai kayan miyar yana ganin su ya washe hakora ya ce “Yan biyu kune a tafe".



Hafsa mutuniyar shi ta ce
“Malam Sabo kayan miya na dari biyu zaka ba mu"



Malam Sabo ya ce “to h
Hafsatutu matar mai shayi” ya karasa cikin dariya.



Hade rai ta yi Khadeejatu ta yi mumushi tana tafa hannu ta ce “Yau dai munji kan ku" ta kalli Hafsa ta sheke da dariya.



Hafsa ta chuno baki gaba.



Malam Sabo yayi dariya ya kalli Hafsa ya ce “Rabu da ita kinji bari in zuba maki "




Ya na gama zuba masu Hafsa ta ce “Malam sabo wannan yar Albasar zaka zuba Mana?"



Malam sabo ya Kama ha'ba ya ce “Ai Hafsatu haka ma dan ku ne na kyauta ma ku ai albasa ta zama yar sarki"



Khadeejatu ta ce “Allah dai ya kyauta" ta karba kayan miyar su ka tafi.



Su na zuwa daidai kofar gidan su Khadeejatu, Khadeejatu ta sa dariya ta ce “Hafsatutu matar mai shayi" ta shige gida a guje.



A zuciye hafsa ta ma ra mata baya Umma da ke wanke shinkafa taji garaf a banko kofa da sauri ta dago ta na dafe kirji.



Da sauri khadeejatu ta banka kofar dakin Umma Hafsa ta bi ta.



Wata sanyayyar Ajiyar zuciya Umma tayi ta ce “wallahi yaran nan sai ku sawa mutane ciwon zuciya kuna girma ko waccen ku ta yi 16 in a kauye ne da tuni an aurar daku kuma tsaff za ku zauna........."



____________



”Hajiya Zainab matar Dr Nuraddeen na ga Kira da sassafe na ce ko lafiya?" cewar Safiyya cikin damuwa Zainab ta kalleta ta ce “ba dole ba Safiyya kinsan matsala ta Nura ne duk ya wa ni chanja mun ko lallabani ba yayi nace ya samon yar aiki yaki
ni gani ma nake ko wanchar banza uwar nan ta sa ce take sa shi".



Safiyya ta kalli Zainab ta ce “ A kan wannan ne duk kika tayar da hankalin ki ?"



Zainab ta ce “ba dole in tada hankali na ba" da sauri Safiyya ta ce “kima kwantar da hankalinki ai muna da mafuta yadda har hanashi zuwa gurin uwarshi zaki iya"



Mamaki dauke a fuskar Zainab ta ce “ta yaya za'ayi haka Safiyya? "



Da murmushi dauke a fuskar ta ce “ta hanyar zuwa gurin boka mana"cewar Safiyya.



Zare ido Zainab tayi ta ce “boka fa ki ka ce gaskiya ni bazan iya ".



Safiyya ta hade rai ta ce “to wallahi nake fada ma ki kina zaune sai dai kiji ana gwuda uwar shi ta aura mashi wata matar kina nan zaune ni shiyasa sam bazan auri wanda uwarshi take raye ba kuma kiji ni da kyau karki sa ke kirana akan wata mstsalar ki" ta mike tare da daukar Jakarta.



Ta mike zata futa ko mai Zainab ta yi tunani da sauri ta ruko mayafin Safiyya tana fadin “Ba za'ayi haka ba kawalli wallahi na amince"



Juyowa Safiyya ta koma ta zauna murmushi tayi ta ce “ko kefa yanxu yaushe kike so muje ?"



Cikin zumudi Zainab ta ce “ni ai ko yanzu ki ka ce muje a shirye na ke".


Safiyya ta ce “kin tabbata kuwa?"


Da sauri Zainab ta ce sosai Safiyya ta ce ”okay kina da kudi?"



Zainab ta ce “ina dashi mana ko bani dashi ai na karba gurin honey ".



Safiyya ta ce “To baki da matsala gobe kamar yanzu zanzo muje gurin bokan" hira suka cigaba da yi.


*WASHEGARI*


Wai ke Zainab meye haka ne ko sallah kin ki tashi kiyi yanzu zan futa office ba ki mun breakfast ba ?"



“Tun bayan Auren mu kika wani chanja kai ka ce ba auren soyayya mukayi ba na kiyayyya ne".


Bude idon ta tayi ta kalleshi ta ce “kaga malam in zaka wuce gurin aikin ka da ya fi ma ka kuma sallar kai zan yiwa? da za ka ishe ni".


Briefcase dinshi ya dauka ya na fadin “Allah ya kyauta" ya sa kanshi ya fice .


Da harara ta rakashi taja bargo ta rufe fuskarta ta cigaba da baccinta.



Shi ko Nura ya na tafe a hanya ya na mamakin Zainab da ta chanja halayyarta tun bayan aurensu da wata biyu ta sauya.



*Da dadddare*


Nura ne ya kalli kanwarshi Maryam ya ce ”Maryam dan zubo mun abinci "



Dagowa tayi ta kalle shi ta ce “to Yaya" kana ta nufi kitchen din.



Sai da Mama ta ga ta shige kitchen din sannan ta mai da kallonta gurin Nura tsaff ta kare mashi kallon ta ce “Nura"



Da sauri ya ce “Naam" ya na ajiye wayar hannunshi dan yadda yaji ta kira sunanshi yasan ba wasa.



Gyara zama tayi ta ce “Wai Nura ina matarka ne da kullum sai kazo nan kaci abincin ita mai yasa bata dafawa ne ?ko meye kuma?


Shafa kanshi yayi ya sunkuyar da kanshi kana ya ce “Dama tace na nemo mata yar aiki nace ni banason yar aiki shine kuwa tace to ita ba baiwa ce ba da zata na wahalar gida ga girki" sai kuma yayi shiru....


Mama ta ringa jinjina maganganun a ranta ta ce “Ba matsala zanga ya za'ayi karka damu".



Maryam ce ta karaso ta ajiye mashi abincin akan stool a gabashi ta ce “Yaya ga Abincin ".


Murmushi yayi ya shafa kanta ya ce “Nagode little sisi Allah nuna mun auren ki".


Da sauri ta rufe fuskarta tana dariya .


Murmushi yayi ya fara cin abincin sai da yayi nak sannan ya wuce gida.


___________


Yau ma asual bai yi breakfast ba haka zai wuce hospital gashi emergency ake nai man shi.


Garage ya nufa ya shiga motarshi ya murza mata key kana ya ba ta wuta mai gadi ya bude mashi gate ya fice.



Ai ya na ficewa Zainab ta mike ta shiga wanka da sauri sauri ta shirya.



Wayarta da kudade ta dauka ta sa a jaka ta yafa wani yalolon gyale.



Ta na futowa falo sai ga Safiyya ta shigo kyalkyalewa da dariya Safiyya tayi ta ce “Uwar zumudi ba dai har kin shirya ba?"



Zainab tayi dariya tana fadin “ba dole ba ke dai muje muyi sauri".


Ficewa su ka yi su ka shiga motarta mai gadi ya bude ma su su na hawa kan titi ta kunna masu kida wani kauye su ka nufa..............🖊️✍🏻




Kubiyo ni kuji ya zata kaya wannan salon da ban yake 🧚‍♀️💃


*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ........✍🏻✍🏻








Takuce har kullum *Addeejerh* ❤️

✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND* *NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.


3~4



A wani guri su kai parking dan mota ba ta shiga gurin bokan.


Wani katon dutse suka nufa a matukar firgici Zainab ta kalli safiyya da ke kokarin hawa kan dutsen ta ce “kardai kice nan zamu hau?" tana maganar tana zazzare ido.



Wata iriyar matsiyaciyar dariya Safiyya ta kyalkyale da kana ta ce “Ehh mana ai gidan bokan a can saman dutsen ya ke ".


A tsorace Zainab ta ce “Ni dai bazan iya hawa ba".


Safiyya ta ce “shikenan tunda bakya so sai mu koma ai".



Da sauri Zainab ta ce “ A'a ina so yanzu ya zanyi"


Safiyya ta kalleta ta ce “haka zaki hau tunda kina so" ita taci gaba da danewa kamar yar biri.


Zainab dai ta na tsaye ta na tunanin ta ya zata hau wannnan tsiririn dutsen.


Safiyya ce ta kallota ta ce “wai ba zaki hawo ba ne? ki na bata mun lokaci"


Da kyar Zainab din ta kama dutsen ta fara hawa ko nisa ba ta yi ba sosai sai kafar ta daya ta ku sa zamewa a rude ta ce “Safiyya zan fa hansila" idanuwan ta duk sun cicciko.


Kyalkyalewa da dariya Safiyya tayi wanda ya kular da Zainab.


Ganin haka kuwa ta kulu tayi ta maza ta cigaba da tafiya amma yagololon mayafinta sai da ya fada.


Da kyar suka karasa su na isa Zainab ta dafe kirjinta sai haki ta ke yi .


Wani dan sumulmulen daki ne an rarrataye kawunan kwarangwal da tukwanen kasa dakin kewaye da jan kyalle.


da wata irin gigitacciyar murya aka ce “ku shigo da baya baya a cire takalma".


Ai jin wannan katuwar murya Zainab ta rukunkune Safiyya kamar za ta cire mata hakarkari.


Dariya Safiyya tayi aran ta ta ce “aikin banza"
shiga suka yi.


Wani yakunannen mutum ne da jan kaya a jikin shi da wata kwarya a gabanshi kansa a sunkuye .


Zama suka yi ita dai Zainab jikinta sai bari ya ke yi.


“Mai ke tafe da kune?". bokan ya tambaya cikin gardiyar muryarshi.


Safiyya ce ta kalli Zainab ta ce “ki mashi baya ni da kanki"


Cikin rawar baki Zainab ta ce “boka ina..so...ne ....a kark..a..to mun da hankalin mijina ko mai nayi kar ya tanka kuma ya koma kamar dan cikina wanda na haifeshi sai abunda nace mashi"


Hhhhhh bokan ya sheke da wata iriyar dariya da har saida Zainab taji hantar cikin ta ta kada Safiyya ko, ko a jikinta.


Haka bokan ya ringa sheka wata iriyar dariya kafin ya ce “ta kwana gidan sauki iya abun da kike so ayi akan shi kenan in ma ki naso a maida shi ko bandaki zai shiga sai ya tambaye ki" yana kwashewa da dariya.


Da sauri ta daga kanta ta ce “Ehh boka ayi hakan"


Hehehehehe yayi dariya ya dauko wata kwarya a ciki ya dauko wani kullin magani ya mikawa Zainab hannun ta na rawa ta karba ya sake miko mata wani kullin.


“Wannan na farkon a abu mai ruwa ruwa zaki zuba mashi ki tabbata ya sha dayan kuma a karkashin filon da yake kwanciya zaki barbada mai hhhhhhh sai kindawo nan boka mai cika aiki kenan".


“Ki tambayi kawarki kiji ya aiki na yake" cewar bokan


Safiyya ta ce “haka ya ke boka aikin ka kamar yankan wuka"


Zainab ta ce ”Nawa za'a bayar toh boka?"


Sai da yayi wasu surutai sannan ya ce “Aljanu sun ce a basu dubu 250 sannan in zaki ajiye kudin ki daga wannan kwaryar ki sa ka za su dauka"


Kudaden Zainab ta ciro daga jaka ta daga kwarya ta saka.


Su ka tashi su ka fito da baya da baya.


Sai da Zainab ta sauke Safiyya har gida sannan ta wuce gidan ta.


___________


“Inna ta kinga Umma ko wai nace ta bani kudi na siyo kifi wai ba zata bayar" ta karasa maganar ta na marairaice murya.


Inna ta janyo ta jikin ta ta ce “Rabu da ita kinji shaleleta," ta kama bakin zaninta da ta ke kulle kudi.


Ta mikawa khadeejatu kudin ta ce “karbi kinji je ki siyo abun da ranki ke so"karba khadeejatu tayi ta ce “Nagode Innata" tana rungume ta.


Umma ce ta ce “Haba inna ya zaki na bawa wannan yarinyar kudi haka ?"


Cikin masifa Inna ta ce “wai ina ruwanki ne Suwaiba ki fita daga ido na akan yarinyar nan in ba so kike musa kafar wando daya dake ba kawai kin takura wa yarinya "sai kikkifta ido take tsabar masifa.


Umma ta ce “Allah huci zuciyar ki inna kiyi hakuri kinji"


Kwafa kawai Inna tayi( Inna kaka ce a gurin Khadeejatu mahaifiyar baban ta ta na matukar ji da khadeejatu suna zaune tare)


Khadeejatu taja hijabin ta a igiya ta fice .


Wani gida ta shiga makotansu gidan su Hafsa kenan (makwataka ce da zaman tare tayi sanadiyar kawancen iyayensu har ta shafi yayansu ).



Tana shiga ta tarar da Hafsatu na bacci a daki sai da ta daidaci duwawunta ta daka mata duka da ma ruf da ciki ta yi.


A firgice Hafsa ta tashi sai mutsitsika ido take taryan ta bude idanunta akan Khadeejatu.


Chuno baki Hafsa ta yi tana fadin “Dama nasan wannan muguntar sai ke"


Khadeejatu ta ce “Naji mai baccin asara k'asa kawai zo ki raka ni mu siyo kifi"


Hafsa ta koma ta kwanta ta ce “baza nin ba nan Khadeejatu ta fara lallaba ta.


*Da daddare*


Zainab ce ta rungumo Dr Nura tana fadin “Oyoyo Darling" ta karbi briefcase din shi , shi dai suman tsaye ya yi ya na kallon ikon Allah.


Jan hannun shi ta yi ta zaunar dashi a kan kujera sai binta ya ke kamar rakumi da akala .


Zainab ta ce “Darling bari na kawo ma lemo mai sanyi kasha nasan ka gaji ko?".


Daga mata kai ya yi ya na binta da ido har ta karasa kitchen sai a lokacin ya sa ki ajiyar zuciya .


Zuciyar shi cike da tarin tambayoyi.


A frigde ta dauko lemon exotic ta tsiyaya a cup ta ciro kullin magani da ta sa a bra dinta ta barbada a cikin lemo tasa cokali ta juya sosai.


Falon ta fito tana rangwada ta zauna akan cinyar shi ta na kanne mai ido ta bashi lemon a baki..........🖊️✍🏻





*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ...........✍🏻✍🏻





Taku ce har kullum

_Addeejerh_ ❤️


✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( *Shalelen kainuwa* )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.


5~6

Ya na shan lemon ya kura mata ido kamar wani dolo hure mashi ido tayi ta na murmushi ta ce “wannan kallon fa?"


Murmushi yayi tsabb ya shanye lemon saboda sanyin shi sai da ta yi kissing nashi sannan ta mike ta na rangwada ta nufi kitchen .


Bin ta yayi da kallo har ta shige fitowa ta yi hannunta rike ta plate da abinci .


Kara zama tayi aka cinyar shi ta debo abincin ta kai bakinshi kasa ma bude bakin yayi ta ce “oyo open ".


Bude wa ya yi ta bashi haka ta ringa feeding nashi har ya koshi .


tashi ya yi ya nufi dakinshi domin ya ji ana kiran sallar isha da harara ta bishi a fili ta ce “zaka ci mai garinku ne bari aikin nan ya fara aiki ne" ta sheke da wata bazawarar dariya kana ita ma ta shige dakinta.


Ya na shiga daki direct bathroom ya nufa ya dora Alwala ya tafi masallaci.


Ta na jin motsin rufe kofar dakinshi ta tabbata ya fice sannan ta salallabo ta fito ta shiga dakin nashi kan gadon ta nufa dai dai gurin da yake kwanciya ta daga filon ta kunce kullin maganin ta barbada a gurin ta rufe da filon ta kara gyara dakin ta feshe da freshner .



Tazo futa sukai gware dashi da sauri ta dafe goshinta ta ce “ochhhh".


Wani irin kallo ya rinka yi mata cikin tuhuma ya ce “mai kika zo yi mun daki?".


Cike da kissa ta bashi side hug tana shafa gemun shi ta ce “laifi nayi dan nazo dakin mijina?".

Ya hade rai ya ce “nasan ba shigowa kike ba "

Hmmm kawai Zainab tace taja hannunsa suka shiga kamshin freshner ya bugi hancinsa har wani lumshe ido ya yi yadda kamshi ya hadu da sanyi AC.


Kayan shi ya fara ragewa taya shi ta yi ranar tare sukai wanka.


Dakinta taje tayi shafe shafe da feshe feshe kana ta koma dakinshi .


Mamaki ya rinka yi ganin yau zata kwana a dakin shi abunda da sai dai yaje nan ya fara tunanin ko da wani abun da take so .


Su ka kwanta su na facing juna Dr Nura ya ce “wai babyna mai kikeso ne haka?"


Cikin rashin fahimta Zainab ta ce “bangane ba?".


Nura ya ce “naga kin chanza ne yau ".

Uhumm kawai Zainab tace.

Ya bude baki kenan zai yi magana ta hade bakin nasu....


__________

*Washegari*


Cikin rashin kuzari ya bude idanuwanshi da su kai mai nauyi tar ya gama bude idanuwan nashi akan agogon da ke makale a dakin ya na ta aiki karfe 8:46 na safe ya gani da sauri ya mike ya shiga wanka Zainab sai barcinta ta ke.


Ya na cikan shiryawa ta farka sakamakon kai kawon da yake magana ta fara yi mashi tana fadin “In ka gama shiryawa kaje kitchen ka hada mana breakfast ”.


Juyowa yayi ya kalleta ya ce “Amma asibiti fa zan tafi "


“Bansan da zuwan naka bane zaka wani ce asibiti za ka kaga Malam in ba zaka girka ba shikenan" Zainab ke wannan maganar cikin masifa da daga murya.


Cikin sanyin Murya ya ce “Yi hakuri zanyi yanzu kuwa"

Ta tabe baki Zainab tayi ta ce “da yafi ma"

Haka ya cire coat dinshi ya fice ya nufi kitchen chips ya fara ferewa ya na soyawa ya na gumi haka har ya gama .


Ya zuba a plate ya hada tea ya kaimata har daki .


Ya na shiga hakima ko tashi bata yi ba ta na zaune ta na latsa waya yazo ya ajiye a gefenta a kan bedside ya ce “Gashi!" banza ta mashi kamar bada mutum ya ke magana ba da dutse ya ke yi.


Bai sake ce mata komai ba ya a gurgije ya fara shirya dan time ya ja ya dau briefcase nashi ya kai kofar fita kenan yaji ta ce,


“in ka dawo anjima zan jika ma underwears dina zaka wanke mun kaji ni ko?"


Ya Amsa da “toh".

A gadare ta ce “ka iya tafiya" sannan ya sa kai ya fice.


Ya na futa tasa shewa tana tafa hannayenta ta ce “Gaskiya aikin boka ya na kyau" ta yi dialing number Safiyya.....



*ASALIN DR NURA*

Asalin babansa fulanin gombe ne Alhaji Saifullahi muhammad sun hadu ne da Hajiya Halima Ahmad ita ma fulanin usul ce yan adamawa lokacin yaje wani aiki ne ya hadu da ita a lokacin sunje shopping ita da y'ar yayar mamanta shima yaje a lokacin yaji ya kamu da sonta bai yi kasa a gwuiwa ba ya sanar da ita abunda ke ranshi kuma Allah ya taimake shi da wuri ta amince ba tare da yasha wahala ba.




Haka suka ringa shan soyayyarsu babu kama hannu yaro har aka kai magana gurin manya aka yi bincike ba a samu wata matsala ba aka fara shirye shiryen biki aka sha shagali bayan an daura aure ne aka dauko Amarya daga Adamawa aka kawo ta kano gidanta da ke Sharada.




Shekarasu biyu da rabi da yin aure amma ko bata wata Halima bata yi ba ba karamin damuwa tayi kullun cikin bata baki Alhaji saifullahi yake yi kullum cikin nasiha dangin mijinta(Allah yayi wa iyayen Alhaji saifullahi rasuwa a hannun kawunshi ya girma)kuwa cikin habaici suke mata ita wai juya ce haka kullum ta ke shan kuka.



Rana daya kwatsan sai gashi ta samu ciki dangi da abokan arziki sai murna ake Alhaji Saifullahi kuwa kamar ya maidata ciki ya dauki son duniya ya daurawa cikin nan , lokacin haihuwa yayi inda ta haifi yan biyu maza murna sosai kowa sai san barka ake mata.



Yan biyu na da wata biyu cikin dare sai Hussaini ya fara wani zazzabi mai zafi haka akai shi asibiti aka kwantar dasu da asuba Allah ya karbi abun shi kafin safiya kuwa shima Hassan yace ga garinku nan.


Halima ba karamin damuwa ta shiga ba wannan karan haka, tayi tawakkali ta barwa Allah komai.


Cikin ikon Allah bayan wata tara da rasuwar yan biyu ta samu wani cikin ta haifi danta namiji inda yaci suna Nura haka Nura yayi wayo bayan ta yaye shi da shekara daya ta sake haifar diyarta mace inda taci suna Amina haka suka ringa rainon yayansu cikin so da kulawa bayan shekara biyar ta sake sullubo diyarta mace mai suna Maryam.



Haka rayuwa ta ringa ja Nura har ya gama degree dinshi a bangare likitanci ita kuma Amina tana level 2 inda take karanta mass com ita kuma maryam tana SS1 lokacin.



Rana kwatsan aka tashi Amina ta dena gani iyayensu bakaramin tashin hankalin su ka shiga ba haka aka ringa kaita asibitoci aka ce gaskiya sai an futa da ita an mata aiki da yiwuwar idanun su bude tinda ba haka aka haife ya ba.



Ranar juma'a 1/10/2018 ita ce ranar da iyalan Alhaji saifullahi suka shiga cikin tashin hankali a ranar ne Alhaji Saifullahi da Amina suka je yankar ticket din tafiya kasar da za su je domin yiwa Aminan aikin ido a hanyarsu ta komawa gida ne suka yi hatsari a ta ke Allah ya dauki ransu


Su Mama da Nura ba karamin tashin hankali suka shiga ba Mama suman ta hudu .


Haka harta futa daga takaba aka yi rabon gado bayan shekara daya Nura ya tsuro da maganar aure inda ya hadu da wata budurwashi Zainab.



Nan mama ta je gombe ta sanar da kawunshi ba tare da bata lokaci ba aka yi abunda zaayi aka daura masu aure inda aka kai Amarya gidanta dake kundila.............🖊️✍🏻






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING..........* ✍🏻✍🏻




Taku ce har

Please Login or Register in order to submit comment