Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com For feedback and support Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ Telegram : https://t.me/NovelsHQ *****Matar khalees***** ✍️Alkalamin Nusaiba ibraheem rimi(Nusy bee) بسم الله الرحمان الرحيم Part 1 Matashiya ce wadda bazata gaza shekaru ashirin da biyar zuwa da bakwai ba, kyakykyawa ce wankan tarwada,tana sanye da golden lace riga da zani,ta yafa babban mayafi tun daga kanta,cikin takun ta na nutsuwa ta nufi bakin motar ta dake ma'ajiyar motoci ta kamfanin nasu Muryar barrister Zee taji tanayi mata magana, Barrister Zee matar engineer Jabir wato mammallakin kamfanin,waigowa tayi fuskar ta cike da faraa ta qarasa kusa da zee suka tafa da raha irin ta qawaye, zee ta dube ta tace "Su DEEJA manyan mata!sau hudu Ina shigowa kamfanin nan bana samun ki,yau ma Allah ya taimake ni" Deeja tayi murmushi sannan tace"to zee me zan zauna nayi bayan na gama aiki na?dole na rinqa komawa da wuri,kin san ɗan rigimar nawa fa" "Gaskiya kam deeja,ai rayuwar Sai haquri kawai"a cewar Zee "Uhm!hakane,ni bari na wuce gida,Sai mun sake haɗuwa"a cewar deeja tana ƙoƙarin bude motar ta "Okay!ki gaida gida"a cewar Zee,sannan ta juya ta nufi cikin kamfanin Kamar yadda ta Saba yau ma bata tarar da KHALEES a gidan ba,hakan bei bata mamaki ba,Kai tsaye bandaki ta fada tayi wanka,bayan ta fito kaya kawai ta zura tayi sallah sannan ta zauna a gaban madubi ta fara kintsa kanta Muryar engineer khalees taji,da alamu ya dawo,ta Dan saurara,ga dukkan alamu waya yakeyi,Don haka batayi gaggawar fitowa ba,ta cigaba da abinda takeyi,tana jinshi ya shige dakin shi Bata fito ba Sai da ta kammala Shirin ta tsaf,cikin riga da skirt na lace orange colour,tayi kyau sosai,kanta Babu Dan kwali Sai mayalwacin gashin ta da ta tufke da ribbon kalar kayan jikin ta,Kai tsaye dakin khalees ɗin ta nufa Da sallama ta shiga,yana zaune a bakin gadon yana latsa waya,ya amsa batare da ya kalle ta ba,bata damu ba ta zauna gami da fadin "sannu da dawowa" Sai da ya bata lokaci sannan ya amsa da "yauwa" Batayi zuciya ba,don idan da sabo ta saba,tace"na hada maka ruwan wanka fa" "Naji"ya bata amsa har yanzu idanun shi Yana kan wayar shi Ta ƙara da cewa "na Kai maka abincin dinning ko na kawo maka nan?" Wannan karon ya dago ya dube ta,amma duban wulakanci yace"duk yadda kika gani,Kinga malama surutun ki ya ishe ni" Batayi fushi ba,Don ta Saba da halin shi tace " I'm sorry"bata jira amsar shi batayi waje Sai a lokacin khalees yabi hanyar da tabi da kallo na ƴan daƙiƙu Kamar wani Mai nazari,zuwa can yaja ajiyar zuciya kafin ya miƙe ya nufi banɗaki Tana zaune a falo tana danne danne a laptop ɗinta ya shigo falon,yadda yayi sallama batare da ya kalle ta ba haka itama ta amsa batare da ta kalle shi ba,bai damu ba yace "Ina abincin nawa?" "Gashi can na kammala shirya maka a dinning"ta bashi amsa,har yanzu kanta na ga laptop ɗinta,hakan bei dame shi ba ya nufi dinning set din ya zauna,ya zaro waya ya kama latse latse Ta tabbatar bazei taba serving kanshi ba,hakan ne ya Sanya ta miƙewa ta nufi dinning ɗin tayi serving ɗin shi,yana ta danne dannen shi har ta kammala,tana kammalawa ta wuce ta cigaba da aikin ta Deeja kenan,MATAR KHALEES!duk tarin ƙalubale da damuwowin da ta haɗu dasu a rayuwar ta hakan bai hana ta neman na kanta ba,Kuma tana matuƙar kama kanta a duk halin da ta riski kanta A shirye take tsaf cikin doguwar riga light blue Mai adon duwatsu,ta naɗe mayafin rigar a kanta,cikin sauri take gudanar da Shirin ta don ta ɗauko hanyar makara,a main parlor ta riski khalees,batayi jinkirin gaishe shi ba Amma ko kallon banza bata Samu ba,Sai ma gyara agogon shi da ya cigaba dayi yana tafiya a cikin isa irin yadda ya saba,bata ƙara bi ta kanshi ba ta ɗauki hanyar waje abinta "Ina zuwa?"taji muryar shi Juyowa tayi cike da mamakin tambayar rainin hankalin da yayi mata,Ina zuwa kuma?bai san tana fita ba dama?Amma Sai ta daure tace "Wajen aiki zan je" Sai da ya bata lokaci sannan ya kalle ta "Anyway!yau duk inda 1:00 pm tayi ki tabbatar kina gida,ki shirya Mana abinci don zanyi baƙi"yana Kai wa nan ya kewaye ta ya fice batare da yaji ta bakin ta ba Itama rufa Masa baya tayi suka fito zuwa harabar gidan,shi ya nufi motar shi ƙirar BMW,ita Kuma ta nufi motar ta ƙirar anaconda Tuƙi takeyi Amma tunani fal ranta,ƙwalla na neman zubo mata,amma tana ƙoƙarin dannewa,gaba ɗaya rayuwar ta tun tana ƴar ƙaramar ta take haɗuwa da wahalhalu dabam dabam,zata iya cewa bata taɓa jin daɗin rayuwar ta ba,a fili ta furta "Gaskiya duk wanda ya rayu babu uwa to da sauran shi a farin ciki" Ta tuna ummu,uwar riƙon ta, Imran masoyin ta,ga khalees mijin ta,hajiya uwar mijin ta,da su farida ƙannen shi,duk mutanen nan Babu wanda take jin daɗin shi Jin ƙirjin ta ya fara motsawa ya Sanya tayi gaggawar kawar da wannan tunanin a ranta,domin ko da wasa bata ƙaunar ciwon zuciyar ta ya tashi Ƙarfe takwas saura minti biyu ta shiga office ɗinta,an gyara shi tsaf, ta nemi waje ta zauna ta harɗe yatsun ta ta tokare haɓar ta gami da yin Shiru,tamkar Mai yin nazarin wani abu,ba komai take tunani ba illa mafita a rayuwar ta,ta kasa gane mei mutane suke nema da rayuwar ta,musamman mijin ta da ta kasa gane kanshi,duk hanyoyin da take tunanin masu bullewa ne tabi amma babu nasara,gaba ɗaya kanta ya kulle,gata ba ƙawaye ta cika ba Koda ace tana da ƙawayen surutu bai dame ta ba,balle har ta sanar wa wani taji sanyi Abban ta ne ya faɗo mata a rai,a lokacin da yake raye shine abokin shawarar ta,bata manta wata rana a lokacin da tana gidan Imran, wani zuwa da tayi gida yaga yanda ta rame yace "Khadija,ko da Baki gaya min halin da kike ciki ba nasan kina cikin matsananciyar damuwa,nasan cewa ke mai haƙuri ce,amma Ina so ki sani shi haƙuri baya yawa Sai dai yayi kaɗan,don haka ki cigaba da haƙuri Allah Yana tare dake" Tace"babu komai abba in Sha Allah zaka same ni Mai biyayya,bazan baka kunya ba" Allah yayi miki albarka"a cewar abban nata Doguwar ajiyar zuciya ta ja bayan ta dawo daga tunanin daidai nan taji an ƙwanƙwasa ƙofar,ta bada izinin a shigo Sa sallama sakatariyar tata ta shiga,ta amsa fuska a sake,a ladabce sakatariyar tata tace "Madam oga na neman ki" "Okay gani nan fitowa"ta bata amsa Tana fita itama ta miƙe ta fice zuwa office din MD ɗin nasu Batayi mamakin ganin khalees a office ɗin ba,sai dai yadda beiyi mata kallon sani ba itama haka,ta samu waje ta zauna,bayan sun gaisa ya dube ta yace"madam ya ake ciki game da aikin da na baki?" "Ai na kammala tun jiya" "Okay idan babu damuwa ɗauko mini su" "Okay sir!"ta fada gami da miƙewa ta nufi hanyar fita daga office ɗin Jim kaɗan ta dawo riƙe da takardu a hannun ta,ya amsa ya duba,ya kalle ta da murmushi yana fadin"very nice madam" "Thank you sir!"inji ta Wasu takardun ya miqo mata a files yana fadin "ga wani aikin nan da fatan Shima zai kammalu da wuri" "In Sha Allah"ta fada gami da amsar takardun ta nufi waje Sha biyu da rabi daidai ta miƙe ba don ta kammala aikin ba sai don umarnin khalees,Amma dai dai taci ƙarfin aikin,ta miƙe ta fito don rufe ƙofar office ɗin,sukayi sallama da sakatariyar ta ta nufi motar ta ta tayar ta ɗauki hanyar gida #Nusy_bee *****Matar khalees***** ✍️ Nusy bee Page 2 Cikin sauri tayi wanka tayi sallah sannan ta shiga kitchen,farar shinkafa ta ɗora da miya sannan ta tayi papper chicken ɗin ta lafiyayye sannan tayi coconut juice,duk a cikin Abinda bei kai awa ɗaya da rabi ba ta kammala,ta jere su a dinning,cikin sauri sauri ta gyara ko'ina ta sanya turare gidan ya ɗauki ƙamshi,ta koma ɗakin ta tayi wanka ta shirya zuwa riga da skirt na atamfa ta ɗaura ɗankwali akanta ta zauna a bakin gadon tana mayar da nunfashi Ta kai mintuna goma a zaune tana chatting taji sallamar su,sai da gaban ta ya faɗi saboda jin Muryar shi,tabbas shine ba amsa kuwwa bane,da sauri ta miƙe ta leƙa ,ga mamakin ta har da Yaya fauwaz,da sauri ta koma ta faɗa kan gado,gabanta yana dukan uku-uku,kanta ya fara sarawa,cikin rawar murya ta furta"wannan mummunar sakayyar taka ta ishe ni haka Imran" Wayar ta ce ta katse ta,da sauri ta duba, khalees ne,ta san kiran me yake mata,da sauri ta janyo hijabin ta ta sanya ta miƙe ta nufi falon Da sallama ta shiga,dukkan su suka ɗago suka amsa,a kallon da tayiwa Imran ta gano tsantsar mamakin da yake yi,wanda bata raba ɗayan biyu mamakin ganin ta a matsayin MATAR KHALEES yake yi,ita dai batayi ƙasa a gwiwa ba wajen gaishe su ba,su shida ne, banda yaya fauwaz da Imran,sai ragowar su huɗu da bata san su ba,suka amsa cikin fara'a, fauwaz ya dubi Khalees cikin tsokana yace "Iyyeeee!ashe kaine kayi wuf da ƴar ƙanwar tamu shine ko mu sani?"ya dubi deeja yace"Dijangala ba'a sanar mana ba ko?ko da yake nasan fushi akeyi damu ko?" Tayi ɗan murmushi tace"I'm sorry banyi gayyata bane,Kuma yazo a gaggauce shiyasa" "Babu damuwa, Allah ya sanya alkhairi"inji shi Ta wuce kitchen tana fadin"ameen,na gode" Cikin ƴan mintuna ta gama halarto musu abincin,sannan ta juya ta shige ɗakin ta Tana kwance tana jiyo hirar tasu sama sama, zuciyar ta na suya,tunani takeyi me ya haɗa Imran da Khalees?wace iriyar mu'amala ce ta haɗa su?ko dama can sun san juna?kai bei zama lallai ace sun san juna ba,don da ace sun san juna Imran zei taɓa bata labarin shi watarana,amma bata taɓa jin labarin shi a bakin Imran ɗin ba,to me haɗin su dashi yake nufi? "Tabbas da wata ƙulalliya a ƙasa!"ta faɗa da raunin murya,idanun ta na kawo ƙwalla Ta ɗaga hannun ta sama tace "ya Allah ga bayin ka nan,idan har da wani abu suke nufi na Allah ka tseratar dani,su kuma ka ganar dasu" Tayi saurin goge hawayen da ya taru a kwarmin idanun ta suke ƙoƙarin zubowa,wayar ta ta janyo ta buɗe data suka cigaba da hira da aunty kiyya akan bikin Yasmin Wayar ce ta soma ruri,sunan aunty Bintu ne taga yana yawo akan fuskar wayar,da sauri ta ɗaga da sallamar ta, cikin farin ciki take faɗin"aunty Bintu yau a gari?" Daga ɓangaren aunty Bintu tace "kya tambaya mana,ke da bakya neman mutane" Tayi ƴar dariya tace "ayya!am sorry aunty,yasu ilham da salim?" Suna nan lafiya,wai da gaske ne kinyi aure?"a cewar aunty Bintu "Deeja ta ɗan yi shiru na ƴan daƙiƙu kafin tace"haka ne aunty,anyi aure na watanni huɗu baya" Aunty Bintu tace"Amma da mamaki Deeja,kinyi aure baki sanar dani ba,ko Mima ma baki sanar mata ba?" "Uhm abinda Yaya fauwaz ya gama ce min kenan, wallahi aunty ba da shiri akayi auren ba,kawai lokaci yazo a haka" "Haka ne kam!"inji aunty Bintu"shi aure lokaci idan yazo a lokacin shi sai anyi shi ko an shirya ko ba'a shirya ba,fatanmu dai Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitinar shaiɗan" "Ameen"Deeja ta amsa cikin sanyin Muryar ta "Kinsan da bikin Yasmin ko?"aunty bilki ta tambaye ta "Eh na sani,Yasmin da hudan momy Aisha sun kawo min invitation card,Kuma tun kwanaki can ita Yasmeen din ta turo min hoton ankon ta WhatsApp" "To shikenan,mu ma sun aiko mana da gayyata,don haka zamu zo,itama Mima next week zasu taso daga Malaysia Cikin ɗoki Deeja tace"wayyo daɗi!da gaske don Allah aunty?" "Wallahi kuwa,da jibi zasu taho,wasu uzururruka ne suka tsare su,amma in Sha Allah nan da five days zasu taho" "To Allah ya kawo su lafiya" "Ameen,me kika tanadar musu ne?wannan zumuɗi haka?" Ƴar dariya tayi sannan tace"wallahi aunty nayi kewar Mima ba kadan ba,ga yaran ta masu shiga rai musamman ma mei suna na Khadija Mee'ad" Dariya sosai aunty Bintu tayi tace"lallai,kiji ki da son kai" "Ba son Kai bane aunty,Ina son yarinyar ne sosai" "To da kyau,saura ke kema" "Aunty Bintu lokaci ne,fatan mu Allah ya kawo masu albarka" "Ameen ya Allah,sai anjuma,ki gaida mai gidan" "Okay zaiji"daga haka suka ajiye wayar Farin cikin zuwan su Mima ya danne damuwar da take ciki,don tasan Mima ko banza zata bata shawarwarin da zasu rage mata damuwa,don Mima wayayyiyar gaske ce sosai,kuma tafi Deeja shiga mutane sosai,hakan ya sanya ta karanci dabiun mutane da yawa Tana jin sanda su Khalees suka fita,sun kwashi a ƙalla mintuna goma da fita,don taji tashin motocin su,sai a lokacin ta fita don kwashe kayan da suka kammala cin abincin,ta kimtsa wajen Ko da Khalees ya dawo ma bei nuna mata komai ba,itama bata tambaye shi komai ba,don tasan bazai taɓa bata amsa ba Da daddare tana zaune tana danne danne a laptop,lissafe-lissafe takeyi na kasuwancin ta,na wani babban shopping mall da ta buɗe, Khalees ne ya shigo da sallama,ya dube ta da fuska babu annuri yace"gobe su Hajiya zasu zo,don haka ki zama cikin shiri"yana gama magana bai saurari cewar ta ba ya wuce zuwa ɗakin shi,a ranta ta furta"oh!wata damuwar dai zan riska na sani" Washe gari da safe babu aiki,don haka a nutse take gudanar da aikace aikace-aikacen ta,tabi ko'ina ta share tas har ɗakin Khalees,batayi tunanin ɗora girki ba,don ta san halin Khalees ba tun yau ba,baayi masa gwanin ta,don sai ta girka yace bazai ci ba,don haka water kettle kawai ta jona ta tafasa tea ta Sha da cake,ta koma kan computer ta cigaba da lissafin ta **** **** **** Cikin sauri take shiri don ta bar su salma jira,riga da skirt ta sanya waɗanda suka ji wani matsiyacin ɗinki,gaba daya jikin ta a waje,gaba ɗaya jikin ta a waje,ko budurwar mutunci bazata iya sanya Waɗannan kayan ba ballantana ita matar aure,ko ɗan kwali bata sanya ba sai wani yalolon mayafi da ta sanya kalar atamfar,sannan ta ɗauko purse dinta ta fito,tana rufe ƙofar kira ya shigo wayar ta,da sauri ta duba,kamar yadda tayi tsammani Yaya najeeb ne,tana ɗagawa tace "hello yaya najeeb" "Haba sister!tun ɗazu nake jira,me ya hana ki zuwa ne?" "I'm sorry bro! wallahi al'amuran bikin Yasmin ne ya sha kanmu shiyasa kaji ni shiru,amma in Sha Allah ko da yamma ne zan leƙo gidan,ba dai Ni nace zan zo ba?" "So why not bazaki zo yanzu ba?" "Saboda akwai abubuwan da zamu siyo yanzu mu da su salma,sai anjuma zamu dawo,kai tsaye gida zan wuto in Sha Allah" "Okay to Allah ya kawo ki lafiya" "Ameen,bye bye!"ta kashe wayar A motar afra ta tarar dasu,afra na mazaunin driver sauran kuma suna baya,wato gaba wajen mai zaman banza ya tashi a matsayin mazaunin ta kenan,ta shiga tana fadin "oh sorry na bar ku jira ko?" Zakiyya ta kalle ta sheƙeƙe gami da taɓe baki,afra kam murmushi tayi tana faɗin"sister kenan,kina wuta" Tayi wani malalacin murmushi tana cigaba da danna waya,lubaisa kam kasa daure wa tayi,ta dube ta cikin ɗaurewar fuska tace "Amma UMAIMA sai nake ganin kamar wannan shigar bata dace ba a matsayin ki na matar aure ko?" A watse umaima ta kalle ta,sai dai tun kafin tace komai zakiyya tace "oh lubaisa ina ruwan ki?ita ƙaramar yarinya ce da za'a ce bata san me ya dace ba?" "Ai kawai tsabar shegen shishishigi ne da hassada"a cewar afra,wadda dama tuntuni basa jituwa da lubaisa Lubaisa na shirin sake magana nuwaira dake kusa da ita tayi mata nuni da tayi shiru,dole tayi shiru gami da zaro wayar ta ta kunna music ta dasa a kunne,don irin surutan da afra take cigaba da yi Shopping mall suka nufa inda zasu yi siyayyar bikin,a bakin mall ɗin wayar afra ɗauki ƙara,ta ɗauko ta duba,ganin wadda take kiran nata ne tayi saurin ɗagawa,bayan sun gaisa take sanar da ita cewa ta shirya,sati mai zuwa zata zo don bikin Yasmin,cikin farin ciki afra tace"to ƙawa ta Allah ya kawo ku lafiya,muna waiting" "Ameen, Sai nazo"sukayi sallama Afra ta kalli umaima da murmushi a fuskar ta ta tace"umaima be ready,muna da babbar baƙuwa,wannan likitar da nake baki labari mun haɗu daita a ƙasar Lebanon,kin gane ta?" Umaima tayi murmushi tace"eh na gane ta" "Yawwa!itace zata zo bikin Yasmin,da alama bikin nan zai yi albarka" #Nusy_bee *****Matar Khalees***** ✍️ Nusy bee Page 3 "Sosai ma kuwa afra,Ni kam zan so in ga wannan matar"a cewar umaima "She is very nice umaima,ga yaran ta guda biyu masu tsananin kyau,mijin ta kuwa akwai class,ba irin abban haneef ba" Umaima ta kwashe da dariya,daidai nan afra ta kammala parking suka fito, umaima ta kalle ta tace"a'a afra,ko dai kin ƙyasa ne na fara taya abban haneef kishi?" Afra tayi ƴar dariya tace"a'a wallahi,shi abban haneef kamar shashasha yake,kowa kawai buɗe masa haƙora yake,ban samu kwanciyar hankali ba sai da na raba shi da Wannan matsiyaciyar yarinyar fa kina gani" Umaima ta taɓe baki,suka jera suka nufi cikin mall ɗin suna cigaba da hira, afra na koɗa kyau da jan aji na mijin ƙawar ta likita Sai wajen ƙarfe uku suka gama siyayyar suka ɗauki hanya,amma sai umaima tace a sauke ta a gidan su Haka kuwa akayi,suka sauke ta sukuma suka wuce gida Da sallama ta shiga cikin gidan,a falo ta iske su umma,har da najeeb ɗin,da sauri najeeb ya taso ya rungume ta yana faɗin"lovely sister oyoyo!" Umma ta kalle su cikin rashin jin daɗi tace"haba najeeb!da auren ta fa!" "No umma!ba ƴar uwata bace?"yayi saurin katse ta Daga haka tayi shiru bata sake magana ba, najeeb ya dubi umaima yace"ki ci abinci zaki raka ni gidan wani aboki na" "Okay!"ta bashi amsa,ta dubi umma tace"umma akwai abinci ne?" "Eh akwai,bari in kawo miki"umma ta miƙe ita kuma umaima ta zube akan kujera don hutawa **** **** **** Tun azahar ta kammala komai,har abin taryar baƙin nata duk da cewa ba baƙin farin ciki bane,ta gyare gidan tsaf,tunda safe da taga Khalees bata sanya shi a idanun ta ba,hakan bei dame ta ba don ganin nashi babu abinda zai tsinana mata, wataqila ma ta samu ƙarin takaici Ƙarfe uku da mintuna goma taji ƙarar gate,da alama su hajiyar ne suka iso mei gadi yake ɗage musu gate ɗin,dam!taji gaban ta ya buga,da sauri ta dafe ƙirjin ta tana fadin"allahumma laa sahla illaa maa ja'altuhu sahla wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahla" Tana leƙen su ta window,har suka fito daga motar su,su huɗu ne, hajiyar,sai farida da jannat,sai direban su da ya tsaya a wajen malam Audu mei gadi Da sallama suka shigo cikin gidan,a zaune suka same ta a falon tana jiran isowar su,da sauri ta miƙe tana ta faman fara'a,ta gaishe su ɗaya bayan ɗaya,duk da cewa su jannat ƙannen Khalees ne,kuma ko itama ta girme su,amma hakan bei hana ta gaishe su ba,don ta san cewa su baza su taɓa gaishe ta ba Hajiyance ta amsa, fuska babu yabo babu fallasa,sai jannat,amma ita Farida kallon ta tayi sheƙeƙe ta maida kai ga wayar hannun ta,da alama chatting takeyi Bata kula ba,sai ma cima data jere musu a gaban su tana jansu da hira, hajiyance kawai mei amsa wa,sai jannat sama-sama,amma Farida ko uhum bata ce mata ba Hajiyance ce ta dube ta tace"am dama ba wai zama nazo yi ba,nazo ne in sanar dake cewa jibi in Sha Allah su Farida da zasu dawo gidan nan da zama da zama,don haka sai ki shirya,na riga na sanar da yaron nan (tana nufin Khalees)tuni,don haka sai ki zauna da shiri" ta ƙarasa faɗa tana miƙewa tsaye Wani irin jiri Deeja ta rinqa ji,amma da yake jarumar mace ce ta dake tace "to Hajiya, Allah ya kaimu jibin" Hajiya ta amsa da "ameen" Deeja tace"Hajiya baku ci abincin ba ma" "A'a mun ƙoshi wallahi,zamu tafi"bata jira cewar Deejan ba tayi gaba,suma yaran suka biyo bayan ta, Deeja bata da zaɓin da ya wuce bin bayan su,ta rako su har bakin motar su Bayan sun tafi komawa ɗakin ta tayi ta ɗaga waya ta kira zakiyya,a lokacin dawowarsu kenan daga shopping mall da suka fita, shigowar ta sashen ta kenan,ko zama batayi ba,sai ga wayar Deeja ta shigo Da sauri ta ɗaga tana faɗin"Hello! Deeja manya" Yanayin Muryar Deejan ya fahimtar daita cewa ba lafiya ba,tace"Allah yasa dai lafiya" "Uhm! aunty kiyya bari kawai,ina cikin damuwa sosai" "Kina bari na ɗan yi uzuri,zan kira daga baya" "Okay I'm waiting"daga haka komawa tayi ta kwanta a rigingine,zuciyar ta nayi mata zafi,ta lumshe idon ta,ta kai mintuna goma sha biyar a haka kafin taji kuwwar wayar ta,ta buɗe idanun ta ta miƙa hannun ta a kasalance ta janyo wayar,ta ɗaga "Hello ina jin ki" Deeja tayi ajiyar zuciya sannan tace"bari kawai aunty kiyya,ina cikin tashin hankali da taraddadi" "Me ya faru kuma?"kiyya ta tambaya tana gyara zama A hankali ta warwarewa zakiyya komai, cikin mamaki da kaɗuwa zakiyya take gyaɗa kai,zuwa can tace "Deeja,ki cigaba da haƙuri,haka Allah yaso dake,ki sani duk mutumin da kika ga Allah yana ta jarabtar mutum ta Allah yana son shi,don haka ki cigaba da haƙuri, akwai lokaci,ki saurari zuwan yaran kawai,ko me zasu yi kar ki kula su,ki kama kanki kawai,in Sha Allah zaki ga ribar abin, kuma ma Allah na tuba abin kwana nawa ne? 'yan mata ne fa,aure zasu yi" Jikin Deeja yayi sanyi,taji sauƙi a zuciyar ta, cikin wata kasalalliyar murya tace"in Sha Allah aunty kiyya zan kiyaye" "Well!yaushe zaki zo bikin ne?ko sai anzo dab?" Murmushi mai sauti Deeja tayi,tace"Kai aunty!Sai kace wani gari dabam?"dariya aunty kiyya tayi tace"sai mun ganki dai" "Okay na gode aunty kiyya" "Nima na gode"sukayi sallama Ai kuwa bayan kwana biyu ta dawo daga aiki ta samu motar su fareedan a harabar gidan,sai da gaban ta ya faɗi,amma da yake mace ce mei kamar maza sai ta dake,ta shiga falon da sallama Dukan su suna zaune sun kunna TV suna kallo,suka ɗago suka kalle ta suka watsar,ta nuna kamar bata san sunyi ba,tace"sannun ku da zuwa"da ƙyar jannat ta amsa da cewa "Yawwa kema sannun ki"bata damu ba ta kewaye su ta shige ɗakin ta,tana jin Farida na jan dogon tsaki,amma ko kallon sashen da take batayi ba,ta shige ɗakin ta Bayan tayi wanka tayi sallah ta fito ta nufi kitchen,bisa mamakin ta sai ta tarar babu abincin sai warmers ɗin nata da akayi mata wancakali dasu,ta shiga bin ko'ina da kallo, girgiza kai tayi kawai, sannan ta fara kwashe kwanukan tana tattare su a water sink,ta wanke su tas ta maida su ma'ajiyar su sannan ta share kitchen ɗin sannan ta ɗora jollof ɗin Talia,don tasan Khalees yana hanya, gashi kuma babu abinda zasu ci ita da Khalees ɗin Cikin azama ta dafa talia jollof da kifi taji kayan lambu, cikin ƴan mintuna gidan ya ɗauki ƙamshi,ta haɗa lemon mangwaro ta sanya a fridge,ta ɗibar wa su Farida itama ta ɗiba,ta zubawa Khalees nashi a warmer ɗin shi #Nusy bee *****Matar Khalees***** ✍️Nusy bee Page 4 Babu komai a fuskar ta ta miƙa musu,ko kallon mutunci bata samu ba,itama bata damu ba,ta ɗauki nata ta shige ɗakin ta Sanda Khalees ya dawo tana jin su,suna ta hira da ƙannen shi,bata kula su ba sai da taji ya shiga ɗakin shi,da alamu wanka zai yi,ta fito ta jere kayan abincin a dinning area,ta shiga ɗakin shi don yi masa sannu da zuwa Har lokacin Khalees yana banɗaki bei fito ba,ta zaro masa kaya marasa nauyi na zaman gida ta ajiye masa a bakin gado,tana gamawa ta miƙe ta fice daga ɗakin Tana cikin ɗakin ta taji Muryar shi,ta fito tayi masa sannu da zuwa,ta sha mamakin amsawar da yayi fuska a sake, amma bata bar hakan ya bayyana akan fuskar ta ba,kuma ta alaƙanta hakan da wanzuwar su Farida a falon,don ta juma da kula cewa basa iya kawo mata raini a gaban shi "Idan ka shirya ga abincin ka nan a dinning"ta faɗa cikin kwantar da murya "Dama shi na fito nema,bari in ci tukunna"ya nufi dinning ɗin,ita kuma ta koma cikin ɗakin ta Da daddare suna zaune a cikin ɗakin nashi ta dube shi cikin kwantar da murya tace"am dama Ina son yin wata magana da kai" Ya ɗan kalle ta sannan ya maida kanshi fuskar wayar shi yace"ina sauraron ki" "It is better ka ajiye wayar nan,don kafi fahimta ta ko?"ta faɗa cikin kwantar da murya Wani matsiyacin kallo ya watsa mata sannan yace"ashe?har kina da maganar da take da muhimmancin da zata sanya ni ajiye waya?"ya faɗa har yanzu idanun shi na kan fuskar wayar shi Shiru tayi bata ƙara magana ba,shima shirun yayi, tsawon lokaci ganin bata da niyyar magana sai ya kashe data ɗin shi ya dube ta yace"ya ake ciki ne?"wacce magana ce take tafe dake?" Shiru tamkar bata ji ba,sai da ya maimaita tambayar, cikin kasalalliyar murya batare da ta kalle shi ba tace "Dama kan batun bikin ƙanwa ta ne" "Ehen,me kike so nayi miki?"ya faɗa yana kallon ta "Kasan tun ana igobe ko jibi za'a fara bikin nake so naje,to yanzu yaya zan yi da su Farida?" Da sauri ya kalle ta cikin mamaki,yace "su Farida mana" "Eh su Farida mana"ta bashi amsa tana kallon shi Cike da mamaki ya gyaɗa kai sannan yace"to nono zaki basu kenan?" Kallon shi tayi cikin mamaki tace"a'a ba batun haka bane,bei dace ace mun bar su a gida ba su kaɗai, Hajiya ma bazata ji daɗi ba,amma idan babu matsala sai in tafi ɗin" "Babu"ya bata amsa a taƙaice,sannan ya juya ya kwanta,itama kwanciyar tayi,duk da ba bacci takeyi ba,kawai nazarin rayuwa takeyi Washe gari basu tashi daga bacci ba sai da ta kammala girki,tana ji Khalees yana tayi musu faɗa,ita dai sauri takeyi don ta tsani makara a rayuwar ta,kunun gyaɗa ta dama da ƙosai sai plantain da miyar ƙwai,sai wainar ƙwai da chips,sai ruwan Lipton Ko da Khalees baya yaba mata a fili,yana matuƙar jinjina baiwar iya girki, tsafta da hikima da Allah ya bata,gashi sam bata gajiya, kullum cikin hidima dashi take ko da ace zai kashe ta kuwa Suna cikin cin abincin ya kalli Farida yace"yau ƙarfe nawa kuke da lecture?"ta amsa"nine zamu shiga lecture" Ya kalli Jannat yace"ke kuma fa?" Ta amsa "by 12:pm" "Good!"ke Farida, kafin ki fita daga gidan nan ki tabbatar kin gyara wajen nan ki wanke kwanuka,ke kuma Jannat ki tabbatar kin yi girkin rana kafin ki bar gidan nan,okay?" Hukuncin nashi yayi masifar bawa Deeja mamaki,amma sai tayi kamar bata sauraron su,sai cin abincin ta takeyi a nutse, lokaci lokaci tana kallon haɗaɗɗen agogon hannun ta gudun kada lokaci ya ƙure, Farida da Jannat suka dubu juna cikin tsananin kaɗuwa da al'ajabi,sannan suka kalle shi a tsorace,suna raya ya raina musu hankali ma,ya ɗebo su daga gaban Hajiya,don kawai ya basu wahala Farida itace tayi magana cikin rawar murya"yaya ina da excuse" "Wanne excuse kenan?"ya tambaya batare da ya kalle ta ba "Zamuyi group meeting yau kafin mu shiga lecture,Kuma rashin halartar shi zai iya jawo min matsala" Shiru yayi yana cin abincin shi a nutse,ita kuwa Farida addu'a takeyi a ranta Allah ya sanya ya bar ta ta fita amma ina! addu'ar ta bata karɓu ba,don cewa yayi "A haƙura da group meeting ɗin,tunda anayi,kuma watarana ma za'a ƙara yi, shikenan ko?" Shiru Farida tayi tana cika tana batsewa,dama ita Jannat ta daɗe da sanin halin yayan nasu,,kaifi ɗaya ne,idan ya faɗi abu,to abun yake nufi , shiyasa bata tanka ba Deeja kam shiru tayi tamkar bata san me yake wakana ba,tana kammala cin abincin ta ta ɗauki jakar ta gami da yi musu sallama ta fice daga falon Ranar bata dawo da wuri ba sai wajen la'asar, Saboda meeting da sukayi,a falo ta same su a zaune sun cika sun batse,falon kaca-kaca ta ko'ina,koda tayi sallama ma babu wadda ta amsa,sai Farida da ta kalle ta cikin fitsara tace"Malama har da zuwa a wani daɗe saboda kin bar bayi ko?to ga gidan ki nan,ki gyara abinci,girki kuma iya mu yamu muka yi,don haka ruwan ki ne kiyi abinda ya dace ruwan ki ne ki bari" Ko kallon banza bata samu daga wajen Deeja ba,hakan ya ƙona ran Faridan, Deeja bata kula ba ta shige ɗakin ta Wanka tayi ta ɗauro alwala don yin Sallah,tana shirin tada kabbarar Sallah kenan ta jiyo faɗan Khalees akan rashin gyara gida da basuyi ba,bata kula ba ta tayar da sallar ta,sai dai tana jin irin rashin mutuncin da yakeyi musu da dukan da yayi musu,cikin sauri ta idar,da gudu ta nufi falon tana faɗin"I'm sorry Khalees,nice nace su bari zan gyara fa" Khalees ya kalle ta na wasu daƙiƙu,bei ce komai ba ya juya ya bar falon,itama Deeja haka ko badan komai ba,ta bar falon don watsatstsen kallon da suke jefa mata Haka rayuwar gidan ta cigaba da tafiya tsawon kwanaki shida, gaisuwar arziƙi bata haɗa su da su Farida,shi kuma Khalees ya kallafa musu yin aikace-aikacen gidan idan suna gidan Ganin wahalar bazata ƙare ba ne ya tilasta musu guduwa, Hajiya na zaune sai kawai taga sun shigo,ta sha mamaki ƙwarai da gaske,don da kansu suka yanke shawarar komawa gidan ɗan'uwan nasu,da ta tambaye su dalilin dawowar tasu suka ce sun gaji da wahalar da yaya Khalees yake basu, Hajiya bata matsa musu ba,don dama su suka so komawar Tafiyar su Farida ya faranta wa Deeja ba kaɗan ba,a ƙalla ko ba komai ta samu sakewa,kuma ɓacin ranta ya ragu,domin shi Khalees ta sani in dai ba harkar shi ta shiga ba ranta bazai ɓaci ba **** **** **** Ƙarfe biyar na yamma suka ji announcement na cewa jirgin su ya sauka,cikin nutsuwa suka sauko daga jirgin,ɗauke da kyawawan yaran su Mee'ad da muneeb,kai tsaye waje suka nema suka zauna, sannan ta kirawo aunty Bintu tare da shaida musu isowar su, aunty Bintu tace gata nan #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 5 Cikin abinda bei wuce mintuna sha biyar ba aunty Bintu da babbar ƴar ta intisar mei kimanin shekaru goma sha bakwai suka iso, cikin murna mai yawa intisar ta rungume meema tana faɗin"wow! aunty meema you are highly welcome, gaskiya munyi missing ɗin ku da yawa"ta dubi hafeez fuskar ta ɗauke da murmushin farin ciki tana faɗin"uncle hafeez yau a gari?ai munyi tsammanin mutanen Malaysia sun riƙe mana kai" Ɗan murmushi hafeez yayi sannan yace"ina!kuna raina intisar,kawai time ne baya samuwa,amma kuma ai auntyn ku tana zuwa ko?" "Eh haka ne,to yanzu dai kuzo muje gida, Mamie na ta shirya muku delicious and wonderful dish" Mima ta wuce gaba tana faɗin"kuzo muyi sauri,a gajiye nake ni"suka ɗunguma suka shiga motar,aunty Bintu taja suka tafi gida Basu samu damar zama cin abincin ba sai da sukayi sallar maghriba,suna cin abinci suna hira,anan aunty Bintu ta sanar dasu batun auren Deeja Cikin madaukakin mamaki Mima tace"kamar a mafarki?Deeja tayi aure kullum mukanyi waya ko chat amma ta kasa sanar dani?" Aunty Bintu tace"kin santa da zurfin ciki,kuma ina zargin akwai matsala ne,duka duka fa kwananta arba'in da shida da yi mata aikin zuciya akayi mata auren fa" Hafeez ya gyaɗa kai yace"lallai babu mamaki,to ina tsohon mijin nata?" Aunty Bintu tace'yana nan" Kuma suna haɗuwa dashi?"a cewar Mima tana tsare ta da ido "Sai dai idan bataje gidan Mamie babba ba,kuma bikin a gidan mamien za'a yi"a cewar aunty Bintu "Yayi aure ne?"hafeez ya tambaya "Tun kafin su rabu da Deeja "a cewar Mima"wata fitsararriya mara kunya mara tarbiyya"ta ƙarashe maganar tana yatsina fuska "Ke Mima!ina raba ki,a ina kika san bata da tarbiyya?"a cewar aunty Bintu Murmushin takaici miman tayi tace"a bar maganar kawai aunty"daga nan suka sauya wata hirar A ranar Mima ta kira Deeja ta sanar mata da saukar su,ihun murna ta rinƙa yi,tace"oh!leemo nayi missing ɗinki da yawa,ina my baby Mee'ad?" "Tana wajen abban su ita da munib" "Yayi kyau,to yaushe zaki ƙaraso?" "Oho miki,mara mutunci kawai,kiyi aure amma ki kasa sanar dani?" "Uhm!"da story sosai Mima,sai mun haɗu kawai,yaushe zaki zo?" "It is better mu haɗu a gidan bikin, saboda abban Mee'ad ya matsa min gobe,jirgi zamu bi zuwa azare,don mu gaida ammin su" "Okay,babu matsala, yaushe zaku dawo?" "Jibi in Sha Allah,Kuma a gidan bikin zan sauka" "Okay babu damuwa,Ni da gobe nace zan je,amma yanzu na fasa sai jibin" "Haba ke kuwa,meyasa?" "Mu haɗu a jibin kawai,da stories" "Okay Allah ya nuna mana da alkhairi" "Ameen"sukayi sallama A ranar Deeja cikin farin ciki ta kwana,walwalar ta ta bawa Khalees mamaki ƙwarai, saboda irin tarin matsaloli da ta tsinci kanta a ciki basa bata damar yin walwala kamar kowanne mutum,amma sai sabgar ta takeyi cikin farin ciki,shi kuma Khalees jin kai irin nashi ya hana shi tambaya Washe gari da safe daga office Kai tsaye wajen kitso da ƙunshi ta nufa,ai kuwa aka tsantsara mata kitso, dogon baƙin gashin ta ya amshi ƙananan kitson,lalle ja da baƙi ya amshi chaculate fatar ta,tayi kyau sosai ga wani haske da ta ƙara a ƴan kwanakin nan A ranar bata koma gida ba sai shida saura ƴan mintuna,tun sanda mai gadi ya wangale gate ta hango khalees yana ta faman Safa da marwa, fuskar shi ɗauke da alamun damuwa,amma ganin shigowar motar ta sai ya tsaya cak yana kallon ta batare da yace uffan ba, fuskar shi har yanzu a ɗaure take Kai tsaye parking space ɗin gidan ta nufa bayan ta daidaita parking ɗin motar ta fito tana ɗan satar kallon Khalees ɗin,ko uffan ba tace ba tayi nufin wucewa cikin gidan "Daga ina kike?" Batare da damuwa ba ta bashi amsa,"naje kitso da ƙunshi ne" "Shine sai yanzu?"ya faɗa da ɗan ɗaga murya Ganin hankalin mutanen da suke yiwa gidan hidima ya fara dawowa kansu ya sanya ta furta"I'm sorry"da sauri ta wuce cikin gidan Ta fito wanka ta ganshi a bakin gado,har yanzu fuskar shi babu walwala,hakan bai dame shi ba,ta zauna a gaban madubi ta fara gyara kanta,sai yanzu Khalees ya ƙare mata kallo ganin tayi kyau sosai,amma duk da haka bai fasa faɗar abinda ya kawo shi ba "Ban amince ki rinƙa zuwa ko'ina kina haura la'asar a waje ba,idan haka ta kuma faruwa rai zei ɓaci"bei jira amsar ta ba ya miƙe ya fice daga ɗakin Wayar ta ta ɗauko daga jakar ta,miscall shida ta gani,shaf ta manta cewa ta sanya ta a silent,duk misscall shidan Khalees ne,a fili ta furta "oh!wato jin kai bazai bar shi yace"ya kira ni ban amsa ba ko?" Washe gari ta kama juma'a,kuma a ranar zata tafi gidan bikin,sai zumuɗi take tayi,Khalees yana kwance yana kallon yadda take ta farin ciki, gaba ɗaya sai yaji ya shiga damuwa,wato farin ciki takeyi Saboda saboda zata nisance shi?" Da yaga zumuɗin yaƙi ya ƙare sai yace"Malama haukan ya isa haka,idan kika matsa ma wallahi sai na hana ki" Kallon shi tayi cike da mamaki,ganin ya ɗaure fuska ya sanya ta ɗauke kanta ta cigaba da abinda takeyi, zuciyar ta cike da mamakin shi Ƙarfe bakwai da mintuna arba'in ta kammala shirya komai,a lokacin tuni Khalees ya wuce wajen aikin shi,ta loda akwatunan ta a Boot taja motar ta ta nufi wajen aikin ta Sha ɗaya da minti bakwai wayar ta ta fara ƙara,tana dubawa,sunan Mima ta gani,da sauri ta ɗaga tana faɗin"sister leemo ya?kun sauka lafiya?" "Lafiya lau sister deejo,mun dawo fa" "Da gaske don Allah?"a cewar ta cikin farin ciki "Wallahi kuwa,yanzu haka ma gamu a airport,aunty Bintu zata ɗauke mu" "To Allah ya iso daku lafiya,Ni ina wajen aiki" "Okay to mu haɗu a can ɗin kawai" #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 6 Sha biyu daidai Deeja ta tashi daga aiki,kai tsaye sardauna crescent ta nufa cikin unguwar Nassarawa GRA,in da gidan professor Ismail yake, kai tsaye gidan ta nufa,horn ɗaya daya tayi mai gadi ya leƙo yana ganin itace yayi mata sannu da zuwa,suka gaisa cikin mutunci,tayi masa alherin da ta saba yi masa sannan ta shiga cikin gidan A makeken tempol ɗin gidan ta ajiye motar ta cikin jerin tarin motocin da ke cikin tempol ɗin,ciki har da motar Imran da Mima,da alamu dukkan su suna nan kenan Bata damu ba ta nufi sashen Mamie don su gaisa,da sallama ta shiga,su huda da yusra da ke falon suka miƙe suka rungume ta suna murnar ganin ta,da ƙyar suka ƙyale ta,ta gaida da Mamie da kuma mummy Aysha,da fara'a suka amsa mata sannan ta yada zango suka cigaba da hira ** ** ** Ita kuwa Mima aunty Bintu ce ta ɗauko su ita da yaran ta,kai tsaye gidan professor Ismail ta kawo su,shi hafeez bai taho ba, Saboda yana da uzururruka a can,sai ranar ɗaurin aure zai zo Bayan sun gaisa da Mamie sai ta kira afra take shaida mata isowar ta,cikin azama afra ta shigo ta rungume ta cikin murna taja su sashen ta,a can ta shirya musu abinci lafiyayye ,sosai Mee'ad da munib suka burge afra,cikin rawar jiki ta kira haneef tana fadin"haneef,zo ga aboki nayi maka"yaron ya shigo falon da sauri yaja munib suka nufi wajen wasan shi Sun kwashi mintuna suna hira ,a ƴar hirar da sukayi Mima ta fahimci cewa afra mace ce mai surutu da rawar kai,don a hirar su ta fahimci cewa matar yaya fauwaz ce,kuma da alamu akwai aminci mai ƙarfi tsakanin ta da umaima,don haka gaba ɗaya taji batayi mata ba,don haka tace "bari naje mu gaisa da mutanen gidan ko?aunty kiyya tana nan kuwa?" Sai walwalar Afra ta ɗauke,ta ɗan taɓe baki tace"suna main parlour Ina ga,muje can"Mima batayi musu ba suka wuce zuwa babban falon A can suka haɗu da da su lubaisa,kiyya da nuwaira,sai aunty salma da aunty nafisa,sai minal da itama zuwan ta kenan,sai umaima Sun gaisa da kowa, cikin mutunci,umaima da kuma suka fara kallon kallo, Afra tace "sisto ga ƙawa ta Dr halima azare" Murmushi Mima tayi tace "nice to meet you umaima"ta miƙa mata hannu sukayi musabaha "Na gode,ya gida?"ya mei gida da yara?"inji umaima cikin sanyin jiki "Kowa lafiya,ya naki mai gidan?" "Lafiya ƙalau,,a cewar umaima"Mima tace"good haka ake so"bata jira cewar umaima ba ta ja hannun kiyya suka bar falon suka nufi sashen kiyyan A can Mima ta zube a kan kujera,ta dubi zakiyya tana fadin"aunty kiyya Ina yara na ne?ban gansu ba" Zakiyya tace"Islam da Hisham suna makaranta,shi kuma Aisar babbar ƴar aunty rahama ta ɗauke shi" "Yayi kyau"a cewar Mima,ta ɗan yi shiru,zuwa can ta kalle ta tace"aunty kinji sisto tayi aure?" "Na sani wallahi,amma bamu samu halartar auren ba,wani irin aure ne kamar taron mutuwa" "Akwai matsala kenan ko?"a cewar Mima "Babu mamaki,amma sai tazo sai muji ta bakin ta" "To Allah ya kawo ta lafiya" "Ameen" Haka suka cigaba da hira akan Deeja,sun ɗan juma kafin su miƙe su nufi main parlour Mima na kula da kallon da umaima da lubaisa sukeyi mata lokaci lokaci amma tayi banza dasu, Afra kam sai zaƙewa takeyi akan miman,a ƙoƙarin ta na samun shiga fiye da zakiyya Deeja ce tayi sallama ta shigo, hankalin su ya koma kanta, Mima tayi tsalle ta rungume ta suka fara ihun murna,zuwa can suka saki juna suna haki da dariya, Deeja ta kalli Mima tana dariyar murna tace"sister leemo! gaskiya Malaysia ta amshe ki,kinga yadda kikayi fresh kika ƙara kyau?ko dai munib ya samu ƙani ko ƙanwa ne?" Dariya Mima tayi gami dukan kafadar ta tace"ai ke za'a yiwa wannan tambayar sister deejo,don Allah aunty kiyya taya Ni dubawa , yarinyar nan batayi ƙiba da haske ba?da alama engineer Abdul yayi ajiya" Gaban Deeja ne ya bada dam!har sai da hakan ya so ya bayyana akan fuskar ta,don dama kwanan nan tana zargin hakan saboda rashin ganin al'adar ta,ga yawan kwaɗayi da ta koya,amma da yake jaruma ce ta dake tare da faɗin"ji sharri,ko don na rafko ki zaki wayance?" "Aunty kiyya tace"wane sharri kuma?da gaske take wallahi,ko dai Khalees ya iya kiwo ko kuma yayi ajiya,cikin biyu ɗaya" Dariya sukayi su duka, duk da cewa Deeja ta yaƙe tayi,ta nemi waje ta zauna tana faɗin"ke dai aunty kice ta Baki cin hanci ne kawai" Su Afra kan mamaki ne ya ƙamar dasu,yaushe Deeja tayi aure?Nuwaira ce ta kasa jurewa ta kalli aunty kiyya tace"Aunty kiyya dama Deeja tayi aure ne?" Mima da Deeja suka kalli juna a tare da sannan suka kalli nuwairan,Mima ce tayi caraf ta amsa da cewa "eh tayi aure,watanni huɗu baya ma,da mamaki ne a cikin ikon Allah? " Cikin sanyin jiki nuwaira tace"babu kam, Allah ya sanya alkhairi" "Ameen"in ji aunty kiyya,ita dai Deeja tana jin su,sai ma danne dannen waya da ta fara don ta nuna musu rashin muhimmancin nuwairan a wajen ta Mima ce ta janye hannun ta tana fadin"zo muje sashen aunty kiyya muyi sallar la'asar, gashi can an fara kira"babu musu ta miƙe,itama Aunty kiyyan ta miƙe suka nufi sashen nata A can bayan sun idar da sallah Mima da zakiyya suka sanya Deeja a tsakiya, Mima ta dube ta cikin damuwa tace"sisto me hakan ke nufi?"kaf family baki da kamar Ni da aunty kiyya Amma auren ki sai ji mukayi a gari,me hakan ke nufi?" Shiru Deeja tayi zuciyar ta tana suya,da tana da saurin kuka da tayi ta samu sauƙin raɗaɗin da zuciyar ta takeyi,amma ina! bata iya saurin kuka ba,ta dube su tace"aure na da kuke gani ban yi shi a mood na farin ciki ba,asalima har na auri engineer Abdul bansan shi bane,kuma wannan hasarar da kuka san shi da ita bai chanja ta ba,,ga mahaifiyar shi da ƴan'uwan shi da basa so na ko kaɗan,a haka mukayi auren duka duka ko kwana hamsin ban cika ba aka ɗaura mana aure dashi,har kwanan yau daurewa zaman gidanshi nakeyi kawai" Shiru sukayi suna kallon yanayin ta ya sauya,alamun damuwa sun bayyana akan fuskar ta,Mima ta dafa kafadar ta cikin kwantar da murya tace "Ki cigaba da haƙuri my Deeja,komai yayi farko zai yi ƙarshe,ki cire duk wata damuwa a ranki komai yayi tsanani yana tare da samu sauƙi in Sha Allah,shi kuma mijin ki ki cigaba da yi masa biyayya in Sha Allah zaki ga ribar abin" #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 7 Zakiyya ma ta ƙara da faɗin"in har kika jure kika cigaba da kyautata masa babu dare babu rana ina mei tabbatar miki da cewa shi kanshi ba zei san lokacin da zai fara son ki ba,duk da cewa mijin ki mutum ne mai wani irin ra'ayi, ba'a tantance gaban shi da bayan shi,amma ai mutum ne shi,yana da zuciya,kuma namiji ne ko ba haka ba? To kamar yadda na sanki baki da saurin fushi ina so ki daure ki cigaba da hakan,wannan shariya da ƙyaliyan ki ajiye su a gefe, Khalees mijin ki ne yayanki ne,ginshiƙin ki ne,kinga yanzu babu in da mama da Abba" Kalaman kiyya na ƙarshe sunyi matuƙar tasiri wajen karya zuciyar Deeja,wato babu idanun mama da Abba,tunowa da shuɗewar gatan nata ya sanya ta fashewa da kuka cikin tausayawa,su Mima suka rinƙa tausar ta suna bata baki har ta daina kukan Kasancewar ta tare da Mima da kiyya ya sanya damuwar ta ta kau,ga yusra da Huda ƙannen Imran da suke uwa ɗaya uba ɗaya,su kam suna matukar son ta,har ta kan ji dama ace suma ƴan uwan Khalees haka suke son ta. Sun haɗu da su Imran ɗin a falon Mamie babba,bata nuna musu komai ba ta gaishe su cike da girmamawa a matsayin su na yayyen ta,Yaya fauwaz ya kalli Mamie yace"Mamie, Deeja fa wannan abokin Imran ɗin ne ya aure ta" Gaban Deeja ya buga da ƙarfi,abokin Imran?tana jin momy na cewa "wanne abokin nashi?" "Engineer abdurrashid mana, Khalees,wanda sukayi secondary tare kin gano shi?" "Au!tooooo!!na gano shi, Allah ya sarki,yaron kirki kuwa,ashe shi ta aura"a cewar Mamie fuskar ta cike da fara'a "Shi ta aura Mamie"Yaya fauwaz ya tabbatar mata "To Allah ya sanya alkhairi" Suka amsa da "ameen" Miƙewa tayi ta nufi ƙofar fita,cikin rashin sani idanun ta suka sauka akan imran,ai kuwa tayi amfani da wannan damar ta zabga Masa harara,ai kuwa ya sunkuyar da kanshi, fuskar shi ɗauke da alamun damuwa,hakan bai dame ta ba tayi saurin barin falon Washegari ta kama asabar,a ranar ne aka fara biki, kiyya da Mima da Deeja sun ɗau wanka cikin lace Pink mai ratsin red flowers,wannan tsarabar Mima ce a wani zuwa Switzerland da tayi ta gano su ta siyo har da aunty Bintu da intisar,ai kuwa sunyi matuƙar haskawa a wajen party ɗin Washe gari ta kama ranar ɗaurin aure,su Deeja ana ta hidima da baƙi,ga wankan da suke ɗauka tamkar amare ita da su Mima,kuma tunda Mee'ad ta ganta ta daina yarda da kowa,gata da farin jini amma ta dage ita sai Deeja kaɗai Rashin son abincin da yawan kasalar da Deeja ke fama da dashi ne ya sanya zargin ta ƙaruwa,amma bata son tabbatar da hakan saboda bata san da wanne ido zata dubi Khalees da batun cikin ba,tun da a iya sanin ta baya son ta,to ta yaya zai so haɗa zuri'a daita?amma ta yanke shawarar tuntuɓar likitar ta Dr su'ad bayan biki don ta tabbatar cikin ne ko akasin hakan Su Afra ne ita da umaima da wata ƙawar umaiman nadiya suka jero suka fito falon Mamie Nadiya ce tayi saurin taɓo umaima tace"umaima!kinga wani handsome guy!da sauri umaima ta ɗago kai don ganin waye Mutum biyu ta gani,wani guy da bata san waye ba sai mijin ta Imran,nan da nan kishi ya turnuƙe ta tace"to ƙwalelen kare da hantar kura,miji na ne" Da sauri nadiya ta dafa kafadar ta tace"I'm sorry friend!ba shi ba fa,na kusa da shi"sai a sannan umaima ta ƙare wa na kusa dashi ɗin kallo Wankan tarwaɗa ne,dogo mai ƙirar ƙarfi, kyakkyawa ne sosai,sai dai da alamu zai yi jin kai yana sanye da shadda,sky blue,ɗinkin yayi matuƙar kyau sosai,ɗan murmushi tayi tace"good,ina taya ki murnar wannan babban kamun,zan Miki hanya daga wajen mai gida na"cikin murna nadiya ke faɗin"na gode sister na" An kammala biki lafiya,an kai amarya gidan mijin ta lafiya,washe gari ta kama Litinin daga wajen aiki kai tsaye Deeja gida ta wuce, zuciyar ta cike da tsoron wane sakamako zata gani game da zargin da takeyiwa kanta Bata samu Khalees a gida ba,batayi mamaki ba don tasan bai ci ace ya taso daga wajen aiki ba,don haka wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa tayi kyau sosai,bata nemi abinci ba duk da yunwar da takeji,don ji tayi tana sha'awar alala,don haka tayi sauri taje inda zata je ta dawo akan kari Asibitin Dr su'ad ta nufa, cikin Sa'a ta same ta da murmushi akan fuskar Dr su'ad ta dube ta tana faɗin"a'a!matan manyan injiniyoyi!kuma manyan akawuntoci,yau kune a asibitin namu?" Murmushi Deeja tayi tace"mune wallahi,ya akaji da aiki da fama da jama'a?" "Jiki alhamdulillah!ya ƙarin ƙarfin jikin?" "Jiki alhamdulillah,mun samu afuwa"a cewar Deeja "To Allah ya sa dai ba shine ya tashi ba ko?" Deeja ta girgiza kai tace"ko ɗaya, dama suspecting nakeyi, Kamar ciki gare ni shine nazo kiyi mini test" Cikin farin ciki Dr su'ad tace"Allah ya tabbatar da abinda yafi alkhairi,naga yaran Madam Deeja da angon ta abdurrashid"murmushin yaƙe kawai Deejan tayi Dr su'ad tayi ƴan gwaje-gwajen ta inda ta tabbatar wa da Deeja zargin ta, Deejan tayi godiya ta ajiye mata kuɗin ta ta tafi Tana shiga Mota ta kira safeena ƙawar ta, safeena na ɗagawa bata saurari komai ba tace"feena ya ma sunan maganin da kikayi amfani dashi kikayi abortion?" Cike da mamaki feena tace"abortion kuma? abortion zakiyi ne?haba Deeja,ko nima a lokacin ƙuruciya ce ta ɗebe ni,kuma naga babyn da na haifa baiyi ƙwari ba,shiyasa" "Wait malama!ba dogon bayani na tambaye ki ba just tell me idan zaki iya" Cike da mamaki feena ta gaya mata,tana gama faɗa mata ta kashe wayar ta nufi chemist Wani katafaren chemist ta shiga da sallama,mai chemist ɗin ya amsa sannan ta tambaye shi maganin,babu musu ya ɗauko mata,ta ajiye masa kuɗin shi ta ɗauki maganin ta juya ta bar chemist ɗin Tana tuƙi kalaman kalaman Dr su'ad nata mata amsa kuwwa"congratulations Mrs Khalees!kina ɗauke da babyn mu na wata biyu da kwanaki shida, Allah ya raba ku da lafiya,sai a kular Mana da baby da kyau" Dogon tsaki taja tana girgiza kai,a fili,ta furta"abinda bazan iya ba, Deeja bazata iya haifar yaran Khalees ba" Gida ta koma,a harabar gidan ta iske Khalees yana karatun jarida,bata kula shi ba tayi shigewar ta shi kuma ya bita da kallon mamaki,a ran shi yana ayyana cewa lallai ba lafiya ba A kan gado ta watsar da komai jakar ta,maganin da ta siyo wanda yazo a hannun ta,mayafin ta da ɗankwalin ta ta ɗauki towel ta shiga bayi don zafi takeji Khalees ne ya shigo ɗakin,gefen gado yayiwa kanshi matsuguni yana jiran ta fito yaji ina taje har zuwa yanzu ƙarfe biyar saura,shi da yace huɗu tayi mata a gida,don masu gadi sun sanar masa dawowarta,kuma ga alamu ya gani,an gyara gidan tas. Kwalin maganin da ya gani ne yaja hankalin shi kamar bazei duba ba sai dai ya ɗauka ya duba Tashin hankali ne ƙarara a kan fuskar shi mei Deeja zatayi da wannan maganin?"ya tambayi kanshi Ajiye maganin yayi ya miƙe ya fice daga ɗakin,baiyi cikakken minti guda da fita ba Deeja ta fito, doguwar riga ta sanya,ko mai bata shafa ba ta ɗauko gorar ruwa dake cikin ɗakin nata,ta ɓalli maganin ya zube a ƙasa Da sauri ta ɗago kanta don ganin me wannan aikin, Khalees ne #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 8 Yana tsaye sai huci yakeyi tamkar mayunwacin zaki, kyawawan idanun shi sun rine zuwa jajaye,alamun tashin hankali sun gama bayyana akan fuskar shi Ita mamaki ya bata ma,amma sai ta ɓoye hakan akan fuskar ta,ta ɗauko maganin da nufin sake ɓalla sai ya fizge,sai taji ya fara bata haushi, cikin ɗaure fuska tace"bani!" Bai bata ba kuma bai amsa ba,sai girgiza kai kai yakeyi,cikin tsawa tace"ka bani abu na mana!meye hakan?" Juyawa yayi ya fita, Deeja ta raka shi da ido zuciyar ta nayi mata suya,a haukace ta miƙe ta ɗauki key ɗin motar ta tayo waje,a falo ta same shi ya rafka tagumi,ko kallon shi batayi ba ta ɗauki hanyar fita,sai jin Muryar shi tayi yana cewa "Idan kika fita a bakin......."da sauri ta juyo tana murmushi tace"Please a bakin igiya nawa?uku?" "Kar ki fita!"ya faɗa cikin wata raunananniyar murya da Deeja bata san yana da ita ba Jin hakan ya sanya Deejan dawowa tana faɗin"to bani magani na" Shiru yayi zuciyar shi cike da damuwa,ita kuwa ganin bashi da niyyar magana taja ƙafafuwan ta ta shige ɗaki ta faɗa kan gadon ta,ko second talatin batayi ba ya shigo da sallama,ta amsa idanun ta a lumshe,har yanzu yunwa na ƙwarzabar ta,amma damuwa ta hana ta bawa cikin ta haƙƙin shi Zama yayi a bakin gadon,cikin sanyin murya ya furta"Khadija!" Zata iya cewa wannan shine karo na farko da ta taɓa jin sunan ta a bakin shi,amma hakan bei hana ta amsawa "Na'am abdurrashid!"itama ta kira cikakken sunan shi "Ki tashi zamuyi magana"ya faɗa cikin marairaicewa "Yunwa nakeji Ni kam,bazan iya fahimtar zancen ka ba" "Don Allah ki taimaka min,zan samo ko me kike so ki ci, maganar ba mai tsawo bace" Zaune ta tashi tana cike da mamakin sauyawar Khalees lokaci ɗaya amma har yanzu ta hana hakan bayyana akan fuskar ta "Khadija me ya sauya ki ne?"me ya sauya min ke ne?me ya same ki ne?" "Me nayi?"ta faɗa cikin ɗaure fuska "Menayi miki da zafi haka kika tsane ni?kike son yi min asarar ɗa na?"ƙwalla ta cika idanun shi Sai jikin Deeja ya fara rawa, Khalees ya cigaba da cewa"ko da ace wani laifi nayi miki bei kamata ki hukunta Ni ta wannan hanyar ba,balle ma me nayi miki?" Deeja ta dake tace"haba Khalees!ai girman ƙiyayyar da kakeyi min ta fi ƙarfin wani gama garin laifi,to baka san saniya me zaka yi da ƙahon ta?baka so na me zaka yi da ɗa na?" Da sauri ya katse ta yana faɗin"Khadija wa yace Miki bana son ki?me yasa kika ce haka?kin san yadda nakejin ki a raina kuwa?kwana biyu da kikayi bakya nan kin san a halin kewar da na kasance kuwa?idan kika ce haka bakiyi min adalci ba" Daga inda take tana iya jin sautin bugun zuciyar shi,hakan ya sanar da ita irin tashin hankalin da yake ciki, cikin sanyin murya tace "To meyasa baka nuna min so kamar yadda kowaɗanne ma'aurata suke gudanar da rayuwar su?ban taɓa yin abu ka yaba ba,sai dai idan nayi kuskure ka janyo min ɓacin rai, tsakani na da kai kallon banza,tsawa,baƙar magana sai kace baiwa,kayi min adalci saboda Allah?"hawaye suka ciko idanun ta Ba ƙaramin abu ne yake sanya Deeja kuka ba,ya daɗe da sanin hakan,da sauri ya goge mata hawayen sannan yace "Khadija, wallahi tallahi ba da nufi nayi miki abinda nayi miki ba,nayi hakane don na nisanta kaina dake kar ki illata ni kamar yadda sauran mata na sukayi min Khadija! mahaifi na bai taɓa bani damar auren zaɓi na ba, karon farko ya aura min fadila,fadila ta kasance malalaciya,babu abinda ta iya sai rashin wda nuna ita wata ce,gashi a ƙarshe tace bazata haihu yanzu ba don kar ta tsufa,wannan ne yayi sanadin rabuwar mu Banyi cikakken wata uku ba daddy ya kuma zaɓa min suhaima,ita kam lamarin ta yafi na fadila muni,don kwata kwata bata zaman gida,ga sace sace kamar ɓera,ban isa nayi ajiya a gida ba sai ta ɗauke,na sanar da Daddy Amma sai yake ganin kamar ƙarya nayi,haka nake ta haƙuri daita Rana tsaka ta tayar da ballin sai na sake ta,na sanarwa Daddy abinda ke faruwa,ya kira mu sa niyyar yayi mana sulhu,amma sai ta baɗawa idanun ta toka ta ci masa mutunci,ganin haka Daddy ya bar Ni na sake ta Bai daddara ba,naje Egypt na dawo bayan naje gaishe shi yake shaida min cewa yayi min aure, hankali na ya tashi,amma hakan na daure na amshi maganar da girmamawa, musamman ma da aka ce min ƙanwa ta ce aka aura min Labiba,itace ƴar ƙanwar Daddy da aka aura min,itama sam bata da lokaci na,ta sha fita ƙasashen waje batare da sani na ba,da sunan tana zuwa kasuwanci,tun abin na damu na har na cire shi a raina Baƙar ranar da bazan iya mantawa daita ba itace ranar da na kama labiba da wasu mata suna sheƙe ayar su,abin nan ya gigita Ni sosai,kafin nasan abinyi labiba ta buga min wani abu a kai na da ƙarfi,na daɗi sumamme, ita kuwa ta tattare duk wani abu mai muhimmanci da tasan inayin amfani dashi ta gudu Sai da nayi kwana biyu a asibiti sannan na samu kaina, mahaifiya ta da sauran ƴan uwana sun shiga matsanancin tashin hankali suka yi ta roƙon mahaifi na akan yayi haƙuri ya bar ni na samu zaɓin raina ko Allah zai sa a dace,amma sai yace har yanzu Ban mallaki hankalin kaina ba,kuma a lokacin ina da shekaru talatin da biyar zuwa da shida Ganin irin kafiyar shi ya fusata mu,muka ɗauki aniyar duk macen da ya ƙara aura min sai mun matsa mata mun takura mata har ta gudu ta bar mu,cikin ikon Allah sai kika zama mace ta gaba Wannan shine dalilin da yasa bakya samun afuwa a wajen mu ko, ko ni ko hajiya ko qanne na Wallahi ba don Bama son ki ba,don uzzurawar daddy,Amma kiyi haquri ki yafe mana,haƙiƙa mun aikata kuskure Kuka sosai Deeja ta fashe dashi na tausayin mijin nata,ya janyo ta ya rungume ta yana sauke numfashi,da ƙyar ya lallashe ta tayi shiru,sannan ya miƙe ya nufi kitchen don samar mata abinda zata ci ***** ***** ***** Tana kwance jikin kafaɗar shi ta ɗago idanun ta ta kalle shi tace "Honey!" Kallon ta yayi batare da ya amsa ba,ta tashi zaune sosai tana fuskantar shi tace"honey tambayar ka nake son yi" "Okay Ina jin ki, Allah yasa na sani" "Ranar bikin Yasmeen na ganka tare da wani,wanene shi don Allah?" "Wa kenan?"ya sake tambayar ta "Wani kyakkyawa kamar kai,amma da alamu zeiyi jin kai" #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 9 Wani mugun kallo ya watsa mata,tayi dariya tace"haba my king, wallahi ka fi dukkan maza a waje na,so nake nasan waye shi?" "Ban gane shi ba"ya faɗa yana sassauta fuska" "Haba!wani mei shadda sky blue!naga kun fito daga falon Mamie tare" "Ooooooo! Na gane, engineer abdurrashid kike nufi" "Yauwa,ƙawa ta Nadiya ce ta ganshi,kuma yayi mata" Wani watsatstsen kallo ya jefa mata yace"to yana da aure idan baki sani ba" "And so what?ba namiji bane?ai shi namiji mijin mace huɗu ne" "Eh lallai umaima!to mijin Khadija ne" Ta ɗan bi shi da kallo kafin tace"wacece khadija?" Ya amsa da cewa"tsohuwar mata ta" Taɓe baki tayi tace"to wacece ita? sai me?" "Kinyi silar barin ta gida na,bazan taɓa bari kiyi silar barin kiyi silar barin ta gidan Khalees ba, saboda ta bani farin ciki ta bani walwala a lokacin da na rasa walwala,ta zamar min bango a lokacin da na rasa masafa,ni kuma na kasa yi mata halacci,na baɗa mata ƙasa a ido,na guje ta a lokacin da take buƙatar kulawa,don haka kawai ki bawa ƙawar ki haƙuri" "Abinda bazei yiwu ba kenan!"a cewar umaima "Okay!sai kiyi duk abinda kike ganin zaki iya" "Zanyi kuwa"tana faɗa ta fice daga ɗakin,ya bi ta da kallo ***** ***** ***** Rayuwar auren Deeja ta sauya,kullum cikin tarairayar ta yake,haka suma dangin shi sun chanja mata sosai,duk wani abin kwaɗayi da take so sukan shirya su kawo mata,nan da nan ta murje tayi kyau,ciwon zuciyar ta ya lafa sosai da sosai,ta kasance cikin farin ciki sosai, yanzu abu ɗaya ne yake damun ta in da zata samu yayyen ta guda biyu,nusaiba da Yusuf da ko ɗuriyar su bata ji,amma Mima ta kan kwantar da mata da hankali da cewa in Sha Allah suna cikin kwanciyar hankali,kuma zasu waiwaye ta duk daren daɗewa Hakan ya sanya ta cire damuwar wannan a ranta,ta rungumi mijinta ta cigaba da rainon cikin ta da a yanzu zai kai watanni biyar ***** ***** ***** Nadiya ce zaune ita da umaima a haɗaɗɗen ɗakin umaiman, Nadiya ta kalli umaima tana faɗin"ƙawa ta ya ake ciki ne?Ni fa na damu da batun wannan sweet guy ɗin" "Sunan shi abdurrashid,kuma tsohon mijin wannan kucakar ne, tsohuwar matar husby"umaima ta faɗa zuciyar ta cike da hassada,don dai ta san Deeja tafi gaban a kira ta kucaka,ban da wannan ma,ko a faifai aka ajiye mai kama da ita da mai kama da Deeja sai an riga ɗaukar Deejan "Da kyau,kice zamu gwara kan shegiya mu ga mei tsaya mata,kaf garin nan waye ya isa ya ja damu?" "Babu kam,yanzu dai mu shirya mu je wajen boka mai gaba ɗaya"babu musu suka miƙe suka ɗau hanya ***** ***** ***** A ƴan kwanakin nan Deeja ta fara ganin sauyi a wajen Khalees,ya rage zaman gida,ya rage tarairayar ta da kulawa da ita,hakan na damun ta sosai,da ta sanarwa fareeda sai tace suma ya chanja musu,sun kasa gane kanshi, Deeja ce tace zata tambaye shi Da ya dawo ta same shi a ɗakin shi,da ta tambaye shi sai yace ayyuka ne suka sha kanshi,bata yarda ba amma sai ga bar shi a hakan Har ma'aikatar su Nadiya taje da zummar tana neman wani,anan ta haɗu da Khalees,ai kuwa ya rikice mata sosai,ta rinqa ja masa aji,da ƙyar ta yarda ta bashi number wayar ta A ranar ta kira umaima ta shaida mata,ihun murna umaima ta rinƙa yi tana godewa bokansu Allah Sarki!Nana khadija baiwar Allah!!zuwa yanzu Khalees baya samun lokacin ta,sai dai su Farida sukan zo ɗebe mata kewa, hakan yana kawo mata sauƙi Yau asabar ce,yana gida,akan gado ta riske shi yana waya,ga dukkan alamu da mace yake waya,sai fara'a yakeyi yana kashe murya, gefen gadon ta samu ta zauna,lura da zuwan ta ya sanya shi saurin katse kiran yana kallon ta tare da faɗin "Ya dai?maman twins?" "Ta zuba masa idanu,tana lura da yanda ya daburce tace"da wa kuke waya haka ne?ko sanin da shigowa ta ma bakayi ba da alamu"ta ƙarashe da ɗan murmushin da za'a iya kiran shi da na yaƙe Al'adar Khalees bei iya ƙarya ba, balle yaudara,don haka ya gyara zama ya dube ta yana faɗin "Luvly Deeja,nasan cewa zaki fahimce ni,nasan cewa zaki iya haƙuri dani Deeja kiyi haƙuri,nan da three days za'a ɗaura aure na" "Aure fa kace!"ta faɗa cikin ɗaga murya, hankalin ta a tsananin tashe "Be calm please! wallahi nima bansan yadda akayi hakan ta faru ba,ban san me ke damu na ba, Please kiyi min uzuri"hawaye suka ciko idanun shi Babu abinda Deeja keyi sai nanata"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"har taji relief a zuciyar ta,ga kalaman kwantar da hankali da yake mata Sun kwashi mintuna a haka kafin tace"to naji Khalees,nasan haka zata faru daman, wacece zaka aura ɗin?a ina take?" "Ƙawar matar abokina ce" Gaban Deeja ya buga tace"wa kenan?" "Aboki na Imran!" "What!a cewar Deeja cikin ƙaraji,tayi wani kukan kura ta ci kwalar shi... #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 10 Duk yadda yayi ya kwace kanshi yaci tura,ta damƙe shi cikin fitar hayyaci tana faɗin"macuta! azzalumai!!mugaye!!!me nayi muku?dama nasan bazaku ƙyale ni ba,dama nasan sai kunyi min haka, Allah ya fi ku!"haka tayi ta sambatu cikin fitar hayyaci wanda Khalees ba fahimta yakeyi ba, ƙoƙarin shima ya ƙwaci rigar shi da ta cukwikwiye Allah ya bashi Sa'a,yana ƙwace rigar tashi kuwa yayi harabar gidan a a guje, Deeja kam yaraf ta faɗi ƙasan tiles tana mayar da numfashi,amma har yanzu idanun ta babu hawaye,amma sun tsumu da tashin hankali Shi kam Khalees cikin azama ya nufi motar shi,yana shiga ya fara yiwa mai gadi horn,cikin azama ya ɗaga gate ɗin,har yayi gaba ya dawo ya cewa mai gadin "Ko da yaya kar ka bari matar gidan nan ta fita,idan kayi wannan kuskuren to a bakin aikin ka"yana gama faɗar haka ya ja motar shi ya bar wajen zuciyar shi cike da tashin hankali Cikin tsananin gigita Deeja ta yunƙura ta miƙe zata fice daga ɗakin,wayar Khalees tayi ƙara,babu dogon tunani ta ɗauki wayar ganin sunan my heartbeat da emoji na heart ❤️,tayi gaggawar ɗagawa amma bakin ta ɗauke da sallama Daga can ɓangaren taji anyi shewa gami da faɗin"MATAR KHALEES a yanzu" "Wacece?"Deeja tayi ƙarfin halin tambaya "Upcoming MATAR KHALEES,don ki sani Khalees nawa ne Ni kaɗai,muddin na shigo gidan nan babu wata mace da ta Isa ta ko da kalle shi ne,amma a yanzu dai na baki aron shi kafin in shigo......"jin bazata iya jurar abinda matar ke faɗi ba ya sanya ta saurin datse kiran,ta miƙe a gigice ta janyo mayafin ta ta yafa,ta nufi harabar gidan ko ganin gaban ta batayi Sai dai duk yadda taso malam Audu ya bar ta ta fita hakan ya ci tura,nan da nan ta fara wani irin haki wanda sai da ya kai ta ƙasa Ma'aikatan gidan ne suka nemo Khalees a waya,dama ba nisa yayi ba,ai kuwa sai gashi yazo,cikin sauri ya sanya ta a mota ya umarci driver ɗin shi da ya kai su asibitin Dr su'ad A can asibiti Dr su'ad da wasu manyan likitoci suka rufu akan ta,sun kai awa guda suna abu ɗaya, Khalees sai kai wa da kawowa yakeyi cikin tashin hankali da damuwa,ya san zancen auren shi ne ya tayar wa da Deeja hankali har haka, amma bayajin zai iya janye maganar auren,da zai iya da ya janye Yana tsaye Dr su'ad ta fito fuskar ta babu walwala,yana ganinta sai da yaji gaban shi ya faɗi,ta kalle shi tace"engineer Abdul biyo ni"babu musu ya bi ta,amma zuciyar shi cike da taraddadin abinda zata ce,yasan ko menene ba mei daɗi bane Suna shiga ta nemi waje ta zauna, shima ta nuna masa wajen zama,ya zauna yana sauraron abinda zata ce Ta zare glass ɗin idanun ta tana kallon shi tace "Wato da farko munyi tsammanin ciwon Deeja ya tafi tun bayan dawowar ta daga Spain,duba da cewa zaka kula da lafiyar ta,sai dai kuma abu ya chanja ba kamar yadda muka zata ba,ciwon Deeja yana nema ya dawo sabo,ga cikin ta da yake barazanar fita, gaskiya Khalees idan baka kula ba zaka iya rasa Deeja da abinda yake cikin ta baki ɗaya,don haka ka kula"tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice daga office ɗin Faɗar irin tashin hankali da Khalees ya tsinci kanshi a ciki ma ɓata baki ne,ji yake a ranshi dai da yanda zai yi da yayi ya fasa auren,amma ina!ji yake idan bai auri Nadiya ba zai iya mutuwa,yayi tagumi da hannu bibbiyu yana tunanin mafita Ganin bai samu komai ba ya tilasta masa miƙewa,jikin shi babu ƙwari ya fito daga office ɗin,yana fitowa wayar shi ta soma ƙara Da yayi niyyar share ta,amma sai ya ɗauko ya duba,fareeda ce Cikin sanyin jiki ya ɗaga, Farida ce ta soma magana"bros meke faruwa ne?ina ta kiran ka amma kaƙi picking" Cikin Muryar tashin hankali yace"Farida ina cikin damuwa, luvly Deeja tana kwance a nan asibiti bata san in da kanta yake ba" "Innalillahi wa Inna ilayhi rajiun!me ya same ta?"a cewar Farida cikin ruɗewa "Ciwon ta ne ya tashi"a cewar Khalees cikin rawar murya A gigice Farida tace"wane irin ciwo ne da ita?" "Heart attack ne"ya bata amsa "Subhanallahi!gamu nan zuwa"ta kashe wayar Yana zaune a reception abin duniya ya dame shi suka ƙaraso,har da Hajiya da ƙanwar shi mai bin shi Aunty sameera,suka ƙaraso fuskokinsu babu annuri kowacce ta nemi waje ta zauna Sun ɗan yi shiru na ƴan sakwanni kafin hajiya ta dubi Khalees cikin ɗaurewar fuska tace "Me nakeji haka ne?wane irin baƙin labari Farida ke sanar dani ne?" Shiru Khalees yayi,kafin ya fara maganar cikin rawar murya "Hajiya ciwon ta ne ya tashi" "Me ya tayar mata da ciwo?"ta faɗa tana tsare shi da idanu "Eh.......to........dama.......dama....zancen a...auren nawa ne"yayi shiru cikin damuwa "Wai auren dole ne yin shi?"ta faɗa cikin ɗaga murya Khalees ya kwantar da murya yace"amma hajiya ya kamata kiyi min uzuri,dukkan ku kun so ace na auri zaɓin raina,amma hakan bei yiwu ba sai yanzu" Hajiya ta girgiza kai tace"tabbas a da naso ka auri zaɓin ran ka,amma banda yanzu,ko a lokacin da naso ka auri zaɓin ran naka naso hakan ne saboda rashin dacen zaɓa maka mata da abban ku keyi maka,amma yanzu alhamdulillahi,an samu dace,to meye na ƙara auren kuma?" "Don Allah Hajiya ku taimake ni ku bari nayi auren nan, wallahi idan har banyi ba zan iya mutuwa,ina matuƙar son Nadiya" Har hajiya ta buɗe baki da zummar yin magana sameera ta kaɗa mata ido tayi shiru Sun samu ganin Deeja, hankalin ya tashi ganin yadda ta rame lokaci ɗaya,sai ɗan cikin ta da shima ya rame,cikin sanyin jiki suka fito suka nufi gida Suna tafiya akan titi,sameera ce mai tuƙi,sai hajiya a gefen ta,sai Farida da Jannat a baya,sameera ta kalli hajiya tace"hajiya dole fa ki ƙara ƙaimi da addu'a, alamu sun nuna akwai hannu cikin lamarin yaya Khalees" Hajiya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace"Ni kaina zargin da nakeyi kenan surayya,kuma babban abin takaicin da mahaifin shi yaƙi mara masa baya ya nemo matar aure amma yanzu don Allah ji ya amince da wannan auren,kuma wallahi tausayin yarinyar nan nakeyi,don bansan me amaryar nan tazo dashi ba,amma kuma ai akwai Allah" "Hakane,inji Aunty sameera"Allah ya shige mana gaba"suka amsa da "ameen" Sai da Deeja ta samu awa shida sannan ta dawo hayyacinta,a firgice ta farka tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin da aka kwantar da ita, Dr su'ad da ta shigo yanzu tayi saurin kwantar da ita tana fadin"Ina zakije ne?" Ta kalli Dr su'ad da rinannun idanun ta tace"Dr rabu da ni kawai"ta ƙarasa tana ƙoƙarin zame hannayen ta daga na Dr ɗin,kuma a lokaci guda tana ƙoƙarin miƙewa tsaye "Cool down madam,me yayi zafi haka?don Allah ki bi komai a sannu,komai zei warware in Sha Allah,Amma wannan zafin ran da kike nunawa ai bashi da wani amfani ko?" Cikin Muryar ɓacin rai tace"Dr duk bayanin da zanyi miki baza ki gane bane,kawai ki bar ni naje in da zanje" "No bari na sanarwa engineer,don bazan kwana a ciki ba" #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️ Nusy bee Page 11 Kafin Deeja ta kuma cewa wani abu ta zaro waya ta fara kiran Khalees,ganin kiran doctor su'ad ya Sanya shi azamar ɗaga kiran,yana ɗagawa tace"kazo ɗakin da aka kwantar da Madam ɗin ka"bata jira amsar shi ba ta kashe kiran Minti biyu tsakani sai gashi ya shigo cikin sauri,ganin ta a zaune yayi saurin nufar ta,amma ta dakatar dashi cikin ƙaraji "Kar ka ƙaraso in da nake Khalees,kar ka soma, Wallahi na tsane ka macuci, mayaudari, azzalumi,wanda bei san darajar mace ba,wallahi abinda kukayi min sai Allah ya saka min,don bazan taɓa yafe muku ba, munafukai annamimai,kuma na gama auren ka,dole ka sake ni,maƙaryaci kawai"idanun ta sun kaɗa sunyi jawur,amma ko ɗigon hawaye babu,don dama can ita ba mai saurin kuka bace Ba Khalees ba,itama Dr su'ad abin ya ɗaure mata kai,suka shiga bin ta da kallo, Dr su'ad ta matsa kusa da ita tana faɗin"haba malam!mijin ki ne fa,a ƙalla ya samu wannan alfarmar ko?"ita kanta Dr jikin ta rawa yakeyi, ballantana Khalees da ya shiga mummunan tashin hankali Deeja ta ƙarasa zare hannun ta gami da faɗin"a da yake amsa sunan miji a waje na,amma a yanzu"ta girgiza kai gami da miƙewa tsaye Duk yanda suka so Deeja ta saurare su hakan yaci tura,a ranar Khalees yaga ainihin kalar matar shi,dole suna ji suna gani ta fice daga asibitin Bin ta sukayi da kallo,tana fita Khalees ya lallaɓa ya bi bayan ta,napep ta tsare,ta shiga, shima ya shiga motar shi ya bi su Kai tsaye gidan Aunty Bintu ta nufa,mai adaidaita sahun yayi parking, wajen mai gadin ta ranci kuɗi ta sallami mai adaidaitan,sannan ta shiga cikin gidan Khalees ne ya fito daga motar shi ya baiwa mai gadin maƙudan kuɗaɗe,mai gadin ya fara godiya,yayi saurin dakatar dashi yace"kuɗin da Deeja ta karɓa a Wajen ka ne,ragowar kuma ka riƙe"yana gama faɗar hakan ya koma cikin motar shi ya tayar ya tafi Deeja kuwa a hargitse ta shiga cikin gidan,intisar tana zaune a falo tana buga game a wata Deeja ta shigo Cikin tsoro da mamaki intisar ta tare ta tana faɗin"sannu da zuwa,lafiya Aunty Deeja?"don ta san Deeja da nutsuwa Deeja ta kalle ta da rinannun idanun ta tace"ina Aunty Bintu?" "Ta tafi dubiya,ɗan wata ƙawar ta aka kwantar a asibiti" Deeja ta nemi waje ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,ita dai intisar kallon ta kawai takeyi a ɗimauce,zuwa can Deeja ta kalli intisar tace "Kina da ɗari biyar?" "Eh,amma dubu ɗaya ce" "Babu laifi,kai wa baba mai gadi ki ce ya ɗauki kuɗin shi"babu musu intisar ta miƙe ta nufi harabar gidan,jim kaɗan ta dawo ta shaidawa Deeja cewa baba mai gadi yace wani ya biya kuɗin Sai da gaban Deeja ya faɗi,don bata raba ɗayan biyu Khalees ne, saboda tayi zargin ya biyo ta,amma sai bata nuna ba,sai ma kwanciya da tayi tana tunanin mafita Intisar bata sakeyi mata Magana ba,ta koma kan computer ta cigaba da danne-dannen ta A haka suka kasance har sanda aunty Bintu ta dawo,da sallama ta shigo falon Dukan su suka amsa mata,tayi mamakin ganin Deeja,amma sai ta ɓoye,sukayi mata sannu da zuwa,ta amsa da sakin fuska,ta dubi Deeja da sigar tsokana tace "A'a!mai jegon gobe,yau wacce rana mai girma Khalees ya bamu aron ki?" Dukan su sukayi ƴar dariya, amma Aunty Bintu ta gane dariyar dole Deeja takeyi, saboda alamun damuwa sun bayyana akan fuskar ta Amma a lokacin Aunty Bintu bata nuna mata komai ba,ko ba komai bai kamata ta sanya ta tona cikin ta a gaban intisar ba Wajen ƙarfe tara na dare Aunty Bintu suna tare da Deeja a ɗakin Auntyn,in da suka bar intisar da salim da mei bi wa salim sumayya suna kallo a parlour,su Kuma suka zame suka nufi cikin ɗaki Cikin kulawa Aunty Bintu ta kalli Deeja tace"Deeja,ko baki gaya min ba akwai alamun damuwa a tare da ke,damuwar da ce ta dawo ko wata sabuwa ce?" Duk abinda ke faruwa zuciyar Deeja a dake take,sai yanzu ta fashe da kuka mei cin rai,sai da tayi mai isar ta,aunty Bintu batayi ƙoƙarin dakatar daita ba,ta kalli aunty Bintu tace "Aunty Ina cikin wani hali,aunty ina cikin tsaka mai wuyar fita,Aunty Ni dai tawa ta ƙare,Aunty Ni kam......." "Wait!wait!!yaya kikeyi min wasu zantuka kamar wata jahila?me kike nufi da hakan?ki fito kiyi min bayani sai nafi fahimtar ki,ko sakin ki Khalees ɗin yayi?" Cikin kuka tace"ƙanin saki yayi min aunty,Wai.....Wai kishiya zeiyi min" Cikin takaici Aunty Bintu ta ja dogon tsaki tace "to sai me?kishiya kan ki aka fara?ko akan ki za'a ƙare?ko a kanki zata zauna?"duk da cewar maganar ta doki ran ta "Aunty ƙawar matar Imran fa zai aura,,tace wai sai ta raba Ni dashi fa" "Ƙawar matar Imran kamar yaya?"Aunty Bintu ta tambaya a ɗan firgice "Wallahi ƙawar matar Imran zai aura,saura kwana uku ɗaurin auren" Aunty Bintu ta danne damuwar tava matsayin ta na babba tace"to sai me?ya auro ko waye ma?me zai tsorata ki?ke fa jinin ISHAQ ce,kuma kin san mu Bama sanya da addini,don haka kar kiyi wasa da addu'a,idan da nufi akayi auren kina zaune gayyar zata watse,idan ba da nufi bane ma zaki gani,na sanki da dauriya,to ki ƙara daurewa,kiji ki nuna baki ji ba,ki gani ki kauda kai,kar ki kuskura ki nuna musu ɓacin ranki,don zasuyi miki dariya, Allah shine gatan mu baki ɗaya,duk abinda ya samu bawa dama can tun kafin halittar shi Allah ya ƙaddara haka,don haka ki maida dukkan lamuran ki ga Allah" Kalaman Aunty Bintu sun sanyaya mata jiki,tayi shiru tana nazari, cikin kwantar da murya Aunty Bintu ta ƙara da cewa "Ki daina saka damuwa irin wannan a ranki, tabbas nasan akwai ciwo amma idan baki ɗauke shi da zafi ba zai zo miki a sauƙaƙe,kinga dai baki da wadatacciyar lafiya,kuma bake kaɗai bace,idan kika yi ganganci da Rayuwar ki har kika mutu mu kikayiwa asara,mijin ki wata zai auro,burin kishiyar taki kenan,to ina ranar wannan abu?" Likers sa commentors wannan naku ne👍👍👍🥰 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 12 "Nayi Miki alƙawari in Sha Allah zan bi maganar aunty,bazan Sanya damuwa a raina ba"Deeja ta faɗa tana mai son bawa kanta ƙwarin gwiwa "Yawwa little sis, Allah ya Miki Albarka, kwanta maza ki huta"Deeja ta kwanta batare da ta sake magana ba Wajen ƙarfe ɗaya na dare Deeja ta farka tayi ta sallolin nafila tana roƙon Allah ya kawo mata sassauci Washe gari Aunty Bintu da kanta ta kai ta akayi mata gyaran jiki,sannan aka mata lalle ja da baƙi,ga gyaran gashi,ba don cikin da ke jikin ta ba babu mai cewa tana da aure,ai kuwa Aunty Bintu ta rinƙa koɗa ta har ta saki ranta Kai tsaye daga nan gidan ta suka wuce,duk dakiyar Deeja sai da tsoro ya ɗarsu a ranta,amma dai haka ta cije ko don ganin idon aunty Bintu A harabar gidan suka samu Khalees,yana ganin ta ya taho da sauri,suka gaisa da Aunty Bintu a Mutunce, fuskar ta babu yabo babu fallasa ta dube shi tace"ga auta nan na dawo maka daita,ni zan wuce, Allah ya sanya alkhairi"tana gama faɗar hakan ta faɗa mota Khalees yazo daidai windon kusa da ita yana faɗin"Aunty mun gode Allah ya saka da alkhairi"ta kalle shi tace "a'a babu komai wallahi" Kuɗi ya zaro masu ɗan yawa ya miƙo mata yana murmushi,amma tace bazata karɓa ba ta gode,ta ja motar ta bar shi nan tsaye Ya mayar da hankalin shi kan Deeja,a lokacin ma tuni ta shige cikin gidan,don haka shima ya rufa mata baya A ɗakin ta ya riske ta,tana ƙoƙarin shiga banɗaki,amma shigowar shi bai hana ta shigewar ta ba,don haka bashi da zaɓin da ya wuce ya nemi waje ya zauna Bata wuce mintuna biyar ba ta fito, yana kallon ta ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa da suka amshi jikin ta,cikin ta ya fito ɗas gwanin sha'awa Ganin tana shirin ficewa ya sanya shi faɗin"Deeja zauna muyi magana" Babu musu ta nemi waje ta zauna, fuskar ta babu alamun damuwa,ta zuba masa idanu jin me zai ce Cikin taushin murya ya kalle ta yace"Khadija,kin san dai ina son ki ko?" "Me ya kawo wannan maganar kuma?"ta faɗa tana kallon shi Hannayen ta ya riƙo yace"ga dukkan alamu kina kallo na a macuci, mayaudari,kuma wallahi ba haka bane, maganar aure na dabam matsayin ki a cikin zuciya ta dabam,inayi miki son da ban taɓa jin irin shi akan wata ƴa mace ba,don haka kar kiyi tsammanin na daina son ki,aure na da Nadiya wata ƙaddara ce da bazan iya kauce mata ba,kiyi ta min addu'a kin ji?"ya ƙarashe maganar cikin Muryar tausayi Shiru ta ɗan yi,kafin tace"shikenan Khalees,komai ya wuce, Allah ya sanya alkhairi" Yayi ɗan murmushi yana faɗin"ameen na gode my dear wife" Mima ma babu shiri ta tattaro ta dawo daga Malaysia,Ana igobe ɗaurin aure ta iso,gidan Deeja ta wuni tana ƙara wayar mata da kai tare da jaddada mata ta riƙi addu'a, don itace makami,kuma makari ga mumini Anyi biki sosai,an sha shagali, Khalees sai faman rawar kai yakeyi,su Mima ne suke nunawa Deeja cewa kar ta damu,idan namiji yayi sabon aure haka yakeyi Ta ɗau wanka kala-kala da kwalliya,mai kwalliya ta musamman Aunty Bintu ta ɗauko,sai ta zamo tamkar itace amaryar Da daddare aka kawo amaryar,a lokacin Aunty Bintu bata ɗakin,sai Mima,kiyya da barrister zee da suke tare da Deejan Jin guɗa da iface-iface ya tayar da hankalin Deejan,ta miƙe tsaye a firgice,zee tayi saurin kamo ta ta zaunar da ita, Mima tace"cool down my sister,ki kwantar da hankalin ki,wannan damuwar ba mafita bace,kuma idan suka gano cewa kin sani sun fara samun lagon ki,don haka ki daure, Allah yana tare dake, Please my sis"da waɗannan kalamai zuciyar Deeja tayi sanyi,ta samu waje ta zauna Kai tsaye babban falon aka nufo da amarya,suma su Deejan duk a babban falo suka zauna, Deeja tayi kwalliya har ta gaji da kyau Umaima tana sawun farko a masu shigo da amarya, sukayi wa juna kallon-kallo ita da Deeja,daga bisani tayi mata murmushi mai nuni da zamu ganar da ke kuren ki, Deejan ma murmushin nuna ƙwarin gwiwa tayi sannan ta kawar da kanta Suka shigo gaba ɗaya,har da Afra,su Deeja kam basuyi mamaki ba, Saboda sun san Afra da Deeja jirgi ɗaya ya kwaso su suka sauka a tasha ɗaya,nan dai aka gabatar da al'ada sannan masu kawo amarya suka juya suna ta habaice-habaice,babu wanda ya tasamma kula su Umaima da wata ƙawar su mai suna siyama ne suka zauna da amarya,a cewar su suna ɗebe mata kewa,babu wanda ya damu da su,Aunty Bintu, kiyya da zee suka wuce gidajen su,ya zamana saura Mima kaɗai A zaton su umaima sun ɗauka duk sun tafi saura Deeja kaɗai,don haka kai tsaye ta shiga ɗakin Deejan a gadarance,ko sallama babu,gashi kuma tayi babbar Sa'a Mima ta shiga banɗakin da ke cikin ɗakin A lokacin Deeja ta chanja kayan ta zuwa na bacci,baby Pink,sai wata ƴar hula da ta ɗora akan ta, Alqur'ani ne a hannun ta tana karantawa a zuci,sai ganin mutum tayi a gaban ta Duk da ta ɗan tazama hakan bei hana ta ɗagowa cikin nutsuwa ba,tana ganin umaima ce ta maida kanta ga abinda takeyi Umaima ta saki shewa tare da faɗin"da kyau MATAR KHALEES ta wucin gadi,ko da yake nayi miki uzuri,da alama giyar soyayya da miji ce take ɗiban ki,amma nan gaba idan zaman gidan Khalees ya gagare ki,ko mukayi miki adalci muka maida ki baiwa a nan gidan,nasan dole za'a girmama mu ko?" "Ke jahila daƙikiya!ke har kin isa ki maida ta baiwa?ke dai ki lallaɓa auren ki da aka samu aka liƙawa saunan mijin ki,amma Deeja tafi gaban bauta ko a gidan ubanki ne,banza mei toshashshiyar ƙwaƙwalwa,kije ki nemo ilmi ko Allah zai sa a rage asara, Deeja tafi gaban bokan ku ko malamin tsibbun ku"Mima dake fitowa daga banɗaki ce ke faɗin haka A tsorace umaima ta kalle ta,har ga Allah tana tsoron Mima,don da ganin ta bata da mutunci,Mima ta ƙaraso inda umaima take ta nuna mata ƙofa tana faɗin"maza ɓace min da gani tun kafin wannan koɗaɗɗiyar fuskar taki ta yayyage yanzun nan"sum sum sum umaima ta fice daga ɗakin,cikin sanyin jiki Tana jin Mima na jan dogon tsaki,amma bata da damar magana don duk masifarta mimab ta sha gaban ta Mima ta dubi Deeja tace"sister sai haquri fa,kar ki tsaya zub da ajin ki akan Waɗannan karnukan" Deeja ta mere baki tace"ai tuntuni na bawa banza ajiyar su,don da alama basu san ƙimar kansu ba" Ina gaishe ku likers da commentors,kune ƙwarin gwiwa na😁🥰😍 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 13 A hargitse umaima ta shiga ɗakin Nadiya tana faɗin"ƙawa!ashe wannan shegiyar likitar tana nan?tsinanniya masifaffiya" Nadiya tace"rabu da ita,ai dole ta tafi tunda dai ba gidan ubanta bane" Mima bata juma ba ta wuce gida,tana fita Deeja tayi saurin datse ɗakin ta da makulli,kamar ta sani kuwa,motar Mima na barin gidan su umaima suka zo suka fara buga mata ƙofa,cikin sauri ta ɗauko airpiece ta kunna Suratu Yusuf a wayar ta ta toshe kunnen ta, a haka bacci yayi awon gaba da ita Washe gari a kitchen ta Samu amarya da ango,cikin shauƙin soyayya suke sarrafa abinda zasu ci,ta sha mamakin ganin Khalees ko kallon ta baiyi ba,amma ta dake tace "Yallaɓai ina kwana" Ya waigo yana kallon ta kamar mai yin mamaki,sannan yace"lafiya,bazaki gaida amarya ba?" Wani watsatstsen kallo tabi amaryar dashi kafin tace"amarya ina gajiya?" Cikin salon kissa Nadiya tace"gajiya kam babu ita bata da muhalli, saboda na mallaki gwarzon namiji Ni kaɗai,ya zama nawa" Wani malalacin murmushi Deeja tayi,sannan ta ɗaga babban ɗan yatsan hannun ta alamar jinjina tace "Ina taya ki murna,kuma na sara miki babbar mace"tana gama faɗin hakan ta ɗauki abin da ya kawo ta tayi hanzarin barin kitchen ɗin Abin yazowa nadiya a bazata,don tayi tsammanin zata ƙuntata ran Deejan amma sai taga akasin haka,don haka ta bi ta da ido zuciyar ta cike da ƙunci Duk da hakan ya ɓata wa Deeja rai amma sai tayi ƙoƙarin dannewa,ta shirya ta karya sannan ta fice zuwa office Daga office gidan barrister zee ta wuce,zee ta rinƙa tausar ta,tare da ƙara jaddada mata ta riƙi addu'a,kuma sam kada ta daina bawa mijin ta kulawa,anan ta yini har bayan la'asar sannan ta koma gida A falo ta iske su, Nadiya ta kwanta a jikin shi tana ta zuba masa shagwaɓa,shi kuwa duk yabi ya ruɗe,ta shigo da sallama,amma babu wanda ya amsa,itama sai ta ɗauke kanta da nufin faɗa wa ɗakin ta "Ke dakata!"a cewar Khalees Cak ta tsaya batare da ta juyo ba,bai damu ba yace"daga ina kike?" "Daga office,da na taso sai naga ya kamata na bawa amarya da ango waje su sake,don haka nima nayi nawa wuri"ta bashi amsa "Tabbas kinyi tunani mai kyau"a cewar Nadiya Deeja ta kalle ta sannan tace"ai ni koyaushe tunani na mai kyau ne,bana abu mara kyau,ba kamar sauran gama garin mutane nake ba,ina fatan kin gane"bata jira amsar ta ba ta shige ɗakin ta Nadiya tana mamakin Deeja,amma idan ta san wata ai bata san wata ba,dole a haɗa da asiri da tuggu don ganin bayan ta,don haka ta ɗaga kai ta kalli Khalees cikin kissa tana faɗin "Love da alama gidan ka yafi ƙarfin ka ko?"ya kalle ta cikin kulawa tare da faɗin"me kika gani?" "Ace kamar ka da kuɗin ka da martabar ka amma ace matar ka tana fita aiki?me za'ayi tunani kenan?baka bata abinci kenan fa,wannan ai sai ya zubar maka da mutunci"ta tsare shi da idanu don ganin yanayin shi Shiru yayi kafin daga bisani ya gyaɗa kai yana faɗin"zancen ki gaskiya ne love,dole nayiwa tufkar hanci" Wani sanyin daɗi ya ratsa Nadiya,ta sake gyara kwanciyar ta tana faɗin"Weldone my love,lallai ka cika jarumin maza"yayi wani murmushin nuna jin daɗi yana kallon ta A ɗaki ya samu Deeja tana danne-danne a laptop ɗin ta,ganin yadda ya shigo mata fuska babu rahama ya sanya itama ta dake ta sha mur, tun daga amsa sallamar shi bata sake duban inda yake ba,shima bai damu ba ya dube ta yana faɗin "Ban amince miki ki qara fita aiki a gidan nan ba, saboda ba zaman kanki kikeyi ba,da fatan kin gane"yana gama faɗin"hakan ya juya ya fice daga ɗakin Ta ɗan bi shi da kallo,kafin tayi ɗan murmushi,ta sani sarai aikin Nadiya ne,ai kuwa zata basu mamaki Washegari ta fito cikin shirin riga da zani na lace,ta ɗora ƙaton mayafin ta a kanta, hannun ta rataye da jakar ta Yau ma kamar kullum a falo ta tarar dasu suna ciyar da junan su abinci,ko kallon banza basu ishe ta ba tayi hanyar fita "Ke dakata!"taji Muryar Khalees a fusace Ta juyo fuskar ta babu alamar damuwa,ta zuba masa ido tana jiran mei zai ce "Ina zakije?"ya tambaye ta "Idon ta fes cikin nashi ta amsa"in da na saba zuwa,wato wajen aiki" "To ban bada izini ba" Ai dama ba kai ka bani izini na fara aikin ba "To sai ki zaɓi ɗaya,auren ki ko aikin ki? Maganar ta dake ta sannan ta qara jinjina wa kaidin Nadiya,Amma da yake jaruma ce idanun ta fes cikin nashi kanta tsaye ta amsa"na zaɓi aiki na" Ba Khalees ba,hatta Nadiya ta tsorata da jin furucin Deeja, Deeja bata kula ba ta juya ta fice daga falon Da shirin ta ta dawo daga wajen aiki,a nufin ta duk abinda Khalees zai yi mata ta tanadi abinda zata mayar masa,sai dai ko da ya dawo ko kallon sashen ɗakin Deejan bai yi ba A haka rayuwa ta kasance musu har zuwa tsawon sati biyu, Nadiya da umaima babu irin asiri da tuggu da basuyiwa Deeja ba amma a banza,duk da anyi nasarar raba ta da mijin ta, tsakanin ta dashi sai kallo daga nesa,amma Allah ya cire mata damuwar hakan Da farko su Farida suna kawo mata ziyara suna ɗebe mata kewa,amma sai da Nadiya tayi tuggun da Khalees ya hana su zuwa,hakan bai dame ta ba don sau tari ta kan je gidan hajiyan suyi hira,hajiyar tayi ta mata nasihohi da ƙarfafa mata gwiwa #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 14 A haka har lokacin haihuwar ta yayi,tun safe takejin ciwo,amma hakan bei hana ta fita aiki ba,don ciwon ba sosai yake damun ta ba,sai dai ta sanarwa Aunty Bintu da Aunty kiyya cewa EDD din ta ya cika, kuma ga dukkan alamu zata iya haihuwa yau Daga wajen aikin ta kai tsaye gidan Aunty Bintu ta wuce,ai kuwa ko mintuna ashirin batayi da zuwa ba ciwo ya buɗe mata,aka gaggauta nufar asibiti daita Sun kai kimanin awa biyar kafin ta haifi sankacecen yaron ta mai tsananin kama da mahaifin shi,sai a sannan hankalin su ya kwanta,Aunty Bintu ta kira kiyya ta sanar da ita,nan da nan tace gasu nan zuwa Aunty Bintu ta kira Khalees ta sanar masa,amma sai yace bazei samu ɓullo wa ba sai anjuma,yana gama faɗin haka ya kashe wayar Hakan ya bawa Aunty Bintu mamaki ƙwarai da gaske,sai dai bata sake saurarar shi ba ta zauna jiran su kiyya Kafin su kiyyan su iso har an shirya baby,ita Kuma Deeja an kai ta ɗakin hutu,su Aunty Bintu suna zaune riƙe da yaron su kiyya suka shigo Nasir mijin kiyya ne ya kai su,momy Aysha,Mamie babba, nuwaira,lubaisa,sai aunty salma babbar yayar su fauwaz Nan suka zauna suna kallon baby mai tsananin kama da mahaifin shi,da murmushi a fuskar kiyya tace "Babyn nan kyakkyawa ne,ya kwaso abban shi da yawa"lubaisa ta leƙa fuskar shi tace"ƙwarai kuwa, Allah ya raya Basu dauki lokaci ba suka tafi,sai dai sun kawo duk wani abu da suka san mai jego da jariri zasu buƙata Deeja kam ta sha gata kala-kala,bayan ta nutsu Aunty Bintu ta haɗa mata tea ta bata,haka tayi ta kulawa da ita sosai Sai dai rashin zuwan mijin nata ya ɓata mata rai duk da cewa batayi mamaki ba,amma sai ta bar abin a ranta Daga asibiti gidan Aunty Bintu suka wuce kai tsaye,har lokacin Khalees bai zo ba,amma hajiyar shi da ƙannen shi sun zo,don a tare suka fito daga asibitin,hajiyance take tausar Deejan,ita kuma Deeja tana nuna mata babu komai Khalees ko kiran ta a waya baiyi ba sai da ta kwana shida sannan yaje shi da Nadiya,an karɓe su babu yabo babu fallasa ba'a nuna musu wata damuwa ba, Nadiya ta Sha kwalliya amma sai da ta raina kanta da taga su Bintu da su Mima, don itama a lokacin tazo Mima ce ta kawo musu jaririn,ya ƙura masa idanu yana kallon shi,wata ƙaunar shi tana ratsa shi,a hankali moments da sukayi da Deeja ya fara dawo masa,ya shagala yana ta kallon shi ƙwalla na ƙoƙarin taruwa a kwarmin idanun shi, nadiya tana kallon shi tana ganin ikon Allah,ganin kallon yayi yawa sai nadiya tayi saurin amshe shi tana kallon shi,tace"babyn kyakkyawa kamar baban shi" Bai fi second goma a hannun ta ba ta miƙawa Mima shi,dama dabarar shi ta raba shi da hannun Khalees Ya kalli aunty Bintu yace"yanzu sai ayi min list na abubuwan da ake buƙata sai na bayar da kudin ko?" "Ai ko nawa ka bayar ma yayi"a cewar ta Sai ya zaro bandir na 50k ya dire mata yana faɗin"to ga dubu hamsin" Abin ya basu mamaki da haushi, amma suka dake,Mima tace"yayi,an gode,sai ka zaɓar wa yaron suna" Ya miƙe tsaye yana faɗin"ace na bar mata zaɓi,Ni zan wuce, Allah ya raya" "Ameen,sai anjuma"a cewar Mima suka ɗauki kuɗin suka fito, suma su Khalees suka biyo bayan su, zuciyar Nadiya kamar ta fashe don baqin ciki,ta so tsiya ta tashi, dama ita ta yanke nawa Khalees ɗin zai bayar,amma kuma idan sun san wata basu san wata ba A cikin mota nadiya ta kalli Khalees tace"honey, gaskiya wadannan mutanen basu da mutunci da alama" Ya kalle ta yana faɗin"me kika gani?"tace "don Allah kalli abinda sukayi mana,suna magana sai wani ciccin magani sukeyi,ga ƴar wulaqancin ko ƙeyar ta bamu gani ba,kuma ka bayar da kuɗi amma an kasa yi maka godiyar da ta dace, maganar gaskiya bakayi dacen mata ba" Yayi ɗan shiru yana nazari,ganin ya ɗauki lokaci baiyi magana ba ya sanya ta faɗin"bakace komai ba" Ya amsa mata da cewa"ai na riga na tanadi hukuncin da zan yanke tuntuni,don ta gama fitar min a rai,gashi ko ke shaida ce bata jin magana ta,kuma kalli irin wulaqancin da tayi mana,ta nunawa duniya Ni ba komai bane a wajen ta,don haka dole nayiwa tufkar hanci" Wani sanyi ya ratsa Nadiya,amma sai tace"No Kar kayi saurin yanke hukunci,ina da shawara" Ya kalle ta yana faɗin"menene shawarar ki?" "Why not bazaka saka wa yaron sunan dad ɗi na ba?"ta ƙarashe tana tsare shi da idanu Batayi mamakin ɗan murmushin da yayi ba,yace"good idea,haka za'a yi" Shiru tayi tana kallon shi fuskar ta ɗauke da murmushi,a ranta kuwa yabawa takeyi da aikin bokan ta mai faɗa da cikawa Waya ya ciro ya danna number din Deeja,wadda rabon da ya kira ta har ya manta,a da yayi saving number din da luvly Deeja,amma Nadiya ta mayar da sunan Khadija Bugu ɗaya ta shiga,a lokacin tana zaune tana kallon su Mima da suke ta surutun wulaqancin Khalees ita da intisar da Farida matar yaya Ma'aruf,ta san za'a rina,shiyasa batayi mamaki ba Wayar ta ce ta soma ruri,ta kai hannu ta ɗauka,ganin sunan Khalees ta tsaya tana kallon wayar da mamaki,amma dai sai ta ɗaga "Assalamu alaikum"tayi masa sallama "Wa'alaykis salam,sannu uwar isassu" Tayi shiru zuwa can tace"ina wuni!" "A'a riƙe gaisuwar ki,na gode da wulaqanci,sannan da na bar miki zaɓi,amma yanzu na fasa" "To ba laifi,wanne suna ka zaɓa masa?"ta tambaye shi babu alamun damuwa a tare da ita "Sa'eed nake so a saka masa" "Kamar sunan mahaifin Nadiya"ta faɗa da mamaki da ɓacin rai "Eh,haka nake buƙata" "To bazan sanya ba,idan tayi zuciyata haifi nata ta sanya"tana gama faɗin hakan ta kashe wayar baki daya tana masifa Su Mima suka mai da kallon su kanta,ta kalle su tana faɗin"kunji wai sunan mahaifin Nadiya zaa saka?" "Kamar yaya sunan mahaifin Nadiya?ba cewa su Aunty Bintu yayi ki sanya sunan wa yaron ba?"cewar Aunty Farida cikin mamaki "Ya chanja shawara,wai na saka sunan baban matar shi, saboda ni daga sama na faɗo bani da uba"ta ƙarashe tana watsa hannayen ta a iska "Kan bala'i!lallai ma wannan mutumin ya cika ɗan rainin hankali,to me ya mayar da ke?sokuwa ko me?"a cewar Mima cikin fushi,dama a cikin family ɗin su Mima tana daya daga cikin masifaffu Murmushin takaici kawai Deeja tayi,don tafi zargin akwai abinda Nadiya tayi masa yakeyi mata haka #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy_bee Page 15 Ranar suna an sha shagali,yaro ya amsa sunan Mahmud,sunan mahaifin Deeja, amma Mima ta ɓoye sunan da Affan,anyi hidima sosai,mai jego ta sha ado cikin manyan kaya kala-kala ita da jaririn ta, wasu ita ta siya,da yawan su kuma siya mata akayi,don daga gidan professor Ismail an kawo mata sama da kala ashirin kayan fitar suna,banda na jaririn ta ma,ga su Aunty Bintu,hidima dai sai son barka Har da umaima akazo suna,sarai sun gane cewa leƙen asiri tazo yiwa Nadiya,don haka Deeja ta zage gayu da facaka iri iri,mai make-up din da tayi mata lokacin bikin mijin ta da nadiya ita Aunty Bintu ta sake ɗauko mata,ga sutura masu asalin tsada da ɗinki mai kyau,ga adon gold abin sai son barka,ga cima kala-kala sai wanda Mutum ya zaba,ba umaima ba kaɗai,hatta da lubaisa sai da ta raina kanta Umaima bata wani dade a gidan sunan ba ta tafi gida,tana komawa ta kirawo Nadiya ta shaida mata abinda ya faru a gidan sunan, Nadiya taji takaici sosai don so tayi ace Deeja ta wulaƙanta,amma wai umaima ke sanar mata yadda Deeja ya haska kuma ake tarairayar ta a wajen sunan,don haka tace "Ƙyale ta umaima, alƙawari fa na ɗauka,sai na rusa mata farin ciki,zata san cewa da ni Nadiya gagari kowa takeyi,sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane,sai na sanya ya ɗora hannu aka na rasa mafita,don wallahi sai na sauke mata wannan ji da kan nata,sai tayi data sanin zuwa duniya"ta ƙarasa cikin ɗaukar alwashi da ɓacin rai "Wallahi ina bayan ki,ke dai kawai ki shirya,dole mu komawa boka"a cewar umaima "Ai haka za'ayi kawai,don naga alama tana ɓata min aiki,kuma idan nayi mata baya kama ta" Umaima ta jinjina kai tana fadin"wannan ai mei sauƙi ne,tunda kin gama da wanda take taƙamar ai shikenan" "Ke dai bari kawai umaima,duk da na raba su harkar gaban ta kawai takeyi,ko kaɗan bata da damuwa,kuma ya kasa kataɓus akanta" "Keep on trying, watarana zakiyi nasara"a cewar umaima,tana mai ƙarfafa mata gwiwa" "Har sai kin faɗa?ai na riga na gama yanke abinda zanyi mata na samu ta fita daga rayuwa ta" "Okay!to Sai na jiki"suka kashe wayar Taro ya tashi lafiya, hankalin Deeja ya kwanta sosai,don yadda aka tarairaye ta aka nuna musu kulawa ita da jaririn ta ya sanya ta kuma sakin ranta,rashin damuwa da al'amarin ta da Khalees yakeyi kwata-kwata baya danun ta,don ta sani ba yin kanshi bane,kuma bata taɓa fashin saka shi a adduoin ta ba Gyara sosai aunty Bintu tayi mata,ga ƙara wayar mata da kai da takeyi, kullum cikin tofe ɗan ta da adduoi kala-kala take,kuma dare da rana bata gajiya da yiwa mijin ta addu'a,tare da addu'ar Allah ya bayyana mata yayyen ta,tana son zuwa Yola amma fargaba ta hana ta Watan ta guda amma har lokacin bata koma gidan auren ta ba,sai dai ta koma bakin aikin ta,Affan kuwa yayi kyau yayi ɓulɓul abin shi,kamannin shi da Khalees sun ƙara fitowa sosai Zaman Deeja a gidan Aunty Bintu ya taimaka ƙwarai wajen tafiyar da kaso mai yawa na damuwar ta,ta nutsu sosai tana aikin ta,tana son komawa makaranta don ƙaro karatu amma tana tsoron tunkarar Khalees da batun,don haka taga gwara ta haƙura kawai,har sanda al'amura zasu daidaita Don haka ta cire damuwar komai a ranta,ta riƙi aikin ta da yaron ta sosai Watanni biyu suka shuɗe,Deeja tayi kyau tayi haske sosai,a lokacin sati biyu ya rage su Aunty Bintu su tafi kasar Syria,don haka Deeja ta fara shirin komawa gida Ranar da zata koma Aunty Bintu ta aika aka gyara mata ɗakin ta,nadiya na zaune tana jin kiɗa sai ga su intisar sun shigo da sallama Su shida ne,intisar,ilham ƙawar intisar sai masu aikin Aunty Bintu su huɗu Sheƙeƙe ta kalle su sannan ta zare airpiece ɗin kunnen ta tana kallon su a wulaƙance,cikin isa da gadara tace "ku kuma fa?daga ina?" Intisar ta kalle ta sama da ƙasa tace"yi haƙuri,ba wajen ki muka zo ba,kin gane?"tana gama faɗin haka tayi wucewar ta ciki,suma sauran suka biyo bayan ta Nadiya ce ta biyo bayan su tana faɗin"maza maza kuzo ku fice min daga gida,matsiyatan yara kawai"ko kallon ta basuyi ba suka wuce suka kama aikin su Basu juma sosai ba suka koma gida,suka zayyane wa Auntyn Abinda Nadiya tayi musu amma suka mayar da ita mahaukaciya,sukayi ta dariya Da yamma su Aunty Bintu suka raka Deeja gidan ta tamkar masu kai amarya, nadiya ta tsorata sosai ganin dawowar Deeja,ganin Deejan babu alamun damuwa a tare da ita ya firgita Nadiyan,amma sai tayi tsammanin ko ta san da tafiyar da Khalees yayi ne, kasancewar Khalees yaje wata seminar a Abuja jiya,Kuma bazai dawo ba sai bayan sati uku Su Aunty Bintu suka gama abinda ya kawo su suka tafi, Nadiya na ganin sun tafi sai tayi azamar shigowa Deeja na zaune tana shayar da Affan Nadiya ta shigo,kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kanta,don ta san ko ma menene ya kawo ta ba na arziki bane,don ko sallama batayi ba. Nadiya ta dube ta a wulakance tace "Ai dole ki ɗauke kanki,don ni na baki damar shigo min gida har zan shigo in da kike ki ɗauke kai,wato kinji labarin miji na baya nan ko?hakan yayi kyau,amma ki shirya karɓar tanade tanade da nayi miki......." Karatun Alkur'ani Deeja ta sanya,ta janyo airpiece ta saka a jikin wayar ta toshe kunnuwan ta dashi hakan ne ya tilasta wa nadiya ficewa daga ɗakin tana jan tsaki,a ranta tana ayyana ko me zatayi sai tayi don ganin ta kuntatawa Deeja Daga lokacin ya zamana kowa harkar shi yakeyi,sai dai Nadiya ta tsani ta buɗe idanu taga Affan,ta tsani yaron tsana mafi munin,don haka ta sha alwashin sai taga bayan shi,har da uwar tashi ma Har da zan ɗauki hutun ma'aikata na yau nima,kawai sai nayi tunani na fasa😁😉 Ayi min afuwa biki mukeyi shiyasa akaji ni shiru #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Kwanan nan fa sai ana min uzuri 😅 saboda ciwo na da yake yawan tashi yana buƙatar hutu,still ayyuka sunyi yawa,gashi nan dai gashi nan dai,duk da haka ina godiya kuma at the same time Ina neman afuwa 🙏 Page 16 Sai dai bata samun damar,hakan, saboda Deeja bata taɓa barin Kofar dakin ta a buɗe matuƙar ba fitowa zatayi ba,kuma indai zata fita goya shi takeyi ko ta datse ɗakin Kwanan ta tara da dawowa da yamma bayan tayi sallar la'asar tana zaune tana gyara kayan Affan a taji ƙaurin miyar da ta ɗora,da sauri ta miƙe ta fito ta gyara miyar sannan ta koma ɗakin ta Tun kafin ta ƙarasa ɗakin taji Affan ya canyare da kuka,da gudu ta ƙarasa don ta san bacci ta fita ta bar shi yanayi Abinda ta gani ne yayi matuƙar gigita ta, Nadiya ce take shafawa Affan niƙaƙƙen barkono a fuska,wani ihu Deejan ta saki sannan tayi kan Nadiya, Nadiya ta firgita da zuwan ta amma tayi saurin watso mata ragowar yajin, Deeja ta goce sannan ta hankaɗe Nadiyan ta ɗauke ɗan ta Kai tsaye banɗaki ta nufa da yaron tayi masa wanka sosai,amma har lokacin bai daina kuka ba,ta fito duk jikin ta rawa yakeyi,a lokacin Nadiya bata ɗakin,ta cire zanin gadon ta sanya wani ta kwantar da yaron tana kallon yadda fuskar shi tayi ja yana ta tsanyara ihu,kamar wadda aka tsikara tayi maza ta ɗauke shi da nufin shayar dashi amma yaƙi kamawa,sai kawai ta fashe da kuka mai motsa rai, hankalin ta ya kai ƙololuwa wajen tashi,tana tunanin mafita amma ta rasa dabara Wayar ta ta soma ruri,a firgice ta ɗauka ko ganin sunan batayi ba ta ɗaga Muryar ƙawa ta safeena taji tana faɗin"Hello! Deeja bakya ji na ne?" Sabon kuka Deeja ta saki, safeena tace"subhanallahi!ina hanya gani nan zuwa" A harabar gidan ta samu Deeja tsaye tana jiran ta,ko daidaita parking batayi ba ta fito tana faɗin"lafiya dai?" Deeja bata iya magana ba illa nuno mata Affan da zuwa yanzu ya fara rage kuka,da sauri safina ta amshe shi suka faɗa mota suka nufi asibitin doctor su'ad Tayi masa abinda ya dace,ya samu bacci,sai a lokacin Deeja ta samu nutsuwa,tayi musu cikakken bayanin abinda ya faru Salati suka sanya suna tafa hannaye, doctor su'ad tace"lallai matar nan bata da ko ɗigon iymani, jariri yaron da bazai iya aikatawa kanshi komai ba ballantana ya aikatawa wani me yayi zafi haka za'a yanke masa ɗanyen hukuncin da ko babba bazai jura ba?" "Wanne laifi kuwa?bakin hali ne fa kawai,ke dai Deeja ki ƙara kula da yaron ki kawai"a cewar safeena cikin ɓacin rai "Ina kula dashi sosai, duk da cewa Allah ne mai tsarewa,yanzun ma Allah ne kaɗai yasan abinda zai faru ya taƙaita mana wahala"a cewar Deeja Doctor su'ad tace"hakane kam,yanzu dai gashi nan an magance matsalar,a shawarce Kar ki nuna mata damuwa,ki rabu da ita,ki bar ta da halin ta kawai" Deeja ta girgiza kai tace"Ni dama ko kallo bata ishe ni ba,ko me zatayi bata gaba na,idan tayi min na rabu daita ai idan tayiwa wani bazai ƙyale ta ba ko?" "Hakane kam, to Allah yasa mu dace"a cewar safeena Doctor su'ad ta amsa da"ameen Sun daɗe suna hira har maghriba,sukayi sallah sannan safeena ta mayar da Deeja gida Har parlour suka shigo suna hira da dariya, Nadiya ta fito da sauri,ganin su Deeja a haka ya tabbatar mata da babu matsala,nan da nan ranta ya ƙara ɓaci,Deeja na kula da ita,amma sai ta nuna tamkar bata ganta ba Deeja ta cigaba da gudanar da rayuwar ta yanda ya kamata,har zuwa sanda su Aunty Bintu zasu tafi ƙasar Syria,tafiyar ta kama ranar Lahadi,don haka ranar ta kama babu aiki,don haka Deeja taje yi musu sallama A can ta yini,itace ta kai su airport,a gaban ta akayi komai ƙarfe biyar na yamma jirgin su ya tashi,itama ta juya zuwa gida A falo ta samu Nadiya da umaima da ƙawar su siyama zaune suna hira,da farko ƙin shiga tayi ta tsaya daga bakin ƙofa don jin mei zasu ce Umaima taji tana faɗin"ai tunda kin ce aikin baya cin ta na samu wani boka ya bani wani magani tace ayi haƙa a ƙofar ɗakin ta a binne,to tabbas zata gamu da hauka idan ta tsallaka,kinga tana can tana hauka,ga miji ya dawo naki ke kaɗai,yaron kuma zai dawo ƙarƙashin ki,kin ga sai kiyi abin da kika ga dama ko?" "Kuma nima akwai wani hatsabibin boka da na samo,ya bani siddabaru yace na binne a maƙabarta,hakan zai sanya ya tsane ta har yaji baya ƙaunar ko ganin ta a kusa dashi,kinga dole ta bar gidan ko na uban ta ne" Nadiya ta amsa"good job! Allah ya bar mu tare,da alama kuna damuwa da al'amura na,idan na gama da ita sai na koma kan waɗannan matsiyatan ƴan uwan nashi,nan gaba ko kallon shi zasu yi sai dai daga nesa Umaima ta buɗe baki da niyyar yin magana Deeja ta faɗa falon fuskar ta babu alamun damuwa,duk da cewar ta tsorata da lamarin su,ganin ta sai suka sha jinin jikin su,ta ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya a raine,sannan ta ɗauke kanta ta shige ɗakin ta Sun firgita sosai,don sun ga alamun hirar su,don haka suka chanja hira Tun daga lokacin ta sake zage dantse ga kulawa da take bawa kanta da yaron ta,a haka har tsawon sati guda A lokacin ne Khalees ya dawo,a lokacin Deeja bata nan tana wurin aiki,don haka Nadiya ta samu cikakkiyar damar ƙulle ƙullen ta na kissa da kisisina da sharri,shi kuwa Khalees ya bi ya haye kai Da ta dawo tun a parking space taga motar shi,hakan ya tabbatar mata da dawowar shi,hakan bai dame ta ba,kanta tsaye ta shigo cikin gidan Bata same su a parlour ba,hakan bai dame ta ba ta shige ɗakin ta Bayan Isha'i tana jin su a parlour suna ta shewar su,ta so ta fito amma sai ta tuna da cewa zai iya yi mata wulaƙanci a gaban Nadiya,don haka tayi zaman ta a cikin ɗakin ta Washegari sun haɗu dasu a kitchen,batare da damuwa ba ta gaishe su,amma ko kallon banza bata samu ba,bata damu ba ta cigaba da harkar gaban ta, Nadiya sai kwarkwasa da kisisina takeyi masa,shi kuwa sai faman tarairayar ta yakeyi,ko kallon su Deeja bata sake yi ba,tayi aikace-aikacen ta ta kammala ta fice daga kitchen ɗin Tsawon kwanaki uku kenan,da dawowar Khalees,amma ko sannu bata haɗa su da Khalees ba,idan tayi masa magana ma baya amsawa, don haka ta haƙura da yi masa magana Dawowar ta kenan daga Wajen aiki,tana shigowa parlourn taji an bangaje ta,da sauri ta ɗago don ganin waye, Nadiya ce Ganin Nadiya ce ta san magana take nema,don haka ta mayar da kallon ta kan fuskar wayar ta Dawowa tayi da baya ta kalli Deejan a ƙasƙance tana faɗin"oh sorry fa!na ɗauka akuya na bangaje shiyasa kika ga ban damu ba" Wani banzan kallo Deeja ta watsa mata sannan tace"kar ki damu,nima dama sai naji kamar bangazar batayi min kama da da ta mutum ba,nayi tsammanin tinkiya ce ta bangaje ni shiyasa ban kula ba" A zafafe Nadiya tazo wajen tana yi mata kallon wulaƙanci tace"ke!ki shiga taitayin ki ko kuma jikin ki yayi tsami" Wani watsatstsen kallo Deeja ta watsa mata na sama da ƙasa sannan tayi wani murmushin rainin hankali tace"haba yarinya!ko wanda ya dire ki bai isa ba ballantana ke!!" Cikin ɗaga murya ta shiga faɗin"wanda ya kawo ni fa kika ce, luvly kana jin abinda kike cewa" Faɗar hakan ya tabbatar wa Deeja cewa Khalees ne ya shigo parlourn,sai ji tayi yace "Ai tuntuni dama ta nuna tafi ƙarfi na,don haka dole ta bar min gida na"ya ƙaraso inda Deeja take ya zaro takarda a envelope ya miƙa mata yana duban ta a wulaƙance yace"kije na sake ki saki ɗaya,ki tattara ki bar min gida,dama ban ɗora miki idda ba" Gaban ta ne yayi mummunan faɗuwa a ranta ta furta"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"tare da amsar takardar,bata kuma magana ba ta wuce ɗaki Tana jiyo shewa da habaice-habaicen nadiya,tayi mata banza,ta kwashi abubuwan ta masu muhimmanci ta zuba su a mota ta fice daga gidan Sai da tayi ƴar doguwar tafiya sannan tayi parking tana nazarin wajen zuwa,daga bisani ta yanke shawarar wucewa gidan ta da ta gina, saboda dama tuni ta zuba komai Ƙerarren gida ne dake unguwar Na'ibawa,duk da ƙarami ne amma ya tsaru sosai,ta shigo da motar ta ta rufe gidan ta shiga ciki Kwanan ta biyu babu wanda ta sanarwa mutuwar auren ta,sai dai akwai abinda ta shirya,don a ganin ta lokaci yayi da ya kamata ta samu farin cikin da ta rasa shekaru masu yawa,don haka ta ɗauki hutu a wajen aikin ta,ta soma shirye shiryen barin garin Satin ta biyu ta gama shirya komai,motar haya ta hau airport,daga nan ta haye jirgin su zuwa in da take fata... Ayi min afuwa Please "Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 17 Ƙarfe uku na yamma ta sauka a garin jimeta da ke Adamawa,ta sha wahala sosai kafin ta gano address ɗin gidan da Dr Mahmud ya taɓa bata kafin rasuwar shi saboda bata san garin ba,bata samu kanta a ƙofar gidan ba sai bayan huɗu na yamma A bakin gidan ta samu wani dattijo,tayi masa sallama ya amsa,ta durƙusa cikin ladabi ta gaishe shi cike da girmamawa,ya amsa yana ƙare mata kallo,bayan sun gaisa ya dube ta yana faɗin "Yarinya idan na gane ki zan iya cewa autar wajen ZAINABA ce ko?" Murmushin Deeja ya faɗaɗa,tace "eh baba,nice autar ta" "Allah sarki zainab! Allah yayi mata rahama ya kyauta makwanci,ita da mai gidan na ta" Deeja ta amsa da"ameen cikin sanyin murya" Yace "ki tashi ki shiga ciki,mariyan tana ciki"Deeja ta miƙe zata shiga,yace "kawo yaron,ko bacci yakeyi?" Deeja ta amsa da"bacci yakeyi" "Allah sarki!yaya sunan shi?" "Sunan mahaifi na ne amma ina kiran shi da Affan" "Allah sarki! Allah ya raya shi" Ita dai Deeja tayi shigewar ta gidan Da sallama ta shiga tana rarraba idanu,wata dattijuwa na zaune tare da samari da ƴan mata a tangamemen tsakar gidan, ƙarƙashin wata ƙatuwar bishiyar mangwaro,sai hira sukeyi,da alamu dai jikokin ta ne,duka suka dawo da hankalin su kanta Ta ɗan daburce kafin daga bisani ta daidaita nutsuwar ta,ta gaishe su sannan ta fara bayani cikin dakiya "Ni ƴar gidan zainab ce,ƙanwar su nusaiba da Yusuf" "Ai na ga alamu, Allah yaji ƙan zainaba, Hadiza ce ko?"a cewar dattijuwar "Eh nice"ta bata amsa kanta a ƙasa "Masha Allah!ke suwaiba maza kai ta ɗaki tayi sallah ta huce gajiya,ki kai mata abinci maza"kafin ta rufe baki ɗaya daga cikin ƴan matan ta miƙe ta karɓi akwatin Deeja ta jagorance ta zuwa wani ɗaki Bayan Isha'i Deeja ta kammala komai da komai,ta nufi ɗakin Hajiya Mariya,tayi sallama Hajiya Mariya ta amsa tare da yi mata yi mata izinin shigowa,ta shigowa,ta shiga gami da neman waje ta zauna,Hajiya Mariya ta dube ta cikin kulawa tana faɗin"ina mahmudun?" "Yayi bacci"ta amsa mata "Da kyau,kinyi masa adduoi kuwa?" "Ai bana sanya,inayi masa sosai" "To Allah yayi muku albarka gaba ɗaya" "Ameen Inna" Hajiya Mariya ta kalle ta sosai tace"da alamu akwai magana a bakin ki ko?" Deeja ta gyara zama tace"eh Inna,dama Abba ya sanar dani cewa kece kika raini yayye na Nusaiba da Yusuf,shine nazo na gansu, saboda tsawon lokaci ban gansu ba" Hajiya Mariya tayi murmushi tace"hakane,tabbas Ni na karɓi Yusuf da nusaiba,a gaba na suka tashi,amma daga baya sun koma hannun babban ɗa na dake can ƙasar America dazama,a can sukayi karatu,a can nusaiba tayi aure,shi kuma Yusufu ya matsa sai dai yanzu ban san a in da yake da zama takamaimai ba, kasancewar ba ma a American ya zauna ba" "Amma ina meyasa aka raba mu?gashi ban shaƙu dasu ba"a cewar Deeja cikin damuwa "Labari ne mai tsawo Hadiza,idan zaki yi jumuri sai na gaya miki,har da labarin mahaifiyar ki ma" "Ki bani Inna,dama an ce mahaifiya ta ma tayi haƙuri sosai,zan so na san labarin ta" Hajiya Mariya tayi murmushi tana kallon Deejan WAIWAYE............ Malam Ishaq cikakken malami ne mai cikar kamala da sanin ya kamata,yana daga cikin manyan malamai masu karatu da akeji da su a wancan zamanin Yana da mata ɗaya da yara biyu,matar shi ruƙayya mace ce mai sanyin hali da sanin ya kamata,gata da kirki da mutunci,babu wani wanda zai ce ga abinda tayi masa na ƙuntatawa Sai dai dangin malam Ishaq sun matsa mata ƙwarai da gaske,a cewar su ta hana shi ya ƙara aure,shi kuma yace aure lokaci ne,idan lokacin ƙarawar yayi ba sai an gaya masa ba Ismail da sakina yaran su sun taso cikin gata da tarbiyya,sai dai basa iya kaiwa dangin su ziyara saboda tsangwamar da suke sha daga wajen su Daga baya kuma sai suka dami malam Ishaq da batun ruƙayya bata haihuwa sosai,tun daga kan sakina bata ƙara haihuwa ba,kuma sakinan shekarunta goma sha shida Rana tsaka malam Ishaq yazo da batun abokin shi ya bashi yarinya,zai ƙara aure,hakan ya tashin hankalin ruƙayya sosai,don tsoro take ji kar ya zamana dangin mijin ta zasuyi amfani da amarya su fitar daita daga gidan,amma sai ta fawwalawa Allah Anyi auren malam Ishaq da Amina, yarinya ce da bazata wuce sa'ar Isma'il ba,sai dai ga dukkan alamu yarinyar ta samu ingantacciyar tarbiyya,don duk zugar da dangin mijin ta suke mata sai dai ta ji su da kunne,wanda hakan ya dawwamar da zaman lafiya tsakanin ta da ruƙayya,kuma babu wanda ya kai ruƙayyar jin daɗin dacen da tayi na abokiyar zama Zama yayi daɗi tsakanin ruƙayya da Amina, Amina na girmama ruƙayya, itama ruƙayya taba mutunta ta, hakan ne ya wanzar da zaman lafiya a gidan Watan ta shida a gidan ta fara laulayi,duk yadda su dangin Ishaq suka so shiga tsakanin ruƙayya da Amina hakan bai samu ba,tilas suka sanya musu idanu Sakina ta zamto babbar aminiyar Amina, kullum suna tare,hakan ya sanya suka saba,tun kafin zuwan Amina dama sakina ce nauyin komai a gidan,yanzun ma ita ɗin ce maiyin komai a gidan,da kafin Amina ta fara laulayi tare sukeyi,amma yanzu Aminan bata iya yin komai A haka har lokacin haihuwar Amina yayi,kai tsaye tace a bar ta ta haihu a gida,hakan kuwa akayi,don babu kulawar da bata samu a wajen su sakina,hatta da Isma'il ya kan siyo duk wani abu da yaji tace tana so har ya ishe ta,wannan hadin kan nasu yana matuƙar sanya malam Ishaq cikin farin ciki A haka har Allah ya sauke ta lafiya ta haifo ƴar ta mace, ruƙayya ce ta karɓi haihuwar ta gyara mai jego da jaririya,nan da nan gida ya cika da mutane,ana ta murnar wannan ƙaruwa Sai dai Inna Mariya ta katse musu hanzari,don kuwa cewa tayi da ita zata tafi can Adamawa in da take aure,sam hakan baiyi musu daɗi ba,amma tunda malam Ishaq ya amince haka dole suma suka haƙura,don dai ita Amina marainiya ce mahaifiyar ta ta rasu tun tana ƙarama,sannan uwar riƙon ta ko da wasa bata ji daɗin ta ba,dole Inna Mariya ƙanwar mahaifiyar tata itace zata maye gurbin yayar tata Ranar suna malam Ishaq ya raɗawa jaririya suna zainab,an sha shagali sosai, sannan suka shirya suka tafi Adamawa Mutanen gidan sunyi kewar Amina da zainab ba kaɗan ba,su kenan kullum a lissafin kwana nawa ya rage su dawo Ranar da zasu dawo Mutanen gidan sai ɗokin dawowar su sukeyi,aka gyara ko'ina akayi ta dafa abinci kala-kala,duk don dawowar Amina da zainab Sai dai mummunan labarin da suka ji yayi tsananin tayar musu da hankali, Amina sunyi hatsari ita da waɗanda zasu dawo da ita,cikin tsananin tashin hankali gaba dayansu suka nufi asibitin da aka kwantar dasu #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 18 Sai dai a halin da suka same su ya ƙara firgita su,kuka suka rinƙa yi sosai,zainab ta samu karaya shida a hannaye da ƙafafuwan ta,banda manyan raunuka,sauran mata uku da suka rako ta biyu daga cikin su ma rai yayi halin shi,har an kai su mutuary,sai dai wani ikon Allah zainab ko ƙwarzane batayi ba,asalima a lokacin baccin ta takeyi hankali kwance Amina ta dube su cikin zafin ciwo take faɗin"ga zainab nan,ku kular min daita,Ni bazan rayu ba,na bar amanar ta a hannun ku,don....don....don....."yadda maganar take sarƙewa ya ƙara ba su tsoro,a gigice sakina ta fice da gudu zuwa office ɗin babban likitan Amma ko da suka dawo gani tayi mahaifiyar su ruƙayya riƙe da hannun Aminan, Isma'il dama bai shigo ba yana daga bakin ward din, ruƙayya sai kuka takeyi,likitan ya duba pulse dinta ya tabbatar musu da Amina tayi tafiya mai nisa,jiri ne ya ɗebi sakina,sai da likitan ya taimaka ya riƙe ta Basu juma sosai ba aka yi cike ciken da ya dace aka basu gawar Amina,aka sanya ta a ambulance aka tafi daita zuwa ainihin gidan iyayen ta Tabbas anji mutuwar Amina,don Amina yarinya ce ta gari bata da abokin faɗa,gata da girmama na gaba da ita Baba talatu itace uwar goyon Amina,sai a yau tayi nadamar abubuwan da ta aikatawa Amina ita da yaran ta, domin ko babu komai Amina ta kular mata da yara,amma ita kullum talatu bata da burin da ya wuce ta ci zarafin Amina,yau dai ga Amina ta bar mata duniyar An yiwa Amina sutura an kai ta gidan ta na gaskiya,su kuma su ruƙayya suka dauko zainab suka dawo gida Sun daɗe sosai kafin mutuwar Amina ta sake su,suka mayar da hankali wajen rainon zainab baiwar Allah Shekarar zainab ɗaya akayi auren sakina da Kabiru,Kabiru da kowa nashi ƴan garin azare ne,don haka can aka kai su,wannan dalili ya janyo shaƙuwar zainab da sakina tayi rauni Sai Isma'il ya zamana makaranta ce kawai take raba su da zainab,kuma shima sai anyi mata dabara yake samu ya tafi,idan tayi kukan bai dawo ba sai ta haƙura taje wajen ruƙayya,amma da zarar ya dawo to ta bar wajen ruƙayyan Sun saba sosai,hakan ya faranta ran malam Ishaq,sakina ma ta kawo musu ziyara sau biyu a tsayin shekaru uku da tayi aure,a lokacin zainab na da shekaru huɗu A lokacin ne ruƙayya ta kama wata iriyar cuta da aka kasa gane kanta,wadda taso tsaidawa da Isma'il karatun shi,amma tawakkali irin nata ya sanya take matsa masa akan yaje makarantar kawai,babu abinda zai same ta Tun tana kwanciya yau gobe da sauƙi har ciwon ya kwantar da ita gaba ɗaya,sunyi zaryar zuwa asibiti amma an kasa gano kan abin,har ruƙya anyi mata amma duk babu cigaba Sai da ta shafe shekara biyu tana fama,a lokacin ne Isma'il ya ƙare karatun shi ya dawo don jinyar mahaifiyar shi Dangin malam Ishaq ganin har lokacin yaƙi aure sai suka rinƙa zuga mahaifiyar shi,ai kuwa tace ko dai ya ƙara aure ko ta tsine masa Haka dai ba don ya so ba aka aura masa lubabatu, auren luba uku amma bata zama, saboda fitinanniya ce ta gaske,gashi kuma sam sam bata da tarbiyya Zuwan luba gidan ya haifar da fitina, saboda irin cin zalin da takeyiwa zainab,abinda sam Isma'il da ruƙayya basa jura, shiyasa kullum suke rigima da Isma'il,ƴan uwan mahaifin shi kuwa dama tuntuni sun daɗe da yi masa tambarin rashin tarbiyya,don sam baya ɗaukar shirmen su Watan luba uku a gidan Allah yayiwa ruƙayya rasuwa,mutuwar ga jijjiga malam Ishaq da Isma'il ƙwarai,ita kanta zainab da bata gama wayo ba amma ta fuskanci anyi musu rashi itama ta sha kuka, hakanan itama sakina da aka sanarwa mutuwar Sakina ta so tafiya da zainab,don dama ita har yanzu Allah bai bata haihuwa ba, Isma'il yace tayi haƙuri don bazei iya jurar rashin zainab ba Basu juma sosai ba jarabawar su ta fito,inda tayi kyau sosai,don haka aka bashi scholarship inda zai tafi san Francisco University donyin degree ɗin shi na biyu a can Yayi murna sosai,amma sai ya fara tunanin yadda zai yi rayuwa ba tare da zainab ba, mahaifin shi ya nuna masa kar ya damu,ko shi zai iya kula da ita To fa!tunda ya bar ƙasar zainab ta fara rayuwar wahala,duka,zagi,cin mutunci,horon yunwa,babu abinda luba bata yiwa zainab,amma ta kaɗa mata warning cewa kar ta sanar da mahaifin ta,idan ta sanar masa sai ta yanka ta,zainab akwai tsoro gashi bata da wayo don haka ko da wasa bata taɓa gigin sanar da malam Ishaq ba Ɓangaren abinci kuwa,idan luba ta bata abinci tun safe bazata sake bata ba sai dare,kuma shima ba wanda zata ƙoshi ba,ga aikin da take sanya ta wanda yafi ƙarfin shekarunta,idan tayi ba dai-dai ba tayi mata mugun duka,da malam Ishaq ya taɓa kama ta ta tula mata wanki ya tambayi ba'asi sai cewa tayi "Haba malam!idan ban koyawa zainaba aiki yanzu ba sai yaushe?idan ta girma fa ba yi zatayi ba,kuma bazata iya ba,kuma ai abin kunya ne a ce an kai zainaba gidan miji bata iya komai ba,kaga sai a zage mu a duniya a ce don uwar ta bata raye yasa muka kasa koya mata ƴan aikace-aikacen gida" Jin hakan ya tilastawa malam Ishaq zuba musu idanu,ƴan'uwan shi suna sane da abin da takeyi mata amma ko a jikin su,sai ma ƙara zuga ta da sukeyi A haka zainab ta cigaba da rayuwa har Allah ya nufi Isma'il da kammala karatun shi,kuma ya samu nasarori da yawa,juna a can san Francisco Allah ya haɗa shi da faɗima, faɗima dai balarabiyar ƙasar Yemen ce Sun shaƙu sosai da faɗima,daga mutunci lamarin nasu ya juye zuwa soyayya,amma yawanci hirar su akan zainab ne,take taji tana son yarinyar duk da bata san ta ba,amma kullum sai ta ga hotunan ta,a ƙarshe dai da kanta ta nemi idan Allah yayi sunyi aure ya dawo da ita gaban su su rike ta,yaji daɗin hakan sosai Zainab na durƙushe tana faman yin wani uban wanki,duk da cewa zazzaɓi ne a jikin ta, sakamakon mahaukacin dukan da luba tayi mata, saboda ta aike ta da kuɗi sun faɗi, dai-dai nan Isma'il yayi sallama ya shigo Da sauri ta ɗaga kai gami da amsawa,ganin Isma'il sai ta nemi zazzaɓin da takeji ta rasa,da gudu ta nufe shi ta ƙanƙame shi,sai ta fashe da kuka,shima hawaye ya fara cikin tsananin baƙin ciki da mamakin halin da yazo ya same ta a ciki,ya ɗago kanta cikin raunin murya yace "Zainaba kinyi jinya ne?" #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 19 A hankali ta girgiza masa kai,yace"amma kuma jikin ki da zazzaɓi"ita dai shiru tayi bata ce komai ba Gefe ya ja ta ya zaunar da ita,sannan ya kalli uban tulin kayan wankin,ya maida kallon shi kanta gami da tambaya "Waye ya baki wannan wankin?" Cikin yanayi na ciwo ta amsa"gwaggo ce" "Ita ta baki wannan uban wankin?"ya tambaya a fusace A hankali ta ɗaga kai Ya girgiza kai zuciyar shi cike da damuwa, lokaci guda kuma ya miƙe gami da kama hannun ta,suka shiga cikin gidan,ko ta kan kayan da ya shigo dasu bai bi ba Kai tsaye ɗakin ta ya nufa daita ya kwantar da ita,yana fitowa suka yi kiciɓus da luba,ta firgita ƙwarai da gaske,don tasan waye Isma'il musamman akan ƴar gudaliyar nan zainaba,amma sai ta basar,cike da yaƙe da inda-inda take faɗin "Ah!mutanen Amurika ne yau a gidan namu?Barka da sauka" A daƙile batare da ya kalle ta ba yace"Barka" Bai fi mintuna goma ba suka suka shigo da likita,ya dudduba zainab ya rubuta mata magunguna sannan yace a tabbatar taci abinci kafin ta sha,bayan likitan ya fita Isma'il ya tambaye ta ko ta ci abinci,ya sha mamakin jin cewa bata ci ba,cikin ɓacin rai ya fice daga gidan Abinci ya samo mata mei rai da lafiya da kanshi ya bata sannan ya bata magani,da yaga ta ɗan dawo hayyacinta sai ya miƙe ya ɗebo kayan da ya shigo da su,ya juye mata tsarabar da yayi mata a gaban ta Kayan sawa ne,sai takalma da kayan ciye-ciye iri-iri, sai ta hau murna da tsalle-tsalle,ta manta da ciwon da ke jikin ta,shima Isma'il sai ya damu kanshi da farin ciki,ya tattare mata kayan sannan ya fita zuwa ɗakin luba Da sallama ya shiga ta amsa da rawar jiki,ya gaishe ta fuska babu yabo babu fallasa,ta amsa tana ta faman wage baki haɗe da faɗin"Masha Allah ismaila!Yaya karatun?" "Karatu mun gama alhamdulillahi" "To Masha Allah!yanzu sai aiki ko?" Ya ɗan kalle ta a kaikaice ya ƙara ɗauke kanshi yana faɗin"shima an samu" "To lamari yayi kyau,sai aure ko?" Kamar yace shima an samu sai yaga kamar tambayoyin nata da rainin wayo a ciki,don haka sai yace"gwaggo bari na leƙa cikin gari"bai jira cewar ta ba ya fice daga ɗakin Yana fita Luba ta leƙo ɗakin zainaba,a lokacin zainaban ɗin bacci takeyi,a fili ta furta"eh lallai,wato an samu sake har da bacci!to dole ki tashi ki ƙarasa aikin nan,ke zainaba! zainaba!!"ta shiga ƙwalla mata kira A firgice zainab ta farka, Luba ta tsaya a kanta tana yi mata kallon banza,gaban ta ya faɗi,ta miƙe zaune tana kallon luban,cikin gadara Luba tace"wato don isa da ƙwarewa har da bacci don kinga wancan saƙagon ya dawo ko?to maza ki tashi ki ƙarasa yi min wanki na" Shiru zainab tayi gami da zuba mata idanu, Luba ta daka mata tsawa har sai da ta firgita,ta miƙe jiki na rawa ta nufi tsakar gidan domin ƙarasa wankin Tana cikin yin wankin malam Ishaq ya dawo tayi masa sannu da zuwa ya amsa cikin kulawa, cikin farin ciki take shaida masa dawowar Isma'il Shima ya cika da farin ciki,ya tambaye ta "Yana ciki?"ta bashi amsa "A'a ya fita,amma inaga ya kusa dawowa,ka zauna ka jira shi"babu musu malam Ishaq ya shige cikin gidan,ita kuma ta cigaba da aikin ta Tana cikin yin wankin Isma'il ya dawo,da sallama ya shigo,ta amsa cikin farin ciki,ganin ta tana wankin ya sanya ranshi yayi mummunan ɓaci,cikin fushi yace "Zainab ba na hana ki wannan wankin ba?" Tsoro ya kama zainab,ganin shi cikin fushi tace"gwaggo ce tace nayi wallahi" "To ajiye,wuce mu je"babu musu ta ajiye ya kama hannun ta suka wuce cikin gidan Jin Muryar malam Ishaq ya wuce ɗakin mahaifinsa,da sallama ya shiga,malam Ishaq na zaune yana cin abinci,yayi matuƙar farin cikin dawowar ɗan nashi,suka zauna suka kama hira,basu ɗau lokaci ba ya sako masa batun zainab Cikin rashin walwala yace"gaskiya baba ya kamata a tausayawa zainab,don a ƙananun shekarun ta bai kamata ace ana bata ayyuka fiye da ƙima ba,gashi bata da lafiya" Malam Ishaq ya numfasa yace"wallahi Ni kaina abin yana damu na Isma'il,don dai bani da yadda zanyi ne,amma na bar komai a hannun ka,ka ɗauki matakin da ya dace" Isma'il ya gyara zama yace"na gode baba,yauwa,dama ina so na shaida maka wani Company ya bani ya bani aiki a can san Fransisco ɗin,kuma nan da next month zanje na fara yi musu aiki" "Masha Allah alhamdulillahi! gaskiya nayi farin ciki, Allah ya taimaka" "Ameen baba, godiya nake" "To batun aure kuma fa?"ismaila?"a cewar malam Ishaq Ismail ya ɗan sunkuyar da kanshi cikin jin nauyi yayiwa malam Ishaq bayanin faɗima balarabiyar ƙasar Yemen Har malam Ishaq ya fara murna sai ya ɗan yi shiru kafin yace"anya ismaila?baka ɗauko fin ƙarfin ka ba kuwa?" Ɗan murmushi Isma'il yayi sannan yace"ai tuntuni mun fahimci juna har iyayen ta sun sanni,kuma sunyi na'am da ni" Murmushin malam Ishaq ya faɗaɗa yace"to Allah ya sanya albarka, Allah ya kaɗe fitina". Isma'il ya amsa da"ameen baba" Cikin sati biyu zainab tayi kyau ta murje ta maida jikin ta,bata kowane aiki sai wanda baza'a rasa ba,sai wanda Isma'il ya bar ta tayi,abin yana damun Luba sai dai babu yadda zatayi Ana isaura kwana Shida ya koma san Fransisco ya shawarci malam Ishaq akan cewa yana so ya mayar da zainab gidan sakina,malam Ishaq ya nuna musu babu damuwa,don haka ya sanar da zainab cewa ta shirya kayan ta Ba ƙaramin murna tayi ba, washegari ya ɗauke ta zuwa azare,sakina tayi matuƙar murnar ganin ƴar'uwar ta, Isma'il ya damƙa ta a hannun sakina tare da yi masa fatan alkhairi Watannin shi uku da fara aiki a ƙasar America akayi auren shi da faɗima,bayan auren ne ya ɗauki zainab ya tafi da ita,a lokacin ma sakina tana laulayi,yayi matuƙar taya ta murnar samun ƙaruwa,domin zuwa yanzu babu wulaƙanci da gore-goren da bata sha daga wajen dangin miji duk sai akan haihuwa,to yanzu dai ta samu ciki bayan shekaru goma sha biyu da tayi da yin aure Rayuwar zainab ta chanja a ƙasar US,yanda faɗima take son ta da nuna mata kulawa yana faranta mata,haka shima Isma'il,kuma ya sanya ta a makaranta mai matuƙar tsada, cikin lokaci ƙanƙani ta sauya baki ɗaya Isma'il bai manta da mahaifin shi da kuma ƴar'uwar shi ba,don haka yana kula dasu sosai,da sakina ta haihu faɗima da zainab sun zo suna,sun taho mata da kaya tuli guda, yarinyar ta ci sunan surukar ta hajiya Fatima amma suke kiran yarinyar BINTU Yau dai na karya record nayi post biyu a rana ɗaya 🤣🙃😅 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️ Nusy bee Page 20 Wannan shafin naku ne matar Khalees fans, readers,more especially likers da commentors, Deeja da Khalees sun ce a gaishe ku🥰 Itama faɗima bata rufa shekara ba ta haifo ƴar ta salma,itama sakina tazo suna,itama sakina tazo suna,kuma ta ga Garba ta mutunci a wajen faɗima da ƴan'uwan ta,babban abin farin cikin ma shine,yanayin da suke zaune da ƙaramar ƙanwar su zainab,hakan ya faranta mata rai sosai A haka suka cigaba da rayuwa,har zainab ta kammala karatun ta na secondary,kuma ta fara karatun babbar makaranta cike da nasara,a lokacin faɗima na da yara biyar,sakina kuma uku gare ta,akwai shaƙuwa mai tsanani tsakanin zainab da yaran faɗima,salma,nasir,fauwaz,abdallah da Minal,tana kula dasu sosai,Kuma basa rabuwa dare da rana,sai dai makaranta ko bacci A shekarar ne auren ƙanwar faɗima mai suna AYSHA ya mutu,ta zo ta samu yayar ta ta cikin kuka take shaida mata wulaƙancin da mijin ta yayi mata "Aure ya ƙara shikenan ya juya min baya,da Ni da IMRAN yanzu bamu da maraba da bola,wani lokacin abinda zamu ci ma gagarar mu yakeyi,duk a tunani na komai zai wuce,kawai shekaranjiya sai gashi ya kawo min takarda,wai ya sake ni saki uku"ta ƙarashe cikin rushewa da kuka Shiru faɗima tayi tana jin babu daɗi na abinda mijin ƙanwar ta yayi mata,ta san wacece ƙanwar ta Aysha,duk da cewa ɗan adam na iya chanjawa,amma tana yiwa one and only qanwar tata kyakkyawan zato "Nayi nadamar auren ɗan Nigeria wallahi,sun cika son kansu"Aysha ta cigaba Murmushi faɗima tayi tace"kayya Aysha!Kar ɓacin rai ya sanya ki yanke hukunci cikin fushi,idan mutum yayi miki laifi sai ki yanke hukunci gwargwadon laifin da yayi miki,shine adalci. Amma hukunta wani da laifin wani rashin adalci ne, Aysha Nima ɗan Nigeria nake aure,kuma ina zaune da ƙanwar shi,amma koda yaushe da shi da family ɗin shi ƙoƙarin su su faranta min,rashin dace ne kawai da jarabta daga Allah ya same ki,ki roki Allah ya baki ikon hayewa,sai kiga yayi miki sakayya mai girma" "Hakane ukhty!da har nace zan zubar da cikin nan nan jiki na amma na fasa,sai dai ina tausayin Imran,don yana da haƙuri da zurfin ciki,ina tsoron kar a cutar min dashi,don matar nan bata da iymani" "Ki bishi da addu'a,a duk inda kike a faɗin duniya addu'ar ki zata riske shi,kuma addu'ar uwa a kowanne lokaci tana tasiri akan ɗan ta"haka faɗima tayi ta kwantar mata da hankali har ta samu sauƙin damuwa Akwai wani abokin Isma'il mai suna MAHMUD,likita ne babba,yana aiki a wani asibiti dake cikin san Francisco University inda zainab take karatu,kuma abokin Isma'il ne sosai,yana da mata ɗaya hajiya bara'atu,da yara uku,Ma'aruf,Abida da faiza, kwata-kwata bara'atu bata daraja mai gidan nata,yaran duk sun raina shi, Ma'aruf ne kawai ya fita Zakka,domin shi ɗabiun mahaifinshi gare shi kuma dama sun fi sabawa dashi,amma matan duka mahaifiyar su suka biyo Lokacin da yaga zainab ya yaba sosai da nutsuwar ta,don haka ya miƙa tayin shi a wajen Isma'il, Isma'il yaso yi masa musu don yasan halin matar shi,amma haka ya danne,ya bawa Mahmud auren zainab Ana i saura wata uku biki suka dawo Nigeria gaba ɗaya,suka sauka a tangamemen gidan Isma'il da ke sardauna crescent Nassarawa G.R.A,gida ne ba garari,babu abinda babu a ciki,sannan ya gina parts a ƙalla goma a gidan saboda yace so yake ya haɗe kan yaran shi ko da bayan sunyi aure,ya so malam Ishaq ya dawo gidan amma ya nuna masa a'a,a cewar shi shi da tsufa ya cim masa ma jiran lokaci yakeyi,anan suka cigaba da zama har lokacin biki yayi Anyi biki lafiya, Isma'il ya nunawa zainab gata sosai,an kai amarya gidan mijinta wanda ke badawa layout, kasancewar shi dama iyalan shi a Nigeria suke zaune ba kasafai suke zuwa US ba Sai dai tunda ta tare take fuskantar matsaloli daga wajen abokiyar zaman ta,ga yaran ta basu da kunya ko kaɗan, Ma'aruf ne kawai mai tausayin ta da girmama ta Duk abinda akeyi doctor Mahmoud bai sani ba,kuma zainab bata taɓa shaida masa ba,ba shi ba ma,ko ƴan uwan ta bata shaidawa,idan abin ya dame ta sai dai ta shige ɗaki tayi ta kuka A haka ta kasance har tsawon shekara guda,a lokacin ne ta haifi ƴar ta ta farko wato NUSAIBA,a lokacin bayan an kammala suna gida aka maida ita gaban faɗima har ta murmure Ranar da zata koma tun safe take zullumi,har faɗima ta fahimci halin da take ciki,amma da ta tambaye ta sai tace ba komai,tilas ta ƙyale ta,amma ta rinƙa yi mata nasiha cikin hikima da kara ƙarfafa mata gwiwa Shekaru biyu tsakani ta kuma haifar ɗan ta YUSUF,a lokacin doctor Mahmoud ya fara gane makircin da bara'atu,ta sha haɗa su faɗa,zainab ta san aikin ta ne amma bata taɓa gaya masa ba sai da ya gane da kanshi,wannan shine dalilin da yasa ya raba musu gida,sai a sannan zainab ta samu kwanciyar hankalin gidan auren ta Sai da Yusuf ya shekara bakwai sannan zainab ta sake haihuwar ƴar ta mace,a lokacin bara'atu ƴaƴan ta bakwai,bayan faiza akwai sadiya,fadila,Mubarak da shukra sadiya sa'ar nusaiba ce,Yusuf ya bawa fadila wata bakwai,Mubarak shekarar shi huɗu,ita kuma shukra watan ta tara Nusaiba da Yusuf kamannin doctor Mahmud suka ɗebo,har gwara Yusuf ya dauko chaculate skin ɗin zainab,amma nusaiba har farar fatar doctor Mahmud babu abinda ta bari,amma ga wannan sabuwar jaririyar abin ba haka yake ba,don babu abinda bata dauko irin na zainab ba,hatta da farce, Mahmud bai taɓa ɗorawa wani ɗan shi so irin yadda ya ɗorawa wannan jaririyar ba,ya zaɓa mata sunan uwargidan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama wato NANA KHADIJA sai a wannan karon sakina ta samu halartar sunan ƴar uwar tata,itama a lokacin tana goyon yarinyar ta halima wadda suke kira da MIMA,a lokacin tana da watanni tara Soyayyar da Mahmud yakeyiwa Deeja har tayi yawa,ya zamana sunyi tsananin sabo tun tana ƴar ƙarama,hakan sam bayayiwa zainab daɗi don tana tsoron abinda zai je ya dawo, musamman ma da ya kasance ba ita kaɗai bace,amma shi Dr Mahmud ko a jikin shi,duk wasu abokan shi sun san Deeja Muna miki maraba da zuwa duniya Deejan mu🥰kuma mu ma fa muna son ki kamar yadda doctor yake son ki🤗 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 21 Shekarar Deeja ɗaya da haihuwa Allah ya amshi ran malam Ishaq bayan ya ɗan yi fama da jinya, mutuwar ta girgiza ƴaƴan shi sosai,don ita zainab tun daga nan ma lafiya ta ƙwace mata Bayan shekaru biyu kuma ta sake haihuwa,sai dai wannan haihuwar tazo da matsala,don itace silar rasuwar zainab da abinda ta haifa, Mahmud da Isma'il hauka ne kawai basuyi ba,babu wanda bai tausaya musu ba,hatta da sakina ma ta jijjiga iya jijjiga,amma suka fauwalawa Allah suka bita da addu'ar neman rahamar Allah Inna Mariya da tazo gaisuwa itace ta nemi alfarmar tafiya dasu Nusaiba,kallo ɗaya zakayiwa yaran su baka tausayi ƙwarai, Dr Mahmud yace ta tafi dasu amma ta bar masa Deeja don ta rinƙa ɗebe masa kewar zainab,ba haka ta so ba amma ta ɗebe su,a lokacin idanun ta taf da hawayen kiran "ammi na!"da Deeja takeyi Daga baya dai Deeja hannun Bara'atu ta koma, Bara'atu kam dama ta samu, don babu kunya take gallazawa baiwar Allah da batayi mata komai ba, Ma'aruf ne yayi masa hannun ka mai sanda,wanda a silar hakanne ya samar mata masu aikin da zasu kula da ita ta bar hannun Bara'atu,amma duk da haka sai dai idan ƙannen Ma'aruf basu ga ta fito ba,uwar tayi musu huɗuba,haka zasu doddoke ta ta koma wajen mariƙiyar ta tana kuka Yau ma Ma'aruf suna zaune da babban abokin shi kuma ɗan aminin mahaifinsa abdurrashid wanda suke kira da KHALEES,suna hirar makaranta yadda suka saba,sai ga shukra ta biyo Deeja da gudu, Ma'aruf ya daka mata tsawa,a tsorace ta koma,ya kama hannun Deeja ya mayar da ita wajen mai rainon ta sannan ya dawo wajen abokin shi suka cigaba da hira Lokacin da Dr Mahmud zai sanya Deeja a makaranta ma bai saka ta makarantar da ƴan uwan ta sukayi ba,wadda tafi ta komai da komai ya saka ta,ya ware driver mai Kai ta yana dawo da ita Shekarar ta goma sha shida ta kammala secondary,babu ɓata lokaci ya nemar mata admission a university of Sydney Australia inda ta karanci accounting,duk da soyayyar da yake gwada mata haka ya tsaya tsayin daka ganin bata lalace ba har ta kammala karatun ta cike da nasara,ta haɗe kan kwalin ta cike da farin ciki ta roƙi abban ta ya samar mata aiki Sai dai karo na farko yace a'a ga uzurin Deeja,duk kuka da taɓarar da tayi ya kafe akan ra'ayin shi hakan ya bawa Deejan mamaki sosai,amma saboda bata iya musu ba haka ta haƙura "Babu Abinda kika nema kika rasa auta na(da yake haka yake kiran ta)ba sai kinyi stressing kanki da aiki ba,duk abinda kike bukata duk girman shi I'm there for you"tayi murmushin yaƙe bata ƙara cewa komai ba Ranar birthday dinta da ya zagayo Dr Mahmud ya bata mamaki inda ya gwangwaje ta da dalleliyar mota sabuwa fili,kuma mai ainihin tsada,a ranar tayi farin cikin da ta dade rabon ta da irin shi,kuma batare da ɓata lokaci ba driver ɗin ta ya fara koya mata motar,bata wani daɗe ba ta iya Ma'aruf da Khalees lokaci ɗaya sukayi karatu a ƙasar England, Ma'aruf ya karanci banking and finance,shi kuma Khalees ya karanta mechanical engineering,sai da suka haɗa master's degree din su da PhD sannan suka dawo gida,batare da ɓata lokaci ba sukayi aure,sai dai Khalees ya riga Ma'aruf aure kasancewar mahaifinsa mutum mai tsari da tsanani,da shi da sauran ƴan uwan shi mata shi yake zaɓar musu abokan rayuwa Anyi shagali sosai a bikin Ma'aruf,duk wulaqancin da ƙannen Ma'aruf sukeyi mata bai dame ta ba,don dai ita ta hannun daman ango ce,sannan bayan amarya tazo sai suka fi shiri da Deejan, saboda a bayyane yake ƙannen Ma'aruf basu da kunya ***** ***** ***** Dawowar ta kenan daga gidan su ƙawar ta zee da suka haɗu a Australia, abokiyar karatun ta ce,sai dai zee ita law ta karanta,ita kuma accounting,tasu tazo ɗaya da zee sosai saboda kirkin yarinyar,gashi mahaifiyar zee tana janta a jiki tamkar ƴar ta,hakan ne ya sanya Deeja take jin shauƙin zuwa gidan don a bayyane yake Deeja ta rasa soyayyar uwa,yanzu dai shirye-shiryen bikin ta sukeyi da CEO din kamfanin da Deejan take so tayi aiki,dama zee din ce mai zuga ta ta nemi aiki a can,amma da mahaifin ta ya nuna baya so tilas aka haƙura Tuƙi takeyi tana bin waƙar da ta kunna Justin Bieber mai taken love me, batayi aune ba sai ganin mutum tayi a gaban ta,kafin ta kauce tayi sama dashi,ta shiga tashin hankali da gigita irin wadda bata taɓa shiga,tayi parking jikin ta na rawa ta nufi wajen da mutumin yake kwance har mutane sun fara zagaye shi Sai da gaban ta ya faɗi ganin mutumin, tsananin kamar shi da su Mamie babba ts ɓaci,yana kwance zuwa lokacin baya hayyacin shi,sawa tayi a sanya mata shi a mota,ba'a Musa mata ba suka sanya mata shi a mota suka miƙo mata ƴar jakar kayan shi kai tsaye ta ja mota zuwa asibitin mahaifin ta da ya gina a kano,kafin ta ƙarasa ta kira shi tana kuka ta shaida masa abinda ya faru,shima nashi hankalin ya ɗan tashi Tana zuwa aka karɓe shi aka fara treating din shi,tana rungume da jakar kayan shi tayi tagumi,zuwa can ta ɗago tana sauke ajiyar zuciya,tasan babu likitan da zai tuntuɓe ta ko da da akwai matsala sai dai mahaifinta,don haka ta ɗauki jakar jiki babu ƙwari ta wuce parking space don mayar daita mota Sai dai har ta kusa wajen jakar ta zame ta faɗi,ta durƙusa don ɗauka sai ta ci karo da wani hoto ya leƙo,har zata mayar sai ta fasa,ta zaro,gaban ta ya faɗi ganin momy Aysha maman su Aunty Ramlah,qanwar Mamie babba,da wani yaro a hoton, wannan hoton idan bata manta ba momy Aysha na da irin shi,kuma tace shine only son din ta IMRAN,Wanda ta bari a gidan mahaifin shi a Bauchi Jikin ta yayi sanyi,sai yanzu ta gane ɗan momy Aysha ne kenan,to me ya kawo shi Kano shi da yake Bauchi?ko momy Aysha da ta ƙara aure yanzu ai tana Abuja ne,amma maybe wajen Mamie babba yazo,da wannan tunanin ta mayar da jakar sannan ta koma asibitin Few hours ya dawo hayyacin shi,sannu take ta jera masa amma sai bin yake da idanu kamar bai taɓa ganin ta ba,itama ta gaji don kanta tayi shiru Kwanan shi biyu a asibitin aka sallame shi,zuwa lokacin ya saba da Deeja,har ta bata labarin irin wahalar da yasha a hannun matar uba,a ƙarshe dai ta sanya mahaifin shi ya kore shi da ƙazafin wai yana leƙa mata yara mata Tausayin shi ya rufe Deeja ƙwarai,tace "in Sha Allah daga yanzu ka fita a sharrin ta,ita kuma taje rayuwa ce" Har gida ta samu baba Prof (professor Ismail)ta bashi labarin komai da kuma tabbacin da ta samu na cewar Imran ɗan momy Aysha ne, baba Prof yaji dadi kwarai,da kanshi ma yaje asibiti ya dauko Imran ya ware masa part a gidan ya bashi,amma lokacin baiyi wa yaran shi bayanin komai ba,gashi mamie da ita kanta momy Aysha sunje Yemen ganin gida Ko sati baiyi da zuwa ba Deeja tayi insisting abban ta ya bawa Imran aiki a asibitin shi, kasancewar shima likita ya karanta,shi kam yayi farin ciki da haɗuwa da Deeja matuƙa,ya fara aiki cikin kwanciyar hankali, saboda zirga-zirga ta sauƙaƙa baba Prof ya bawa Imran kyautar motar hawa,Deeja ta taya shi murna ƙwarai da gaske Kusan kullum Deeja sai ta kawowa Imran ziyara,wani sain ma ta kanyi girki ta kawo masa,shaƙuwa mai tsanani ta shiga tsakanin su,duk gidan Professor sun san da haka,kuma suma su fauwaz tun suna ɗari-ɗari da Imran ɗin har suka gane cewa mutumin kirki ne #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy_bee Page 22 A Asibitin da yake aiki ne suka haɗu da NAJEEB,shima likita ne,kuma matsayin su ɗaya da Imran ɗin,sai kuma tasu tazo ɗaya Abokan aikin su basa son mu'amalar Imran da najeeb, saboda sun san Najeeb ba mutumin kirki bane,shi kuma Imran da alamu mutumin kirki ne,ga iya mu'amala da mutane da girmama na gaba dashi,ga tausayi Shi kuwa Najeeb Imran ya burge shi ganin shi kyakkyawa mai ilmi da nutsuwa,ga tsafta da iya gayu,gashi bashi da hayaniya da kwaramniya,sai yaji sha'awar haɗa shi da ƙanwar shi UMAIMA kwanan Imran tara da fara aiki Mamie babba da momy Aysha suka dawo, Deeja ta cika da murna,ta je har garden da Imran kan zauna yana dudduba manyan litattafan su na likitanci ta kira shi su gaisa da Mamie,baiyi mata musu ba ya bita,amma me? Tun kafin ya kai ga gaisuwar idanun shi suka sauka akan momyn shi da tayi stiff tana kallon shi,a wajen ya zube idanun shi suka tara hawaye,Muryar shi tana rawa ya furta "momy na!" Tabbas tun kallon farko faɗima ta gane cewa ko waye wannan daga ahalin su ya fito, saboda tsananin kamanni,dama babu abinda bana prof yace musu har yanzu,su kansu su fauwaz basu san komai ba "Ukhty Imran ne! Imran ɗi na ne ukhty!!"a cewar momy Aysha cikin gigita,sai ta fashe da kuka,Imran ya ƙarasa ya rungume mahaifiyar shi yana ƙara fashewa da kuka Bayan an nutsu Imran ya bayar da labarin yadda rayuwa tayi dashi a gidan su "Momy bayan kin tafi kin barni ban sake farin ciki ba,ban sake jin daɗin rayuwa ba,bani da abokin hira,Bani da abokin kuka, Hajiya zulfa'u da agololin ta sune kawai suke rayuwar farin ciki a gidan, abinci wannan da zan ci gagara ta yakeyi,ta sanya daddy ya sauya min makaranta mara kyau kuma mai nisa,ta sanya aka sallami driver na,da ƙafa nake zuwa nake dawowa,da na dawo kuma zata fara sanya Ni aikace-aikace,kamar su wanki,wankin mota,share-share da sauran su,sai na gama sannan idan an ga dama a bani abinci,don ma Allah ya sa mama ladi mai aiki tana fakar idanun su ta ɗibar min abincin Haka na gudanar da rayuwa ta har na kammala primary,sai tace a tura Ni boarding Kar na dame su,haka Daddy ya kaini boarding,tun daga js 1 har ss3,daga nan kuma na samu da ƙyar ta yarda ya biya min kuɗi na karanci medicine a ATBU,shima rayuwar cikin makaranta nayi,don tafi min kwanciyar hankali da zaman lafiya,a wani zuwa weekend da nayi na farka cikin dare naji tana kiran suna na,da na leƙa ta window dai naga tana zuba wani ruwa akanta tana kiran suna na, hankali na ya tashi na tabbatar tsafi takeyi,don haka ko da wasa ban taɓa wasa adduoi ba dare da rana,a ɓangare ɗaya kuma na dage da karatu na wanda nakejin cewa shine gata na,ko ta dalilin shi wataran zan iya haɗuwa da ke A wannan halin na ƙarasa karatu na na medicine mai wahala a yanayi mai matuƙar wahala,amma alhmdllh takardu na sukayi kyau,a satin da na karɓo takardu na ne ina kwance a ɗaki na sai ga ƙaramar ƴar ta tazo tace na zo na duba yayar ta ameera numfashin ta ne yake ƙoƙarin ɗaukewa,sam banyi tunanin mutanen basa kyautata min ba,iyakar abinda na sani shine profession ɗina,naje Ina ƙoƙarin duba matsalar sai ji nayi uwar ta rafka salati, wai ina ƙoƙarin haiƙewa ƴar ta,sai ga yarinyar ta miƙe tana mitstsika idanu wai bacci takeyi taji kamar an danne ta,abin ya bani mamaki nace ai salma ce tazo kira na tace ameera ba lafiya,salma ta zabga wani ihu tana faɗin"ita wallahi bata fito daga ɗakin ta ba tunda garin Allah ya waye sai yanzu,abin ya bani mamaki na kasa magana,sai ji nayi Daddy yana sauke min maruka hagu da dama,yana faɗin na gado uwa ta na zama mutumin banza,a nan ne naji bazan jure ba nace Ni uwa ta ba mutuniyar banza ce sai dai matar shi da gayyar agololin ta,nan ya hau Ni da duka tamkar ya samu ɓarawo,Ni kam ko ƙoƙarin kare kaina banyi ba sai da ya illata ni,ameera ta miƙe tana hawaye wai sai ta bar gidan tunda na kira ta da agola,buɗar bakin Daddy sai cewa yayi sai dai Ni na bar gidan ba ita ba,don ta fini Amfani,haka inaji ina gani na kama tattara dukkan kaya na zan bar gidan,sai ga Hajiya zulfa'u tazo tana murmushi tana faɗin"nayi ƙoƙarin jefe ka amma hakan bai ci tura ba,to da sauƙi dai tunda na jefe ubanka,kaima gashi ko sisi na batayi ciwon kai ba na kaɗa ka kamar yadda na kaɗa uwar ka, Allah raka taki gona"ban kalle ta ba itama bata damu ba tana gama bayanan ta ta juya ta bar wajen Shine dalilin da ya sanya ni barin Bauchi na shigo Kano,ranar da nazo Kano a ranar Deeja ta buge Ni a mota, saboda tunanin yadda zanyi da kaina bai bani damar kallon gaba na ba,amma a ƙarshe hakan ya zame min alkhairi tunda gashi na dawo gare ki momy"ya ƙarashe hawaye na zubo masa Kusan kowa a parlourn hawaye yakeyi, Deeja kamar zata shiɗe duk da kasancewar ta mara saurin kuka da dakiyar zuciya, a hankali momy Aysha ta ƙaraso ta rungume shi tana faɗin"babu komai, ƙaddara ce, alhamdulillahi alaa kulli haalin,nayi farin ciki da rayuwar ka bata lalace ba, Allah yayi maka albarka"shi dai murmushi kawai yakeyi yana goge hawaye Bayan ta nutsu tace"Imran lokacin da na bar gidan mahaifin ka na bar shi da ciki wata uku,ga abinda na haifa nan"ta nuna masa Ramlah wadda a lokacin zata kai 27-28 years Murmushi yayi yana kallon Ramlah, Ramlah ta ƙaraso ta rungume shi tana faɗin"yaya momy tana yawan bamu labarin ka,tana nuna mana hotunan ka,munyi missing dinka sosai,yana murmushi yace "nayi missing ɗin ku,amma yanzu alhamdulillahi" Babu wanda ya kula da sanda Deeja ta zame ta fice daga falon,sai daga baya Imran ya kula,babu ɓata lokaci ya miƙe ya nufi garden din gidan inda suka saba zama suna hirar su,a can ya hango ta ta jingina kanta da kujerar da ta zauna ta lumshe idanu tana ajiyar zuciya,a hankali ya ƙarasa inda take zaune,ƙamshin turaren shi yasa ta buɗe idanu tana kallon shi, yayi murmushi yana faɗin"da tsoro zan baki ai,kuma na manta ashe sister ɗin tawa jaruma ce" Itama murmushin tayi,ya samu waje ya zauna,ya ɗan yi shiru sannan ya fara magana "Khadijah, I have no enough words da zanyi miki godiya,kinyi min abinda har abada banajin zan manta,kin cika min farin cikin da na rasa tun ina ɗan ƙaramin yaro,bani da bakin yi miki godiya,bani da abinda zan iya biyan ki,fata na Allah ya buɗa miki dukkan alkharin shi duniya da lahira,na gode sosai Deeja" Deeja ta girgiza kai tace"wannan duk ya wuce ya Imran,yanzu tare zaku koma da momy?" "A'a,a nan zan zauna,ko don aiki na,amma zan rinƙa kai mata ziyara"tayi murmushi tana faɗin"nima dai Allah yasa Abba ya barni nayi aikin nan,kowa yana aiki ban dani,Mima ma tace ta samu aiki,ga zainab,amma Ni daga ci sai kwanciya kamar wata saniya"ta ƙarasa tana yamutsa fuska Imran ya fashe da dariya yana faɗin"kaji min mata,don kin samu kin zama ƴar hutu shine zaki yi mana iyayi?zan zuga Abba ya janye miki tallafi tunda daɗin yayi miki yawa" Ta tura baki gaba tace"Ni da ya daina tura min tallafin ya bar ni nayi aiki nafi son haka,yanzu fa duk na zama malalaciya"ta ƙarashe kamar zatayi kuka "Common ba wani malalaciya,ke fa jaruma ce,ko baki sani ba?" "To amma ai rashin aiki zai saka experience ɗina na aiki na aiki ya gudu fa!" "A haba!babu inda zashi,ki kwantar da hankalin ki, wataran ma Abba da kanshi zai yarda kiyi aiki ki daina saka damuwa a ranki,gata fa Abba yayi miki, common cheer up please!wannan fuskar ko kyau batayi miki ba"da haka ya sanya ta koma yadda take da #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 23 Momy Aysha ta so tafiya da Imran amma sai yayi mata bayanin aikin shi,kuma ma still baya son rabuwa da Deeja, saboda halaccin ta a gare shi,don haka momy Aysha ta bar shi a gidan tayi tafiyar ta Abuja da yaran ta Shi kam Najeeb shirye-shiryen haɗa Imran da umaima sunyi nisa,don haka ya fara kiran umaiman ta rinƙa kawo musu ziyara,ya rinƙa gabatar da ita a wajen Imran,tun Imran baya damuwa har ya fara ba da kai,umaima fara ce ƙal, kyakkyawa sosai mai gashi har gadon baya,bata da ƙiba kwata-kwata amma ba ramammiya bace,tana da yawan fara'a da iya hira,ga ta da son gayu da kwalliya,ga iyayi,da wannan ta samu ta fara janye shi daga wajen Deeja,wadda shi mu'amalar su a abota ya ɗauke ta da ƴan'uwan taka,da babu soyayya a tsarin shi a yanzu,amma umaima ta tarwatsa komai Najeeb ne ya rinƙa sukar Deeja a wajen Imran da dabara da wayo,don tuni ya fahimci Imran cewa bashi da wani wayo sosai,a hankali a hankali ya fara cin nasara,dama Najeeb ya kwaɓe shi kar ya kuskura ya bawa Deeja labarin umaima don zata iya raba su,ya nuna masa tun farko ba don Allah ta cece shi ba,ta cece shi ne don taga zai yi mata amfani,har ya ƙara da cewar mata irin su Deeja basa ɓata lokacin su wajen abinda bai shafe su ba,har da misalai,tabbas he is on point,don Deeja bata shiga shirgin da bai shafe ta ba,ko wajen al'ummar gidan bata cika zuwa ba sai wajen shi,yanzun ma takanyi sati bai ganta tazo gidan ba,hakan ya sanya shi yarda da batun Najeeb, zuciyar shi ta cika da haushin Deeja Rana tsaka Deeja tazo da farin cikin ta wajen Imran tana shaida masa abban ta ya amince tayi aiki a asibitin mijin zee,Amma yadda yayi mata ya sanyaya mata jiki, ko da ta gaya masa baiyi wani appreciating ba sosai, don haka bata wuce minti goma ba ta tafi gida Daga lokacin ya zamana ba sosai suke haɗuwa ba ma, musamman da ya zamana kowa cikin su aikin shi ya ɗauki zafi,a waya kam sukanyi wata babu wanda ya taɓa wani,tun abin na bawa Deeja mamaki har ta watsar Shekarar shi guda da zuwa mahaifiyar shi ta bukaci yayi aure a wata ziyara da ya kai mata Abuja,babu ɓata lokaci ya gabatar mata da umaima wadda zuwa yanzu sunyi nisa a soyayya, Deeja kam yanzu sun zama baƙin juna Ya ɗauka momy Aysha zatayi farin ciki amma sai yaga ta ɗaure fuska ta fara faɗa "Wacece wata umaima?to ban amince ba, ba da yawu na ba,ga yarinya ƴar mutunci wadda tayi maka halacci amma saboda tsabar butulci ka guje mata,to wallahi dole ka aure ta,zan shigo kanon ma next week, wallahi bazaka mayar dani ƙaramar mutum ba,a cewar momyn cikin faɗa Shiru yayi cikin ɓacin rai,shi kam duk kusan mutanen da yake tare dasu haushin shi suke ji akan Deeja,a ƙarshe ga mahaifiyar shi ma,take yaji wata tsanar ta ta dirar masa,haka dai yayiwa momyn nashi sallama ya tafi Kwana biyar da faruwar haka Deeja tazo gidan,a lokacin ma bata san abinda yake faruwa ba,dama wajen su Yasmeen tazo,bayan sun gama hirar su ta fito,har ta nufi parking space ta tuna sun kwana biyu basu gaisa da Imran ba,don haka ta wuce lambun gidan kai tsaye da hope ɗin zata same shi Ilai kuwa yana zaune,sai dai maimakon karatu yadda ya saba yau waya yakeyi yana lumshe idanu yana murmushi da alamu yana jin daɗin wayar da yakeyi Ta nufe shi kai tsaye,a dai-dai lokacin da ya kammala wayar tayi masa sallama,ya amsa fuska a ɗaure, bata damu ba ta gaishe shi,nan ma ya amsa ciki-ciki sannan yace "lafiya dai ko?" Ɗan murmushin da bai kai zuci ba tayi ta zauna tana faɗin"lafiya ƙalau,dama zuwa nayi wajen Yasmin shine sai na biyo wajen ka mu gaisa" "To yayi kyau,kina iya tafiya"ya faɗa idanun shi a kan wayar shi Tabbas ranta ya ɓaci amma bata nuna ba,sai tace"wai yaushe momy zata dawo daga China?naji su Yasmin sun ce taje China shekaranjiya" "Ki tambaye ta,kun fi kusa ai"ya bata amsa idanun shi na kan wayar shi Ta buɗe baki da zummar yin magana ya ɗaga mata hannu yace"kinga!tashi kije kawai,kin fiye shishshige min,Ni kuma na tsani mace mai shishshige wa namiji!!" Tunda take ba'a taɓa furta mata kalmar da tayi mata ciwo ba irin wannan,don haka ta miƙe batare da tace uffan ba ta bar wajen Kwana goma da faruwar hakan taji Labarin auren ta da Imran a bakin mamie,sai da gaban ta ya faɗi don a lokacin ko sannu bata haɗa su da Imran,sai dai bata ce komai ba Kwance tashi har bikin yazo,komai proffesor Isma'il ne yayi mata,ya hana Dr Mahmud komai,an shirya biki na garari an kai amarya gidan mijinta Kusan lokaci guda akayi bikin su da Mima,sati biyu ne tsakanin su,don haka Mima ta samu halartar auren Deeja,itama Mima ɗin ɗan ƙanin baban ta zata aura,shima ɗan azare ne amma baki ɗaya zaman su da iyayen shi a Malaysia suke,sai dai su auren soyayya zasuyi ba kamar su Deeja ba To fa!tunda aka kawo Deeja gidan Imran ta gane ainihin kalar shi,babu irin izayar da baya mata da shawarar babban abokin shi Najeeb,wanda ya nuna idan har baiyi yadda zai yi ya kori Deeja ba bazai bashi ƙanwar shi ba,hakan ya tayar da hankalin shi ya dage cikin rufewar idanu ya cigaba da ƙuntatawa Deejan,bata taɓa faɗawa kowa ba duk zuwan da akeyi gidan,sai dai ramar da takeyi tana bawa Kowa mamaki,amma idan an tambaye ta dalili sai dai tace babu komai Watannin su biyar da aure Imran ya bijiro da maganar umaima bayan ya shawo kan Najeeb da ƙyar,amma momyn shi sam bata bashi goyon baya ba,sai ya tuntuɓi proffesor,shi kam ya wuce gaba,nan da nan akayi komai aka gama aka sanya lokacin aure Lokacin da momy Aysha taji Labarin tayi baƙin ciki sosai,amma yadda bai same ta da zancen ba itama bata tuntuɓe shi ba Professor da kanshi ya kira Deeja ya sanar mata maganar auren,ya lallashe ta da kalaman kwantar da hankali,bata nuna masa damuwa ba don ta san hakan zai faru watarana, amma duk da haka hankalin ta ya ɗan tashi,sai dai ta fauwalawa Allah komai don ya san shine mai iko a bisa komai Anyi biki lafiya,anyi sharholiya sosai, amarya ta tare a gidanta Tunda umaima ta tare Deeja ta fara ganin yadda ake soyayya,sam basa jin kunyar ta,wani abin ma basayi sai sun ga idanun ta a wajen,gashi ta zama tamkar baiwa,duk wasu aikace-aikace na gidan ita takeyi,sai dai bata taɓa nuna damuwa ba duk da abin yana cin ta a zuciya Makirci kala-kala babu wanda umaima bata taɓa yiwa Deeja,da taimakon Najeeb,Imran kam ya ƙara tsanar ta har ta kai yana dukan ta,ga horon yunwa da yake mata,ta sake lalacewa,da yawan mutane zargi sukeyi kishi ke damun ta Lokaci ɗaya ta fara wani irin ciwon ƙirji,wani lokacin numfashin ta har ƙoƙarin ɗaukewa yakeyi,ita kaɗai ta san me takeji idan ciwon ya tasar mata,sai dai ta sani bata da Muhimmanci a wajen Imran da zai tsaya ya saurare ta Zuwan Mima daga Malaysia ya faranta mata rai sosai,a lokacin miman har da ƙaramin ciki,kuma anyi Sa'a lokacin su Imran sunje Abuja gidan momyn shi,don haka suka baje a falo suna hirar yaushe gamo #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️ Nusy bee Page 24 Mima ta ƙare wa Deeja kallo,tace sister deejo,me ya same ki ne naga kin rame haka?ko baki da lafiya ne?" Deeja ta ɗan yi shiru, Mima abokiyar sirrin ta ce,ba don haka ba da baza ta iya sanar da Mima abinda yake damun ta ba,amma saboda muhimmancin Mima sai ta bata labarin irin wahalar da take sha a gidan Tabbas lamarin ya bawa Mima mamaki da tsoro,kuma ta tausayawa Deeja sosai,tayi shiru cikin alhini tana kallon Deeja,zuwa can tace"amma Imran ya cika butulu,yanzu duk irin soyayyar da kukayi ta zama tarihi saboda ya samu wata?" Deeja ta girgiza kai tace"ba soyayya mukayi da Imran kamar yadda kukayi tsammani ba,abota ce kawai,kuma shigowar maganar aure ciki ita ta watsa abotar" Shiru Mima tayi tana jinjina abin,zuwa can tace"gaskiya lamarin da mamaki sister,Imran ya bani mamaki sosai" Deeja tace"Ni kam sam,don ya gwada min tun Kafin auren" Mima tace"to Allah ya kyauta,ki cigaba da haƙuri watarana sai labari"Mima dai tayi ta kwantar mata da hankali,duk da cewar abin ya dame ta,kuma abin da ta sani shine da ace itace Imran bazei fara abinda yayi wa Deeja ba A ranar Mima a gidan ta kwana, Deeja taji daɗi sosai, saboda Mima ta ɗebe mata kewa,dama kuma gwanar surutu ce da barkwanci Washegari Mima ta tafi,Deeja sai taji dama kar ta tafi saboda taji daɗin zuwan ta,kuma a ɗan zaman da sukayi taji sauƙin ciwon kirjin ta Kwanan Mima biyu da tafiya su Imran suka dawo,ta fuskanci ya ƙaro wulaƙanci, saboda momyn shi tayi masa faɗa sosai akan rashin zuwa da Deeja,sannan batayi wani marari akan umaiman ba,don haka ya ƙudurce a ranshi Deeja sai ta gane kuren ta Tunda tayi masa sannu da zuwa ya daka mata tsawa ta shige ɗaki bata sake yarda sun haɗu ba,da sassafe zata fice aikin ta,sai ta kai biyar na yamma bata dawo ba,da zarar ta dawo sai ta rufe kanta a ɗaki,haka tayi ta gudanar da rayuwar ta tsawon sati guda Baƙar rana a gare ta,ranar da baza ta taɓa gogewa a cikin ranta ba,itace wata ranar talata takwas ga watan biyu Dawowar ta kenan daga aiki,ta jefar da jakar ta akan tiles abinda bata taɓa yi ba,yau tun safe jinta takeyi wani iri kamar ba ita ba,ta rasa me yake damun ta, wanka ta shiga,tana fitowa tayi sallar la'asar da taji ana kira,tana idarwa ta ɗan kwanta don ta huce gajiya,sai bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita Bata farka ba sai bayan maghriba,tayi matuƙar mamakin baccin da tayi,ta miƙe tayi sallah,haka kawai yaji gaban ta na faɗuwa,ƙirjin ta ya tsananta ciwo,abu ya dame ta,ta ɗan yi shiru,zuwa can ta janyo jakar ta dake yashe akan tiles don ta ɗebe kewa sai taji ta a kashe,abin ya bata mamaki sosai,don ta san wayar ta akwai ragowar chaji,amma hakan bai wani dame ta ba ta sanya ta a chaji,sai bayan ƙarfe tara na dare ta kunna ta Saƙonni da miscalls ta gani barkatai,da sauri ta fara duba miscalls ɗin,yaya Ma'aruf ta gani Mamaki ya kamata,indai Ma'aruf da ta sani ne baya kira sama da biyu,amma yau shine mai kira har sha ɗaya,to lafiya?sai taji gaban ta ya faɗi,da sauri ta buɗe saƙonnin don ganin abinda suka ƙunsa Tashin hankalin da ta gani ne ya sanya ta ƙwala ƙara tana faɗin"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"jikin ta na matsanancin rawa "Aslm auta,Abba Met with an accident on his way back from Abuja today,and sadly we lost him,I called you several times but you are not picking" Tashin hankalin hankalin da Deeja ta shiga baya faɗuwa,daga tsaye ta saki wayar tana jan numfashi,amma saboda tsabar ƙarfin hali da tashin hankali haka ta nufi parlourn tana haki,still ta kasa yarda abban ta abin ƙaunar ta ya tafi ya bar ta,kuka take so tayi amma ta gagara,ko a mafarki bata taɓa kawo abban ta zai tafi ya bar ta a wannan halin ba A parlour ta iske Imran da umaima suna shan soyayyar su hankali kwance, umaima ce ta fara ganin ta,cikin masifa tace"Malama Lafiya,uban me kika zo yi mana?" "Abba na!yaya Ma'aruf ne yace wai ya tafi ya barni,yaya Ma'aruf yace na rasa Abba na garkuwa na"ta faɗa cikin fitar hayyaci lokaci guda kuma tana ficewa daga cikin parlourn Imran ya bi ta da kallo,karo na farko kenan bayan auren su da yaji tausayin ta,ganin har ta fice daga parlourn cikin sauri ya miƙe ya bi ta,amma kafin ya riske ta a waje ta hau napep ta tafi,bai bi ta ba sai ya dawo gida,duk da ya tausaya mata Ita kam kai tsaye gidan su ga nufa,tana zuwa ta samu yaya Ma'aruf a harabar gidan da shi da aminin shi na amana Khalees, dukkan su sai sharar ƙwalla sukeyi,ta jefa musu tambaya cikin tashin hankali "Ina Abba na?" Bin ta sukayi da kallo,don sun sani sai tafi kowa jin mutuwar,don itace favourite ɗin shi kuma shi kaɗai gare ta a yanzu,gaba ɗaya tausayi take basu,ta ƙanƙame Ma'aruf tana faɗin"yaya Ma'aruf abbana!Abba na kar ya tafi ya bar ni,wallahi ina son shi,idan ta tafi ya zanyi?" Yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali amma ina!kafin ya ankara sai gani yayi ta sulale ƙasa sumammiya Cikin kuma mai motsa rai Ma'aruf ya durƙusa ya ɗago ta,cikin sauri Khalees ya miƙo masa ruwa ya amsa ya yayyafa mata,ta ja ajiyar zuciya Zumbur ta miƙe tana zare idanu,sai ta fashe da kuka mai ban tausayi, Ma'aruf ya kama hannun ta suka shiga gidan tana ta sambatu A ranar babu wanda ya runtsa saboda tashin hankali da suka shiga, Deeja ta gigice sai suma takeyi,tilas aka ɗauke ta sai asibitin da suke zuwa wajen likitar ta Dr su'ad Cikin lokaci ƙanƙani likitoci suka rufu akanta,sun ɗau kimanin awa uku kafin su fito, hankalin Dr su'ad a tashe Office ta ja Ma'aruf ta sanar dashi cewar zuciyar Deeja ta kamu da ciwo Hankalin Ma'aruf yayi matuƙar tashi,yace"ciwon zuciya kuma doctor? innalillahi wa Inna ilayhi rajiun! Deejan har nawa take da zata kamu da irin wannan ciwon?" "Ko kwanan ta ɗaya da haihuwa idan Allah ya ƙaddara sai kaga ta kamu da ciwon, ballantana ma ana haifar jarirai dashi,amma ita nata ta same shi ne due to depression and anxiety,tana cikin tsananin damuwa,why baka san abinda ya janyo ciwon ba a matsayin ka na yayan ta?" "Dr Ni dai nasan na sanar mata rasuwar mahaifin mu,and I know she is his favorite,and they love each other,but Bana tunanin wannan dalilin can lead Deeja to this stage,ko babu komai itama musulma ce ta yarda da ƙaddara" Dr su'ad ta girgiza kai tace"ba wannan bane,don da alamu ciwon ya kwana biyu a tare da ita, and it's better a kula da ita yadda ya kamata,gudun samun wata matsalar again"bai sake magana ba ya juya ya fice daga office ɗin cikin mutuwar jiki,Dr ta biyo bayan shi Waje ya samu ya zauna yayi tagumi,ya kai mintuna sha biyar a zaune kafin abokin shi Khalees ya shigo reception ɗin Ya kai mintuna biyar a tsaye a kan shi amma bai san yazo ba,sai da ya taɓa shi sannan yayi firgigit kamar wanda ya tashi daga bacci Khalees ya samu waje ya zauna kusa da abokin nashi,ya zaro wayar shi daga aljihu ya miƙa masa,ya amshi wayar, cikin nutsuwa Khalees ya kalle shi yace "Ana ta kiran ka don ayi maka ta'aziyya amma baka tare da wayar ballantana ka ɗaga,sai yanzu naje gidan naku Abida ta shaida min abinda yake faruwa ta bani wayar na kawo maka,ya mai jikin?" "Da sauƙi"ya bashi amsa cikin matsananciyar damuwa Shiru sukayi su duka, Ma'aruf damuwar da yake ciki ta hana shi magana,shima Khalees duk da cewa akwai damuwar dama can shi ba mai yawan magana bane Sun kwashi kusan rabin awa kafin Imran ya shigo reception din,yayi musu sallama suka amsa,cikin mamaki Khalees yace"isn't you Imran alƙasim?" "Yeah abdurrashid Abubakar!dama zan sake ganin ka?many years ahead!"Ma'aruf yana kallon su da mamaki akan fuskar shi, Khalees ya kalli Ma'aruf cikin murmushi yace"he is friend of mine lokacin da nayi boarding school a Bauchi,a good friend of mine" "Wow!very nice!Ashe kun san juna?"a cewar Ma'aruf da ɗan murmushin yaƙe a fuskar shi,don ya fara zargin kamar Imran ne silar ciwon Deeja Imran ya gyaɗa kai yana murmushi,sannan ya ɗan kalli Ma'aruf yace"ya ƙarin haƙuri kuma?"Ma'aruf yace"haƙuri mun godewa Allah" Imran yace"to Allah yaji qan shi yayi masa rahama, Allah ya albarkaci bayan shi ya sada shi da annabin rahama, Allah ya bada haƙurin rashin shi"Khalees da Ma'aruf suka amsa da ameen,Imran ya ƙara cewa "ya mai jikin? fauwaz ya sanar dani tayi collapse tun jiya?" Ma'aruf ya ja ajiyar zuciya yace"yeah,Amma for now da sauƙi,don ta dawo hayyacinta yanzu ma bacci takeyi". Imran fa ka tara maƙiya,ya kamata ka kama kan ka,don kowa yace baya yin ka😁 #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy_bee Page 25 "Okay to bari na shiga na ganta"a cewar Imran,bai jira cewar su ba ya shiga don ganin Deeja Kwanan Deeja shida a asibitin aka sallame ta,,ta rame tayi zuru-zuru,ta sake zama so silent,Wai a haka kullum Ma'aruf,matar shi fareeda da su Aunty Bintu suna kusa da ita suna tausar ta,baba Prof ma sau uku yana zuwa duba ta, mamie kam ita da yaran ta kullum suna hanya,yanzun ma da aka sallame ta kai tsaye Mamie ta wuce da ita can gidan Ta kai kwana goma kafin ta dawo hayyacinta,su mamie da yaran ta suna tarairayar ta da mantar da ita damuwar ta,hakan ya sa ta fauwalawa Allah komai ta kwantar da hankalin ta Ta kai kimanin sati uku a gidan bana Prof kafin mamie ta mayar da ita gidan ta,tun a ranar da ta koma umaima ta tare ta da wulaƙanci iri-iri,sam bata gaban ta don yanzu abinda ya dame ta ma dabam, tuni ta kama harkar gaban ta Cikin lokaci ƙanƙani shima Imran ya dawo da ainihin siffar shi,suka ƙara santa Deeja a gaba da cin mutunci iri-iri Sai ya zamana idan ta fita aiki bata son dawowa, Saboda Imran ya ƙuntata mata sai ya hana ta zuwa aikin,haka tana ji tana gani ta ajiye aikin ta da take matuƙar so Yau watan ta biyu da dawowa gidan Imran,da kaɗan kaɗan sai da ciwon ta ya kai ta ga kwanciya,yau kam ta wayi gari da tsanantar ciwon don yadda numfashi yake wahalar daita kamar mai athma,don haka ta yanke shawarar zata je asibiti don gwada lafiyar ta,don haka Imran yana shirin fita ta same shi shi da umaima a bakin motar shi tana zuba masa shagwaɓa Tayi musu sallama,Imran ya amsa amma fuska a ɗaure,ita kuwa umaima wani kallon banza ta bi ta dashi kafin ta taɓe baki ta ɗauke kai Cikin sanyin murya ta gaishe shi,ya amsa a daƙile sannan yace"me ya kawo ki?" "Bana jin daɗi ne,ina son zuwa asibiti"ta bashi amsa cikin yanayin ciwo Ƙare mata kallo yayi daga sama har ƙasa,eh tabbas ga alamu nan ya gani,amma sai yace"sai ki jira,ƙarfe tara zan zo na kai ki asibitin" Cikin Muryar ciwo ta amsa da cewa to "to na gode, Allah ya dawo da kai lafiya"ta juya ta koma cikin gida,tana jin umaima na jan dogon tsaki,ko kallo bata ishi Deeja ba Kafin ƙarfe tara fa gama shirya wa duk da bata da lafiya,amma Imran shiru,har goma shiru,da taga sha ɗaya tayi sai ta fara neman shi a waya,amma sai ya rinƙa danna mata busy,ganin hakan bai wani bawa Deeja mamaki sosai ba, instead ma sai ya kira ya'yan ta Ma'aruf ta shaida masa Shiru yayi cikin mamaki da haushi,can yace"shi Imran ɗin ne yace ki jira shi kuma yake katse miki kira?" Deeja tace "eh" "Gaskiya Imran ya bani mamaki,ban zaci zai yi haka ba,kar kiyi wasa da lafiyar ki,maza ki shirya kije ki ga doctor su'ad,don kema kin san ciwon ki bana wasa bane" Ta amsa da"to"sannan ta kashe wayar Shiryawa tayi cikin ƙarfin hali ta fice zuwa asibitin Dr su'ad, Dr tayi mata gwaje-gwaje ta tabbatar mata dole sai anyi admitting ɗin ta,don babu wani improvement da aka samu yanzu Deeja Imran ta fara turawa text message ta sanar masa sannan ta turawa Ma'aruf Ko awa ɗaya baayi ba Ma'aruf da Farida suka bayyana, Farida ce ta zauna a wajen Deeja,shi kuma Ma'aruf da ya ga babu matsala ya wuce wajen aikin shi Wajen ƙarfe uku fareeda na zaune a kujerar da ke gefen gadon da Deeja take kwance,sai kallon ta takeyi tana mamakin yadda ta ƙara ramewa ta lalace,Imran yayi sallama ya shigo Cikin nutsuwa ta amsa,ya shigo cikin ɗakin,suka gaisa a mutunce ya tambayi ya mai jikin?ta amsa da sauƙi sannan ya dire mata dubunnan kuɗaɗe a matsayin kuɗin magani,sannan ya ɗora wata envelop akai yace "Kuɗin nan na magani ne,wannan envelop ɗin saƙo ne idan ta tashi ki bata" Ta amsa da"to shikenan"ya miƙe ya nufi hanyar fita yana faɗin"Allah ya bada lafiya" Farida ta amsa da"ameen" Wajejen ƙarfe huɗu da rabi Deeja ta farka,Farida tayi mata sannu,ta haɗa mata ruwan wanka,tayi wanka ta ɗauro alwala tayi sallah,sannan ta gabatar mata da abinci, kaɗan taci saboda gaba ɗaya hankalin ta yana gida Bayan ta dawo nutsuwar ta fareeda ta bata saƙon mijin ta, kuɗi ne kimanin 500k,sai envelop,ta ajiye kuɗin sannan ta buɗe envelop ɗin Sai da taji gaban ta ya yanke ya faɗi,don haka sai ta fasa warware takardar tayi shiru tana fargabar abinda zata riska A lokacin Farida bata ward ɗin,ta fita zuwa office ɗin Dr su'ad Cikin dakiya ta ɗaga takardar ta warware ta a hankali,gaban ta yana dukan uku-uku ta soma karantawa Assalamu alaikum Nasan ba za kiyi mamakin ganin saƙo na ba saboda kema kin san me kikayi kuma tun da can ma kin san zaman haƙuri nakeyi da ke, saboda ba son ki nakeyi ba,kullum cikin saɓani da mahaifiya ta nake a dalilin ki,wato yanzu har ta kai zan ce kar kiyi abu,kuma kiyi, gaskiya bazan iya da halayen ki ba A don haka na yanke duka igiyoyin aure na da ke,inayi miki fatan alkhairi, Allah ya baki wanda ya fi ni" Imran alƙasim Bayyana irin tashin hankalin da ta shiga ma ɓata baki ne,ta miƙe a gigice tana furta"innalillahi wa inna ilayhi rajiun"dai-dai nan Farisa da Dr su'ad suka shigo Da sauri suka ƙaraso suna faɗin"lafiya dai Deeja?me yake faruwa?"bata ƙarasa faɗa ba sai gani sukayi Deeja ta sulale ƙasa,ko alamar motsi babu a tare da ita A gigice tayi ƙasa ta fara girgiza ta tana ambaton"Deeja! Deeja!!"amma ina babu alamun rai a tare da ita,ita ma dai Dr su'ad a gigicen take, sai dai tayi ƙoƙarin saita kanta ta bata taimakon gaggawa Hakan yayi matuƙar gigita su ganin still babu wani improvement,Farida tayi waje a matuƙar kiɗime,karo sukayi da Ma'aruf..... Gaskiya fa ko ni na fara jin tsoron Imran 🥺 #Nusy_bee ****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 26 Zubewa tayi a ƙasa tana haki cikin tashin hankali,da sauri Ma'aruf yaja baya yana faɗin"subhanallahi!me ya faru ne?" "Deeja!Deejan mu ta mutu"a cewar ta cikin tashin hankali Cikin sauri ya faɗa ɗakin,daidai lokacin wasu nurses suka shigo alamun Dr su'ad ta sanar dasu,da sauri aka ɗauke ta aka nufi emergency room da ita An kai kimanin awa biyu kafin a shawo kan matsalar,abin ya ɗagawa kowa hankali, musamman Farida da take ta gursheƙen kuka, saboda ta sani tuntuni kaf ƙannen Ma'aruf da Deeja kaɗai suke shiri saboda su faiza basu da mutunci sam,haka ya janyo musu shaƙuwa,ta sani in dai ta mutu to tabbas zata shiga wani hali Su kansu likitocin sunyi mamakin abinda ya taɓa ciwon nata lokaci guda,sukayi musu warning akan cewa su kula da duk abinda zai ɓata mata rai Abin ya bawa Farida mamaki, saboda ta san dai har ta fita babu alamun damuwa a tare da Deeja A sanyaye ta koma ɗakin da aka kwantar da Deeja,ta fara tattare kwanukan da Deejan ta kammala cin abinci,har ta gama sai ta kula da takardar saƙon Deeja a yashe a ƙasa,kamar kar ta ɗauka sai kuma taga gwara ta ɗauka,ta ɗauka ta buɗe ta karanta "Innalillahi wa Inna ilayhi rajiun!!!"ta furta cikin ƙaraji Sai ta zubar da kayan ta ruga wajen da Ma'aruf yake tsaye,cikin kuka ta miƙa masa takardar Ma'aruf ya girgiza sosai ya gyaɗa kai tare da faɗin"lallai babu shakka Imran ya cika butulu" Farida cikin kuka tace"ai wallahi bazai gama da duniya lafiya ba, Allah ya sai ya bi mata haƙƙin ta" Baƙin ciki da takaici ya hana Ma'aruf sake magana,ita kuwa Farida kuka take tana la'antar Imran Da Deeja ta dawo hayyacinta Farida ce mai tausar ta tare da bata shawarar ta manta da wani Imran ta cigaba da rayuwar ta,Hajiya mamie tazo,jin abinda Imran yayi ya girgiza ta matuƙa,abin yayi mata ciwo,amma ganin momy Aysha ta fita shiga tashin hankali har da kuka sai ta saukar da nata fushin Gashi kuma Imran yana sakin Deeja ya ɗauki umaiman shi suka wuce US in da fauwaz ya tafi honeymoon da amaryar shi Satin Deeja uku ta samu sauƙi sosai,mamie da kanta ta ɗauko ta a asibiti,ta dawo da ita gidan baba Prof,cikin ɗan lokacin aka sake mayar mata da matsayin ta na auta, saboda gata da sakalcin da ake mata, tarairaya sai abinda aka manta, yaya abdallah ƙanin fauwaz kullum sai ya fara zuwa wajen ta a falon Mamie yayi ya tsokanar ta sannan yake fita aiki,idan ya dawo kuma ya taho mata da favourite ɗin ta,nan ma su sha hira,hakan yana damun matar shi lubaisa wadda itama ba wani sakewa Deejan take sosai ba,itama Deejan ba shiga sabgar ta takeyi ba Cikin ɗan lokaci Deeja ta mayar da jikin ta tayi kyau,fatar ta tayi fresh asalin chaculate skin ɗin ta ta fito,ta cigaba da rayuwar ta cikin farin ciki Watannin ta uku a gidan su fauwaz suka dawo,shima Imran gidan ya wuto instead of gidan shi da ya saka Deejan da umaima a ciki. Shi kanshi fauwaz bai ji daɗin abinda Imran yayi ba amma ƙarairayin da suka yi ta zuba masa ya sanya shima ya fara ganin laifin Deeja An tarbe su cikin mutunci,babu wanda ya nuna musu komai,don dai baba Prof yayi warning kan kar a sake tayar da zancen,don haka ko a fuska babu wanda ya nuna musu komai,umaima sai yatsina takeyi Lokacin da suka dawo ko ƙeyar Deeja basu gani ba,don bata nan ma ta je yiwa yaya Ma'aruf da Aunty Farida sallama da zasu wuce turkey gobe,bata dawo gidan ba sai bayan maghriba,a lokacin dukan su suna zaune a main parlour ana hira cikin raha da farin ciki,tayi sallama da yawan su suka juyo,ciki har da su fauwaz da umaima,shi kam Imran all of a sudden yaji wani guilty conscience ya shige shi,ya kasa ɗaga kai ya kalle ta Kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kai ta gaishe su babu yabo babu fallasa,wasu sun amsa,wasu basu amsa ba,ta tsallake su ta wuce part ɗin Mamie in da ɗakin ta da aka kashe wa kuɗi kamar na amarya yake To fa!ganin Deeja a gidan,gashi Imran da alamu ya dawo gidan shima,sai umaima taji hankalin ta ya tashi,ta samu aminiyar ta afra ta karanta mata komai sannan ta nemi shawarar ta Itama afra tana tsoron fauwaz zai iya auren Deeja,don tun ba yanzu ba yana yawan ba ta labarin ta,don haka suka fara ƙulle-ƙullen yadda Deeja zata bar gidan,tunda dai ba gidan ubanta bane (a cewar su umaima fa 😁) Kwanan su biyu da dawowa Imran na zaune a lambun gidan inda ya saba zama yana duba wani littafin su na likitoci anatomy sai sallamar Deeja ya ji,yayi saurin ɗago kanshi yana amsawa,duk da cewar yayi mamakin zuwan nata amma ko a fuska bai nuna ba,don shi dai tun ranar da suka dawo sai dai ya gano ta daga nesa,don ko ya shiga parlourn mamie gaishe ta baya ganin Deejan Sam bai ji daɗin yadda ya ga ta koma so lean ba alamun dai har yanzu ba wani daɗin jikin ta takeji ba,ko kuma tana cikin damuwa "Sannu da hutawa!"ta furta fuskar ta babu yabo babu fallasa "Sannu Khadijah,mun same ku lafiya?"ya furta da ƴar fara'a a fuskar shi Maimakon ta amsa sai gani yayi ta dire masa kuɗi a kan ɗan table ɗin da ke gaban shi,har yanzu fuskar ta babu yabo babu fallasa ta kalle shi cikin idanu tace "Wannan kuɗin ka ne,kasan a musulunce idan aure ya rabu batare da ma'auratan sunyi wata mu'amalar aure ba namijin yana da rabin sadaki,dama 300k ka bayar ko?to ga 150k ɗin ka Sannan wannan kuma"ta faɗa tana nuna wanda yafi yawa ta cigaba"kuɗin da ka kai asibiti ne,tunda a lokacin da ka bayar auren ya ƙare responsibility na zuwa lafiya ta ya koma kan iyaye na,so shine na dawo maka da kuɗin da ka bayar na asibiti,na gode"tana kai wa nan ta juya ta bar wajen tana yunƙurin ɗaga kiran da akayi mata a waya Imran da mamaki ya ƙamar dashi ya taso da sauri ya biyo ta da kuɗin duka yana faɗin"haba Deeja!yanzu waɗannan kuɗin zaki dawo min dasu bayan kema kin san ninkin su ma kin fi ƙarfin su a waje na? Please Deeja menene na dawo dashi kuma?" Fasa ɗagawa wayar tayi ta kalle shi cikin idanu tace"bana buƙata ne,zai fi ka samu waɗanda suke buƙata ka basu zaka fi samun lada,ko ka ganni a buƙace ne?" "Kin raina kyautar da na miki ko me?"ya faɗa zuciyar shi na sake karyewa Yatsina fuska Deeja tayi tace"bakaji abinda nace bane?bana buƙata,idan ma kace na fi ƙarfin su ne to babu laifi,kyauta kuma bana so,na gode, Allah ya sa ka gane"tana kai wa nan ta juya ta bar wajen tana ɗaga sabon kiran Mima da tayi mata a lokacin Tabbas idan yace baiyi nadamar sakin Deeja ba yayi ƙarya,bai yarda shi wawa ba ne sai yanzu da har aboki zai shiga rayuwar shi ya tarwatsa masa farin ciki,ya tabbatar yana son umaima Amma Sam baya mata kallon mutum mai ƙima,yasan bayan momyn shi babu wata mace da ta bawa rayuwar shi gudunmawa,ta magance masa damuwa kamar Deeja,amma shi kanshi baya son ma tuna irin abubuwan da yayi mata waɗanda ya san har abada bazata taɓa mantawa ba Jiki a saɓule ya koma ya zauna yana kallon kuɗin da kawo masa,ba sai an gaya masa ba ya san definitely Deeja ta fi shi kusan komai na rayuwa, musamman gata,duk da cewa a yaran professor ta girmi Yasmin Amma ita yake kira autar shi, ballantana sauran mutane,tana samun gata da kulawa fiye da tunani,kowa son ta yake, saboda tsabar gata da soyayyar da ake mata ma lokacin da ta kammala karatun ta ta dawo Nigeria abba ya hana ta aiki,baba Prof ma ya goyi bayan shi,su a ganin su zata je ta sha wahala,don haka suka yanka mata kuɗi mai kauri a matsayin albashi,kuma ko da ta samu suka bar ta ta fara aikin ma basu daina bata albashin ba,amma duk da haka ya kan tuna duk ƙanƙantar abinda ya bata a lokacin ko ya siyo mata tana karɓa da farin ciki tayi masa godiya,karo na farko da Deeja ta dawo masa da wani abu da ya bata,wanda ba sai an gaya masa dalilin ba Duk wannan tattaunawa da Deeja da Imran sukayi akan idanun umaima,amma bata jin mei suka ce,ai kuwa ta cika tayi fam tana ta huci,a ranta ayyanawa takeyi dole ma ta ci uban Deeja don ta fara kai ta bango,ta kama ƙugu ta tsaya tana huci,ita kuwa Deeja ko lura ma da ita batayi bata tana magana da miman ta a waya suna dariya,sai kawai ji tayi an damƙar mata wuya Da sauri ta juya tana kallon umaima,tare da faɗin "zan kira ki leemo"ta kashe wayar Cikin mamaki tace"baiwar Allah lafiya?" "Oho ban sani ba,meye alaƙar da ta haɗa ki da miji na?wai ma ba an rabu ba?" Abin ya bawa Deeja haushi,ta kalli umaima da ke girgiza jiki tana ɗaure fuska,tana kuma sake riƙe mata wuyan hijabi Ta san dai ko dambe zatayi da umaima sai ta karya ta ma umaiman bata mata ko mintsini ɗaya ba,ture ta tayi tana faɗin"dalla sake ni,har wani miji ke gare ki?me ya shafe Ni dashi?" "Oho naji,to me ya kai ki wajen shi?" Deeja ta ja tsaki ta kalle ta cikin idanu tace"shi da kika isa dashi kije ki tambaye shi"daidai nan afra da zakiyya suka iso wajen,zakiyya itace matar Nasir Wanda yake bin salma Kwata-kwata ba ta shiga shirgin su Afra sai ta kama, saboda ta fuskanci basu da tarbiyya kwata-kwata, musamman afra da umaima,har gwara gwara lubaisa ma,don haka Deeja itace mutuniyar ta Fuska ɗaure ta kalli su Deeja tace"lafiya kuwa?" Umaima ta kalle ta a yatsine tace"wannan ƙaruwar gidan ta daina bibiyar min miji" Zakiyya ta kalle ta cikin ɓacin rai tace"karuwa?" "Eh karuwa!"a cewar afra cikin tsiwa, zakiyya zata sake magana afra tayi mata nuni da tayi shiru,sannan ta ja hannun ta suka bar wajen,tana jin umaima na jan dogon tsaki Ɗaki suka shiga, zakiyya ta rinƙa tausar ta amma sai Deeja ta nuna mata abin bai dame ta ba, dama kuma bata saka su umaima a layin masu hankali ballantana suyi abu ya dame ta Umaima da Afra kuwa sashen afra suka wuce suna shawarar yadda zasu ɓullowa Deeja,a ƙarshe dai suka samo hanyar da zasu fara musguna mata,sukayi shewa suka tafa Kwana biyu tsakani Mamie ta wuce Abuja,wanda daga nan zasu Yemen ita da momy Aysha Deeja ta shigo main parlour tana tafiya tana chatting da Aunty Bintu,labari take bata cewa yaya Ma'aruf da Aunty Farida zasu dawo next week,dama tafiyar ta yaron su ce Ayman da yake fama da matsalar ciwon ƙoda,amma yanzu da sauƙi sosai,tana cikin karanta amsar Aunty Bintu da take sanar da ita sun yi waya da Aunty Farida ɗin sai kayi taji santsi ya kwashe ta ta tafi luuu ta bugu da ƙasa,sai ji tayi an kwashe da dariya ta rainin hankali,ta kalli ƙasa don ganin abinda ta taka,ɗanyar kuɓewa ce kuma ga dukkan alamu zuba ta akayi,ta kalli masu dariyar, umaima,afra ce da lubaisa Afra ce ta ƙaraso wajen tana kallon ta a wulaƙance tace"kaɗan kika gani, indai kin nacewa zaman gidan nan,tunda baki da zuciyar da zaki zauna a gidan naki uban Deeja batayi jinkirin mayar da amsa ba"gaskiyar ki,tunda ko babu komai a gidan naki uban nake da zama"tayi ƴar dariya tace"shashashu"ta miƙe a zafafe ta tsallake kubewar ta bar wajen Umaima ta ɗura wani ashar ta nufe ta tana huci, lubaisa ta riƙe ta, umaima tana huci tace"sake ni,wannan karyar har ta isa ta zage ni?" Afra tace"easy sister,rabu daita,kema kin san bazamu ƙyale ta ba" Kai amma umaima kina da ƙarfin hali😥ko da yake banga laifin ki ba, saboda kinga Imran a mutum,baki ganshi lokacin da yake wulaƙantaccen shi ba #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 27 Tun daga ranar su umaima suka matsa wa Deeja lamba,duk abinda zasuyi don su ɓata mata rai yi sukeyi,kuma ta hanyar da ba kowa ne zai gane ba ballantana a tsawatar musu,bugu da ƙari ma Mamie bata nan, ballantana ta saka idanu Sai dai Deeja bata taɓa ɗaga kai ta kalle su duk da cewa suna ɓata mata rai,ta cigaba da harkar gaban ta kamar bata san sunayi ba A lokacin ba ƙaramin kewar aikin ta takeyi ba,da akwai shi yanzu ta san ganin ta ma sai yayi musu wahala ballantana su sanyo ta a gaba,amma yanzu babu aikin,sai dai ranar da ta gaji da zaman gidan ta tafi gidan Aunty Bintu ko gidan zee ƙawar ta,ko safeena,itama ƙawar ta ce tun ta secondary School,dama ita bata tarin ƙawaye Ganin irin takurawar da sukayi mata ya fara yunƙurin tayar mata da ciwo ya sanya ta ƙuduri aniyar ɗaukar mataki akan su Tana tsaye daga gefen ƙofar main parlour tana danna waya sai ji tayi an bangaje ta har wayar hannun ta ta faɗi,sai da ta firgita,ta ɗago da sauri tana kallon mai wannan aikin,sai taga Afra Tsaki ta ja ta sunkuya ta ɗauki wayar ta da har ta ɗan tsage,a zafafe ta furta"ki rinƙa kallon gaban ki idan kina tafiya,idan kuma makancewa kikayi sai kiyi magana a samo miki ɗan jagora" Kamar jira Afra take tayo baya da sauri tana nuna Deeja da yatsa tana faɗin"ke kama kanki,don dai kin san nafi ƙarfin wata trash ke,kar kiyi min abinda zai ɓata min rai na wulaƙanta ki a gidan nan wallahi" Deeja na kallon cikin idanun ta har ta kai aya sannan ta amsa mata"mijin naki bai karanta miki cewa ba'a nuna ni da yatsa bane?fara sauke yatsan idan yaso sai nafi fahimtar magana kikeyi" "An nuna ki da yatsan,kiyi abinda zakiyi,mijina kuma yafi ƙarfin yin magana akan wata kucaka ke" Deeja tayi wata dariyar rainin wayo sannan ta kewaye afra zata wuce, Afra ta finciko ta baya tana huci,Deeja ta kalle ta a nutse tana ƙoƙarin danne ɓacin ran da ke yunƙuro mata,kamar zatayi magana sai ta fasa tayi gaba Batayi aune ba sai ji tayi Afra ta ɗauke ta da mari, Deeja tayi stiff a wajen cikin tsananin mamaki da ɓacin rai,don samun waje Afra ta fara zazzaga mata masifa tana nuna ta da yatsa da tayi mata magana Batayi aune ba sai ji tayi anyi sama da ita an buga da ƙasa,aikin Deeja ne,a cikin tsananin fushi ta rinƙa wanke fuskar ta da maruka hagu da dama,tsabar gigita ma ko kukan afra ta gaza yi,umaima ce ta shigo parlourn ganin halin da Afra take ciki ya sa ta taho da gudu don ƙwatar ta,amma cilli ɗaya tayi daita umaima ta gane wannan ba kalar su bace,wato cika baki ba ƙarfi,da gudu ta kwasa zuwa part din afran,nan ta samu fauwaz ta shaida musu yayi hanzari yazo kar Deeja ta kashe Afra,a bala'in sauri ya ƙaraso wajen,kafin ya ƙaraso ma Deeja ta gama abinda zatayi ta watsar da umaiman can gefe ta ɗauke wayar ta da ta faɗi tana ƙoƙarin barin wajen Fauwaz ya kalli afra da umaima take taimaka mata ta tashi,ya kalli Deeja da ta sha mur tana ƙoƙarin shigewa ɗakin ta,a fusace yace"Deeja mahaukaciyar ina ce ke da zaki kama mata ta kiyi mata irin wannan dukan sai kace kin samu banza?" Wani kallon rainin wayo ta watsa masa fuska a ɗaure tace"shafa kaji! Ba fauwaz ba,hatta umaima da afran da ke fama da kanta sai da suka kalli Deeja da sauri saboda tsananin mamakin amsar da ta bawa fauwaz, fauwaz Sarkin zuciya ya kai mata mari,tayi saurin gocewa sannan ta kalle shi cikin idanu tana kaɗa babban yatsan ta da dan tsakiya a fuskar shi tana faɗin"mafi girman kuskuren da zakayi a rayuwar ka shine marin DEEJA! don't attempt it again!"tana kaiwa nan ta samu waje akan two sitter ta zauna don zuwa yanzu ita kaɗai ta san me takeji a ƙirjin ta "Okay! that's right!tattaro kayan ki ki koma gidan ubanki,wato mugun halin da kikayiwa Imran shi zakiyi mana ko?" "Imran!"ta maimaita da wani yanayi a fuskar ta,sam korar da fauwaz yayi mata ma bata gaban ta,amma ambatar Imran da fauwaz yayi ya daki ranta,wato sharri ma Imran yayi mata,hawaye Masu zafi suka silalo a fuskar ta, bata sake magana ba ta miƙe ta shiga ɗakin ta ta ɗauko ɗan ƙaramin trolley ɗin ta ta zo ta wuce ta gaban shi,don lokacin afra da umaima basa parlourn,ko kallon tsiya batayi masa ba ta fice daga parlourn Sai fauwaz yaji babu daɗi abinda yayi mata,cikin sanyi jiki ya biyo ta,har ta kai main entrance na gidan yace "Deeja dawo,kar ki fita" Banza tayi masa ta cigaba da tafiya,ya sake cewa"Deeja bakya jin ina miki magana,i said don't move an inch daga in da kike" Juyowa tayi ta kalle shi sama da ƙasa tace"kwantar da hankalin ka yaya fauwaz,bari kawai na bar muku gida kuyi sakewar ku yadda kuke so da matan ku,dama Ni na matsa muku"tana kaiwa nan ta sa kai ta cigaba da tafiya "Deeja nace......" "Hold it Yaya fauwaz!"ta faɗa a ɗan tsawace sannan ta juya ta cigaba da tafiya Kai tsaye gate ta nufa, fauwaz ya ƙwalawa driver din su kira yana bashi umarnin ya ajiye ta a duk inda zataje,ko kallon fauwaz batayi ba cikin ɗan sakin fuska ta kalli driver din tana faɗin"yi zaman ka kawai baba,na gode"ta fice daga gidan Fauwaz yayi mamaki,ya tsorata sosai da zuciyar Deeja,ko da yake yasan Deeja tana da ɗauke kai akan abubuwa da yawa, kuma sau tari ko da anyi mata abu bata rama ba lokaci take jira,amma tana da uzuri,kuma tana da haƙuri,sai dai yau ga dukkan alamu an ƙure haƙurin ta A sanyaye ya juyo yana nadamar abinda yayi mata,ya san shi da ya sake samun fuska a wajen ta kamar da sai wani ikon Allah Ita kuwa Deeja gidan Aunty Bintu ta wuce,ta so tafiya gidan yaya Ma'aruf amma har yanzu basu dawo ƙasar ba,don haka ta wuce gidan Aunty Bintu Wujiga-wujiga ta shiga parlourn Aunty Bintu,sallama kawai tayi ta shiga, Aunty Bintu ta ɗago da sauri tana kallon ta,bata sake kallon ta ba ta nemi waje ta zauna,Aunty Bintu tayi mata kallon tsaf sannan tace "Auta lafiya dai?" Bata tanka ba kuma babu alamun zata tanka ɗin,ganin hakan sai ta ƙyale ta,don kowa ya ga Deeja kallo ɗaya zaiyi mata ya gane da matsala Ta kai mintuna biyar kafin ta miƙe don yin alwalar sallar la'asar da taji ana kira,sai kawai ta yanke jiki ta faɗi, Aunty Bintu ta rafka salati da ihu, intisar da ke ɗakin ta bata ma san da zuwan da Deeja ba ta rugo a guje, ganin Deeja a kwance a ƙasa ta tafi tana girgiza ta tana kiran sunan ta,ganin ba tashi zatayi ba ta fita compound ɗin gidan tana ihun neman taimako, within few minutes ma'aikatan suka hallara a parlourn Kai tsaye asibitin Dr su'ad aka wuce da Deeja,sai dai wannan karon abin yafi ƙarfin asibitin,dole Aunty Bintu ta sanar da Ma'aruf da ko cikakken awa uku da sauka a ƙasar basuyi ba,haka ya sake shirya tashin su zuwa ƙasar Spain,don dama ya daɗe yana nema mata damar ganin wani babban likitan zuciya Dr Nicolas Alfred,babu ɓata lokaci kuwa suka wuce zuwa can ƙasar Spain A ranar ya gayawa Mima,ai kuwa nan da nan ta shirya ta wuce garin Barcelona da ke can ƙasar in da a can Dr Nicolas yake Awanni biyu da saukar jirgin su Ma'aruf da Farida sai intisar a Barcelona Mima ta sauka a ƙasar,dukan su babu walwala a fuskokin su,a lokacin da Mima taje har an shiga da Deeja observation room Dama kafin su tafi Ma'aruf ya shaidawa Alhaji Abubakar mahaifin Khalees da baba Prof,dukan su sunyi mata fatan samun lafiya tare da bada kuɗi mai yawa na gudunmawa Binciken Farko likitocin suka gano zuciyar Deeja ta kumbura,tana buƙatar aiki,wanda babu ɓata lokaci Ma'aruf ya saka hannu aka shiga daita theater room Aikin ya ɗauki tsawon awanni shida,su Ma'aruf suna ta addu'ar Allah yasa ayi aikin a Sa'a Bayan sun fito an tura ta ɗakin hutu ba tsawon awanni ashirin da huɗu,su ma su Ma'aruf suka koma masaukin su suna jimami Anan Farida take bawa Mima labarin mutuwar auren Deeja,Deeja ta sha mamaki matuƙa,take tsanar Imran ta sake ninkuwa a ranta, ranar dai Imran ya sha tsinuwa da la'anta da alkaba'i daga wajen Farida da Mima har ma da intisar da bata saka musu baki ba,amma tana aika Tata tsinuwar a ranta Sai da Deeja ta kwashe watanni biyu aka sallame ta,ta samu kulawa sosai,sau wajen biyar baba Prof yana zuwa duba ta,haka masu mamie da su yaran ta su fauwaz,duk da cewa ko sau ɗaya fauwaz ɗin bai ga haƙorin ta a waje ba kuma ya san dalili Sosai Deeja ta mayar da jikin ta ta koma walwalar ta,daga Spain Kai tsaye Umrah suka wuce Saudiyya,daga nan suka wuce Malaysia,kwanan su goma suka dawo Nigeria,amma a can suka bar Mima Kwanan su uku da dawowa Alhaji Abubakar yazo har gidan marigayi Dr Mahmud, kasancewar yanzu Deeja ta koma gidan su da zama,a babban parlourn Dr Mahmud ɗin Ma'aruf ɗin ya sauke shi da girmamawa,bayan ya gaishe shi ya umarce shi ya kira masa Deeja Jidda Ahmed,Deeja tace a gaishe ki yadda kike supporting ɗin ta da taya ta yaƙar Imran 😁 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 28 Da sallama ta shigo parlourn,ta durƙusa cikin girmamawa ta gaida shi,ya amsa cikin kulawa yana tambayar ta jiki,ta amsa da alhamdulillah, fuskantar ta yayi sosai sannan yace "Khadija naji duk abinda ya faru,kar ki sanya hakan a ranki ya dame ki,ki ƙaddara cewa jarrabawar ki kenan,amma in Sha Allah komai yazo ƙarshe yanzu,yau juma'a ko?to in Sha Allah zuwa juma'a mai zuwa da kaina zan aura miki mutumin da ya dace,in Sha Allah hakan zai kawo ƙarshen dukkan matsala" Kan Deeja a ƙasa tana sauraron aminin mahaifin nata da maganar shi tayi mata gingirin aka,shi kanshi Ma'aruf maganar ta zo masa a bazata,amma duk a cikin su babu mai iya cewa komai,sun daɗe da sanin aminin abban nasu baya magana biyu,kuma ba'a chanja masa magana, Ma'aruf ne yayi ƙarfin halin yin fatan alkhairi,ya miƙe yayi musu sallama, suma sallama sukayi masa suka biyo bayan shi suka nufi cikin gidan suna tunanin wanda za'a bawa Deeja Babu wanda Deeja ta sanar wa sai Mamie da Aunty kiyya,don ko Aunty Bintu bata sani ba ballantana kuma Mima,a lokacin ma mamien bata nan tana Abuja,momy Aysha bata da lafiya taje dubiyar ta Ɗaurin aure kawai akayi,don ko walima ba'a yi ba,Deeja sai tarar rabin wanda ta aura takeyi,Aunty kiyya da Aunty Farida ne suke kula da ita,sai zainab ƙawar ta wadda zuwa yanzu ta gama yi mata komai don komawa bakin aiki Da daddare bayan Isha'i aka kai Deeja gidan ta,sai rarraba idanu take na fargaba,don bata san me zata tarar a wannan auren ba,to Imran ma da ta san shi ta saba dashi ya aka ƙare ballantana wanda ko ganin shi bata taɓa yi ba? Da wuri suka tafi ya rage saura ita kaɗai, ban da sunan Allah babu abinda bakin ta yake ambato Sai wajen sha ɗaya taji shigowar motar shi,takure kanta tayi a cikin kujerar da take zaune,gaban ta sai dukan uku-uku yakeyi Da sallama ya shigo,ji tayi kamar ta san muryar,har bata san sanda ta ɗaga kanta da sauri don tabbatar da zargin ta ba Ai kuwa mamaki mai tsanani ya mamaye fuskar ta ta kasa amsa masa sallamar,ba kowa bane face engineer abdurrashid Abubakar Yusuf wanda muka fi sani da KHALEES. Shima wani kallo ya bi ta dashi alamar mamaki,kafin ya wuce zuwa ɗakin shi Itama a saɓule ta tashi ta wuce ɗakin ta,a ranar dai bata runtsa ba saboda tsananin mamaki da takaicin wannan haɗin,to ya ta ƙare da Imran ma da suke shiri ballantana wannan dimkin ɗin da ta daɗe da daina gaishe shi saboda tsabar rashin amsawa? "Oh Ni Khadija!"ta faɗa a fili"nan kuma rayuwa ta jefo ni?wancan dai ga irin rayuwar da nayi a gidan shi,saura wannan mai fuskar mala'ikan tsaron wutar, kullum fuska a ɗaure yana cin magani, ko Ni da na rasa iyaye na duka biyun ai bana daure fuska sai wannan da duka iyayen shi suke raye, Allah ya sani na tsani a ɗaure min fuska wallahi idan naga ya cigaba da wannan mugun halin wallahi sai in........." Maganar ta maƙale tare da hannun ta da take ƙoƙarin cire rantsatstsiyar rigar lace da ke jikin ta,jikin ta ya kama rawa sosai,ta sake murza idanu tana kallon Khalees da ya biyo ta zuwa ɗakin nata,shima dai kallon nata yake cikin idanu, fuskar tashi a ɗaure amma bazata iya cewa ga expression ɗin da yake kai ba Dama biyo ta yayi ya kawo mata kazar da ya kawo ta al'ada daga nan ya gani ko bata lacking komai,sai yazo ya samu tana kwashe masa albarka Sunkuyar da kanta tayi ƙirjin ta na dukan uku uku,shi kam ya taɓe baki ya ɗauke kai ya ajiye mata kazar ya fice daga ɗakin Deeja bata sake tabbatar da baƙin miskilancin Khalees ba sai da zaman su ya miƙa,yayi mamakin samun ta a matsayin cikakkiyar budurwa duk da cewa ta taɓa aure,amma bai nuna ko a fuska ba ballantana har ya tambaye ta Zaman nasu dai babu yabo babu fallasa,baya zama daita suyi hira,idan tayi kuskure yayi ta faɗa da tsawa,baya yaba mata,tun tana tsoron shi har ya zama jiki ta daina Sai dai yana sauke haƙƙin auratayya da ya rataya akan shi,sannan bata rasa ci ko sha, kazalika yana matuƙar kulawa da ita idan ciwon ta ya so tashi ko wata rashin lafiyar,sannan kuma ya bata dama ta koma aikin ta,don ana i gobe zata koma yayi mata kyautar sabuwar mota Ƴan uwan shi ma ba wani zuwa sukeyi ba,idan taje kuma bata samun fuska shiyasa take janye jikin ta,kuma tana shakkar shiga cikin su Wannan shine tarihin Deeja da gwarazan ta Imran da Khalees 🥰 CIGABAN LABARIN....... Ƙarfe biyar da mintuna biyar haka agogon ƙasar US ya nuna,a hankali take saukowa daga matattakalar jirgin janye da trolley ɗinta,tana rungume da yaron ta Affan, zuciyar ta cike da tunane-tunane,a wani ɓangaren kuma cike da farin cikin haɗuwa da ƴar uwar ta Sai da ta samu waje ta zauna sannan ta ciro wayar ta tayi activating international mode ta fara kiran number din da Inna Mariya ta bata,bugu biyu aka ɗaga Sai a sannan fargaba ta shige ta,cikin rawar murya tayi sallama,wata murya mai cike da nutsuwa ta amsa,cikin rawar murya take faɗin "Good evening ma!I am Khadija Mahmud,am talking to Dr nusaiba mahmud please?" Matar tayi dan murmushi tace cikin harshen Hausa"eh nice auta,Inna Mariya ta sanar dani zuwan ki,kin sauka ko?" Haba!ai Deeja ji tayi kamar an tsunduma ta a aljanna,ta washe baki tana faɗin"yeah na sauka few minutes ago" "Okay!just wait for few minutes, you will be home very soon in Sha Allah"daga nan aka kashe wayar Cikin farin ciki ta cigaba da kallon masu kaiwa da kawowa a reception na airport ɗin, lokaci ɗaya kuma zumuɗin ta ya ɗan ragu tuno Khalees da tayi,ta san duk lokacin da ya dawo hayyacin shi akwai daru,to mutumin da in dai tafiyar kwana ta kama ta ko kwana ɗaya ne sai tayi da gaske ballantana wadda ita kanta bata san ranar komawa ba? Ta sauya layi, kuma babu wanda ta sanarwa tahowar ta sai Mima,wadda ta korawa warning ko da wasa kar ta sanarwa ko Aunty Bintu, ballantana yaya Ma'aruf Ta kalli ɗan ta wanda babu inda ya baro Mahaifin shi, Allah sarki!a yadda ta san soyayyar yara irin ta Khalees da yanzu tare suke rainon abin su,amma shigowar Nadiya cikin rayuwar su ya tarwatsa musu farin ciki,ta goge ƙwallar idanun ta da sauri tana bin danƙareriyar G-wagon ɗin da ta gani tayi parking ɗan nesa da ita Wani kyakkyawan matashi da zai iya yin Sa'an ta ne ya fito daga motar,sai sai wasu yara mace da namiji da suka biyo bayan shi #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 29 Macen zata Kai shekaru goma,namijin bai wuce shida ba,kallo ɗaya tayiwa macen gaban ta ya faɗi,don ko ina yarinyar nan ta fito bata da maraba da abban ta,tayi musu kuri har suka ƙaraso in da take zaune da murmushi a fuskar su Sallama sukayi mata,ta amsa itama fuskar ta a sake,cikin murmushi matashin yace"Deeja, right?" Gyaɗa Masa kai tayi tana murmushi tace"yeah"yace"wow!very nice!!you are highly welcome, let's go, Aunty nusaiba is waiting for you"ta miƙe tsaye,yarinyar tayi saurin amsar Affan suka wuce suka nufi motar A motar ƴar ta macen ta kalli Deeja tana murmushi tace"Aunty Deeja what's his name?"tana nuno mata Affan "Mahmud,known as Affan,what about You and your brother?" "I am ZAINAB known as amra,my brother is Ismail known as ajmal,and this is Uncle safwan"ta ƙarashe tana pointing matashin, murmushin fuskar ta yana nan Wata ajiyar zuciyar farin ciki tayi tana sake rungume yaran tana jin ƙaunar su a ranta, Safwan da ke gaba yana driving yana kallon su ta madubi yana murmushi Suna isa bakin tangamemen gate ɗin gidan Dr nusaiba Safwan yayi horn, guard ɗin ƙofar ya ɗage, zumuɗin Deeja ya ƙaru, Allah Allah kawai take ta ganta a gaban sister ɗin ta A balcony ɗin suka tsaya,shi dai Safwan bai ma shigo ba,daga nan fita yayi uzurin gaban shi don ya bawa ƴan'uwan damar ganawa da junan su sosai Intercom Amra ta matsa,within some seconds Aunty nusaiba ta bayyana Fara ce tas kamar abban ta,babu in da tabar shi sai yanayin idanun ta irin na maman su(zainab)doguwa ce mai madaidaicin jiki,ta saki baƙin gashin ta irin na Deeja sak da suka gado daga zainab har gadon bayan ta,alamun hutu da gyara sun gama bayyana a tare da ita,wani idan ya ganta zai ɗauka bata wuce sa'ar Deeja ba Ba sai ance wa Deeja ga yayar ta ba,babu ɓata lokaci ta faɗa jikin ta ta ƙanƙame ta ta fashe da kuka,ita dai nusaiba murmushi takeyi tana shafa bayan ta,wata nutsuwa ce ta shigi Deeja,don sai ta ji tamkar jikin mahaifiyar ta ne,lallai Bature yayi gaskiya da yace(blood is thicker than water Sai da Aunty nusaiba ta ja ta zuwa parlourn sannan ta sake rungume ta tana goge mata hawayen tana faɗin"is okay! shikenan,ai kuma kuka ya ƙare,ko nima taɓarar zaki yi min?don ance min dama baba da Abba sun sakalta ki ko?"ta ƙarasa da sigar tsokana tana murmushi Tura baki Deeja tayi tana faɗin"Ni Allah bani da taɓara" "Naji,ina su yaya Ma'aruf?"da sauri ta kalle ta ta ɗaure fuska tace "bai san nazo ba,bana son ya sani for now please" Nusaiba ta buɗe ido ta kalle ta tace"to ta yaya zai sani?" Deeja ta juya hannu tana faɗin"na sani ko kuna communicating?" Ƴar dariya nusaiba tayi tana dungure mata kai tana fadin"lallai dai naga autar mamma,babu inda kika bar halin ta Allah yaji ƙan ta,bari nayiwa su Amra magana su kawo babyn nan ku samu ku yi wanka ku ci abinci ku huta"daga nan ta wuce zuwa ɗakin su Amra ***** ***** ***** Cikin shagwaɓa ta kalle shi tana faɗin"haba honey!kana kallo na maƙaryaciya ne?ka duba da kan ka ma ka gani,wallahi abubuwa da yawa sun ƙare,idan baka siya ba wa zei siya min? Please mana my gentle"ta ƙarashe tana kwanciya kan kafaɗar shi Ya kalle ta cikin ƙosawa da halayen ta yace"umaima!wallahi na gaji,daga Ni sai ke kawai a gida amma ko waɗanda suke rayuwa su goma basu kai mu cin kuɗi ba,yau kwana tara kawai da yin monthly shopping Amma har abubuwa sun ƙare,zubarwa kikeyi ne ko me?naga dai ba ƙananan kuɗi nake kashewa ba amma a banza,to wallahi nan da next one week Kar ki saka ran zan sake siyo ko tsinke" "Haba my heart,ka daure mana,Ni a gani na duk abinda kayi min ai baka faɗi ba ko?"cikin shagwaɓa da kissa take maganar Ko kallon ta bai sakeyi baya miƙe yana ƙarasa sanya rigar suit ɗin shi, yana gama shirya wa ya ɗauki briefcase ɗin shi bayan ya saka sau cikin shi ya fice daga ɗakin,ta biyo shi har harabar gidan kamar yadda suka saba Yana ƙoƙarin buɗe motar shi yaga mai gadin yana ɗage gate ɗin gidan,daga shi har umaima suka bi motar da ta shigo da kallo,wata farar mota ƙirar GMC ce ta shigo cikin gidan,suka bi motar da kallo don ganin waye wannan ya kawo musu ziyara da wannan farar safiyar Sai da hantar cikin su ta kaɗa ganin mamallakiyar motar, umaima har wani jiri ne ya fara ɗibar ta ta dafa motar Imran tana kallon ta tana nufo su, fuskar nan kamar koyaushe a ɗaure Ba kowa bace baƙuwar ta su sai likitar zuciyar nan uwar khadija Mee'ad,wato Dr halima Kabir azare,wadda dai muka sani da MIMA Sanye take da doguwar rigar abaya da mayafin ta,ta rufe idanun ta da baƙin spec,tana ƙarasowa gaban su ta sanya hannu ta cire glass ɗin tana watsa musu mugun kallo,kafin ta mayar da kallon ta ga Imran tana kallon shi a ƙasƙance tace "Da kyau malam Imran!jarumin jarumai,mai iya sakayya,ka kyauta!! Wato ka muzgunawa sister na,sannan kayi mata wulaƙanci,ka auro wannan ƙazamar kun haɗu kun ƙuntata mata,a sanadin ku ta kamu da ciwon zuciya,sannan kayi mata sakin wulaƙanci,duk wannan bai ishe ka ba sai da kukayi abinda kukayi kuka kashe mata auren ta da ya fara samar mata peace of mind,sannan ka ɓatar da ita, da kyau mr cinnaka,ko nace ɗan kunama!!" "Ke Malama!dalla dakata!! ba'a haifi wadda ta isa tazo har gidan miji na taci masa........"bata ƙarasa ba taji saukar wasu mahaukatan maruka kamar ba hannun mace ba,aikin Mima ne,a fusace tace"kika sake interrupting ɗina idan ina magana sai kin raina kanki,ba da ke nake ba,da wannan sokon mijin naki nake,na sake jin kinyi tari anan!" Tsit umaima tayi ganin cewa Imran ɗin da taso ya kare ta idan tayi kurin ko motsawa baiyi ba,ko niyyar tari ma bashi da ita,idan ba idanun ta ke mata gizo ba ma kamar shima jikin shi ɓari yakeyi Mima ta sake kallon Imran da ya kiɗime,kafin tayi magana ya riga ta "Deeja ya ɓata? yaushe?ina ta je?" Wani watsatstsen kallo ta jefa masa tace "ban sani ba munafuki, na ba ka nan da 24 hours,ko dai sister na ta dawo ko na ɗaure ka"tana gama magana ta juya cikin kwanciyar hankali ta koma motar ta,ta fizge ta ta bar gidan Sai da ta hau titi sannan ta kira Deeja tayi mata Barka da sauka, a lokacin Deeja tana ɗakin da aka kai ta tana hutawa,bayan sun gama gaisawa cikin kwanciyar hankali Mima ta kora mata bayanin abinda ta aikata,salati Deeja ta rafka tace" leemo kanki ɗaya, Allah ya shirye ki" "Ameen!wallahi sai na hana su zaman lafiya baki ɗayan su musamman wannan tainannen Imran ɗin,i hate him wallahi"dariya Deeja tayi ta kashe wayar ta tana girgiza kai Imran kam Mima tana fita shima ya fice daga gidan,kai tsaye ya nufi gidan Khalees da mugun speed,hankalin shi idan ya kai dubu ya tashi Yana isowa ya danna wa Khalees kira,sai da yayi masa kira na huɗu a na biyar ya ɗaga A lokacin Khalees yana dining yana juya abincin gaban shi, zuciyar shi cunkushe da damuwa amma ya rasa takamaimai abinda yake damun shi,can ƙasar zuciyar shi yana jin wani abu mai kama da gurbin da bai cika ba,yana jin wani abu mai kama da kewa amma ya kasa gane menene Wayar shi ce ta ɗauki ringing, Nadiya da ke zaune tana chatting ta kalli wayar ta cigaba da chatting ɗin ta,shi kam yayi zurfi a tunani bai ma ji ba,sai da wayar ta damu Nadiya ta ɗauko,ganin Imran ta dungura masa tana faɗin"Dr ke kiran ka" A kasalance ya ɗaga wayar,kafin yace komai yaji Imran yana cewa"Abdul ka fito ina ƙofar gida"ya kashe wayar Miƙewa yayi batare da yace uffan ba ya nufi ƙofar fita,! Nadiya ta bishi da kallo kafin ta taɓe baki A bakin gate yaga Imran sai safa da marwa yakeyi,Imran ya riga shi magana da tambayar "Khalees ina Deeja?da gaske ne Deeja ta ɓata?wai me ya faru ne?me kayi mata ne? Please Khalees kar kayi mata abinda nayi mata har yanzu ina regretting nima" Shiru Khalees yayi yana kallon Imran kamar wani sabuwar halitta,Imran ya kama kafaɗar shi yana jijjiga shi yana faɗin"Khalees Are You okay? are you with me?" "Imran me yake faruwa dani ne me ya same ni?"a cewar Khalees cikin wani irin firgice "I don't get you Khalees,what do you mean?" "I'm serious Imran,I don't know what came over me,me nayi ne?ne na aikata?ina Deeja na?me nayi mata?why Imran why?"babu ɓata lokaci hawaye suka fara wanke masa fuska,ya dafe kai cikin karayar zuciya Imran ya zuba masa idanu cikin mamaki ya kasa magana, Khalees ya kamo hannayen shi cikin karayar zuciya yana faɗin"Please Imran kaga kai aboki na ne,help me to find my life,idan na rasa Deeja ban san ya zanyi ba, Please friend,she is my everything,my happiness" Cikin tausayi Imran ya dube shi yace cikin sanyin murya"in Sha Allah zamu nemo ta,zamu ganta,zata dawo gare ka da ikon Allah,mu bi komai a sannu Please friend,in Sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya"da haka ya samu ya kwantar masa da hankali har ya koma cikin gidan,shima Imran ya shiga motar shi ya tayar ya tafi cikin tsananin tashin hankali da ruɗani Ɗakin umaima ya dosa,amma sai yaji tana waya,don haka ya tsaya yana kallon ta ganin bata ma kula da ya shigo ba "Kayi haƙuri don Allah,wallahi Ni kai na ƙoƙarin da nakeyi kenan,a yanzu ya chanja min bana samun yadda nake so sosai" "Don Allah kayi haƙuri,nayi maka alƙawarin nan da kwana uku zanyi maka ƙoƙari" "To shikenan" Tana ɗaga kai taga Imran,sai da gaban ta yayi mummunar faɗuwa,alamun rashin gaskiya suka bayyana a tare da ita "Da wa kike waya?" Kai!anya kuwa? Mima ina jin fa kamar baki kyauta ba,ki je gidan mutane ki tayar musu da hankali ki mari matar gida ki yiwa miji rashin kirki?? a'a ba dani ba!kai kam malam Audu ihu bayan hari kakeyi don dai Deeja ta haure boarder😅ke kam umaima anya kuwa? gaskiya ban gane ba🥺 Yau dai nayi zuciya na sakeyin post biyu a rana ɗaya,ba don kowa ba sai don ku likers da commentors, Allah ya sani ina matuƙar jin daɗin hakan, Allah ya bar mu tare🥰 *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 30 Cikin in Ina tace"eh.....um....uh ......wawwallhi.....da...da... qawa ta nake waya"duk ta firgice Kwata-kwata bai yarda ba,amma da yake ba ta wannan yake ba ya kalle ta fuskar shi babu rahama yace "Ina kuka kai Deeja ke da ƙawar ki? Me kukayi mata? Me yasa kuka raba ta da mijin ta?" Miƙewa tsaye tayi,tana so tayi tsiwa amma babu fuska ba,a tsorace tace"ni ban san inda take ba,ni ban ma san auren ta ya mutu ba" Imran yayi ƴar dariyar takaici yace "Are You for real? Baki San auren ta ya mutu ba,ashe ban san wacece ke ba!" Kuka ta fara tace"Ni wallahi ban san me yake faruwa ba,kawai dai......." "Hold it please!"ya daka mata tsawa"wallahi sai na wulaƙanta ki if I find out da sa hannun ki a ɓatan Deeja, wallahi sai kinyi nadamar sani na" Ranta ya fara ɓaci,a zafafe ta fara magana tana kuka"shikenan babu dama tayi tafiyar ta wani wajen sai a zarge ni?ita ƙaramar yarinya ce da......."bata ƙarasa ba taji shuuuuu a kunnen ta,sai daga baya ta fahimci marin ta Imran yayi,irin marin da rabon da ayi mata irin shi ta manta lokacin,zuruu tayi tana kallon shi kukan ma ya ɗauke batare da ta sani ba "Don't let me repeat my self,ki nemo Deeja,ko zama na dake ya ƙare"yana kai wa nan ya juya ya fice daga ɗakin Zamewa Umaima tayi ta zauna akan tiles tana jan numfashi,tashin hankali ba'a saka maka rana!take kanta ya fara juyawa saboda shiga tashin hankali,a wannan yanayin ta ɗauki mayafi da key ɗin motar ta tayiwa gidan Nadiya tsinke Nadiya tana zaune a parlour tana cin cup cake tana danna waya umaima ta faɗo kamar daga sama A firgice Nadiya ta kalle ta tace "lafiyar ki kuwa?" Umaima ta zama yaraf akan kujera tana faɗin"ba lafiya ba Umaima, Umaima ina cikin wani hali,a kowanne lokaci aure na zai iya mutuwa,kinga kunci na Nadiya"ta juya mata side ɗin da Imran ya mare ta tace"Dr ne ya mare ni kinga" "To fa!me kika masa haka?"Nadiya ta faɗa tana gutsirar cake ɗin hannun ta Umaima ta share hawayen ta tana faɗin"wai cewa yayi in nemo Deeja?yanzu ina zan fara neman Deeja fisabilillahi?" "Deeja kuma?wacece haka?"a cewar Nadiya tana kwanciya a kan three sitter da take zaune Umaima ta kalle ta da mamaki tace"Deejan ce baki sani ba?matar mijin ki fa da suka rabu" Nadiya ta yamutse fuska tana taɓe baki tace"ɓata tayi ashe?shine ake tuhumar ki?lallai ma an gaishe su" Umaima ta marairaice tace"don Allah ki taimaka min mu nemo ta kar aure na ya mutu Please" "Toooo!Ni kuma da nemo Deeja?au Allah?gaskiya ya kamata a daƙile siyar da wiwi a ƙasar nan"duk wadannan maganganun da takeyi ko kallon banza umaiman bata ishe ta ba Umaima da ta fuskanci raina mata hankali Nadiya takeyi sai ta fusata tace"Nadiya naga kamar maganar nan ma Baki ɗauke ta a matsala ba ko?" "Matsala? Allah ya kaɗa ta can ya bar ku da kayar ku hajiya" Hawaye ya zubowa Umaima tace "kenan baki ɗauki matsala ta a taki ba?" "Me ya shafe Ni da matsalar ki har da zan cusa kaina a cikin ta?" Umaima ta miƙe a fusace tace"eh zaki faɗa hakan bayan nayi miki komai,to wallahi ko ki fito da Deeja ko na tona miki asiri idan yaso aurenki ya mutu kafin nawa,don nasan halin ki nasan abinda zaki aikatawa" Wata dariyar rainin hankali Nadiya tayi sannan ta gintse kamar ba ita ba tace"yaro yaro ne!kar nake kallon ki Umaima,wai ma kin manta ni malamar ki ce kuma uwar ki a makirci da tuggu?to kar ki fara abinda bazaki iya ba,kar ma ki jefa kanki a uku" Zama dirshan Umaima tayi ta fashe da kuka cikin karayar zuciya tace"don Allah Nadiya Kar kiyi min haka,ya zanyi,kin juya min baya,yaya Najeeb ya juya min baya,ga Dr ma,ku kaɗai ne hope ɗina,ya kuke so nayi ne?" "Kije ki tambayi ragowar biyun don wataƙila su suna da Lokacin ki,amma ni kam bani da lokacin sauraren haukan ki"tana kai aya ta nufi uwar ɗakin ta,har ta kai ƙofa ta juyo tana kallon umaima da har yanzu take kukan tashin hankali tace "idan kin fita ki ja ƙofar parlourn"ta sa kai ta shige ɗakin ta Cikin tashin hankali Umaima ta miƙe ta fice daga gidan,kai tsaye gidan fauwaz ta nufa, Afra na zaune tana yanke wa haneef farce sai ganin Umaima tayi a kanta,a ɗan tsorace tace"Malama Lafiya?"daga yanayin fuskar ta za'a iya gane haushin da taji na abinda umaiman tayi mata Amma da yake umaima tana cikin tashin hankali bata kula ba,ta zauna gefen Afra tana faɗin"ina fa lafiya Afra, Imran zei iya rabuwa dani,ina cikin tashin hankali" Afra ta ɗan buɗa ido da mamaki tace"ikon Allah!to me kikayi masa?" Umaima ta warware mata labarin kaf tun daga lokacin da nadiya taga Khalees har auren su da sakin Deeja da abinda ya faru yau bata ɓoye mata komai ba Shiru Afra tayi cike da ɗimbin mamaki,zuwa can tace"ya kuke da wannan nadiyar ne?" "Nima ban sani ba,amma yaya na Najeeb yace cousin ɗin mu ce"wani kallo Afra tayiwa Umaima tace"shine dalilin da yasa kikayi mata hanyar da ta auri engineer ko dai da wata a ƙasa?"Umaima ta sunkuyar da kai ta kasa bata amsa Afra tayi murmushin takaici tace"uhm!umaima kenan!Ni kishin miji na nakeyi da Deeja, saboda ina da yaƙinin babu wani mai hankalin da zai samu Deeja a matsayin mata yayi wasa da damar shi,tunda na samu labarin auren ta da mijin da yafi nawa komai na zubar da makaman yaƙi na,lubaisa ma haka,amma ke saboda ƙiyayya da hassada ce a ranki sai da kika shigar da wata ƙawar ki kika tarwatsa mata farin ciki da ta ɗauki lokaci mai tsawo tana nema Mu kanmu son zuciya ne ya rufe mana idanu saboda Imran ɗin nan a wulaƙance ta samo shi ta mayar dashi mutum,amma yau an wayi gari akan wata can da bai san asalin ta ba yayi mata cin mutunci,to Ni dai babu abinda zan iya,kuma wannan haliman da kike magana duk wani rashin mutunci da wata fitsara da kike taƙama da ita ta zarce ki,don haka Ni kar kija min magana,miji na yana nan,tun wuri ki koma gidan ki,nima kar kija yaji aure na ya fara rawa" "Allah sarki Deeja baiwar Allah!"Muryar fauwaz sukaji,a firgice suka waiga suka kalle shi,yana sanye da jallabiya milk colour yana tsaye fuskar nan babu Rahama Sai da hantar cikin su ta kaɗa,afra ta firgita don tasan itama nata auren zai iya fara rawa A nutse ya ƙaraso ya samu waje ya zauna sannan ya dube su yace"kun bani mamaki,wannan abu yayi min ciwo sosai, Afra,wallahi ba don kinyi nadamar abinda kukayi ba da yau babu abinda zai hana Ni sakin ki Ku in banda rashin iymani bakwa ganin cewa Deeja marainiya ce?kuma ita mutum ce da ko magana bata dame ta ba ballantana shiga shirgin wani?to don Allah meyasa zaku matsawa rayuwar ta? Shi kanshi Dr auren ki da yayi shine sakayyar abinda yayi wa Deeja,don ke dai wallahi ba matar zama bace Duk halin da kuke ciki da najeeb ina sane" A tsananin kiɗime umaima ta ɗago ta kalle shi idanun ta a waje, fauwaz yayi murmushi yace"well!you think kuna yin dabara kuna ɓatar da hankalin mutane ke da Najeeb babu wanda ya sani ko?to tun barowar ki garin ku taura,da Abinda yayi silar zuwan ki garin nan na sani,kuma saura ƙiris mijin ki ya sani" Faɗuwa tayi a gaban shi tana faɗin"don girman Allah ka taimake ni ka rufa min asiri,na roƙe ka" "Zan rufa miki asiri but in one condition"gyaɗa Kai takeyi tun ma kafin taji sharaɗin,bai damu ba ya cigaba"sai kin datse kowacce alaƙa dashi wanda ya mayar da rayuwar ku kamar waina a tanda daga ke har Imran,idan nace alaƙa ina nufin kowace iriyar alaƙa"da sauri tana share hawayen ta tace"Ni dama don babu yadda zanyi ne,amma na kai watanni biyar ma yanzu ko haɗawa bamuyi ba,nima dama bana son alaƙar" "Wannan ya rage naki kuma,na biyu kuma wanda shine ma yafi Zama wajibi,ki nemo min ƴar'uwa ta" Umaima kukan ta ya ƙaru,tashin hankali ya mamaye ta,ita ina zata ga Deeja? meyasa ake ɗora mata alhakin ɓatan ta,ko kallon ta fauwaz bai sakeyi ba ya kalli Afra yace "Ke kuma,duk abinda kikeyi kinayi ne don kinga alamun ina son Deeja ko?to Kar kiji da wai,ina son ta fiye da yadda kike tunani ina son ki,kuma duk ranar da na ganta ki shirya zama daita a matsayin kishiya ko ki bar mata gidan" "Wallahi abban haneef na amince,na yarda zan zauna daita a matsayin kishiya nayi alƙawari"Afra ta amsa har yanzu zuciyar ta bata daina bugawa ba Ɗaga kafaɗa yayi gami da taɓe baki alamar bai damu ba,ya fice daga parlourn Umaima babu shiri ta koma gida,zama tayi tana tunanin mafita,zuwa yanzu kukan ma ya ɗauke mata,sai kanta da yake sarawa, abubuwa sun taru sun cunkushe mata Wayar ta ce ta ɗauki ruri,a ɗan firgice ta kalli wayar,ta janyo tana duba mai kiran Ganin Najeeb sai da gaban ta ya faɗi,ta daure ta ɗaga ta kai kunne,kafin tace komai taji yana faɗin "Malama kina raina min hankali!na buƙaci kuɗi daga gare ki naji shiru,na buƙace ki kina ta min yawo da hankali,to na baki nan da awa uku,ina son ganin ki" Cikin kuka tace"haba yaya Najeeb!wai me yake damun ka ne?na gaya maka ina cikin damuwa amma maimakon ka tausaya min sai ƙara min wata damuwar kakeyi,ya kake so nayi ne wai?"ta ƙarashe cikin ɗaga murya "Ke ballagaza!kama kanki!!kar ki sake ɗaga min murya,or else na ɗauki mummunan mataki akanki,ina ruwa na da wata damuwar ki ta banza? Abinda nace idan bazakiyi ba ki gaya min!" Cikin kuka tace "bazan yi ba wallahi,na gaji da halin ka,haba!" Wata dariyar rainin hankali yayi yace"I see,to ko me kika gani kar ki zarge ni,ki zargi kanki"yana kai wa nan ya kashe wayar shi Takurewa tayi tana zubar da hawaye, rayuwar ta ce ta baya take rotating akan ta,wani irin kuka mai ciwo ya ƙwace mata,amma duk da haka gwara waccan rayuwar akan ƙazamar rayuwar da Najeeb ya jefa ta, mahaifin ta ya faɗo mata a rai, ta sake fashewa da kuka mai ciwo,zuwa yanzu kaso saba'in da biyar cikin ɗari na hope da take dashi a komai ya tafi To pa 🥺 umaima ya dai?? #Nusy bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 31 Zama tayi dirshan a ƙasa tana tunanin mafita,ji takeyi dama tun farko mutuwa,amma tabbas tayi wauta,tayi tsalle ɗaya mai jefa mutum rijiya yayi dubu bai fito ba,duniya ta ruɗe ta da yawa,ta sake fashewa da kuka tana faɗin "Ni umaima na cuci kaina,naga ta kaina,nasan abinda nayi ne yake bibiya ta,kaicon rayuwa ta!" "Ai baki fara kaico ba umaima!munafuka,matsiyaciya, tsinanniya,amma dai bakin uwa ne a kanki ko?dama ke mutuniyar banza ce? dama ke ɗin karuwar Najeeb ce?na godewa Allah da bai bani haihuwa da ke ba annamimiya!"Imran ne mai faɗar wadannan maganganu cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya, fuskar shi a matuƙar ɗaure da ɓacin rai da tashin hankali Wayar shi ya jefa mata a fusace yana faɗin"Umaima!a yau na fahimci kuskure na na auren ki,nayi nadama mara amfani ta auren ki,ashe ragowar wani ƙato ce ko ma nace ƙatti?kuma da auren ki kike fornication?the worst part ma da aboki na?wato da ke dashi dukkan ku mutanen banza ne,Ni zaku cuta Ku ci amana,shine kuka shiga tsakani na da khadija ya cuso ki don ku cuce ni"yayi murmushi mai ciwo yana kallon umaima da ke daskare tana kallon wayar shi da hotunan ta da najeeb suna sheƙe ayar su yake,ya cigaba da cewa "Nayi miki alƙawarin sai na ganar da ke kuskuren ki daga ke har babban matsiyacin,sannan magana ta ƙarshe,ki nemo min ƴar uwa ta,idan ba haka nima na ɓatar dake"yana kaiwa nan ya ɗauki wayar shi ya take ta ya fice daga ɗakin Sai a yanzu ta ji wani kukan ya kubce mata,nadama mara amfani ta cika zuciyar ta,a fili ta furta "ya Allah ka taimake ni,Deeja ina kika shiga ne? Allah ka bayyana ta" *** *** *** Ita kuwa Nadiya ta kunna ta ƙure volume tana bin waƙar tana rausaya, Khalees ne ya shigo ɗakin kamar an jefo shi,a raine ta kalle shi tace "Tun ɗazu ka fice,ina kaje?" Wani watsatstsen kallo ya bi ta dashi,sai da taji hantar cikin ta ya kaɗa,bai ce mata uffan ba ya wuce closet ɗin shi ya fara loda kaya a cikin trolley,yana gamawa ya janyo ya fito,da mamaki ta dube shi tace"ina zaka?" "Kar ki kuskura ki biyo NI,zakiyi danasani"abinda yace mata kenan ya fice Mamaki ne ya ƙamar daita,lallai ba shakka aikin ta yayi sanyi,don ita dai a iya sanin ta ko kara ta ajiye Khalees baya iya tsallakewa ballantana har ta kai su ga haka,da sauri ta ɗauki figigin mayafi ta ɗora akan English wears ɗin ta tayi waje,tun kafin ta baro parking lot take zuba mahaukacin horn,bawan Allah jiki na rawa ya buɗe,kafin ta fita sai da ta tsaya ta auna masa zagi da cin mutumci sannan ta fice,tana fita yace"da izinin Ubangijn ka'aba yadda asalin matar gidan nan mutuniyar kirki ta bar gidan nan kema sai kin barshi ita ta dawo,ai Allah nace"ya koma kan benchin shi yana tuna nagarta da halin ƙwarai irin na Deeja Ita kuwa Nadiya Kai tsaye gidan bokan ta ta nufa,bayan ya gama ƴan dube-duben shi ya kalle ta rai a ɓace yace"kinyi sake mahaifiyar shi ta ɓata mana aiki,yanzu ko da wasa bata sakewa da addu'a,har ƙannen shi ta shi ya sanya sunayi,sannan bata tsaya anan ba,akwai wani abokin aikin shi mijin naki, mahaifiyar shi ta haɗa kai da wannan mutumi tana bashi ruwan addu'a yana bawa mijin ki,aikin mu ya lalace sosai" "Na shiga uku!"ta faɗi cikin ƙaraji tana dafe kai,"yanzu ya zanyi?" "Mafita ɗaya ce,ga wannan maganin"ya miƙa mata wani ƙulli yace"ki zuba masa a abinci,ki tabbatar yaci,yana ci shikenan zaki samu kanshi kamar baya ko ma fiye,amma idan bai ci ba za'a iya samun matsala"da rawar jiki ta amshi maganin tana faɗin"zai ci ma,zan tabbatar da yaci"ta ajiye masa kuɗin shi ta fice daga ɗakin nashi Tana komawa gida babu ɓata lokaci ta ɗora girki,white rice ta dafa da miya taji kifi,ta san shine favourite ɗin Khalees,ta tsala wanka ta sanya sexy English wears ta zubo da kitson attachment da tayi bayan ta,tayi wa fuskar ta light make up ta zauna tana danna waya tana taunar chewing gum,a lokacin ana ta sallar Isha'i amma ba ta ita take ba Tun lokacin take jiran dawowar shi shiru,har tara shiru,goma shiru,sai hankalin ta ya fara tashi,ta ɗauki waya ta fara kiran shi,amma switch off,hankalin ta ya fara tashi,don sai lokacin ta tuna cewa ya ɗauki jakar kaya,ai bata san lokacin da ta ɗora hannu aka ba ta kama gunjin kuka,faɗi take "na shiga uku na lalace,asiri na ya tonu" Kafin washegari da safe wasu ƙuraje masu ruwa da mugun wari suka feso mata a dukkan ilahirin jikin ta,ga ƙaiƙayi da raɗaɗi da suke mata,da ta kalli kanta a madubi ita kanta sai da taji ƙyanƙyami, bata taɓa shiga matsanancin tashin hankali da masifa irin wannan ba,ta koma bata da aiki sai kuka da tunanin mafita ***** ***** ***** Ta nutsu sosai a gidan Auntyn ta Nusaiba tana jin daɗin rayuwar ta,yau kwanan ta shida kenan a US, Rayuwar su sukeyi ciki ita da Aunty nusaiba da yaran ta Amra da Ajmal,sai auta Adnan,gaba ɗaya ta manta da wani abu wai shi ɓacin rai ko damuwa Affan kuwa koyaushe yana hannun ƙanin mijin ta Safwan da Allah ya ɗora masa ƙaunar yaron,shi kanshi Affan yanayin san Francisco ya karɓe shi yayi fresh abin shi Suna zaune a parlour suna kallon wani American film,yaran duk basa nan sun tafi makaranta,hatta Safwan ya fita aiki, Deeja ta ɗago ga kalli auntyn tata tace cikin shagwaɓa"Aunty" Cikin kulawa Aunty nusaiba tace"ya dai auta?" Deeja ta zauna daga kishingiɗar da tayi tana kallon ta tace"Aunty na ganki Amma banga Yaya Yusuf ba" Murmushi aunty Nusaiba tayi tace"inna bata gaya miki baya US ba?" "Ta gaya min,amma kuma ai bazaki rasa sanin inda yake ba ko?" "Eh!yana tokyo,a can yayi karatu kuma ya fara aiki,yau kwanan mu sha shida da dawowa matar shi ta haihu,yaushe kike zuwa?" Da mugun zumuɗi Deeja tace"ko yau a shirye nake wallahi" "Lallai kam,to be ready next week in Sha Allah zamu tafi,amma muna dawowa zan nema miki admission ki yi masters ɗin ki idan kin yarda" "Yeah Aunty!na yarda, wallahi dama na so ɗorawa kawai ban samu dama bane" "Okay,in Sha Allah idan muka dawo sai ki ɗora karatun" Murna Deeja ta rinƙa yi har da tsalle,Aunty nusaiba sai kallon ta takeyi tana murmushi Satin ta biyu a ƙasar suka cale zuwa ƙasar Japan,tun a airport taga yayanta Yusuf,sai da gaban ta ya faɗi da ta ganshi,don babu in da ya baro mahaifin su sai hasken fata,da gudu taje ta rungume shi tana hawaye,ya rungume ta yana shafa kanta,kafin ya ɗago ta yana kallon ta da murmushi,yace"Are little sister? Kin girma fa! lokacin da muka bar ki You was just a little girl" Murmushi Deeja tayi tana nuna masa Affan da ke hannun Aunty nusaiba tace"yanzu nima gashi na dire little baby"dariya sukayi daga shi har matar shi hanan da ke rungume da ƴar babyn su safna Farin ciki iya farin ciki kam Deeja ta shige shi,taga soyayya ta ga kulawa daga kowanne angle, Yusuf ma daina fita aiki yayi,kullum yana tare da ƴan uwan nashi ana ta shan raha da hira,ga matar shi mai kirki da barkwanci Satin su ɗaya a Japan suka tattara suka koma US,Deeja taji tamkar su kar su rabu,amma hakan bai hana ta farin ciki ba Satin su uku da komawa Deeja ta fara ɗaukar lecture a Cambridge University cikin farin ciki da nasara,karatun nata yana gara mata yadda take so,don taji sauƙi ma Aunty nusaiba ta samar mata Nanny da zata rinƙa kular mata da Affan,ƴar ƙasar Uganda, dattijuwa mai tsafta ***** ***** ***** Babu irin cigiya da neman da Khalees da Imran basu yiwa Deeja ba,gidajen rediyo da na tv babu in da basu kai cigiya ba, Khalees har wani ɗan ƙaramin hauka yayi,ya zabge ya rame ya fita hayyacin shi,ko abinci baya iya ci sai Imran ya lallaɓa shi yake shan yoghurt ko tea,yanzu haka ma ya janye shi zuwa Lagos don abin nashi ya fara yawa Suna zaune a ɗakin hotel ɗin da suka sauka,waya ce a hannun Khalees ɗin ya ƙurawa hoton su shi da Deeja idanu,sunyi kyau a hoton dukkan su sunyi murmushi,sunyi hoton ne a wani lokaci da suka shirya zasu je gaida Hajiya yace mata"ƴan matan Abdul kinyi kyau fa" Tayi murmushi tana masa hararar wasa tace"don kar nace ka chanja kar ƴan mata suyi min shigar sauri shine kayi riga malam masallaci?ko baka san ka fi Ni kyau ba?"shine yayi dariya ya janyo ta yayi musu hoton suna dariya,suka hau musu akan wanda yafi kyau,ƙarshe sai da suka ɓata lokaci suka fita, dukkan hotunan Deeja da ke wayar Nadiya ta goge su,wannan ne kaɗai saboda son hoton da yakeyi ya ɓoye shi Nadiya bata ganshi ba Imran da ya shigo yanzu ya tsaya yana kallon yadda hawaye ke zubo masa yana kallon wayar shi,yasan abinda yake kallo don wannan hoton shine abokin hirar shi,abincin shi, walwalar da duk wani farin cikin da ya rage masa, tabbas ya jinjina irin son da Khalees yakeyiwa Deeja,ya ƙarasa inda yake yayi tapping kafaɗar shi,ya ɗago a sanyaye yana kallon shi,ya samu waje a gefen shi ya zauna Cikin kwantar da murya yace"Ni kam Khalees why not mu koma gida mu tuhumi matan mu kan batun Deeja,nasan Umaima bazata iya ɓatar da Deeja ba,amma nasan idan Nadiya ta aikata wata ɓarnar musamman wadda ta shafi umaiman zata gaya mata,so definitely indai sune suka ɓatar da ita idan muka tuhume su zamu samu hint" "Kana ganin hakan mafita ce?"a cewar Khalees yana kallon shi "In Sha Allah,mu jarraba hakan" #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 32 "To shikenan,muje" A ranar Imran ya yankar musu ticket suka dawo Kano,a gidan Imran suka sauka,ko mintuna talatin da sauka basuyi ba Imran ɗin ya ɗebo ƴan sanda suka shiga suka fito da umaima da ke ta gunjin kuka,dama already ya tura wasu gidan Khalees, sai da aka tafi dasu sannan suka shiga cikin parlourn gidan suka zauna jugum,an rasa mai yin magana a cikin su Turo ƙofar akayi da karfi,da sauri suka kalli ƙofar, Ma'aruf ne,yana zuwa ya shaƙe wuyan rigar Imran ya hau zazzaga masa masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,babu abinda bai kira shi ba,matsiyaci,butulu,maci amana,wanda bai san ciwon kanshi ba,a ƙarshe ya kaɗa masa warning cewa ya nemo masa ƴar uwar shi ko ya ɗauki duk matakin da ya ga dama akanshi,sannan ya juya kan Khalees da shima ya zuba masa idanu kamar yadda Imran ɗin yayi yace "Ka bani mamaki Abdul,ban taɓa tunanin za'a haɗa kai da kai a cutar da wani wanda yake da alaƙa dani ba,zuwa yanzu nasan waye kai,na gode"yana gama bayani ta take ƙafar Imran ya juya ya fice daga parlourn Shiru ya ratsa parlourn,Imran ya sunkuyar da kanshi ƙasa, Khalees kam ya rasa mai ya kamata yayi ma,duniyar baki daya tayi masa wani irin ƙunci,da wanne zai ji?da ɓatan Deeja da yaron shi ko da laifin da wasu suke ɗora masa,a sanyaye ya miƙe yana goge ƙwallar da ta cika idanun shi,da sauri Imran yace"ina zakaje?"bai amsa ba ya nufi ƙofa,da sauri Imran ya riƙo hannun shi yana faɗin"I'm sorry gaskiya bazaka fita a wannan halin ba" Cikin sanyin murya yace"gidan mu zan koma,wajen Hajiya ta" "Okay bari nazo na mayar da kai,don bazan bar ka kayi driving a wannan halin ba,bai sake magana ba ya samu waje ya zauna, Imran ya shiga don ɗauko makullin mota ** ** ** Babu irin wuyar da su Umaima basu sha ba don su faɗi in da Deeja take,amma basu faɗa ba saboda basu sani ba,ga Nadiya da take fama da jinya,cikin wannan halin Khalees ya aikowa da nadiya takardar saki,da ƙyar dai ƴan uwan ta suka samu suka karɓe ta, Umaima tayi kuka sosai,ta ji inama ace tana da wani a kusa da ita nata,dama Najeeb ne ya ɗauko ta daga ƙauyen su, kasancewar bata da iyaye sai ya mayar da ita gidan su,amma ya mayar da ita tamkar matar shi Yanzu kuwa ta sani bata da gata,bata san yadda rayuwa zatayi da ita ba ***** ***** ***** Lokaci guda Deeja tayi kyau tayi ƙiba,ta zama abin burgewa, hankalin ta ya kwanta sosai,amma dai tana matuƙar kewar mijin ta Khalees,ko ya yake zuwa yanzu bata sani ba Tsawon shekara guda ta ɗauka tana karatun ta kafin ta kammala, result ya fito tayi murna sosai ganin sakamakon yadda yayi kyau,a lokacin ne hankalin ta ya koma gida,sai taji sam bata kyauta ba abinda tayi,don haka ta shawarci auntyn ta kan cewa tana son komawa Nigeria Aunty nusaiba ta kalle ta tace"tuntuni ya kamata ace kin je ko da da ziyara ne,amma bazan matsa miki ba, shiyasa na ƙyale ki,yanzu dai ki bari sai nan da three weeks sai mu tafi gaba ɗaya,nima Ina son naje na ga ƴan uwa na" "Su Aunty masu ƴan uwa,to Allah ya nuna mana dai"cewar Deeja tana dariya Itama dariyar tayi tace"ameen,ko kin ɗauka ke kaɗai ake so?" Kafin lokacin yazo Deeja ga ƙasa,sai ƙirga kwanaki takeyi,ranar tafiya Deeja sai zumuɗi takeyi,su Aunty suna ta tsokanar ta suna dariya A gidan baba Prof suka sauka,basu sanar da zuwan su ba,amma anyi Sa'a yawancin jama'ar gidan suna nan,ganin Deeja ya haifar da sowar murna da farin ciki,don kowa ya cire rai daita,duk da har zuwa lokacin ana saka ta a adduoi,Aunty Bintu ma satin su biyu kenan daga dawowa daga Syria,bata samu shigowa gidan ba sai yau,ashe dai ta taki Sa'a Fauwaz ne ya kira Ma'aruf, Khalees da Imran da basa nan,bai gaya musu abinda yake faruwa ba,sai da suka zo kusan a tare,Imran ya riga su shigowa,yana zuwa Ma'aruf ya shigo,bai kai ga fitowa daga mota ba ma Khalees ya shigo,sai dai har kwanan yau Ma'aruf baya yi musu magana,don haka ko da sukayi masa sallama ma tsallake su yayi ko kallon su baiyi ba,suma suka bi bayan shi zuwa cikin gidan Sunyi matsanancin mamaki da farin cikin ganin Deeja,da alamu ma hankalin ta a kwance yake,ɗan jaririn yaron ta Affan yanzu yawon shi da gudu babu inda baya zuwa,babu abinda baya ci maganar ce dai ba sosai ba,kallo ɗaya Deeja tayi wa Khalees ta fashe da kuka,don yadda ya rame ya lalace abin tsoro,shi kam da sauri ya ƙaraso inda take ya riƙe hannun ta gam yana faɗin"Deeja ina kika shiga? hankalin mu ya tashi sosai,komai ya ƙare min Deeja,komai yayi min duhu saboda babu ke,nayi missing ɗin ki sosai Deeja" Deeja ta girgiza kai tace"ka yafe min Khalees,na aikata kuskure,nayi abinda bai dace ba,na daga muku hankali,amma komai ya wuce,ga yaron ka nan"ta miƙa masa Affan"shima yayi kewar ka" Ya ƙanƙame shi yana kallon shi yana murmushi,idanun shi cike da ƙwalla,kusan kowa a parlourn sai da ya jinjina irin soyayyar da sukeyiwa juna, Ma'aruf yace"Weldone auta,mu ba'a ganmu ba ko?"da murmushi ta tashi ta ƙarasa kusa dashi ta rungume shi tace"kaima nayi missing ɗin ka yaya,ina Aunty Farida?" "Tana gida,ashe all this while gidan nusaiba kika je kika tare kika barmu da tashin hankali?" Nusaiba tace"yaya Ma'aruf ita tace bata son kowa yasan tazo,shiyasa nima nayi shiru" "Yanzu fisabilillahi idan tana shirme sai ki biye mata?" "To yaya Ma'aruf nasan abinda aka mata?"Ma'aruf yayi ƴar dariya kawai,ya kama hannun Adnan suka fice daga parlourn Ɗaya bayan ɗaya Deeja ta gaisa da yayyen nata,suka rungume junan ita da kiyya, Afra ma tazo ta rungume ta cike da farin ciki,daga nan suka ja ta sashen kiyyan,don yanzu ita da lubaisa ne kawai a gidan, fauwaz da Imran kowa ya koma gidanshi A can taji labarai iri-iri,har da na Umaima,sai taji tausayin ta sosai,har ma tayi alƙawarin zata nemo ta ta taimaka mata jin wacece ita,abin ya bawa su Afra mamaki, Afra ta kasa haƙuri tace "Gaskiya ke ta dabam ce Deeja,yanzu duk wahalar da Umaima ta baki har zata baki tausayi bayan ta fita daga rayuwar ki ki sake dawo da ita?" Murmushi Deeja tayi tace"kika sani ko hakan ya zama silar shiryuwar ta,ke ce fa yanzu kika ce min bata da iyaye,Najeeb ya kawo ta kuma yanzu basa tare,kika san a wanne halin rayuwar take?kuma ma Ni sam banga hikima don mutum ya aikata maka sharri ka rama masa da sharri ba" "Hakane kam, Allah ya sa hakan ya zamo silar shiryuwar ta ta" "Ameen ya Allah"inji Deeja Khalees ya nemi izinin tafiya da Affan,don dama Deeja ta yaye shi,babu musu ta haɗa masa ƴan kayayyakin shi,yana ta ɗaga mata ɗan hannun shi ta rako su har bakin mota,sai da suka tashi sannan ta koma gida #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 33 Kwanan Deeja da dawowa ta ja Afra suka nufi gidan su Umaima ko nace gidan su Najeeb,sun sha mamakin a halin da suka same shi,yayi haɗari ya faɗo daga mashin ya gamu da matsalar spinal cord,ko iya tashi bayayi, mahaifiyar shi mai jinyar shi Da sallama suka shiga parlourn da Afra ta rinƙa bin shi da kallon mamaki ganin yadda ya sauya,suka gaida mahaifiyar tashi,da ke bin su da idanu,ta amsa da fara'a, Deeja ta gaishe da najeeb da ke kwance yana jin jiki,don bayan wannan matsalar har da brain cancer da ta kama shi,ya amsa cikin rawar murya, Afra kam ko kallon banza bai samu daga gare ta ba, Deeja ta kalle shi tace "Am dama gidansu umaima muke son zuwa,to bamu san address ɗin ba,shine nazo idan Allah ya sa ka sani ka sanar mana" Shiru Najeeb yayi na ƴan sakwanni kamar bazai ce komai ba,ƙwalla ta tarar masa a idanu,cikin karayar zuciya ya fara bayani "Umaima ƴar garin taura ce,tana zaune a wani family house mai suna gidan cheɗiya,kaf garin su ansan gidan,sai dai umaima bata ji dadin gidan ba,don haka ko Ni bani da tabbacin zaku same ta ko bazaku same ta ba" Deeja ta miƙe tana faɗin"zamu jarraba zuwa mu gani,in Sha Allah zamu same ta"daga nan tayi wa mahaifiyar shi sallama ta dire mata kuɗi 20k, mahaifiyar shi sai godiya take kamar zatayi wa Deejan sujjada, shima Najeeb cikin karayar zuciya yace "Deeja,ki yafe min,kinga yadda rayuwa tayi dani,idan kika haɗu da umaima itama kice ta yafe min,don na cutar da rayuwar ta da yawa" Deeja ta goge ƙwallar idanun ta tace"na yafe maka"sannan ta fice daga parlourn, Afra ta biyo bayan ta Kai tsaye Deeja ta nufi taura jihar Jigawa,daga ita har Afra suna fatan Allah yasa su ga umaima Basu wani sha wahalar gano gidan ba,amma da suka tambayi wata mata da ke tatar gasarar koko ina Umaima?sai ta yatsina fuska tace"bata dawo daga kasuwa wajen sana'ar ta ba,sai dai ko ku jira ta ko ku bi ta"Deeja da Afra suka kalli juna suka sake kallon matar,Deeja tace"babu matsala zamu jira ta,inane ɗakin nata?matar ta nuna musu tsohon ɗaki mai tsohon ƙyaure batare da ta sake magana ba Allah yaso da bishiya a kofar ɗakin umaiman, Deeja ta koma mota ta ɗauko musu babbar dadduma suna hira suna shan iska,babu wanda yayi musu tayin ko ruwan sha,in da Allah ya taimake su suna da ruwan gora a mota,shi suka sha sukayi,Deeja ta ɗauko musu ƙatuwar dadduma sukayi alwalar azahar sukayi sallah. Zaman awa biyu da mintuna sukayi umaima ta dawo, Deeja tana bawa afra labarin Cambridge University ta hango Umaima tana shigowa gidan,shiru tayi tana kallon yadda ta fice a hayyacin ta tayi duhu sosai,tana sanye da atamfa da hijabi da suka ji jiki,amma fes take,fuskar ta ma babu alamun damuwa sam a tare da ita, Afra ma kallon ta takeyi,har taje wajen wata igiya ta kwaso kayan shanya sannan ta nufo ƙofar ɗakin nata Sam bata kula da wasu a zaune ba sai da ta ƙara matsowa, Deeja ta fara gani,don tafi saitin inda take tahowa,ƙamewa tayi tana kallon Deeja da tunanin ko mafarki takeyi, Deeja tayi murmushi ganin irin shock ɗin da Umaima ta shiga ta miƙe tana murmushi ta rungume ta, Umaima ta ƙanƙame Deeja tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya,afra ma ta miƙe tazo ta rungume ta, Umaima ta haɗa su duka ta rungume tana kuka,sai da ƙyar ta ɗago tana kallon Deeja tana faɗin"Allah Sarki Deeja!ina kika shiga ne?yadda na ɗauke ki ba haka kika ɗauke Ni ba,na shiga tashin hankalin ɓatan ki,ki yafe min Laifuka na Deeja......"maganar Tata ta katse saboda kukan da jaririyar bayan ta ta fara tana mutsu mutsu,wadda Allah bai sa Deeja da Afra sun kula da ita ba Sakin Deeja tayi ta ɗanyi baya tana sauko da babyn,kallo ɗaya Deeja tayi wa jaririyar ta waro idanu tana faɗin"umaima haihuwa kikayi?" Murmushi umaima tayi,Deeja ta amshi yarinyar tana ƙara kallon ta,bata da maraba da mahaifin ta Imran, Umaima ta ɗauke daddumar da suka shimfiɗa da suka shimfiɗa ta buɗe ƙofar ɗakin ta suka shiga cikin ɗakin Siminti ne malale a ɗakin,amma duk ya faffashe,daga gefe kuma yaloluwar katifa ce da aka shimfiɗa mata zanin gadotsoho,sai dai ɗakin ƙal yake,dama umaima ba daga nan ba wajen tsafta Cikin rawar jiki ta dauko murhun ta na gawayi tana ƙoƙarin hura wuta, Deeja ta dakatar da ita, Umaima tayi murmushi tana kallon Deeja tace"ko dai bazaki iya cin cimar mu ta ƙauye bane?" Da sauri Afra ta kalle ta,nan da nan hawaye suka ciko idanun ta,tace "Umaima yau ke kike kiran kanki ƴar ƙauye?" Umaima ta waro idanu tana murmushi tace"to da Ni ɗin ƴar ina ce?nan ce mahaifata,nan ce mahaifar baba na,kinga kuwa bani da inda yafi nan"bata ƙara sauraren su ba ta cigaba da ƙoƙarin hura wutar ta, Deeja tace"mu fa ba yunwa mukeji ba,ki zo mu zauna, magana zamuyi tukunna"Umaima tace"duk da haka dai sai mun ci abinci tukunna"tilas Deeja ta ƙyale ta, Umaima ta ɗora musu faten tsaki da yaji yakuwa da gyaɗa Bayan ta gama a kwano ɗaya ta zuba musu,ta ɗebo musu ruwa a ƴar randar ta,suka ci a tare suna hira,bayan sun gama ta kwashe kwanukan don wankewa, Deeja kuma ta gyara wajen, Umaima tana shigowa tace"kai!daga zuwa kawai sai ki fara aiki?" "Ke dai zauna kawai Umaima"a cewar Deeja,babu musu ta zauna tana fuskantar Deeja Deeja tace"umaima me ya faru bayan tafiya ta?kuma dama kina da ciki kika taho baki gayawa Imran ba?ya na ganki haka?me yake faruwa ne?" Murmushi mai ciwo umaima tayi,ta karɓi jaririyar ta daga hannun Afra,ta fara shayar da ita,ta jingina kanta da jikin bango ta fara magana cikin sanyin murya "Iyaye na dukka biyun na rasa su ina ƙarama, mahaifiya ta ta rasu ina da shekaru biyar, lokacin da ƴan uwan ta suka zo gaisuwa bayan an share makoki sun so tafiya dani,amma mahaifi na yace a'a, tabbas ran ƴan uwan mahaifiya ta ya ɓaci,ƙarshe dai baayi rabuwar daɗi ba,don baba na jadaddawa ya rinka yi ƴa tashi ce babu mai raba su,dangin shi suka shiga maganar suka ƙara dagula lamarin Haka dangin mahaifiya ta suka koma garin su suka barni a hannun mahaifi na,babu irin gatan da baiyi min ba, makaranta boko da islamiyya da kanshi yake kai ni,ya zauna yayi hira dani,yayi wasa dani,don sam bana iya shiga cikin yara kamar kowa nayi wasa,don haka idan mahaifi na bayan na dawo daga makaranta ɗakin mu nake shigewa nayi ta wasanni na da kayan wasan da baya gajiya da siya min Haka rayuwa ta kasance har tsawon shekaru uku,a lokacin ina da shekaru takwas,a wannan lokacin ne nasan ma'anar rashi duk da ƙarancin shekaru na,don a shekarar ne na rasa mahaifi na bayan rashin lafiya da yayi ta kwana ɗaya"umaima ta kasa cigaba saboda kukan da yafi ƙarfin ta,da alamu har yanzu tana jin zafin mutuwar,su kansu Deeja da Afra kuka sukeyi,Deeja ma mutuwar mahaifin ta ce ke dawo mata #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 34 Umaima ta cigaba"lokacin da mahaifi na ya rasu na samu tausayawar al'umma da dama, musamman ƴan gidan mu,amma abin mamaki wannan karon ko mutum daya daga dangin mahaifiya ta bai zo ba, ina jin ƴan gidan mu suna zunɗen wai dangin mahaifiya ta basu san mutuwa ba,kuma soyayyar ƙarya sukeyi min don babu yadda za'ayi ace basuji mutuwar mahaifi na ba,tun maganar bata wani dame ni ba,amma da aka ɗauki lokaci da mutuwar mahaifi na sai ta dame ni A lokacin duk masu nuna min soyayya da tausayawa sun janye daga gare ni, ba'a maganar dangin mahaifi na da muke rayuwa gida ɗaya amma duk da haka abinda zan ci sai sun ga yunwa tana neman kwantar dani suke san min, ba'a yi shekara guda da mutuwar baba ba na daina zuwa kowacce makaranta, don sharaɗi ƴan gidan mu suka saka min, sharaɗin cewa sai na ɗauki talla tukunna za'a bani abinci,babu musu na amince don bani da wata mafitar bayan wannan Kusan kowa a gidan nan yana ɗora min talla,masu iymani a cikin su ne ke bani abinci,amma wasu cikin su yadda na siyar na kawo musu kuɗin su haka zasu cafke batare da sun yi min ko godiya ba, ballantana na saka rai da abincin,idan kuwa ƙwandala ta ɓata a kuɗin ina cin mugun duka irin na rashin gata,wasu ma sai suyi ta rantsuwar sai na biya su Sutura kam idan aka ganni da ita to wasu bayin Allahn ne sukaji tausayi na suka bani kunce,tunda mahaifi na ya rasu ba'a sake yi min sabon ɗinki ba,nayi ƙanƙanta da yawa ballantana nayi tunanin ko da sana'a,Ni ba ƙawaye ko abokan wasa gareni ba,tallar da aka ƙaƙaba min shine aboki na,an sha kawo min farmakin lalata rayuwa ta amma Allah yana tsare Ni Shekaru na goma sha uku,a lokacin rayuwa tayi min ƙunci sosai, kullum aikin ɗaya ne na ɗauki talla na fita,a lokacin na fara dabarar idan yunwa ta ishe ni na sauke kwanonin abincin na rarrage a leda na samu wanda zanci,har na fara rarrage abincin ina siyarwa ina samun ɗan kuɗin kashewa batare da sanin masu ɗora min talla ba Ina da shekaru sha biyar muka haɗu da Najeeb,a lokacin sun zo garin nan aiki a wani asibiti, ciwon mara na al'ada ya riƙe Ni a hanyar dawowa ta daga siyar da dambun da nayi A yashe suka ganni a gefen hanya na dafe ciki ina murƙususu,gefe kuma kwanukan abincin da na siyar ne, Najeeb ne da kanshi ya ɗauke Ni ya saka Ni a Mota muka nufi asibitin da suka kawowa ziyara Da kanshi ya duba ni ya bani magunguna,da na dawo hayyacina sai na kasa zaman asibitin,nayi ta kuka sai da ya mayar dani gida Sai dai kafin muje gida ya biya ta shago ya siya min kayan ƙwalam da maƙulashe,da kayan shayi sannan ya bani kuɗin da ban taɓa ganin irin su ba yace na kashe matsalar gaba na Da farko na tsorata,har na ƙi amsa,amma da ya nuna min shi kawai taimako na yayi sai nayi ta masa godiya,na kwashi kayana na kai ɗaki sannan na mayarwa mai dambu kwanukan ta da kuɗin dambun ta Daga lokacin na daina talla,dama don abinda zanci ne nakeyi,yanzu kam wannan ya kau,amma ban koma makaranta ba,sai dai na kasa cire wannan saurayin da ya taimake ni a raina Kusan watanni biyu Najeeb ya dawo,nayi farin ciki sosai,amma sai ya tambaye Ni dalilin talla bana zuwa makaranta ban ɓoye masa komai ba na bashi labarin kaina,ya tausaya min sosai,yace to mai zai hana na bishi ya kaiwa umman shi ni?don bata da ƴa mace,kuma nima ina buƙatar kulawar uwa a shekaru na,sannan zai mayar dani makaranta Faɗar hakan da yayi yasa ko musu banyi ba na amince,washe gari babu wanda nayiwa sallama na biyo Najeeb muka nufi kano Babu laifi maman shi ta tarbe ni da kulawa,aka bani ɗakin da na ganni tamkar amarya, saboda kyan shi da tsaruwar shi A gidan su Najeeb na samu ƴanci sosai,abinda naso shi nake ci,sutura sai wadda na so zan saka,gashi kuma ya sanya Ni a tsadaddiyar makaranta,ya ɗaukar min lesson teacher Ban ɗauki lokaci ba nayi wani irin haske,nayi kyau sosai,sau tari haka Najeeb zai yi ta kallo na kamar wani wawa,wani sa'in har kunya yake bani Shekaru biyu da dawowa ta kano,babu wanda zai ganni yace na taɓa yin rayuwar ƙauye, amma kuma a kullum umarnin Najeeb nake bi,ya hana ni kula ƙawaye,sai Nadiya da aƙalla zata bani shekaru biyar zuwa sama, Nadiyan ce take haɗa ni da ƙawayen ta,ƴan gayu ne sosai, rayuwar su tana matukar burge ni Rana tsaka Najeeb yace nazo na raka shi unguwa,sai dai maimakon unguwa hotel ya nufa dani,anan yake gaya min manufar shi ta shekara da shekaru,na tsorata sosai,sai dai ya nuna min zaɓi biyu gare ni,ko dai na amince da buƙatar shi ya nuna hidimar da yake min,ko kuma naƙi amincewa ya mayar dani in da ya ɗauko Ni, hankali na ya tashi sosai,ba tsorata matuƙa da makircin Najeeb,yace ya bani nan da gobe na yanke shawara,ko na yarda dashi ko na koma gidanmu,daga nan bai jira komai ba ya ɗauko Ni ya dawo dani gida Nadiya na kira ina kuka nace don Allah tazo ina son ganin ta, Kasancewar duk wannan abin da akeyi Najeeb ya saka min doka mai tsanani,bana fita sai ya san in da zanje,don haka idan naso ganin Nadiya sai dai na kira ta,ita kuma babu ɓata lokaci tazo,yanzun ma haka akayi,cikin ƴan mintuna tazo Ɗaki na na ja ta cikin kuka na sanar mata yadda mukayi da Najeeb,ga mamaki na sai naga ta kwashe da dariya,tace"Ni wallahi har kin bani tsoro,yanzu akan wannan minor problem ɗin zaki wani tattago ni?to shikenan kar ki amince,sai ya mayar dake can ƙauyen,a banza za'a yi miki fyaɗe a yasar dake a titi a wulaƙance,kowa yana kallon ki a yatsine,amma idan kika amincewa Najeeb ko babu komai zaki ga tarairaya da kulawa, kuma cikin farin ciki zaki rayu" Cikin kuka nace"to me zai hana ya aure ni?idan yaso ko ma menene sai yayi dani"wani kallon rainin wayo Nadiya tayi min tace"lallai na yarda yarinta ke damun ki,Malama idan zaki saki jiki ki saki jiki,wanne aure kuma ana zaune ƙalau?ki bar wani batun aure har ki kammala makaranta,amma yanzu kiyi rayuwar ki"haka tayi ta min zuga tana kawo misalai har na yarda na amince"umaiman ta rufe fuskar da tafin hannun ta tana kuka mai soya rai, Afra ma kuka take har da shashsheƙa, Deeja ce dai kukan ya ɗauke sai ajiyar zuciya take saukewa,daidai nan aka tsuge da ruwan sama,da sauri Umaima ta miƙe ta saki asabarin ɗakin da windon ɗakin sannan ta koma ta zauna,sai da ta daidaita nutsuwar ta sannan ta cigaba "Washegari Najeeb yaje ɗauko ni daga makaranta,a hanya yake tambaya ta,me na yanke game da maganar jiya?a sanyaye nace masa na amince,sai naga fuskar shi ta faɗaɗa da murmushi,yaja hanci na yana min godiya A taƙaice dai,a ranar Dr Najeeb ya fara sani na ƴa mace,ya gama wulaƙanta rayuwa ta,amma ya kula dani sosai,ya tarairaye ni kamar sabuwar amarya,daga hotel ɗin da ya kai ni ya wuce dani ƙaton store ya siya min sababbin kaya da kayan kwalliya da kayan ƙwalam,ya sake min Sabuwar waya,ya kai ni tsadadden eatry yayi min order na favorite ɗi na, sannan ya mayar dani gida. Ni da ya kamata ace tun biyu da rabi ina gida ban koma ba sai biyar,amma umma ko uffan ba tace min ba, gani na cikin yanayin damuwa ma bai saka ta tambaye ni komai ba"Umaima ta kuma yin shiru tana share hawayen ta Bayan ƴan sakwanni ta cigaba"duk lokacin da ya kwanta dani yana bani wata ƙwaya, ashe ta hana ɗaukar ciki ce,tun ina jin tsoro ina ɗari-ɗari har na saki jiki,wani lokacin ma nice nake kai kaina gare shi, a haka muke kasance har tsawon shekaru biyu A lokacin ina da shekaru goma sha tara da haihuwa,a shekarar ne na gama secondary School ɗi na,kuma still a shekarar ne Najeeb ya jefa Ni a rayuwar Imran Da farko bai gaya min shirin shi akan Imran ba,nasan dai yana yawan kira na ko yace nayo girki kala kaza na kawo masa,sai da ya samo kan Imran yake shaida min so yake na aure shi Da farko ban so ba,amma Najeeb ya nuna min wannan itace mafita dole,da haka ya samu na sauko na fara kula Imran,kuma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Allah ya jarabce ni da son shi #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 35 Komai zanyi sai nayi shawara da Najeeb,da farko naso na auri Imran lokacin da ya aure ki na zauna lafiya da ke,ko babu komai zan samu sauƙi daga Najeeb,don har a lokacin bana ƙaunar yadda yake kwanciya dani,wani lokacin ma a ɗaki na musamman idan mahaifiyar shi bata nan Amma sai Najeeb yayi ya zuga Ni har naji nima na tsane ki,naji bana buƙatar zama da koma wacece wadda akace Imran ya aura Ban tashi sanin Najeeb shaiɗani bane sai da aka tashi auren mu da Imran,don zama na musamman yayi dani ya shaida min adadin kuɗaɗen da zan rinƙa tatso masa a hannun Imran,da kuma cewa har gobe duk sanda ya buƙace ni zan zo,na tsorata sosai, kuma na shawarci Nadiya, Nadiya ta nuna min ba wata matsala,kuma hakan ta kasance,duk sanda Najeeb ya neme Ni zan san dabarar da zanyi naje gare shi,gashi kuma har lokacin bai daina bani maganin hana ɗaukar ciki ba Deeja,abinda baki sani ba shine,bani ce naso Imran ya rabu dake ba,shima Imran bai so rabuwa da ke irin haka ba,duk shirin Najeeb ne,mafi girman laifin Imran shine bakin shi baya shiru, kullum a asibiti bashi da magana sai taki da irin ƙauna da sadaukarwar da kikayi masa,wannan shine dalilin da ya jefa tsanar ki a zuciyar Najeeb, Nadiya ma sai daga baya na gane ƙawar Najeeb ce, saboda tsanar da yayi miki ya tura ta rayuwar ki ta san yadda zatayi ta auri mijin ki Khalees don ta ƙuntata miki Da farko bansan hanyar wajen boka ba, Amma a sanadin Nadiya na sani,ba don kaina ba sai don buƙatun ta,a tsawon zama na da Imran ban taɓa kai shi wajen boka ba,amma Nadiya ta saka Ni na kai ki, na kai Khalees, na kai mahaifiyar shi da ƴan uwan shi Bayan Khalees ya sake ki kinyi ɓatan dabo Imran yazo ya tuhume ni,na nuna masa bansan zancen ba,duk da ina zargi biyu a lokacin, ko dai ke kika ɓoye kanki ko kuma Nadiya ta ɓatar dake,don na santa,hatsabibiya ce ta gaske A saboda haka naje gidan Nadiya,Amma sai ta nuna min babu ruwan ta da maganar,ƙarshe ma bamuyi rabuwar daɗi da ita ba,don a lokacin Imran yayi min abinda bai taɓa yi min ba saboda ke,wato mari Ina cikin wannan tashin hankalin ne Najeeb ya turawa Imran evidence ɗin abinda muke aikatawa, saboda ya neme ni naƙi bashi haɗin kai, daga nan kawai na saddaƙar aure na ya gama mutuwa,gashi Imran sai nanata min yake na nemo ki duk inda na kai ki Ina cikin wannan mugun halin tsawon kwana huɗu Imran ya zo da ƴan sanda suka kamani ina kukan tashin hankali,sai da suka kaini station naga Ashe har da Nadiya,wadda na firgita sosai da ganin ta yadda ta fice daga hayyacin ta,ƴan sandan nan babu tausayawa suka rinƙa gallaza mana don mu fito dake,amma amsa ɗaya muke nanata musu itace bamu san in da kike ba,kwanan mu shida a hannun su muna shan azaba iri-iri,ƴan uwan Nadiya sukayi bailing ɗin ta da ƙyar,a lokacin na ƙara kukan rashin dangi,don Ni dai nasan babu mai bailing ɗi na Ilai kuwa babu wanda yazo min,amma bayan kwana uku suka sake ni,kai tsaye gidan su Najeeb naje amma yayi min korar kare,dole na koma gidan Imran,amma tun a compound ya bani takarda ta yace na fice masa daga gida,nayi ta kuka ina roƙon shi kan bani da in da zan je,yace wannan bai dame shi ba,na fice masa daga gida,da yaga naƙi fita ya janyo Ni kamar bola ya jefar dani sannan ya gargaɗi mai gadin kar ya kuma bari na na shiga Ban daddara ba naje gidan fauwaz,amma abinda Imran yayi min nafila ne,don shi sakawa yayi mai gadin nashi kore ni da bulala,na koma bakin gate ɗin gidan Imran na raɓe,ga dare,ga yanayin sanyi,ga sauro,haka na kwana har asuba,da ya fito zashi sallar asuba ya ganni ranshi ya ɓaci,Ni kuma na fashe da kuka don a lokacin bansan yadda zanyi ba,ya tsallake Ni yayi tafiyar shi masallaci,to bayan ya dawo ne da ya shiga gida ya fito da kuɗi a envelope ya bani yace yayi min iya abinda zai iya,na fita daga rayuwar shi ko ya wulaƙanta ni,nayi ta roƙon shi ya yafe min,amma magana ɗaya yake nanata min,baya son sake gani na a rayuwar shi Da kuɗin da ya bani nayi kuɗin mota na dawo garin mu taura,yadda na tafi ba'a sani ba hakanan babu wanda ya damuwa da dawowa ta,na buɗe ɗakin mahaifiya ta na gyara na shiga,nayi ga jinyar kaina tsawon sati ɗaya Bayan na dawo dai-dai nayi amfani da kuɗin wajen Imran na saro kayan miya da omo da sabulu na fara siyarwa,amma saboda rashin kasuwa yasa na fara fita bakin kasuwa na kasa kayan na siyar,idan nayi ciniki na sayi abinda zan ci,idan banyi ba ciniki ba na zauna da yunwa,don na gwammaci yunwa akan baƙar rayuwar da Najeeb ya jefa Ni a baya,don nayi alƙawarin bazan sake ba Bayan watanni biyu na fara yawaitar ciwon kai,da kai amai,alamomin ciki masu yawa suka bayyana a tare dani,har a lokacin ban wani gane ba, kasancewar bani da wannan wayewar Sam ban fahimci ciki gare Ni ba sai da naga ƴan gidan mu suna nuna ni,daga karshe dai wata matar ƙanin baba na tazo ta zage Ni da gori,wai naje nayi karuwanci nazo zan haifa musu shege Tabbas na tsorata da jin ina da ciki,ba don komai ba sai don bani da ƙarfin gwiwar tunkarar Imran,don dai nasan ba na Najeeb bane,don na kai watanni biyar inayi masa hanya-hanya idan ya neme ni, saboda all of a sudden kawai naji na gaji da rayuwar dabbobin da mukeyi Nayi laulayi sosai,don sai da ta kai bana iya fita sana'a ta,amma ƴan gidan mu babu mai zuwa inda nake Sai da ciki na ya shiga wata na biyar sannan na samu sauƙin laulayi,na cigaba da sana'a ta,haka zan ɗauki kaya,ga nauyin ciki,kuma ko sau ɗaya ban taɓa tunanin zuwa awo ba Sai da ciki na yayi wata takwas sannan wata dattijuwa maƙwabciyar mu,tace na daina fita zata ɗauki abinci na,nayi ta mata godiya Ai kuwa ta cika alƙawari,don safe, rana,dare sai ta aiko min da abinci,in da na godewa Allah cikinnawa ba mai tsirfa bane,komai na samu ci nakeyi. Ciki na yana cika lokacin haihuwa na fara yawan ciwon mara akai akai,sai nayi zaton haihuwa ce sai kuma abu ya lafa,sai da nayi kwana tara a haka sannan na fara naƙudar gasken Na sha wahala sosai,don sai da na fara tunanin ko mutuwa zanyi,amma saboda taurin kai yadda ƴan gidan basu nemi taimaka min ba nima ban nemi taimakon su ba,da dai naga ciwo ya ƙi ci yaƙi cinyewa sai na faki idanun su na kira wani yaro nace ya kira min dattijuwar da ke aiko min abinci Inna laraba,ai kuwa bata juma da zuwa ba na haihu Tsawon kwanaki bakwai inna itace ke shigowa tayi min wanka ta wanke jaririya,ɗan ta ta sanya yayiwa yarinyar huɗuba,da aka tambaye Ni suna ke kika zo min rai,don haka nace a sanya mata Khadijah Inna laraba ta kula dani har nayi kwana talatin da biyar,a lokacin na cigaba da fita sana'a ta Saboda kula da little Deeja Yanzu watannin Deeja ƙarama huɗu da haihuwa, Allah ya rufa min asiri da ƴar sana'a ta bana rasa ci ko sha,sannan bana fashin yi miki addu'ar Allah ya bayyana ki ya tsare ki a duk inda kike Rabo na da karatun addini tun bayan rasuwar mahaifi na babu jumawa,don haka lokacin da aka buɗe wata makarantar matan aure banji ƙyashin shiga ba,a lokacin Deeja watannin ta biyu da haihuwa A haka nake rayuwa har zuwa yau,ko da bana farin ciki amma bana cikin baƙin ciki,kuma ina zaune lafiya da Ni da ƴar jaririya ta Wannan shine labari na Deeja,haƙiƙa ni ɗin mai kuskure ce,amma kuma na kasa gane wanene silar hakan,mahaifi na da ya kasa mayar da raino na wajen dangin mahaifiya ta,ko dangin mahaifiya ta da suka kasa nema na tsawon shekaru,gashi ni bazan iya kai kaina gare su ba,ko dangin mahaifi na da basu mayar dani dangin uwa ta ba bayan sun san ba riƙe Ni zasuyi ba,ko ma dai menene, alhamdulillahi,na godewa Allah da ya nufe ni da shiriya tun kafin lokaci ya ƙure min" Menene ra'ayin ku game da labarin Deeja da na Umaima?wannene yafi ban tausayi kuma yafi Zama matsala a cikin al'ummar mu?sai naga ra'ayoyin ku a comment section, Allah ya barmu tare MATAR KHALEES fans 🥰 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 36 Shiru ɗakin ya ɗauka na wasu ƴan mintuna bayan gama labarin Umaima,bakajin komai sai shashsheƙar kukan Afra da Umaima,da ajiyar zuciyar Deeja,kiran sallar la'asar ne da akayi ne ya sanya Umaima miƙewa tana goge kumburarrun idanun ta,a lokacin ruwan yayi sauƙi,ta ɗauki ƴar butar ta guda ɗaya ta zuba ruwa a ciki tace"gashi ku fara yin alwala,akwai makewayi idan kuna buƙatar shiga"Afra ta miƙe ta ɗauki butar batare da tace uffan ba,don har yanzu kuka takeyi Ita kam Deeja har yanzu idanun ta suna kan little Deeja da ke kwance a jikin ta tana shan baccin ta cikin kwanciyar hankali,ko alamun hawaye babu a idanun ta,amma a zuciyar ta ji takeyi da zata samu tayi hawayen da taji sauƙin raɗaɗi da ciwon da takeji,ta juma bata ji tashin hankali irin wannan ba,shiyasa bahausheyace kai dai kaga mutum,amma bakasan yaya yake gudanar da rayuwar shi ba,baka san kalubalen da yake fuskanta ba, lallai rashin uzuri a rayuwa babbar masifa ce Afra ce tayi sallama ta shigo tana duban Deeja tace"kije kiyi alwalar Deeja,nayi"sai a sannan Deeja ta kwantar da little Deeja ta miƙe cikin mutuwar jiki ta fice daga ɗakin Umaima ma ficewa tayi Afra kuma ta tayar da sallah Bayan sun idar da sallah ma zama sukayi jugum jugum kowa da tunanin da takeyi,don ma ita Umaima ta ji sauƙin nauyin da ke zuciyar ta,a ƙalla tayi magana da waɗanda ta san sun fahimci halin da take ciki,basu daɗe da idar.da sallah ba ruwa ya dawo kamar da bakin ƙwarya,cikin sanyin murya Deeja ta kalli Afra tace"Afra anya kuwa zai yiwu mu koma yau?"kafin Afra tayi magana Umaima tace"mai zai hana ku kwana anan?kunga yadda akayi ruwa hanyar ba lallai tayi daɗin tafiya ba"Afra ta kalli Deeja don jin me zata ce,cikin sanyin murya tace"to Allah ya kaimu goben" Sosai fara'a ta bayyana a fuskar Umaima,taji daɗi sosai,ko babu komai dai yau ɗaya zata sake da wasu mutane da ta sani a rayuwar ta,cikin murna tace ameen ya Allah"su dai su Deeja sai kallon ta sukeyi cike da tausayawa Deeja ta kalli Umaima da ke chanjawa little Deeja kaya tace"yanzu Umaima idan Allah ya fito miki da miji zakiyi aure?" Umaima tace"ƙwarai kuwa,bayan haihuwa ta wani abokin ƙanin baba na ya nemi aure na,da farko har na amince masa,har Wajen sana'a ta ƴaƴan shi sukaje sukayi min rotse suka watsa min kaya na suna faɗin uban su bazai auri karuwa mai ƴar shege ba, dalilin haka na tsorata na sallame shi" Daga Afra har Deeja sakin baki sukayi suna kallon ta da mamaki, Deeja tace"saki nawa Imran yayi miki?" "Saki ɗaya ne,takardar ma tana nan har yanzu" "To shine kike tunanin auren wani bayan Imran?"a cewar Deeja tana kallon ta Daga Umaima har Afra a firgice suka kalli Deeja, Umaima cikin in Ina tace"I....I... Imran kuma?...yace baya son gani na fa,yace ba fita a rayuwar shi, kuma kema ba sai na gaya miki ba kin san Imran yafi karfi na yanzu"Deeja bata sake magana ba ta amshi little Deeja da take ta kallon ta,don ruwan da akayi da sakin asabarin da Umaima tayi yasa ɗakin yayi duhu,sai Deeja ta kunna torch da ke jikin power bank ɗin ta,ta haske ɗakin tarwai Murmushi tayi tana kallon ta, itama yarinyar kamar ta sani ta fara ɓangale baki tana dariya, Deeja ta shagala tana mata wasa,dama ita fa tun ganin ta da babyn a farko ta shiga ranta Umaima ce ta miƙe tsaye tana ɗaukan hijabin da tayi Sallah bayan ruwan ya tsaya,tace"bari naje nayo cefanen girkin dare,biyar ta gota yanzu"itama Deeja ta miƙe tana faɗin"nima dama ina son zaga garin,mu je, Afra ke kam nasan bakya jure wahala zauna ki jira mu" Afra ta kalli Deeja tana ƴar dariya tace"ai kuwa sai naje,idan na gagara ai kuna da ƙarfin goyo ni"sukayi dariya su duka,Afra ta miƙe ta ɗauki mayafin ta, Deeja ta goya little Deeja, ta kalli Umaima tace"da me za'a lulluɓe ta saboda sanyi?"Umaima ta ɗauko ɗankwalin atamfar ta ta miƙawa Deeja, Deeja tace"wannan ai bazai yi ba,akwai showel ɗin Affan a mota,bari nayi amfanin dashi" "Ni kam zan ce yayi yawa ma ban tambaye shi ba,banga kinzo dashi ba"a cewar Umaima "Yana wajen ubanshi,da yake na yaye shi"ta ƙarasa faɗa tana ficewa daga ɗakin,su Umaima suka biyo bayan ta A bakin motar ta suka same ta tana ƙulle showel ɗin da ta ɗauko,sosai take tausayin yaran saboda bata da wasu kaya masu yawa,hulunan ta guda biyu ne kacal,kuma su ma ba masu kauri ba,rigar sanyin ta guda ɗaya ce,ta dubi umaima tace"muje kasuwa kawai,akwai abinda nake son siya"babu musu suka wuce kasuwar a ƙafa,don babu nisa Suna shiga kuwa sukayi Sa'ar ganin shagon kayan sakawa na manya da na yara,kai tsaye Deeja ta nufi can ta siyo kayan jarirai da diapers masu yawan gaske,sannan ta siyo dogayen riguna da undies sannan suka fito,cefane sukayi mai kyau,duk yadda Umaima ta so biyan kuɗin Deeja bata saurare ta ba ta biya,suka ɗebo kaya niƙi-niƙi sukayo gida Shinkafa jollof da kifi Umaima ta dafa musu, sai haɗiyar yawu takeyi don zata iya cewa rabon ta da kifi ta manta,bayan ta gama ta ɗora ruwan wankan little Deeja a ɗan murhun Bayan Isha'i bayan sun gama cin abinci Deeja tayiwa little Deeja wanka ta sanya mata ɗaya daga cikin sababbin kayan sanyin da ta siyo mata ɗazu har da hula da safa,ɗan ƙaramin baby net ɗin da ta siyo ta buɗe ta sanya ta a ciki,don dama ƴar ƙarama ce sosai,watan ta huɗu amma ko wata ƴar wata biyun ta fita girma, Deeja ta lulluɓe ta tana tapping bayan ta a hankali har bacci ya ɗauke ta,tayi mata addu'a ta tofe tada ita ta mayar da net ɗin ta rufe ta ɗago tana kallon su Afra da Umaima da suka zuba mata idanu suna kallon ta Murmushi tayi tace"ina matuƙar son ƴa mace,amma na godewa Allah da ya bani namijin ma,yanzu gashi na kuma samun macen"Umaima tana murmushi tace"idan zaku tafi ki tafi da ita na bar miki,nasan zatafi samun ingantacciyar rayuwa a hannun ki fiye da hannu na"Deeja tayi murmushi kawai "Bayan wasu mintuna Deeja ta kalli Umaima ta fara magana cikin kwantar da murya"Umaima,da ace Imran baya buƙatar ki a rayuwar shi da saki uku zai yi Miki kamar yadda yayi min,ranshi ya ɓaci ne,amma har yanzu yana sob ki,irin soyayyar da Imran yayi miki I don't think it can be vanish a dare ɗaya,sannan ki goge dukkan abinda ya faru,ki ɗauka irin taki kaddarar kenan,baki san abinda Allah ya rubuta miki ba,don haka gobe tare dake zamu koma,akwai sabuwar rayuwar da take jiran ki a Kano,da ke da takwara ta" Umaima ta girgiza kai tace"Deeja ki barni kawai na cigaba da rayuwa ta anan,bani da inda yafi nan" "Wannan ba mai yiyuwa bane Umaima,ko kinji daɗin rayuwar da kikayi har haka da kike fatan ta wa ƴarki?ko kinsan abinda zai faru gobe?so kike itama ta tashi tana jin haushin ki kamar yadda kike jin haushin magabatan ki?" A sanyaye umaima ta girgiza kai tace"a'a, idan zaku tafi ku tafi da ita,ku tambayi baban ta idan yana so sai ku bashi,idan baya so kuma na bar miki" Duk da cewa jikin su a sanyaye yake sai da suka kama dariya, Deeja tace"umaima akan takwara ta nake magana fa,ba jaka ko ɗan kunnen ki ba"Umaima ta wara idanu tace"na sani mana,nima akanta nake magana"suka ƙara fashewa da dariya, Afra har da riƙe ciki, Deeja tace"lallai na yarda da abinda ake cewa akan ɗan fari,amma a hakan kuke cewa kun fi mu wayo"itama Umaima dariya tayi tace"kema kinsan ƴan fari sun fi auta wayo"Deeja tace"ga evidence na gani"daga nan suka shiga tsokanar juna suna dariya,soon ta manta da damuwar da take ciki Washegari da safe Deeja ta kalli Umaima fuskar ta babu wasa tace"Umaima ki haɗa dukkan ababen ki masu muhimmanci,zamu wuce Kano in less than one hour" Kallon ta Umaima tayi,zatayi abinda ta saba wato musu,amma ganin yadda Deeja ta ɗaure fuska alamar ba wasa sai tayi shiru,a sanyaye ta janyo jakar Ghana must go ɗin ta ta fara jera kayayyakin ta, wadanda duk yawanci na little Deeja ne,Afra ta taimaka mata, Deeja kuma ta shirya little Deeja ta goya ta Bayan sunyi wanka Deeja ta fito da dogayen rigunan da ta siyo,ta ɗauki ɗaya ta basu ɗaiɗaya,ta Deeja light blue,tayi mata kyau sosai,ta hau sosai da chaculate skin ɗin ta,ta Afra blue Black ce, kasancewar tafi Deeja haske itama Tata tayi mata kyau,ta Umaima maroon colour,Wai don ma yau da taɓa ta fatar tayi ɗan duhu,amma da yake kyan na nan da ta shirya sai gata ta fito a umaiman Imran ɗin ta, Afra tace"awwwn!naga manyan mata anan", Deeja tayi murmushi tace"dama kyan akwai wanda aka adanawa na Musamman,sai yanzu zai bayyana"Umaima tayi murmushi tana girgiza kai tana ƙoƙarin ɗaure dogon gashin ta Yau da shagali🤗 Deejan Khalees da umaiman Imran sun haɗe kai sun bar mu🥺oho dai mu ma biye muku zamuyi mu haɗe kai🙈 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 37 Wajen ƙarfe goma na safe suka fito don tafiya gida,babu yadda Deeja batayi da Umaima ba tayiwa mutanen gidan sallama ba amma taƙi,da ta matsa mata ma kuka ta fashe mata dashi,sai kawai ta ƙyale ta,ta saɓa little Deeja a kafaɗa,wadda tayiwa kwalliya da overral ta ɗora mata doguwar riga mai kyau da hula har da Safa,ta lulluɓe ta da sabon showel,fari tas sai ɗaukan idanu yake Tafiyar awanni uku da rabi ya kawo su kano,kai tsaye ƙaton shopping mall suka nufa,anan su Afra suka ga yadda ake haukar siyayya,ashe ba komai Deeja tayi a taura ba,don sai ta ta cika Boot taf da kayan little Deeja masu tsada,da kayan wasa,na Umaima da ta siya a backseat ta zuba su,ta fara biyawa gidan fauwaz ta sauke Afra sannan ta ɗauki hanyar gidan ta na Na'ibawa A falo suka zube suna hutawa, Umaima sai kallon gidan takeyi don ya burge ta sosai,Deeja ta miƙe ta shiga kitchen ta samo musu drink ta zubo akan ɗan plate da glass cup ta kawo ta zuzzuba musu a cup Suna sipping a hankali Deeja ta kalli Umaima tace "Nan gida na ne,zaki zauna anan,duk abinda kike buƙata zan saka a kawo,ranar asabar idan Allah ya nuna mana zan kawo miki wadda zata taya ki zama da aikace-aikace,that same day kuma zan kai ki islamiyya ki cigaba da karatun kina addini,ranar Monday kuma in Sha Allah zan kai ki don kiyi registration na JAMB" Umaima ta buɗe baki da zummar yin magana kuka ya kubce mata,cikin kuka ta fara magana "Deeja ban san da me zan biya ki ba,haƙiƙa a dukkan rayuwa ta babu wanda yayi min rana ya sanya na ji Ni a mutum kamar ki,na gode Allah ya saka miki da mafificin alkhairi" Ta sauko daga kan kujerar da take zauneta durƙusa ta kama ƙafafun Deeja,wadda tayi shiru kawai tana kallon ta,tace "Don girman Allah Deeja ina roƙon ki ki yafe min abinda nayi miki,don Allah ki roƙar min yafiyar Imran da duk wanda na cutar,na...."Deeja ta toshe mata baki tana girgiza kai cikin ɗaure fuska tace"indai kin san idan nazo kuka zaki rinƙa yi min gwara ki gaya min kar na sake wahalar da kaina na dawo"da sauri ta share hawayen ta tace"na daina in Sha Allah"Deeja ta ɗan yi murmushi ta dafa kafaɗar ta tace"don Allah ina so ki manta da duk abinda ya faru a baya kiyi facing new life ɗinki,ki ɗauke ni a matsayin yayar ki da kuka fito ciki ɗaya,wadda a kowane hali sai dai ta ƙaurace miki na ɗan lokaci,amma bazata guje ki ba,don haka ki kwantar da hankalin ki ki manta da baya,ki goge shi a ranki,you are starting a new life,wadda a cikin ta babu Najeeb,babu Nadiya,babu talla,babu ƙuncin rayuwa,babu kaɗaici da kewa,in Sha Allah very soon komai zai wuce"tana gama magana tayi mata side hug ta miƙe ta ta ƙarasa kan two sitter da ta kwantar da little Deeja, yarinyar sai kallon juyawar fanka takeyi tana ƴan wasannin ta,babban ɗan yatsan hannun ta ta zurmuƙa shi a baki, Deeja ya durƙusa tana shafa fuskar ta tana murmushi tace"to Angel,zan tafi,i will miss you so much, much luv sweetheart"tayi kissing ɗin ta a goshi da kumatu,sai wulla ƙafa takeyi tana dariya, Deeja ta waiga ta kalli Umaima tana murmushi tace"to maman takwara,sai Saturday"bata jira amsar ta ba tayi sauri ta fice ganin umaiman tayi wani irin sanyi Ai kuwa ranar asabar ɗin Deeja ta dawo da wata mace dattijuwa,zata kai 47-48 years, sannan ta ɗauki umaima suka je wata makarantar matan aure,ta gama mata komai suka dawo gida A ranar ta sa aka ƙaro kayan abinci masu yawa,sannan ta bawa Umaima tsadaddiyar waya da makullin tsadaddiyar mota, Umaima bata taɓa tsammanin zata sake tuƙa mota a rayuwar ta ba,duk yadda taso kar tayi kuka ta kasa sai da ta fashe da kuka tana rungume Deeja ta kasa magana, Deeja na goge mata hawayen tace"ki shirya jibi zakiyi registration ɗin JAMB" Umaima ta ƙara goge hawayen ta tace"amma lokaci bai ƙure min ba kuwa?ina nufin a karatun" Deeja tace"shekarun ki nawa?"Umaima tace"I'm turning 25 next month"wani kallo Deeja tayi mata tace"dudud nawa kike,har ƴan 60 years ma karatu sukeyi ballantana ke haihuwar kwanan nan,c'mon malama ki koma makaranta,don wannan karatun shine best pride ɗin ki,kar ki kuskura kiyi wasa da opportunity ɗinki na karatu"Umaima ta gyaɗa kai cikin sanyin jiki ta kama hannun Deeja tace"na gode sosai, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"Deeja bata daɗe sosai ba tayiwa umaima sallama ta tafi bayan ta gama wasa da takwarar ta,amma ta dawo ranar Litinin,a motar umaiman suka je sukayi registration na JAMB Satin Umaima uku a Kano aka mayar da auren Deeja da Khalees, Deeja ta zama MATAR KHALEES a karo na biyu,ita da Khalees cike suke da farin ciki don wannan shine auren su na farin ciki a iya tsawon rayuwarsu,an sha shagali sosai,su Mima suka miƙa ta sabon gidan mijin ta da ya siya a state road Satin su biyu da aure suna shan soyayyar su Aunty nusaiba ta dawo musu da Affan,mijin ta da yazo ya saka su gaba ita da yaran ta suka koma US, Deeja tayi kewar su sosai Watan ta uku da aure tana zaune a parlourn ta tana duba wasu files da zatayi submitting gobe a Company ɗin su,don tuni ta koma companyn su ta cigaba da aiki Ji tayi an rungume ta ta baya,ta san Khalees ne,ta ɗan yi murmushi tana faɗin"sannu dai yallaɓai,ya kamata a rinƙa sallama dai" "Ke fa ba'a razana ki,na manta"ya faɗa yana dungure mata kai" "Akan me za'a razana ni?ka san dai na fika juriya ko?"ta faɗa tana murmushi gami da kashe ido ɗaya Murmushi yayi yana faɗin"to anji"ya dauko hijabin ta da ke gefen ta ya fara ƙoƙarin saka mata,ta kalle shi don neman ƙarin bayani,ya raɗa mata a kunne"we have a visitor, very best friend"karɓar hijabin tayi ta ƙarasa sakawa,shi kuma ya fita ya shigo da baƙon Mamaki ya kamata ganin Imran,wanda rabon ta da shi ma tun ranar da ta sauka ƙasar ita da su Aunty nusaiba,Amma bata nuna masa komai ba a fuska tayi masa sannu da zuwa,ya amsa da fara'a ya zauna suka gaisa a mutunce,yanayiwa Affan wasa Deeja ta kawo musu soft drinks sannan ta samu waje ta zauna,Imran yayi ɗan murmushi yana faɗin"thanks"sannan ya zuba lemon a kofi ya fara sipping a hankali Ya dubi Deeja cikin sanyin murya yace"Khadijah,zuwa nayi na musamman don neman afuwar inconveniences ɗin mu, I know we did alot to you that I'm sure you will never forget with it,can you find a place in your heart to forgive us please?I regret my evil act definitely and.......wasu abubuwan barin faɗar su inaga yafi amfani,ina roƙon ki yafe mana Ni da Umaima,duk da cewa zuwa yanzu Ni kaina ban san inda take ba" "I can't get baka san in da umaima take ba"ta faɗa tana kallon shi "Mun rabu ai" "Na san da haka"shiru yayi yana kallon ta don bai gane abinda take nufi ba Murmushi yayi tayi tace"duk abinda ya faru ya wuce, abinda baka son faɗa min ma na sani, kuskuren ka baka iya dogon nazari kafin ka aikata abu,da ace kana dogon nazari babu yadda za'a yi Najeeb ya rinƙa juya rayuwar ka har ma da ta matar ka,kuma na biyu,meyasa zaka kori Umaima?ina ce ta gaya maka bata da wajen zuwa? meyasa baka saurari uzurin ta ba,to ka sani duk wani hali da Umaima ta shiga bayan barin ta gidan ka kaine sila" Mamaki mai tsanani ya ƙamar da Imran,kenan dama Deeja ta san Najeeb ke juya rayuwar su?ya akayi ta san cewa Umaima ba ƙanwar Najeeb bace,amma sai yace"babu abinda nayi Deeja,of course bana buƙatar ta a rayuwa ta anymore,tace zata koma garin su,na bata kuɗin da na tabbatar zai ishe ta kuɗin mota?idan ita marainiya ce bata da iyaye bata da family ne?idan har da gaske take why not ta koma wajen su?me zanyi mata after that? openly ta ci amana ta da aboki na, shiyasa naga gwara na bar masa ita, seems like bata shirya wa zaman aure ba,sai suje su cigaba da abinda sukeyi kawai"daga yadda yake maganar kaɗai ya isa a gane irin raɗaɗin da yake ji a zuciyar shi Deeja tace"shine kuskuren da ka tafka Dr,baka san wacece umaima ba,baka san komai daga gare ta ba amma ɗauki zafi daita,ba sai na gaya maka ba,ka san na san yadda Umaima take mutuwar son ka,yadda take son ka haka take gudun ɓacin ranka,kasan da haka ko?" Imran ya ɗan yi shiru in confusion yana kallon ta,shi dai Khalees kallon su kawai yakeyi,bayan wasu ƴan seconds yace"what are trying to say Khadija?" Wayar ta ta ciro babu ɓata lokaci ta nemo wani hoto ta miƙa masa,ya amsa yana kallo,kallo ɗaya yayiwa hoton gaban shi ya faɗi,shima Khalees kallon babyn yakeyi,da ya kalle ta sai ya kalli Imran,tana zaune akayi mata hoton,sanye take da farar dogon riga mai adon pink flowers,kanta an sanya mata pink ɗin bandana,gashin ta irin na larabawa anyi masa style mai kyau da kayan kitso masu ɗaukar hankali,tana rike da abin wasa tana kallon wani wajen ta ɓangale baki haƙoran ta guda biyu sun fito, Imran ya tsurawa yarinyar idanu ko kiftawa baya yi, Khalees ya ɗago ya kalli Deeja yace"baby luv wannan babyn fa? resemblance ɗin su da Imran is too obvious" Batare da ɓata lokaci ba tace"ƴar shi ce"a tare suka zaro idanu suna kallon ta a firgice, Deeja tace"yeah, Umaima ta tafi garin su da cikin ka kuma alhamdulillahi ta haihu lafiya,an samu yarinya ta saka mata suna na"ta ƙarashe tana murmushi,daga nan ta basu labarin Umaima,ta ƙara sa cewa"yanzu haka na ɗauko ta,tana nan gida na na Na'ibawa,yanzu zancen da nake ma ta koma makaranta,don na tabbatar da ace Najeeb a hanyar makaranta yaga tayi collapse da bai isa ya wulaƙanta rayuwar ta har haka ba,kuma duk da cewar Mima ta fara min takwara nafi jin na Umaima a raina" Dukan su shiru sukayi na ƴan daƙiƙu cike da tausayin Umaima,Imran ne yayi gyara murya ya fara magana cikin sanyin murya"ban san komai dangane da rayuwar ta,bata taɓa bani labarin rayuwar ta ba,na ganta tana rayuwar ta comfortably,da farko nayi tsammanin Najeeb yayan ta ne,na shiga shock sosai lokacin da ya tura min hotunan su da videos ɗin su suna baɗalar su,har da ce min gudowa tayi daga garin su ta biyo shi,wai kuma lokacin da zata aure ni tayi masa alƙawarin duk runtsi bazata guje shi ba,amma babu komai,na yafe masa,don yanzu haka fama yake da kanshi,yanzu dai ina rokon ki ki taimaka ki shawo min kan Umaima,tunda kuka fara haka da ita mawuyaci ne ta dawo min, because Umaima is too stubborn"dariyar babu shiri ta ƙwacewa Deeja,tace"wallahi kuwa akwai ta da taurin kai na bala'i ma kuwa,batayiwa ƴan gidan su magana fa,ranar da muka taho fa don na matsa mata ta shiga tayi wa ƴan uwan ta sallama sai ta fashe min da kuka" Imran yayi murmushi mai sauti yace"of course naji daɗin zama da umaima but ta cika kafiya da taurin kai, shiyasa lokacin da kika ɓace nace tasan in da kike,kuma na matsa mata ta fito dake" Tunda dai ƴan adawar Umaima suka shirya daita nasan zasu shirya da likita bokan turai,ina nufin jidda da Juliet 😅 Proud of you commentors and likers🥰 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Post 38 Deeja tayi murmushi tace"zanyi maka ƙoƙari in Sha Allah,duk da stubbornness ɗin ta tana jin magana ta, a matsayi na na babbar yaya Wani kallo sukayi mata duka su biyun, sannan suka fashe da dariya a tare,buɗa ido tayi sosai tana musu kallon ƙarin bayani, Khalees yana dariya yace"karo na farko a tsawon rayuwa ta da naga babbar yaya da auta sun haɗu waje ɗaya"kawar da kai tayi tana ɗan murmushi,ita fa a tsawon rayuwar ta dama ba wai tana ƙaunar sunan bane,amma bata taɓa jin sunan ya yarfa ta irin yau ba,amma saboda ƙi faɗi sai ta kalli Khalees tace"ai suna ne kawai,a family Mutum nawa na girma?ko baku san ina da ƙani ya rasu ba?idan Dr baka sani ba ai shi abban Affan ya sani"Khalees yana dariya yace"anyi haka,kin girmi mutane na manta,kamar yasmin,kin girmi fadila,kin girmi Mima,kin girmi Mubarak,kin......" "Aa Ni fa ban ce na girme su ba,kunga a bar maganar kawai"ta faɗa tana shan mur Imran yace"Hajiya Deeja kenan,ko bayan shekaru ɗari kaga mutum ka tambaye shi komai amma banda halin shi,ke kam Allah yayi miki arzikin son girma sai gashi kin zo a kalen hanji" "Naji nace a bar maganar"ta faɗa tana zaro idanu"zanyi magana da umaima,zata dawo in Sha Allah" "Kiyi mata barazanar yace idan bata amince ba zai amshi ƴar shi"a cewar Khalees yana murmushi, Deeja tace"wa?umaiman?ita da tace na ɗauki yarinyar ta bar mini?amma idan baban ta yana so sai na bashi,tun ma lokacin ko zama batayi,"Imran yayi dariya yace"shiririta!baka san Umaima bane idan ta kafe akan abu,nayi mamakin yadda ta yarda ta biyo Deeja, gaskiya kinyi Sa'a,ko kuma yet she is feeling guilty na abubuwan da tayi miki ne"Deeja tace"whatever,sannan akwai abu ɗaya da nake roƙon ka Please" Yace"ina jin ki"Deeja tace"ka koma Bauchi ka daidaita da mahaifin ka, it's already time,ko ba komai ka san abinda ya faru ba laifin shi bane,no matter what bazai taɓa juya maka baya ba,kuma for now ka bashi enough space, kusan six years,why not baza kayi letting komai ya wuce ba? I know yadda bai san Aunty Ramlah ba dole zaiyi kewar ka as the only son da ya mallaka"ta ƙarashe tana tsare shi da idanu Da Imran da Khalees duk kallon ta sukeyi har ta ƙarasa bayani,a hankali Khalees ya mayar da kallon shi ga Imran da ya sunkuyar da kanshi yana tuna baya, Khalees ya dafa kafadar shi yace"all is well friend, Deeja tana da gaskiya, ba'a fushi da iyaye no matter what happen,I know you well friend,nasan ba fushi kayi ba but it's already time ka nemi sasanci da dady,You will never regret it in Sha Allah"Imran ya jinjina kanshi,a sanyaye yayiwa Deeja godiya sosai,yayi mata sallama suka fice shi da Khalees,ya ɗauki Affan da yake ta ƴan wasannin shi suka fita tare Sati biyu tsakani Deeja, Afra,lubaisa da zakiyya suka ziyarci Umaima a motar Deeja,tana parlour ta goya little Deeja da ke jin rigima sai zaga parlourn takeyi,ta kunna suratul Nur a waya sai bi takeyi,ita kuma mama lami tana kitchen tana dafa musu abincin dare,sai jin sallamar su tayi Da sauri ta leƙo,tana ganin Deeja ta tafi da gudu ta rungume ta tana dariya,duk da cewa kiyya ta san labarin komai amma tayi mamakin chanjin da ta gani a wajen umaiman,gashi yanzu asalin farin ta ya dawo,tayi fes da ita, dama umaima akwai gayu da iya kwalliya, yanzun ma tana sanye da English wears riga da wando pink colour,ta ɗauke gashin ta da baƙin ribbom. Afra tana kallon ta tace"lallai umaima!wato mu duk baki ganmu ba ko?"da sauri ta saki Deeja ta rungume su ɗaya bayan ɗaya tana murmushi,ta ja su suka shiga parlourn, kiyya ta amshi little Deeja tana kallon ta Nan da nan ta kawo musu drinks da snacks tana faɗin"yau anyi surprising ɗina"lubaisa tace"sistern ki ce ta tattago mu"Umaima tayi murmushi ta kalli Deeja da take danna waya tana murmushi itama, kiyya tace"Ni kam ban ma san sanda aka tambayi abban su ba,sai ce min yayi wai khadija tace zamu fita"Afra tana dariya tace"ballantana kuma abban haneef,jira yakeyi auta tace ayi yace an gama"da tsokana ta faɗa tasan Deeja bata ƙaunar,ai kuwa ta ɗago ta zabga mata harara,duk suka kama dariya Sun ɗan taɓa hira da raha, Deeja ta tambaye ta game da karatu,cikin zumuɗi take sanar mata da cigaban da ta samu,yanzu haka tayi wajen izu ashirin da biyar,ga litattafai na addini,game da institution kuwata fara lecture a MAAUN in da take karantar business administration,su kansu su Afra ba ƙaramin burge su Deeja tayi ba,a hankali Deeja ta shigo da maganar Imran Ɗif umaima tayi bata sake magana ba,suka haɗu suna ta roƙon ta ta koma, Afra tana murmushi tace"nayi missing ɗinki sosai sister,gidanmu ma yayi missing ɗinki,kuma Dr ma yayi missing ɗinki sosai"Deeja tace"kuma ko ba don shi ba ki taimaka ki koma don takwara ta,she will be very happy ace ta tashi gaban iyayen ta duka biyun,sai ta fi jin dadin tarairayar da zaku mata"kiyya tace"seriously Umaima ko da nasan da Bama shiri ranar da Imran ya sake ki da abban su Aisar ya sanar min komai game da ke banyi bacci ba,I wish kin koma ɗakin ki,mu haɗa kanmu gaba ɗaya"ta ƙarashe tana murmushi, lubaisa ma tace"indai kika ƙi komawa Dr Imran to daga yau na daina yarda da love,indai naku ya mutu to I'm very sure namu Ni da ya abdallah yana mutuary"sukayi ƴar dariya,cikin sanyin murya Umaima tace"zan koma,ko don yarinya ta,i still remember Imran yayi min komai"shewa suka saka dukan su kamar ƙananan yara suna tafi Baayi cikakken wata guda ba aka mayar da auren Umaima da Imran,har taura Imran yaje ya nemi auren ta,bayan sati uku kuma ya mayar da ita can ya sasanta tsakanin ta dasu,daga can suka wuce Bauchi A Bauchi ya gamu da abin mamaki,don mahaifin shi kuka ya rinƙa yi yana neman yafiyar shi da mahaifiyar shi,ya sanar masa Zulfa'u ta haukace tun sanda aka samu ƙaramar ƴar ta da salma da ciki,ita kuma Ameera da cutar AIDS,shi kuma ya tattara yaran ya mayar da su wajen mahaifinsu ita kuma ya sake ta Imran ya sha mamaki sosai,ya jinjina ikon Allah,ya gabatar da Umaima a matsayin ta na matar shi, Alhaji alƙasim ya sa musu albarka sosai Imran ya bawa mahaifin shi labarin ƙanwar shi Ramla da mahaifiyar shi ta haifa,tayi aure itama a Abuja,har da yaran ta uku,dady yace"Allah sarki Aysha,don Allah ka nemar min yafiyar ta" Kwanan su shida a Bauchi yau,sosai Umaima take girmama dady, kullum cikin yi masa hidima take,don sai taga kamar nata mahaifin Deeja ce ta kira ta tace ta tambayi Imran zata je bikin ƙanwar Mima idan ya amince su tafi tare,tunda Deeja ta ambaci Mima gaban ta ya faɗi,don Allah shaida tana mugun tsoron Mima,gashi yanzu zata je gidan su,kuma bazata iya yiwa Deeja musu ba Wajen ƙarfe biyar suka sauka gidan su Mima a azare,Mima bata wulaƙanta umaima ba,amma ko kaɗan bata sake mata ba,suna zaune a ɗakin miman suna hira, Mima na bawa Deeja labarin zuwan inna haleema takwarar ta gobe, wadda ta kasance ƙanwar mahaifin su ce Mima tace"Allah ya kaimu goben,kice gobe da shafta,mama bilki fa?" "Mama bilki maybe itama tazo goben, maybe kuma sai jibi" "Allah ya kaimu"a cewar Deeja,suka cigaba da hirar su Ita dai Umaima tana takure a gefen gado tana kallon yadda suke yin hira,sai su koma musu,sai su fara zagin juna sai su cigaba da shewa,a hankali ta goge hawayen ta tana jin kewar ƴan uwa,don ba wai sun saba da dangin ta bane har yanzu Gashi tsoron maman su Mima ya kama ta ganin irin kallon da take bin ta dashi, shiyasa ma tunda ta rakuɓe a ɗaki bata fita ko'ina ba Mima ta shiga ɗakin mahaifiyar su da sallama,mama sakina ta amsa, Mima ta samu waje ta zauna tace"gani mama" Mama sakina tace"Mima wacece wannan wadda Deeja tazo tare da ita" Mima ta taɓe baki tace"oho,kwashe kwashen auta ne,amma wai naji ance surukar ƙanwar Mamie babba ce" "A ina take?"a cewar mama tana kallon ta "Nace miki ban sani ba fa,ki tambayi Deeja"mama bata sake magana ba, Mima ta fice ya koma ɗakin ta Bata samu Deeja a ɗakin ba sai Umaima da babyn ta take ta kuka,dama bata saka ran samun Deejan ba saboda zataje gidan Aunty Aziza,wadda itace immidiates ɗin Aunty Bintu,ko kallon Umaima da ke fama da little Deeja batayi ba,ta faɗa toilet don yin wanka Umaima ta san matsalar little Deeja,bata bacci sai anyi mata wanka,gashi ita dai bazata iya tambayar ruwan wanka ba,dama dai Deeja tana nan ne,kuma mugun tsoron Mima takeji,haka ta miƙe tana ta jijjiga little Deeja da take sake mimmiƙewa tana tsala ihu Sai da Mima ta gama shirya wa,ganin abin na little ba na ƙare bane ta kalli Umaima fuska babu yabo babu fallasa tace"ko bata da lafiya ne?"umaima ta girgiza kai,Mima tace"to lafiya take irin wannan kukan?" "Ina ga ko wanka take buƙata"Umaima ta bata amsa "Ko an saba mata wankan kafin tayi bacci?"Umaima ta gyaɗa kai "Ikon Allah!shine bazakice a baki ruwa kiyi mata wanka ba?"bata jira cewar umaima ba ta fice daga ɗakin,bayan ƴan mintuna da dawo da baho da ruwan zafi,da kanta ta daidaita ruwan ,ta amshi little tayi mata wanka ta shirya ta,tun kafin ta gama little tayi bacci,ta kwantar da ita a hankali,tayi mata addu'a ta tofa mata,batare da ta kalli Umaima ba ta fice daga ɗakin, umaima sai bin ta takeyi da kallo,tana fita tayi murmushi ta koma kusa da ƴar ta ta kwanta itama Sai wajen ƙarfe tara Deeja ta dawo,a parlour ta samu Mima tana yiwa Mee'ad kitso, ta sauke Affan da yake bacci ta kwantar da shi a kan kujera tana faɗin"wash Allah na" "Gantali daɗi,sai yanzu?"a cewar Mima, Deeja ta harare ta tace "sai dai uwar gantali daɗi"Mima tace"seriously Baki da kirki Deejo,kin bar matar mutane kin tsallake kinyi tafiyar ki" "Ayya!wallahi nayi mata tayin zuwa, tace a'a naje na dawo"Mima ta taɓe baki tace"ƴar ta sai kuka takeyi,wai ashe wanka take buƙata,tsabar sokwanci ta kasa tambayar ruwan wanka"Deeja ta kwashe da dariya tace"tsoron ki take ji ne, kullum kina haɗe mata rai kina mata tsawa,gashi don wulaƙanci kika je har gidan mijin ta a gaban mijin ta kika faffalla mata mari, leemo Allah ya shirya min ke"Mima tayi ɗan murmushi tana taɓe baki tace"ai kuwa ta haɗu da wahala"Deeja tayi dariya ta miƙe ta shige ɗakin da Umaima take Washe gari ƴan biki suka fara halarta, kasancewar yau za'ayi event na Farko, Umaima dai ba don Deeja ba da tuni ta koma gida saboda har yanzu tana da tsoron shiga mutane,tana lafe a ɗakin Mima,daga ita sai wayar ta,don little ma Deeja ta amshe ta suna tsakar gida ana raha,bayan la'asar inna haleema da mama bilki suka iso kusan a tare,Mima sai raha da wasa da dariya sukeyi,bayan sun gaisa da mama sakina suka wuce ɗakin Mima inda Umaima ke zaune tana chatting da mijin ta Sai da suka zauna sannan umaima ta gaishe su cikin girmamawa,bin ta sukayi da kallo suna amsawa,ɗauke kanta tayi ya cigaba da danna wayar ta,mama bilki ta kalli Mima tace"Mima ina kuka samo ƴar INNALE?" Mima ta ɗago kanta cikin mamaki tace"wacce innale kike magana akai mama?kuma wacece ƴar tata?"daidai nan Deeja ta shigo da sallama Inna halima tace"nima Ina ganin ta innale kawai na gani a tare da ita" Mima ta kalli Umaima da tun ambaton innale na farko ɗago kanta a firgice tana kallon su inna haleema,mama bilki ta ciro wayar ta ta fito da hoton innale, wadda asalin sunan ta maimunatu ta miƙawa Mima To pa 🥺me yake shirin faruwa ne? #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 39 Mima ta kalli hoton sannan ta kalli Umaima da ke kallon su idanu waje,tabbas basu da maraba, Deeja ma ta kalli hoton ta kalle ta,ta kalli su inna haleema tace"inna wacece innale?" "Autar mu ce,asalin sunan ta maimunatu,ta rasu shekaru wajen ashirin baya, shiyasa baki santa ba,amma takwara ke zaki iya tuna ta ko?"Mima tace"sosai ma kuwa,kin manta na santa?mama tace Kafin auren ta tayi raino na sosai, lokacin da ta rasu ma da wayo na,na kai shekaru tara ma" "Kin tuna lokacin da tazo zuwan ta na ƙarshe da ƴar yarinya ko?"a cewar mama bilki Mima ta ɗan yi shiru,can tace"tabbas anyi haka,wai ma ni tunda ta rasu ban sake jin labarin yarinyar ba,gabanin rasuwar yadikko(kakar su)na taɓa tambayar ta ina ƴar innale amma bata bani wata gamshashshiyar amsa ba,Ni kuma tun daga sannan na watsar" "Ai kuwa dai babu wanda ya sake bi ta kan yarinyar saboda wulaƙancin da mijin innalen yayi mana a lokacin da muka so amsar yarinyar"a cewar Inna haleema Deeja da tun fara maganar su bin su take da kallo tace"inna a wane garin tayi aure ne?" "Inna haleema tace"a jahar Jigawa ne,wani ƙauye taura"gaban Deeja ya buga,ta daure ta sake cewa"yaya sunan yarinyar ta ta?" Inna haleema tayi ƴar dariya tace"nan fa ɗaya,wani sunan iyayi ta sa mata,duk sanda tazo ba wani iya faɗa mukeyi ba,Ni na manta sunan ma,sai dai ko yaya"Mima dai sai binsu da kallo take tana mamakin waɗannan tambayoyin na Deeja,don ta san halin ta kamar yadda ta san yunwar cikin ta,bata taɓa abu a banza Mama Bilki tace "sunan dai gashi nan gashi nan dai,yana kama da hama,don Ni hama ma nake ce mata hankali na kwance"Deeja tace"ko dai UMAIMA?"mama Bilki tace"wallahi haka sunan yake? tabbas haka sunan yarinyar yake" Deeja ta sunkuyar da kai tana jin wani iri,batayi aune ba ta ji hawaye ya ciko idanun ta,a sanyaye ta ɗago ta kalli Umaima wadda already hawaye ya fara zarya akan kuncin ta,kafin tace komai Umaima ta fara magana cikin kuka "Amma baku kyauta min ba,wannan itace soyayyar da kuka nuna wa mahaifiya ta bayan babu ita a raye?kuka raye amma kuka bar ni rayuwa tana walagigi dani,na koma tamkar marainiyar da bata da asali?"saukowa tayi daga gefen gadon da take zaune,da rarrafe ta ƙarasa gaban su ta haɗe hannayen ta tana kuka mai sauti tana faɗin"meyasa?don Allah meyasa?a sanadin watsar da rayuwa ta abinci ya gagare ni, sutura ta gagare ni, ballantana ilmi na boko ko na addini,babu wanda zanyi shawara dashi,babu wanda zan kaiwa kuka na, azzalumai suka shiga rayuwa ta sukayi ya ƙwallo dani,don Allah laifin me nayi na cancanci wannan hukuncin daga gare ku? meyasa kuka rinjayar da ƙiyayyar mahaifi na akan soyayyar mahaifiya ta da kukeyi?"a haukace ta miƙe tana gunjin kuka tayi waje,ta bar su da bin ta da kallo, Mima tsabar shock bata san ma ta zauna ba,idan ta fahimta kenan ita da Umaima cousins ɗin juna ne Deeja ce ta girgiza kai tana kallon su yadda suke bin umaima da idanu cike da mamaki,a takaice tayi musu bayanin rayuwar da umaima ta fuskanta har zuwa sanda ta ɗauko ta a garin su, Mima sai kallon Deeja takeyi ta kasa magana Mama bilki da inna haleema kuwa fashewa sukayi da kuka,mama bilki ta miƙe batare da tayi magana ba ta zaro wayar ta ta soma neman babban yayan su wato abban Mima Ita kam Umaima backyard ɗin gidan ta nufa ta zauna tana kuka mai motsa rai,babu abinda yafi mata ciwo kamar yadda taga suna rayuwar su cikin farin ciki da ƙaunar juna,amma ita sun banzatar da tata rayuwar da ta tunda har zina tayi da auren ta saboda rashin gata sai ta sake rushewa da kuka Mima ta kalli Deeja cikin sanyin murya tace"abin mamakin deejo,wai ashe yarinyar nan cousin sister ɗi na ce?"ɗan murmushi Deeja tayi tace"ikon Allah kenan leemo"Mima ta juya tana kallon little Deeja da ke ta wasannin ta akan gado hankalin ta a kwance,sai ji tayi tausayin yarinyar ya kamata,ta matsa bakin gadon ta ɗauko ta tana kallon ta tana murmushi,ga ƙwalla a idanun ta,suna haɗa idanu yarinyar ta fara dariya, Mima ta rungume ta hawaye na zubo mata A ranar mahaifin Mima ya dawo bayan maghriba,da sai gobe,amma dalilin issue ɗin Umaima ya bar abinda yake yazo,zuwa lokacin da ƙyar Mima da Deeja suka lallaɓa umaima ta taso daga backyard suka kai ta ɗakin amaryar da za'ayi bikin ta shukra suka kwantar da ita,don da kafewa tayi bazata koma gidan ba tafiya zatayi,tana shiga kuma ta nemi waje ta kwanta, sallah kawai ke tayar da ita, little kuwa tuni ta fita lamarin ta ko kallon ta batayi Allah ya sa yarinyar akwai haƙuri, Mima ta dama mata cerelac ta bata,da ta fara rigimar bacci kuma tayi mata wanka ta goya ta har tayi bacci,ta kwantar da ita A lokacin ragowar yayyen Mima ma sun hallara,Aunty aziza, Aunty Na'ima,da Yaya mukhtar da shi ma baya ƙasar yana UK,sai Mima da amaryar da ke gidan ƙanwar yadikko Inna salame,sai ƙannen abban su Mima,banda inna haleema da mama bilki,akwai baffa Tahir,mama fati,sai autan su,wanda innale take bi,wato baffa mukhtar Sai da suka kammala haɗuwa sannan Alhaji kabir wato abban su Mima yace a kira masa Umaima,Aunty aziza da Mama bilki ne suka shiga ɗakin shukra in da Deeja ke zaune a wajen ta,jikin ta ya rine da zazzaɓi,da ƙyar da suɗin goshi Deeja ta samu ta sha shayin da ta haɗa mata ta bata magani,da Imran ya kira Umaima a waya ita ta daga tayi masa bayanin abinda yake faruwa, kam yayi farin ciki sosai,yayi tayiwa Deeja godiyar ta silar ta duk wani cigaba yake ta samun su,ya ƙara da cewa shima zai shigo,ita dai Umaima tana jin su, kasancewar a speaker Deeja ta saka wayar,amma bata tanka ba A wannan halin su Aunty aziza suka zo kiran umaima,tana ganin su ta sake fashewa da kuka, Cikin fusata Deeja tace"amma kinyi min alƙawarin bazaki sake kuka ba, wallahi sai in ƙyale ki in kama harkar gaba na"Umaima tayi saurin goge hawayen batare da tayi magana ba ta miƙe ta bi su zuwa parlourn Da sallama suka shiga,ta gaishe su cikin girmamawa,suka amsa suna kallon ta,ita kuwa kanta a ƙasa ta kasa kallon kowa,har yanzu hawaye na ƙoƙarin zubo mata amma tana dannewa Alhaji Kabir yayi gyaran murya ya bude taro da addu'a,bayan ya gama ya fara jawabi "Kamar yadda muka sani shekaru ashirin baya mun rasa autar mu maimunatu,ko nace innale,mun so tilon ƴar ta ta dawo hannun mu amma mahaifin ta da dangin shi suka nuna sun fi mu iko da ƴar, dalilin haka muka bar musu ƴar su wanda shine mafi girman kuskuren mu A yau ga yarinyar innale ta dawo gare mu amma kuma maimakon mu kasance cikin farin ciki sai akasin hakan dalilin irin rayuwar da ta samu kanta a ciki"a taƙaice ya basu labarin Umaima,da yawan su sai da sukayi kuka,wanda ya sanya Umaima fashewa da wani sabon kukan, Alhaji Kabir ya cigaba"don Allah muna roƙon ki Umaima,da kiyi haƙuri abinda ya faru ya faru,a irin soyayyar da mukayiwa autar mu banda ƙaddara da jarrabawa babu abinda zai hana mu dawo da ke cikin mu,kar ki saka a ranki wai mun girmama ƙiyayyar mahaifin ki akan soyayyar da mukayiwa mahaifiyar ki,sam!mu bamu ƙi Aliyu ba,abinda zai je ya dawo muka guda,gashi kuma mun tarar Definitely dangin mahaifin ki sun fi mu ƙarfi akanki, lokacin da mahaifin ki ya rasu da kusan watanni biyu Na tura Tahir don ya ɗauko ki,amma sai wan mahaifin ki yace bazasu bamu ke ba,idan ma muka cigaba da bibiyar ki sai kotu tayi mana tsakani,hakan yasa nayi tunanin zasu kula da ke na ƙyale ban sake bibiyar lamarin ki ba,amma kuma komai na rayuwar bawa a rubuce yake,babu wani bawa da ya isa ya sauya ƙaddarar ɗan uwan shi ko tashi,bazamu iya sauya ƙaddarar ki ba Umaima,so erase off damuwoyin da ke ranki ki manta da ɓacin rai,dama rabon haihuwar ki da jarrabawar da zaki fuskanta yasa innale ta auri Aliyu,amma definitely bamu so innale ta aure shi ba,don sanda ya haife ki ma bata kai 17 years ba, lokacin ma makaranta takeyi ta auri mahaifin ki,gashi shi baiyi karatu ba,don ma yayi ƙoƙari da yayi enrolling ɗin ki,kiyi haƙuri Umaima kinji? dukkan mu muna son ki,muna ƙaunar ki" Sosai Umaima taji relief a ranta,kusan kowa na parlourn sai da ya bata haƙuri ya gabatar masa da kanshi,ita dai sai bin su takeyi da idanu tana jan ajiyar zuciya, fuskantar ta gaji ya sanya Mima tayi musu sallama ta kama hannun umaima suka koma ɗakin shukra Ita ta haɗa mata ruwan wanka tace ta shiga wanka, Deeja dai na gefe tana kallon su,har yanzu ji takeyi kamar a mafarki wai Mima da Umaima cousin sisters ne Mima da Umaima cousins 🤔Nima dai naji kamar a mafarki 😴 #Nusy_bee *****MATAR KHALEES***** ✍️Nusy bee Page 40(last page) Bayan Umaima ta fito sababbin kayan bacci Mima ta bata,sai da ta gama shirya wa sannan umaima ta kawo mata abinci A sanyaye ta girgiza kai tace"na sha tea ai" Mima tace"amma dai kin san shayarwa kike ko?kuma yau through out banga kinci wani abin kirki ba,c'mon malama kin ci abinci,nan ɗin gidan baban ki ne,raɓe raɓe ya ƙare kuma"Umaima tayi murmushi ta karɓi abincin ta fara ci Mima ta zauna gefen gadon tana kallon Deeja da tayi sakare tana kallon su,ta fashe da dariya, Deeja tace "bazan kula ki ba,nasan magana kike nema" Mima tana dariya tace"really deejo,gani nayi kin zama kamar wata tsuntsuwa da aka figewa gashi aka saka a ruwan sanyi"Deeja ta yatsina fuska ta kuma cewa"ba fa zan kula ki ba leemo,don yanzu sai ki saka min tension" Mima tayi dariya tace"bari na kira injin miya shi nasan zai kula ni"babu shiri Deeja ta kama dariya tace"wallahi leemo kin raina min miji,meye kuma injin miya?" "Eh saboda shi a ƙani na ne"a cewar Mima tana kallon Deeja a ɗage Deeja ta ja tsaki tace "leemo baki da kunya wallahi,mutumin da a haihuwar kaji ya haife ki shine ƙanin naki?" Mima ta tafa hannu tace"ai ya faɗo tunda ya auri ƴar autar mu" "Ke fa waɗannan watanni taran jin su kike kamar shekaru ɗari tara"ba Mima ba,ita kanta Umaima da ke kallon su cikin burgewa sai da ta ɗan yi dariya Gyara zama Mima tayi akan daddumar da ta shinfida akan tiles ta kalli Umaima da ke zaune gefen gado tana cin abinci a hankali tana kallon su,Mima tace "idan an ƙare biki zan kai ki gidan mama iyami,itace wadda ta riƙe mahaifiyar ki Kafin maman ki tayi aure kullum aikin mama iyami tace innale tayi kaza tayi kaza,kuma ana cewa za'a yi mata faɗa zata kama kuka tana faɗa wai don an ga bata girma da uba ba,komai tayi mata sai dai ace Allah ya kyauta Lokacin tana siyar da kayan yara su carbin malam,tsami gaye,aya,ɗan tamatsitsi,to yawanci Aunty innale ke cinye riba har ta taɓa uwa,idan taga babu tayi ta faɗa,a gaban idanun ta kuwa muƙus take tayi ta zare idanu Akwai lokacin da ta soya aya mai gishiri da daddare ta kwashe a ƴar langar ta, suna ta hira da baffa Tahir,sai ga Aunty innale tayi sallama ta dawo daga makarantar dare,tana gani tace"ah!yau mama ta tuna aya kenan"ta cika hannu ta watsa a baki,tana tauna tace"kwana biyu mama bakiyi aya ba,tayi daɗi"ta ƙara cika hannu ta watsa a baki ta sake cewa"gishiri yaji"sannan ta cire hijabin ta ta saƙale, baffa Tahir yace"auta ba magana?"ko kallon shi batayi ba tace "ina wuni"tayi shigewar ta,yana kallon mama iyami ta miƙe da sauri Sanda Aunty innale ta gama shaunin ta a ɗaki ta fito ta samu waje ta zauna tana faɗin"wai!yau fa na gaji da yawa,malamin da ke mana karatu bai zo ba,wani ɗan takura aka turo mana"daga nan ta matsa kusa da kwanon,shi dai baffa Tahir ƙoƙarin danne dariya yakeyi,mama iyami kuma ta ɗauke kai tana sakace haƙuri,Aunty innale ta faki idanun su ta watsa a baki,ai da mugun sauri ta fito dashi tana tofarwa,wai ashe Inna juye ayar tayi ta zuba bushashshen kashin awakai a kwanon ta ajiye shi a inda yake, shiyasa baffa Tahir yake ta danne dariya,yanzu kuwa a bayyane ya kama dariya har da ƙyaƙyatawa"ita kanta Mima mai bada labarin dariya takeyi ballantana Deeja da Umaima, Mima ta cigaba"ai kuwa Aunty innale ta kwanta tana burgima tana ihu,mama iyami ta ɗauko kwanon ayar ta dire mata,ta zauna tana aikin lallashi,da ƙyar ta haƙura,kuma bayan ta haƙura mama iyami ta kora baffa Tahir da bulala Lokacin da ta fitar da baban ki wai ita aure take so,kakar mu yadikko tace bata yarda ba,sai da mama iyami ta daina mata magana,a ƙarshe dai haka akayi auren Aunty innale da ƙananun shekaru,don har ta haife ki bata cika 17 years ba"Deeja tace"gaskiya dai Aunty innale akwai rigima,wai!" Mima tace"ai auta ce,banga abin mamaki anan ba"Deeja tayi kamar bataji Mima da ke dariya ƙasa-ƙasa ba, Umaima kam tayi dariya tana kallon Deeja,don zuwa Yanzu itama ta gane Deeja bata son sunan autan nan Hirar su suka cigaba da yi suna tsokanar juna,ko da Umaima bata saka musu baki amma tana nishaɗantuwa,har dare ya kusan raba basu sani ba Washegari akayi event ɗin da ba'a samu anyi jiya ba,babu ƙarya sunyi kyau sosai, dama dukkan su gwanayen kwalliya ne, Umaima dai a lokacin taga dangi taga ƴan uwa,ko'ina ta zaga sai taji ana ga ƴar innale,amma fa rayuwar ta abban Mima ya hana tayar da batun,don yaga umaiman tana shiga damuwa,a ranar ta sake sosai,tare suka fita da ita da Deeja da Mima sai yaran su,kuma tare suka dawo gida Washegari ta kama ɗaurin aure,bayan an ɗaura Imran ya kira Deeja a waya,itace tayi masa iso babban parlourn gidan ta kawo masa abinci da drinks,sannan ta kira Umaima da suke zaune da ƴan matasan matan family ɗin,har da intisar ƴar gidan Aunty Bintu,sai kallon Umaima takeyi da mamakin abinda ya kawo ta,itama umaiman kallon ta takeyi tana son tuna inda ta santa,babu wanda ya yiwa wani magana dai Suna ta hira a ɗakin ya cika da hayaniya Deeja ta shiga,janyo hannun Umaima tayi ta dauko mata mayafi tace"mu je,mijin ki yana neman ki"bata jira amsar ta ba ta ja hannun ta suka nufi parlourn baƙi,tana zuwa bakin ƙofa ta saki hannun Umaima ta koma ciki Da sallama Deeja ta shiga,Imran yana zaune akan two sitter ya ɗago daga danna wayar da yakeyi ya kalle ta yana murmushi,duk da dauriyar da ta koya kwanaki biyu saida taji ta karye,suna haɗa idanu ta fashe da kuka,da murmushi ya taso daga inda yake zaune ya ƙaraso kusa da ita ya kama hannayen ta yana faɗin"yanzu gaba ɗaya kin zama cry cry baby,abu kaɗan sai ki kama kuka"sai ta ɗaure fuska ta fizge hannayen ta tana huci,ƴar dariya yayi ya sake kamo hannayen yana faɗin "sorry Please,don Allah ki manta da komai Umaima,kamata yayi a ce kina cikin farin ciki,kar kiyi wa Allah butulci,ki godewa Allah wanda ya juya miki rayuwa daga ƙunci da damuwa ya canja miki zuwa ganiyar farin ciki,just move on kinji mon amé sóuiré?"kwanciya tayi a hankali akan ƙirjin Imran,ya sanya hannu ya kewaye ta,a hankali ta furta"Deeja tayi min komai a rayuwa,me zanyi na biya ta?" "Ki riƙe ta da kyau,ita ɗin alkhairi ce ga duk wanda ya raɓe ta"umaima tayi murmushi batare da tace komai ba Anyi biki lafiya an kai amarya ɗakin ta, washegari Deeja ta dawo Kano ta bar Umaima a azare,Mima ta raka ta ta zaga dangi sosai,ta ga soyayya ta ga gata,wanda ya goge mata duk wani tabo da ciwo a ranta,kwanan ta biyu da dawowa Bauchi sukayi wa dady sallama suka dawo Kano ** ** ** Cikin sauri take shirya little Deeja,Imran ya leƙo yana faɗin"Madam You are wasting my time" "I'm sorry gani nan"ta kama hannun little wadda yanzu babu inda bata zuwa da ƙafar ta,suka fito Sai da suka shiga mota ta kalle shi tana faɗin"wai ina zamu je ne?"batare da ya kalle ta ba yace"ziyara mana" Tafiyar rabin awa ta kawo su asibitin shi da ya gina,aka buɗe shi sati uku da suka gabata,bayan sun isa parking lot suka fita zuwa cikin asibitin Kai tsaye ɓangaren Male wards suka nufa, Umaima tayi matuƙar firgita da ta ga Imran a kwance a wani ward,male nurses na ta gyara shi da alamu ma babu abinda yake iya yiwa kanshi,a guje ta juya zata fice daga ward din Imran ya riƙo ta,ta fashe da kuka cikin fitar hayyaci,bai ce mata komai ba ya ja ta suka fice daga ward ɗin A reception suka tsaya,ya riƙe mata hannu gam,don sai ƙoƙarin tirjewa takeyi tana son fizgewa ta fice daga asibitin, Imran ya riƙo ta sosai yana ɗago haɓar ta yana kallon ta,cikin kwantar da murya yace"is okay Umaima,calm down,ki nutsu zamuyi magana"batare da tayi magana ba ta daidaita nutsuwar ta tana share hawayen ta Ya kalle ta sosai yace"ban kawo ki nan wajen ba don kiyi kuka ko don ki tayar da hankalin ki,i bought you here don ki sake fahimtar rayuwa" Cikin mai motsa rai Umaima tace"bana bukatar sake ganin shi a rayuwa ta,shi ya raba ni da farin ciki na,shine ya sa na kware muku baya,shine ya hana ni sukuni ya raba ni da dukkan walwala ta,ya guje Ni a lokacin da na rasa komai,bana son ƙara ganin shi kuma bazan taɓa yafe masa ba" Tausayin ta ya kama Imran,ya sa hannu yana goge mata hawayen yace"You need to forgive him Umaima, rikon bashi da amfani musamman yadda rayuwa ta juya muku ku duka,kika koma matsayin da yafi nashi ɗaukaka,shi kuma ya mayar dashi matsayin da yafi naki ƙasƙantuwa,ki yafe masa,ko ba komai albarkacin yafiya muke ci baki ɗayan mu,ba don yafiya ba da yanzu kina taura kina rayuwa da ƴa ta ɗaya tilo wadda bansan ta ba,ba don yafiya ba da Ni da ke bamu haɗa kai da family ɗin mu ba,ba don yafiya ba da Yanzu ina rayuwa cikin kewar ki da rashin ki,kema haka,the most beautiful part ba don yafiya ba da yanzu baki san maternal relatives ɗin ki ba" Murmushi tayi tana share hawayen ta tuno da Deeja da tayi,wadda a yanzu ita da Khalees basa ƙasar,a cewar su sunje honeymoon ɗin da basu samu sun je ba a farkon auren su "Now forgive him wife"cikin sanyin murya tace"na yafe masa" "That's my girl"ya faɗa yana murmushi yaja kumatun ta,sannan ya kama hannun ta suka nufi ward ɗin da Najeeb yake A bakin ƙofa ya tsaya,ita kuma ta shiga ciki tana kallon yadda gaba ɗaya ya lalace ya ƙwanjale,sai hawaye yake tun shigowar su ta farko Murmushi mai ciwo Umaima tayi tana kallon Najeeb,cikin sanyin murya tace"sannu ya jikin?" "Ki yafe min Umaima"a cewar shi cikin kuka "Na yafe maka,ko babu komai silar ka nasan Imran kuma nasan Deeja,waɗannan mutanen sunyi min komai a rayuwa,duk da abinda kayi min ka bani gata,ka bani ilmi,ka bani mijin aure da nake alfahari dashi,na yafe maka"kuka ya ci ƙarfin ta,har Yanzu tana jin ciwon yadda Najeeb ya wulaƙanta mata rayuwa ya mayar da ita kamar matar shi, musamman yanzu da tayi ilmin addini sosai tasan hukuncin hakan Tsayar da kukan tayi tace"ina Nadiya?" Cikin shaƙewar murya yace"nadiya ta rasu watanni bakwai baya,bayan ta sha jinya" "Allah yaji qan ta,itama na yafe mata"a cewar Umaima,ta juya cikin sanyin jiki ta fice daga ward ɗin Imran ya tako inda Najeeb yake yana murmushi,yace"Finally,komai ya wuce,kuma kamar yadda Umaima tace ne,a sanadin ka muka san juna,we are grateful for that,a sanadin ka na rabu da Deeja,banyi bakin ciki ba saboda Allah ya rubuta Deeja ba mata ta bace, MATAR KHALEES aboki na ce,ka jefa min tsanar ta,amma bakayi laifi ba saboda nine na zamo wawa har na bari aboki yake wasa da tunani na,na barshi a hakan ƘADDARAR MU CE(my next novel), Allah ya baka lafiya"yana kai wa nan ya fice abin shi, Najeeb ya bishi da kallo yana hawayen nadama mara amfani BAYAN SHEKARU BIYAR Abubuwa da yawa sun faru, Najeeb ya rasu shekaru uku da suka wuce, Umaima ta gama karatun ta cikin nasara, Deeja ta buɗe companyn ta nata na kanta,a yanzu Umaima ce M.D a companyn, Afra da fauwaz sun koma Columbia da zama baki daya, Deeja ta sake haifar yara biyu, babbar mai sunan Mamie babba,sai ƙaramin mai sunan mahaifin Khalees, Umaima ta ƙara haifar mace an saka mata sunan mahaifiyar su,Afra ƴan biyu ta haifa mata,ɗaya sunan mahaifiyar ta,ɗayar kuma sunan Deeja, lubaisa ma yara biyu ta haifa,babbar mace sai ƙanin ta namiji, zakiyya ma ta haifi mace ta saka mata sunan Deeja,Mima ma ta haifi ɗan ta namiji a Malaysia an saka masa sunan mahaifin mijin ya hafeez,wato Abdulhakim A yanzu rayuwar family ɗin ta zama abin sha'awa,ko da Umaima da Mima take da alaƙa,kuma yanzu sun daidaita,har da Imran ma,amma ta ɗauki Deeja a matsayin uwa da ta rasa,yaya da bata da ita,sun haɗe kansu baki daya,zaman lafiya ya wanzu sosai, kowace tana rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali tsakanin ta da mijin ta TAMMAT BIHAMDULILLAH 🙏 Anan na kawo karshen littafi na na MATAR KHALEES wanda Ni Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)na rubuta,kuskuren da nayi ina roƙon Allah ya yafe min,abinda na rubuta mai amfani kuma ina roƙon Allah ya sa ya amfani al'ummar mu Ina matuƙar godiya ga waɗanda suke yi min likes da comments,kune kuka bani ƙwarin gwiwa har nazo wannan matakin🤗ban manta da waɗanda har zuwa na musamman nakeyi don ganin comments ɗin su ba😁 jidda da Juliet,akwai sharhi da ƙarin bayani, Allah ya bar mu tare Allah ya saka muku da alkhairi baki daya Sai mun haɗu a littafi na na gaba ƘADDARAR MU CE #Nusy_bee Downloaded from NovelsHQ.com This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com to download more hausa novels visits our site at www.Novels.Com For feedback and support Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ.com Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ.com Telegram : https://t.me/NovelsHQ.com