Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da
amare na ta fafutikar shirye-shiryen biki, ita
kuwa Nusaiba wani abu ke daure mata kai, mai
kama da al'amara. Al'adar ta d'if, ta dauke
wata 2 kenan. Ana neman a shiga na uku. Ga
wani ciwon kan safe da take fama da shi, yawan
kasala da taruwar miyau a bakin ta. Bata gane
kan gadon ta ba, ko alama sai dai bata fidda
shakkun ciki take dauke da shi. Ta runtse idonta
tamau? Ta dauki salatin Manzo ta yi wa Allah
tasbihi mai yin yadda ya so." Watau rabon Da,
ya kawo ni cikin gidan nan kenan? Ta dan yi
murmushi, domin take nan ta tsinci soyayar
abinda ke cikin ta.Tana so ta nuna wa Antin ta
alamomin da za ta gane, amma tana jin tsorin
kar Naseer ya sani. Watakila ba zai so haihuwa
da ita ba, tunda baya sonta. Kar ya munafunce
ta da wani abin, ya zubar da cikin. Saboda haka
ta ci gaba da 6oye yanayin ta, babu wanda ya
fahimce ta, illa tsiyar k'iba da Antin na ta
kullum take yi mata. A haka suka sha bikin
Sageer. Amarya ta tare kusa da gidan su Sageer
din, ya kama hayar gida karami dakuna 2, kicin
da bayi. Sageer ya kama angwanci, babu kama
hannun Yaro. Sati da ya zagayo tun ranar
alhamis Nusaiba na Kaduna, ko dama duk ta
kosa ta sami 'yar damar da za ta gida, ta dan
kwana 2. Tana like jikin Umminta, dadi ya ishe
ta, ga madarar Holandia mai sanyi take ta
faman sha, tun isowar ta. Haka Ummi ke cikin
farin ciki ganin yadda Nusaiba tayi k'iba, ta
k'ara haske sosai. Tana ta kallon ta, tare da lura
da yanayin ta, ita kuwa Nusaiba ta k'i yarda
wani abu yanke a bakin ta, kar miyau ya taru,
kamar dai yadda take yi a gida Zariya. Bikin
Kausar yayi armashi kwarai da gaske, angonta
Injiniya Abdul-Malik yayi bajinta. Haifaffen
Unguwar Sarki, amma yana aiki da hukumar
gida da ke Lagos.Ta tare a makeken gidan sa da
ke (Abuja Road) kafin lokacin da za su d'aga
Lagos. Ranar asabar Zarah ta zo, kuma ta so
kwana. Kiri-kiri Naseer ya hana, ya kasa, ya
tsaye da yamma dole ta biyo shi, ya dawo da
ita. Nusaiba kuwa sai da ta kai litinin.
Alh.Basheer yayi ta ciwon baki, yana wa Ummi
fada yana ganin kamar da hadin bakin ta
Nusaiba ta kai Mondy. Karfe 4 kayanta an gama
kintsa su a mota. Direba zai maida ta. Tayi tsaye
tsakar falo tana kallon iyayen ta, kamar kar ta
tafi. Hawaye ya gangaro kafadarta,"Kuka za ki yi
shagwa6a66iya? Ta tsura masa ido, hawayen
suka zubo shar-shar! Yasa hannu ya goge su, ya
sake cewa,"Menene abin kuka? Kin ga kama
hanya ku tafi. Allah ya kiyaye hanya. Ki kula da
kanki da kyau. Kin ji? Ga katon 4 nan na
Holandia, na ce a sa miki a but." Umminki ta
ce,"Yanzu shan ta ki ke yi sosai ko? Ta dan
sadda kai kasa. Yayi murmushi, ya dago
ha6arta,"Haka Umminki ga gaya min, ga ta dai
a tsaye, ko ba ke ki ka gaya min ba? Ta wuce
shi da gudu ta koma gun Ummi, rungume ta. Ya
ce,"Ummita, sai mun yi waya." Kafin ta ce wani
abu, ta bar wajen da gudu, ta fita. Me za su yi,
ba dariya ba, kamar almara ta ga Naseer na
fakin a harabar aje motici. Ta ja tsaya, tana
kallon sa. Mamaki ya ishe ta. Daga bayan ta, ta
ji muryar Abbanta na fadin , "Ah , ga ma mijinta
nan ya zo." Ya zo ya wuce ta, ya nufi wajen
Naseer da ke fitowa daga mota. Da sauri ya
tsugunna. Alhj ya mika masa hannu tare da
sallama. Ya mika na sa yana amsawa. Sannan
suka gaisa, kafin Alhj ya ce,"Ashe za ka sami
zuwa? Ai tun jiya na tambaye ta, ta ce min ka
na da.(Exams), ba za ka zo ba." Kan sa tsaye ya
ce,"Mun fito da wuri, shi ne na ce bari in zo
kawai in dauke ta." "Yayi kyau. Dama fitowar na
ta kenan zu su tafi. Bari direba ya kwashe
kayan, ya mayar but din ka." Ya bude but din.
Direba na juye kaya, shi kuma ya shige cikin
gidan, don gaisawa da Ummi. Ko dama Nusaiba
tuni ta koma ciki, kan ta daure, tana tambayar
kan ta." Wai ashe maza ma sun iya kisisina?
Kurame sak! Suka zama cikin mota, yadda ya
like kunnensa da Ear piece haka ta manne na ta
da sauraren tafisr din Marigayi Sheik Jafar
Mahmud Adam Kano.
(Allah yajikan Mallam Ja'afar na Gadon kaya me
Ahlussuna, tare da iyayenmu baki daya




Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment