Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com
to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ

Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ

Telegram : https://t.me/NovelsHQ

[12/23/2017, 18:37]
__
*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*



©Zeetty

_GARGA'DI_
_Wannan labarin nawa da abin da ya k'unsa, duk mallakar marubuciyar ce. Saboda haka sai a guji juya, ko sarrafa wannan labarin batare da izini ba. In kunne yaji........_


_TUNATAR WA_
_Wannan labarin kagaggen labari ne, don fad'akarwa da Nisha d'antar da masu karatu. Saboda haka sai a guji yin zargi ko zaton cewa anyi wannan labari ne domin a musgunawa wani ko wasu, haka sunaye da garuruwan dake cikin wanna labari, an sane kawai don k'ayata labarin._


_GAREKU MARUBUTA_
_Ina kira a gareku, da mu gyara rubutun mu, musan abinda zamu dinga sakawa dan gyara rayuwar k'annemu da 'ya'yanmu, kar mu 6ata musu tarbiya da sakawa yara buri, abinda bazai yiwu ba a wannan zamanin mudaina rubutawa, mutuna online novels mafi akasari 'yan mata yanzu sun raja'a a kansa, dan Allah muhankalta._


```NOTE```:- *Masu karatu kuyi hak'uri bazaku samu cigaban Labarin littafin Hanyar libiya ba, saboda wani dalili mai karfi, ku gafarceni, dalilin haka nema yasa nafara sabon novel.*

*LITTATAFAN MARUBUCIYAR*
*HANGEN DALA*
*DAGA ALLAH NE*
*HANYAR LIBIYA*
*'DABI'A*
*ZUBAR HAWAYE*
*NAMIJIN DUNIYA*

```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.```


PAGE 1-2
Shigowa gida yayi ko sallama babu, yafara ball da wani baho daya gani a gefen tsakar gidan, cikin bala'i yafara magana"aikin banza aikin wofi, ni za'a kawoma iskanci a cikin gidan nan?, toh zan yimiki wulak'anci, Aysher ina kike, yooo gani d'an iska ko? Ina magana kina ciki kin maidani shashasha, kai uban giji kayi mana arziki ina ganin wulak'anci a gurin matar nan, bazaki fito ba saina shigo har d'akin na nakad'a miki duka, a gaban 'ya'yan naki kaza uwar son 'ya'ya.?"

Da sauri har tana cin tuntu6e ta fito, tana cewa"kayi hak'uri Abban Aslam, wallahi Afra ce take so tayi bacci, shine nake lalla6ata dan nasamu tayi bacci na k'arasa aiki na."

Doguwar tsaki ya saki, kafin yafara magana cikin kumfar baki"Kinji tsiyar ba, daga anyi miki magana sai kice 'ya'ya sai bala'in son 'ya'ya, wuce kibani guri nidai Allah kawomin ranar da zan rabu da wannan bala'in, saboda banda kud'i kin mayar dani d'an iska, shashasha ko?"

"Kayi hak'uri Abban Aslam ba haka bane, ka gafarceni idan na 6ata maka rai." Ta k'arasa fad'a tare da juyawa dan komawa d'akin ta.


Fusgota yayi kafin ya wanketa da mari, yafara magana cikin hargagi"Ehhh mana wato gani d'an iska ina magana kin tafi kin barni wato nagayawa iska ko.?"


Hanunta dafe da kuncin ta tafara magana tana hawaye tace"Kayi Hakuri Abban Aslam, kace natafi, na juya domin tafiyar, amman yanzu kace nayi maka badai-dai ba, kadaure ka sanar dani laifin dana aikata gareka kake hukunta ni, ta wannan hanyar dan Allah, auren so mukayi ni dakai, bawanda akayima dole amman kwata-kwata baifi zaman shekara d'aya mukayi cikin kwanciyar hankali ba.?"


"Hmmm tuhumata kikeyi,? Nace tuhumata kikeyi, tunda na aureki wane cigaba nasamu sam babu wani cigaba kullum sai komawa baya nakeyi, duk abokaina sun fini kud'i da arziki, nikam tabbas na auro mai farar k'afa, zama nin nan ina ake auren so? Sai dai auren kud'i, to bari kiji dakyau, ina nan nasa ayimin binciken matar aure, auren jari zanyi, 'yar alasawa, muga tsiya, shashasha kawai."

Yana gama fad'in haka yasa kai yafice dan barin gidan.


Komawa tayi da baya ta shige d'aki, zama tayi ta rafka tagumi, shin me natsarema Abban Aslam lokaci guda ya canja min?, talaucin nan bani na d'ora mana ba, lallai nice ma mai farar k'afar?, ikon Allah.

Bayan ta gama komai ta gyara gidan tsaff ta d'auko turaren tsinke mai rangwamen kud'i ta kunna, kud'in da Yayanta Nasiru ya bata shekaran jiya da taje gida dashi ta sake amfani yau dan yimusu cefane, Macaroni ta dafa da dankalin turawa, ta siyo d'ayen kifinta ta soya ta watsa a ciki.
Bayan ta gama komai ta share gidan, ga goge ko ina tsaf, tashiga wanka ta fito ta kimtsa, cikin kwalliyarta mai sauk'i, hak'ik'a AYSHER tanada kyau, koda ace batayi kwalliya ba, dubeta yanzu kamar bata ta6a haihuwar yara har guda biyu ba.

Tana zaune a falo ya shigo yana cika yana batsewa, salama yayi ciki-ciki, Aysher ta amsa tare da fad'in"Sannu da dawowa Abban Aslam."

"Yauwa sannu" ya fad'a a dake.
Tace"Me zaka farayi wanka ko cin abinci.?"
"Bazanyi wankan ba, nace bazanyi wankan ba ko dole ne, zoki mak'ureni nayi dole uwata."

"Yi hakuri barin kawo maka abinci."
(Tak'arasa fad'a tare da mik'ewa dan zuwa kawo mashi abinci)
Try ta d'auko mai d'auke da food flask da plate da cokali, ta k'araso gaban sa ta ajiye tare da bud'ewa ta zuba masa, ruwa ta d'auko a roba ta ajiye masa a gaban sa, duk yana binta da kallo saida ta gama tace"Bismillah"
Yace"Kina wani yimin abu isa-isa idan tak'amarki yau ban baki kud'in cefane ba kiyimin list, in sha Allahu zan biyaki idan nayi kud'i."

"Kayi hak'uri duk maganar baikai haka ba."

"'Daukar abincin yayi yafara ci kamar dole, daga k'arshe dai zagewa yayi, yaci yayi kat, kafin ya mik'e a 3 seater, yana satan kallon matar sa, tayi masa kyau take wani sha'awata ya lullu6eshi."

"Zan shiga ciki Abban Aslam saida safe, saika shigo."

Yace"Aikin kenan, toh banyadda ba kijira nagama kallo, har lokacin tashina yayi mushiga tare, inada buk'ata, kinsan ai dole zan buk'ace ki wannan kwalliya haka dan tsabar jarabarki ta motsa shiyasa kika yimin ita, kijira zan biyaki hakkinki, kar Allah yakamani kodan saboda haka narasa ganin dai-dai, barin gama mushige dan nasan ko kinshiga ciki ba bacci zaki iya ba, mayya kawai."

Maganar tasa tayima Aysher ciwo, amman ba yadda zatayi, komawa tayi ta zauna tana kissima abubuwa dayawa a ranta, wato yanada buk'atar ta amman shine zai juya maganar kanta, Allah kayimin agaji........


MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/23/2017, 18:37] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*



©Zeetty



PAGE 3-4
Washe gari da wani masifar yatashi, ko karyawan safe bai tsaya yayi a gidan ba.

Ita dai Aysher baiwar Allah fara gyaran gidan tayi tsaff tayima yaranta wanka ta shirya Aslam yatafi School.

Tagumi tayi tana tunanin halin mijinta da zaman su na da, da kuma na yanzu, tashare hawayen dake zubowa daga fuskar ta, hannu ta d'aga tana rokon Allah ya kawo mata mafita, amman cikin ranta ta kuduri wani abu a cikin sa.

12:00pm yashigo gidan da sallama kafin ya d'ora daga inda ya tsaya fad'i yake"Ke matsiyaciya fito, za'ayita ta k'are nagaji da wannan bak'in talaucin naki, daman tunda naga kinnace saini abin yabani mamaki, ashe kinsan kalarki wato mai farar k'afa ne ke, Mamana da kanta yau tace na hak'ura da wannan auren da kullum babu cigaba sai ci baya."


Cikin K'walla Aysher ta fara magana"Kayi hakuri Abba Aslam, karka rabu dani a wannan yanayin, koma zaka sakeni ina rok'onka Alfarma kabarni nayi zaman 'ya'yana dan Allah."


"Mtswwww kinji tsiyar taki ba?, ana magana sai ki fara cewa yaran ki, toh ke kika haifarmin su, kinsan dai ke kad'ai bazakiyi cikin su ki haife ba, sai da taimakona, yara kuma 'ya'yana ne dan haka zan sakeki yau basai gobe ba, ko Allah zai azurtani na huta da wannan bak'in talaucin da kika jefani tunda na aure ki, gurin aiki nawa ina kai takadduna amman haryau ba wanda suka kirani."


"Kayi hakuri Abban Aslam idan har kayi hakuri ni kaina akwai lokacin da zan rabu dakai, lokacin nakejira yazo, zan rabu dakai rabuwa ta har abada."

"Zancen banza zancen wofi, sai sanda kika gama tatseni na rasa wanda zan kama sannan kikeso na rabu dake ko?, muna fuka dabadan nasan halin yan gidan ku ba kuma yayan ki abokina ne, dasai nace ko mayya na aura."

Kafin Aysher ta bud'i baki tace wani abu taji duka ta ko ina a gaban k'aramar yarinyar ta, Aysher tana kuka Afra tana kuka, baikula suba saida yayi mata ligis kafin ya tsalleke k'afarsa yabar gidan ko kallon 'yar tashi baiyi ba, ballantana ya waiwayo yaga halin da matar tashi take ciki.


A hankali Aysher ta rarrafa taje kusa da 'yarta ta rungumo tana lallashinta, itama yarinyar tasa hannu akan mahaifiyar ta alamar tana lallashinta, abin gwanin ban tausayi.

Aysher tana yashe a tsakar gidan takasa motsawa nan da can, saboda jikin ta gaba d'aya yagama tsami ciwo yake mata, 1:00pm k'anwar ta Maryam tashigo gidan Hannun ta d'auke da Aslam wanda yataso daga school suka had'u a hanya.

Dasauri Maryam ta saki hannun Aslam ta zura da gudu, dan ganin halin da yayarta take ciki, ta k'arasa tare da kamo hanun 'yar uwar nata tana girgiza mata kai tana cewa"Aunty kardai ace haryanzu bakiyi girman daina duk ba a gurin YAYA SAMIR?, toh wallahi anyi na farko, anyi na k'arshe, yau saina fad'ama Umma da Baba dan wallahi bazaiyiwu ki zamo jaka a gurin sa ba, bayan duk hallaccin da kikayi masa a baya, aiban manta da d'an kunne da sarkarki da Gold da kika siyar kika bashi kud'in akan yaja jari ba, yace ya had'u da 'yan damfara bayan shine cikakken madanfari saboda tayaya zaka bada kud'i kace ayi maka kud'i, saboda son banza, toh yau za'ayita ta k'are dole ya rabu dake Aunty Aysher." Cikin fad'a da 6abin rai Maryam take fad'in haka kasan cewarta masifaffiya ce ta k'arshe.

Cikin sanyin ta Aysher ta d'ago kanta tace"Kiyi hakuri Maryam karki fad'a a gida, wannan abun yazamo sirri tsakanina dake, karki manta sau nawa Baba da Yaya suke zuwa sunayi masa fad'a akan dukan nan amman haryau ya kasa bari, idan kika fad'a agida raba auren za'ayi dan haka Yaya yace, nikuma banshirya rabuwa dashi ba yanzu, dan haka dan Allah kirufamin asiri, akwai lokacin da zaizo dole na rabu dashi, kid'auka wannan abin da Abban Aslam yakemin a matsayin tawa kaddaran da zan tarar a gidan aure na, taimaka ki juyemin ruwa nayi wanka, na shirya ko zanji sauk'in ciwo jikin nan Maryam."

_"Aunty Aysher bazata ta6a canja wannan sanyin halin nata ba, shiyasa take cutuwa dayawa."_


Cikin Zuciyar maryam take fad'in haka, sannu Aunty Allah kawo miki mafita, (tafad'a tare da kamo hanun yayar ta dan Zuwa band'aki). Ameen Maryam (tabata amsa)


Aslam da baisan wainar da ake toya ba, bayan baya gida amman jikin sa yabashi cewar Abban sane yayima Momy irin abin da yake mata kullum a gaban su (Duka).

Aslam yanada wayau kasan cewar shi yaro d'an shekara shida yana primary Two a School, haka Islamiyya yana Aji 2 duk aji d'aya yake tafiya da boko da Arabiyya.
Binsu yayi da kallo cikin Zuciyar sa yana mai k'ara tsanar Abban nasa.

Da taimakon Maryam Aysher tayi wanka tare da gasa jikinta, bayan tafito Maryam ta bata maganin ciwon jiki tasha anan bacci ya d'auki Aysher, bacci mai cike da alamun wahala.


Da wurwuri yadawo gida hanun sa d'auke da wani farin takarda, fuskar sa tana d'auke da alamun farin ciki.
Da sallama yashigo gidan ya tarar da Maryam a kitchen tana d'ora musu abincin dare, fuskar ta a tur6une ta gaisheshi, ya amsa da fara'a sosai yak'ara da cewa"Maryam kece a gidan namu, ya su Umma da Baba?"

"Suna nan lafiya" tabashi tare da shan toka (lols 'yan skt)

"Ina Momy'n Aslam?".

" Tana d'aki a kwance batajin dad'i."

Sai yanzu Samir ya tuna da abinda yayi mata da safe kafin ya fita, cikin mutuwar jiki ya shige d'akin da take kwance.

A zaune yasameta tayi tagumi, yashigo da sallama ta amsa tana murmushin yak'e kafin tace"sannu da dawowa Abban Aslam, ya k'ok'ari?."

"Alhamdulillah Sulty na, yau Allah ya kar6i addu'ar mu, ga takaddata ta d'aukar aiki a NNPC."

Hannu Aysher ta d'aga sama tare da fad'in"Alhamdulillah, Allah nagode maka Allah maji rokon bawansa, nayi maka murna Abban Aslam Ubangiji yasa kafara a sa'a."

Kai ya gyad'a yana fad'in"Ameen ameen Sulty na, kifagar ceni dan Allah."


Shiiiiii Aysher tayi masa alamun yayi shiru kafin tace"karka fara Maryam tana gidan nan, kabari sai ta tafi."


_Cikin zuciyar sa mamakin sanyin halin Aysher yakeyi da hak'urin ta, yana godiya da Allah baisa ya datse igiyar auren su dayayi niyyar yi yau ba._


"Bakomai Sulty barin je na dubo miki magani, ina ne yake maki ciwo yanzu."

"Bako ina dan nasha magani, kasan cewar na tanadeshi tuntuni, saboda irin haka."

Kallon matar tashi yay, yana tausaya mata abubuwan dayayi mata, kafin ya girgiza kai yafice dan barin d'akin.


Aysher kuwa mamaki ne ya rufeta yaushe rabon da Abban Aslam yakirata da wannan sunan *SULTY* tun farkon samun cikin Aslam.



```Kukasance tare dani, dan jin farkon tarihin wad'an nan ma'aurata.```

MAMAN HANAN
ZAUTEN LITTATTAFAN HAUSA
[12/23/2017, 18:37] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*



©Zeetty


PAGE 6-7
Cikin lokaci k'ank'ani al'amura suka canjama Samir da Aysher, kai tsaye aka bashi gida a NNPC dake cikin Quaters na Kaduna, komai da komai ansa a gidan bazasu shiga da komai ba sai kayan sakawan su, dan haka Aysher tayima 'yan uwanta sallama da danginta, suka d'auki hanyar kaduna, bisa rakiyar k'awanta da wasu daga cikin dangin Mahaifiyar ta.

Kwanan sh d'aya 'yan rakiya suka juyo dan komawa gida, Aslam da Afra ansamo musu makaranta anan cikin NNPC Quaters d'in. Wani kana kallonsu Aysher da Samir a wannan lokacin dole subaka sha'awa, dan tabbas hutu yazo musu sosai, gaba d'aya sun canja, musamman Aysher tak'ara wani fresh da haske, gata daman tubarkallah akwai kyau.


Satin su biyu da dawowa Al'amura duk sun canja, wani kulawa da soyayya Samir yake yima matar shi, wanda baita6a yimata ba a farkon.

Tausayin matar sa sosai yakeyi idan yatuna da abubuwan daya aikata mata abaya, lallai talauci baiyiba, dole anemi tsari dashi, kullum tunanin samir kenan a gida ko Office idan yakad'aice.

Fara aikin sa bada dad'ewaba aka k'ara masa matsayi a gurin aiki, wannan abu bak'aramin dad'i yayima Aysher da Mijinta ba.

Washergari har gurin aiki Aysher tarakashi bayan sunkai su Aslam School, tare suka bud'e sabon Office d'in Abban Aslam. Suka shiga da bismillah addu'a Aysher tayima mijin ta sosai kafin su shafa.

Samir rungumo Aysher yayi yana hawaye "Sulty na, kiyafemin na zalunceki dayawa, na biyewa sharrin shaid'an da zugin abokai, dan Allah kigafarceni (yak'arasa fad'a tare da k'ok'arin durk'usa mata)."

Saurin dagoshi Aysher tayi tana share mishi hawaye kafin tace"Abban Aslam na yafe maka, amman dan Allah nima kayimin alk'awarin idan natashi neman wani abu a gurinka bazaka hanani ba."

Dasauri Samir yace"Namiki Alk'awari Sulty na, banga abinda nake dashi a duk duniyar nan, dazaki nema nakasa yimiki ba, anjima za'a kawomiki sabuwar motar ki, saboda yanzu hanun ki ya fad'a, zakidinga taimakamin dakai su Aslam makaranta da d'auko su."

Kai kawai Aysher ta gyad'a masa.

Soyayya Samir yake nunama Sulty Aysher sosai.


*BAYAN SATI BITU*

Komai yawuce a gurin wad'an nan ma'auratan.


Ranar Monday da misalin k'arfe 2:00pm, akayima Samir waya daga School d'insu Aslam cewa yazo yad'auki yaranshi dan andad'e da tashi a School kuma gashi ankira wayar Madam akashe.

Arikice Samir yabar Office kai tsaye School d'in ya isa, yad'auki yaranshi ransa a 6ace, yana mamikin inda Sulty ta tafi batazo tad'auki yaransu a School ba, wayar ta kuma a kashe, Afra sai surutu take masa amman yak'i kulata, yana tunanin halin da zaije ya riski matar sa a ciki idan sun k'arasa gida.

Yana Parking yafito yabud'ema yaran baijira fito warsuba yasakai cikin gidan da sauri, yayi amfani da da key d'in gurinshi ya bud'e gidan, kiranta yafarayi yaji shiru, kai tsaye d'akin ta ya nufa dammmm kirjinsa yabuga sakamakon ganin Akwatinan Aysher a zube a kan gado, babu babban cikin sa, a hankali ya k'arasa kan gadon, ya k'arasa kan gadon cikin sanyin jiki, takadda yagani akan gadon a hankali yasa hannu yad'auka ya fara warwarewa, rubutun Aysher yagani kamar haka:-

_ASSALAMU ALAIKUM_
_Abban Aslam kayi hak'uri da hukuncin dana yanke a tsanin zamana dakai, zanyi hakan ne bawai dan bana sonka ba, a'a sai nace duk duniya bayan iyayenka nafi kowa sonka._
_Karka manta da alk'awarin dakayi min nacewa duk abinda na nema a gurinka zaka yimin, bakomai nake soba Abban Aslam dan Allah kataimaka ka sauwak'emin, murabu dakai rabuwa na har abada, bawai dan bana sonka ba saidon lokacin da nakejira yazo kenan naci gaba da hak'urin zamadakai, dan inaso na k'aryata duniya cewar ni mai farar k'afa ce, nashanye duk abubuwan da kakemin, har zuwa yanzu da Allah ya axurta ka, nayanke rabuwa dakai._
_Kataimaka kayimin abinda nakeso cikin ruwan sanyi, wallahi wallahi nagama zama dakai har abada, sai naji daga gareka._
_Ma'assalam._
*Matarka a baya, Aysher Muhammad Rogo.*




Muje zuwa.......



MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite Group Novels: [11/19, 5:59 PM] Zeetty: 💐💐💐💐💐


*MAFARIN LAMARIN*




DAGA TASKAR
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION (Z.W.A)*



©Zeetty


```Ayimin afuwa wajen rubuta PAGE nayi kuskure 5-6 zan saka, but nasa 6-7 so yanzu zan gyara.```


PAGE 7-8

Samir yana gama karanta wannan wasik'ar ya sunkuyar da kansa k'asa yanajin zubar wasu hawaye masu zafi daga idanuwan sa, hak'ik'a abokan sa sun kaishi sun baro, yakasa yadda da k'addara, lallai imanin sa bai zamo cikakke ba, daga kansa yayi yana tunanin irin abubuwan daya aikatama Sulty Aysher a baya, lallai da wuya ta iya yafe masa.............

~ASALIN LABARIN~

_Aysher Muhammad rogo itace yarinya ta 4 a gurin iyayen ta Dr.Muhammad Rogo da Fatima, Isah ne babba sai Usman,Auwal sai Aysher, Hadiza da Auta Maryam._

_Iyayen Aysher 'yan boko ne musamman Mahaifin ta wanda likitan hak'ori ne, Aysher sun had'u da Samir ne tun tana aji biyar a makarantar sakandire, abokine ga Babban yayanta Isah, tare suka gama karatu a B.U.K, kuma margayi malam Bashir amini ne sosai a gurin Dr.Muhammad mahaifi ga Aysher._

_Malam Bashir malamin makaranta ne kafin mutuwar sa, mutum ne nagari mai halin dattako._
_Sosai Dr.Muhammad yakar6i maganar auren Aysher da Samir, dan yasan halin mahaifin sa, kuma yana ganin hankalin Samir d'in ganin yadda suke tafiyar da al'amuransu da d'ansa Isah._
_Dakanshi ya samo musu aiki tare da Isah a ma'aikatar kar6an haraji ta garin kano, Aysher tana gama karatun Sakandire aka sha bikinta da Angon ta Samir._
_Farkon zaman auren su abin sai son barka ga duk wanda yaje gidan, wani irin soyayya suke yima junan su, wanda basa iya 6oyewa a gaban kowaye, mafi akasari ba'ason zuwa gidan musamman ranar Week end dan Samir dakan sa yayi gargad'i da hakan, a cewar sa, wannan ranar, ranar sa ne shi kad'ai, salon bai canja ba a lokacin da Aysher ta samu ciki, kulawa yake nuna mata sosai tare da tsantsar soyyayya ga abinda zata haifo masa._
_Lamarin yafaro ne bayan Haihuwar Aslam, lokacin yanada shekaru uku, a wannan lokacin sabuwar gwabnati ta hau kujerar mulkin kano, dan haka aka sallami ma'aikata dayawa, cikin su harda Samir. Hankalin Dr.Muhammad yayi bala'in tashi dajin wannan labarin._
_Shikansa Samir dafarko yad'auki al'amarin dacewa kaddara ne, amman daga baya yasamu wasu shaid'anun abokai suka zugeshi da cewa had'in baki ne daga gurin surukin nasa idan ba hakaba, meyasa ba'a kori Isah ba?, wannan kawai anyine dan a tozarta Samir d'in._
[11/19, 6:57 PM] Zeetty: _Dan anga yafara tara Iyali, tun Samir bai d'auki maganar da mahimmanci ba, har yad'auka, dan haka lokaci guda yafara canjama Sulty shi, abu kad'an idan tayi saiya rufeta da masifa da bala'i, wata rana har dukan ta yakeyi agaban Aslam, tun yaron baya fahimta har yafara ganewa, a haka Maryam k'anwarta tazo takawo mata ziyara wata rana ta risketa jiki duk shatin bulala kamar wata Jaka, hankalin Maryam yatashi dan haka takira yayan su Isah a waya tana sanar masa, hankalin sa a tashe ya k'araso gidan ganin irin dukan dake jikin k'anwarsa wani tausayin ta ya kamashi._
_Bayan ankaita asibiti binciken likita nafarko daya fara ganowa shine, Aysher tana d'auke da hawan jini, Dr.Muhammad ransa ya6aci dajin haka, yakuma tausayama 'yar sa, dan yasan may be tana fuskantar matsala a gidan mijin ta, dan su kansu yagama canja musu baya zuwa gidan, idan suka had'u da Isah saidai Isah yayi mishi magana._


_Bayan ankirashi awaya an sanar masa suna asibiti fad'a yafarayi tare da borin kunya yana fad'in"akan meye za'ad'auki matar sa a kaita asibiti batare da sanin shiba, saboda an gama rainashi anga bashi da kud'i ko meye?,_ _ran Isah ya 6aci dajin haka, dan haka yaso bashi amsa, amman Mahaifinsa ya dakatar dashi, tahanyar nunama Samir cewar sunyi kuskure yayi hak'uri._
_Hakadai Zaman yaci gaba da kasan cewa, dan wata rana idan yayi mata dukan ma kulleta yakeyi a d'aki, dan gudun kar 'yan gidan su, suzo suganta ballantana a taimaketa._
_Abokan sa suna ka'ara ingizashi musamman wani mai suna Kabir da cewar matuk'ar baya k'untatawa Aysher bazai huce takaicin abinda mahaifinta yasa akayi masa ba (Kajifa mai karatu)._
_Dan haka yak'ara kaimi wajen sambad'o mata rashin mutumci, horo da yunwa, baya bata kud'in cefane, akwai sanda tasiyar da Gold d'inta tabashi kud'in yaja jari, yace 'yan damfara sun kwashe kud'in, idan yatashi zaginta kuwa sai yace"Shashasha wawuya wadda batasan ciwon kanta ba, muguwa irin mugaye masu bak'in hali, mai farar k'afa", wannan zagin yana damun Aysher tasha zaunar dashi tace "meye laifin datayi masa", sai yace"Mahaifinta yasa an koreshi a aiki, dan mugunta kuma duk inda yaje neman aiki mahaifinta yasa an toshe ba'a d'aukar sa, dan haka itama tayi bankwana da jindadin gidan aurenta."_

_Dukan dayayi mata nak'arshe shine wanda ya sumar da Aysher, yatsallake yabarta a kulle a d'aki, Isah yakawo matarsa ziyara gidan Aysher yatarar gidan shiru sai kukan Aslam, kuma ya buga ba'a bud'e ba, dan haka yakira aka 6alle k'ofar anan yatarar da Aysher yashe a tsakar gida alamun bata numfashi, cikin tashin hankali yad'auki Aysher dan zuwa Asibiti._
_A wannan lokacin Aysher har targad'e yayi mata a guri biyu, (wannan wane irin zalinci ne kadaki mace, sannan ka kullota a gida kota rayu, kota mace, lallai dole a raba auren nan, dan Samir mugu ne, bason Aysher yakeyi ba), tunanin da Isah yakeyi kenan a ransa._
_Toh bayan Aysher tawarke Samir yagama borin kunyar sa da bayarda hak'uri, dan Isah yace saiya sakar musu k'anwa, Dr.Muhammad ne yakashe rigimar da cewar Samir yayi alk'awarin bazai sake bugun Aysher ba, nan take yayi wannan alk'awarin dan yanason matar sa tsabar talauci ne kawai da kuma zugan abokai._
_Bata sake zani ba, dan duka da zagin cin mutumci sai abinda yak'aru a gurin Samir, a haka aka samu cikin Afra, albarkacin cikin yarage mata wasu abubuwan, har aka haifi Afra, idan kaga Aysher dole kasan tana cikin wani hali duk ta rame ta lalace, Kabir yacema Samir" Hakanne dai-dai abokina, kaci gaba da aiki dole idan mahaifinta yaganta ransa ya6aci, kaga karama abinda yayi maka akan 'yarsa."_
_Sosai Samir yake amfani da shawaran da Kabir yake bashi, aganinsa bashi da wani aboki masoyi sama da Kabir d'in._
_A haka dai har aka haifi Afra, wulak'anci salo-salo ga kyara da hantara a gaban 'ya'yanta, idan tayi magana ya wanketa da mari, Aysher tak'i fad'a a gida, dan a cewar ta akwai lokacin da zata rabu dashi, lokacin da Allah yasa yasamu aiki, zata nemi ya sauwak'e mata._

*Mai karatu kaji irin halin da Aysher ta tsinci kanta a gidan auren ta, menene ra'ayinku?.*

A hankali Samir yadawo daga duniyar tunanin daya tafi, yaji ihun yaran sa a falo, dasauri ya mik'e yafito ya samesu yace"kuzo kuje kushiga mota natafi gurin Momyn ku", da sauri Suka ruga suna cewa"Abba yunwa mukeji."

"Zan siya muku abinci a restaurant kuyi shiru" dan bayason damuwa, mafita yake nemowa kansa, baya fatan Aysher ta tona masa asiri a gurin mahaifinta bayan alk'awarin da ya d'aukar masa na cewar yad'aina gasa mata aya a hannu............



MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[12/28/2017, 10:29] Zeeett Zamaniwrite

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment