Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin bazata iya cigaba da irin wannan zaman ba ,minti biyar kawai Aunty shahida tayi  da fita amman ganin take Kmr awa biyar tayi da barin office din ,shi kuwa  mr ATA banda tsaki babu abinda yake yana qarawa domin ya fara gajiya da zamansa tare da abinda yafi tsana arayuwarsa ."

Aunty shahida na fita ko cikakken minti goma batai yi ba sai ga nuzla ta shigo office din bakinta dauke da sunan Aunty shahida,turus tayi sakamakon ganin maryam zaune gefe guda kuma mr ATA ne zaune kallon tsoro tayi masa ta dauke kanta tana gaishesa bai amsa mata ba kamar sauran lukuta ta qarasa ta dafa maryam "marsi ina Aunty shahida ."?
"ta dan fita amman tace bazata jima ba ki jirata ,
"okay da ido tayi mata tmby me ya Adam yake yi ? itama da kwayar idanunta ta bata amsa da bata sani ba dan babu damar ayi magana mai sauti kasamcewar sun san baya son hayaniyar komai saurin ciro wayarta tayi ta maida silet ."


sadiya wacce ta kasance me koyon aiki ce a asibiti ta shigo bakinta dauke da sallama "Assalamu alai...... kasa karasa sallamar tayi sakamakon gani mr ATA zaune idanunshi na kallon screen din wayarsa sanye cikin kanan kaya ,gbdy ta rikice akansa madadin ta karasa ta ajiye file din dake hannunta ta kasa ko daga dan yatsan kafarta garin kallonsa ma har file din hannunta ya subuce daga hannunta ya fadi kasa da sauri ta tsugunna ta dauka jikinta na rawa ta karasa ta ajiye fayal din akan table ,tana faman kallonsa  sai lokacin ta lura da maryam dake zaune  tana kallon yatsun hannunta yayinda nuzla ke tsaye a gefenta "sannuku da hutawa ta furta a hankali ."
maryam ta dago tana murnushi tace "yauwa ya kokari ? alhamdulillah sadear ta bata amsa tana kallon nuzla sannan ta fita tana waiwayen Mr ATA tana yaba kyawunsa acikin ranta shi kuwa Mr ATA ko ajikinsa dan iskar ma data debota bai gani ba idan da sabo ya rigada ya saba  da irin kallon da suke masa haka ma kallon da mrym da nuzla Ke masa bai sa ya dago daga duban wayarsa da yake ba .

Nurse sadiya na fita daga office suka ci Karo da husaina itama maakaciya ce "ke lafiyarki kika fito a hargitse Kmr wacce aka koro ?"uhm ke dai bari husseina wani matashi na gani a office din doctor shahida mutumin yayi min kyau matuka ya dauki hankalina wallahi irin mijin da nake nema kenan mijin duniya Mijin novel ya hadu sosai da gani yana da kudi yana da tarin ilimin boko da Arabic uwa Uba kyau "ke sadear raba kanki da wahala, kina diyar talaka dake naci ma da kyar kuke samu kullum Kuna yawo a gidan haya , yayanki ma da kyar yake daukar dawiniyarki Amman kin kashe kanki da mugun buri  , ki roki Allah idan yaga dama zai Baki ki Daina zafafa burin akan auren me kudi ."
sadear ta Dan turo mata karamin Bakinta tana yatsina fuskar ,jikin Sadia yayi sanyi sosai husaina taja tsaki ta wuce ta barta Nan tsaye tana maganar a fili ."

Wayar hannunsa da yake ta faman daddanawa ce ta dauki qara ya manna a kunnensa tare da zamowa kad'an daga Kan kujerar da yake zaune yana lumshe idanunshi "na barota a gida ne ,okay suna bukatar  new design's da kaya ?shikenan ki  bawa kwararrun wadan da suka iya domin  bana son a samu matsalar komai aikinsu  dan last time sunyi complain okay may be tomorrow  yana magana yana lumshe idanuwa yana lasar lip's dinsa  na kasa ."
uzla,maryam duk suka zuba masa idanunsu suna kallonsa kowacce da abinda zuciyarta take saqawa jikinsa ya bashi  kallonsa  suke dan haka ya tsaida  lumtsatsun idanunshi akansu  yana masu wani irin kaskantacce kallo  sannan ya dauke kansa ya cigaba da waya a daidai lokacin da husseina da sadiya suka shigo tare ita kanta husseina ta jinjinawa kyawunsa dan sai da tabawa idanunta abinci suka dauki abinda ya shigo dasu suka juya ."


Ya sake tsaida idanunshi akansu ganin still shi din suke kallo har lokacin Kmr basu san shi ba wani irin taikaci ya kamashi dan baya son yawon kallo arayuwarsa wani abu ya hadiye mai daci a makoshinsa kafin ahankali yaja tsaki yana cigaba da kallonsu yayinda su kuwa a matukar firgice suke kallonsa cikin tsananin tsoro da firgici sam basuyi tsamanin zai sake  kamasu suna kallonsa ba irin kallon da yake masu yasa suka sake shiga rudani dan basu san abinda zai biyo bayan kallon da yake masu ba sannan basu abinda zasu fad'a dan kare kansu ba nuzla ta kalli maryam itama ta kalleta gabadaya jikinsu ya kama rawa nuzla tayi saurin durkushewa kasa bisa gwiwowinta dan tasan na lahira zai fisu jin dadi idan bata hanzarta bashi hakuri ba dan taga maryam bata da alamar bada hakuri "ka..! kayi hakuri ya Adam magana yake son yi amma ina  jin isa acikin ransa yasa ya gagara furta komai illa kafarsa daya daya shiga jijigawa yana takaici ."

ganin har kusan minti talatin aunty shahida bata dawo ba yasa mr ATA ya Mike a fusace ya tura hannunsa daya cikin aljihunsa ya bar office din dan jikinsa ya fara bashi so take ta hadasu da Maryam ta fayyace mata komai a gabansa,yana fita nuzla  ta nufi kofa cikin sand'a itama mrym ta biyo bayanta, nuzla  na gama bude kofar turus  sukai yi sakamakon ganin sadiya da husseina tsaye rungume  da file suna kallon byn mrs ATA suna magana can kasa kasa sakamakon mutanen dake kai kawo " ai wannan ba bakon fuska bane sadiya matashin dan kasuwan nan ne  da duniya Ke ji dashi  sannan kani ne ga sister shahida  yana zuwa lokaci zuwa lokaci ke baki ga kamarsu ba "?lallai kam sai yanzu na ganesa ko dan na rikice ne amman yafi kyau a fili km suna matukar kama sosai da Sister shahida sai dai har ya fita kyau ,wallahi husseina mutumin nan ya shiga raina sosai ban ta'ba ganin halittar daya dauki hankalina ba  kamarsa komai nashi irin mafarkina "uhm uhm sadiya na sha gaya miki ki daina irin wannan hange  ki tsaya matsayinki kin kasa fahimtata ."kisani babu abinda allah bayayi bansan dalili  ba gani daya nayi masa amman na kamu da matsanancin soyayyarsa  " wallahi wannan yafi karfinki Ke ko yaronsa yafi karfinki bareshi  idan zaki dawo haiyacinki ki dawo taja hannunta sukai wuce  sadiya na juya bayanta ."


Naunayen ajiyar zuciya nuzla da maryam suka sauke atare suna dafe qirji "marsi wallahi ba qaramin tsorata nayi ba ,koni kusan nafiki tsorata wallahi kadan ya rage ban saki fitsari ajiki ba qaramin saa muka ci ba da yau mun sha maruka suka kwashe da dariya "kinga bari na wuce bazan iya jiran Aunty shahida ba daman nazo karban test din hjyrmu ne nace nazo mu gaisa kinga wucewata sai mun hadu a gida ta zame hannunta dake cikin na maryam ta wuce tana daga mata hannu , maryam ta koma cikin office zaman jiran Aunty shahida ."
Bai Dade da wucewa ba doctor shahida ta dawo ta ga wayam bashi Babu alamunsa "sarkin zuciya halan ya gaji ya wuce "eh Maryam ta fada muryarta a sanyaye "okay ta shiga tattara kayayyankinta muje kou daman akwai maganar dana so muyi mu uku Amman zanzo gobe inshallahu idan na tashi daga aiki muyi a gida "magana kuma aunty.?"ta tmbyeta a tsaro ce .
"Eh!
" wacce magana ce haka Kuma har da ya adam zaayi ?aunty shahida tace ",magana ce me mahimmam ci , dan girman Allah aunty shahida wallahi bana son duk abinda zai hadani dashi nifa tsoro yake bani culmdown my sister ki cire wannan tsoro ba wani Abu bane face alkhairi shiru mrym tayi tana nazarin maganar aunty da tunanin wacce magana ce wannan da har sai anyita da ya Adam Kuma tace alkhairi ne ...?
suna fitowa haraban asibinti suga direbansa na jiransu "a ruwa Ina mai gidanka ? sai daya rusuna mata sannan yace "ya kira anzo an daukesa da wata motar aunty shahida ta girgiza Kai ta shiga mota ita da maryam inda take fad'a mata zuwan nuzla "Ayya kanwata ai kuwa na gode sosai itama kuwa ina son ganinta nan hankalin maryam ya dan kwanta jin har da nuzla sai dai har sanda a ruwa ya sauke aunty shahida a kofar gidanta zuciyar mrym bata bar Saka da warwara ba Allah Allah take gobe tayi taji ko meye .."


washegari da misalin karfe goma na safe sakon mutuwar sadiya ne ya riski doctor shahida, tayi matukar firgita da Jin wannan mummunar labari saboda cewar da akayi yankar rago akayi mata ta zabura ta mike daga zaunen da take jikinta na rawa ......."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
Arewabooks username
Ayshabagudo

bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page4

"Wani  irin   gumi  ke tsatsafowa   ajikin  aunty  shahida   yayinda zuciyarta  ta  dinga bugawa da  karfi  fiyye  da  kaida ,nan  take ta mike tsaye ta shiga zariya  a office   ta kasa  zaune ta kasa tsaye  tana  sake jin wani sabon tashin hankali   tana cikin wannan halin sai ga doctor  sa'a   ta shigo  a  rud'e  ta tsaya  suna  kallon  juna  yanayin  doctor  shahida  ya  tabbatar  mata taji abinda  ya  shigo daita office  din  dan  duk ta fita  haiyacinta ,a matukar  tsorace  aunty  shahida  take kallonta qirjinta  na  dokawa  "nasan  kinji  abinda  ya  shigo dani ? wai  an yiwa  sadear  yankan rago a gidansu."
har  lokacin  fargaba da  tashin hankali bai bar gangar  jikin  aunty  shahida  ba ,da kyar  ta iya motsa labbanta  "yanzu   doctor zinnira  ta kirani   take  fad'a min wannan mummunar tashin
hankali alamarin nan ya  d'aure  min Kai  matuka ,
hakika  mutuwar  sadear  ya gigitani  jiya  fa  iwar haka muna  tare  daita  har  tana  cewa  zatayi magana mai mahimmanci  dani yau idan mun
had'u ko me  zata  fada  min ? ta   k'arasa  maganar idanunta na ciccikowa da ruwan  hawaye "gbdy  mutuwar  mubina ce ta dawo  min , Allah sarki rayuwa , Allah  ya  jikansu ya  tona asirin duk wanda yayi  sanadiyyar  barinsu duniya  , "duniyar  nan ma guda nawa take da zaka kashe dan'uwanka ?cewar  doctor sa'a  "ya  kamata  muje gidansu   yanzu ko ? "Eh ! wannan  gaskiya  ne ya kamata muje " da sauri aunty  shahida ta tattara abubuwanta dan bata   Jin  zata dawo asibiti  daga can gidan hajiya  zata  wuce doctor sa'a  ta  nufi  kofar  fita itama  aunty  shahida ta biyo bayanta da s auri ta rufa mata baya suka jera tana kokarin neman number doctor  zinnira  suje tare ."


"Kai  tsaye gidansu sadear    dake  ijora olopa
suka  nufa   a kofar  gidan  suka  iske 'yansanda   suna tambayar  aminu   yayan   sadear  yadda  abun ya kasance  "to ni dai bazan qarar da komai  ba , kawai  dai na  tashi da asuba  na shiga d'akinta  Inda take kwana tare da yarana guda  biyu  domin suyi sallah kawai   naga gawarta   cikin   jini  amman  babban yarona  sadi  yace  yaga  bayan matar Kuma ya ganeta   duk  da   jikinta lullube yake da  bakin  kaya  ba'a iya  ganin  komai   nata ".ya qarasa maganar Idanunshi  na  sauya kala." yauwa haka muke so yanzu    Ina  yaron yake ?  police  officer ya tambayi aminu yana gyara tsayuwarsa "  kan aminu  na kasa  hawaye  na tsiyaya daga idanunshi  cikin rawar murya  yace "yana  ciki   gida  " girgiza Kai  aunty  shahida  tayi  cike da  tausayawa masa   ,."

a tsanake  suka   gaisa   sannan     gbdy   suka had'a  baki  da doctor sa'a  da  dr   zinnira sukai masa gaisuwa   "aminu  ya  qarin  hakurinmu  Allah  ya  jikan sadear Allah  yayi  mata  rahma halinta na gari ya bita  "Ameen  ya   Allah , na gode  Allah  ya  bada  lada  "Allah  ya  tona  asiri duk wanda keda  sa  hannu  a kisan sadear  ya sake amsawa da" amen
na gode Kwarai da gaske yana kukan an cucesa an rabashi da yar'uwarsa tilo ,  a  lisafinsa  yanzu   tayi  awa hud'u  a  kabarinta   shiru yayi yana juya girman  alamrin zuciyarsa na zafin da bai san ranar dainawa ba ."

"Nan su aunty shahida   suka  barsu tsaye suka  shiga  cikin  gidan suka nufi  bangaren   yayan  sadear Inda  suka tadda  tsirarun  mutane zaune 
a  cikin d'akin ana karba gaisuwa  ,a natse  suka  gaisa  da mutane tare da yi musu  gaisuwa   suka  zauna  Inda  ake  ta jimamin mutuwar kowa  na fad'ar  albarkacin bakinsa  ,wasu  na cewa ai  hadiza ce ta kasheta tunda  daman  ta furta cewar itace zataga bayanta a bayyanan  nasi    ,yayinda wasu na cewa  ba  lallai  bane ya kasance itace ta kasheta ."
Suna  zaune  police officers suka shigo tare da
aminu da yaronsa  sadi dan kimani shekaru goma shabiyu yana musu bayanin wacce ya gani ."
'yansanda na  sauraron  yaron   daki daki gefe  guda kuma  suna  dudduba   gidan  a karshe suka tsaya a kofar   d'akinsu  hadiza   tare   da   tambayar   wacce   ake   zargi da aikata kisan ."


batare da 'bata lokaci ba akayi sallama a bakin kofar  d'akinsu, hadiza  kam  tunda taji sallama police  cikinta ya duri ruwa ta soma juya Kai zuciyarta  na  tsinkewa    dan tunda  akayi mutuwar take  cikin  tsoro da matsanacin  firgici mara iyaka gabadaya komai nata ya tsaya cak ."mahaifiyarta  ce  ta amsa   sallamar  tana fitowa daga  cikin  d'akin "muna son ganin hadiza ko  tana  ciki ?"."eh  ! tana ciki   ta fad'a muryarta na d'an rawa  "hadiza  ki fito ana son  ganinki  da  kyar hadiza  ta  fito kamar wacce  kwai ya fashewa aciki   ta tsaya a bakin kofar  d'akinsu , kana kallonta  zaka fahimci  a tsorace take , sai da suka mata duban tsanake sannan daya daga cikin police  din yace "kece  hadiza  ko ? ta  gyada masa Kai alamun "eh! gabanta na faduwa da sauri da sauri suka ce "muje akwai wasu tambayoyi da zamu miki a office dinmu ."

"akan wani laifi kenan?   mahaifiyarta  tayi 
karfin halin tambayarsu".  idan  muje office
dinmu   kwaji   akan wani laifi ne " suka  tasa  keyarta gaba mahaifiyarta   ta biyosu  da sauri 
tana cewa "bazan bari  ku tafi min da yarinya ba ku zubar mata da  mutunci  ba ." jin maganar  mahaifiyarta yasa  hadiza ta tsaya cak  taki  cigaba da tafiya police suka ce "muje ko!" "shiru  tayi  jikinta  na rawa  taki motsawa daga Inda  take   aiko daya daga cikin  yar sanda mace ta rike tsintsiyar hannunta "zaki   da girma da arziki ko kuwa mu tafi dake ta karfin tsiya  ? "cike da tashin hankali hadiza ta  fixge hannunta daga hannun yarsanda  tare da marairaice  fuska  kamar zatayi kuka "ni bazani koina ba har sai na san dalilin da yasa zaku tafi dani office dinku ". zata sake magana suka daura bakin bindiga keyarta "idan kika sake furta wata Kalma zamu sakar miki  wuta  mu tasheki aiki," oya  muje  "tsimi tsimi  hadiza ta soma tafiya  mutane  gidan na kallonta  cikin tsananin farinciki dan daman taadabi kowa acikin gidan  kowa tsoronta  yake ."

"wani mummunar tashin hankali   ya   shigi mahaifiyar  hadiza  da hadizan  karon kanta, ana  k'okarin turata cikin motar  'yansanda su aunty  shahida  suka  fito suka   kama   gabansu zuciyoyinsu   cike  da tsoro  da  fargaba ,direban  aunty shahida ya  sauketa a kofar gidansu  sannan  ta bashi   umarnin   ya kai  doctor   sa'a  da zinnira ya dawo, suka yi sallama da abokan aikinta  da  zumar  sai  sun had'u gobe , Jiki  a sanyaye  aunty shahida  ta  shiga  cikin tangamemen  falon mahaifiyarta  parlour'n   shiru babu   alamun  akwai wani  bil adama   acikinsa  hatta    'yan aikin  gidan bata  ji motsinsu  ba ."

Ta samu  guri  ta  zauna  jagwab  akan d'aya  daga cikin kujerun Parlour'n   tana sauke ajiyar zuciya har lokacin wani iri take ji ajikinta , shiru parlour'n   baka Jin motsin komai sai na AC  dake aiki a falon  .
ko cikakken    minti   biyar batayi ba ta fara Jin motsin mutane , ta d'ago a hankali  masu aiki ta gani cikin shigarsu ta kullum  dukkaninsu rike da farantin silver suka rusuna tare da had'a baki "barka da zuwa hajiya "barka sannuku  ya aiki ?"
"alhamdulillah !   suka amsa tare da ajiye tire suna tambayar abinda za'a kawo mata  " me za'a  kawo miki hjy  akwai rice and stew akwai tuwon shekafa akwai dabmu  shimkafa akwai ......? "duk  babu wanda zanci aciki ta fada tana runtse idanunta dan kanta wani irin sarawa yake kmr ana buga mata guduma  ,tana nan zaune hajiya zulaiheart ta shigo cikin shigar alfarma doguwar rigar lace  har kasa wanda kimanin kudinsa ya Kai 500k ta zauna akan kujera mai zaman mutun d'aya  tayi shiru  tana duban fuskar babbar diyarta "lafiya  shahida duk na ganki haka ?a hankali ta bud'e idanunta ta saukesu  akan  hajiya zulaiheart   "wallahi  mami wata mutuwa akayi mana agurin aiki mai shiga jiki ko ince an kashe yarinyar  ......"

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun oh ni zulai me mutane suka d'auki rayukan mutane ne yanzu
kashe mutun bai musu wahala ?"wallahi mami sai ma Kinga yayan yarinyar abun tausayi marayu ne babu uwa babu uba sai Allah abun daya fi d'aga min hankali yankar rago akawa yarinyar abun tausayi sam babu Imani a zukatan  wasu  mutane taya zan iya kashe mutun da hannuna ?ta karasa maganar hawaye na zubo mata."uhm  duniya  kenan  Allah dai ya tona asiri ko suwaye  suke bin ya'yan mutane  har gida suna kashesu to Kalli mutuwar mubina kigani abu kamar wasa har an kusan shekara biyu amman har yanzu babu labarin wanda yayi kisan."
Allah dai ya kyauta sam kasar nan babu tsaro shiyasa  nasa aka qara  tsaro mai karfi a gidan nan."

"hajiya ai ita sadear ana zargin makwafciyarsu ce tabi dare ta  kasheta yanzu haka maganar da nake miki tana hannu jami'an tsaro zasu fara bincike akanta  "alhamdulillah ai gara kam ita kuwa me yayi zafi haka ko akan me zata kasheta  ?mutumin  duniya   hjy ai  ba'a  iya mutumin  duniya sai Allah daya haliccesa, Allah dai ya sawaka kawai zamuce ."
"Ameen inji cewar hjy "wai  Ina maryam  da  auta suka shige ne ? sunje gidan zabiba amman dai
nasan zuwa la'asar idan anci sa'a babu traffic zaki gansu sun dawo " Anya kuwa zan jira har wannan lokacin ? bari kawai nazo na wuce  gida ."


"kin kuwa fada ma maryam   batun wannan sarkin zuciya ?"wallahi a'a jiya dai  nayi kokarin had'asu  gbdy a office dina  sai Kuma hakan bai yiwu ba ga yau ma ,Ina ganin sai dai weekend  zanzo  dan gbdy  jina nake wani iri, wallahi  mutuwar nan  ta shigeni  yarinya mai kirki da biyyaya  da sanin ya kamata  sam sadear bata da matsala a rayuwarta  sannan bata da abokin fada kowa nata ne agurin aiki  ga wasa  da  dariya ga ..."kira ne ya shigo wayar aunty shahida wanda yayi sanadiyyar katse mata magana  ta d'auka tana duba screen din wayar  direbanta  ne mlm garba  dan  haka ta mike  ta d'auki jakarta tayi wa hjy zulaiheart sallama ko a gidanta  ma kasa tabuka komai tayi babbar  yarinyarta madina duk  ta damu sai  faman tambayarta take ta fada abinda ke damunta bata ,boye mata komai ba ta fada mata mutuwar , mutuwar tsaye madina tayi dafe da qirji dan tasan sadear sosai tana janta ajiki idan taje gurin mamanta ,addua tayi mata hawaye na zubawa aunty shahida lokacin da take tuna moment dinsu da yarinya babu abinda yafi daga mata hankali kamar maganar da tace zasuyi a yau din gashi ta mutu batare da san ko akan me zata mata magana ba kwarai  taso tasan ko akan meye , Allah sarki rayuwa  kenan ta dade zaune tana jimamin mutuwar sadear   kafin daga baya ta mike ta shiga dakinta ta kwanta zuciya da gangar jikinta na mata ciwo    .."

Har  yansanda  suka karasa office dinsu  kuka hadiza take , aka  nufi d'akin  bincike daita aka nuna mata gurin zama sannan  bayan kamar awa daya wasu qararrun 'yan sanda suka shigo nan suka fara Aiko mata da tambayoyi d'aya daga cikinsu tace  "ko zamu iya sanin dalilin da yasa kika kashe  makwafciyarki sadear ? hadiza taji tambayar tamkar saukar aradu
take idanun  sukayo waje  tare da dafe qirjinta "wallahi  bani na kasheta ba nima tashi nayi naji labarin mutuwarta ,"karki wahalar da hukuma zai fiyye miki sauki ki fito ki fada mana gskiya kunyi fad'a da sadear ko ba haka ? cikin tsananin firgici da tsinkewar zuciya tattare da tsoro ta  gyada Kai  alamun "Eh!"can km  ta girgiza musu  Kai alamun "a'a!   police ta gyada Kai sannan ta cigaba "kenan kina nufin babu wata matsala ko fada wacce tasa kukayi sa'insa daita ? nan ma ta gyada Kai alamun babu cikin kankanin lokaci ta fita haiyacinta saboda  tambayoyin  da suka dinga mata tana  kare  kanta   a karshe daya daga cikin police mace tace ' kinyi furucin zaki kasheta Kuma kinyi nasara ko ba haka ba ?ta girgiza kanta alamun a'a juyin duniya akayi da hadiza amman  ta tsaya akan ba itace ta kashe sadear ba  suka  barta tare da turata  wani d'aki tana shiga taji an rufeta da duka cikin kankanin lokaci kamanin   hadiza ya sauya tayi laushi  sosai tana ihu tana Komai aka shiga daita wani daki aka garkame . tayi kuka sosai idan ka ganta sai ta baka tausayi gabadaya ta tabbatarwa kanta tata takare Ina ma batayi fad'a da sadear ba ,a she da me kararen kwana tayi fada ? wayyo Allah ni hadiza kaicona me ya kaini fada da gawa  ....?yau dai ga Inda karshen wahalana ya kawoni ni hadiza nayi nadama   ,nayi danasani ban bar yara ba ,ban bar  manya ba ,ban bar matan aure ba, ban bar tsofafi  ba , ga dai karshena ban san me gobe zata haifar ba  ta karasa maganar tana matso ruwan hawaye mai zafi daga idanunta ."



Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
   MAR'ADAMS
   💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
Arewabooks username
Ayshabagudo
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page5

" da  misalin karfe   tara  na daren ranar Juma'a mr ATA ya fito daga bathroom jikinsa sanye da  rigar wanka iya gwiwarsa yayinda hannunsa  d'aya ke rike da white towel yana goge kanshi  zuwa  wuyansa ,ahankali ya  qarasa  gaban mirrow ya tsaya  yana kallon  kyakkyawar  fuskarsa  yana qoqarin zare  rigar jikinsa ."shiru yayi yana kallon faffad'an qirjinsa dake  kwance da  laulausan suma tamkar na jariri sabuwar  haihuwa ga Kan nipple's dinsa a tsaye makale da  qirjinsa sai sheki suke, babu lafiyayyar macen da zata gansa a haka bataji sha'awarta ta motsa ba  saboda kyawun cikar halittar da allah yayi masa ."

kusan minti goma ya dauka tsaye  yana qarewa kansa kallo kafin  daga bisani ya juya  a natse ya koma  bathroom ." ko  cikakken  second  uku bai yi ba ya fito  ya  d'auki  kwalbar bodyspry ya feshe ilahirin  jikinsa ya saka white singlet

Please Login or Register in order to submit comment