Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com For feedback and support Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ Telegram : https://t.me/NovelsHQ [5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: *🧳 HASASHE🧳* *Sabon littafin* *HALIMA ABDULLAHI K MASHI* https://chat.whatsapp.com/Cg5ZwzwtDQ1A4W6sJ0mLgl *Page 1* *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/100083170164617/posts/668798479235818/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* Halifa ya kalli Abokan sa dake ta daga ɗinkin Sulaiman daya daga cikin su , suna ta farin cikin gabatowar bikin Halifan wanda ya rage saura kwana tara, dai dai lokacin ma ƴan kai lefe suna can gidan su Bilki amarya. Kati suke kasaftawa wanda za su fara rabon shi nan da kwana uku. Wayar Halifa ta yi kara, cikin zumuɗi ya ciro da zaton amaryar ce dan yana ta dakon kiranta. Hafsi ce yariyar Antysa wadda tana cikin yan rakiyar kai lefe. Ya ɗaga da tambaya. •Hafsi har kun fito?” Muryoyi ya ji suna tashi kamar ana rigima. Ta katse shi da fadin “Uncle Halifa wallahi sun raina kayan nan. Kuma wai ba a sako kaya sa lalle ba, Baba ta fada musu yanzu ba a yin kayan sa lalle tunda turare ake fesawa sai suka ce su har yau suna rike da wannan al adar. Wai atamfa goma leshi biyar shadda biyu wannan harkar tsiya har ina… “Me Umman su Bilki tace? Halifa ya katse Hafsi. Tace “Cewa ta yi Allah ya so ba ta gayyato ƙawayanta gurin kaɓar lefen ba da ta sha kunya. Wai a saka su ƙasan gado gara ace ba a yi lefen ba, kuma wai kayan tukwicin ba za a bamu ba wai tunda mun sha fiya wata a mai da lemun da cincin ba kuma zata bada ko nera ba.” Halifa Ya sauke wata wawuyar ajiyar zuciya sannan yace ina Bilkisu? Tace “Gata can tana kuka.” Yace kai mata wayar, karki kashe. Yana jiyo muryar ƙanwar mahaifiyar shi Baba tana cewa mun zata kayan nan al adace kuma kowa yana yin daidai ƙarfin sane. Yaji lokacin da Bilkisu take cewa Hafsi bazan amshi wayar sa ba, sai kuma tace kawo dai. ya ji daya daga gare ni. Ta shiga zazzaga masa bala’ i tana fadin ya bata mamaki ashe duk kiran sun shiga kasuwa da cewa ya yi aike Dubai da yake yi iya tsiyar da ya siya kenan aƙwati uku da gana masgo. Wallahi Halifa ka bani kunya. Halifa ya share zufar fuskarshi ya kalli abokan shi da suka yi cirko cirko cikin sanyin murya yace Bilki kin raina waɗannan kayan? Cike da gadara tace “Na raina su Halifa!! Yace kenan dan kaya ki ke sona? Tace “Halifa zan fison a ce ba a kawo ba sam!” Yace shike nan ku basu kayan su maido min. Tace. “Yanzu kuwa har katin daurin aurenka da ka bado dashi. Bai kuma cewa komai ba ya kashe. Take ya soma kiran layin Baba. Ta daga yace Baba ku dawo da kayan kawai,. Baba tace “Bari mu gani ko za a samu maslaha. Megidan muke jira . ” Yace Baba kawai ku rabu da su ku taho. Ta katse wayar tare fadin zan kira ka ga Antyn ka tana kira na.” Ya dubi. Abokan sa da suka cika da al’ajabi yace ku kona katunan nan Wallahi na fasa. Suka ce ka a hankali Suka fito suka zauna a dakalin kofar gidansu Sulaiman suna bashi baki tare da shawarin yadda ya kamata a yi. Bashir ne kadai ke goyon bayan shi dan yace ko shine fasawa zai yi. Da idon ya ke binsu amma ba lallai yana fahimtar inda suka dosa ba. Zuciyar shi da kwakwalwar shi suna maimaita masa zafafan kalaman Bilki. Wanda kullum ta ke nuna mishi in bashi bazata iya rayuwa ba amma sai gashi akan lefe gaskiya Antynshi ta yi gaskiya da tace su gwada su. Gefe kuma yana tuna kudin da Abokan shi suka kashe na game da shirin fati wanda Bilkin ta matsa sai anyi. Iya Hall dubu dari uku su ka biya banda sauran abubuwa ga shi abokan nashi ba masu karfi bane. Siririyar murya ta katse masa tunani, sannunku Yaya Sulaiman. Halifa baya ciikin waɗanda suka amsa, amma ya bita da kallo bazata fi shekara sha bakwai zuwa takwas ba, sanye da kayan islamiya waɗan da suka jeme suka kode kwadat. Sai yaji bakın shi ya furta cewa ke zo. Ta dawo baya ta ce “Gani.” Ga zaton ta aiken ta zasu yi. Halifa yace "Zaki aure ni? Ta ce “Mene?” Yace nasan kinji amma bari in maimaita kuma ki bani amsa zaki aureni? Tayi yar dariya zata wuce, yace na yi miki kama da wanda zai miki wasa? Su Sulaiman sun kasa magana dan mamaki. Domin dai sun san gaske Halifa baya cikin yanayin da zai yi wasa, ko da dama ba mai wasan bane. Ta daga kai alamar eh. Halifa ya kalli Sulaiman “ina ne gidan su?” Sulaiman yace Asiya ki shiga gida. Sannan ya dubi Halifa “Dan Allah ka nutsu ka bari a sasanta waccan maganar yarinya nan kamar kanwata take kaga gidan su da namu katanga ta raba, ba zan so wata matsala ta same ta ba. Halifa yace wallahi ita zan aura, kawai sanar dani ina Baban ta? Sulaiman yace Halifa wannan halayyar ta ka ta saurin yanke hükünci kayi kokarin rabuwa da ita, Baban ta yana cikin gida yana fama da ciwon suger kafa daya ma gare shi an cire dayar, dan Allah kar ka sa su a damuwa. Yarinyar nan ga wurin da take tuyar awara can, yayar ta Sadiya bazawara ce mijinta ya mutu tana gidan da yaranta biyu , aikatau take zuwa gidan masu hali kusan su ke rike da gidan. Namijin su karamine tallar fiya wata yake zuwa a danja, tuni sun dai na boko sai islamiya. Na san ba irin matar da ka ke so bace Asiya. Halifa ya mike, muje kamin sallama da Baban su kawai na canza ra ayi irin wadda nake son yar gayu yar birni wayayya baga shi kana gani abinda suka min ba . Usman ya dagawa Sulaiman hannu tare da fadin kar ka hana shi kaje kawai. A soron gidan suka zauna a tabarma kallo daya zaka yi wa Baban ka tabbatar yana jin jiki. Bayan sun yi masa sannu, sai Halifa ya fara magana. Baba dama ni ne nake son auren.. ya kalli Sulaiman dan baima san sunan ta ba. Sulaiman yace “Asiya ya gani yake so. Halifa ya amshe da fadin kuma Baba ina son nan da kwana tara in zai yiwu,aure na za ayi suka raina lefen maganar ta watse, in har ka amince min yanzu za a kawo kayan nan gidan nan Baba.” Baban su Asiya ya yi dan tari, murya can kasa yace “Samari , ba a saurin yanke hukunci gaggawa wani lokacin daga shedan take, hakika naji dadi har da ka ga ‘ya ta ka ce kana so, amma ita tana son ka? Wannan abu na farko da ya kamata in sani. “. Halifa ya yi karaf yace a kira ta a tabbatar Baba amma ni ta fada min cewa ta amince. Ya kalli Sulaiman “Leka kace. Asiya ta zo” Daidai lokacin tana ba Sadiya da Innar su labarin yadda su kayi da abokin Sulaiman kuma shine wanda ya yi sallama da Baba. Innarsu duk sai taji tsoro ya kamata domin bata taba ganin irin wannan abu ba. Sadiya kuwa cewa ta yi Allah ya sa ya zama alkhairi tasan Sulaiman ba zai cutar da su ba. Kiran da Sulaiman ya kwado cikin gidan shine ya sa hantar cikin Asiya ta juya har taji tana jin bayan gida. Innarsu tace “kije amma karki ce kin yarda kice wasa ki ke yi. Asiya tace to. Ta tsuguna Baba yace Asiya kin yarda cewa zaki auri wannan yaron abokin Sulaiman? Ta daga ido ta kalle su, baza ta iya tantance waye a cikin su yanzun ba. Ta sake sunkuyar da kai sai tace daga kai alamar eh ta kasa yin yadda Innarsu ta fada mata. Baba yace mata kin tabbata? Ta sake daga kai, yace ta koma ciki, Ya dube su. “Sulaiman tunda Asiya ta yarda kuma abokinka ne gaka ga shi ni bansan shi ba amma na sanka, duk wani bincike kai ne dama zan sa a gaba dan Asiya kanwarka ce, ina son ka bani wani tabbaci game da shi.” Sulaiman yace Baba bansan wani mutum mai saukin kai kamar Halifa ba, sannan yana da ilmi duka biyu yana da sana’a kuma yana da a kida ahlissuna ne, ga ibada. Tare mukayi karatun sakandire mu hudun nan duk cikinmu ya fimu sukuni amma komai tare muke, ya yi ta taimaka mana a makaranta kuma har zuwa yanzu, bai canza mu ba. “ Baban Asiya yace “To shike nan amma wani hanzari ba gudu ba, ni dai kaga a yadda nake da ina da hali ma yanzu ace ina gadon Asibiti dan haka bani da sukunin aurar da ita a yanzu. Sai dai a sa lokaci Muga abinda Allah zai yi.” Halifa yace me cece damuwar Baba? Baban Asiya yace “kayan daki mana na yarta kuma kwanaki da jikina ya motsa lokacin da za a yanke kafar nan aka sai da su da sai a kaimata duk da suma ba na zamani bane. Itama lokacin sasantawa mukayi da yaron suka kawo kudi madadin lefe ya yi mata dan kala biyu na fitar biki muka hada da dan abinda ke hannunmu a ka rufa asiri. Kai kuma gashi da lefanka a hannu bare a yi hakan. Halifa ya gyara zama Baba ni dai yarinya nake so ba kaya ba. In katifa ta samu ko da sadakin ta ne ku sai mata Allah shine mai yalwatawa. Dadi ya rife Baba yace “To yaro na amince, sai dai ina son ka kawo magabatan ka. “ Halifa ya ce za su zo amma dai yau ina son ku karbi kayan ku ajiye gobe zan kawo su. Baba ya amince. Suka fito suna mamki lamari kamar wasa yana neman zama gaske. Halifa ya daga kiran da ke ta shigo wa wayar sa yana katsewa lokacin da suke magana da Baban Asiya. Baba ce, tace ina ta kira kazo mu tafi an sasanta da Abban su ya zo akan za a karo wası abubuwan kuma za a kawo kayan sa lalle Antyn ka ta amince akan haka. “ Halifa ya yi wata yar dariya takaici kamar yarda ya zata shima Abban su Bilki jeka na yi ka ne. Yace Amma kuna gidan har yanzu? Tace e sun bamu kayan tukwaicin. “. Yace ku dai jirani a gidan. Ya dubi Bashir zo muje ku kuma ku jiramu a nan. Suka fita a layin zuwa inda ya aje mota kasancewar layin in an shigo da mota sai dai a fita ta baya to baya shigowa da mota. Suna isa yace Bashir kayan nan zamu amso fa. Bashir yace “Shine daidai fa. “ Suka sallama Hafsi ta fito Tana ta tura baki tana fadin”Wallahi Uncle duk da haka suna ta yarda magana“ Yace kuje ke da Bashir ku kwaso min kayana. Baba tana ‘A a. " yace kiyi hakuri wani gurin za a kai kayan. Abinda wani ya raina shi wani ke farin ciki da şamun shi. Umman su Bilki ta ce ya haka ? Bashir yace za a canza ne sai a hado da karin. Suka sa kaya a mota Halifa yace a maida ruwan da lemon da cincin din. Bashir yace baza a maida ba, kamar yadda na tabbatar baza su maido maka da kudin auren ka ba, banda hidin dimu da kayi mata. Kamar wasa sai ga kaya ankai gidan su Asiya makota suka shigo aka amsa cikin girmamawa ba kayan tukwici amma Innar su Asiya ta kebe da Umman su Sulaiman ta ari dubu biyar ta basu.... *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: *🧳 HASASHE🧳* *Sabon littafin* *HALIMA ABDULLAHI K MASHI* *Page 2* *Zaɓi biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* Anty ta kalli Baba cike da tashin hankali tace, "Baba wai garin yaya kuka bar Halifa ya yi son zuciyar sa Ya zai kai kaya gidan wata wadda ba a san ko wacece ba? Menene asali da tushenta shi kanshi na tabbata bai sani ba." Baba ta numfasa tace " Habiba ni fa iyakacina kai kaya duk yadda ake ciki da yadda akayi gidan su Bilkisu munyi waya da ke, shi ya zo ya sa abokinshi da Hafsatu sune suka fito da kayan, mu muna waje ma. Anty ta kwalawa Hafsa kira, ta shigo tana cin cincin din da su ka ta ho da shi daga gidan su Bilkisu tana fadin ya yi dadi kyanshi da shayi. Anty tace Wai Hafsa ya akayi ba ku dawo da kayan nan ba in ma bai amince da sharaɗin da akayi da gidan su Bilkisu ba? Hafsa tace "Anty kinsan Uncle Halifa babu wanda zai saurara in ya yi fushi. Wayata mutuwa ta yi shiyasa ban kira ki ba, ita kuma Baba katinta ya kare. Anty tace Ya Salam! Ta kai ta kawo a tsakar falon ta ce Baba zo kiga kayan da aka shirya tun farko za a kai gidan su Bilkisu. Baba ta bi bayan Anty zuwa wani daki, akwatuna guda sha biyu blue da pink ga wasu adudu shake da kayan al ada an daure su da madaurin ado irin na zamani. Cike da mamaki Baba tace Amma me ya hana a kai wadan nan? Hasashe na yi Baba.(, Anty ta cafke tambayar) . yadda suke nuna wa Halifa Kauna yarinyar nan kamar ta kawo kanta, sai na kalubalanci Halifa cewar yarinyar nan da bata kula yana samu ba da ba zata yi masa irin wannan son ba, sai yace sam ko bashi da ko sisi zata zauna da shi. Dan haka sai nace masa kar a kai kayanta wancan da aka kai na iyayenta ne da sun karba sun yi godiya sai a ba su mamaki da wannan. Baba tace "Kash kinga rashin rabo amma kuma fa Habiba ba ku kyauta ba, ai wannan gwajin ba kowa zai cinye ba a wannan zamanin,domin 'ya' ya da iyayen su yanzu sun daura buri akan lefen nan." Anty ta tabe baki ta ce, nifa dama yarinyar nan bata min ba idanunta sun bude da yawa wayo zata zo ta yi ta wa Halifa to shi bakar zuciya ce da shi, ga kafiya ko me zaki fada masa ba zai yarda ba sai ya gani da idanunsa shine na harba shi a haka bukata ta biya amma ya sake yin wani shashancin. Baba tace "Su wadannan ai sai dai a kira musu babu, bashakka ba su da shi amma suna da mutunci kuma sunyi murna sosai." Anty ta zuba ido tana kallon Baba kamar wadda ta ji wata sabuwar kalmar da bata taba ji ba. Ta maimaita kalmar Babu!! Wai Baba kina nufin talakawa ne?!! Baba tace 'Yan uwana ne talakawa tilis kuwa amma ai wannan ba zai hana aure ba, domin baya cikin dalilan da suka hana a auri mace saboda shi." Anty tace Baba muje in raka ki, Baba ku na da ne bazaki gane ina lamarin ya sa gaba ba, yanzu ba duniyar ku bace irin ta da, yanzu sai dan yanzu, wake harka da talauci,ai ko a tafiyar kan hanya bana fatan haduwa da malam talaka bare aure wannan maganar babu ita ko me zai yi, ashe gara ma su Bilki su da dan abin karyar rayuwa ce tai musu yawa, karyar tafi arzikin na su yawa, wannan babu fa ake kira tab. Baba ta cika da mamaki, tace"Habiba yau she ki ka zama haka? " Anty ta yi yar dariya dama fa Baba baki sanni ba ganina ka wai kike yi. muje a kai ki ki hau adaidaita sahu ki koma gida ko menene kwa ji daga baya. Hafsi ce ta tafi saka Baba a Napep Anty kuwa kamar ta yi hauka domin ta kira Halifa ta gaji amma bai daga ba. Daidai lokacin yana gaban wanda ya buga musu kati suna magana kan cewa ya sake buga musu wani amma ya canza sunan. Sulaiman ya kira ya mikawa mai buga katin wayar tare da fadin fada masa sunan yarinyar nan. Bayan ya fada masa sai Halifa ya amsa yace yawwa ka sanar da mahaifin yarinyar nan goben zan zo da magabatana a ko wane lokacin daga goman safe zuwa azahar, ita kuma ka fada mata zan zo da dare ya kamata ko sunan ta in rike. Sulaiman ya sa dariya tare da fadin Halifa sai a barka. Insha Allah zan isar da duk sakunanka. Kiran Anty ya sake shigowa yana kokari kiran masu Hall da za ayi fati. Ya daga bai bari ta yi magana ba, yace Anty kiyi hakuri gidan fa zan kwana komai dare dole zan dawo bari na gama da kacaniyar waje, bai yarda ta furta komai ba ya katse domin yasan duk damuwarta ya yanke shawara kai tsaye bai tuntube ta ba. Ya fadawa wa masu Hall an fasa party su ba wani date din ya maida musu kudin su. Anty ta rasa inda zata sa kanta ta danno number aminiyarta Hajiya Talatu domin neman dauki na shawarar abinyi cikin gaggawa. Hajiya Talatu ta kalli sunan dake kan screen din wayar Sahiba ta furta tare da kallon yarta Ma u, tace "Ga matsiyaciyar nan tana kirana duk yadda aka yi neman fatawa ta zo, ai Habiba in har ta ci gaba da nuna min cewar bata gane wai ke nake son Halifa ya aura ba sai na koya mata yadda ake duniya." Ma u ta taɓe baki Mama tace" Bar yar hau sai jininta ya yi sama zan daga in ta kira kamar sau biyar." Ma u ta sheke da dariya, tace Mama da Sahibarta. Hajiya Talatu tace yar Hassada ce tuntuni ta ke aiki akan Halifa wai kar ya yi aure sai wadda ta zaba masa tun ina shuna mata ke cikin Hikima har na furta mata cewa a hadaku kai tsaye ta ce bazakiyi masa ba, abin yamin ciwo amma na danne kuma abinda bata sani ba, wannan auren da Halifan zai yi tuni na saka Malam na shuri ya tarwatsa komai na san ma yanzun kiran nan labarin fasa auren zata bani da neman yaya zata yi. " Ma u tace Wai shi Halifan ba kaninta bane me ya sa ta ke masa haka? Hajiya Talatu tace, ' Dalilin da yasa na ke son ya aure ki ya kamata ki tambaya, kuma shine dai dalilin ta na hanashi auren sai ta nemo wadda ta ke so, dafa zai yiwu Hafsi zata bashi, dan dai muharraman juna ne. Ma u tace Wai duk menene dalilin ku? Hajiya Talatu ta dauki wayar ina zuwa bari in daga yanzu na san tana wuya. Cike da barkwanci tace Sahibata yi hakuri kin kira ina salla banyi la asar ba ga magariba ta doso kai. Anty ta ja tsaki "Wai yau she zaki tsaida sallah ne Sahiba. Ni ba wannan ba, kinsan auren Halifa ya wargaje?" Hajiya Talatu ta dau salati tare da danna Hansfree domin yarta Ma u taji. Anty ta ci gaba da fadin "Menene a bin yin salati ni ai gaba ta kaini dama ni na saita hakan kuma hakan nake son ya faru. Sai dai wata masifar yanzu haka ya kai kayan gidan su wata wadda ban santa ba, ya kuma ki sauraro bare. ma in fahimci komai dan insan ta ina zan bullo masa in ya shigo gidan." Hajiya Talatu cikin mamaki tace Wai shi wannan yaron wane irin raini ne a tsakanin ku haka, na rasa sam bai maidake a bakin komai ba wallahi, banda haka ya Isa ya yanke irin wannan hukuncin kuma cikin gaggawa. Wai in tambaye ki Sahiba, kin yi masa aikin gurin Malam na daji kuwa? Anty ta ja tsaki "Shin wai kin manta Halifan ne gurin Malamai nawa muka kai shi da ke, amma kamar ana shuka dusa. furar da Malam na kauye ya bani in dama masa, da yake gwanin fura ne a gabana ya shanye ta amma dan nan ko gezau." Hajiya Talatu tace kira Malam na kusfa ya yi miki binciken gaggawa yanzu ki samu bayani, kinsan shi maza maza ne. Nima bari in kira na Shuri yanzu. Anty tace." To kirashi kin dai ki hada ni da shi. " Talatu tace Zan hada ku bari a gama wannan badakalar. Suna kashe waya Anty tace Matsiyaciya muguwa sai na gano shi in ma baki hada mu ba, kuma sai na gano dalilin ki na kin hadani da shi. Itama Talatu a nata gefen cewa ta yi Bazan hada din ba mai mugun hali cinnaka baka San na gida ba, ni ce maganin ki. Anty ta danna kiran Malam na kusfa a rude take fada masa cewa ya yi mata istihara yanzu a kan kaninta Halifa ta karanta masa komai yace bani mintuna, ta sake kiran wani malamin ta sanar da shi. Malamai ukun duk sun bukaci sunan yarinyar ko na Mahaifiyarta. rashin sanin sunan ya kawo tsaiko game da binciken dole sai zuwa gobe in Halifa ya shigo ya fada mata sunan domin kowa ya ce mata ya ga auren Halifa Amma baiga matar ba. Halifa ya shiga gidan cike da gajiya ga damuwar abinda Bilkisu ta yi masa, ya kalli bangaren Anty bazashi yanzu ba ta kara masa wani zafin bandaki ya fada ya sakar wa jikinsa shawa sanyin ruwan ya ratsa shi, Har ya ji kamar zazzabi zai rufe shi ya fito ya dauki jallabiyya ya zura, ya nufi gadon sa zai kwanta idanunsa suka sauka kan hoton Bilki wanda ya kafa shi domin sanyaya idanunsa a duk lokacin da ya kalla. Ya isa gurin hoton cikin rangaji ya sa hannu ya ciro. kalamanta suna kaikawo a zuciyar sa ya nufi kwandon shara zai saka ya yin da wasu hawayen takaici suka sulalo akan kumatun shi. Kafadar shi ya ji an dafa lokaci guda kuma ta soma magana. "Dan uwana ka bani zuwa gobe zan gyara komai tsakanin ka da Bilki tunda ka zubda hawaye a kanta lallai sai ta karbi hukunci, ina son ka auro ta kuma ka rama abinda ta yi maka." Ya dubi Anty bai ji ko matsin ta ba bare takun ta,sai kalamanta da suka dirar masa. Ya sa hannu ya sauke nata hannun a Kafadar sa Sannan yace Kar kiji cewa kin damu Anty, bana bukatar cutar da ita, na gode da hasashe ki domin kadan ya rage inyi kitso da kwarkwata na samu madadin ta ina hasashen alkhairi ga sabuwar yarinyar da na kaiwa kaya kuma zai tabbata khairan insha Allah. Ya kai karshe maganar tare da zama bakin gado. Anty tace "Halifa ina kasan wannan yarinyar mecece nasabarta, menene matakin karatunta, wace gogewa gare ta game da duniya, wacce yadda kai mata?" Ya zame ya kwanta, tare da fadin duk ba sune a binda ya kamata in duba ga uwar 'ya'yana ba. Ta kara matsowa" Halifa ka tashi muyi magana ban amince da wannan huce haushin da za ka yi ba, kai ba mijin kowace irin mace bace, kana da bukatar macen zamani yar gidan girma." Ya tashi da sauri ya dauki makullin mota dake kan durowar gefen gado tare da fadin, zan nemi wani gurin in kwanta ko hotel haka dan ina son zafin da kaina ya dauka ya sauka ko zan samu bacci. Da sauri ta nufi kofa dan tasan halinsa ficewa zai yi, tana fadin yi kwanciyar ka da safe zamu yi magana domin bazan laminta ba. Har ta kai kofa sai ta tuna sunan yarinyar tazo tambaya, dan Haka ta tako ta dawo, to "Wai ya sunan yarinyar ne ma? " Cikin kagara yace ban rike ba Anty amma kamar Sadiya ko wa, ina ga kamar haka. Tafice cikin sauri. *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: *🧳 HASASHE🧳* *Sabon littafin* *HALIMA ABDULLAHI K MASHI* *Page 3* *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* Daga sallar asuba Halifa ya wuce gidan Baffan sa Alhaji Ali wanda babu nisa mai yawa da gidan nasu, kanin mahaifin sane wanda shine ya rage masa Uba duk sai Yayinsa wanda suke uba daya a bangaren Mahaifinsa. Kamar yadda ya zata ya same shi yana karawa wa su dattijai karatu ya zauna gefe yana sauraro Har suka gama, ya sallame su, sannan ya dubi Halifa yace " Umaru kai ne da safe Haka?" Halifa yace ni ne Baffa, ya gaida shi cikin girmamawa sannan ya soma magana akan abinda ya kawo shi. Baffa zuwa na yi in sanar da kai anjima kamar sha daya in ba wani uzri zamuje kai da Dady Mijin Anty gidan su yarinyar da zan aura. Baffa Ali ya dube shi. " Lokacin daurin auran za a ɗaga ne, naga sai rana ita yau ne, koko wani abin ne ya taso?" Nan dai Halifa ya zayyane wa Baffansa komai game da matsalan su da gidan su Bilki da kuma canjin da aka samu na Asiya. Baffa yace "Wannan dalilin ya sa yanzu maza ke kai lefe in da mazane ba za a tsaya wannan shirme ba, to sai muce Allah ya sa hakan shine alkairi sai mu tafi kamar shadayan ya yi." A hanyar Halifa ta komawa gida ya kira mijin Anty a waya ya san lokacin basa tare da ita ya sanar da shi sha daya zasuje gidan surukansa. Hafsi ta kawo masa karin kumallo bayan ta gaida shi tace " Anty tace tana jiranka" . Ya dan kurbi kunun kadan sannan ya ce ki fada mata sai na dawo tukunna. Anty ta kalli Hafsi me yake yi to? Hafsi tace na dai same shi yana danna waya ne, ta mike bari ni inje. Ta same shi yana kokarin shiga wanka, ta kalli wayar shi da ke ta ringing ta ce, "Ka daga mana." Yace barta Bilkisu ce tun asubahin fari take kirana kuma ni na rufe shafin ta inna zauna ma zanyi blocking din number ta ne, gaba daya. Anty tace "Haba Halifa, ka sawa zuciyar ka salama mana, yanzu ya ake ciki ne?" Ta yi maganar cikin sigar lallashi. Yace game da me kenan? Tace kajika, maganar yarinyar nan mana aikwai bukatar ka nutsu ka yi adduo'i kafin ka fadawa wata maganar auren. " Halifa ya dube ta Anty a wannan karon gaskiya sai na yi aure, abin ya isa haka kadan ya rage in kai arba in, dubi Adam Bros nafa girme shi amma yaran shi biyu, auren kawai nake bukata da koma wacece indai sunan ta mace, an wuce gurin sai wance da sauran su. Anty tace "Kaji ka da zaka kawo batun Adam shi da ya yi gaggawar yanzu ina matar ba sai yaran ba, kuma hakan dadi ne? Matar sa fa zagina ta yi kasan komai nace kuma sai ya sake ta. Ta saki huci sannan ta danne zuciyar ta ta kuma tausasa murya. Ta ci gaba da fadin" Halifa ka san dai kai kanina ne maraya ne kuma amana a gurina, duk da ni na Haifi Adam wallahi na fi son ka akan shi, kai ne wanda na fara raino kafin shi, bana son abinda zai cutar da kai yin hakan cin amanar da mahaifiyar mu ta mutu ta bar min ne a tsumman goyo." Ta soma shashshekar kuka. Halifa ya numfasa. Karki damu Anty nima Kallon mahaifiya nake miki, nasan kina kokari a kai na. Ina son kiyarda da batun yarinyar nan ina yi mata Hasashen alkairi. Ta ce shike nan" Ina son ka kaini gidan su yarinyar in gani ko zan samu natsuwa. " Yace shike nan. Ta fita tana fadin Allah ya yi albarka. A fili ya furta Anty bazan kai ki ba hakuri kawai zakiyi. Mijin Anty bai sanar da ita komai ba game da inda za suje domin tunjiya ta ke yi masa mitar abinda Halifa ya yi, shi kuma a nasa gurin yana kallon Halifa a matsayin wanda ya san kanshi kuma duk abinda Halifa zai yi yana da tabbacin abin nan yana kan daidai. A mota Halifa ya sanar da Dady Mijin Anty komai. Dady yace ai kaima da baka tsaya biyewa Antynka kuka yi wani gwaji ba, sai dai tunda mai aukuwa ta auku sai muce Allah ya sa hakan ya zama alkairi. Baffa yace ai maza ke kai kaya na fada masa dazu. fatanmu dai wannan din ya zama alkairi sannan tunda yace Fage ne ina da wani aboki na da mukayi harkar goro da shi a kurmi iyayen su sune suka kafa unguwar na tabbatar zan samu cikakken bayani game da yarinya da kuma iyayenta. Mijin Anty yace yawwa nima dai ina son a samu dan wani bayani game da yarinyar duk da nasan Halifa baya abu da ka. Ko tak Halifa bai furta ba A kofar gida suka samu Sulaiman domin Halifa ya sanar dashi da suka taso. An saka shimafida a soro inda mahaifin su Asiya ya dogaro ya fito ya zauna, ya tarbi baki cikin fara a da murna duk da yana cikin yanayin rashin lafiya mai tasanani, ya umarci Sulaiman ya sanar da mahaifin sa da daya makocin na su cewa bakin sun iso domin tun Daren jiya ya tura mahaifiyar su Asiya ta sanar da makotan zuwan bakin, bayan ya samu labari daga bakin Sulaiman. Kamar arashi sai gashi ashe Abban su Sulaiman shine abokin Baffan su Halifa da yake maganar zai nema, dan haka Baffa ya ce shike nan kaya ya tsinke a gindin kaba ai muna tahowa yanzu a hanya nake tadin ka. Baban su Sulaiman yace "Yace ashe ni abin duk nawa ne, dama shi Halifa nasan shi duk da bansan iyayenshi ba yaron kirkine abokin dan waje na ne, ko azumin da ya wuce ya kawo min kayan shayi. Ita kuwa yarinyar kamar diyata haka take." Baffa yace Allah sarki, hakika Halifa dana ne wanda dan uwana Alhaji Umaru ya haifamin ai sunan mahaifinsa yaci, domin kwana uku da rasuwar mahaifinsa aka haife shi, kafin a yaye shi kuma uwar ta rasu sai rukonsa ya koma hannun wannan bawan Allahn ya nuna Mijin Anty ya ci gaba da fadin shi wannan ya auri Yayar Halifa ko wata biyu ba su yi ba, ita kuma Uwa suka hada da Halifa su shida ne Ubansu ya mutu ya bari rabon Halifa sai Uwarsu ta auri Dan uwana Alhaji Umaru shine aka samu Halifa to kunji yadda muke da Halifa. Wannan ne Ubanshi duniya bashi da sama dashi, amma yana da yan uwa su shi da suke uba daya amanar da ya rika yasa ko dukiyar Halifa da aka raba gado gaba daya muka basu, kuma har yau bamu taba jin wani korafi daga Halifa ba. Yaro kuma gashi yanzu ya zama mutum. Mijin Anty ya yi gyara murya, yace "Gaskiya dai Halifa dana ne, domin ko Adamu dan nawa bani da shakuwa da shi kamar Halifa, duk inda ka ke neman Yaro dan albarka Halifa ya kai. Fatanmu Allah ya sa a kulla alkairi. Baban su Asiya ya ji dadi kuma ya tabbatar musu ya ba Halifa auren Asiya ya kara da cewa ko bai kai rana ita yau da rai ba yana rokon karsu daga auren daga wannan ranar su tabbatar sun ba Halifa matar sa. Nan dai suka yi adduo'i aka shafa bayan sun bada kudi dubu dari biyu harda sadaki. Halifa da Sulaiman suna zaune a dakalin kofar gidan su, suna kara tattaunawa game da batun daurin aure har suka yi yar gardama kan batun fati Halifa yace na saka su maido muku kudin ku, dama waccan yarinyar ce ta matsa. Sulaiman yace "To wannan ai bakaji ra ayin ta ba. " Halifa ya ce na yi hasashe a kanta bata bukata amma ka fada mata zanzo anjima da dare, inna zo na tambaye ta lokacin in tana so zan mata. Sulaiman yace to ai shike nan. Suka fito inda suka raka su har mota. Anty tana idar da salla ta kira layin Malami na farko danjin sakamakon bincike. Ko gaisawa basu yi ba tace Malam yaya? Yace "Kedai ban taba ganin mai wutar ciki irinki ba, to gaskiya sunan da kika bada na Sadiya babu wata alaka ta aure sai dai kuma ga auren nan yana tunkarar sa wanda ba wani abu dai zai dakatar da shi." Tace ka bincikami taurarin wadda zai aura din da kuma yadda auren zai kasance. Yace na yi yunkurin haka amma ban iya gane komi ba, kila da a kwai sunan yarinya sai mu fahimta sunan da kika bada kuwa in har itace to sam tauraron su bai zo daya ba, kuma arzikin sa zai karye,abinci sai ya gagare shi. Sai dai ita kamar yadda na fada miki ba muga aure a kanta ba. A gigice ta kira sauran malaman suma dai kusan bayanin daya ne sunga aurensa amma ba su ga na yarinyar ba. Dole ta tafi gidan Hajiya Kaka dan ta watsa wuri ta yi bincike a gaban ta kuma ta dakatar mata da auren. Tana shirin fita Mijinta yana shigo wa yace ina kuma zaki yanzu? Ta bishi da kallo daga ina kake kuma yau she ka fita? Yace " Kina can kina baccin asara na fita.,kuma daga gidan surukan Halifa muke mutanan kirki sun bashi yarinyar. " Tace to be karba ba, nifa ba zan yarda da auren yar matsiyata ba kuma kilama baƙi ne tunda naji an ce Fage ce unguwar ta su. Dady Yace wallahi ba matsiyata bane, yana da kyau ki gane arziki daban da kudi, sannan maganar baƙi a kano ke ki fada min tushen ku,? Ajiye batun wannan ma har akwai wani mutum a duniya wanda ba bako ba, wadanda a kayi duniyar domin su ina suke yanzu ke da har abada bazaki canza ba, ina son ki sani zaki iya duk abinda kike so, amma abinda Allah ya yi shine kadai wanda zai wanzu. " Ya wuce ya barta tsaye cike da mamakin Dady, kenan shima aikin da ta yi akan sa ya yi kasa, lallai a kwai bukatar sabunta aiki domin yana da ga cikin wanda za su bata matsala. Hajiya Talatu da Ma u suka yi sallama Har cikin falo ba a amsaba da alamu basa nan. Ta zauna kan kujera tace da Ma u aje jakar kema ki ki zauna kila ta tafi shegen yawon malamnta yaran kuma kila suna makaranta. Tana zama Hafsi na shigowa falon tace "Oyoyo Hajiya ku ne da yamma haka, ta dubi Ma u Sis harda ke yaushe rabona dake tun bikin Bros Adamu." Ma u cikin murna tace shine ai nace nima sai nazo bikin Halifa. Hafsi tace "Ai dama bikin Uncle Halifan kuka zo sai rana ita yau fa? " Hajiya Talatu tace To zamu zo sayayya muka hada tafiyar ma yi zuwa biyu, kuma banda abinki suwaye abokan sharawar, kinga Hafsa je ni ki kawo mana abinci mun kwaso yunwa da kishi. Hafsa tace "Aiko sai dai a dafa muku taliya dan dazu yarannan suka cinye ragowar abincin rana da za su islamiya. Ta dubi Ma u zomuje mu dafa." Hajiya Talatu tace taliya ba wata tsiya ba sai an mata gayya kije ki dafa mana Ma u tasha gajiyar mota daga Zariya zuwa kano lafiya ba ne. Hafsi ta wuce tana kunkunan cewa nifa shiyasa na tsani matar nan wallahi ta zo gidan ku ta kama yi maka iko, masu shagen kwadayi. Ita kuwa Hajiya Talatu ta kalli Ma u, tace tun yanzu zaki fara baza kafasitin ki a gidan nan domin ke ce zaki auri Halifa kuma shine gidan. Kinsan fa wannan gidan daya daga cikin gidajansa ne suke zaune, Haka gidan da Adam danta ya sa matarsa kafin ta sa ya sake ta. Haka kudin Halifa Adam ke juyawa a kasuwar kwari sannan shi kanshi Dadyn na su store dinshi na singa ai dukiyar Halifan ce gidajansa ance sunfi a shirin na haya domin komai da ki ke gani nashi ne. wannan ce amsar tambayar ki ta rannan, shine dalilin da yasa nake son ki auri Halifa, kuma shine dalilin da yasa ita Habiba take son sai wadda ta ga dama zata aura wa Halifa. A haka ma ta boye min wasu abubuwa fa. Ma u ta mike ta yi rawa tace "Allah ya nuna min in auri Halifa duk sai na yi maganin kowa wallahi. " Sai sun tashi a gidan nan. Hajiya Talatu tace abinda ya sa muka zo gidan nan da wuri saboda ki aiwatar da abubuwan da Malam na shuri ya bada, kuma ki natsu ki yi su cikin hankali kar a samu kuskure, sannan ki hada da kirsa. Hafsi ta kira Anty a waya yafi sau Talatin amma bata daga ba, dan haka ta dafo musu farar taliya da mai da yaji. Hajiya Talatu ta ce "Lallai Hafsi mu zaki ba mai da yaji kamar yan iska?" Hafsi tace ba kayan miya ne ta wuce warta dakinta sai lokacin Anty ta kira, tana dagawa ta soma yi mata fada. "Kiran uban me ki ke min ne?!! Kinsan a tashin hankalin da nake ciki kuwa ance min masifa zata sauka min a gida ina nan ina ta fadi ta shin ganin na samu mafita ke kuma kin ishe ni da kira. Hafsi tace " To ai masifar har ta sauka ina ta kira kin kasa daga wayata." Innalillahi wuta ce ko mutuwa aka yi? Hafsi tace kawarki ce Hajiya Talatu da Yarta Ma u suka iso da katuwar akwatin su wai sun zo bikin Halifa. " Anty ta kasa magana dan mamaki wato dama Talatu ce masifar da Hajiya Kaka mai wuri ta fara gani tana watsa wurin ta na bincike. Hafsi ta katse mata tunani da cewa kin taho ne.? ' Humm na taho lalai tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkairi ba.... *ƘARSHEN FREE PAGES* *Zaɓi biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: Fage 4 Kafin Anty ta karaso tuni Hajiya Talatu ta yi wa kanta masauki a dakin Anty Har ta cire kayan jikin ta ta dauki zanin wankan Anty ta daura, zata fada bandaki ta ji sallamar Anty, da yake munafukan juna ne nan suka hau ihun murna kowace tana fadin sahiba ta ga sahiba. Idan matan nan biyu suka hadu ko shedan nasan gefe yake komawa ya yi kallo, domin dukkan su sunfishi hau. Nan suka zube a kan gado suna hirar yau she gamo tare da nuna kewar juna, Anty ta yi ta nuna jin dadin wannan zuwa da Sahibar ta ta yi. Tace ai kin fi min yan uwana su hudun duk mata ne amma ko kai lefen Halifa ba su zo ba, ke ko ganin kayan ba su zo ba. Hajiya Talatu tace,, "Watsar da su ai gani, sai ranar biki su zo su ishemu da kararrafi." Sai kuma suka bige da labarin dangin su kowa yana aibata na shi suna zagin su. Halifa ya shirya tsaf cikin shadda mai ruwan siminti ya kalli madubi ya so ya saka hula amma kanshi ya yi masa nauyi tun da ya sako kafarshi gidan, ga wani bacin rai da ya ke ji kamar ya hau kowa da zagi. Cikin zuciyar shi yake nanata La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin. Ya sani duk bacin ran da Bilkisu ta haifar mishi ne, amma ko ajiyan baiji irin wannan yanayin tabbas ba. Ya fesa turare ko ma me yake ji dole ne yanzu ya tafi gurin yarinyar nan dan suga juna, domin yanzu in aka sata cikin wasu matan kamar ta ba lallai ya gane ta ba. Ya fito yana rufe daki kamar daga Sama ya ji sallama a bayan sa, muryar mace ce dan haka bai amsa ba kuma bai jiyo ba saida ya gama kulle dakin, yana jiyo wa ga mamakin sa sai ya ga ta feso mishi wani gari kamar hoda, da sauri ya rufe fuskar shi tare da fadin a'uzu bikalimatillahi tammat min sharri ma kalaka. Ma u ta kyalkyale da dariya "Ango nice fa Asma u, ka tsorata ne hodar angwanci ce fa na fesa maka irinta al adar garinmu." Ya bude fuska ya kalle ta rai bace. Ya daga murya "Ke wacece da zaki zo kina min irin wannan wasan ni sa an ki ne? Tace "Yi hakuri ta juya da gudu ya bita cikin gidan inda ya samu Hajiya Talatu da Anty a falo. Ko sallama bai yi ba ya dubi Anty Wace irin mara tarbiyyar yarinya ce ta shigo gidannan ta zo tana watsamin wata hoda wai wasa, da wa nake wasa a gidan nan har ita tasamu irin wannan damar!! Anty ta mike, cike da fargaba da kuma zargin Hajiya Talatu. Tace Halifa nutsu ka fada min me ya faru? Hajiya Talatu ta yi caraf yanzu haka Ma u ce, Sarkin tsokana al adar mutan garinmu ta yi maka, ka yi hakuri. Halifa ya kalli Hajiya Talatu dan Allah ki gaya mata ita mace ce ya kamata ta kama kanta, amma ni in har ta sake yimin irin wannan haukan to zan mata jahilci. Ya juya ya fice ya koma ya bude dakinsa dan gyara jikin sa. Anty ta kalli Hajiya Talatu ta ce Sahiba da wace fuskar kuka zo gidan nan? Talatu ta yi yar dariya "Wai har kin saka wani tunani daga dan wannan wasan Sahiba? To zuciya daya muka zo kuma lafiya zamu rabu." Anty ta soma kwalawa Ma u kira ta zo da sauri tana dariya kamar wata sakarya tun kafin Anty ta tambaye ta har ta soma zuba, Anty na ba Uncle Halifa tsoro ashe haka yake da fusata? Tsawar da ya yi min har yanzu hanjin cikina bai kwance wani kulli da ya yi min ta nan gefen ba. "Da Allah yi wa mutane shiru! Anty ta daka mata tsawa. Indai ma wani tunani ki ke akan Halifa to ki sani ba irin mace da yake so bace ke.!" Hajiya Talatu ta danne fushi da ke son ta so mata. Anty ta sake fadin "Ina mai gargaɗin ki da babbar murya daki bar bala i ya yi bacci, ki bar hanyar dakin shi har kubar gidan nan ke rashin kamun kan naki ko a ina sai kin nuna shi?!" Ma u ta zo wuya ta kalli Mahaifiyar ta sai ta girgiza mata kai, sannan ta yi mata alama da ido wai ta bada hakuri. Dan haka cikin sauri tace Kiyi hakuri Anty bansan zaiji haushi ba. Ta kalli Hajiya Talatu Mama ki bata hakuri. Hajiya Talatu tace, " Ba zan bata ba, ai dama zane ki tayi ko shi Halifa ya daura miki mari kinga Ma u bana son dibar albarka ai da nasan haka zakiyi bazan taba zuwa dake ba sakara da Allah wuce mana a nan." Anty ta cika da mamaki domin wannan ne karo na farko da Sahiba ta yarda yarta ta yi ba daidai ba. Dan haka ta saka a ranta cewa da walaki goro a miya domin banza bata kai zomo kasuwa. Dan haka dole ta baza idanu ko ta ina dan kula da abinda Sahiba da yarta za su aikata mata a gida. Kalaman Hajiya Kaka suka dawo mata inda take cewa ga wata masifa nan zata sauka a gidan ki, gobara daga daji maganin ta sai Allah. Hajiya Talatu ta mike ta bi bayan yarta, bari in je inci kaniyar ta. Ta katse wa Anty tunani. Anty ta taba baki in ma lallashinta zaki je ku dai kuka sani. Hajiya Talatu ta samu Ma u tana kai da kawo a cikin dakin Hafsi inda nan ta kwana. Ma u ta tari numfashin uwar da cewa amma Mama kina jin irin bakaken maganganun da matar nan ta yi min kuma wai ke ma ki ka biye mata. Hajiya Talatu ta yi kasa da murya tace "Dadina dake gaggawa, Ma u shifa yaki da ki ke ji da gani dan zamba ne. Kar wannan abin ya daga miki hankali nan gaba kadan komai zai dawo hannunki sannu a hankali sai kin rama duk wani wulakanci da kowa ya yi miki. Yanzu fada min kina ganin ya shaki wannan hodar? " Ma u tace duk da dai ya sa hannu ya tare fuskar sa amma har atishawa naga ya yi, wannan ke nuna ya shaka. Hajiya Talatu tace angama sai mu jira sakamako nan da gobe. Asiya tana yanka awara ta kalii Sadiya tace, Maman Annur kinji wai anjima abokin Yaya Sulaiman zai zo da bayan Isha i. Sadiya ta sa dariya tace "Mijin ki zaki ce." Inna tace to ai da baki yi awarar ba me ya sa baki fada ba? Asiya tace to zamu fasa yin abinda zamu samu abinci? Ni ina ganin ko Abba zai iya zama ya siyar min idan ya zo. Inna tace shike nan in kin shigo sallar Ishai sai ki jira shi a gida kar ya same ki gurin suyar. " Asiya ta ce to. Sadiya tace" Inna a ciro mata dan turare a kayan lefen nata ko? " Inna tace e mana har da Hoda da janbaki. Murmushi Asiya ta yi a zuciyar ta tana kara sallamawa ga lamarin Allah. Wai ita ce yau zata yi aure wadda ko saurayin bata da shi, wadda yan matan layi suke mata Kallon kazama, gashi ita ba wata kyakyawa ba sirantaka kuwa wasu har ce mata suke sullen kara. Masu tura kurar ruwa sunfi nuna suna sonta wasu ma da lalata. Sai gashi jiya zuwa yau Allah ya kawo wani sauyi nan take. Tana ta sauri ta kwashe awarar da ke cikin mai ta. tashi ta shiga gida domin ga shi can ana ta salla a massalaci. Tana cike da tunanin yau yanmata layin su sun bata mamaki sai zuwa suke suna tambayarta Wai lefenta aka kawo yau she ne bikin? Har da masu cewa ta kawo masu ankon in an fitar. Hakan ya sa taji ashe ita ma takai. "Nawa awara?" Aka katse mata tunani da tambaya. Uku Hamsss ta kasa karasawa lokacin da ta dago ido ta kalli mai tambayar ba zata tantance saurayin nata ba, amma wannan taga ya mata kwarjini ya kuma cika gurin. Ya tsuguna ya dauki guda daya, tare da fadin." Akwai alakoro kasuwa?" Ta sunne kanta a cinya sannan ta tashi da gudu ta nufi cikin gida. Sadiya ta taimaka mata ta gyara duk da wata zuciyar tana tambayar ta cewar tana da tabbacin shine? Ta fesheta da turaruka ta yi gayunta cikin atamfarta raifes ta sallah ce. Sadiya tace to kije zan zubawa Abba awarar ya kawo masa. Inna tace ga hamsin yazo ya amso fiya wata me sanyi gida Maman Huda. Asiya ta kalli dakalin bayan ta fito. Yana zaune yana danna waya hasken fitilar kofar gidan ta haske masa fuska. In banda Allah wa zai maka Haka. Asiya ta darsa a zuciyar ta. Tasan ko kusa da ajin wannan gayen bata zo ba. Ta taka a hankali ta isa gurin ta rusuna sannu da zuwa. Ta furta tana Kallon fuskarshi dan samun tabbacin ko shidinne.. Ya Kalle ta "Tashi mana ammmm Sadiya ko?" Tace Asiya dai Sadiya yayata ce. Yace sorry tashi Asiyatu. " Yanzu kam ta tabbatar shine. Ta zauna da yar tazara tsakanin su. Ya kalleta "Asiya ya jikin Baba ina fata yana samun sauki?" Tace so sai ma kuwa musamman jiya zuwa yau tamkar ka zo masa da waraka Muna ta yi wa Allah godiya. Ya yi murmushi ashe tana da magana haka. Ya darsa a zuciyar sa. Sannan yace, "To Malam Asiya ya ki ka ga angon na ki?" Ta dan yi murmushi sannan ta sunkuyar da kai, tace me kake son infada? Yace Duk abinda ya zo bakin ki. " Ta danyi jim wani jin kai wanda bata san tana da shi ba ya motsa ta saci Kallon shi ta ga ita yake kallo, tace masha Allah barakallah. Ya yi murmushi ya ga wani hali guda daya da yake so, yana son mace mai jin kanta cewa ita mace ce, yarinyar in ta samu kula zata yi yadda yake so. A zuciyar sa yace Bari ya sake latsata. Ya dan yi gyaran murya. "Na yi mamaki fa wai ya akayi kika amince da ni haka? Da ga ganina fa baki sanni ba." Ta danyi jim tana nazarin me zata fada, can tace Duk abinda na roki Allah a kai yana amsa min. Kullum Babana yana cewa "Allah ka kawo wa Asiya da Sadiya miji wanda zai kula da su ko bayan raina. Kasan ina girmama kalaman Babana jin haka sai nima na dora da adduo'in ina rokon Allah ya cika burin Babana ya kawo min mijin wanda yake zabin sa shi. To kana ganin cewa ba kai ne amsar addu a ta ba? Ya yi murmushi Ni ne gaskiya domin ba zance ga dalilin da yasa na yi miki maganar aure ba, Allah ne ya aiko ni, to kuma kina so na?" Tace Ni ban san so ba, amma zaka iya yimin bayani yadda ya ke. Yace shike nan zan koya miki "amma sai na cire son wata a zuciyata." ya tsura mata ido. Itama ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kai. Tace" To. " Abba ya yi sallama ya aje flas din awara da fiya wata a Leda. ya gaishe da shi ya amsa tare da tambayar kai ne Abba? Abba yace,"Nine. Halifa ya ce to Malam Abba maida wannan abin gida naci dazu." Ta kalleshi. baza ka kara ba? Ya girgiza kai, tace shikenan Abba wuce da shi amma ka aje masa ruwan. Ta ciro daga Leda ta mika mishi, wani abu da yake ji tun da ya shaki wannan hodar ya kuma taso masa, ya danja tsaki sannan ya ce" Ki barshi . " lokaci guda kuma ya mike tsaye, ina ga zantafi ina jin kamar bana jin dadi." Gaban Asiya ya fadi. Allah dai yasa ba ni ce na bata maka rai ba. Ta fada cikin damuwa. Yace ko kadan ya cije game da sabon yanayin yace "Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida, haka Hausawa suke fadi ko?" Asiya ta marairaice murya tace Yaya ban iya hira ba ko? Ta. mike ita ma, ka yi hakuri ban taba zance bane amma zaka koya min? Yace "Ai zancen mu bashi da tsawo ya kamata daga yau ma a dena wanna awarar a soma gyaran jiki ko?" Ta ce to duk yadda ka ce. Ya soma tafiya tare da fadin dan takamin mana." Suka jera a hankali suke tafiyar yace Wai kuwa kina samun nawa a rana wannan awarar? Tace "Gaskiya muna samu, har dubu biyu fa wata ran muna ci a kwano daya, kai ko anyi kwantai fa muna samun abinda Baba zai ci mu kuma sai muci awarar ka san ba kowane abinci yake ci ba. Wataran kuma sai Maman Annur Sadiyarmu tana zuwa da abincin da zai iya ci daga gidan aikin ta sai musaka kudin sai masa abinci a bankinmu na kudin maganinsa. Yace Allah Sarki Ubangiji ya baku lada, ku kuke ta fama da gidan da kudin jinyarsa, ba masu taimaka wa ne a unguwar? Tace "Sun yi fa, yanzun ne kowa yana fama da kanshi, kuma gaskiya ni nafi son mu yi sana a da mu tsaya neman taimakon." Yace Haka ne yanzu kuma gashi zan dauke ki wa zai ke yin awarar? " Asiya tace Abba zai ci gaba ko don kula da Baba, ta fada a rauna ne, domin sai taji wani yanayi na kewar rabuwa da ahalin ta. Daidai lokacin sun Iso shagon saida kayan masarufi ya ce ina zuwa, ya shiga, tana bakin shagon daya daga cikin masu saida kayan yace " Asiya waken awara kwano nawa? " Tace ba siya na zo ba yanzu. Yace "Asiya Wai ance za ki yi aure da gaske ne?" Tace injiwa? Wani daga ciki ya am she da fadin gaske ne mana, har lefe an kawo. Wanda ya yi tambayar yace harda su lefe abin azimun amma waye wannan haka zai yi jihadi?" Sai lokacin Halifa ya sa baki don tunda suke magana bai ce kala ba yana dai ta fadin a miko masa wannan nawa wancan. Yace Ba musulma bace dama? Suka ce Musulma ce yace me ya kawo batun jihadi? Wanda ya furta kalma yace to Megida duk yan matan garin nan ga sunan kosassu wannan kalleta fa kamar ka hureta ta fadi, anya ma ta isa aure? Halifa yace " Ina dai tana da halin kwarai?" har suna hada baki gurin cewa wannan kuma sai ince kaf unguwar nan da wuya asamu wadda tafi yarinyar hankali ga nutsuwa inda wata ce muna fara mata wannan wasan kasan da yanzu ta zage mu. Halifa yace "wannan ai ba wasa bane, kuma ni ne wanda zai yi jihadi da ka ke magana, ni ne mijin Asiya sai ka duba ka gani dame ka fini kai da kake kushe ta?" Mamaki ya ishe su, duk harda masu siyayyar suka kalleshi babu wanda ya kara magana cikin su sai wani da shima ya zo siyayya yace Allah ya sanya alkairi. Kayan shayi da sabulan wanki da omo su makilin su ya siya da bread leda biyu ya biya su ya dakko. Asiya wadda taji duk ta muzanta a gaban saurayin ta an ci mata fuska kuma tanaji duk jikinta a sanyaye ta kalli fuskar Halifa. Tace kaji me mutane suke fada game da ni ko? Kamar bai ji me tace ba ya mika mata ledojin "Amshi wannan maza kije gida zan kira ki". Tace ai ba waya a gidan mu. Ya ciro wayoyin sa guda biyu ya mika mata babbar ki rike ta da kyau akwai muhimman abubuwa na aciki, zan kira ki. Duk wanda ya kira ki daga ki ce a neme ni ta daya layin. Tace To. Mun gode Allah ya jikan mahaifa ya kara budi. Cikin jin dadi ya ce "Ameen." Ya nufi can inda ya yi fakin ta kwashi kaya Niki niki ta nufi gida. Kafin Halifa ya kai gurin mota ya soma amai da kyar ya ke jan motar, yana ta amai. Yana shiga gida ya aje motar ya fito. Kanshi ya sara da ciwo ya nufi dakin shi, jiri na dibar shi. Yana kokarin ya bude kofa sai ya fadi a gurin yana maida numfashi. Yana son ya ciro Wayar shi daga aljihu Hafsi tana isowa gurin kamar yadda Anty ta turo ta ta duba mata ko shine dan taji shigo war mota. *** *** Bilkisu ta kalli mahaifiyar ta tace na gama jan Ya Wadudu kafa dubu kuma ba wanda na kuskure ban hada da sunan shi ba, yanzu saura sadakar kosan da zanyi da safe ko? Mahaifiyar tace e "Ai insha Allah gobe da kafarshi zai shigo gidan nan yana baki hakuri har sai kin ja masa aji." Bilkisu tace humm ya dai zo din Umma ko ban ja masa yanzu ba muna komawa daidai sai ya gane Allah daya ne, dan zan rama abinda ya yi min. Umma ta sa dariya "Sun isa su sani inji kunya Asa bikin shekara guda sai da lokacin ya zo ya fasa, aiko da na kai shi Human rayit su bi miki hakkin ki na bata miki lokacin da ya yi sannan ya hana ki kula kowa, ta ina zaki fara yanzu shekarun ki a shirin da bakwai fa dan ma muna zabge uku muna cewa ashiru da hudu ki ke. " Bilkisu tace ai Halifa ma ba zai iya rabuwa da niba, na fa san irin son da ya ke min, duk barazana ce. *** *** Hafsi ta juya tana kuka, da ihu ga Uncle Halifa ya fadi. Da gudu suka fito Hajiya Talatu da Anty shigowar Dady kenan ya dakko mota sai Asibitin. Likitan ya gama gwaje sannan ya sa a bashi taimakon gaggawa sai da aka gama tsaf yana kwance an sa masa ruwa. Ya dubi su Anty me ya ci na karshe? Duk suka yi Jim Anty tace sai dai kuma shine zai fada tunda daga waje ya ke. Dady ya kalli Likitan menene a cikin abinda ya ci?... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: Page 5 Likita yace "dole aƙwai abinda ya ci ko ya shaƙa ko kuma ya jima bai ci komai ba kuma yana da ulser. Halifa dake jinsu sama-sama har dai bacci ya yi gaba da shi. Hajiya Talatu ta kira Ma u suka fita waje, ta Kalle ta tace, Allah ya sa aikin nan bai baci ba, dan Malam bai ce mana zai yi jinya ba. Ma u tace "Ki kirashi mana, shi malamin." Uwar tace sai dai in tafi gobe kinsan na Shuri baya son daga waya a tsakiyar wata sai farko ko karshe. Ma u tace "To Wai saboda me?" Uwar tace Aljanu sun hana, Ma u kin kuwa binne layun nan? Tace " Tun yaushe Mama nifa yanzu jiran sakamako nake yi zuwa gobe. Tace to Bari mugani in ta kama sai na koma Shurin gobe zance zani Rimin kebe ko Wudil sai kawai in koma Zariya in tafi shuri. Ki koma ki kwanta kar waccan anamimiyar yarinya ta farka. Hafsi dake labe ta girgiza kai bayan taji komai domin lokacin da Uwar ta zo ta tashi yar Hafsi ba bacci take yi ba tana chatin ne a cikin bargo da saurayin ta. Biyun dare su Anty da Dady suka dawo Bros Adamu aka kira ya kwana gurin sa. Hafsi tana jin shigo war mota ta fita da sauri ta fara tambayar iyayenta jikin uncle Halifa. Suka ce mata da sau ki Sannan ta ja Anty gefe ta rattafa mata komai game da abinda taji. Tace banyi mamaki ba, domin na san ruwa baya tsami banza, matar nan da shirin ta ta zo. Shike nan kici gaba da samun ido sosai a kan duk wani motsin su. Tana shiga dakinta Hajiya Talatu ta baje tana bacci sai uban minshari ta ke saki, Anty ta harare ta ta ja tsaki Sannan ta wuce bandaki. Asiya ta ji waya tana ringing ga zaton ta shine duk da taga an rubuta favorite ba Wai ta iya waya bane, ta san dai koren shine dagawa. Ta daga da sallama cikin wata muryar da bata san tana da ita ba. Sai taji an katse ta da cewa "Ke wacece ke? Ta ce ni ce Asiya ki kira daya layin nasa. Bilkisu ta yi shiru ko zata tuna mai irin sunan a dangin su Halifa. Rashin tunawa ya sa ta danja tsaki tare da sake fadin " Ke yanzu me ya kawo wayarsa gurin ki.?" Asiya ta danyi jim tana tunanin ko yan gidansu ne. Bilkisu ta katse ta da fadin cewa "Ni matar sa ce ina miki magana kin min banza." Wani abu Asiya taji ya daki kirjinta matarsa kuma. Ta sauke ajiyar zuciya tace A iya sanina ni ce matar sa domin ya biya sadaki na, ko da yake ki kirashi ta daya layin kinga sai da safe. Asiya ta kashe cike da tashin hankali. Cikin dare Halifa ya farka bayan ya yi wani mummunan mafarki, Bros Adam ya gani yana zaune kan kujera ya kifa kai a jikin gado. Jin motsin shi sai shima Bros din ya farka. Ya yi masa ya jiki, ya amsa da sauki. Yace jiya naji zuwan ka ashe baka tafi ba bacci ya dauke ni. Bros yace "Ni ai mamaki naji kai da baka fiye yin ko zazzabi ba. ". Halifa yace Aii gara a dan dinga taba mu muma abin ne ya zo ba zato Allah ya kara mana lafiya. Kai kwana biyu bamu hadu ba, tunda aka soma hatsaniyar bikin nan ban ganka ba. Bros Yace "Munyi sabani na zo Anty take min korafin abinda ya faru, to bance komai ba domin kun fi kusa." Halifa yace au Haka ma zaka ce? "To me kake so ince Uncle Halifa, nan ka goyi bayan Anty aka wai dole saina saki mata ta, ina sonta yaran mu biyu amma aka kasa min uzri." Halifa yace Bros kaga dai Anty Yayata ce kai ta haifa ba ni ba ko? To mace ko yar uban waye zan iya sakin ta matsawar ta zagi Anty kamar yadda aka ce matar ka ta yi. Bros yace to ba komai ai gobe saurin zuwa gareta, baga dai auren zaka yi ba, Allah ya kade fitina. Yanzu bikin yana nan a lahadi din?" Halifa yace ameen. Yana nan insha Allah Wai kuwa ina wayata? Sai ya tuna ya ba Asiya sai karamar dake kusa da shi, yasan yanzu tana bacci ya dakko kirane Kala kala. Bros yace jiya har zan shigo kasuwar ku in duba wa Maman Nihal waya bakin kwastomomin mu na nijar ba su tafi da wuri ba. Halifa ya Kalle shi " Wai kai duk da kun Rabun da kyar Amma har hanzu kuna tare? Bros yace " Nifa na maida mata ta kuma tuni na kama mata haya yanzu ma cikin ta ya kai wata biyar." Halifa ya tashi zaune har yana yarda karfen dake dauke da ruwan da ake kara masa, Nus ta shigo da sauri tana ta bayar lafiya? Ta taimaka masa yace ta cire ruwan haka ya isa tun jiya ake dura min ruwan nan. Tace ka yi hakuri ya karasa, kafin ta rufe baki ya tuge allurar karin ruwan ya rataye, jini ya biyo baya. Bros yace kalli to abinda ka yi Uncle. Ya dafe masa gurin da yatsa. Ta kawo auduga ya manna ya dafe. Bros yace "Kai Uncle dan Allah ka rage wannan dabi ar mana ace shi mutum komai sai yadda yake so harda lafiyar taka ma sai ka yi wasa?". Halifa yace Amma dai Anty bata San ka dawo da matar ka ba. Bros yace "Sai dai ko in kaine zaka fada mata yanzu. " Halifa yace ai da kasan zan fada din baza ka fada min ba, amma ina tausaya maka duk radda ta sani. Bros yace Matata fa bata zagi Anty ba kawai Anty ta raina arzikin sune kamar yadda na yi ta kokarin fahimtar da kai, kuma wai ita ce ta yi silar karayar arzikina wanda kasan I yan damfarane ba kuma ni ka sai suka cuta a kwariba har Anty tana tutiyar wai yanzu da muka rabu gashi komai nawa ya dawo, bata san muna tare ba. Ta amshe Nihal da Nur a gurinta. Halifa yace Kabi a hankali mahaifiyar ka ce ka samu ku rabu lafiya. Amma ina jiye maka radda ta sani to yanzu ya maganar auren da take nema maka? Bros yace "Ni dai ba ina bita da to ba. " Halifa ya yi dariya shiyasa muka matsa ka dawo gida ka ki yarda? Bros yace Kai Anty in ta sako mutum a gaba sai Allah, harfa zuwan bazata take tayi akai akai gidana kamar tana zargin zata samu Aisha a gidan lokacin ma ban samu gida ba muna Hotel ai wannan cikin a Hotel muka yi shi, gidansu fa basu da labarin wani saki, kai Bari ma dai in bude ka a mutum lokacin da Anty ta matsa ta tsaya gaba na ita da wannan shedaniyar kawar ta ta ta Zariya wai in rubuta takarda a take in bawa Aisha a jikin takarta na rubuta cewa taje ta jirani a can wani kebabben guri za muyi waya. Ina bata ta karanta sai ta hau kukan murna su kuma sun zata saki ne suka kwashe yara suka wuce. Tun a ranar naje na kama mana Hotel na kai mata kayan ta ni kuma sai da safe nake zuwa inyi shirin kasuwa lokacin ne take zuwa Wai ta duba ko ta dawo Shine kai kuma ka bullo da zance wai in koma gida. Na ce kaji Uncle zai ha wata fitina. Lokacin kam na kashe kudin abinci ma ka dai ba sauki. Da Anty ta matsa su zo su kwashe Kaya sai na kama gida muka bi dare muka kwashe. " Cike da mamaki Halifa ke Kallon Bros. Yace to wace Unguwar kuka koma? Bros yace Kuntau na samu wani gida mai kyau" . Halifa ya numfasa. To Allah ya kawo abin da sauki, ina jinjinawa ace Anty ta samu labarin nan. Bros yace kullum ina adduo'in Allah ya fahimtar da Anty gaskiya wannan kawayen nata su ke zugata. " Halifa yace jiya ai na kusa doke yarinyar kawarta ta Zariya din nan kawai ta fesa min wani abu wai murnar biki. Tun abine fa har yanzu bana gane kaina so sai wallahi Bros. Bros yace dama ka doke ta wallahi Allah ya sa ba wani mugun asirin na su bane suka fesa maka. " Halifa yace Sai sun jira, asiri su zai ci su da suka yarda da masu yin shi, ni ina tare da kariyar Allah ko da yau she bana wasa da azkar kaga kuwa sai dai wata kaddara. Sunata hira sai kiran salla suka ji. Bilkisu ta shirya tsaf da safe ta hada abin kari ta nufi Asibiti ta samu labarin rashin lafiyar Halifa ne daga bakin Hafsi lokacin da Bilkisu din ta kira ta domin ta samu tabbacin abinda Asiya ta fada mata. Sai Hafsi tace mata ba shakka haka ne yanzu wata zai aura kuma a wannan ranar sai dai yanzu haka yana Asibiti bashi da lafiya. Mahaifiya Bilkisu itace ta hada abinda za a zubawa Halifa a abinci dan sake maido shi ga Bilkisu suna son su gyara abinda suka bata. Halifa ya kosa likitan ya shigo ya bashi sallama domin kwanakin biyu bai leka kasuwar shi ba, yau kam zai fita. Anty da Dadi suka shigo da sallama Tace "Alhamdulilah jiki ya yi sauki Amma na tsorata jiya Halifa." Suka sa dariya, suna cikin gaisawa Bilkisu ta shigo da sallama bisa Jagorancin wata Nus. Halifa ya kalleta sai kuma ya kauda kai yana jin su Anty suna amsa gaisuwarta har ma da bata gurin zama, zuciyar shi ta shiga harbawa da sauri, tabbas yana son Bilkisu har yanzu fa. Ta ce "Yaya Halifa ya jikin? " Yace da sauki ba tare da ya kalleta ba. Bros yace nifa ina son inje in fita da wuri yau muna da baki a kasuwa. Halifa ya kalleshi ya yi murmushi domin ya tuna da hirar su ta dazu. Yace to ya kamata ka tafi nima dai in likitan nan ya kai goma bai zo ba Allah zanyi tafiya ta. Anty Tace "Zuwa ina ai ka kwanta sai gobe ka kara warware wa. " Halifa yece kin san Allah Anty ba zan wuce goma ba, karma ki bata baki ki. Anty ta yi shiru tana tunani inko haka ne dole ta koma gida kafin goma domin ta sa a nemo gurin da Sahiba da yarta suka yi biso. Bilkisu ta katseta da fadin Anty ga abinci a ba Yaya Halifa. Anty ta kalleta to an gode zuba masa ya ci. Halifa yace na koshi ina godiya sosai ki koma da shi. Bros ya fice Anty ta kalli Dadi zo muyi magana ta jashi waje da fatan su daidai ta zata fiye mata waccan yarinyar. Bilkisu ta tashi da sauri ta zube gwiwoyinta a gana gadon da Halifa ya ke zaune tace "Halifa dan Allah Don girma da darajar mahaifanka ka yafe min wallahi na yi kuskure. Bazan sake yin wani Abu mai kama da haka ba kar ka fasa aurena Halifa ina son ka. Kaima na sani Halifa kana sona." Halifa ya mike tsaye ya bata baya Ki tashi Bilkisu na yafe miki tun a ranar, sai dai kin makara domin zance na da Asiya ya yi nisa, ki gyara a gaba. Maganar so gaskiya ne ina sonki sai dai dama ba kowane abu bane da ka ke son shi ka ke samu. Ki yarda cewa labarin soyayyar mu ya kare tun ba a fara cin gajiyar soyayyar ba. Bana son ki tsaya Kiyi ta magiya domin ban cika maimaita magana ba duk da nasan baki cika fahimtar hakan ba. Tafashe da kuka, ya fice a dakin domin bazai jure ba. Anty ta biyo shi har harabar Asibitin inda ya zauna a kofar masallacin Asibitin. Tace Me ya faru kuma naga ka fito. Yace "Anty dan Allah ki ce ta tafi ko kuma ni in tafi." Wani takaici ya zo wa Anty wuya, tana bakin cikin yadda Halifa ke kara fito da wannan shegen ra ayi na shi. Tace Yanzu Halifa ni ban isa ba sam bani da wata daraja a idon ka. Sai yadda ka ke so? Kala baice ba ya nufi hanyar fita. Da gudu ta nufi Dadi ta kira shi tace yabi Halifa. Ko kafin su fito har ya dauki Keke napep tunda bakin titi Asibitin yake. Dady yace "Wai me kika fada masa ne haka gaba daya Yaron nan a rikice yake fa tun da ya samu matsala da yarinyar nan wai ma me ya kawo ta ne.?" Cike da jin haushi Anty tace Kaga dan Allah ka sama min lafiya ina ce muna tare da Kai ta shigo sai kuma ta ja tsaki ta fice daga Asibitin domin bata bukatar Halifa ya shiga gida saboda binne binnen Sahiba. Asiya ta wayi gari kamar mara lafiya domin bata samu kiran Halifa ba, ga kuma batun waccan da ta kira ta duk da tana ta son ta nuna wai kamar abin bai dame ta ba. Gabanta yana tsananta faduwa idan ta tuno da wani mafarki da tayi wai wasu macizai suna ta kaiwa Halifa sara shi kuma yana ta fesa musu wuta da bakin shi. Ta shiga gidan su Sulaiman ta gaida mahaifiyar su sannan ta ce, ko Yaya Sulaiman ya na ciki? Ya fito ta gaida shi da girmamawa. Yace ya aka yi ne Asiya ta nufo waye sai ya biyo ta. Ta tsaya a soro ta dube shi cike da kunya tace Amma ka samu labarin Yaya Halifa kuwa? Yace "Me ya faru jiya dai kafin ya zo gurinki ya biyo shagona yace in amshi dinkunan ki na biki nace masa sai yau zan saka yarinyar shagona ta zo ta gwada ki ta amshi kayan nan da shabiyu ta ke zuwa." Asiya tace jiya ya bani wayarsa ka gan ta, kuma yace zai kira ni, sannan kuma bai kira ba. sai naji kuma kamar wani abu ne ya faru da shi. Sulaiman ya yi murmushi," Ki kirashi shi mana to da wannan Wayar." Ta girgiza kai bayan ma ban iya wayar ba kuma akwai lambobin sirri, banda hakan ma bai bani Umarnin in kira ba, yace shine zai kira. Sulaiman ya ce Ina zuwa. Ya dakko wayar shi ya danna kiran Halifa. Bayan sun gaisa yace kana ina ne haka.? Halifa yace "Yanzu na shigo gida Asibiti na kwana jiya bayan na bar unguwar ku sai a mai nake ta yi wai ance Ulcer ce." Sulaiman yace Subhanallah Allah ya baka lafiya. Shiyasa mutuniyar tazo min ka ga ta nan wai taji a jikinta kamar da wani abu kace zaka kirata baka kira ba. Halifa Yace" Allah sarki kace zan kirata. Bilkisu ta dauki abincin ta cikin kunan rai ta nufi gida ba a taba wulakanta ta kamar haka ba. Suka yi jugum ita da Uwar suna lissafin mafita. Ina zata sami malami me zafin hannu wanda aikin shi zai zama sha yanzu magani yanzu. Can ta mike tare da fadin duk wanda ya ci tuwa dani miyar ma baisha ba. Halifa zai gane shayi ruwa ne tashi mu tafi indai na haifu sai Halifa ya zama abin sarrafawar ki. Hafsi ta kawo masa wani makullin domin bai San yadda ya yi da na hannun shi ba jiya. Anty ta shigo ta kwada masa kira tun daga bakin gate ya tsaya bai bude dakin ba, tace Halifa ka fita waje gidannan an binne wasu asirai saboda kai bari a tone ko kaje gidan Bros tunda shi kadai ne na dan wani lokaci. Halifa ya yi murmushin takaici ya fara gajiya da wadannan zantukan, shi baima fahimci me take fada ba. Anty kije ciki kawai ki huta dan Allah bana gane me kike cewa. Tace Halifa kana cusa min bakin ciki da wannan gaddamar taka, dan Allah iya yau ka saurare ni in ceci rayuwar ka. an binne mugayan asirai dan a cutar da kai a gidan nan. Yace "Anty waye shi a gidan nan da zai min wannan mijinki ko yayanki haba Anty dan Allah karki ruda kanki mana." Hajiya Talatu ta kara so tana fadin sannu mai jiki, yanzu nake cewa Sahiba nace mata zani duba ka sai suka wuce bata tashe ni ba. Halifa yace na samu sauki sosai. Anty tace Halifa In mutum zai cuce ka ai ba sai na gida ba, amma tabbas gidannan anyi binne binne saboda kai, ta kalli Hajiya Talatu wadda ta zaro ido cikin faduwa gaba tana sake tambayar Anty waye kuma zai masa hakan.? Anty ta yi murmushin yake, Sahiba kenan ke dai ki ga mutum ni dai kawai ya fita. Halifa ya dafa kafadar Anty yace kiyi hakuri babu wani abu da zai same ni wanda Allah bai kaddara min ba, karyar mutum ko aljani. Ya jiya ya bude dakinsa ya shige. Shirin kasuwa ya yi yana fitowa falonsa Hafsi na kawo masa kunu yace a sa sugar a ciki? Tace "E" Yace je ki kawo min mara sugar. Tace "Sai dai a dama." Yace to ayi hakan bakina babu dandano. Kafin ta kawo sai ya yanke shawara kiran Asiya. Tana kwance kan yar yaloluwar tabar marta baza ta iya fassara halin da zuciyar ta ke ciki game da Halifa ba, amma dai da ace akwai dama to zata so ta ganshi ta ga jikin shi ta kuma bashi wata kulawa wadda zai samu sauki. Kamar daga sama wayar ta soma kida, ta dauka da rawar hannu sannan ta sa a ku ne bayan ta tashi zaune, sai kuma abin ya motsa wato jin kan. Tayi sallama a natse, ya amsa, ta gaida shi gami da tambayar jiki, yace da sauki. Tayi dan dim saboda yadda ta ke jin muryar shi tana ratsa dodon kunnen ta. Yace to ya shirye shirye nace Sulaiman ya zo ya amshi kayanki. Ta lumshe ido,. "Ya fada min dazu zan bashi." Yace kin gano nawa ne ake yin gyaran jikin? Tace a a ai ban ma san wa zan tambaya ba, domin Maman Annur a bikin ta ita ta yi a gida na kurkur. Yace to bari zan bincika sai in kai ki ko baza ki bini ba? Ta yi yar dariya. Bana tunani su Baba za su hanani zuwa tunda kai ne. Yayi murmushi salon maganar ta yana birge shi. Sai me ki ke bukata bayan wannan kamar paty ko Walima haka? Kamar munyi wannan maganar ranar da ka zo nace saboda jikin Baba baza yi komai ba, garama dai walimar tunda akwai lada a cikin ta." Halifa yace haka ne yarinya da hankalin manya. Yaci gaba da fadin ina fatan baki ji haushin abinda masu shagon nan suka fada Akan ki ba jiya? Ta yi yar dariya " Zan iya tambayar ka? " Yace Sosai ina sauraron ki. Tace," Abinda suka fada ya kankare wani abu na daga kima ta a gurinka?" Sam Sam sai ma karuwa da ta yi bayan sun bani tabbacin da wuya a samu wadda tafiki hankali a cikin kaf unguwar . Ya fada cike da jin dadin hirar ta su. Ta yi yar dariya. Kasan ya nake jin kaina daga ranar da kafurtamin kamar aure? Yace a a, tace duk wata mace in dai ta wannan karnin namu ne farace ko baka mai kudi ko mai sarauta bata kaini ba. Halifa ya sa dariya lokacin Hafsi ta shigo ta kawo masa kunu. da hannu ya yi mata alamar ta aje ta fita ba tare da ya saurari abinda Anty ta aiko a fada masa ba, ko kadan baya son abinda zai katse masu hira. Kina nufin duk kin fisu? "Tace" Nisa sosai nake Kallon na yiwa kowace mace, bafa alfahari bane tuntuni inajin hakan a raina, samun ka a matsayin miji ya tabbatar min cewa yadda na ke Kallon kaina haka ne, domin na samu mijin da shima babu wani namiji sama da shi a cikin karninmu kaga na kara yi wa mata tazara. " Mamaki ya cika Halifa yace In tambaye ki? Tace" Baka bukatar izni ranka ya dade." Yace kina karanta littafin soyayya? Ta ce ban taba ba, amma in hakan zai fara ta maka zan fara." Yace ina mamakin yadda ki ka iya magana haka, farko na miki kallon mai shiru wadda magana bata dame ta ba. Asiya ta yi yar dariyar kirsa wadda hakan ke sa tsigar jikin Halifa tashi yarr." Kasan fa shiyasa ba kyau ka yanke wa mutum hukunci daga ka kalle shi akwai kuskure, sai dai kuma nima ina magana ne kurum a gurin da maganar tawa take da muhimmaci, kaga ai bai kyautu mutum ya yi asarar kalaman sa ba musamman a inda basu da amfani ko?" Yace Haka ne. To wai kin fara jin wani abu game da ni kuwa?" Kamar me kenan? " Ya gyara zama so nawa kika tuna ni daga jiya zuwa yau.? Ta numfasa sannan ta lumshe ido. Zan yi karya ida na fadin adadin domin da tunanin ka zuciya ta tare su ke bugawa, harma na tambayi kaina ko wannan shine son da kake magana, in kuwa shine Yaya Halifa ya min kamun kazar kuku, kasan Allah da girma yake yau kowa ya jiki yace min a gidan nan, to alamun rashin lafiya ya bayyana kanshi a gare ni, yanzu haka fa kwance nake ka kira ni, Innarmu ta aiki Abba ya siya min magani. Kasan abin da nake mamaki yanzu haka bai dawo sayen magani ba kaga har na warke da ka kira ni.. Halifa ya saki dariyar da bai san yana yin irinta ba. Yace Asiya kin iya wasa. Tace "Kila in na rantse da girma Ubangiji zaka yarda ba wasa nake ba a cikin duk maganganu na yanzu haka da zan ganka bansan kuma me zanji ba." Yace ko in zo kasuwa zanje yau. Kaje kasuwar ka, amma zan roki wata alfarma a gurinka. * Yace Na miki. Tace "Zaka iya tunani duk awa daya ko ta yi yawa?" Halifa yace zan kokarta. Amma baki tambaye ni ko na cire son wata ba da nace zan cire? Asiya ta tashi zaune. Kar ka wahalar da kanka gurin cirewa nice mai hakkin cire maka shi. " Yarinyar ta tashi kan Halifa sosai wanda har ya kasa shan kunun ya fita ya rufe dakin ya bar kunun a ciki, sakamakon yana tafe suna wayar har ya isa kasuwa sai da yaran shi suka soma bude shagon ya ce mata zai kira anjima. Famcenter a nan ne Halifa yake kasuwancin sai da waya da kayan gyaranta. Shaguna ne guda uku a hade shake da kaya kuma sari yake bayarwa domin kai tsaye daga Chaina da Dubai ya ke kawo su. Da shi yake zuwa daga baya kuma sai dai oder tunda ya shahara. Tabbas Halifa ya gaji dukiya daga gurin mahaifi sa Alhaji Umaru Madugu wanda tsohon attajiri ne, haka kuma 'Yan uwan shi da suke uba daya duk attajirai ne yanzu haka. Gidaje kawai Halifa yana da sama da goma banda wanda suke ciki da su Anty hatta wanda Bros ya zauna da matar sa na Halifa ne. Banda stor stor na aje kaya da ake haya, Shaguna a kwari da Singa duk ya mallaka. Saidai shi Sam bai taba damun kansa ba tun da aka tsakura mishi mikiyan a shirin bayan ya kammala digirin shi a Jami ar Bayero ta Kano ya fara kasuwanci lokacin ne aka ba Bros aron a shirin din shima ya shiga kwari. Duk da Anty ta na yadda take so da kudin Halifa amma ta kasa wadata kullum ya zata mallaki fin haka saboda akwai lauyoyin su na iyalin gidan mahaifinsa masu lura da shigi da fice kudin. Halifa ke biyawa yaranta kudin makaranta kuma ya kawo abincin gidan Dadi cefane kawai yake yi, har su Nihal da Nur yaran Bros tunda suka dawo gidan lokacin da Anty ta sa a saki Uwar su da za a sasu makaranta Halifa ta fadawa ya bada kudi aka kai su, Bros lokacin ya samu karayar arziki Anty ta ce matar sa ce Malamanta suka fada mata, dan haka tace ai ta zage ta dole a sake ta. Halifa na cikin wadanda suka taso Bros saboda shi ya dogara akan inhar ta zagi mahaifiyar sa to ta cancanci saki, shine Bros ya yi kamar ya sake ta. Anty ta kara imani ganin yadda harkokin suka sake budewa Bros bayan ya saki matar sa kamar yadda ta ke zato. Duk wani hakkin Allah kamar zakka Halifa baya Wasa gurin cireta, ga sadaka kullum a kasuwa akwai mutanan da shi suka dogara banda daidai kun almajirai. Baya yin rayuwar karya ko kuma ya nuna kansa a me kudi ko kamar mara shi. Har zuwa yanzu da ake daf da daurin aure Asiya bata san waye Halifa ba, abinda take hasashe a ranta shine yana neman kuma ya samun abinda zai iya rike ta da shi, ko Keke bata sa rai ya na da shi ba bare wata mota. Hajiya Talatu ta shiga Rudani ganin magani bai yi tasiri a gurin Halifa ba, wannan ya sa ta fadawa Sahibar ta zata je wata gaisuwa a Wudil ta juya ta nufi Zariya gurin Malam na shuri, ita kuwa Anty sai ta yarda cewa Malamanta sun turo Aljanu sun cire bison kamar yadda suka yi mata Alkawari. Sai da suka shiga Adaidaita sahu Sannan Anty ta kallo Hafsi in munje fage zaki gane gidan da kuka kai Kaya? Gaskiya in dai ba ta layin ya shiga ba to gaskiya bazan gane ba. Dan Adaidaita yace "Hajiya Fage tana da yawa in baku San gidan ba ku kira waya." Anty tace kira Halifa ki masa siyasa ya fada mana sunan layin. Ta kira ya kai sau biyar bai daga ba, dan haka suka yita yawo, sai Hafsi ta ga kamar layin ne da sunje sai ta ga ba nan bane.. Cikin sa a ta hango Sulaiman a shago suna ta dinki shida yaran sa. Tace yawwa Anty ga Sulaiman can abokin nan na Uncle Halifa kinsan makotan su yarinyar ne. Tace Shike nan wahalarmu ta kare, bari mu same shi. Dansahu yace kodai tawa wahalar ce ta kare. Anty ta Kalle shi, wai kai da kake ta damun mutane da mita, ba kudi ka fito ne ba? Yace "Sune Baba." Tace to in zamu kai wata muna yawo baka da matsala shiyasa ko farashi ban tambaya ba dan haka ka daina damu na. Sulaiman ganin Hafsi ya gane su. Bayan sun gaisa Anty tace gidan su amaryar Halifa muka kasa ganewa, yace Allah Sarki muje in kai ku. Ya fito yana saka takalmi. *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* [5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: ____ Daga ni sai Baba a gidan Inna da Maman Annur sunje kasuwar kurmi za sai min tukwane da ɗan tsince tsince. Ina hura gawayi zan dora taliya wadda Halifa ya sai mana ajiya, kamar yadda Inna ta barmin sallahu tunda yanzu na daina awara su kuma sai bayan biki za su ci gaba. Cike nake da shauƙi da kuma nishadi nan da wasu kwanaki kadan ina gida na kuma zan ɗora girki nawa na kaina ba tare da wani ya bani Umarni yin abinda zan yi ba. Ko iya haka aure ni ima ne ba shakka. Allah kenan duk yadda ya so haka yake faruwa kamar yadda na kabari bai san cewa zai mutuba ya wayi gari ya ganshi an turbuda shi cikin kasa, haka ma wanda zai yi aure ko haihuwa sai dai mutum ya yi hasashe. Fargaba takan darsu a zuciyata idan na tuna zan koma rayuwa ta har abada da mutanan da ban san su ba, ko sati ban yi da sanin abokin rayuwata ba amma ina yi masa kyakyawan zato. Sallama ce ta katse Asiya daga tunani ta amsa tare mikewa tana yi musu sannu da zuwa, ba Wai dan ta san su ba, sai dan girmamawa. Sai dai kuma kallon da taga baƙin suna yiwa ko ina na gidan nasu tare da yatsina fuska gami da taɓe baki shine abinda ya fi daure mata kai. Ba shakka waɗannan ba alkairi ya kawo su ba. Ta ɗarsa haka a zuciyar ta,. "Ina matar gidan?" Anty ta tambaya cikin daga murya da izgilanci. Bata nan Asiya ta bata amsa cike da tsoro. Anty tace "Ina amaryar da Halifa zai aura? " Asiya ta ji gabanta ya yi wata mummunan faduwa, ta sunkuyar da kai alamun kunya. Hafsi tace Innalillahi kar dai ke ce? Asiya ta kalli Hafsi ta kasa magana. Hafsi ta matso ta kama fuskar Asiya ta dago tace kalli Anty munshiga uku wannan ai bakwaini ce kalli ta, ta kama hannun Asiya ta saki kamar kara. Gaskiya dai Anty kiyi wani abu dan kuwa karshen abin fadi ne zai faru a zur"iar mu. Baba daga cikin daki ya yi karfin hali yace "Wai su waye ke magana?" Mu ne Anty ta amsa tare da nufar gurin tana cewa " Wai dama megidan yana nan?" Bakin ƙofa ta tsaya tare da toshe hanci " Wai ɗaɗɗaɗoya, ta fada tana duban Asiya. Ta ci gaba Baba zuwa nayi in bada sako a baka ashe ma kana gidan to hakan ya yi, Baba Kana ji? Ƙanina dai ba zai auri wannan yarinyar taka ba haka sai kace sullen kara, Haka a tsiyace, kwarya ta bi kwarya wannan ai matar yan dako ce. ba irin Halifa ba shi ba ajinta bane. " Baba yace Au haka ne? To ko ya makance ne lokacin da yazo yana neman a bashi ita? Ya cije lefe dan karfin Hali ya ci gaba da fadin, to kije ki ce da yaron ya zo da kansa ya ce ya fasa kamar yadda ya zo yace yana so, ko da kike uwarsa ce ba yayarsa ba. Ko kuma ki turo waliyyan sa, wannan yarinyar a yanzu matarsa ce domin na bashi. Anty tace zanga kuwa yadda za a fara tusa ta hura wuta. Dole ka bashi mana kullum burin matsiyaci shine ya hada kafada da mai arziki. Na san ta inda zan biyo wannan auren bazai taba faruwa ba. Baba Yace Ko bana raye za a daura. Ta dawo gaban Asiya "Ke kuma munafuka mai kama da muciya in har kika yarda kaddara ta kawo ki Auren Halifa zaki gwammaci kida da karatu.. Asiya jiki na bari tace Kuyi hakuri. Hafsi tace Ke in har kika shigo zuri armu Ba Anty ba ko ni sai na gallabi rayuwar ki. Ta yi gaba tana faɗin Anty waɗannan ba su kai kiyi cacar baki da su ba, ki zo muje ni amai nake ji ma. Suna fita ta shiga gurin Baba da sauri tana fadin Baba Dan Allah a janye maganar Auren nan ni tsoro nake ji. Yace "Shigo Asiya," Ta shiga ta zauna tana kuka, ya ce "Share hawayen ki. Ta share, ya ci gaba da fadin, wannan shine ya nuna cewa akwai alkairi a cikin wannan Auren na ki, kin san dalilin?" Ya jeho mata tambaya. Ta girgiza kai. Yace " Duk abinda ya fara da ƙalubale ba shakka nasara ce ke biyo baya. Babu abinda hargaginta zai sa, ko ya hana dan haka ko Innar ku karki sake ki fada mata in su dawo, ki bar abin tsakaninmu." Asiya tace Saboda me Baba ai da ka bari na fada musu, wallahi duk na tsorata. Yace" Asiya alkairi ake fada ba sharri ba, ki zama mai fadin alkairi karki tada mata hankali,kinji ko yar albarka. Ki fara da shanye kalubalen ki, ki koyi aje sirrin miji ki a kirjinki ki yarda Allah shine mai maganin duk wata masifa. da haka zaki zama Jaruma ranar da ki ka rasa Innarki ko ni zaki iya daukan damuwar ki, Asiya tace to Baba bazan fada mata ba insha Allah. *** *** *** Anty ta wuce gidan Baffa Halifa wannan shine karo na farko da taje gidan sa, domin tana mugun Jin haushinsa yadda suka saka lauyoyi a kan dukiyar Halifa in tana son wani abu dole sai Halifa ya saka hannu anbi wasu kaidojin banza, karshe ace aro ne, har sai in Halifa yace mata ya yafe. ita da kullum burinta yadda zata hau kan dukiyar ta barje gumin ta yadda take so. Taje America taje Dubai irin na wayayyun mata masu kafasiti da aji. Bayan sun gaisa tace Baffan Halifa zuwa nayi a yiwa Halifa fada kuma a bashi shawara, gaskiya yanzu duk ya canza, baya saurarona ko wannan Auren da ya rungumo na waccan yar matsiyatan bai kamace shi ba, yarinyar bata ma da lafiya aljanu gare ta naje na bincika har unguwar sun rufe masa ne. Baffa Yace "Kin tabatta haka ne? Tace ko kaffara ba zanyi ba inna rantse. Ance su ke tsotseta in sun tashi kuwa hauka tuburan. Baffa yace" In maganar nan ta tabbata ba shakka basu kyauta ba sun yi abinda Manzo Rahma ya hana a yi, sun boye aibinta a neman aure. Amma In Dan su ba masu kudi bane wannan baya cikin sharadin da musulunci ya saka akan aure. Anty tace shiyasa nace Bari inzo in fada maka tun wuri kar ayi aikin nadama. Yace "Ba damuwa zan kira shi a waya domin ya zo ya janye wannan maganar. Anty ta fashe da kuka tana fadin Na gode Baffa dama na san kai kadai ne zaka taimake ni in cika a amanar da mahaifiyarmu ta barmin. Yace Dai na kuka ni ba zan barshi da kanshi ba, duk taurin kansa sai ya hakura. ai mu iyayensa ne, Anty ta bar gidan Baffa cike da kwarin gwiwa. Asiya ta kalli wayar Halifa dake ringing shine yake kira, a sanyaye ta dauka muryarta can kasa ta gaishe shi. Yace " Amma dai kina lafiya?" Ta ce to lafiya lau.zance. Yace "Naji muryar ki wani iri bayan ba haka muka rabu ba." Tace An tsoratani ne Yaya, wai kana ganin idan. na zo gurinka da zama zan zama cikin aminci kuwa? Cikin mamaki Yace "Zaki zama cikin aminci bana shakkar haka insha Allah." Ta sauke wata ajiyar zuciya mai karfi. Sai yanzu ta da ji sanyi a ranta. Yace wani Abu ya faru daga jin yadda ki ke magana sanar da ni. Asiya tace ya wuce ai tunda na samu tabbacin cewa barazana ce aka zo aka min. ina rokon ka kar ka ce sai ka matsa na fada maka. Yace "Shikenan zan dai kira ki anjima Baffa na ke kira bari na daga. Bayan sun gaisa yace Umaru wai kuwa kayi bincike game da yarinyar nan da ka canza? Halifa yace sosai kuwa. Baffa yace ciwon hauka fa aka ce tana fama da shi. Halifa yace Baffa gaskiya da Sulaiman zai fada min Sannan ba abokin ka ne makoci su ba, ka buga masa waya domin ka samu tabbaci. Baffa ya yarda da haka. Mamaki ya kama Halifa duk yadda aka yi wani Abu yana faruwa in ya auna kalaman Asiya da na Baffa. Da wannan tunanin ya kai gida. Yarinyar nan ya fara karo da ita bayan ya fito a mota wato Ma u tsigar jikinshi ya ji ta tashi, yace Auzubikalimati lahitammat min sharri ma kalaka. Take ya ji wata tsanarta a zuciyar shi. Ta nufo shi tana yanga tana fadin sannu da zuwa Yayana. Tsawa ya daka mata, karki sake ki karaso nan shedaniya. Ni bana son ko ganinki a rayuwata. Mamaki ya cika Ma u Mamanta ta bata tabbacin cewa yau dai Halifa ko dame yake takama sai ya rusuna kuma zai birkice yace sai an daura musu aure nan take kuma wata sha awar ta ce zata kama shi harma ya ji yana da bukatar saduwa da ita, in ya nemi hakan su amince, domin daga ranar kuma sai yadda suka yi da shi. To ya kuma abin ya fara da haka tafi awa tana wanka na magani ta jima tana kwalliya amma tana zuwa ga abinda ya biyo baya. Ya kalli Anty wai ina makullan gidan nan ne? me hada sola nan ya same ni a kasuwa dazu, yana son kara sa aikin shi. Tace "Wa zaka sa a gidan? " Ya kalle ta cike da mamaki. Yace Wai Anty meyasa ki ke min Haka fisabilillahi bakwa wani shirin biki kamar yadda kuka fara a farko kin daina tattaunawa komai na shirye shirye ko da yake ni bani da matsala in aka daura aure an gama min komai. Anty ta ce "Kai ashe yarinyar tana da aljanu hauka tuburan take yi in sun. tashi shine iyayenta basu fada mana ba. Halifa yace wace yarinya ke nan? Tace wadda zaka aura yanzu. Halifa ya danne mamakin sa yace ni sun sanar dani tun a ranar da nace zan aure ta kuma na musu Alkawarin, zan rabata da su. Anty ta tsaya tana Kallon shi cike da mamakin yadda ta zabga karya kuma ya kare hakan duk da ya sa mata kokwanton ko dai da gaske tana da aljanun ne?. Shi kuma mamaki yake tana da aljanu aka boye masa, ya dai sha alwashin in Allah ya yarda sai ya auri Asiya ko ma wane aibu gareta. Anty ta katse shi to gaskiya tunda tana da larura, ba zai yiwa ka kaifa wannan katon gidan ba, ka kawo ta nan gidan ku zauna a sashen ka har muga kamun ludayin jikin,kada wata rana ta fita ba a sani ba suje su halakata. " Shiru Halifa ya yi can kuma ya ce kawai ki bani makullan zan ga ya za ayi. Magana kamar wasa sai gashi ta watsu a dangin Halifa cewa mai ciwon hauka zai aura *** *** *** Asiya ta saka hijabin ya mata ƙato har kasa kasancewar ba dai dai girman ta bane na cikin lefen ne Halifa ne ya kira ta a waya yace ta fito yana gurin shagon Sulaiman zasu unguwar da ya faɗi mata duk da be ce mata ga wajen da zasu ba ya ce ta shirya ne kawai,ta rasa wane hijabin zata saka Inna tace saka na lefenki sai gashi ya mata ƙato tunda Bilki tana da tsawo da kuma kiba, ita kuma yar tsuntsuwa. Halifa ya fashe da dariya lokacin da ya kalli Asiya, Kingan ki kuwa kamar wata tattabara a cikin leda? Asiya ta yi takwa takwa da fuska, cike da shagwaba tace yaya harda kai a yi min ba 'a ko? " Kamar ya zube damun daɗi, yana son shagwaba sosai abinda Bilkisu bata iya ba ita sai izza. Yace. " Yi hakura kanwata, ni nafi son ki a haka, yadda zan jefaki sama in cafke kayana." Ta sunne kai a tafukan hannayen ta cike da kunya da nauyin abinda ya fada. Yace zo muje tabishi ya nufi wata mota yana yi wa Sulaiman alamar sai ya dawo da yatsan sa. Ta Kalle shi kasa kasa yana cikin motar kwayar idanunta dauke da alamar tambaya. Yace" Shigowa za ki yi mu tafi. " Tace Ina Kenan? Ta tambaya cikin salo. Yace" Saida ke zanyi. Ta kama murfin motar ta bude tare da fadin lahiya lau, inji katsinawa. Ya tintsire da dariya, "Ina matukar samun nishadi in muna tare, da alamu na yi sa ar mace wadda ta iya hira." Ya kai karshen maganar tare da juya motarsa dan fuskantar inda za su bi. Nishadin na ka ai ba zai yi tsawo. ba" Saboda me? " Ya fada yana kokarin tattara hankalinsa gareta. Saboda ga shi zamuje ka sayar da ni. Ya girgiza kai," Ba saida ke zan yi ba, gurin mai magani zamu je." Ya fada cike da son bugun cikin ta. Ta Kalle shi da sauri Wani ne ba lafiya? Ta jefa masa tambaya cikin sauri. Ya Dan yi shiru domin kamo bakin zaren, tana da wayo fiye da shekarunta. Ya yi gyaran murya sannan ya soma magana a hankali, Asiya zan kai ki gurin mai rukkhya ne kinsan in mace zata yi aure ana bukatar ta zama komai lafiya a yi gwajin jini da sauran su," . Ta ce rukiyya ai sai masu Aljanu Yaya ni kuwa tunda Allah bai dora min ba ai sai mu gode masa. Jinin dai muje a gwada dama Innarmu ta yi wannan Hasashen cewa jini zamuje gwaji lokacin da kace in zo. Kuma kasan abin mamakin shine ni A A ce, kasan yadda aka yi na sani wata rashin lafiya na yi, kowa ya ganni sai ya ce sikila ce shine aka yi min gwaji ashe ma nidin AA ce. Ya kalleta da mamaki " Allah na zaci ke As ce, kuma duk da cewa ni A S ne wallahi ban damu ba ko ke din AS ce na fi damuwa da ace kina da Aljanu amma kin taba yin su?" Tayi dariya nifa ko mugayen mafarkai bancika yi ba domin bana manta adduo'in idan zanyi bacci Allah ya tsare ni da sharrin su. Yace"Alhamdulilah yanzu bari muje gwajin jini." Ta kasa danne Hasashen ta tace. Labari ka samu cewar ina da Aljanu kenan. Ya yi yar dariya." Ina zan samu wani labari kawai dai kinsan anayin gwaji." Tace nasan ana gwaji amma ban taba jin na Aljanu ba, Yayata ta yi aure amma ba ayi mata rukiyya ba, bana son ni da kai mu samu shakkar wani abu tsakanin mu, ko me kake son sani game da ni kar ka damu ka tambaye ni kai tsaye zanyi maka bayanin shi. Haka nan nima zan yarda da duk abinda zaka fada min. Dan Allah kar ka yi min karya a duk irin rayuwar da zamu yi bana so ta sam. Kunya tana son kama shi lallai wannan yarinyar itace matar da ta dace da rayuwarshi, dole ya yi taka tsatsan ta sake kashe shi da cewa. Ka dai yi min Alkawarin zan rayu cikin aminci ko? Bai amsa mata ba sai da ya yi fakin a cikin asibitin Malam Aminu Kano sannan ya dauki waya ya kira wani likita ya sa a sanar da shi sun karaso yace to ya jira shi gashi nan zuwa. Ya kalleta na miki wannan Alkawarin matsawar ina numfashi. Ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin na yarda. Bayan angama dibar jini suka dawo mota tare da rakiyar abokin na shi tanaji su suna tattauna yadda akayi aka fasa da Bilkisu Abokin yace " Ka samu yar shila. Suka sa dariya yace ka fa yi dabara abokin a in namiji yana da jiki yar shila zai samu, Halifa yace au ni yanzu ina da jiki? Suka yi dariya suka tafa. Asiya dai ta kashe kunne tana jin su. Wani shagon gyaran jiki na yan birni ya gani akan titin gidan su kawai ya ja birki suka shiga. Yace yana bukatar su yi mata gyaran jiki na amare nawa ne, suka fada mishi farashin daban daban yace mai tsadan nake so amma ta yi kyau sosai, suka ce to zata zo na kwana uku gobe zata fara zuwa, ya basu rabin kudin da suka caje shi, yace sauran sai ya ga yadda sukai mata. Bayan ya yi mata siyyar kayan kwalama suka tsaya inda yake fakin ya taka mata sannan ya ce to zai kirata anjima. Asiya tun a ranar ta tabbatar rayuwarta ta canza Wai ita za abiya irin wadannan manyan kudin dan kawai a mata gyaran jiki. Gashi ashe Halifa yana da mota, sai taji ta kara aji kuma ya shiga ranta, dan gaskiya bata taɓa sa ran auren mai mota ba, amma ta na mugun son mota sosai. Halifa ya kebe da Sulaiman ya tambaye shi akan dan Allah ya fada masa gaskiya ko Asiya tana tada Aljanu. Sulaiman yace gaskiya bata da su, ita tace maka tana da su? Yace a a, kasan sharrin mutane wani aka samu ya fadawa Baffa na da kuma Anty. Sulaiman yace shiyasa Anty da Hafsi suka zo gidan su Asiya jiya kenan.? Halifa ya zaro ido, Anty da Hafsi fa kace kai gaskiya ba su ka gani ba. Sulaiman ya ce ni fa na raka su har gidan. Mamaki ya cika Halifa daga Anty har Asiyan ba wanda ya fada mishi. Ko shine dalilin da Asiya ta dage cewa ya mata Alkawarin cewa za ta samu aminci a gurin sa.?"Dole dai akwai wani abu.. Ya yi sallama da Sulaiman ya tafi. Yan mata ne kyawawa guda biyu suka amsa mishi sallama a Falon Anty, shi bai cika kallon mutane ba musamman mata, dan haka ya amsa sannun da suka hada baki suka yi masa ne ya nufi Dakin baccin Anty. Ya kwankwasa ta ce waye, yace "Anty ni ne, ta fito tana fadin dan Halas ka ki ambato irin albarka kai nake ta kiran wayar ka taki shiga. Ya katse ta Anty me kukaje yi a gidan su Asiya?" Tace zo muje zan amsa maka wanna tambayar daga baya. Kamar ƙaramin yaro taja hannun shi zuwa falo da kyawawan yan Matan ke zaune. Tace duba a cikin su ka zaba dukan su wayayyu ne in sun yi maka duk biyun ma baka da matsala. Suna Jami a ƴaƴan masu da shi ne, kuma'ya'yan kawaye na ne. Ta kalli dayar Amina mike ya ganki. Ta mike tsaye tana takun kasaita, ta zauna, dayar ta tashi ita ma tana rangaji. Anty tace wannan kuma Kamila sunan ta. Ya bita da kallo domin gaskiya tana da kira ta jan hankalin ɗa namiji, ya kasa dauke idanun sa daga kirjinta.... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* [5/26, 09:17] Ummi Tandama😇: Cike da farin ciki Aunty ke kallon Halifa ganin yadda ya kasa magana, da alamun yarinyar ta dauki hankali sa daga ganin yanayin kallon da yake mata. Ganin haka yasa ta katse shi da faɗin Amina zo mu basu guri su yi magana. Cikin sauri yace "a a," Gaskiya bana bukatar ko daya ciki su. Ki zo muyi magana ya koma dakinta. Tsaki ta ja ta zauna a falon tana fadin kai ka yi kaɗan ka bi mutane wato sai dai kai a bika ko? To kowa ya rike maganar sa. Ta kalli yan matan tace ku yi hakuri, zan zo gidan. Wata ce take son mallake shi. Muryar Hafsi Halifa ya jiyo a cikin kicin sai ya nufi can ya tsare ta da ido, me kuka je yi gidan su Asiya? Hafsi tace Uncle ni kawai rakiya na yi sai dai ka tambayi Anty. Yace "Karya kike yi, to da kuka je gidan me kuka ce?" Hafsi ta fito daga cikin kicin din, dan ta fara tsoron abinda zai biyo baya, zai iya yi mata duka, tace Uncle Anty ce tayi magana da su fa. Halifa ya yi tsaki ya fita. *** *** *** Ƙarfe goma kamar yadda masu gyaran jiki suka bukata Halifa ya kira Asiya yace ta shirya yana hanya. Yau Asiya nutsuwa ta yi domin tun amsa gaisuwarta Halifa bai sake magana ba, wannan ya sa ta shiga taitayin ta, tare da kame kanta. Har suka isa shagon yace in sun gama ta kira shi zai wuce kasuwa ne, ta yi masa addu'ar Allah ya bada sa a. ko da ya tafi bata bar mamaki ba tsoronta kardai wani laifin ta yi masa, ko kuma yanayi ne da ke sa mutum kan canza oho. Yana tsaka da kasuwa kamar daga sama sai ganin Bilkisu ya yi a gaban shagon sa, duk da facemaks ɗin da ta saka hakan ba zai hana ya gane ta ba. Daya daga cikin yaran shi yace, me take son siya? Tace gurin Megidansu ta zo. Yace Bari a sanar dashi. Halifa yace ta shigo ta zuna a kujera suka kawo mata lemo. Yana ta rubutun sa a wata takarda sai da yagama sannan ya kalleta. Lafiya na gan ki a kasuwa? Ta cire fasemarks din da ke fuskarta,ƙwalla na taruwa a idon ta ta ce. "Kaima ka san abinda zai kawo ni gurinka. Yanzu duk yadda muke baza ka yi min uzrin karamin kuskure ba? Afwa a soyayya wajibi ne Na maka Alkawarin har abada bazan sake ba, Wallahi Halifa ina son ka sosai bana bacci bana iya cin komai, zan iya mutuwa fa."ta ida maganar hawaye na ida saukowa kumatun ta. Ya kalli yaran shagon sa dake ta Kallon kallo, domin kowa najin abinda take fadi. Ya yi kasa da murya domin zuciyar shi tana rawa, haryanzu yana son ta in har ya barta ta ci gaba da zantuka nan ba shakka zata iya shan kansa. Yace kije gida za muyi magana. Tace " Kai min rantsuwa akan cewar zaka zo, in har ka rantse na yarda ya yi shiru. Yana son ya Lallaba ta kawai ta tafi." In baza ka zoba kawai ka sanar dani gaskiya." Baka saba yin karya ba kar ka fara domin ka faranta min. Ta sake daure shi,. Kije zan zo amma gaskiya ba yau ba, amma tabbas zan zo. Ta mike tare da faɗin "Ina jira dan Allah. " Zuciya Halifa ta fara rawa game da Bilkisu dan yana son ta, harya fara ganin kamar bai kyauta mata ba. Dole ya duba ya gani menene ya kamata ya yi. Sam ya manta da batun Asiya tana gurin gyaran jiki yace in an gama ta kira shi zai zo da kansa ya maida ta gida,, kiran mai gyaran jikin ta sanar dashi sun gama tun dazu ya sa ya tuna. Ya tashi ya sallami yaran shagon sa ya nufi titin gidan zoo. Sai dai ya na zuwa gadar dangi sai ya samu kanshi da tunanin ya fara zuwa cikin gari akwai bukatar ya yi magana da Bilkisu. Ta yi mamaki sosai lokacin da ta fito tabbas kuwa shine. Ta zauna a kujerar gefe bayan ta bude motar. Suka kalli juna tausayin ta ne ya cika zuciyar shi. Yace Bilkisu gaskiya har yanzu ina son ki, ina kaunarki matuka, amma kaddara ta sa zan auri Asiya, babu yadda za ayi in kaucewa Auren ta. Ina son ki dan bani lokaci kema zamuyi aure. Ta yi Dim domin taso ace ya hakura da batun wata sun shirya kan su. Ta soma hawaye cikin shashshekar kuka, tace "Bakomai na hakura zan jiraka, kuma ko ta Hudu ce in har zan same ka zan jira dan in ceci kaina daga mutuwa, nasan in har na rasa ka mutuwa zanyi." Yace baza ki rasani ba. Sun jima suna tattaunawa game da son da suke yi wa junan su daga bisani suka yi sallama bayan mai shagon ta sake kiran sa cewa sun kusa rufe shagon su. Haka ya taho yana dan jin haushin Asiya. Kallo daya ya yi mata tare da amsa sannu da zuwan da ta yi masa. Yace ta taso, bai kula wasan da mai shagon take tsokanar sa da shii ba tana cewa ya kaga amaryar fatan mu zamu yi mata kwalliyar ranar biki, ya dan yi yake tare da fadin " Insha Allah. Asiya ta yi tsam da ranta sannan ta kame kanta ganin yadda Halifa ya zo mata ayau. Sai da suka hau titi sannan ta dan saci kallon shi tace" Shi bawa yana barwa Allah lamarin shi a duk yadda ya tsinci kansa. Kuma nuna bacin rai a yayi da aka samu kai a cikin wata jarrabawa tamkar kin karbar ƙaddara ce. "Wani Abu ne kika ga ya faru?" Ya jeho mata tambaya cikin kamewa.. Ta girgiza kai ba da kai nake yi ba ina kokarin haddace karatun mu na jiya ne na islamiyya. Ya kalleta ita ma ta dake kamar gaske. "Ina wayata?" Ya tambaya ta dakko cikin sauri tace gata nan. An cika ta da chaji a shagon matar nan. Ya kallo Wayar sannan ya maida kai titi tare da fadin " Zaki iya gane gurin nan gobe kar ki jirani zan baki kudin mota ki zo ki koma." Tace sosai kuwa ina fage ina gidan zoo da kafa ma zan iya zuwa sai in bullo ta gadar Nasawa. Gidan Murtala ina tsallakawa sai layin gidan IG in fito layin gidan Bashir Tofa. " Ya aka yi kika san duk wadannan guraren? " Ya katseta da sauri. Tace na yi tallar Kankana da abarba a lokacin kakar su, yanzu ma ba dan zuwan ka ba da lokacin su na yi zanje Na'Ibawa yan lemo insaro in hau Dansahu zuwa titin gidan zoo daga nan in jera a tire ina tafe ina siyarwa har fage kafin naje ya kare. Kaga kuwa dole insan hanya. Bai kara magna ba har suka tsaya abin ya dame ta ta kalle shi. Tace To bansani ba nice ko a kasuwa ne wani ya sosa maka zuciya, amma dai ina mai baka hakuri Allah ya huci zuciyar ka a madadin koma wa nene . Bata jira amsa ba ta bude mota tafice ta nufi gida. Ya kira Sulaiman a waya yace yazo mota za suyi magana. Ya dubi Sulaiman ya ce ina jin wani bacin rai game da Auren Asiya kamar in fasa, gaba daya da yamman nan haushinta nake ji. Sulaiman ya rasa abin cewa dan takaici dan haka ya zuba masa ido yana ta kallo da sauraron abinda yake fada. Sai daya gama Sulaiman ya bude mota zai fita. Halifa ya rike masa gefen riga tare da fadin ka ce wani abu mana. Sulaiman yace babu abinda zance ka yi duk yadda ka ke so. Ya fizge rigarshi ya wuce. Lamura sun cude, an taso Halifa gaba Hajiya Talatu na yi ga Anty, gidan su Bilkisu suma basu, zauna ba. Duk da Halifa mutum ne jarumi yana tsaye kan ibada, ga sadaka ance tsafi gaskiyar me shi, dan haka sai da abin ya taba shi har ya rasa gane abinda ya kamata ya yi. Lamarin ya Shafi Asiya sosai har zuwa Ana gobe daurin aure bata samu ganin shi ba tun ranar da ya sauke ta. Dan haka bata koma takan mai gyaran jiki ba ga kuma jikin Baban su ya yi zafi. Ya sa aka kira mishi Baban su Sulaiman. Ya bar masa wasiyya cewar Koda Allah bai nufa ya ga gobe ba, yana rokon shi da su tabbatar an daura Auren Asiya, kuma yana son dan Allah ya sanar da Halifa cewa ya rike amanar Asiya kar ya barta ta yi kukan maraici. Ana gobe daurin auren aka wayi gari da mutuwar mahaifin su Asiya, Babansu sulaiman shine ya kira Baffan Halifa ya sanar da su mutuwar mahaifin su Asiya kuma ya fada musu za a daura aure bayan an dawo daga Jana iza sakamakon ya bar wasiyya. Halifa ya girgiza da jin labarin mutuwar kuma ya tausaya wa Asiya Dan haka shima ya nufo gidan mutuwar. Daren jiya ya gama yanke shawara da zuciyar shi cewa zai sa a daga bikin, sannan ya fara Auren Bilkisu, harma ya sanar da Anty hakan tana ta farin ciki tsarinta ya tafi yadda take so kuma aikin malaman ta ya yi ba shakka. To zata koma kan Bilkisu dan ta tsaya kar abin ya yiwu. Ita ce zata kawo wadda zai aura kamar yadda ta ke so. Bilkisu ta yi farin ciki komai yana tafiya yadda malamin ya tsara mata, gashi dai Halifan nata ya dawo gadan-gadan. Asiya suna ta kuka lokacin da za a dauki mahaaifinsu, ji take komai na duniya ya ishe ta, ina ma ace itace ta tafi ta bar su. Ji take bazata iya sake dariya ba har abada, Baban su ya tafi da dukkan farin cikinta. Lokacin da aka dawo daga kai shi makabarta gidan cike da dangi da makota, sai kuma taji wai za a daura mata aure. Sabon kuka ta soma domin kanshi Auren ya fita a ranta, musamman yanda shi wanda zai aureta ya ja kafa cikin yan kwanakin nan har zuwa yau batasan ya lamarin ke tafiya ba. Mijin Anty shine ya shiga da alawa da goro da kuma dabino yana sanar da ita an daura Auren Halifa. Kamar saukar aradu haka Anty da kawarta suka samu labarin, Cikin rawar baki Tace "Halifa munafirta ta ya yi kenan." Kar ki zarge shi. Inji Dady Baban yarinyar ne ya bar wasiyyar lallai a daura auren ko da bai tashi ba, sukuma dangi suka ga da cewar a daura bayan an dawo daga jana iza tunda duk watse wa za suyi ba zaman makoki za ayi ba. Cike da izgili Anty tace ba dole a watse ba, tunda in sun zauna me zasu ci, sai dai ma su ci da su. " Dady yace Ai dama haka musulunci ya koyar ba a ce wai dan an yi maka mutuwa ba ka zo kana ci da mutane, cewa a kayi mutane su tausayawa iyalan mamaci su basu sadakar abinci. Dan haka na yi waya Singa nace a kawo musu buhun shinkafa da taliya. Anty ta ja tsaki "Wannan Auren ban yarda da shi ba, sannan kuma ka kira waya ka sa a dakatar da kai wani abu gidan. Alama ta rashin sa a ta bayyana ga yarinyar nan ba yar albarka bace, ubanta ya mutu ana maganar aurenta kai gaskiya akwai abin dubawa a lamarin nan. Tsaki ya ja sannan ya wuce. Halifa suna tsaye da su Sulaiman mutane suna ta zuwa suna yin hannu da shi tare da masa murna. Shi dai amsawa kawai ya ke yi yana dan yake. Kana gani ka ga angon da ba shiri domin sanye yake da jallabiyya mai ruwan kasa wadda yake zuwa masallaci sallar asubashi da ita. Kiran Bros ya shigo cikin sauri ya daga yana cewa Bros ka dawo ne.? Yace na dawo tunda an daura maka aure yanzu haka ina kan titin IBB yi min kwatance in same ka a gidan inyi ta aziyya. Halifa ya yi masa kwatance . Sulaiman ya ce ya kamata mu shiga cikin gidan nan muyi ta aziyya. Halifa yace "Kalli jikina duk da dai gaisuwa zamuyi amma daga ni sai jallabiyar salla. Asiya ma bata san sun zo ba, sai ji tayi Ana cewa wannan shine angon. Bata ko leka ba dan babu wani abu dake birge ta. Halifa ya kira Bilkisu ya sanar da ita abinda ya faru ta zube tana kuka wiwi. abin ya zo mata a bazata sam bata taba zato ba. domin Malamin ta ya bata tabbacin cewa Halifa zai dawo fiye da baya kuma za su yi aure. Sulaiman ya kira sauran abokan su ya sanar da su abinda ya faru,bajimawa suka nufo gidan su Asiya. Daf da magariba Sulaiman ya kira Halifa Dan jin ya ake ciki game da kai Amarya? Yace to shi bai yi wani shiri game da haka ba, amma yana ganin zai fi kyau a bar shi sai anyi uku. Duk da haka Sulaiman yace yana ina za su same shi, yace yana gida. Can gidan suka same shi ya fito suka gaisa saura suka yi masa gaisuwa da murna ya amsa. Sulaiman yace na so a ce da ka yarda an kai ta yau an wuce gurin. Halifa Yace " Abarta sai anyi ukun kawai zai fi.kafin nan na gama abinda ya dan saura a gidan. Suka amince da haka. Halifa kwance a kangadon shi, ya rasa wane tunani zai yi tsawon dare har ƙarfe uku, ya mike ya dauro alwala ya fuskaci Ubangiji. Bai tashi ba har aka soma kiran salla ya fita zuwa masallaci, ko da aka idar da salla bai fito ba sai da ya zauna ya yi karatun safe wanda suka saba yi ya gama ya dawo gida kanshi har sarawa yake, idanun sa sun yi masa nauyi, ya kwanta bacci ya tafi dashi, sha daya bugun kofa ya farkar da shi. Sai ya ji zuciyar sa ta yi masa fes ya bude Hafsi ce ta sanar da shi Anty na kira. Tare suka tafi. Anty tace Halifa lafiya tun jiya nake neman ka. Yace "Ina gida jiya da yamma bakya nan, saboda rasuwar nan da kuma daurin auran nan shiyasa banje kasuwa baa." Ga mamakin sa sai yaji tace "To Allah ya jikan sa, ita kuma Allah ya sa matar gida ce, ga abinci can na sa a dafa anjima zamuje gaisuwa. Ya ce Anty ni gaba daya kuma abin ya dame ni, naji haushin kaina da banyi wa Bilkisu uzri ba. Tace" Halifa ka gane matar mutum kabarin sa, nima shiyasa na zubar da komai Allah ya baku zama lafiya. Yau she za a dauki amaryar ne? "Yace sai ranar uku ni yanzu zan shirya ne in tafi kasuwa. Tace" To bari in shirya mu tafi ka kaimu da abincin kuma ka kara gaisuwa ya kamata ace yau ka hakura da kasuwar kaje gidan ka yini. Yace jiya ban leka kasuwa ba shine dalilin amma ku shirya na kai ku din sai mu kara gaisawa. Duk an watse sai wasu daga cikin dangi kadan sai makota da suka dan kara shigowa. Asiya tana zaune tana kara tun ƙur ani iya abinda ta ke iya yi kenan ta ji sanyi, sai ta jiyo ana fadin sannun ku da zuwa ku shigo. Ta baza kunne sai taji ana ayi musu shinfida a dakin Baba inda a nan take a zaune. Kanwar innarmu ta shigo tana cewa ku shigo nan, har barin jiki take yi dan ta yi musu shinfida. Hajiya Talatu ce a kan gaban shigowa dakin sannan sai Anty A gigice Asiya ta Mike tsaye. *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [5/29, 13:51] Ummi Tandama😇: Suka kalli juna da Anty, ta yi wani murmushi mai wuyar fassara ga Asiya Allahumma ajirni fi musibati Asiya ta fada a kasan zuciyar ta. Anty tace Allah Sarki baiwar Allah sannu kinji Allah ya baku hakuri ina Uwar ta ku? Asiya ta fita da sauri tana fadin Inna kije ku gaisa. Inna ta zauna daga bakin kofa, suka gaisa. Anty tace "Allah Sarki sannu da kayan lada gaskiya wannan mutuwa ta dake ni ta fashe da kuka. Hajiya Talatu ta saki baki tana kallon al ajabi Anty tana kuka tana fatar hanci ana ta bata hakuri. Lallai akwai wani makirci Babba da ta hada. Inna tana sharar kwalla tana fadin Kiyi hakuri muma dai hakuri muka yi. Ta ce Ina Amarya mijinta yana waje ta leka su gaisa. Nan take kanwar Innar su Harira ta ce ki saka hijabi ki fita. A soro ta tsaya ta leka, yana zaune a dakalin gidan su Sulaiman yana waya. ta daure ta fita tana isa ya katse wayar ya kalle ta ta risina ta gaishe shi. ya amsa tare da fadin "Ya hakuri?" tace Alhamdulilah. Yace Alllah ya jikan Baba tace ameen ya rabbi. Ta ce sai anjima ta juyo ya bita da kallo cike da tausayinta. Duk ta kara ramewa dama ya lafiyar giwa. Ta koma cikin gida. Bayan tafiyar su aka yi ta maganar yadda Anty ta ci kuka Ana bata hakuri, nan aka shiga nuna wa Asiya cewa ta rike Anty ƙauna ce ya sa ta nuna kulawar ta gare su. ta yi mata biyyaya kuma ta rike ta tunda ita ce ta tamkar uwarshi kamar dai yadda ta basu labari. Asiya dai tana sauraron kowa amma zuciyarta ta kasa nutsuwa da abinda Anty ta yi, ta tuno zagi da kuma gargaɗin da ta yi mata cewar karta sake ko da wasa ta auri kaninta, ta nuna kyama da kyankyami gare su amma yanzu wai tana kukan mutuwar wanda ta ciwa zarafi. To duk da haka ta kudurce zata yi mata biyayya fiye da yadda aka fada mata.. Halifa yana kwance yana tunanin gobe za a kai Amarya duk da gida ya kammala amma ya san su Asiya ba su da abinda za su zuba a gidan dan haka dole ya yi daya cikin biyu ko dai ya sayi kaya ya zuba a gidan ko kokuma ya bata bangaren bakin gidan tunda bashi da girma abinda Allah ya hore masu sai su zuba mata a gurin. Wata zuciya tace ka zuba kaya kawai. To shi komai lissafine a gurin dan kasuwa. Ya tura oder bata karaso ba, sannan ga wasu kudade da yake jira shiru ba su shigo ba. A haka bacci ya kwasheshi. Da safe ya shiga ya samu Anty a falo ana yi mata kitso ta can baya ya jiyo hayaniya yace lafiya? Anty tace ango da kanshi ka ke tambaya yaune taron mu na nan tunda yau za a kawo Amarya dukda dai mutuwa a ka yi ai ma Ɗan taru ko? Halifa ya yi murmushi, mata sarakan bidi a. Tacewa me kitson dan tsaya zamuyi magana ta nufi tsakargida tare da fadin Halifa ya zo su yi magana. Ta dube shi, tace "Ka kai musu makullin gidan ne? Ya yi dan tsaki yace Ni na rasa ma ina za a kaita gidan can ya mata girma sai dai na bata gefen baki sai yanzu nake ganin gaggawa ta da tuni har za a tashi wani cikin kananan gidajan nan na Kundila ya isa a Sakata a ciki . Anty tace zo muje, suka nufi gefen shi, tace dubi dakinka sai anso a kara fenti zata yi zaman ta a ciki in ta kara wayo ta warware sai ku kama can. Ya danyi shiru baya ra ayin zama da matarsa a inda ya yi samartaka. Sai dai dole ayi hakan na wani lokaci. Ya dube ta, to Bari zan kira me fenti in zai yiwu yau din ayi a maida kayan. Anty Tace " Ba zata zo da kaya ba kenan ko yaya?" Ta tambaya cike da kwanciyar hankali. Yace To naga Babansu ya rasu kuma dama yana cikin halin jinya. Anty tace hakane to ka daure ko baka canza komi ba ka canza gado, kayan aikin kicin dai na san ko da sadakin ta zai yi mata. *** *** *** Kamar yadda Baban su Sulaiman ya sanar a masallacin sallar asubahi cewa dan Allah kowa ne makoci ana son ya bada gudunmawar abinda Allah ya hore masa za ayi wa yar gidan marigayin kayan daki, abin Allah sai gashi nan da nan an hada kudi masu kauri a ranar bayan gama addu a ya nufi Gwauron dutse shi da daya maƙocin na su inda ya saya mata kayan gado da kujeru katifa kadai ya saya da kudinsa. Innar su Asiya ta saka kuka dan murna ga sadakin ta ya kawo ya danka mata. Kamar yadda Anty ta tsara hakan ne ya faru, domin da Sulaiman ya kira Halifa yace za a kawo kaya suna son makullin gida, sai yace ai gidan su za a kawo amaryar can gidan ba a gama gyara ba. Lokacin da kayan suka Iso tara da yan jere Kanwar Innar su Asiya itace Amara gashi ta kaunaci Anty tunda Antyn ta nuna kauna da tausayawa dan haka masu jere na yi tace bari taje ta gaida Hajiya mutuniyar kirki. Gidan cike da mutane Harira kanwar Innar su Asiya ta taje gaban Anty tana mika gaisuwa Anty ta amsa tana kare mata kallo, tace inaga kuwa na san ki ok kawar mai aikin gidan su kawata ko? Harira tace "A a kanwar mahaifiyar, su amaryar. Anty ta kalli Hajiya Talatu, oyoyo sannun ku da zuwa, kai ku bata gurin zama cike da izgili take maganar, ita kuwa Harira dadi ya rufe ta abinka da mutan kauye, sai take jira a bata gurin zama. Hajiya Talatu ta kasa kunshe dariyarta sai da ta sheke da wata dariya tare da wasu ƙawayan su..Anty Umaima kanwar Anty ce itama yayar Halifa ce, sun zo ne kawai dan Halifa amma ko ziyara ta haka kawai ba su cika zuwa gidan Anty ba, yadda ta ke musu gadara akan komai. Ta kalli Harira tace " Baiwar Allah ki koma can gurin jeren naku kar yara su yi muku barna. " Harira tace za ko su iya ta juya da sauri tana cewa Anty Hajiya muna godiya. Anty ta bi bayanta da daƙuwar zagi tare da fadin to ga yan rakiya nan. Asiya ta fito wanka aka bata sabon Kaya cikin dunkunan da Sulaiman ya yo, ta saka tana hawaye tunda akace ga motoci nan hankali ta ya tashi ta shiga kuka wiwi, Da kyar aka banbareta a jikin Inna tana cewa dan Allah ku barni sai anyi bakwai Inna tace kije gidan ki Allah ya baki sa a. Ta kalli Dakin Baban su zantukan sa suke mata yawo a kai. Inda yake cewa"Asiya bazaki yi da kinsanin yin aure da Halifa ba. Allah ne ya kawo miki shi." A haka aka sa ta a mota sai gidan miji. Gidan babbane da bishiyoyi a yankin masu hannu da shuni, su Anty ne ke zaune a ainihin gidan ya yin da su Halifa da bros suka yi rayuwar su a gefen daukar baki duk da cewa gidan mallakinsa ne bai taba damuwa da hakan ba. Nan aka kai Asiya Falo ne da daki biyu kichin a falo sai bandaki a dakin da aka sa mata gado. Shi kuma gadon da ya siyo aka sa a ɗaya dakin. Kamar yadda yake a al ada bayan sallar Isha abokan Halifa har da wasu daga cikin yan kasuwa suka rako shi. Asiya tana zaune ita daya a falo sanye da hijabi ta sunkuyar da kai a haka suka gaisa. Anyi nasihohi suka aje ledojin hannun su suka yi mata sallama ya tafi rakasu. Gaban Asiya ya yawaita faduwa ba wai tana tunanin ko Halifa zai nemi hakinsa ba a a, yaya ma zai karbeta. Ya shigo da sallama ta amsa tare da bin fuskarshi da kallo ko zata fahimci wani abu. Shima ya kalleta yanayin da ya nuna bai wuce ace kamar yanda yaya zai mu amalanci kanwar sa ba, yace kina jin yunwa, ta girgiza kai alamun a a. Yace ki yi magana da baki mana. Tace "A 'a. Yace me kika ci? Tace" Ba komai bana jin yunwa ne., " Ya ce To, kije ki kwanta,ta kalleshi a wani littafin Hausa da ta karanta ance ango da Amarya suna yin wata salla dan neman samun zama lafiya. Tace" Sallar fa" Wace salla kuma ko bakiyi Isha bane? Tace "Nayi mana naji ne ance ne ana yin salla domin neman zama lafiya." Ya yi dan murmurshi. To kuma gashi ni ban iya ba, ban taba ji ba ma, amma zan tambaya. Tace ka tambaya mana yanzu ance fa a rana irin ta yau ake yi ranar da miji ya fara shiga dakin matar sa, in ya wuce ranar kamar fa baza a karba ba. Dariya ta kufcewa Halifa ya je ya kulle ƙofa. Ke dai ki kira ki tambaya a inda kika ji. Asiya ta zuba mishi ido cikin mamaki iya gaskiyarta take magana, amma sai taga kamar baima fahimce ta ba, ko kuma auren ta bashi da wani mahimmanci ne a gunsa. Ta sa kai ta nufi dakinta ta cire hijabi jikina ta bude akwati tana duba kayan bacci. Maman Annur ce ta ce mata su zata saka duk in zata kwanta. Lokacin da suke kallon kayan lefen. Ta saka ta je ban ɗaki ta dauro alwala, ta saba da kwanciya da alwala ta yarda sosai cewa babban tsari ne. Ta mike a kan lallausan gadon, Allah sarki ƴar tabarmarta ta yi kewar ta. Tayi juyi a fili tace Allah ka bamu ni'imar kabari. Ta tuno da mahaifinta wanda yanzu yana can kwance, Allah ya sa yana cikin dausayin Aljanna. Hawaye suka soma kwaranyo mata suna bin gefen fuskarta, kuka take a hankali har bacci ya yi gaba da ita. Halifa ya shigo dakin, bacci take yi sosai ga iskar fanka ga ta laushin katifa ba sauro. Ya kalli hawayen da ya bushe a gefen fuskarta, sai tausayin ta ya kama shi. Karan wayar sa ya jiyo daga falo, ya tafi ya duba Anty da wannan daren ya furta a fili. Tace Ta katse shi da fadin, "Kana jina ko Halifa nace Dan Allah kar kaji wani iri akan maganar da zanyi maka. Dama zance ne karka takurawa yarinyar nan Dan Allah, ka kyaleta ta gyagije, ga mutuwa anyi mata tasamu kamar sati biyu, ni nasan abincin da za a ke bata yadda zata murje." Maganar ta zo wa Halifa a wani banbarakwai. Yace to sai da safe. Anty tace ina jin dai ka gane me nake nufi?" Yace A haba kar ki damu. Ya kashe cike da mamakin yadda Anty ta iya yi mishi wannan maganar. Anty ta aje wayar cike da jin daɗin haƙan ta zai cimma ruwa. Saboda malamin ta ya Tabbatar mata da cewa aure ba makawa zai auri yarinyar sannan matsawar zata matsa kar ayi to zata mutu, tauraron ta yana da girma da kuma haske da yafi na shi Halifa, da tazara tsakanin su kamar kimanin Sarki ya ka sa bafaden sa, yace in son samu ne kada ta bari a samu daidai to a tsakanin su, saboda duk ranar da ya sadu da ita sai fa abinda suka gani. Cikin tashin hankali tace Malam yanzu Sai ina saka ido Kenan? Yace ko kusa, aiki za ayi amma yana da sharadi tunda har ankai ga daura aure to ki kwantar da kai ki hana a tare har zuwa daren Alhamis zan hada miki aikin da washegari juma'a zai tafka mata saki. Kinsan masu irin wannan tauraron da su masu kudi ke hada tsafi ta hanyar dauke musu shi. Shine zaki ga anba yarinya wani abun duniya an karbe mata tauraro ta hanyar saduwa da ita akwai abinda muke sawa su kawo mana muna hada musu asiri da shi. Nima dai ladan aikina shine ku kawo min yarinyar nan zan yi amfani da taurarinta dan samun shuhura. Anty ta yi masa Alkawarin hakan. Da wannan take son hana Halifa aiwatar da komai. da iyalinsa. Ta lissafa auren da Juma a ne, sai aka daura Alhamis ta tare lahadi, zata tsaya tsayin daka dan ganin komai ya kammala. Halifa kuwa zantukan, Anty sun tsokano mishi abinda ya sha na maganin basir da sanyi, ga hadin maza da wani abokinsa shima ya sa yake ta banka lokacin maganar su da Bilkisu da abubuwa suka cabe shine ya manta da komai, yanzu kuwa kamar ta masa allura, sai dai bisa adalci ya kamata ya kyaleta ko Don zafin mutuwa, dama ba dan ita ya sha ba. Da sassafe Anty ta kira Halifa wai sun kuwa tashi tana son ta zo su gaisa. Yace "Haba Anty zata zo. ta gaishe ki, ai ko gidan giya akwai Babba. Tace ai bakonka Annabin ka, ni din ma sai inzo..... . *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,alfarmar following zata ƙare a 10-june-2025, daga ranar duk wacce batayi following ba,sai dai tabi hanya ta biyu, hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank,* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [6/2, 18:43] Ummi Tandama😇: Asiya ta idar da sallah ta zauna tana adduo'in fatan Allah ya jikan Babanta, ta yi godiya da ni imar Allah a gare ta, ɗakin nan irin dai wanda take gani a fim. Insha Allah zata jure komai domin ta samu kan mijinta. Ya shigo sanye da jallabiya ta tashi da sauri sai ya tsaya Kallon ta ya zata wani abu ta gani. Tace Ina kwana? Yace "Lafiya lau ina zaki naga kin tashi da hanzari?" Tace Aljanna. Ya dan yi dim bai fahimta ba. Tace to ance min gurinka zan samu kuma gaskiya ni dai ina son shiga. Ya yi murmushi" Allah ya baki iko.," Tace Ameen kai kuma ka bani dama ba." Na ma baki tunda na aure ki. Yanzu kiyi wanka ki canza kaya waɗanda suka miki daidai zaki sa ki fito ina jira ki a falo. Tace to mabudin Aljanna ta yanzu zan yi yadda kace. Ya fita yana mamakin Asiya to ko dai ba yarinya bace. Ta saka riga da siket na atamfa ta yafo mayafi ta fesa turare ya kalleta shi mutum ne ma'abocin kamshi. Ya bita da kallo tace a kwai wani abu da bai yi daidai ba ? Ta tambaya cike da salo. Yace babu tashi muje ku gaisa da Anty. Gabanta ya yanke ya fadi. Tace Anty kuma, bata tafi bane? Yace ina zata? ai nan gidan take. Ta hadiye yawu ai ban sani ba. Ta fada in'ina Yace "Menene naga duk kin canza?" Ta girgiza kai, babu komai kawai dai na zata jiyan sunzo ne. Suna kan gado ita da Hajiya Talatu suna ta zantukan su da suka saba, Hajiya Talatu tana son taji abinda Anty ke boye mata na game da canzawar ta game da Asiya. Anty ta diro da sauri, a a Halifa kune shigo kinji Asiya ta kama mata kafada Asiya ta zube da sauri tana fadin Ina kwana Anty. Lafiya lau zo nan ki zauna bakin gado mana. Asiya ta zame ta zauna kan kafet tare da fadin nan ma ya isa. Hajiya Talatu tace"jiya da aka kawo ki ba'yi irin yadda ake yi in an kawo Amarya a zo a bada amanarki ba,da kinga dangi sosai. " Asiya ta kalleta ta rasa ita kuma wannan din wacece ta kula da wani kallo da take mata irin na ke kuma ke da wa. Anty ta amshe ai ba komai, zata san kowa tunda an zama daya ki saki jikinki kinji Asiya. Ta daga kai alamun to. Anty ta ce yanzu za a kawo miki abin kari, ki zage ki ci kinji ko? Nasan har yanzu akwai damuwar rabuwa da mahaifinki, Kiyi ta masa adduo'in kin ji? Asiya tace to na gode. Halifa yace ni Bari inje inyi wanka. Asiya ta yi zarab ta mike Hajiya Talatu tace ki dan tsaya mana ana miki nasiha shi yaje ya shirya. Anty tace e dan jira kadan. Daya fita sai Anty ta ce Asiya ina baki hakuri akan zuwa na gidanku dana ci zarafinku lokacin karya aka zo aka yi min a kanku ance ke mahaukaciya ce kina da aljanu. Ni kam ina tsoron cin amana Halifa maraya ne shiyasa. Amma kii yafe min Allah ya huci zuciyar ki, shiyasa nayi ta kuka ranar da na zo gidanku ba yadda zan nemi afuwar Babanku ya mutu shiyasa, ta sake sassauta murya cikin yanayin tausayi, dan Allah kin yafe min? Zuciyar Asiya ta karye, tana da saurin yarda ga tausayi ba shakka Anty duk abinda ta fada gaskiya ne dan haka sai ta ji ta yarda da Anty, tace Anty ai ba wani abu ya wuce ba komai. Anty tace "Allah ya miki albarka ki rike mijinki Halifa bashi da matsala. Hajiya Talatu ta fara kokwanto ko dai Anty har zuciyarta tana son yarinyar nan. Asiya ta kalli Anty wannan ma Antyn Halifa ce? Anty tace e amma kawata ce ba wani abu suka hada ba. Hajiya Talatu ta yatsina baki tana Kallon su. Sam bataji dadin wannan yarfin ba, Asiya ta mike tace to bari inje ko ya gama. Anty ma ta mike zaraf ta biyo ta. "Kina jina ko Asiya. Ta tsaya ta kalleta Anty ta ci gaba da magana kasa kasa, nasan kina cike da jimami na rasuwar mahaifin ki, ina so ki kwantar da hankali ki, shi kuma Halifa na san zai miki uzri ki warware. Duk da Asiya bata fahimce ta ba, sai ta gyada kai alamun eh tace yawwa to jeki maza. Tasamu ya gama wanka yana sanye da shadda ruwan kasa ya yi kyau. Ta yi murmushi haka ka ke da kyau dama, kamar wani Ango. Ya ce "To da wanene in ba Angon ba?" Tace Gaskiya dai kai ba Ango bane. "Dalili?" Ya tambaye ta cike da wani shuki da yake ji. Tace baka ƙiyin sallar ma'aurata ba. Ya rike baki, wai ke me kike nufi ne? " Ta dube shi bana nufin komai wallahi, kawai dai ban so ka ki yarda muyi sallar ba, to kai me yasa baka zo munyi ba baka son zama lafiya din ne kokuwa dai ni ce matsayi na bai kai a yi sallar da ni ba? Ta kai karshen maganar tana dariya. Halifa ya sauke ajiyar zuciya, in an idar da sallar fa me ake yi. Ta girgiza kai bansani ba gaskiya sallar dai ka dai nasan ana yi. Ya yi murmushi ni kuma na san saura abubuwan da ake yi in kin yarda zamu yi to. " Tace Shima din ibada ne? Yace sosai kuwa har yafi salla din ma. Ta saka dariya, to azumi ne? Yace " A'a tace to ni ko wace ibada ce wannan da ba zan santa ba? Ko kuwa zikiri da salati ne? Yace ki dai yarda kawai zaki gani. " Tace to shike nan na yarda amma na so a daren farko mukayi Sallar nan. Hafsi ta yi sallama suka amsa ta aje tiren a teburin gaban kujera. Sannan ta ce Uncle ina kwana suka gaida. Asiya ta kalleta, tace sannun ki yama ni kuwa sunan matar? Ta tambaya cike da son nuna kulawar ta. Hafsi ta kalle ta kallon ke kuma a su wa, Sannan ta fice. Halifa wanda bai kula da abinda Hafsi ta yi ba yana bude abincin yace sunan ta Hafsatu muna ce mata Hafsi. Asiya tace Yawwa na rike. Bayan sun karya Asiya ta na ta jin kuyar cin abinci gaban Halifa har yana tsokanarta da cewa a haka za mu yi sallar ma auratan da ki ke ta fada? Bayan kina jin kunya? Tace to salla menene damuwarta ita kuma.? Yace shikenan har na matsu dare ya yi muyi salla da sauran ibadu. " Asiya ta shiga daki tana yar dariya. *** *** *** Wayar ta shiga ruri ta dakko sunan. Sabon malamin ta ne, ta kalli Talatu wadda ke gyara farce, Anti ta kai makura da gajiya da Talatu lokuta da dama tana son sirri amma ta zo ta yi mata katutu, ya ma zata amsa kiran Malam a gaban ta, bayan bata son ta san shi. Wayar ki ake kira fa. Talatu ta fada tare da kokarin leka fuskar wayar. Anty ta dauke wayarta tare da fadin bana son tsegumi Talatu dan Allah tunda an gama biki sai ku hada kayanku ku koma gida kin bar mijinki shi kadai gashi kin gama da shi ba zai iya cewa kala ba. Talatu ta taba baki shege yi da mai zina, Allah ya sa kema dai naki Mijin a shanye yake, au korarmu ki ke yi ne, to gobe zamu daga mu bar miki gidan ki. Talatu ta fada tana danna Rikodin na wayarta. Ta aje wayar ta mike bari ince Ma u ta hada kayan ta mu wuce. Tana fita. Anty ta kira Malam suka gai sa, tace yanzu na ga missed call Malam. Yace Kinga da zaki yi wani abu da kun samu biyan bukata da daukaka sai dai yana da wahala. Anty tace menene zanyi? Malam yace ki kawo min yarinyar nan gobe da safe, ya zama ni ne zan fara kusantar ta akwai wani lakani da rauhanai suka bani yanzu sunce in yi biyan bukata da sabuwar Amarya mai irin tauraron ta, da maijego sabuwar haihuwa da kuma tsohuwa muharramata ko Mahaifiyata ko wata yar uwarta. In na yin wannan aikin Hajiya zan samu wasu damarmaki ne da iko, zan iya yi miki aikin da in kina bukatar dukiyar Halifa ta dawo hannunki kaf zata dawo ba lauyoyi ba ko alkalai ne sai sun kawo komai da kan su na game da dukiyar shi sun baki matsawar ki ka tambaya za su baki, kuma ba wanda zai taba tambayar ki ina wata kadara ta sa. Sannan zaki zama mai shahara a Duniya ta yadda ko ina za a sa ki, gwamnati sai ta so ta yi hulda da ke ko da kuwa ba wani Abu da zaki amfana mata." Anty ta mike cike da jin dadi Malam ka tabbatar hakan da ka fada za su faru? Yace "Kar ki yi wata shakka hakan zai bata mana aiki. Abinda kawai nake son ji zaki kawota?" Anty tace to ina zaka samu sauran Matan? Yace " Duk na samu, domin matar ɗana ta haihu zan yi amfani da ita kuma ina da Uwa ina da kanwar ta samu daya cikin su ba zai min wahala ba, samun sabuwar Amarya ma ba zai min wahala ba mai irin taurarin ta ne wahala dan baifi kamar a watsa biyar a cikin dubu ba, haka ta ke, yanzu dan ba a bude taurarinta ba ne shiyasa bazan gane ba, yana kwanciya da ita kuwa shikenan ya bude mata taurari kuma tauraron sa da nata tamkar bawa ne da ubangidan shi.kuna kallo zaku hakura dashi. Dan haka ni zan bude su taurarin na ta." Anty tace na gane zan San yarda zanyi tun yau ba sai goben ba in kawo ta. Sai dai ina tsoron karta zo ta fada masa. Ya saki dariya mai karfi. Zan mantar da ita komai, banda wannan tauraron nata ai kasheta zan yi kuma ba wanda zai tambayi ina take har abada. Anty tace to Malam ina godiya in mun samu zuwa yau in kuma sai goben to ba matsala? Yace "Ba damuwa kar a wuce gobe dai. *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [6/9, 10:43] Ummi Tandama😇: Anty ta yi sallama a kofar dakin Asiya, Halifa ne ya amsa, gabanta ya dan fadi amma saita dake, yace ki shigo Anty mana. Ta shiga tana waige waige," Ina yarinyar nan ta ke?" Yace tana bandaki bari na kira ta. Tace Dama so nake anjima idan rana ta kara sanyi zan kai ta gidan Baaba harda Baffanku Dan 'yan uwanta ba su kai ta ba, sun bada sallahu cewa a kaita, to bana son abin ya ja lokaci ya zama shiri ririta." Halifa yace Anty ki barshi kawai ni sai muje tare in kaita na hutar da ke. Da sauri tace, " Wa ya fada maka ana haka? Ai wannan al adace mai girman sai a dorawa iyayenta laifi ace sun rai na danginka , kuma bayan sun bar sallahu. Dan haka ni zan kaita. " Halifa yace to ba matsala ni sai in kai ku. Da sauri tace. "Sai kuma ya zama abin magana, ba a zuwa da Ango." Halifa yace a musulinci ne zai zama abin maganar ko a me? Anty wani abin ma ku mata kuke ruruta shi, to yanzu sai a kira Bros ya kai ku ko? Tace Dan Allah ka samin ido kawai bazan jera da shi ba, dan shima ina cike da shi na tura mishi lambar yarinyar da na samo mishi yaki kiranta, sai yana ce min wai wayar bata shiga kuma karya ne. Halifa ya ce Anty Dan Allah ki kyale Bros da batun auren nan, kawai ki bari ya zaba da kansa, ko zamanin ku fa ba ayi muku haka ba. Karo na farko da Halifa ya kware mata baya akan maganar Bros. Ta dan yi dim Dan tana samun kwarin gwiwa daga gunsa da kuma tirsasa Bros din ta gurin shi. Tace "Bar maganar shi kawai ka fada mata in ta fito sai ta shirya. Yace to ba damuwa. Asiya tana toilet ta gama ta kasa Floshing tana ta tarar ruwa tana makawa amma yaki wucewa duka, bata san Halifa ya shigo ba. Sai taji maganar shi a dakin yana fadin lafiya kuwa fin minti arba in. Ta leko ta bata rai ni kam in da wani ban daki a tsakar gida can zan na shiga. Ta fada tana tura baki cike da shagwaba. Yace to wannan menene matsalar shi?" Tace ina ta zuba ruwa amma yaki wanke wa. Halifa ya gane fuloshin ne matsalar, yace" Kuma kin danna gurin zubowar ruwa?" Tace ina ne gurin? Ya nufo ban ɗakin ta kulle da sauri tace ka fada min yace to ki danna wani guri a sama tukunyar nan ta makale. Allah ya ba Asiya sa"'a ta danna sai taji ruwa da gudu ya wuce da bayan gidan nata. Ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin Allah ya kyauta rashin sani. Ta fito ban ɗakin domin ta fesa turare duk da ba wari amma sai tana jin kunyar fita. Daga can cikin falo ta jiyo ana magana kamar muryar Maman Annur da sauri ta leko, su ne kuwa da yan layin su wasu yan mata. Murna Asiya kamar ta cinye su. Halifa ya gaisa da su ya koma daki, suka zauna ta bude firji ta dakko musu ruwan roba da lemo, suna ta Kallon ta cike da shi awa. Ta nufi dakin tana ce musu ina zuwa. Yana zaune bakin gado yana danna waya, tana shiga kamar ya dan razana ya aje wayar ta share kamar bata kula ba, tace zan dafa musu abinci. Yace "To ai kinga ban kawo kayan abinci ba, kawai ki kawo masu kayan tea da baredi kajin da baki ci ba suna firji sai ki kunna gas ki sa su a oven su yi zafi." Tace Ban iya. ba fa ko kunna gas ban taba yi ba, kuma bansan ina ne ma oven din ba. Yace muje in nuna miki ya koya mata komai sannan yace yar kauye, cike da tsokana. Tace naji Dan birni na samu karin ilmi yanzu ko ina naje na san oven da yadda zan sarrafa shi, kuma na iya kunna gas. Ya fito yana dariya ya shiga daya ɗakin ya sake daga kiran da Bilkusu take masa ta Vedio call. Kuka sosai take tana tambayar shi cewa "Dan Allah ya fada mata ya kwanta da Asiya ajiya? Yace Bilkisu ina rokonki ki daina wannan maganar sirrin gida na ne, bana cikin masu irin wannan shirme, ki yi magana akan abinda ya shafe ki ya shafe ni kawai. Ta sake fashe wa da kuka "Wai tafi ni kyau ne ko ta fini dirin jiki ne har da zaka kwanta da ita bayan ka jima kana fada min cewa tun da kake baka taba sanin wacece mace ba a kaina zaka fara, me yasa ka kasa sadaukar min da kyautar da ka jima da bani. Halifa ya yi shiru ya kasa magana, abinda bata sani ba, zantukan ta suna motsa shi suna tada masa hankali yana jin bukatar sanin macen. Ya jure yace, "Ki yarda da kaddara mana. Asiya ce ta sake murda kofar ta shigo ya sake kife wayar da sauri yace ya aka yi na barki na gudo nan kin biyo ni?" Tace dama zance maka in kai su su gaida Anty ko? Ya kalli sashen kirjin ta, sai ya ji wani abu tundaga tsakiyar kan sa ya dira babban dan yatsan sa. Da gira ya amsa mata tace Kamar kana jin bacci yace" Sosai ma zan kwanta Dan Allah ki saurari bakin ki ko? Tace to, ta Juya yabi dan kugunta da kallo "Shine halas dinka wata zuciyar ta sake rada masa ya yi mika ya kwanta sannan ya daga wayar shi da ya kifa ta ganin ta kashe, ko data kira ya ki daga wa. Asiya ta raka su Maman Annur gurin Anty sun gaisa ta yi musu fara a ta sa aka aiko musu da abinci. Suna gidan har bayan magariba haka ya yi wa Anty cikas, dan ta kira Halifa yafi sau shida yana cewa bakin ba su tafi ba, ya kara da cewa Anty a bari sai gobe mana tunda yanzu magariba ta yi ba iya gaisuwa zataje ta musu bane ki daina daga hankalin ki akan karamin abu mana. Tace so nake in wuce gurin kawai in huta ba wai dan wani abu bane. Yace ki bari sai gobe, tace to Allah ya kaimu, sannan ina sake roka mata alfarma ka barta ta warware kaga yadda take a jeme. " Cike da kosawa yace to Anty ya kashe wayar. Asiya ta idar da sallar ta dakko maganin da maman Annur ta kawo mata a jarka ta daga tana sha, duk da bata fada mata ko na menene ba ta san dai na mata ne tana karantawa a litattafai. Ya shi go ta yi sauri ta boye dan tace mata karta bari ya gani. Ya tako a hankali zuwa kusa da ita ya kai hannu ya dakko robar, yace menene wannan ki ke sha ki ka boye dan kar ki sammin? Yar rowa ce tsakanin mu. Ta ji kunya ta turo baki cike da shagwaba tace Haka aka ce kar in Bari ka gani, nima bansan ko na meye ba wai ance maganin sanyi. Ya yi dariya ya dan kurba tare da fadin "Wai nan ke harda maganin mata ki ke sha ko? Ta zaro ido tace me yasa ka sha ance fa banda maza. Ya aje robar" Ta shi muyi sallar jiya da ake ta min korafi. Suna idar wa ya kawo kaza mai dumi daya ciro a oven da madara mai sanyi ya aje gefen Sallaya yace, wannan ake fara ci idan aka idar da sallar. Ranar kam ta ci, suka gama yace sai kuma ibada ta gaba nace miki a hade suke. Tace gashi bani da carbi ko zaka bani naka. Ya yi dariya yace kiyi wanka ki shafa turare ki sa kayan bacci ki same ni a wancan dakin tace to. Duk da gabanta yana faduwa kuma sarai tasan nufin shi, amma ta yi alwashin zata jure komai dan ta same shi. Yana kwance rigingine yana danna waya ta shigo ya bita da kallo ki cire hijabin mana. "Ta zaro ido yace in ba zakiyi ba koma ki kwanta shiyasa ai na fada miki. Cikin kunya.,ta cire sai kayan baccin sun mata yawa wando gere da riga wando ma kulle shi ta yi da dankwalin jallabiya, ya yi kamar bai gani ba ya kumshe dariya. Ya taso ya janye mayafin da sauri wando ya fadi ta tsugunnna da sauri tana fadin innalillahi na bani. Ya kamo hannun ta, "Kina ta yin saurin cewa mu yi salla to munyi sai kuma ki zo mu kwanta. Kallon shi cikin firgici ta yi, a idanun shi da zargi abinda ke shirin faruwa, ta zauna shima ya zauna. a gaban ta. "Ta so muje gado. Ta girgiza kai me zai faru? Ya kai bakinsa kunnen ta yace ibadar zamu yi." Tace a gado kuma? Ya ce "E mana." Ta girgiza kai ina jin tsoro. Ta fada cike da tsoron. Ya dauke ta cak domin shagwabar tana kara tsuma shi.ya dire ta kan gado. Wayar shi ta soma ringing tace ana kiranka a waya. Cikin rawar murya yace ki barta kaiwa. Hajiya Talatu ta gama sauraron rikodin din da ta yi, ta girgiza kai, tare da fadin Koda naji, lallai ruwa baya tsami banza tasan dole akwai wata a kasa. Anty ta zarce ta a mugun hali. Aiko zata ga yadda ake yin bariki ta sha alwashin sai ta cimma nata burin da wannan muryar da ta dauka. Ta shiga shirin tafiya Dan tsarawa ta yarda zata fita da fitar ta. Duk su biyu sun wahala kafin su cika wannan ibada. Halifa har ya ji tsoron kar wani ya jiyo muryar Asiya da irin magiyar da take masa, Amma sai ya rasa dalilin yadda ya ke jin cewa kaimi take. kara masa. Ya kai hannu ya rungumota zuwa kirjin sa yana maida numfashi. Ya kasa magana. Asiya ta lumshe ido tabbas tasan ana cewa ana kwanciyar aure domin tana karance karance amma batasan lamarin ya kai haka ba,amma ta gode wa Allah da ya sa mijinta shine mutum na farko da ta sha wannan wahakar a gunsa, a hakan mata suke mika kansu gurin wasu mazan na waje a banza kawai a ba su wasu yan kudi. Gaskiya ita dai aure kadai zata iya yi wa wannan sadaukarwar.. Halifa ya ji wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali, sannan ya ji wata kauna ta yarinyar ta mamaye shi..Duk da cewa a. makarantar su ta islamiya an koya musu wankan tsarki amma sai Asiya tace wa Halifa bata san ya ake yi ba a aikace yace yanda ki ke yin na wata wata ne, niyarce banbanci. Tace to. Da safe ma Halifa yana ta ji da Asiya duk wani motsin ta yana kula da shi sosai.. Anty da kanta ta kawo musu abin kari tace Asiya ta shirya kamar karfe sha daya za su tafi. Halifa ya kalleta zaki iya zuwa? Anty ta yi zaraf tace lafiya ka ke tambayar ko zata iya zuwa? Halifa yace bata jin dadi ne. Anty tace ashsha meke damu ta? *Asiya ta yi saurin cewa dan zazzabi ne zan iya zuwa. Bayan ta fita, Halifa ya kama tafin hannun ta me yasa ki ka bata amsa ai da kin bari na fada mata abinda mukayi. Asiya ta zaro ido" Da gaske kuma zaka iya fada mata? " Zan iya mana harma in fada mata irin kukan da kika yi kina bani hakuri. Ta saka fuskar ta a cikin cinyarta tana cewa Yaya bana so. Hajiya Talatu suka fito Dan tafiya cike da murna Anty ta ba Ma u dubu goma gashi kwayi na mota. Ma u ta karba tana taba baki. Hajiya Talatu tace akwai dawowa fa Sahiba lokacin da Sabon malamina ya fada min cewa idan har sabon malamin ki ya yi nasarar kwanciya da Amaryar Halifa za a samu sabuwar daula a wannan gidan zan zo lokacin domin aurawa yata Halifa duk da cewa a cikin kudurorin ki shine ki amshe masa komai, to ni kuma a nan ne nawa Malamin zai banbance miki tazarar da ke tsakanin sama da kasa. Anty ta saki baki ta bi Hajiya Talatu da kallo. Har suka bar gidan bata samu bakin magana ba. Lallai wannan babban lamari ne, amma zataji da ita Bari ta gama da wannan. Ta gama shirin ta tsaf ta saka hijabi ta fito falo inda yake zaune, ya kalleta bari dai ku dawo zan yi miki wata ba zata. Asiya ta kalli Halifa "Amma dai ba irin na jiya ba ko?" Yace a a sai dai ko zaki bani tukwici. Ta Harare shi, "Bani da abinda zan baka. " Ke ce kuwa mai abin badawa. Je dai ki dawo bari muje in raka ki gurin Anty. Dan ma ta ki yarda ma wallahi ni zan kai ku, dan Allah ki kula min da kanki sosai kinji? Kuma kar ki kalli kowa wani kishi nake ji za ayi ta Kallon min ke. Dadi ya kama Asiya tace Bazan kalli kowa ba, bare ma in san da wani, ta danyi kasa da murya nifa kasan Allah duk mazan nan a mata nake kallon su, bayan kai ina mazan suke? " Anty dake labe ta cika da mamakin wannan cilligar yarinyar ce ta iya fadawa namiji haka. gara ta hanzarta kar ta bata musu aiki. Ta rafka sallama tare da fadin Asiya ta gama shirin" Asiya da Halifa suka amsa tare, shine ya raka su har titi ya saka su a Kekenapep Tunda ya yi ya yi da Anty ya kaisu ko a kira Bros amma sam ta ki. gidan Baaba za su soma zuwa kafin daga bisani su tafi gidan Baffa. Baba ta yi murna harda kudi ta ba Amarya, daga bisani suka nufi gidan Sabon malami a zuwa shine Baffa. Tafiyar da nisa sosai a wani kauye a gwarzo. Suna sauka suka nufi wani gida shi kadai ne mai kyau kaf kauyen tamkar an kawo shi an dasa. Asiya ta na jin wata fargaba a zuciyar ta kuma kamar wani abu zai faru. Dan haka ta tsananta adduo'in a kasan zuciyata. Wani Falo ne na alfarma suka shiga wani dattijo yana zaune sanye da manya kaya ya rufa kansa da fari da kuma koren hirami. Ya dago idanu ya kalli Asiya idanun shi manya sosai kamar za su fado kasa ga su jajir sai ta ji tsigar jijinta ta tashi. Ya nuna wani farin buzu "Zauna a nan yata." Asiya ta zauna ya yin da Anty ta zauna gefe suka gaisa. Asiya ma tace Baffa barka da rana ya daga mata hannu tare da yi wa Anty alama da yatsa Wai ta fita.... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [6/11, 10:51] Ummi Tandama😇: Asiya ta mike ita ma ganin Anty ta tashi tana cewa bari in shiga mu gaisa. Yace" Zauna ƴata" Asiya ta zauna ta na jin zuciyarta babu daɗi, ga fargaba sai ta dora karanta addu a a zuciyar ta. Ya ta so a hankali yana kanshin wani iri turare mara daɗi kamar zai sata jiri, ya zo ya tsaya a gaban ta. "Bari in yi miki addu'o'i ƴata ki nutsu kuma ki rufe idanunki. Asiya ta cika da mamaki rufe ido kuma kamar addu ar wani addini. Amma sai ta rufe tana addu ar nemantsari. Ya shiga zagaye ta yana wasu zantuka da bata jiyo me yake fadi. Ta ji kamar jiri kamar garin yana juya mata dan haka ta mike zunbur ta yi hanyar fita, cikin zafin nama ya kamo ta, kokowa suka shiga yi Allah ya bata nasara ta yanka mishi cizo Ya sake ta tare da nufar kofa ya rufe ya dakko wata ƴar buta ya watsa mata ruwan ciki. Take ta zube bata kuma sanin ina take ba. Ya kira wayar Anty yace ta shigo, ya kalleta yace yarinyar nan ba budurwa bace, Tace "Har ka yi ne ka tabbatar? " Ya dube ta, ban yi ba, idan nayi ai komai lalace wa zai yi, ta yi yunƙurin ta tonamin asiri ne,, ni kuma na sumar da ita, dan haka ki kwasheta ku bar nan kafin ta farka, har cizo na tayi, gaba daya kin bata min aiki da ace ba su sanar da ni ba na yi amfani da yarinyar bayan wani yariga ya yi amfani da ita, Allah da kin cu ce ni! " Ya kara sa maganar cikin fusata. " Ku bace min da gani bana bukatar in sake ganin ku. Anty ta shiga bashi hakuri tana fadin Malam zan kawo maka wata dan ka cika bukatarka nima burina ya cika. Ka yi binciken Taurarin ƴata ta cikina Hafsa, in har zata yi yanzun nan zan kawo maka ita. Ya koma kan buzun sa yana fadin ki kauda wannan kazamar tana cike da datti... Anty ta shiga tashin hankali da damuwa ga mamaki ya ishe ta wai yarinyar nan ba buduwar bace ke nan sai da ta gama lalacewarta a waje. Ya dakawa Anty tsawa yana cewa maza ta bar mishi gida bayan ya duba Taurarin Hafsa ya ga cewa babu wani amfani da zata yi masa. Da taimakon wani yaron Malamin suka saka Asiya a Kekenapep suka nufi komawa, me Keke dai yana ta mamakin yadda Asiya ta zo da kafar ta amma yanzu sai da aka debota. Son jin tsegumi me Kekenapep ya ce bata da lafiya ne dama naga da kafarta ta zo? Anty a fusace tace "Shafa kaji mana, ku masu keken nan kun fiye shegen tsegumi gashi bakwa ganin zarau sai kun tsinka." Yace Tofa! daga tambaya? Bani na kar zomon ba. Tace " Ka ga in ka gaji sauke mu. " Daga nan. Yace a a mai ya yi zafi? bai sake magana ba. Sunyi nisa kafin Asiya ta farka jikinta kamar anyi mata duka, ta na son tuna me ya faru amma ta kasa sai wani ciwon kai ta ke ji. Ta kalli Anty take ta tuna sun fita tare sunje gidan wata gyatuma, sun tafi wani kauye nan take komai ya dawo mata sabo. A firgice tace wa Anty me Baffa ya yi min? A tsorace Anty tace ba Baffa bane wani Dan uwan sune yanzu zamuje gidan Baffan. Asiya tace Anty kaina ciwo yake min muje gida kawai, tace ai gidan Baffan hanyar gida ne. Asiya bata sake magana ba, amma fa tana tunanin abinda ya wanzu ita da tsohon nan ya kamata ta san waye shi kuma ya samu nasarar yin amfani da ita.? A tsorace ta shiga gidan Baffa nutsuwa da kamalarsa ya sa ta dan rage firgici ya yi mata nasiha suka tafi. A zuciyarta kuwa tana ganin ta fada fushin Allah in har wannan tsohon ya samu damar cin zarafinta. Halifa ya fita kasuwa tun fitar su. ya yi ta kokarin kiranta amma ya kasa samu. Ji yake wata dangantaka ta shiga tsakanin su da Asiya mai karfi. Wata kimarta yake gani a yanayin da ya same ta. Kira da sakon Bilkisu sun fara sosa masa zuciya har ma ya yanke shawarar saka ta a cikin wadan da ya toshe layin su. Ya shigo gidan dauke da leda wadda ya siyo kayan marmari dangin kankana. Ganin ya murda kofar ta budu sai ya Tabbatar cewa sun dawo. Kwance ya sameta kan doguwa kujera tamkar wadda aka zarewa lakka. Ta jiyo fuskarta cike da tsoro ta Kalle shi ga hawaye na zuba, ganin shine sai taji wani kwari ta tashi da sauri ta rungume shi kam, tana kuka. ya matseta a jikin shi yana shafa bayan ta, yana tambayarta menene? ga abin a ranta amma ta kasa fada masa ta kuma rasa dalilin hakan bata san ya zai amshi abin ba. Abinda ta iya fadi kawai shine bazan sake zuwa Unguwa ba. Ya zauna tana jikin shi, ya gyara mata zama a cinyar shi tamkar dai yadda zaka yi wa kara min yaro, cike da sanyi murya gami da lallashi yace "Me ya faru a unguwar." ta girgiza kai, nifa ina jin tsoro. "Na me" Ya kuma tambaya. cikin sauri. Ta girgiza kai alamun babu. Abin mamaki ta hanashi motsi ko ina, hatta salla magriba da isha i duk agida ya yi suka yi tare abinci kuwa kasa ci ta yi dan haka shima bai iya cin na kirki ba. Ya rasa dalilin faruwar duk wadannan abubuwan. Ya tofa addu'o'i a ruwa ya bata ta sha ya shafe mata jiki suka kwanta ta kudundune masa ajiki kamar yaro irin mai kiwar nan anzo cikin mutane. A haka suka kwana da safe, yace su je su gaida Anty Ya kula kamar ta dan tsorata amma baice komai ba. Anty ta na falo zaune Halifa yace Anty lafiya kuwa yau da sassafe a falo jiya na dawo na samu wannan agigice kamar wani Abu ya sameta. Anty wadda ta yi kamar mara lafiya ta kalli Halifa ta kuma kalli Asiya, cikin tsana " Matar ka tana da matsalar aljanu ta tayar min cikin a daidaita kamar matacciya muka dawo. " Sannan ina son zan maka wata tambaya ta dan bamu guri. Asiya ta mike da sauri ta fita daga falon domin zuwa yanzu tana zargin Anty kuma tana son sani waye wanda suka je gurin shi. Kamar ta tafi sai ta dawo bakin kofa ta makale. Anty tace" Halifa yarinyar nan da nace ka kyale ta sai ta warware ashe abinda nake tunani ba haka bane, yarinyar nan ta gama lalacewa tun a waje, abin ya dame ni kwarai. " Halifa yace kamar yaya ban fahimta ba? Tace jiya muna cikin a daidaitasahu sai muka tsaya a danja, wani yaro yana cikin dan sahunsa ya kwala mata kira Asiya gaba daya sai naga tana Kallon shi ta gigice, ta tsorata amma sai ta ki ta kula shi, sai yace ke Asiya ni zaki yarfa dan kinga kinyi aure to kije dakin Bangis ki dauki breziyar ki da fant. Tun daga jin haka shike nan na dauki salati yarinyar nan ta rikice ta gigice ta fita hayyacinta ta tada min aljanu har muka zo gida. Halifa ya yi shiru yana mamaki tabbas ya sameta a rikice to kuma dai duk da bai san ya 'ya mace ta ke ba sai a kanta, irin wahalar da suka sha ita da shi har rauni yaji mata, shima yaji dan rauni irin kuka da neman dauki da ta yi gaskiya wadda ta taba sanin namiji hakan baza ta faru gareta ba. Ya kalleta Anty kinsan mutane da sharri ba mamaki kazafi ne kawai, tace "To ai zaka gane hakan dan kuwa zaka sameta fanko ragowar maza. " Yace Dan Allah Anty a bar wannan maganar duk shirme ce, ya mike ni bari in tafi. Asiya ta wuce da gudu cike da mamakin wannan sharrin da Anty ta ƙaga mata bayan ta kai ta gurin wani tsoho zai yi lalata da ita, ko ma ya yi shine abinda bata sani ba har zuwa yanzu kuma shine abinda ke firgita ta, duk da ta duba jikinta babu wata alama da ke nuna an kusance ta, amma fa tana zargin kanta. *** *** *** Ya zuba mata ido, Anty ta jefa mishi shakku, domin nashi ganin babu wani dalilin da zai sa Anty ta yi mishi karya ko ta shirya labarin da ta bashi, tsorata da firgita da Anty ta yi magana gashi ya gani. Yace Asiya fada min jiya da su wa kuka hadu a dan sahu suka miki magana? Ta girgiza kai, ni bamu hadu da kowa ba babu wanda ya yi min magana mai kama da wannan. Ni da muka tashi kai tsaye gidan wata dattijuwa mukaje har ta bani kudi gasu can a kan gado, sai muka je wani kauye tafiya mai nisa gidan wani tsoho yace in zauna akan buzu in rufe ido ya soma zagayani Ina ta adduo'in. Ta fashe da kuka cikin zakuwa Halifa yace ci gaba ina jinki. Ta bashi labarin abinda ta sani duka. Halifa ya girgiza kuma ya kasa yarda da abinda Asya ta fada, kamar yadda ya kasa yarda da abinda Anty ta fada, sai dai Anty ta fi Asiya hujja tunda ga yadda ya sameta, to da labarin wa zai yarda a cikin su. Iya sanin shi da Anty mutuniyar kirkice ya zata kai amaryar sa ayi lalata da ita, ko dan ta tona mata asiri shine zata kirkiri labarin karya ta ce anyi?. Ya zauna ya tausasa murya Asiya ki fahimta bana zargin ki domin ni a budurwa na same ki, ko kin taba zuwa dakin wani ya yaudare ki amma bai samu nasara ba shine ya ke son ya fallasaki a gaban Anty, shine ke kuma yanzu ki ka kirkiri labarin da kika bani dan ki kare kan ki.? Asiya Ta yi shiru tana kallon shi. Yace haka ne ko? Tace " Hasashe ka yi ko tabbaci ka samu? Dan Allah inyi maka wata tambaya? Yace ina jin ki. Menene alakar labarin da ta bayar da kuma wanda na ba yar ta ina suka yi kama?" Ya danyi shiru sanan yace duka labaran suna magana ne akan ki da kuma yin amfani da ke. Ta ce "Ka wai ka dauki labarin da kake ganin shine na gaskiya a cikin guda biyun ka yarda wanda ka ke ganin shine ba na gaskiya ba. Allah shine mafi sanin gamshashshen labari,ina ganin zaifi kyau mubar zancen a haka. Ya yi shiru cike da damuwa. Dole ya goge shakku ta hanyar bincike... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [6/14, 21:18] Ummi Tandama😇: Gaba daya Asiya ta gama gane cewa Anty har yanzu bata sonta kuma ta shirya mata gadar zare ne domin ta hau ta fada. Sai dai shi Halifa ba zai fahimci haka ba, da alama ma bai san wacece ainihin Antyn ta shi ba. Sannan ba zai gane ta da wuri ba, domin kuwa ya yarda da ita sosai. Dole ta dage da adduo'i akan Allah ya kare ta daga sharri da kuma makircin ta. Bros Adamu ya ɗakko maman Nihal daga Asibiti sunje awo,danja dai dai kofar famfo ta tsaida su kamar ance waiga Hafsi ta hangi motar Bros da wata mace a ciki tana shan mangwaro, kamar Maman Nihal take gani amma bata san ta da kayan jikin ta ba, suna hira suna dariya. Tana tunanin ta fita daga Dan sahun taje dan ta tabbatar da abinda idonta yake zargi sai aka basu hanya. Da ita kadai ce ba wasu fasinjan sai ta bisu. Har tsuma take yi ta isa gida ta bawa Anty labari. Wani abu taji tun daga yatsanta har tsakiyar kanta. Adamu tare da Matar sa wannan wane irin sabon bala'i ne!! Ta mike jiri ya debeta ta koma da sauri yaraf ta fada kan kujera. Hafsi tace "Anty kiyi a hankali fa,ba zai kashe mana ke ba." Anty ta sadda kai tana tunanin ta ina zata fara, da wancan aikin na gurin matar Halifa ya yiwu da ko shakka babu zata samu iko mai karfi wallahi da sai ta lalata rayuwar matar nan,. Ta Mike. Ko shakka banayi Maman Nihal ta shiga malamai ne ta dawo da Yayanku cikin rayuwar ta. Bazan taba kyale wannan ba. Ta soma danna waya ta kira Numbar shi daidai lokacin sun tsaya a gurin wani mai takalman yara tana zabar wa su Nihal da Nur. Ya daga tare da fadin Anty barka da yamma. Adamu!!! Anty ta furta cikin ihu da kara ji. Cike da firgici yace na'am Anty me ya faru? Domin a duk lokacin da yaji ta ambaci sunan sa, ya tabbatar cewa wani babban bala'ine zai faru. Ubanka ne ya faru. Ta furta a fusace, me ya hada ka da Maman su Nihal? Gaban shi ya yanke ya fadi, wanene ya fada mata kenan. "Ina tambayar ka ne fa."!! Ta sake katse shi. Yace Anty mamaki nake yi kuma waye da wannan maganar ni dai ina Kaduna tun sassafe? Tace "Kana nufin ban ma san ka ba kenan, to nice da kaina na ganka ko ni da na haife ka ma bazan gane ka ba?" Zufa ta shiga keto masa ya yin da Maman Nihal ta shiga tashin hankali. Ya daure yace Bazan taba karyata ki ba Anty amma zaki iya bincikawa ki tabbatar idan ina gari, kila wani kika gani da irin mota ta na yi miki gizo, to amma a wajen inane haka? Hafsa dake gefe tana jin su ta ce a kofar famfo a danja. Anty ta ce. "Adanja ta kofar Famfo tunda so kake sai ka titsiye ni.. " Ya jiyo wata muryar tana fada mata Dan haka ya tabbatar ba ita bace ta ganshi ba, yanzu haka munafukar yarinyar nan ce Hafsi. Dan haka ya samu kwarin gwiwar faɗin to ni kuma me zai hada ni da kofar Famfo ko ina garin ma Anty kinsan ba hanyata bace, amma dai ki bincika din dan ki tabbatar ba na ma garin ni. Ya jefa mata shakku dan haka sai ta dan sassauta murya tace ai dai ina son ka sani ko a mafarki na ganka kai da wannan mai kashin tsiyar mai farar kafa tauraruwa mai wutsiya sai na yi maka baki bare kuma ace a fili kaji na fada maka. " Yace To! Da sauri ya kalli Maman Nihal ina wayar ki? Tace tana mota yace su tafi su bar batun takalma ɗin nan, a mota ya yi amfani da wayarta ya kira Halifa yace Dan Allah ko da Anty zata kira ka, ina Kaduna. Halifa yace" Yanzun kuwa ta kirani kana ina na ce mata wallahi ba sani ba, sai dai ina zaton baka gari domin hakan nake tsammani da gaske, amma me ya faru? " Bros ya bashi labarin komai. Halifa yace" Kasan Allah Ramin karya kurarrene kawai ka fito a mutum a yi wacce za ayi. " Bros yace Halifa bawai bazan iya bane muna da banbancin, kai kani ne, ni kuwa ɗa ne dole inyi taka tsantsan in ta jefeni da kalaman la ana sai in lalace. Halifa yace Allah ya kyauta sai ka yi ta addua. Ya kira yaran shagon sa ya fada musu duk wanda ya kira ya tambaye shi ace yana Kaduna. Kiran Hafsi ya shigo wayarsa Maman Nihal ta Mika masa yana daga wa ta katse. Ya yi dariya yace kinsan me yasa na kira da wayar ki, zasu yi ta kira na wai ko zasuji tana busy sai su ce ina fadawa mutane ace bana gari. Har ta kira Uncle Halifa. Maman Nihal ta sauke ajiyar zuciya har lokacin a tsorace ta ke, tace "Baban Nihal kullum zullumina Anty ta san muna tare, shiyasa nace maka da mun hakura. Ya kai hannu ya shafi cikinta. to da ta yaya zakiyi da wannan? Ta lumshe ido tare da fadin"Allah gamu gare ka." *** *** *** Nihal ta kwankwasa kofa Asiya ta bude ta ga yarinya tsaye tace shigo ta zaunar da ita a kusa da ita tana tambayarta sunan ta. Ta ce Nihal kanwata kuma Nur.Asiya Tace ina ne gidan ku? Cike da wayo yarinyar tace nan gidan muke Bros ne fa Dadynmu."Asiya ta danyi shiru tana jin sunan Bros amma batasan shidin waye ba. Dan haka tace ya yi kyau,mamanku ma tana cikin gidan? Nihal Uwar zuba tace a a, Momin mu ai Anty ta koreta shine ta kwace mu ta kawo mu nan gidan." Gaban Asiya ya yi mummunan faduwa Tofa! Yarinyar ta ce, Anty kullum sai muce ta kaimu gurin mamanmu amma ta ki sam sam". Cikin tausayi Asiya ta shafa mata kai, karki damu zaki ga Maman ki kinji. Nihal ta daga kai, alamun eh. Tun bayan zuwan su gidan malamin Anty tace a daina kaiwa Asiya abincin rana da na safe, shima na daren ta ce a kai ne domin ko wani dalili zai samu na zuba mata wani maganin. Halifa ya samu Anty da maganar rashin kai abincin, tace ita gaskiya tunda suka fita aka fadi maganar nan akan Asiya yarinyar ta fice mata a rai, dan haka su yi girkin su na dare kawai za a ba su, kuma shima ya shirya ya koma kasuwa, ranar kwanan Asiya uku a gidan. Shine da ya dawo daki ya samu Nihal a dakin. Har yanzu ya kasa natsuwa da Asiya akan abinda Anty ta fada hakan ya sa yanke ɗan dake mata, sai kawai ta dake ita ma, domin bazata yarda da irin wannan sharrin ba. Nihal ta Kalle shi Tace Uncle Halifa kana da Number Momin mu ka kira min ita? Yace kullum sai kin tambaya bakya gajiya Nihal Number Dady ku gare ni ki bari in ya zo sai ya kira miki ita. " Tace ai shima haka yake cewa bashi da Number Momyn mu." Halifa yace to tashi kije Anty Hafsa ta shirya ki lokacin islamiya ya yi. Bayan fitar su Asiya ta mike ta nufi cikin daki dan tana jiyo kiran sallar la asar. Halifa ya bi bayan ta da kallo wani abu ya tsirga mishi, ya so ya dake amma sai tsigar jikin shi ta kama tashi. Ya mike yana mika ya nufi cikin dakin ta aje dankwalinta a kan gado, dogon gashin ta ya zubo, ta daga ido ta kalle shi ya iso daf da ita ya tsaya. Ya kai hannu ya shafa gashin sai kuma ya janyo ta zuwa jikin shi, ta tuna wuyar da tasha ranar tace dan Allah Yaya Halifa karka sake da zafi bazan iya ba. , cike da shagwaba ta yi maganar. Yace a hankali zan miki ai na yau bazakiji zafi ba,. Tace " To ba kana jin haushi na ba." . Yace Inji wa na isa inji Haushin ki kawai duk shedan ne ya ke so ya shiga tsakaninmu. Zata sake magana ya datse mata baki da nashi sai labarin kuma ya canza. Abinda Anty ta manta su mata da miji sai Allah, alaka ta saduwa a gurin ma aurata tana kara kusanci da shakuwa dan haka ko an shiga dole aji kunya bare sabbin ma aurata. Shi Halifa da alamu yana da karfin shi awa dan haka ko a daren ranar bai barta ba haka kuma da safe, duk ta jure musamman da ta lura da yadda tsakanin jiyan zuwa yau wani tattalin ta ya ke yi, sai ta sha alwashin in zai zo so goma a rana zata amshe shi ba tare da nuna gajiyawarta ba. Halifa ya koma kasuwa zuciyar sa tas ga hasken angwanci duk tunanin shi yana gida, kadan kadan yake kira yaji halin da Asiya take ciki, domin ya baro mata wayar shi, da zai koma gida ya duba a shagon sa ya daukar mata waya IPhone komai ya gani na kwadayi sai ya sai mata. *** *** *** Wajen ƙarfe shida Asiya fesa wanka bayan ta gama girka taliyarta jolop ta ji kifi. Tana bude masa kofa ya shigo ya aje ledojin sai ya rungume ta. Tace muje ka watsa ruwa ka warware Yayana ko mai yana nan fiye da jiya. Haka tayi ta janshi har aka yi Isha I bayan ya ci taliya yana mamakin ashe ta iya girki. Kicin ta koma ta fashe kwai guda biyu ta rumtse ido ta shanye ta zo ta dibi madararr da ya kawo musu mai sanyi ta shiga dakin tana sha. Ya na waya da wani kwastoma ya nuna mata jikinsa ta lafe a cinyar sa zuwa kirjinsa sai maganar sa ta soma canzawa yace zai kira shi da safe yanzu akwai matsalar network. Asiya ta sa masa kofin madarar a baki tana fadin nice Network din ko? Yace ""Ai ke kin fi network karfi Babyna. " Sunan ya mata dadi, ashe itama za a kirata baby kamar dai yadda take karantawa a littattafai. Gaskiya ne labarin littafin yana faruwa akan mutum...... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [6/18, 20:04] Ummi Tandama😇: A tsawon sati biyu ma"auratan sunyi kaffa kaffa da juna, sun shaku da yawa ta yadda Halifa yake ganin ba shakka ya dace da abokiyar rayuwa matsalar guda daya ce akwai wasu girke girke wadanda bata iya ba daga taliya sai wake da shinkafa sai tuwon masara bata boye ba ta sanar da shi, ta bukaci ya sai mata littafin girki yace ai yanzu ko a Soshiyal midiya zaki koyi yadda ake girke girke na zamani ya sa mata data ya bude mata kafofin sadarwa na zamani ya ce duk ta koya. Wata safiyar Juma a taje gaida Anty da safe suna tare da Hafsi, ta gaida Anty wadda ta ke amsawa da kyar kullum cikin lissafin yadda zata bullowa wannan shegiyar yarinyar take, ta dubi Hafsi tace ina kwana? Hafsi tace "Ni bangan shi ba, kwana nan. " Asiya ta kama hanyar fita Hafsi ta ce "Dubi yarinyar nan tafa murmure Anty wai ace ubanka ya mutu amma ka manta ka zo ka yi ta shagalin ka da namiji. Anty ta saki dariya Asiya ta fice da sauri dan bata son jin abinda Anty zata fada. Ta samu Halifa ya fito wanka ta hada masa shayi da wainar kwai da dankali. Yana karyawa suna hira, ya gama ya mike yana mika tare da fadin zan tafi kasuwa gashi bayana na ciwo zo kimin tausa. Suka shiga daki kasuwa dai ranar sai da ya yi azahar ya ci abincin rana. Lamarin da ya sa Anty shige da fice, da dogon nazari, yadda ta san Halifa ina ka fito kasuwa ina zaka kasuwa ko ciwo Halifa ya ke yi sai ya fita kasuwa amma wai ace shine saboda wannan mokadaddiyar yarinyar wai Halifa har azahar yana gida me gareta ne da zata bashi har ya zauce irirn haka. dole taje ta yi masa magana tun goma na safe ta ke aike ana duba mata motar sa har aka yi salla bai fita ba. Ta iso kofar dakin daidai lokacin da Asiya ta rako shi zai tafi tana fadin Dan Allah Yaya idanun ka amana ne karsu kalli kowa sai kwastoma. Yace "Kar ki damu kanwata ai nima yanzu idanun na sun rikide sun zama irin naki, ba sa ganin Kowace mace a matsayin mace face ke,sauran mata yanzu duk Kallon maza nake musu." Yakai karshen maganar tare da kamo hancin ta cike da wasa. Turus suka yi ganin Anty. Ta kalli Halifa cikin fuskar tausayi tare da fadin Jikin ne Halifa?" Yace jiki kuma Anty kamar yaya? Ta kalli gurin motarsa, gani nayi nafita motarka tana nan baka dauka ba har na dawo baka fita ba wanda hakan ba al adarka bace baka wasa da nema." Ya dan sosa kai, Wallahi Anty ga wadda ta cikani da hira nan. Ya nuna Asiya cike da wasa. Asiya tace au Yaya haka ma zakace, cike da shagwaba ta kalli Anty tana fadin Wallahi Anty ba ruwa na nikam shine nan yaki tafiya.... Ke dalla yi ma mutane shiru inda zama yake a gidan ya samu abinda zai kawo ki gidan? Halifa ya kalli Asiya da sauri saboda hantarar da Anty ta yi mata. Ji ya yi har cikin zuciyar sa baiji dadi ba. Asiya ta sunkuyar da kai ta ki dagowa Halifa ya tausasa murya yace Baby ki koma ciki kinji za mu yi waya. Ta dago kai ta dube shi cike da fuskar tausayi ta daga masa hannu tana masa bye bye ta Juya ciki da dan gudu. Ya bita da kallo ta kullo kofar. Ya kalli Anty yace Wannan fa bai dace ba Anty, dan Allah ki kama girman ki banji dadin abinda ki ka mata ba. Anty tace "Ba shakka lallai Halifa ni kake jawa gargadi akan matar ka, har zamu fara da haka? To ina mai baka shawara ka kama kanka kaima. Ya wuce rai bace baice komai ba. Tunda ya fita a motar ya kira Asiya ta daga tare da fadin" Baby ki yi hakuri kinji ni?" Asiya cike da shagwaba tace haba yayana ai ni ba haushi naji ba, Anty ai Anty mu ce, tana da dama ta yi mana fada in munyi ba daidai ba taya zanji haushi kai ne kace wai in koma ban raka ka mota ba, kuma baka min wannan sumbatar da kake min ba kuma bakace in kula da kaina ba kamar yadda ka ke yi. Ya yi yar dariya "Shike nan ayi hakuri zan biya bashi gobe Allah ya yi miki albarka."Ameen na gode mijina Allah ya tsare gaban ka da bayan ka, ya kai ka lafiya ya kawo rabo mai amfani." Ameen masoyiyata ina kaunarki. Tace me zan dafa maka anjima? Komai me dadi, in babu wani abu na girki da ki ke bukata kimin waya zan aiko. Asiya ta ce to. Bayan sun yi sallama Asiya ta yi shiru tana tunani ba shakka zata sha wahala da Anty amma ta san yadda zata bi da lamarin insha Allah. Anty ta kara tunzura sosai karfa yarinyar nan tace zata shigar mata hanci da kudundune. Ta koma tana fadawa Hafsi abinda ya faru. Hafsi tace " Anty gara ki dauki matakin ɗan hakin daka raina shine yake tsole maka ido. Anty ta yi kwafa, tace ina takaicin sakacin da nayi ne har ta samu dama ta shigo cikin gidan nan. Hafsi Tace" Anty ai baki makara ba,,ki ka kori mai 'ya' ya ma bare wannan tsuntsuwar karamar alhaki. " Anty tace To Hafsi in kin haifu cikina ko ke din nan zaki fidda ta gidan nan. Hafsi ta sa dariya tana fadin " Sai dai in baki bani Umarni ba ta jima ta yi sati daya in na dinga tashin balli a gidan nan... " Anty ta sa dariya ke abinda ba kamar yadda ki ke tsammani bane. Halifa zai iya raga min amma ke ubanki zai ci ba ruwa na. Hafsi ta saka dariya tace "Anty in har dai kin bani dama to ki zuba min ido ki bani sati daya, kowa dai da irin baiwar sa da kuma tasa Basirar ke tsohon lissafi ki ke yi, ni kuwa yar zamani ce. Anty cike da mamaki tace ba shakka dama ance magaji mafiyi. To na baki dama sai dai ina son ki rinƙa sanar dani duk abinda zaki yi. "Ba matsala." Hafsi ta fada cike da yakini. Asiya ta gama aiki tana zaune tana tunanin yadda zata bullowa Halifa ya yarda ya kai ta gida, tun jiya take latsa shi amma yaki zancan. Ko abinci take ci sai ta tuna Umman su da Sadiya da yaranta da kuma Abba, ta yanke shawara in har yaki kaita zata sa ya kira mata Yaya Sulaiman ya je ya kai ma su Inna waya mu gaisa. Sallamar Hafsi ta katse mata tunani ta amsa kamar abin kirki ta shiga ta zauna Asiya tace za a kawo miki abinci? Hafsi ta ce tab "Gaskiya ni ba kowane kwado nake ci ba, da ƙazanta shi kanshi Uncle na yi mamaki yadda yake da kyankyami amma har kike yin jagwalgwalo yake iya sawa a cikinsa mai daraja!. Asiya ta yi murmushi tare da fadin Kina da gaskiya sai dai kuma shi Uncle din naki kullum cikin yabon wannan jagwalgwalo da ƙazantar ya ke, ga shi yana santi, ta kai hannu ta dakko wayar tare da fadin kiga, kalli tukwaicin da ya bani. Hafsi ta kalli IPhone 13, ta zaro ido wayar da take ta naci Anty ta sa Halifa ya bata shine ya ba wannan wadda bata san darajar wayar ba. Asiya ta ce ya kikaji a ranki? Kin taya ni murna? Hafsi ta mike tsaye ta nuna Asiya da yatsa, tana fadin "Yana da kyau ki shiga hankalin ki, domin ni ba sa ar ki bace, kuma duk bala'inki wallahi sai ki fita a gidan nan banza yar matsiyata" . Asiya ta yi yar dariya tace to zamu gani, gaskiya domin mutuwa ce kadai zata iya rabani da mijina, ina miki addu a Allah ya baki mijin irin nawa. Ta kaici ya kama Hafsi ta rasa me zata ce ta zuba ma Asiya ido tana huci . Asiya tace to ya kika ji a ranki, ba dadi ko? To ki kiyaye da cin zarafin mutane. Hafsi tace zaki yi da kinsani ta fice tana huci. Halifa ya yarda zasuje gidan su Asiya tare sannan da dare murna gurin Asiya zata ga Inna. Sun fito suka shiga dan yiwa Anty Sallama ya ga Hafsi tana ta cika tana batsewa, cike da raha ya ce Dota lafiya kuwa? Ta turo baki tace lafiya lau Uncle dama so nake ka dawo in kawo maka karar matar ka. Anty Asiya. Anty tace Kash Amma dai tun da kuka yi abinnan dazu nace kiyi hakuri ko? Shi aure ai lokaci ne da shi. " Cike da mamaki Halifa yace me ya faru? Anty tace waya sanar musu ni ko sauraron ta banyi ba, banda abinta ma da me zai sa tace wai zata je ta koya mata girki? Hafsi tace Uncle Dan Allah laifi ne idan naje sasanka na taya matar ka aiki? Ya girgiza kai alamun a a. Taci gaba shine ina zuwa wai ta ce wai in tafi bata so kuma in je inyi aure nima wai na tsaya yawo banza banda ko saurayi Wai me bakin jini. Halifa ya kalli Asiya wadda mamaki ya hana ta yin magana sai Kallon Hafsi ta ke ta yi cikin daga murya yace menene gaskiyar lamarin?? *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [6/24, 08:20] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w/9223372036854675807 *🔉 NASIHOHIN MALAMAN SUNNAH🔉* Manzon Allah (saw) yace duk wanda wani bala'i ko damuwa na daga al'amuran duniya ke damunsa, idan ya yi ɗaya daga cikin waɗannan addu'o'in Allah zai yaye masa damuwarsa:- 1️⃣ LA'ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZA'LIMIN. 2️⃣LA'ILAH ILLALAHU AZEEMUL HALIM,LA'ILAHA ILLAHU RABUL ARSHIL AZEEM, LA'ILAHA ILLAHU RABBUS SAMAWATI WARABUL ARDI WARABUL ARSHIL KAREEM. Asiya tace a ranta wai haka abin ya zama kenan, dan haka sai ta yanke shawarar zuwa musu ta yadda basa zato. "Ina sauraron ki, Asiya cike da kwanciyar hankali tace duk yau yaya banga Hafsi ba sai yanzu. Gaskiya ba dani bane. Halifa ya kalli Hafsi" Kinji me take fada? Hafsi tace ki fadi tsakanin ki da Allah." Da karfin gwiwa Asiya tace ke zance ki fadi tsakanin ki da ALLAH. Hafsi tace " "Humm kamar nasan zata musa na yi recording a wayata ta. Ta dakko wayar wadda ta zauna ta gama editing ta cire maganganun ta. Gaban Asiya ya fadi da ta ji yadda aka jera maganganun tiryan tiryan, ita kanta banda ta san yadda suka yi ita da kanta da sai tace tabbas haka ne. Halifa ya cika da mamaki ya kalli Asiya a fuskar shi ta ga Bacin rai karara. "Me kuma zaki fada yanzu? Asiya ta ce bani dashi domin ko na fada bazaka yarda ba tun da na riga nayi karya tun a farko nace ba ayi ba. Gaskiya dai tazo kuma duk maganganun na da ta dauka amsar magaganunta ne, da ta fada min inda za a sake kunnawa tsaf zan fidda yadda zantukan suka faru a tsakanin mu. Anty ta amshe, da fadin ni dai abar maganar kawai ke Asiya ki daina gorin aure ga budurwa komai lokaci ne. Ke kuma kiyi hakuri. Ta kallo Halifa wanda har lokacin bai ce komai ba ka rinƙa yi mata faɗa duk da cewa harda kuruciya. Halifa ya Ja tsaki yace wace kuruciya a nan. Ya juya. Asiya ta kalli Hafsi sannan ta kalli Anty tace Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Ta wuce tabarsu suna dariya, basu san wannan addu ar da ta yi ta ce Allah ya isar mata komai babbar magana ba ce. Kamar yadda ta zata Halifa ya bude daki ya shiga, ranta ya sosu, kenan sun fasa fitar, ta daure ta cije domin dai fushin fari ba nata bane. Ya yi matukar bata rai yana zaune akan kujera. Ta kwantar da hankalin ta kafin ta ce Yaya munfasa zuwa duba su Innar tamu ne? Tun kafin ta rufe baki ya ce, na fasa. Asiya. tace saboda me? Ya dube ta cikin daga murya "Kina ganin cewa abinda ki ka yi ba laifi bane ke nan? Asiya kin bani mamaki kin iya karya har haka? Ina son ki sani duk duniya na tsani karya, duk lokacin da mutum ya zama makaryaci a idona darajar shi zubewa ta ke yi, yanzu fa ba wata magana da zaki fada min inji cewa gaskiya ne ko da kuwa gaskiya ce sai na tsaya kokwanto. Sai yanzu Asiya ta gano illar da suka yi mata. Ta kwantar da muryar ka yi hakuri, na yarda cewa na yi karya, kuma karyar cewa duk yau banga Hafsi ba iya itace laifina na zabi in faɗi haka saboda kawo karshen rigimar da tazo har daki ta takale ni da ita. Yace Malama yi min shiru, me ya hana ki fada tun a lokacin gaban kowa, ina son ki sani a duk yadda Duniya ta rikice miki ko rayuwa ta riske ki kar ki taba daukar karya wai ta zame miki mafita. Kirike wannan domin bazan sake maimaita shi ba. Asiya ta lumshe ido hawaye suka kwaranyo cike da nutsuwa tace na rike kuma insha Allaahu bazan sake yi maka karya ba, ta silalo kasa ta zube gwaiwa biyu a gaban sa cikin sanyi murya tace natuba. Halifa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yi mata alama da hannu wai ta tashi. Ta mike ta nufi cikin dakinta tana kuka yanzu kam ta tabbatar yaki dan zamba ne kuma dole ta kara sanin da suwa take zaune. Anty ta saka dariya bayan Nur tace Anty naji Uncle yana ta yi wa Amarya fada tana kuka shine ban shiga ba na dawo dama kince in naji yana fada in dawo. Anty tace jeki kuyi kallon ku kin gama aikin ki. Dama ta tura tane wai ta amso mata chajar waya amma in taji Uncle Halifa yana fada to ta dawo. Sako ya fado wayarta ta dauka ta duba Hajiya Talatu ce. A fili tace lalatacciya har na manta da rayuwar ki, sakon uban me kika turo min in bashi ki ke nema dai bani da shi. "" Ki duba whatsapp din ki. " Abinda aka rubuta Kenan, bata iya magana ba sai dai ta wuce kai tsaye zuwa whatsapp din nata. Odiyo ne Ta kunna wayar su da Malam ne tiryan tiryan kafin Anty ta gama saurara zufa ta rufe ta, sannan ta tsine wa Hajiya Talatu babu Adadi. Ta danna kiran Hajiya Talatu cike da karfin hali tace, Talatu manya, to wannan Odiyo din da kika turo min me zai amfane ni da shi? Talatu ta yi yar Dariya. "Kawata ta kaina, ke kuwa zai amfana da zarar angoge shi, amma in aka tura musamman ga Halifa ko da bana nan nasan kin aiwatar da abinda kika yi kuduri, daga nan sai asirin ya tonu." Anty ta zaro ido amma sai ta cije tace. Ba shakka na cika kuduri na, amma ki sani shi kanshi Halifa ko yaji wannan babu abinda zai iya, domin na samu damar juya shi a yanzu haka. Hajiya Talatu ta danyi shiru cikin sanyin jiki, jin haka sai Anty ta san cewa karyarta ta samu shiga dan haka cike da kwarin gwiwa ta ce. Amma zaki iya tura masa din ki gwada ki gani. Talatu kin bani mamaki shiyasa naki kai ki gidan malamin tunda na fahimci da sharri kika zo min gida. Kuma duk abinda kike ciki wannan malamin yana sanar dani hatta wannan kuduri naki, da wannan Wayar da zamu yi duk ya fada min. Kuma ni da na so zan saka ya cutar da ku ke da Ma'u din amma nace masa zan sake baki lokaci ko zaki nemi yafiya ta. Talatu ta tsorata matuka Tace "Sahiba to duk ba wani abu bane, kawai dai ina son Halifa ya auri Ma'u ne, duk kan haka ne na miki rakodin kuma da zan tura mishi ai da tuni na tura. Anty ta yi dariyar samun nasara, tace Talatu baki gama sanina ba har yanzu, ni yanzu jini nake ba aljanu suna kawo min bayanai yanzu haka sunce min maganar da muke yi dake kin sake kunna rakodin to ina gargaɗin ki, zanyi hadaya dake matsawar baki goge duk wadannan Odiyo din ba, zan basu jinin ki ba ruwana. Hajiya Talatu jiki ya soma rawa domin ta danna din dan samun wasu bayanan. Ta kashe wayar Tana mamakin Anty gaskiya ta zama abin tsoro dole ne ta goge su. " Anty kuwa ta shiga tintsira dariya tana cewa Kai gaskiya barazana ta yi, da na tsaya rokonta da yanzu tana nan zata hada min jangwal. Da Hafsi ta dawo take bata labarin abinda ya faru suna ta dariya. Kiran Hajiya Talatu ya shigo. Hafsi tace Anty kar ki daga sai a kira na uku dan tasan abinda gaske ne, kuma in tace ta goge sai kice Aljanun sunce saura daya ne bata goge ba, kinga in ta makale wani zata kara gaskata hakan kuma zata goge, in kuma ta yi ta rantsuwa akan ta goge sai kice mata dayan shine wanda ta turo miki ta goge shi da kanta. Anty tace kai gaskiya kin haifu Hafsi ina ma ace haka yayanku yake, da yaushe zan sha wahala. Haka kuwa suka yi wa Hajiya Talatu kuma ba shakka lissafin ya tafi yadda Hafsi ta tsara. Cikin bacci Asiya taji Halifa yana lalubarta, duk da cewa harta kwanta yana fushi da ita hakan bai hana ta bashi hakkinsa ba, ya kunna wuta ya kalli fuskarta, ya kai hannu ya shafi busassun hawayenta kina yawan kuka sai dai nafi son irin wanda kike yi din nan idan mun kasance tare. Ina jin dadin da farin ciki. Asiya ta rufe fuska ita fa batasan tana wani kuka da yake yawan fada mata ba. Zuwa da safe kamar babu wani abu da ya faru na fitina tsakanin su. Ya dai kara yi mara nasiha akan karya, yace "Bana son karya sam sam kuma bana zama inuwa daya da me yinta. Asiya tace zan kiyaye nima ba ɗabi ata bace. Tace to ya kira Yaya Sulaiman ya kai waya gidan su, sai yace ta bari da dare zasuje. Anty ta cika da mamakin ganin Halifa sun sake zuwa sallama kamar dai jiya. Dole ta wage baki tana yake tare da fadin ki gaida Innar taku, sannan Halifa kar aje hannu rabbana. Yace "ai dama." Sahat suka fara zuwa kayan abinci ya saiwa su inna sannan suka wuce. Murna Asiya ba a magana Inna ta kara yi mata nasiha da shawarwari, sannan suka tafi. Kwana biyu tsakani Asiya ta shiga gaida Anty sai tace mata anjima masu allurar riga kafi za su zo, za a yi ta annobar sankarau saboda zuwan zafi. Asiya ta tsorata dan ita bata son allura sam. Tace Ni kam ba sai anyi min ba. Anty tace ai kuwa yi ya zama dole domin bazan bari ki kamu da cuta ki yada mana ba. Da rana da ya dawo take fadawa Halifa ita bata son allura. Yace Anty ta faɗa min tun jiya wai za ayi riga kafi ki hakura a yi miki don bana son magana yanzu Sai wannan karamin abun ya zama issue. " Asiya tace shike nan. Tana bacci aka tashe ta ake faɗa mata ga me allura. Tayi mamakin ganin an tsaga mata hannu an saka wani abu an like. Ta sha kuka sosai domin azaba da kuma rasa ko me aka sa mata. Halifa ya yi mamakin ganin yadda gurin allura ya yi tsagu, da ya yi wa Anty magana wai ita ce Taki tsayawa shine ya sa har aka karce ta. Bayan kwana biyu sai jini ya balle wa Asiya wanda bata san kanshi ba. Ta zaci lokacin al adarta ne ya canza. Tun abin baya damunta har ta shiga tsoro. Halifa kuma ya shiga takura, saboda jini yafi sati kuma sai ya dawo kwana biyu uku da daukewa sai ya kuma dawowa. Halifa ya samu Anty ya fada mata. Tace Aljanu ke yin haka, an fada maka yarinyar nan Aljanu ne suka aureta amma ka ki yarda.gashi sun nuna kansu gidan magani kawai za a kai ta. Hankalin Halifa ya tashi sosai, kuma ya amince da suje gidan magani. Asiya tace masa bata da komai ita babu gidan maganin da zataje. Hakan ya kawo musu matsala wadda ta sa Halifan Kauracewa gadon su. A kasuwa yake fadawa wani abokinsa abinda ke faruwa da matarsa, yace gaskiya ana samun haka shima wata kanwar su budurwa haka aljanu suke sakar mata jini. Halifa ya sake yarda dan haka yace lallai Asiya ta shirya Anty ta kai ta gidan magani. Farin ciki ya cika Anty domin malamin nan ne ya bukaci ta kawo masa Asiya zai yi mata wani wanka wanda zai wanke abinda ya sa aljanun ba su yarda sun karbeta a waccan ranar ba, wato da suka ce ba budurwa bace. Sun bincika sosai ba su samu mai irin tauraro ta ba.... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [6/28, 21:44] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w/9223372036854675807 Tace masa sha biyu za su fita dan haka ya basu kudin kekenapep ya bawa Anty kudi yace su dauki shatar abin hawa kuma duk yadda ake ciki su kira shi. Ƙala Asiya bata ce ba lokacin da zai fita ya kalleta yace "Kiyi hakuri baby gaskiya dole ayi maganin wannan ciwo yana shiga hakkina da yawa yanzu yau kwana nawa rabon mu da ke? Ta kalle shi, me yasa baka yi tunanin mu fara zuwa Asibiti likita ya tabbatar ciwon ba? Na yi mamaki yadda ka ke ahalissuna kuma ka yarda a kaini gurin yan tsibbu masu amfani da aljanu. Yaya Halifa bani da kowa a kaina ban taba ko mummunan mafarki ba, to yawanci masu bada maganin nan wallahi ance suna lalata da yaya da kuma matan mutane yanzu kai ka yarda a kaini wani ba kai ba ya kwanta da ni? Ta kai karshen maganar tana kuka. Halifa ya ji wani abu ya soki zuciyar shi yace amma ai Anty ba irin gurin zata kai ki ba, Anty bata hulda da masu zuwa irin wannan gurin. Asiya ta yi shiru tana tunanin dole fa ta sa Halifa ya janye zuwanta gurin wannan maganin. Babbar matsalar shine Halifa bai san wacece Anty ba. Ta sau ke ajiyar zuciya cike da kwanciyar zuciya tace. Zanfi yarda muje tare da kai a yi komai a gaban ka kokuma yanzu muje Asibiti muga likita ya tabbatar mana da matsalar bata su bace,, domin nifa tundaga wannan ranar da aka min allurar riga kafi komai nawa ya canza ina zargin likitan bai yi abinda Anty ta saka shi ba. Halifa yace "Kin tabbatar tun daga ranar ne kika fara samun canji? " Asiya tace gaskiya haka ne. Halifa yace me ya sa baki fada min ba? Bari in yi magana da Anty. " Asiya tace Yaya kar ka fadawa Anty domin zata ga kamar munki shawarar ta ko taji babu dadi akan ita ta kawo me allurar aka samu matsala. Inda zaka yarda kawai mu tafi in mun dawo sai mu fada mata, in kuma likitan yace ba na Asibiti bane shike nan sai mu yi shiru. To muje ya fada ya na daukar wayar shi akan kujera. Hijab Asiya ta saka suka fice. Likita ya kalli Asiya "Baki yi makaranta bane?" Asiya tace nayi makaranta amma bangama ba. Ya kalli Halifa wannan gurin ba allurar riga kafi bane, tsinke aka sa mata na tsarin iyali wato tazarar haihuwa,, tana me bata sani ba? Halifa yace likita wallahi ta fada min cewa kamar an saka mata wani abu amma sai aka ce min taki tsayawa ne ayi mata allurar kuma dama tun farko ta nuna cewa tana jin tsoron allurar dan haka sai kawai na yarda da abinda Antyna ta fada. Likita yace gaskiya babu wani kuskure wannan abin ana sane aka yi shi dan karta haihu. mamaki ya cika Halifa yana kokwanto cewa anya Anty tana sani zata yi haka. Likita ya kira nurse ta cire mata abin Halifa ya kalla yace tabbas wannan babu kuskure daga cewa yi allura sai kawai mutum ya saka wannan. Ya dai yi godiya tare da tambayar jini ko zai daidaita. Likita yace zai daidaita insha Allah. Asiya ta lura da yanayin da Halifa ya shiga na tashin hankali yana ta maimaita me ke nan Anty ta yi? Ta sanyaya muryar tace, kar ka zargi Anty fa babu mamaki laifin shi mai allurar ne. Halifa ya sauke ajiyar zuciya yace ina fatan ya zama haka, dan zaifi yi min sauki a bisa a ce wai Anty da nake mata kallon mahaifiyata nake mata kauna irin ta ɗa da mahaifiya, ace tana da hannu a yunkurin hana ni samun ɗa. Ga mamakin Asiya sai taga hawaye sun kwaranyo daga idanunsa. A firgice Asiya tace ka samu guri ka dan tsaya dan Allah. Kamar mai kar ɓar umarnin ta sai ya tsaya cak. Sannan ya yi gefe. Asiya ta matsa ta rungume shi, kamar hakan yake bukata sai shima ya rungume ta tsam sai kuma ya saki kuka. Asiya bata hana Shiba har kusan minti daya sannan ta fara fadin "Ya isa haka Yaya, ka yi hakuri dan Allah insha Allah ba ruwan Anty, ni da zaka yarda ma da sai mu yi shiru mubar maganar kawai kace mata gurin wani maganin mukaje shike nan. muryar Halifa a dashe yace" Kinsan matsalata daya da zarar na zargi abu in har na cika bibiya sai ya zama gaskiya. Asiya tace ka yi hakuri insha Allah ba haka bane. Sun iso gida suka samu Anty tana ta faɗa. Halifa ya kalleta cike da zargi lokacin da take cewa "Sakar cin banza kawai banda shashanci sai ku fice bayan kun san zamu fita, ba sai ku bari sai mun dawo ba. Halifa ya yi karfin halin cewa mun samu magani a Asibiti yanzu da muka je. A firgice Anty ta ce," Asibiti kuma bafa ciwo Asibiti bane". Halifa yace tsinken da kika sa a saka mata ne aka cire. Ta dau salati wane tsinke kuma ni Habi. Halifa yace Na allurar riga kafi mana wanda aka ce min karcewa ta yi. Anty ta dauki salati ta sallame. Ta dakko waya tana fadin sai na sa an daure dakta din nan, tsarin iyali kuma yaya ya yi haka ne. Ta kira ya daga ta saka a free. Tace kai "Dakta dama haka Na fada maka daga allurar riga kafi kuma sai ka saka mata tsarin iyali? Yace Hajiya dan Allah kiyi hakuri, ranar gida biyu zani da nan gurin ku da wani gidan wancan gidan suma ni ke duba su. Mijinta ya kira ni ya fada min inje in saka mata wannan tsinke to kuma nima ina fama da matsalar mura a ranar sai na saka mata sai da naje wancan gidan sannan na gane abinda na yi. Halifa ya fisge wayar tare da fadin To amma kai jahilin ina ne da zaka sawa matar wani abin tsarin iyali, ina son ka sani daga yau ka daina domin sai na shigar da korafin ka a hukumar lafiya ya kamata su bincika lasisinka. Sai an dakatar da kai. Anfy ta karba tace dole kuwa mu kai kararsa. Bani wayar in kira masa yan Sanda. Halifa yace "Anty ai wannan ba karamar matsala bace ni zai tsarawa yayan da zan haifa, ni da ubana yake da yaya sama da talatin kuma sai na gaje shi. Bazan taba kyale shi ba ko waye ma ya turo shi sai ya fada, domin yadda nake ji zan iya kashe mutum ko waye shi. Ya nufi dakin sa a fusace. Asiya Ta kalli Anty sai tsuma take tana zufa tana fadin ina bayan ka wallahi karka yarda zan kaika har gidansa. Asiya ta girgiza kai tare da fadin Allah ya kyauta. A ban daki ta samu Halifa ya sakarwa jikin shi shawa ko single da gajeran wando bai cire ba. Ta aje hijabin taje ta shige jikinsa ita ma da kayan jikinta. Kam ya rungume ta ruwan yana ratsa su, tsawon minti hudu sannan ta ce muje ka kwanta. Baya shige umarnin ta suka kwanta tana shafa masa baya har bacci ya dauke shi. Asiya ta zame a hankali taje kicin tana girki. Anty ta aiko wai taje. Ta samu Anty a falo. Tace "Kije ki shirya mu tafi gurin magani ba biye tashi za ayi ba, lafiyar ki ce. da kin lalace wata zai auri" Asiya tace Anty kiyi hakuri kawai in ya huce sai ki tambaye shi, yana cike da tashin hankali. Anty ta mike tana magana cikin lallashi, ki daure muje banda shirmen ki harna mallaka ba sai ki samo ba namiji fa ba dan goyo bane dan yana nawa bazan ƙi ki ba. Asiya ta juya tare da fadin Na tuna na saka mai a wuta Anty, zan dawo. Hankalin Anty ya gama tashi, ko da wasa ta san Halifa bazai taba yarda ya bar Asiya Zuwa gurin Malam ba. Ta kira Malam din ta sanar da shi halin da ake ciki. Yace Wannan kuma ke ta shafa ba ni ba. Anty sai kai da kawo take a falo. akwai bukatar ta samu mafita cikin gaggawa. Halifa ya dawo sallar azahar ya ci abinci sannan ya ce zai tafi kasuwa. Asiya tace Anty tace min ko zamu je gidan magani ɗin, ni kuma dai nace insha Allah ai ciwon ya warke ko? Yace babu inda zaki je zan ma fada mata dan ta sani. Asiya ta rakashi ya tafi. Anty ta na ganin fitarsa ta kira Malam tace "Dan Allah Malam ka zo ka yi mata wankan a gidan nan mijin ya fita baya nan sai dare zai dawo. Malam wanda ke cike da tashin hankali tun bayan da ya ji cewa a hakan ma yarinyar bazata samu ba. Sai da ya bi matakai ya bi sharudda ya yi hadaya sannan aljanun suka kawo wannan hanyar. Ko me zai faru kam dole ne yaje gidan. Yace kin tabbatar ba wata matsala? Anty tace ba matsa ka taho kawai. Ta kira Hafsi ta ce tattara kan ƙanannan naki da su Nihal da Nur ki kai su shoprite su hau lilo kar ku dawo sai gaf da magariba. Hafsi ta soma murna amma dai Anty da abinda ki ke kullawa, ko wata kyauta kika samu? Ta yi murmushi kawai yau naga ya dace su shakata. Nima zanyi baki ne za su yi wani aiki a gidan. Suna tafiya ta sake kiran Malam a waya taji ko ya kusa. Yace "A kwatancen da kika bani direban yace muna gab. Ta fito ta nufi sasansu Asiya. Tana zaune tana Kallon TV Anty ta kwankwasa kofa tare da fadin Asiya. Gaban Asiya ya yi wata mummunan faduwa bata san daliliba sai ta kama fadin La ilaha'illallahul Azimul Halim! La'ilaha'illallahu rabbul arshil Azim!! La'ilahaillallahu Rabbussamawati wa Rabbul Ardi Wa Rabbul Arshil Azim!! Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [7/3, 08:23] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w/9223372036854675807 Asiya ta bude Aunty ta danna kai cikin falon. Tace "Asiya Dan uwan Babanmu zai zo yanzu zan rako shi ku gaisa,ya jima bai zoba a Saudiya ya ke da zama. Asiya tace to amma da yaya ya sani ai da ya jira shi, ko kiransa za ayi? " Ba sai an kira shi ba... Anty ta katse ta," Ki barshi kawai, ya tafi kasuwarsa shi Halifa ai suna waya. Asiya tace to Allah ya kawo shi lafiya. Sam bata kawo komai a zuciyarta ba. Anty Na tafiya ta ji karan mota dan haka ta daga labulen windo dan taga ko waye. Bros ne ya shigo a motarsa Abban su Nur ta koma ta ci gaba da sabgoginta. Ba jimawa sai taji kwankwasa kofa tana budewa sai taga Sadiya su maman Annur harda su Annur din ta zo. Ihun murna tayi ta dane ta. Sadiya cikin dariya tace kai Asiya Allah ya shirye ki. Suna zama ta zubo musu abinci ta hado musu shayi mai kauri, tace su sha inma basu koshi ba zata sake dafa musu wani abin. Ta kira Halifa cike da murna ta sanar dashi. Yace ta gaishe su kafin ya zo. Sadiya tace kafin ya dawo mun gudu, ina jin nauyinsa. Asiya tace "La shi ai Yaya bashi da damuwa sam dan Allah ku jira shi. Anty ta gimtse fuska lokacin da suka hada ido da Bros," Uban me ya zo yi yanzu. " Ta furta a zuciyar ta. Ya zauna yana gaishe ta. Ta amsa babu walwala ya soma bata uzrinshi ga zaton sa dan bai zo kiran da tace tana yi masa ba a jiya. "Anty Dan Allah ki min afuwa jiya baƙin mu ne na nijar nan suka kwana har goma na dare muna tare yanzu ma ba mu dade da rabuwa da su ba na yo nan. Cike da kagara Anty tace kaje yau Nima inada uzuri gobe ma yi maganar. Ga zaton shi haushi ta ji dan haka sai ya shiga ba ta hakuri. Ta kalle shi baka gane yaren Hausa ne ko? To baƙi zanyi yanzun.... Ta katse maganar daidai lokacin da kiran ya shigo wayarta. Ta daga tana sake yi wa su Malam kwatance. Ta dube shi "Ka iya tafiya domin zanyi baki. Ya mike yana fadin ina su Nur ne? Tace Sun tafi can gurin lilo na wasan yara. Mamaki ya cika Adamu yau Anty ce zata ce a kai su Nihal shakatawa. Ya dake tare da fadin To Allah ya dawo da su lafiya. Ni to bari in tafi. Cikin sauri tace "Kaje gobe ka dawo. Yana fita harabar gidan motar su Malam tana tsayawa. Ya tsaya yana Kallon su Malam ya fito rike da wani abu kamar carbi amma ba irin diyan carbi bane, ya sha wata alkyabba kamar basarake. Bros ya cika da mamakin ina Anty ta samo wadannan kuma. Bros ya mika masa hannu Malam ya dafa hannun sa a kirjin sa yana fadin "Lafiya lau. Hajiyar tana ciki? " Kafin Bros ya yi magana tuni Hajiya ta bayyana tana yi wa Malam sannu da zuwa. Dan haka Bros ya yi gefen matar Uncle dan su gaisa. Anty tace bata nan dama tafiyar ka kayi. Adamu ya zargi wani Abu tunda ya ga yadda Hajiya take gaida wannan mutum kamar wani abin bauta sai sunkuyawa take yi yaji yana zargin cewa kodai bokane dan ya yi kama da su. Ya juya zai fi ce sai ga Sadiya da Asiya da kuma yaran za su gaida Anty. Bros ya tsaya suka gaisa sannan ya tafi. Ran Anty ya baci da ganin Sadiya dole ta kai Malam falon ta ya jira ta san yadda za ta yi ta kori bakin. Asiya bata ga fuskar Malam ba amma dai tabbas shine wannan mutumin da Anty ta kaita gurin shi, dan haka ta gigice. A Ciki ta amsa gaisuwar Sadiya sannan tace wa Asiya ba nace bako zai zo dan ke ya gan ki matar Halifa ya yi murna shine kuma zaki gayyato wa mutane tarkace. "Asiya tace Anty yayata ce fa, Uwar mu daya Uban mu daya ai kuwa ta wuce ace tarkace. Tace to ki min rashin Kuya ina son ki sallame su yanzun nan. Asiya ta bata fuska tace Anty Yaya Halifa yace su jira shi sai dare in ya dawo. Anty tace ok kice kwadayi da maula suka zo. Sadiya ta kalli Anty cike da mamaki tace Allah ya baki hakuri bari mu tafi yanzu. Dama haka Antyn ke so shiyasa ta yi haka a gaban Sadiyar dan ta yi zuciya ta tafi. Tace dadai ya fi miki ta wuce. Asiya tana ta kuka tana dan Allah kada ki tafi wannan mutumin boka ne zasu cutar da ni.Ta kwashe labarin baya ta fadawa Sadiya tace amma dan girman Allah kar ta fadawa Inna zata shiga tashin hankali. Sadiya tace kira Halifa ki fada masa cewa Anty tace mu tafi saboda zuwan wani bako da zai gana da ke. Asiya tace bana son yin abinda zai kawo sabani tsakanin su ina dai rokon Allah ya sa Halifa ya fahimci wacece Anty. Halifa ya yarda da yar uwarshi, zai shiga tashin hankali sosai in har ya kasance ya fahimci tana cutar da shi. Kawai ki tsaya a nan din in har kina nan wallahi baza su min komai ba. Sadiya tace danno kiran shi kawai ki bani cikin hikima zan fada masa abinda zai taho gidan. Sai dai cikin rashin sa a kira biyar Halifa bai daga ba. Dan haka Sadiya tace dole kam in tsaya Allah ne ma ya turo ni, domin ban tashi da niyyar zuwa gidan ki ba, kawai dazu ina dawowa daga gidan aiki sai na yanke shawarar zuwa gidan nan. Asiya tace Allah ne ya kawo min ke..... "Asiya.! Kiran Anty ya katse mata zance. Gaban Asiya ya fadi, Ta mike tare da fadin gani Anty. Ta shigo dakin ganin Sadiya sai ta yi turus ta daure fuska. Baku tafi ba? Sadiya tace sai mun yi magariba Halifa yace mu jira shi. Nan take Anty ta rikice ta shiga fadin "Akan me zaki ce wai sai magariba ina ce kanwar ki ce ba yarki ba? Ke wannan ba abin kunya bane? Sadiya tana da wata dabi'a sai ta yi banza da mutum dan yana magana ba lallai bane ta tanka. Dan haka ta inda Anty take shiga ba ta nan take fita ba amma Sadiya sai ta zuba wa TV ido kamar ba da ita ake ba. Anty ta koma ta kasa shiga gurin Malam tana ta kai da kawowa a harabar gidan, ta dauki lokaci kafin ta dawo ta kira Asiya tace ta zo su gaisa da bako. Sadiya ta kalla cike da tsoro. Sadiya ta daga mata kai. Yadda Anty ta sata a gaba ne yafi bata tsoro amma ta san Sadiya zata yi wani abu. Wata kwarya ce a gaban shi cike da wani abu kamar tsimi yace "Zonan yata kinji ko insha Allah yau zaki rabu da duk wasu matsalolin ki. Asiya cike da tsoro tace ai bani da wata matsala anyi min magani a Asibiti. Anty ta daka mata tsawa tare da fadin" Kijini da kyau ki matsa kusa ya yi miki magani ana taimakon ki ke kina ganin kamar cutar ki ake yi. Malam yace yi mata a hankali ai bata san tana da matsalar ba. Halifa ya kira wayar Asiya bayan ya gama da kwastomomi ya ga kira da yawa. Sadiya ce ta daga tace taje gurin Anty wai anyi wani bako za su gaisa, amma kuma duk fa naga ta tsorata. Yace "" Kamar yaya ta tsorata ki kai mata wayar please. A kulle kofar Anty Na buga ba a bude ba.. Halifa ya kasa nutsuwa. Kira uku ya yi wa wayar Anty bata daga ba. Asiya wadda suke ta lallashinta akan ta tsaya za ayi mata magani sai kuka take ta na fadin Lahaula wa la kuwwata illa billah!!. La ila hailla anta subahanaka inni kuntu minazzalumin!!! Malam ya mike da nufin zuba mata ruwan da kayan jikinta tunda taki yarda ta cire kayan gashi tana ta kiran Allah. Yana daukar kwaryar sai kamar an ta kade shi can gefe. Ruwan maganin ya zube kwaryar ta tarwatse. Ya zaro ido ya kalli gurin sannan ya kalli Hajiya, wannan yarinyar tana da gaddama gashi ta korar mana Aljanin da zai yi mata wankan. Anty tace tace Na shiga uku da matsiya ciyar nan, yanzu ba wani abu da za ayi Kenan? Bai tanka ba ya nufi hanyar fita a falon Anty ta bi bayan shi tana fadin Allah ya huci zuciyar ka. Ta bude masa kofa daidai lokacin da Sadiya take sake bugawa. Anty ta dube ta tana tambayar lafiya? Sadiya tana kokarin danna kai cikin falon tana cewa ina Asiya ga wayar ta Halifa yana ta kira. Anty ta amshi wayar ta ce kije zata zo. Ta ci gaba da bin Malam tana magana kasa kasa. Bai tanka ta ba sai da ya shiga mota ya zauna sannan ya dube ta, baki shirya ba kika kirani, tun a wancan lokacin na sanar dake ki jata a jiki amma kin ƙi, kin gama tsorata ta yaushe zata yarda. Yanzu kam bansan abin yi ba. Ya rufe gilashin motar suka fice. Sadiya ta koma da sauri ta shiga falon Anty ta samu Asiya tana ta shirbar kuka. Ta kamota cike da fargaba tana tambayar "Me suka miki?" Asiya ta mike suka fito Anty ta kalle su ta ja tsaki tace "Ke menene na rungume ta,? wani abun ne ya faru sarakan zuzuta magana. Magani za a bata kuma ta barar, shine harda wani kiran Halifa a waya to me zaku fada masa? Ta mika musu wayar, ga wayar sai ku sanar dashi abinda kuke son ya sani. Ta wuce kamar ba wata matsala. Sadiya ta amsa suna isa daki Halifa yana kira. Asiya. Ta daga yace Baby Wai me yake faruwa ne? Ta sai saita muryar ta ce ba Anty ta fada maka ba? Ta fadi hakan ne domin bata san me Anty tace masa ba. Yace "Ta fada min amma me yasa zakiyi haka? Ko ba kya son maganin tunda ta nuna kulawa ta karbo miki ai sai ki amsa ko da bazaki sha ba akalla dai zataji dadi. Asiya ta sauke ajiyar zuciya tace zan kiyaye gaba ka bata hakuri ban yi dan taji haushi ba, data bar gurin ne mai maganin yaga bata nan sai yace wai in cire kayan jikina ya yi min wankan magani zai cire min dattin jikina. Ita kuma Anty ta ki tsayawa in mata bayani..... What!! Ya katse ta kamar yaya ki cire ya miki wanka? Anty kuma ta kawo shi gidan? Ni tace min ruwa tofi ne ta sa aka amso miki saboda kariya shine kika zubar a gaban ta kuma kina ta kuka wai zata yi tsafi dake. Haka ne? Asiya ta danyi dim Anty bata jin tsoron Allah bare ranar mutuwarta. Amma nasan ya zan mata. Yace ki bani amsa mana. " Tace haka ne amma ni nayi kuka ne kuma na zubar da maganin ne da nazo fita. Dan yace in cire kayana ya min wanka. Anty ina son in fada mata bata saurari magana ta ba, shine yace mata wai nace za suyi tsafi da ni. Sannan kuma dan Allah ka fada wa Anty lafiya ta kalau masu maganin nan yan iskane, inhar ba za a barni da maganar magani ba ni zan bi Maman Annur mu koma gida ni Ina jin tsoro. Ta fashe da kuka. Halifa ya yi shiru ya rasa wane tunani ma zai yi. Amma shi kanshi yasan gaskiyar magana bai kamata Anty ta matsawa yarinyar nan tace wai lallai tana da aljanu sai ta nema mata magani ba, Sannan baya son ya yi abinda Asiya zata raina Anty yana ganin mafi dacewa kawai ya tare a gidan shi abin ya isa haka. Cikin sarkewar murya yace Baby ki yi hakuri idan Na dawo zan yi abinda ya dace. . Da gaske Asiya har ya dawo a tsorace take, dan haka yace ta shirya sukai maman Annur gida. Sai da yayi musu tsaraba sa anan ya kai su. Inna tana ta godiya da addu"a maman Annur tace da Asiya ta kula da kanta sosai. Asiya tace to Amma dan Allah karta fadawa Inna. Sai da suka biya ta wani gurin shakatawa Halifa ya yi musu oder kayan kwalam suka ci suna hira. A ranar ne ya furta cewa Asiya da zu da kika ce zaki koma gida ko wallahi sai naji kamar kin ce Duniya zata tashi, kamar yadda Na sha alwashi zan yi maganin matsalolin ita Anty bata san halin wasu masu magani ba, sam babu Allah a ransu. Hukuncin da na yanke shine kawai zamu koma gidana shike nan komai ya zo karshe. Asiya tace duk yadda ka ce amma ni dai bana son harkar masu maganin nan ne. Yace zamu biya kiga gidan an gama komai gefe na har na saka kaya. Asiya cike da nurna tace suje ta gani. Gidan ya matukar birge Asiya ya zaga da ita ko ina_ta gani, tace Yaya ni ce a wannan gidan zan zauna kamar gidan Shugaban Kasa? Ya sa dariya suka shiga sasan shi ya kunna wuta haske ya game ko ina. Halifa ya daga ta sama yana juyi a kan kafet din dake tsakiyar falon. Ina son ki Asiya sosai in kika barni wallahi rayuwata zata tsaya cak. Ya zauna tana kan cinyarsa. Tace nima ba zan iya barin ka ba Yayana kai ne Duniyata Aljanna ta. Ni dama tun a ranar farko Na fara son ka. Zo muje ki ga dakin baccin mu a nan zamu samu babynmu yau din nan ba sai gobe ba. Tace a nan zamu kwana? Yace sosai gidan mu ne gobe zamu je can mu kwaso iya kayan sawa, kafin sati daya zan saka komai na gida. Shike nan mun tare. Wata irin rayuwa suka yi a daren wadda baza ta kankaru a zuciyar su ba. Sun kwana cike da nishadi da so da kauna. Da safe suka yi wanka sannan suka maida kayan jikin su suka nufi gida. Anty ta kwana cike da zullumin inda Halifa ya tafi kuma shida matarsa, abu mafi tsoro ya kashe wayoyinsa duk inda tasan zata iya samun labarin sa ta buga amma shiru. Daga karshe ta kira wani malamin ta domin ya yi mata bincike. Jim kaɗan ya kira ya sanar da ita cewa yana raye amma fa yana mugun hannu dan haka ta aiko da dubu dari domin ayi mata wani aiki da zai bayyana da gaggawa asubahin fari. Duk da zuciyar ta tayi farin ciki dajin haka, sai dai dolenta ta danne domin da sauran lokacin, yanzu da Halifa ya mutu ba tare da ya mallaka mata kaf dukiyar shi ba ai aikin banza Kenan. Dan haka ta tura kudin kuma tashiga kiran yan uwa tana sanar da su harma wadanda suke Uba daya. Kafin waye war gari hankula sun tashi domin fa babu wanda ya samu Halifa a waya. Ana idar da sallar asubahi dangin suka soma tururuwa dan zuwa jin ko a samu wani karin bayani game da batan Halifa da matar shi. Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [7/7, 22:15] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Baffa ya yi sallama da Dady, ya fito, bayan sun gaisa Baffa cike da damuwa, yace wai sai na samu labari wadannan mutanan sun sace Halifa to ta yaya abin ya faru? Dady cike da jimami yace "To ni dai na dawo Antyn ta su take sanar da ni cewa an kama Halifa abinda har yanzu na kasa fahimta shine kiran ta suka yi ko waye sanar da ita oho. Sai kuka ta kwana yi. Baffa yace har wayar matar tasa ba a samu ba kenan? Dady yace " Ita ai ba wanda ya san lambarta ma bare a kira. Baffa ya nisa sannan yace " To Iyayenta sun samu labari kuwa? " Dady yace Gaskiya da kyar ne, domin ba wanda ya tuna da su ma, amma bansani ba. Baffa yace" To ni abin ne na rasa gane kansa, ance ba su kira waya ba, ta yaya aka san cewa an sace shi? Jikina yana bani yaron nan ba haka bane. " Dady yace Allah ya sa, domin ina cike da dimuwa. A cikin gida kuwa Yayun Halifa wadanda suka kasance kannan Anty Uwa daya Uba daya duk sun hallara a gidan suna ta koke koke a batan Kaninsu da matar sa. Maman Ummita kuwa tana zargin ko dai Anty ce ta salwantar da shi, domin ita ta jima da fita daga halin Anty ta fada wa sauran sunce ba haka ba, sunsan dai Anty ta kanainaye Halifa ko su zai wa alheri dole sai ta sani in ta ga dama ta hana shi, ko kuma ta amsa ta rage ko ta rike ma in taga dama amma basa zaton zata iya salwantar da Halifa akan dukiyarsa, dan haka ita a gurinta Duk inda Halifa yake dole Anty ta sani. Bros ya Iso gidan cikin wani mugun gudu ya yi fakin sam bai kula da su Dady ba zai yi ciki. Dady ya ce "Kai Adamu.! Bros ya dawo da sauri ya ce Dady ban kula da Kuba, ya gaishe su. sannan yace da safen nan naga sakon Hafsi wai suna ta kirana ban daga ba, wai ƴan kidinafin sun sace Halifa da matarsa.! Dady yace" To, abinda dai muke ta zato kenan Mamanku da zata bamu tabbaci sai kuka take Taki fadin yadda a kayi ta samu labari.... Ya katse maganar sakamakon motar Halifa da ta shigo cikin gidan. Cike da al ajabin ganin Baffansa a gidan da sassafe haka ya fito a motar yana fadin Baffa lafiya da sassafe haka da ka kira ai da sai in zo? Ya kula da yadda duk suke kallon shi, har ya dubi jikin shi ko wani abu ne, yaga ba komai a jikin shi. Daidai lokacin Asiya ta katse su da fadin ina kwanan ku? Babu wanda ya iya amsa mata, sai Baffa da ya dubi Halifa yace "Ina wayarka?" Halifa yace tana mota.Ya juya da sauri ya dakko yana fadin ashe ma a kashe take. Dady yace me yasa ka kashe kuma baka sanar da Antynka ina kaje ba? Sai lokacin Halifa ya tuna da ya kashe wayar sa tun da suka shiga gidan domin su samu sakewa. Yace Tab aini na shafa'a cewa na kashe wayar, Anty ma shafa a nayi munje ganin gidana ne domin ina son mu koma cikin satin nan, to munyi yan gyare gyare muka gaji sai kawai muka kwanta. Bros ya ja tsaki, amma ka dauki alhakinmu ka taso kowa tsaye. Halifa yace Ya Salam! Bros ya ci gaba da fadin "Antynka ta ce yan kidnafin sun sace ka. Asiya ta zaro ido. Baffa yace mikawa Dady hannu yana fadin to ni zan koma tunda Allah ya takaita. Ya dubi Halifa Kai kuma Malam Umar ka daina kashe waya sannan ko baka sanar da kowa cewar ga inda kake ba, lallai Antynka ta sani. Zan kiyaye Baffa ina neman afwa na fito da kai tunda safe. Babu komai yarinya kije ciki ko? " Baffa ya fada yana Kallon Asiya. Ta rusuna a gaida gida. Ta wuce sasanta tana jimanta abin yayin da Halifa da Dady da Bros suka nufi cikin gida. Anty ta mike da sauri lokacin da Halifa ya shigo falon ta na fadin Allah na gode maka ta fashe da sabon kuka ta zo ta rungume shi tana fadin Halifa ba su taba ka ba ko? Da.ma Malam yace zaka dawo da safe. Halifa ya dago ta daga jikinta cike da kauna yace, Anty babu wanda ya kama ni, kuskure na yi na kashe wayata Mun bita gida na ne, dan inason mu koma ciki sai na biya Inga me gidan ke bukata kawai daga kallo muka yi bacci. abin daya daure min kai wa ya fada muku barayi sun kama mu? Anty ta cika da mamaki har anzo lokacin da Halifa zai yanke wata shawara ba tare da ya fada mata ba?! Tadanne abinda take ji na takaici muryar ta a disashe tace shikenan Dan uwana tunda Allah yasa ka dawo lafiya kana cikin koshin lafiya Na gode wa Allah. Sauran yan uwa suka yi ta jajantawa Halifa. Yayi musu alheri kowa ta koma gidanta. Asiya kam ta hada masa abin kari harta canza kaya. Ya kalleta ke ce kika yi kidinafin dina fa, tun jiya kika tada hankalin kowa a dangi na . Asiya ta lumshe ido tana tuno yanayin da suka samu kansu a jiya. Ta bude idanu ta zuba su akan nashi, tace "Jiyan nan ji nake mu kadai ne a Duniya daga ni sai kai, akwai wasu kalamai da ka furta ka yi ta maimaita su, tun jiya ni kam da na tuno su sai inji babu macen da ta kaini sa'a a Duniya. Ta mika mishi tafin hannun ta sai ya dora nashi, tace kamin wani Alkawari guda daya. Ya matso "Fadi inji" Duk yadda rayuwa zata juya mana baza ka sake ni ba? Sosai ya jawo ta jikin shi ya rungume kam. "Babyna kar ki kawo maganar rabuwa ni dake ina fata mutuwa ce zata rabamu, nima kuma ina rokon ki kiyaye. duk abinda zai iya haifar da hakan." Ta dago fuskarta ta dube shi, ta kai hannu ta kama dan gemun sa na gayu tace, Wane irin laifi ne zan maka har ka iya rabuwa dani? Yace Ki ci gaba da girmama magabata na iyayena sun mutu amma suna da madadi kamar Anty da Dady. Kalli yadda suka rude iya jiya da basu jini ba. Dan Allah ki girmama su. "Asiya ta fita daga jikin shi ta koma ta zauna. Idanun ta cikin nashi tace. Zan zame maka rabin Duniya mace ta gari zaka yi alfari da ni insha Allah. Ban san menene so ba, amma ina matukar son ka, ina kaunar ka. Ta kai karshen maganar tare da kai hannu ta shafi kumatun shi. Kalaman suka yi masa dadi. Ya janyo ta jikin shi tare da fadin " Ki gode wa Anty da ta kawo shawarar cewa sai mun gwada gidan su Bilkisu. Har ga Allah lokacin da na ganki banji komai ba, amma yanzu da gaske ina son ki. Dadi ya kama Asiya. Ta shiga hango irin rayuwar da za su shimfida ita da Halifa a sabon gida. Anty tana kwance cikin bargo zazzabi ne ya rufe ta tun da Halifa ya fada mata cewa zai tare kuma har ya iya tafiya ya kwana ba tare da ya kira ta ba, abin ya kona mata zuciya. Wannan ya hadda sa mata zazzabi. Halifa ya shigo yana fadin Subhanallah Anty aje Asibiti mana a duba jikin naki? Tace "Zazzabi ne zai sauka, zuwa anjima. Halifa dama kiranka na yi wannan abu da ka yi ka saka ni a damuwa, ace zaka tashi amma ban isa ka sanar dani ba harma ka dauki matar ka kukaje gyaran gida?" Ba gyaran gida mukaje ba kawai dai mun biya ne, amma to ki yi hakuri Anty bazan sake ba. Idan kin samu sauki kuma sai mu tsaida ranar da zamu tare din. Sannan Anty zan baiwa Asiya kayan lefen nan a gurinki saboda ta yi sabbin dunkuna amma za mu cire wadanda suka yi mata yawa kamar jallabiyun ciki sai a canzo mata daidai ita ko Anty.? Wani sabon takaici ya cikata duk ta saida rabin kayan kuma ta zaci ba zai sake magana ba. Ta cije tace to ba damuwa. Yace to Bari na tafi Na shirya Na fita tun jiya oder ta ta zo,ban samu nutsuwa ba bare a bude kayan. "Anty tace Allah ya taimaka. Halifa yana fita Anty ta tashi zaune ta dakko waya tana tunanin wane malamin zata kira. Wanda ya yi wannan aikin yana da zafin hannu shine ya dace ta kira, domin ai dama ita ce tace yan kidnafin sun kama Halifa, shi cewa ya yi yana mugun hannu kuma wannan yarinyar itama ai mugun hannun ce. Yace mata zai dawo gida da sassafe kuma dai abinda ya faru kenan. Ta danna kiran shi suka gaisa tana sake yi masa godiya tace Dan Allah wani aikin zata bashi tana son ya kulle mata bakin Halifa domin ya bata ajiyar kaya ta siyar da kusan rabi ta kashe kudin. Sannan zai tare a wani gidan sa, tana son ayi abinda gidan zai gagare su zama su dawo kusa da ita. Yace "To yanzu dai yana son ta fada mishi abinda suka fi tsoron maciji ko mage ko dai wani abu a kwari, sannan maganar rufe baki angama amma kudin aikin sa dubu dari biyar. Tace Haba Malam kai matsalar ka cika kudi Dan Allah ka min sauki dubu dari biyu zan bada. Yace "Haka ne kudin, ba wai suna na saka ba, ina son aikin nan harda aljanu zan hada kinsan me za su bukata ni a gurina? Ko zaki iya basu jinin mutum? Anty ta yi shiru tana tunanin kudin inda zata samu. Tace Malam zan bada dubu dari kafin alkalami. Ya ce duk lokacin da kika shirya ki sanar dani, ina nufin in kin tanadi kudin. " Ya kashe wayar sa. Tace Shege mayen kudi duk da nasan cewa aikin shi kamar yanka wuka, dole in San ya zanyi in yaga dari uku cash zai yi aikin,domin dai da kunya Halifa ya zo kan kayan nan ace ba su. Yanzu aciki zan dibi sarkokin nan in yi kasuwa da su. *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [7/14, 07:16] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Kamar da wasa Anty ta hade kan sarkoki ta cefanar, ta shirya ta kaiwa Malami kudi ya amshe dari uku da saba'in ya mata laminin sauran ya bata magungunan da zata yi, yace mata duk ranar da ta gama amfani da maganin ta tunkari Abba ta fada masa cewa bata son ya bar gidan sannan ta sanar da shi cewa ta yi amfani da kayan shi. Yace babu abinda zai iya. Asiya ta ga har ankai sati amma Hailfa bai kara batun tariya ba, ita kuma tana son yi masa maganar amma tana tunani. Ta daure tace Yaya wai kuwa ya batun tarewar mu tunda naga jikin Anty da sauki. Yace Anty ta sameni taroke ni akan wai in taimaka in hakura da tashi zuwa gaba kadan. Sannan ta bani hakuri akan kayan ki na lefe wai ta taba. Duk da banji dadin abin ba, amma dai bani da yadda zan yi tunda matsayin Uwa ta ke. a guri na. Dole in yi hakuri da wasu abubuwan dan haka kar ki damu mu bata lokaci insha Allah komai zai zama daidai. Duk da Asiya bata ji dadin abinda ya faru ba amma bata nuna komai ba, cike da fara a, take fadawa Halifa Allah Sarki Anty tana kaunar ka shiyasa ta haka. Dan ma kaine ka damu mu koma can amma ni gwara nan din da motsin mutane. Halifa cike da jin dadi yace Allah ya yi miki albarka wallahi har ina tsoron ta ina zan fara magana. Asiya tace 'Haba Yayana nifa abin ikon ka ce, umarni kawai zaka bani a kan komai. Ya kama hannuwanta shi yasa nake kara son ki. Anty ta yarda aikin Malam ne ya ci. Dan haka ta kuma wankar jiki ta kuma zuwa gunsa da wasu bukatun tace Tana son a yi wani a bu tsakanin Halifa da matarsa wanda zai hana su zaman lafiya domin bata son ace matar Halifa ta haihu ya samu mai gadon abinda ya mallaka,Malam yaron yana da dukiya da shi kanshi saidai ya yi kiyasi kuma gashi da nasibi, dan abinda aka tsakura mishi a kudin sa yanzu ya ninka yafi sau dari. Ni dana sha wahalar shi har yanzu banda komai in matar shi ta haihu. Malma yace Kash da kin zo nan kafin bikin nashi kika zo da ko auren ma ba zai taba yi ba. Kinga yana mutuwa kin tabbata ke ce mai gadon sa." Anty taja tsaki tace ai lokacin ban San nan ba. Amma yanzu ma in dai da yadda za'ayi a toshe mahaifar ta kar ma ta dauki ciki bare ta haife shi. Ina da burika game da Halifa sosai. Malam ya mata Alkawarin matsa war da kudi magana ta kare. Asiya ta kara so falon da gudu tana ihu,. Anty ta taso a gigice tana cewa waye meye! Gadangare ne ya biyo ni Anty ta ja tsaki tana fadin meye abin gudu a kadangare? Asiya harda shidewa Dan tsoro. Tace "Wallahi Anty sam ni bana son kadangare ina tsoron sa sosai. Bayan fitar Asiya take Anty ta kira Wayar Malamin tana sanar dashi cewa Allah ya saukaka mata yarinyar nan kadangare ke firgita ta. Malam yace sa kudin aiki yau gidan ba za a kwana lafiya ba. Cikin bacci Asiya ta shiga firgita tana tsorata domin farkawa tayi taji ta a jikin Halifa ya rumgume ta gam yana tofa mata addu'o'i ta kalleshi ta hada zufa sharkaf sai ta sake kankame shi. Yace kinyi bacci babu addu'a ko? A wahalce tace na yi adduo'in dana saba kawai dai jiya ne wani kadangare ya biyo ni dama ina tsoron sa, sosai. shi ne nayi mafarkin sa yana ta bina. Halifa yace "Shiya sa cikin baccin naji kina nishi kina karanta addua, to kar ki damu ki canza yanayin kwanciyar ki sai ki sake yin adduo'in,ta yi yadda yace shima ya tofa mata, saidai kuma da bacci ya soma fizgarta zata ga kadangaru bakake sun cika mata kan gado sai ta farka a gigice. Haka suka kwana. Da safe yake fadawa Anty Halin da ake ciki ta yi murna sosai amma sai ta boye ta jajanta tace "To Halifa me zan muku baya ga addu'a ance tana da jinnu kunce ba haka ba, Na kawo mai magani ta masa sharri ka hau kai ka zauna, yanzu kam ai sai dai ku nemi magani da kanku ko ka sanar da iyayen ta. Halifa dai ya mike ya koma ya samu Asiya zazzabi ya rufe ta sai rawar sanyi take yi. Ya rasa ina zai saka kan sa yace tashi ki sa hijabi mu tafi Asibiti. Halifa ya yi wa likitan baya ni game da yadda suka kwana da kuma yadda take fama da zazzabi. Likitan ya tambayi Asiya ta sanar da shi yadda abin ya faru. Yace "Ta tsorata ne sosai, saboda tana jin tsoron kadangare duk da ni ba likitan kwakwalwa bane amma ina da wata yar masaniya kasan, kasan Ita kwakwalwa kamar kwamfiyuta take in ta Karbi abu ba a cikin shiri da tsaro ba sai ta birkice ta yi ta abubuwa ba daidai ba. To itama abin ya zo mata ba zato ta tsorata da yawa ne ba komai da ta samu bacci komai zai zama daidai. Sai dai shi zazzabin ta yuwu rashin bacci ne ko maleriya bari a yi mata gwaji mugani. Kusan gwaji kala uku likitan ya sa aka yi mata. Bayan kawo sakamakon ya tabbata akwai malaria likitan yace to ko wannan maleriya ta isa ta saka ta yin abinda yafi haka. Sannan ya duba daya sakamakon yace saukin ta kuma ba taifot. Ya kalli dayar yace ko wannan ma zai iya saka komai dama tana dauke da ciki ne? Halifa ya mike tsaye da sauri, tare da fadin me kace likita. Yace tana dauke da ciki karami Dan sati biyu. Sai kawai suka ga Halifa ya zube a tsakiyar ofishin ya yi sujjada yana fadin Allahu Akbar. Ya Mike ya rungume likitan yana fadin likita na gode da wannan albushirin naka. Ka dai tabbatar ko? Gani nake yi kamar a cikin mafarki. Likitan yana dariya yana Dan buga ka fadar Halifa yace ko shakka babu mutumina matar ka tana dauke da ciki kamar yadda yake a rububuce. Halifa yace ina mamaki Wai ni ne na yi ciki ya Allah ya juya gurin Asiya wadda kunyar kalaman da Halifa ke furtawa suka sa ta sunjuyar da Kai. Ya rungume ta yana fadin ina kaunar ki maman yarinyata. Ya kalli likitan mace ce ko. Cike da dariya likitan yace "Sai dai in kunje hoto za a fada muku,suma sai ya dan kara kwari. Halifa ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kudin dake ciki bai kirga ba ya mikawa likitan Ba yawa goron albishir ne, ina son ka rubuta abinda ya kama ta ci Sannan ka fada mata dokoki kaga yarinya ce karama kar ta yi ganganci. " Likita ya sa dariya yace ba komai zata iya Allah da ya bata shine zai bata kariya da danta. Halifa yace ka gama magana Allah ya baka lada. Tamkar ya yi wa Asiya tafiya haka ya ruko ta, yana fadin ko in dauke ki? Asiya kuwa ji ta yi karfi ya zo mata tama daina jin komai tunda likitan ya ambaci ciki. Tace "Yaya kana sani jin kunya sosai ka sake ni zan iya tafiya." Duk da haka ya rike mata Hannu duk kunya ta ishe ta cikin mutane, Haka suka ratso har mota. Ya bude mata ta Shiga ta zauna ya rufe ya zagayo cike da farin ciki ya bude gefen shi ya shiga. Ya kallo Asiya wadda take jin ranar yau ta musamman ce a gurinta. Yace " Ina son ki sosai Asiya ya kai hannu ya daga hijabin ta ya zura hannu ya shinfida a cikin ta yace Yanzu dai dana yana kwance a nan ko? To ya naji be yi girma ba? Asiya tace to duka baka ji ance sati biyu ba? Halifa ya dauki waya ya fara danna number dole in fara yi wa Anty albishir sai dai wayar Anty Busy. ya kira Mijin Anty ya fada mishi, ban sha mamaki ba sai da naga ya kira Baffa. Nace Yaya yanzu kuma sai ka fada mishi? Sosai ma zan fada mishi kuwa ai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. Haka dai ya yi ta kiran abokai da yan uwansa. Yace bari dai zan kira Sulaiman ya kaiwa su Inna waya sai ki fada musu. Asiya tace kunya zanji sosai ka bari a hankali sai in fada musu ko sugani. "Anty har yanzu tana waya, ya fada cike da haushi bayan ya sake kiran ta. Ya kira layin Hafsi ta daga yace kina gida ko"? Tace ina gida. Ya ce ki kaima Anty wayar akwai abinda ya kamata ace ita ce farkon ji yanzu za ta zama itace karshe. Hafsi tace menene ya faru Uncle? Yace Anty zata fada miki. Ta shiga gurin Anty daidai lokacin da take fadawa Malaminta cewa ga shi nan ta turo masa kudin aikin daure mahaifar Asiya. Hafcy ta mika wa Anty wayar tare da fadin Uncle zai miki albishir. Anty ta amsa tare da fadin ya wuce kaya sunyi riba oder ta yi kyau. Daidai lokacin ya sake kira. Ta daga yace "Anty albishir mai dadi." Tace miliyan nawa aka samu? Ciike da jin dadi yace Anty girman lamarin nan yafi batun kudi. Zan zama Baba kyautar Dan mutum Allah ya bani sati uku kenan..... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [7/22, 21:10] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w *🔉 NASIHOHIN MALAMAI🔉* *ADDU'O'I MASU MAHIMMANCI. Vol 2👇🏼* 1️⃣ *Addu'ar da ake yi domin ganewa da fahimta da hadda, haka nan gurin warkar da in ina. Wannan ce addu'ar da Annabi Musa,Aminci Allah ya tabbata a gareshi ya yi lokacin da aka umarce shi da ya tafi wajen Fir'auna*. Alƙur'ani sura ta 20 aya ta 25-28 رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي، وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي، وَاحْلُلْ عُقْدَةً مِّن لِّسَانِي، يَفْقَهُوا قَوْلِي Rabbi ishrah li sadri, wa yassir li amri, wahlul 'uqdatan min lisani, yafqahu qawli. _Al-Qur’ani, Surah Taha._ Wani abu ne ya taso tun daga yatsa har tsakiyar kan Anty, take ta Mike tsaye cike da tashin hankali." Halifa ciki matar ka ke gare ta? " Yace Wallahi Anty ashe ma shine yake sata duk Wannan firgicin gamu nan zuwa gidan nace dai bari in fara sanar da ke ne kuma sai kina ta waya. Ta sauke numfashi. "Lallai wannan babban albishir ne Halifa Allah ya kawo ku gida cikin aminci ka yi tuki a hankali. Jifa ta yi da wayar a kan gado tana fadin ya Allah ka kawo min dauki ciki kuma Halifa zai yi ɗa to me zan samu kenan? In yi wahala da shi wata banza ta zo ta haifi Magaji. Ta sake zabura ba zai yiwu ba, gashi Na tura kudin aikin. Ta dauki wayar ta kira Malamin yana dagawa tace Aiki fa ya jika, yarinyar nan dai ta samu ciki. " Malam yace to menene abin daga hankali? Sai a zub da shi kuma a daure mahaifar ni fa in kina so sai in kwantar da cikin." Anty ta zabura kamar tana gabanshi, tace "A a Malam karka kwantar da shi zai iya tashi, inda za'a iya cire ma haifar cak,sai a aika aljanu su cire su yi taushen su su cinye." Malam ya saki dariya Sannan yace, Kai kina da mugunta sosai wallahi. To ba matsala yanzu dai za a cire cikii a kulle mahaifar kowa ya huta. Halifa ya tsai da mota bayan ya shigo gidan Asiya zata fito sai Halifa ya ce tsaya, ya kai hannu ya bude motar yace fito. Asiya ta fito suka nufi daki. Kan doguwar kujera ta kwanta ya yace Bari na fadawa Anty mun dawo. Da murna Anty ta tari Halifa tana addu'a sai kuma ta fashe da kuka. Inama Hajiyarmu tana raye. Halifa wanda bai san mahaifiyar ta su ba saidai kaunar ta da yake ji a ransa yace "Allah ya yi mata Rahma amma Anty ni ai kece Uwata, ina jin ki a zuciyata fiye da ita tunda ban shaku da ita ba. Anty cike da jin dadi tace Allah ya yi maka albarka Halifa yadda kake min biyayya Allah ya sa wannan dan da za a haifa maka Shima ya yi maka biyayya. Ameen Halifa ya amsa da sauri domin ji yake kamar daga makogwaron mahaifiyar shi addu'ar ta fito. Anty cike da makirci tace muje in ga jikin nata. Ido cikin ido suka kalli juna da Asiya a hankali ta furta Allahumma kafini him bina shi"ita. Addu"a ce da malamin su ya basu yace in sun ji tsoron cutarwa daga wani mutum to su karanta masa. Anty ta Iso tana fadin sannu da jiki Asiya Allah Sarki baiwar Allah matar firauna. " Halifa yace Anty ni ne Fir'aunan? Cikin dariya tace" A a kawai dai na tuna da mai sunan nata ne. Asiya ta yi guntun murmushi, tuni ta gane cewa rashin abin fada ya sa Anty fadin haka. Aka shiga rainon ciki, Haka dai Asiya ta shiga laulayi komai taci sai ya dawo dole aka kwantar da ita a Asibitin ana ta karin ruwa Halifa kuwa ko kasuwa daina zuwa ya yi duk ya fita hayyacinsa kamar shine mai cikin. Asiya har tausayin sa ta ke ji. Sadiya ce a gurinta Innar su ma tana kai kawo a gurin. Anty kam kullum tana hanya da girki, sai dai Asiya ta kasa yarda cewa Anty tana murna da cikin dan haka ta Kaurace wa duk wani abu da Anty zata kawo da sunan ta ci ko ta sha. Wannan matakin ya kona ran Anty domin ta lura Asiya ta fake da amai ne dan kar ta ci abubuwan da take kawo mata wanda da ta ci da tuni cikin sai labarin sa. Shi kan shi Malamin ya ji haushi Dan haka yace ta barshi da ita ai dama Wai yaga karamin aiki ne amma zai mata abin da zata yi mafarki kuma da ta farka cikin zai fita. Duk wanda ya yi imani cewa Allah ishashshene babu shakka sai ya isar masa. Abinda Asiya ta dogara da shi kenan. Kwanci tashi a sarar mai rai inji yan magana ciki har ya shiga wata hudu, duk da irin abubuwan da Anty ke yi Amma ko gezau kuma ta kasa ganewa bare ta daina narka kudinta a bokaye. Karshe dai Malamin da yaga Anty ta saka masa kuka wiwi tana fadin har yanzu bai biya mata bukatar ta ba, gashi ya amshe mata kudi. Shine ya ce gobe ta dawo. Wani Apple ya bata yace matsawar ta ci shi to saidai buzunta. Anty ta rasa yadda zata ba wa Asiya Apple. Sai ka wai ta dakko ta Bawa Nur da Nihal tace ga shi maza ku ruga ku kaiwa Antyn ku, kuce Babanku ne ya kawo. Har ga Allah Asiya ta dauka Babansu ne ya kawo dan haka tuni yawunta ya tsine, ta gatsa hakori tana fadin gashi da zaki ta sake gatsa tana ci gaba da fadin shi Babanku din ya tafi ko yana ciki? Nur tace ya tafi. Nihal tace "Ke Nur sannu da karya, Dady bai zoba yau dinnan." Da sauri Asiya ta furzar da Apple din tare da kokarin kakaro na bakinta. Su Nihal suka shiga yi mata sannu. Ta soma karanto addu'o'i domin ta gama gano gadar zare Anty ta ƙulla mata kuma ta fada. Da sauri ta dafa cikin ta ta ce Allah ka tsare min wannan kyautar da ka bani, Allah kar ka bar wani ya cutar da abinda ke cikina. Ta soma jin yanayi Na tashin zuciya da jiri tana daga zaune ta dauki wayar ta da sauri ta danna kiran Halifa, sai a kira na biyu sannan ya daga lokacin muryarta ta fara sarkewa, tace ka zo maza ka kaini Asibiti na ci wani abu ahhh...maganar ta sarke Wayar ta fadi. Ya firgita ainun ya baro kasuwa afujajan tun a hanya ya kira Anty wadda su Nihal suka zo suna fada mata cewa Antyn Uncle ta fadi. Sai taje dakin ta dauke Apple din ta kutsiri mai kyau daidai yadda Asiya ta gutsira ta aje shi inda ta dauki wancan. Ta fice ta bar gidan dan haka Halifa yana kiran ta yace Anty ki duba Asiya bata da lafiya ki yi mata wani Abu kafin in dawo. Tace "Subhanallah bana gida naje Ƴankaba amma yanzu zan nufi gidan. Halifa ya samu Asiya tayi amai ga kumfa kuma ta suma ya sunkuceta zuwa Asibiti da gaggawa. likitoci suka hau kanta. Anyi nasarar shawo kan gubar bata gauraye jikin ta ba, sun gano guba taci mai tsananin haɗari wai dan ma bata ci da yawa ba, kuma tayi amai bayan taci din. Halifa ya girgiza kwarai da jin cewa Asiya ta ci guba to waye kenan ya bata guba, a sukwane ya koma gida ya ga Apple din da aka gatsa da kuma wani karami wanda ta balla ta to far da shi ya koma Asibitin ya kaiwa likitan kamar yadda likitan ya bukaci abinda taci a lokacin dan su gwada su gane wace guba ce a cikin nau in gubar da ake da su Dan su san maganin da za su bata ga ciki. Anty ta shigo tana ganin Halifa agigice tace ina Asiya. Ta so ace cewa zai yi ta cika, sai taji yace tana ciki. Ya tsare Anty da ido Anty waye ya ba Asiya guba.? Ta zabura "Guba kuma Halifa ina za asamu guba?" To waye ya bata Apple? Tace "Wai kana nufin Apple din dana raba musu aka kai mata nata shine aka samu mai guba? Ya sunkuyar da kai, yana jin zargin Anty a zuciyar sa. Amma wani sashen na zuciyar yana hanashi da cewa Sam Anty bazata yi haka ba. Ya dago ya dube ta. Ina aka samo Apple? Ji tayi kamar yana tuhumarta kamar yana zarginta. Ta fashe da kuka "Halifa kar dai zargina ka ke yi? Na siyo ne a Unguwa na zo na raba musu. Yace ba shakka sai ya fito wanda duk ya yi yunkurin kashe min mata da yata. Anty tace ni da kai zan kira masa hukuma zo muje in kai ka gurin da na siya. Likitan ya katse su da cewa zaka iya shiga ta farka. Anty ta ruga tana fadin Allah ka shiga lamarin wannan yarinya. Halifa ya tsaya gaban gado yana kallo Asiya wadda ta kara ware ido tana Kallon Halifa take ta tuna ashe fa ta ci Apple nan take komai ya dawo mata a kai, ta kalli Anty wadda take fadin Allah mun gode maka sannu Asiya. Sai kawai ta ji murmushi ya sauka akan fuskar ta tare da fadin Allah na gode maka da ka sake bani dama ta rayuwa ina me jaddadq imani na agareka ya Ubangijin Musa da Isa ya Ubangijin Sayyadina Muhammad Sallah akai wasallam. Halifa ya matsa kusa ya kara kunne da baya jin me Asiya take fada, ya dai ga ta kafe Anty da ido, zuciyar shi ta darsa cewa kodai Anty tana da hannu a cikin lamarin. Yace me kike fada Asiya? Ta kalli fuskar Anty wadda ta gama tsorata tana fadin me take cewa ne Halifa. A zuciyar Asiya tace, Anty karki damu ba wanda zan fadawa abinda ki ke yi, bazan hada ki da Halifa ba, amma zai ci gaba da kai wa Allah kara, shine zai tsaya mana. Muryar Halifa ta katse ta. "Asiya me kike fada? Naga kina murmushi." Can kasa muryarta tace ina son in karfafawa Anty zuciya ne naga ta tashi hankalin ta. Ka fada mata karta da mu in Allah ya yarda tunda Allah yasa na farka to zan tashi. Yace "Sannu Asiya zan fada mata amma waye wanda ya baki Apple mai guba?. Ka bari in samu kwarin jiki sai a yi magana. Yace shike nan. Anty wadda ke a firgice ta tsaya a gefe gaba daya ta sadakar Asiya tana zayya ne mishi abinda ya faru ne, tunda ta kasa kunne amma ta kasa jin abinda suke tattaunawa kasancewar muryar ta ta yi kasa. Daya daga cikin likitocin ya shigo yace "Kayi hakuri fa, kar ku sakata magana da yawa domin Allah ne yasa ta tashi mu kammu mun kasa gane ko wace nau in guba aka bata amma zamu tura Asibitin Aminu Kano. Babban likita zai yi maka bayani. Sannan bisa shawara ka sanar da Yan sanda dan su yi bincike akan lamarin nan. Anty dai ta kasa magana tsabar fargaba. Halifa yace gaskiya dole muje gaban Hukuma gaba daya na kasa gane ma al'amarin Ya kalli Anty. Duk yadda aka kayi wanda ya turo aka sa wa yarinyar nan abin hana daukar ciki, shine dai ya sa aka zo aka bata guba. kuma wallahi na jikina ne. Har lokacin Anty ta kasa magana. Sai da yace Anty tace ki kwantar da hankalin ki tunda Allah ya sa ta farka zata mike. Anty tace "lnsha Allah ta matsa kusa da gadon tace. Sannu Asiya." Asiya ta saki murmushi, gaban Anty ya fadi ta rasa murmushi me Asiya ke yi. Ta ɗan ja baya tana fadin Allah dai ya baki lafiya. Babban likita ya kira Halifa ofishin sa, yadda wannan likita ya shigo yana bayani haka ya fada masa. Ya kara da cewa a jikin guntun muka samu gubar an canza ainihin Apple din dan kar a gane Allah ne ya sa ka dakko guntun dan haka wannan matsalar tana bukatar jami an tsaro ko da na sirri ne dan su bincika su gano ina ne matsalar take. Halifa ya ce babu damuwa insha Allah da mun bar nan zanje na sanar da su. Halifa yace zaije ya sanar da inna dan ya taho da Sadiya ta zauna da ita. Sai Asiya ta rike masa hannu tace karkaje ka kyale su in Innarmu tana da hawan jini zata damu ko na fito dan Allah kar ka fada musu, ni da zaka yarda daka rufe maganar domin kowa ya ji zai zargi yan gidan. Halifa ya ce To amma kuma sai in zura idanu a kashe min ke da dana, me yin abin nan fa bai fara Dan ya daina ba. " Asiya tace kawai kace wa Anty ko ita ko Hafsa nace wa, ni ya zo ya zauna da ni. Cikin kwana biyu Asiya ta samu sauki ciki kuma yana nan babu abinda ya shafe shi, Hafsa ce ta zauna da Asiya likita ya jaddada wa Halifa lallai gubar mai tsanani ce badan taimakon Allah ba minti biyar Asiya baza ta kara ba a Duniya Dan haka ya hana ta cin kowane abu daga hannun kowaye, domin gudun kar a sake samun matsala. Suka dawo gida Halifa yana cike da zarge-zarge a zuciyar sa. Suna kwance ya kama hannun Asiya wadda har ta soma bacci ta bude ido tace Yaya kana son wani abu? Yace Yace magana zamuyi Asiya ina cike da tsoro ne kar in zargi wanda bai kamata ba, Dadyn gidan nan na ji ina zargi kuma na kasa goge zargin. ". A uzubillahi Mina shaidanirrajim gaskiya kar ka dauki alhakin sa, me zai sa ka zarge shi? "Shine ya hanani in sanar da jami an tsaro kamar yana tsoron asiri ya tonu" ya faɗi mata dalilin zargin. Asiya ta fada masa yadda abin ya faru sai ta kara da cewa ina sunan Dadi zai fito a nan? Yace kenan Bros ne? Asiya tace gaskiya bashi ya kawo Apple ba, Anty ta siyo kuma ina zargin wanda ya kawo Apple dinnan bayan na shiga wanka ya zo ya canza. Dan haka kabar zargin kowa kawai mu kyalle koma waye da Allah yake fada bada mu ba. Halifa ya rungumo Asiya yace yanzu ji nake kamar ke kadai na yarda da ke duk Duniya wallahi Asiya kowama zarginsa nake har Anty. Sai lokacin na yi magana. Ka yi hakuri insha Allah ba wani na jikinka insha Allah. Haka dai suka ci gaba da rainon ciki Halifa ya hana Asiya cin duk wani abu da ya fito daga hannun kowa, kuma ya kasa ya tsare da adduo'i Baffan ya basu ruwan addu a na neman tsari ya zama shine ruwan shanta. Duk inda zata Halifa ke kaita Asibiti kuwa sai ya jirata. Wani lokacin yace kar ta yi girki ya dauke ta su tafi gidan cin abinci. In gurin su Inna ne sai ya kaita in ya taso kasuwa ya jibgo tsaraba ya kai musu. Anty ta na cike da tashin hankali amma dole ta lafa tukunna tunda ta samu Halifa ya hakura da kiran Hukuma. Cikin bacci Asiya taji hayaniya; a tsakar gida amma sai bata fito ba, dan ta saba tunda bata zuwa Kallon fada. Kamar saukar aradu Asiya taji muryar Halifa a fusace, yace, Asiya!! Ta ta shi da sauri tana fadin lafiya? Yace Dan Allah malama ya kike yi kamar baki san komai ba!! Mamaki ya cika ta, ta sakko a gigice ta bi bayan sa zugwi,har tsakar gida. Wani matashi ta gani yasha duka yana durkushe jini na zuba. Ga su Anty da su Hafsa harda da wasu maza wadanda ta ke tunanin cewa maƙota ne... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [7/29, 21:25] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Ga zaton ta barawo aka kama, ta dubi Halifa ta ce a ina ya yi sata? Kafin Halifa ya bata amsa sai taji barawo na cewa Dan Allah ku yi hakuri wallahi sai da nace wa Asi baby kawai ta zo inda muka saba haduwa gidan abokina wanda ya rabu da matarsa can take zuwa idan Halifa ya tafi kasuwa, to da yake ina zuwa wasu lokutan a nan idan ya fita yauma wallahi na musa amma tace yanayin jikinta ya sa ta kasa...... Halifa ya sa kafa ya tokari cikin sa, sai da ya yi kara sannan jini ta hanci ta baki aka rike Halifa yana fizgewa akan cewa a sake shi sai ya kashe shi. Sai lokacin Asiya ta fahimci sharrin da aka yi mata ta daga ido ta kalli Anty sai ta saki wani murmushi irin na takaici. Tace tanan aka sake bullo min? Ta je gaban mutumin ta kalle shi. Ina son ka fadi tsakanin ka da Allah ka taba ganina? Ya fashe da kuka tare da fadin Asiya kalli ki gani kefa ki ka ce inzo gidan ki ke kika ce mijin ya tafi kasuwa amma shine kike alaye kamar baki san komai ba. Zufa ta karyo wa Asiya lallai sun tsara abin su. Ta kalli Halifa Dan Allah Yaya kar ka yarda da shi wallahi ban san shiba. Anty tace amma wannan yazo gidan nan ba so daya ba akwai ranar da na ta tambaye shi ya ce min yayanku ne, to amma ganin yadda in ya fito yake sanda shiyasa na kasa yarda da shi. Halifa wanda takaici ya hana shi magana ya fidda hannu ya wanka wa Asiya mari yace kinsan tin yaushe nake a gidan nan tun ina fita kasuwa Anty ta kira ni tace ga wani ya zo tana ganin shi yana yawan zuwa, har nace kila Dan Uwa ku ne sai kuma na kasa nutsuwa kasancewar yadda mata suka koma a wanna zamanin. Nayi awa daya ina jiran fitowar shi sannan ya fito daga dakin mu dakin auren mu Asiya yana gyara wando ya dakko takalmanshi a inda ya boye ya saka ina Kallon shi ba zan iya barin shi ya fita ba, ni ne nayi masa wannan dukan. Sai Halifa ya fashe da kuka. Asiya cikin firgici da tashin hankali, ta kama hannun shi tace "Yaya kar ka yarda wallahi wannan shiryayyen al amari ne ka yi tunani sosai wallahi ni bacci nake ina kwance a dakina wannan hayaniyar ce ta farkar da ni. Halifa ya hankade ta da karfi ta fadi, yace ki daina taba ni hakikar ke abar kyamace,kin bani mamaki. Zafin maganganun Halifa sun fi mata zafin faduwar kuma ta tabbatar Allah ne kawai zai wanke ta. Sai lokacin ta soma kuka tana furta Allahumma ajirni fimusibati. Ta mike domin bata da sauran wani abu da zata fadawa mijin nata giyar kishi da bakin cikin abinda ya gani ke dibar sa, ta yi masa uzri a yanzu tasan lokacin yi nadamar hakan zai zo a gaba. Bazata yanke hukunci cikin fushi ba, amma tasan auren ta ya gama lalacewa. Ta mike da nufin ta tafi dakin ta ta saurari hukuncin Ubangiji sai taji ana ku rike shi ta bishi da kallo ya kama bishiya ya haye katanga ya dira ta baya wanda kafin a zagaya ta tabbata ya gudu. Ta zauna akan kujera ta fashe da sabon kuka. Tana fadin Allah yau kuma da wannan na wayi gari ya Allah! Allah ka kubutar dani kamar yadda ka kubutar da Annabi Yusuf daga khaidin mata. Allah ka wanke ni kamar yadda ka wanke Uwar muminai Nana Aisha daga sharrin masu sharri. Alwala ta yi da ta samu sanyi a zuciyar ta. Ina ma ace mafarki ne. A tsakar gida kuwa kwarto ya gudu Halifa yaji takaicin haka domin ya so yasa a daure masa shi. Ya shiga dakin a fusace Asiya wadda ta gama sarewa ta dube shi. Yace "Wai Asiya in tambaye ki, dame na rage ki har ki ke kula wannan kazamin daga gani ko sana'a bashi da ita. Ko bana iya gamsar da ke a shimfida ne? Asiya sai Kallon shi take ba shakka ya gama yarda cewa ta aikata laifin. Ta mike ta shiga daki ta gama amincewa auren su ya kare ta sauke akwati tana duba kayan da zata dauka a kayanta na gida dai kala daya ne wata doguwar rigar atamfa Dan haka ta ciro ta da wani hijabbinta na idin da akayi kafin auren su. Ya shigo dakin lokacin ta gama sakawa ta duba jakar ta ta dauki dan kudin ta wanda yakan bata. Ya ce ina zaki ko binshi za kiyi? Ta dube shi cikin wani yanayi wanda bazata iya fassara shi ba. Duk abinda aka yi ba sukai wannan kalmar da ya fada mata yin daci a zuciyar ta ba. Hawaye suka kwaranyo daga Idanuwanta. Cikin rawar murya tace "Ka yi duk zargin da zaka yi bazan hana ka ba. Gaskiyar ita ce, ban aikata komai ba, banda masaniya akan komai, sannan yanzu kuma gidan mu zanje. Zaki je ki tona wannan maganar ta yi ta yawo cikin mutane? Abinda ya sa ban samu ba koda wancan yaron ya gudu bana son in kai shi gaba maganar ta zama abin tattaunawa a satin nan, can kuma abin ya koma Soshiyal midiya. Asiya tace ni ba zan damu ba ko waye ma zaiji ya ji kuma ba zan hana shi yarda ba tunda kaima ka yarda. Kuskuren da nayi na dauka cewa zaka bani kariya a matsayin ka na mijina ashe nayi kuskure. Ta fito fallo ya biyota ban fa baki izinin fita ba. " Halifa bana bukatar izini domin aure da zargi basa haduwa." To kin fi son kije ki tada hankalin Inna gata da hawan jini? Asiya tace bari kaji Inna tafi kowa sani na, ko a mafarki bazata taba yarda da wannan wasan kwaikwayon ba. Ta kama kofa ta bude yace Cikina kar kije min dashi ko ina. Anty dake bakin kofa ta a she. Ta ce ta ina ya zama cikin ka, kana jin me cikin ya fada? Ka barta taje gida tunda tana gaddama cewar bata aikata ba sai ka bincika ka samu Tabbaci. Halifa bai ce kala ba har Asiya ta fice. Shima ya rufe dakin ya fice. A baya yake bin Napep din da ta hau har Unguwar su. Asiya ta shiga gida Inna tana kwance Abba yana girki Maman Annur taje gidan aiki. Inna ta tashi zaune tana fadin Asiya ce yau da wuri haka? Asiya tace inna ai ba zuwan dadi bane. Nan ta kwashe komai ta sanar da ita. Inna ta shiga salati da sallallami tace yau kuma da haka na wayi gari. Allah ka fidda wannan yarinyar sai kuma ta shiga lallashin Asiya tare da bata magana. Inna dai ta boye wa Asiya damuwar ta ne kawai amma fa ta shiga tashin hankali domin duk yadda Asiya take Kallon abin ya fi haka, ga shi su ba karfi ba ta yi imani Asiya bazata taba aikata abinda aka danganta ta dashi ba. Da dare Halifa yana ta kai kawo daga falo zuwa daki yana auna abin da ya faru wata zuciyar tace kai. me yasa baka zo ka shigo dakin ba a lokacin? Ya tuna yadda Anty ta rike shi tana karkaje kar ayi mugun abu, zaka yi mugun gani. To amma gashi yana kokwanto kodai sharri ne aka yi mata masu bata guba din nan. Ya kamata ya fahimci cewa lallai akwai wani abu. Ya fita zuwa sasan Anty tana waya da ƙawarta Wai ta kira tana cewa ta ga abinda ya faru a gidan an dora a tiktok. Anty tana cewa wallahi kuwa nima dazu Hafsa ke nuna min ko suwaye suka dauka suka dora ga shinan shi kwarton an masa duka ita kuma Asiya tana ta kuka, aiko ta sha zagi. Halifa yace Anty me aka dora a Tiktok? Matar tawa aka dora? Waye yake da tabbci ko shedar cewa zina ake aikatawa adakin? Waye ya yi musu kamu irin Na shari 'a? Anty ta juyo da sauri cike da mamaki ta kalli Halifa tana murna ta zare masa yarinyar daga zuciya yanzu Sai batun zubda ciki amma shine zai mata tsalle? Ta mike a fusace " Halifa idan har na isa da kai wallahi sai ka bar yarinyar nan. Wane irin asiri ta yi maka haka wallahi ko waye ya tsaya maka sai ka barta ba dai a zuri a taba. Halifa yace Anty gaskiyar magana ina son mata ta kuma zuciyata ta ki amincewa da cewar Asiya ta aikata wannan abin in halinta ne da ta yi kafin ta zo gidana amma yarinyar nan a budurwa na same ta, ni ne mutum na farko da na fara kusantar ta. Bazan manta hakan ba. Dan haka saina bincika sosai kuma duk wanda na gano da hannun shi a dauka ta a Video ya yada sai na yi shara a da shi. Ya Juya a fusace. Baki Anty ta saki ta bishi da kallo lallai wannan sai ta yi da gaske. Yana shiga daki ya dauki waya Sam bai damu da hawa Internet ba, amma sai ya kunna data da nufin duba Tiktok. Kiran Bros ne ya katse shi ya daga cikin sauri domin yana bukatar jin ta bakin wani. Cike da tashin hankali yace Uncle me yake faruwa ne dazu maman Nihal take nuna min Matar ka a Tiktok. " Ina zan same ka yanzu? Halifa ya tambaye shi cike da damuwa. Bros yace ina gida kuma kaga muna da tazara Amma mu hadu a zoo road yanzu." To Halifa ya furta ba tare da ya tsaya tunani ba. Jikin motar Halifa suka jingina inda Halifa ya zayyano wa Bros komai. Ya kara da cewa kasan menene Bros sam zuciyata ta ki aminta cewa yarinyar nan zata aikata abinda ya faru. Tana ta kawo min hujjoji masu karfi, Bros yace "To ina yarinyar yanzu? Tana gidan su. Halifa ya amsa tare da girgiza kai, ya furzar da huci, ya ci gaba da fadin ban so ta tafi ba, abinda ya bashi haushi ke nan na kyaleta ya kamata ta min uzri a lokacin domin abinda na gani ya isa hujja ko a gaban Alkali cewa ta yi laifin. Bros yace Uncle Baka da wata hujja da ka ke fadin ko a gaban Alkali ka yi mata kamun shara a ne. Ina son ka nutsu ka saurari zuciyar ka wadda ta ki amincewa da zargin da ake yi wa matar ka, kuma dorashi da akayi a Soshiyal midiya ya kamata kasan cewa akwai masu yakar ka da nufi aka yi Allah kuma shine ya san masu yin da kuma dalilin su na yi din. Halifa ya sauke ajiyar zuciya yace yanzu ka bani shawara menene abinda zanyi? Bros yace ka fara kare matar ka daga sharrin yan Soshiyal midiya dinnan Sannan ka sameta ka bata hakuri kuma ka tashi daga gidan nan ka koma gidan ka. Halifa yace tafiyar da ta yi bayan na hanata ya bata min rai sosai har yanzu ina jin haushin abin. Bros yace ka bari nan da sati daya kowa ya huce kai da ita sai kaje ka same ta ku sasanta. Da safe ya gama shirin fita ya dauki kayan sawar Asiya da wayarta ya je har kofar gidan ya ba wani yaro yace ya kai yace gashi a bawa Asiya. Tana kwance ta kasa karin kummalo ta rasa yadda zata yi tare damuwar ta. Bata San tana mugun son Halifa ba sai yanzu da auren su ke gargarar mutuwa. Ta tabbatar in har auren nan ya mutu ita ma mutuwa zata yi. Sai ga yaro da kaya niki niki wai inji Halifa. Ta kalli Inna hawaye suka zubo mata tace ya tabbata Haliifa ya gama yarda cewa na ci amanar sa. Inna cike da tausayawa yar ta cikin lallashi tace. "Bana zaton hakan yana nufin ya yarda muci gaba da addu’ar neman mafita ga Allah. Sallamar Sulaiman ce ta dakatar dani take na fara rokon Allah ya sa tare suka zo da Halifa. Na fito daga daki ina fadin sannu da zuwa yaya Sulaiman. Ko amsawa bai yi ba ya shiga tambayar Asiya wai kuwa me kika aikata na ganki a Tiktok? Gaban Asiya ya yanke ya yi wata muguwar faduwa, Wani sabon Sharrin ya sauka kenan, ta furta tana Kallon idon Sulaiman. Ya ce kalli kiga ni yadda abin ya yadu mutane sai sharhi suke yi suna kara yada abin. Asiya ta gama kallo gaba daya zuciyar ta tana bugawa da sauri, ta mika mishi Wayar ta koma ta zauna Sulaiman ya ci gaba da fadin wallahi nasan sharri ne sai dai na yi mamaki yadda Halifa ya yarda. Asiya tace dole ya yarda ta fada masa duk yadda abin ya faru da kuma yadda ta sani. Sulaiman ya yi ta mamaki tare da yi mata addu"a Allah ya fidda ita, sannan yace yanzu ya za ayi da mutanen Soshiyal midiya din nan? Yan jarida ma nasan in suka ji labari sai sun zo gidan nan yadda abin nan ya yadu kyau ki bar garin nan zuwa nan da kura ta lafa. Inna ta fito cikin mamaki tace "Abin har ya kai Haka? Gaskiya dai ina ganin ba sai taje wani guri ba, kawai dai baza ta fita ko ina ba." Sulaiman yace to shike nan Amma ina mai tabbatar miki cewar yanda kowa ya zama dan jarida yanzu ba sai ta fita ba, har gida zaki ga ana zuwa domin gani da kuma jin ta bakinta. Asiya tace inaga zan zauna a daki kawai. Sulaiman ya ce Allah ya kyauta ya fita. Maganar Sulaiman. ce ta ke neman tabbata, yayan makota suka. soma shigowa daga nan sai iyayen sai kuma ga wani gida radio wai sun zo jin ta bakin Asiya. Ta kulle kanta adaki. Dole Asiya tabi duhun magriba ta tafi gidan wata yar Uwar su a Kurna ta kwana washe gari ta yi asubanci hanyar Malumfashi dangin Innar su..... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [7/29, 21:25] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Ga zaton ta barawo aka kama, ta dubi Halifa ta ce a ina ya yi sata? Kafin Halifa ya bata amsa sai taji barawo na cewa Dan Allah ku yi hakuri wallahi sai da nace wa Asi baby kawai ta zo inda muka saba haduwa gidan abokina wanda ya rabu da matarsa can take zuwa idan Halifa ya tafi kasuwa, to da yake ina zuwa wasu lokutan a nan idan ya fita yauma wallahi na musa amma tace yanayin jikinta ya sa ta kasa...... Halifa ya sa kafa ya tokari cikin sa, sai da ya yi kara sannan jini ta hanci ta baki aka rike Halifa yana fizgewa akan cewa a sake shi sai ya kashe shi. Sai lokacin Asiya ta fahimci sharrin da aka yi mata ta daga ido ta kalli Anty sai ta saki wani murmushi irin na takaici. Tace tanan aka sake bullo min? Ta je gaban mutumin ta kalle shi. Ina son ka fadi tsakanin ka da Allah ka taba ganina? Ya fashe da kuka tare da fadin Asiya kalli ki gani kefa ki ka ce inzo gidan ki ke kika ce mijin ya tafi kasuwa amma shine kike alaye kamar baki san komai ba. Zufa ta karyo wa Asiya lallai sun tsara abin su. Ta kalli Halifa Dan Allah Yaya kar ka yarda da shi wallahi ban san shiba. Anty tace amma wannan yazo gidan nan ba so daya ba akwai ranar da na ta tambaye shi ya ce min yayanku ne, to amma ganin yadda in ya fito yake sanda shiyasa na kasa yarda da shi. Halifa wanda takaici ya hana shi magana ya fidda hannu ya wanka wa Asiya mari yace kinsan tin yaushe nake a gidan nan tun ina fita kasuwa Anty ta kira ni tace ga wani ya zo tana ganin shi yana yawan zuwa, har nace kila Dan Uwa ku ne sai kuma na kasa nutsuwa kasancewar yadda mata suka koma a wanna zamanin. Nayi awa daya ina jiran fitowar shi sannan ya fito daga dakin mu dakin auren mu Asiya yana gyara wando ya dakko takalmanshi a inda ya boye ya saka ina Kallon shi ba zan iya barin shi ya fita ba, ni ne nayi masa wannan dukan. Sai Halifa ya fashe da kuka. Asiya cikin firgici da tashin hankali, ta kama hannun shi tace "Yaya kar ka yarda wallahi wannan shiryayyen al amari ne ka yi tunani sosai wallahi ni bacci nake ina kwance a dakina wannan hayaniyar ce ta farkar da ni. Halifa ya hankade ta da karfi ta fadi, yace ki daina taba ni hakikar ke abar kyamace,kin bani mamaki. Zafin maganganun Halifa sun fi mata zafin faduwar kuma ta tabbatar Allah ne kawai zai wanke ta. Sai lokacin ta soma kuka tana furta Allahumma ajirni fimusibati. Ta mike domin bata da sauran wani abu da zata fadawa mijin nata giyar kishi da bakin cikin abinda ya gani ke dibar sa, ta yi masa uzri a yanzu tasan lokacin yi nadamar hakan zai zo a gaba. Bazata yanke hukunci cikin fushi ba, amma tasan auren ta ya gama lalacewa. Ta mike da nufin ta tafi dakin ta ta saurari hukuncin Ubangiji sai taji ana ku rike shi ta bishi da kallo ya kama bishiya ya haye katanga ya dira ta baya wanda kafin a zagaya ta tabbata ya gudu. Ta zauna akan kujera ta fashe da sabon kuka. Tana fadin Allah yau kuma da wannan na wayi gari ya Allah! Allah ka kubutar dani kamar yadda ka kubutar da Annabi Yusuf daga khaidin mata. Allah ka wanke ni kamar yadda ka wanke Uwar muminai Nana Aisha daga sharrin masu sharri. Alwala ta yi da ta samu sanyi a zuciyar ta. Ina ma ace mafarki ne. A tsakar gida kuwa kwarto ya gudu Halifa yaji takaicin haka domin ya so yasa a daure masa shi. Ya shiga dakin a fusace Asiya wadda ta gama sarewa ta dube shi. Yace "Wai Asiya in tambaye ki, dame na rage ki har ki ke kula wannan kazamin daga gani ko sana'a bashi da ita. Ko bana iya gamsar da ke a shimfida ne? Asiya sai Kallon shi take ba shakka ya gama yarda cewa ta aikata laifin. Ta mike ta shiga daki ta gama amincewa auren su ya kare ta sauke akwati tana duba kayan da zata dauka a kayanta na gida dai kala daya ne wata doguwar rigar atamfa Dan haka ta ciro ta da wani hijabbinta na idin da akayi kafin auren su. Ya shigo dakin lokacin ta gama sakawa ta duba jakar ta ta dauki dan kudin ta wanda yakan bata. Ya ce ina zaki ko binshi za kiyi? Ta dube shi cikin wani yanayi wanda bazata iya fassara shi ba. Duk abinda aka yi ba sukai wannan kalmar da ya fada mata yin daci a zuciyar ta ba. Hawaye suka kwaranyo daga Idanuwanta. Cikin rawar murya tace "Ka yi duk zargin da zaka yi bazan hana ka ba. Gaskiyar ita ce, ban aikata komai ba, banda masaniya akan komai, sannan yanzu kuma gidan mu zanje. Zaki je ki tona wannan maganar ta yi ta yawo cikin mutane? Abinda ya sa ban samu ba koda wancan yaron ya gudu bana son in kai shi gaba maganar ta zama abin tattaunawa a satin nan, can kuma abin ya koma Soshiyal midiya. Asiya tace ni ba zan damu ba ko waye ma zaiji ya ji kuma ba zan hana shi yarda ba tunda kaima ka yarda. Kuskuren da nayi na dauka cewa zaka bani kariya a matsayin ka na mijina ashe nayi kuskure. Ta fito fallo ya biyota ban fa baki izinin fita ba. " Halifa bana bukatar izini domin aure da zargi basa haduwa." To kin fi son kije ki tada hankalin Inna gata da hawan jini? Asiya tace bari kaji Inna tafi kowa sani na, ko a mafarki bazata taba yarda da wannan wasan kwaikwayon ba. Ta kama kofa ta bude yace Cikina kar kije min dashi ko ina. Anty dake bakin kofa ta a she. Ta ce ta ina ya zama cikin ka, kana jin me cikin ya fada? Ka barta taje gida tunda tana gaddama cewar bata aikata ba sai ka bincika ka samu Tabbaci. Halifa bai ce kala ba har Asiya ta fice. Shima ya rufe dakin ya fice. A baya yake bin Napep din da ta hau har Unguwar su. Asiya ta shiga gida Inna tana kwance Abba yana girki Maman Annur taje gidan aiki. Inna ta tashi zaune tana fadin Asiya ce yau da wuri haka? Asiya tace inna ai ba zuwan dadi bane. Nan ta kwashe komai ta sanar da ita. Inna ta shiga salati da sallallami tace yau kuma da haka na wayi gari. Allah ka fidda wannan yarinyar sai kuma ta shiga lallashin Asiya tare da bata magana. Inna dai ta boye wa Asiya damuwar ta ne kawai amma fa ta shiga tashin hankali domin duk yadda Asiya take Kallon abin ya fi haka, ga shi su ba karfi ba ta yi imani Asiya bazata taba aikata abinda aka danganta ta dashi ba. Da dare Halifa yana ta kai kawo daga falo zuwa daki yana auna abin da ya faru wata zuciyar tace kai. me yasa baka zo ka shigo dakin ba a lokacin? Ya tuna yadda Anty ta rike shi tana karkaje kar ayi mugun abu, zaka yi mugun gani. To amma gashi yana kokwanto kodai sharri ne aka yi mata masu bata guba din nan. Ya kamata ya fahimci cewa lallai akwai wani abu. Ya fita zuwa sasan Anty tana waya da ƙawarta Wai ta kira tana cewa ta ga abinda ya faru a gidan an dora a tiktok. Anty tana cewa wallahi kuwa nima dazu Hafsa ke nuna min ko suwaye suka dauka suka dora ga shinan shi kwarton an masa duka ita kuma Asiya tana ta kuka, aiko ta sha zagi. Halifa yace Anty me aka dora a Tiktok? Matar tawa aka dora? Waye yake da tabbci ko shedar cewa zina ake aikatawa adakin? Waye ya yi musu kamu irin Na shari 'a? Anty ta juyo da sauri cike da mamaki ta kalli Halifa tana murna ta zare masa yarinyar daga zuciya yanzu Sai batun zubda ciki amma shine zai mata tsalle? Ta mike a fusace " Halifa idan har na isa da kai wallahi sai ka bar yarinyar nan. Wane irin asiri ta yi maka haka wallahi ko waye ya tsaya maka sai ka barta ba dai a zuri a taba. Halifa yace Anty gaskiyar magana ina son mata ta kuma zuciyata ta ki amincewa da cewar Asiya ta aikata wannan abin in halinta ne da ta yi kafin ta zo gidana amma yarinyar nan a budurwa na same ta, ni ne mutum na farko da na fara kusantar ta. Bazan manta hakan ba. Dan haka saina bincika sosai kuma duk wanda na gano da hannun shi a dauka ta a Video ya yada sai na yi shara a da shi. Ya Juya a fusace. Baki Anty ta saki ta bishi da kallo lallai wannan sai ta yi da gaske. Yana shiga daki ya dauki waya Sam bai damu da hawa Internet ba, amma sai ya kunna data da nufin duba Tiktok. Kiran Bros ne ya katse shi ya daga cikin sauri domin yana bukatar jin ta bakin wani. Cike da tashin hankali yace Uncle me yake faruwa ne dazu maman Nihal take nuna min Matar ka a Tiktok. " Ina zan same ka yanzu? Halifa ya tambaye shi cike da damuwa. Bros yace ina gida kuma kaga muna da tazara Amma mu hadu a zoo road yanzu." To Halifa ya furta ba tare da ya tsaya tunani ba. Jikin motar Halifa suka jingina inda Halifa ya zayyano wa Bros komai. Ya kara da cewa kasan menene Bros sam zuciyata ta ki aminta cewa yarinyar nan zata aikata abinda ya faru. Tana ta kawo min hujjoji masu karfi, Bros yace "To ina yarinyar yanzu? Tana gidan su. Halifa ya amsa tare da girgiza kai, ya furzar da huci, ya ci gaba da fadin ban so ta tafi ba, abinda ya bashi haushi ke nan na kyaleta ya kamata ta min uzri a lokacin domin abinda na gani ya isa hujja ko a gaban Alkali cewa ta yi laifin. Bros yace Uncle Baka da wata hujja da ka ke fadin ko a gaban Alkali ka yi mata kamun shara a ne. Ina son ka nutsu ka saurari zuciyar ka wadda ta ki amincewa da zargin da ake yi wa matar ka, kuma dorashi da akayi a Soshiyal midiya ya kamata kasan cewa akwai masu yakar ka da nufi aka yi Allah kuma shine ya san masu yin da kuma dalilin su na yi din. Halifa ya sauke ajiyar zuciya yace yanzu ka bani shawara menene abinda zanyi? Bros yace ka fara kare matar ka daga sharrin yan Soshiyal midiya dinnan Sannan ka sameta ka bata hakuri kuma ka tashi daga gidan nan ka koma gidan ka. Halifa yace tafiyar da ta yi bayan na hanata ya bata min rai sosai har yanzu ina jin haushin abin. Bros yace ka bari nan da sati daya kowa ya huce kai da ita sai kaje ka same ta ku sasanta. Da safe ya gama shirin fita ya dauki kayan sawar Asiya da wayarta ya je har kofar gidan ya ba wani yaro yace ya kai yace gashi a bawa Asiya. Tana kwance ta kasa karin kummalo ta rasa yadda zata yi tare damuwar ta. Bata San tana mugun son Halifa ba sai yanzu da auren su ke gargarar mutuwa. Ta tabbatar in har auren nan ya mutu ita ma mutuwa zata yi. Sai ga yaro da kaya niki niki wai inji Halifa. Ta kalli Inna hawaye suka zubo mata tace ya tabbata Haliifa ya gama yarda cewa na ci amanar sa. Inna cike da tausayawa yar ta cikin lallashi tace. "Bana zaton hakan yana nufin ya yarda muci gaba da addu’ar neman mafita ga Allah. Sallamar Sulaiman ce ta dakatar dani take na fara rokon Allah ya sa tare suka zo da Halifa. Na fito daga daki ina fadin sannu da zuwa yaya Sulaiman. Ko amsawa bai yi ba ya shiga tambayar Asiya wai kuwa me kika aikata na ganki a Tiktok? Gaban Asiya ya yanke ya yi wata muguwar faduwa, Wani sabon Sharrin ya sauka kenan, ta furta tana Kallon idon Sulaiman. Ya ce kalli kiga ni yadda abin ya yadu mutane sai sharhi suke yi suna kara yada abin. Asiya ta gama kallo gaba daya zuciyar ta tana bugawa da sauri, ta mika mishi Wayar ta koma ta zauna Sulaiman ya ci gaba da fadin wallahi nasan sharri ne sai dai na yi mamaki yadda Halifa ya yarda. Asiya tace dole ya yarda ta fada masa duk yadda abin ya faru da kuma yadda ta sani. Sulaiman ya yi ta mamaki tare da yi mata addu"a Allah ya fidda ita, sannan yace yanzu ya za ayi da mutanen Soshiyal midiya din nan? Yan jarida ma nasan in suka ji labari sai sun zo gidan nan yadda abin nan ya yadu kyau ki bar garin nan zuwa nan da kura ta lafa. Inna ta fito cikin mamaki tace "Abin har ya kai Haka? Gaskiya dai ina ganin ba sai taje wani guri ba, kawai dai baza ta fita ko ina ba." Sulaiman yace to shike nan Amma ina mai tabbatar miki cewar yanda kowa ya zama dan jarida yanzu ba sai ta fita ba, har gida zaki ga ana zuwa domin gani da kuma jin ta bakinta. Asiya tace inaga zan zauna a daki kawai. Sulaiman ya ce Allah ya kyauta ya fita. Maganar Sulaiman. ce ta ke neman tabbata, yayan makota suka. soma shigowa daga nan sai iyayen sai kuma ga wani gida radio wai sun zo jin ta bakin Asiya. Ta kulle kanta adaki. Dole Asiya tabi duhun magriba ta tafi gidan wata yar Uwar su a Kurna ta kwana washe gari ta yi asubanci hanyar Malumfashi dangin Innar su..... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [8/6, 20:53] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Kwatsam Baba Tabawa ta ga Asiya Baba Tabawa Kanwar mahaifiyar Innar su Asiya ce, itace autar su. Itace ta rike Inna har ta yi aure. Ta jima a Kano lokacin rasuwa da bikin Asiya. Taji mamakin ganin Asiya afujajan ta tabbatar ba lafiya ba. Asiya kam bata fada mata komai ba, sai kuka data ishe ta da shi har zuwa washegari da Inna ta iso ita ta sanar da Baba tabawa komai, ta zowa da Asiya kayanta da wayar ta. Tana hawa Tiktok ta ga har yanzu video dinsu ke tashe dan har wasu sun kafe hoton ta sun hada wata murya tana kuka tana fadin ta yi nadamar yin soyayya da wani bayan ga mijina Asiya ta saka kuka wannan wane irin sharri ne me ta yi wa wani har haka. Ta kashe wayar ta maida ita can kasan kayanta. Washegari sai Inna ta hada yan komaatsanta ta koma Kano. Halifa bai san illar yada wannan Video ba sai da yaga yan jarida sun same shi har shagon sa a kasuwa wai suna son su samu labari game da abinda ya faru ga abokai da yan kasuwar su zancen yana ta yawo. Har ya soma tunanin kowa ma shi yake kallo ana ta nuna shi, Hakan ya tilasta masa zaman gida. Bros ya same shi kwance a sabon gidan shi kamar yadda suka yi zai same shi. Yace Bros Ina ganin zan Dan motsa ko zan samu nutsuwa. Bros ya dube shi zaka motsa zuwa ina? " Ya tambayi Halifa cike da mamaki domin ya san shi mutum ne mai nacin gida. Zan tafi China gurin harkokin kasuwanci na, daga can in wuce Saudiyya inyi Umra, zan dawo lokacin abubuwa sun lafa, ina son ka zama shaida bana zargin Asiya kuma aurena yana nan dana ne a cikin ta., ya zama dole ne in bata rata komai ya lafa ita ma ta huce tukunna. Bros yace to amma ko zaka bata rata kar ka wofintar da ita, ka kira ta ka sanar mata cewa za ka yi tafiya dan kar ta dauka cewa kaima kana zarginta. Halifa ya numfasa, Na kira wayarta tun jiya amma a kashe kuma ta tafi gida bayan na hana ta fita kawai sai naga kamar ta soma raina ni, dole ina bukatar uzri ya yin da naga kato ya fito daga dakina. I zuwa yanzu wallahi na gane akwai mai bina da sharri kuma zan kai karansa gurin Allah in naje Umra din nan. .. Ya sani ina ta zargin kowa. Bros yace To nidai addu a zan taya ka Allah ya bayyana maka gaskiya ka ganta da idon ka, amma ko waye zai zama na kusa da Kai ne wanda baza ka taba kawo shi ba. Halifa ya numfasa sannan yace Allah ya fishi. Sai ranar da zai tafi Abuja dan ta can zai tashi sannan ya sanar da Anty ta yi mamaki sosai wai yau Halifa ne ya ke boye mata abubuwa, sannan ta kasa fahimtar me yake nufi da matar sa da bai sake ta ba. Tace "Wai Halifa naga duk ka canza min tun da wannan masifun suke faruwa kai ni wannan auran ma gara dai ya kare kaima ka huta." Yace Anty Asiya fa har yanzu matata ce, Na yi tambaya cikin ta nawa ne ko da ta aikata abinda ake zarginta da shi shari'a ta bani ɗan balle zuciya ta taki sam ta amince cewa ta aikata laifin, kuma dorawa da akayi a shoshiyal midiya shine ya sa na gane cewa tabbas wanda ya so ya hanani haihuwa ta hanyar saka mata abin tsarin iyali shine dai ya bata guba dan ta mutu kar in haihu kuma dai shine ya shigar min daki dan ya yi mata sharri zanje na roko Allah ya nuna min wannan babban makiyin nawa ko da a mafarki ne. Anty ta girgiza da jin kalaman bakin Halifa kamar ya ganeta kuma kamar bai gane ba. Sai ta wayance da fadin "Gaskiya Allah dai ya sa mu gano ko waye in har ta tabbata abinda ka ke zargi haka to kuwa sai na yi shari' a da ko waye. Halifa yace Anty kar ki daga hankali Allah baya zalinci za ayi walkiya abinda ke boye zai bayyana. Anty ta sake zare ido kamar fa ya gane. Halifa dai ya koma ya ci gaba da shirin sa. Yaje har gidan su Asiya ya samu Inna bata nan haka ma Asiya. Maman Annur ta je aikin gidan aikin ta, sai Abba ya fada masa Inna tana kauye. Ya bashi sako cewa Asiya ta kunna wayar ta, kuma ya fada mata ya yi tafiya. Bilkisu ta yi farin ciki da ganin Videon su Halifa kuma tana cikin wadanda suka kara yada abin da yin sharhi sannan tana ganin wannan. wata dama ce da zata samu shiga dan tasan kowane namiji dole ya saki wannan matar. Ita kuma lokacin ta zai fara. Saidai duk kira da sakon jaje da ta ke yi Halifa bai daga ba kuma bai nuna mata cewar ya ga sakonta ba. Dan haka ta soma fadada tunanin ta dan samu dama ta biyu. A kauye Asiya ta kasa ci bare sha ga laulayi ga damuwa haka Baba Tabawa ta yi ta kokari gurin tausarta da kuma sama mata yan jike jike na gargajiya. Ta san zata iya jin saukin jikinta amma bazata iya jin saukin mugun raunin dake zuciyarta na soyayyar Halifa ba.. Sai a yanzu ta sake tabbatar da tana yi masa wani mugun so kuma makaho domin ta daina hango laifin sa a duk wadannan matsalolin ta fara dora alhakin a kanta, me yasa bata rufe dakinta taba har sai an kwankwasa kafin a shiga? Me yasa da Halifa yace karta tafi ta ki sauraron shi. Gaskiya ita kam in har taji sauki zata koma gurin mijin ta wanda take bacci a kafadarsa wanda yake fada mata dadadan kalamai a kowane lokaci wanda ya maida ita macen da zata iya gogayya da kowace mace. Halifa tun da ya sauka a ma sauki ya kasa aiwatar da komai har kusan kwana uku sannan ya fita kasuwa dan duba kayan da zai siya, ko yawan magana baya so abinci kuwa sai mara nauyi, bai sami nutsuwa ba sai da ya dira a Madina Ya yi ta gwada lambar Asiya har yau dai babu labari. Anty ta kira Hajiya Talatu domin tattauna batun su Halifa, duk da tana ganin ta gama da Talatu amma tana zaton zata yi mata wani amfani. Cike da mamaki Talatu ta daga a tsorace ta amsa dan yanzu tana dan shakkar Anty. Kamar babu abinda ya faru Anty ta soma fadin "Sahiba kin dai yarda ni, tun daga biki na rasa me na miki tunda ni na damu da ke sai nace bari ni in kira. Talatu tace" Sahiba haka ma zaki fada ni da kika yi barazanar halaka ni. Anty ta saka dariya cike da makirci tace Ai ranar na tabbatar cewa ke matsoraciya ce wasa fa na miki haba Sahiba karfin jarumtarki na jarraba, in na barki kuma in kama wa? Talatu tace Humm ina jin ki, fadi abinda kike son fadi nasan amfani na ne ya tashi da kin gama sai ki yasar da ni. Anty tace To kin yi min mummunan zato da ba haka bane. Yanzu dai ina son ki saurareni ina ganin lokacin auren Ma u da Halifa ne ya yi nasan dai shine matsalar ki, Anty ta ci gaba da fadin nasan kinga abinda yake yawo a Tiktok na Halifa.? "Mun gani inji Talatu sai dai ko kaffara bazan yi ba Idan na rantse da cewa sharrin ki ne. Anty tace " Banyi mamaki ba dan kin gane, domin a sharri ke uwata ce yanzu dai ina son ki bani haske game da yadda zan fidda yarinyar nan daga Rayuwar Halifa, Na fahimci asirin baya cin su makircin yafi aiki, dubi wannan fa cikin yan mintuna na yi tunanin sharrin nan kafin awa shida har Duniya ta dauka. Talatu ta katse Anty da fadin "Yanzu dai menene muradin ki? Tace Shawara nake son muyi dake game da yadda za a barar da cikin tunda na yi kokarin kar a same shi, amma sai da ya samu, Na sake yin abinda za a zubdashi har wa yau suka rayu to yanzu tunda na yi nasarar rabata da gidan sai dai hankali na ya tashi da naji Halifa yana fadin matar shi ce kuma dansa ne. Hajiya Talatu tace "Kuma muka ji ance ya sake ta ya kuma koreta da muka kalla a Tiktok da Ma u ta kamo gurin? " Anty tace Yan karawa miya gishiri ne mu ai mune muka sa a Tiktok din ba wani ba, sauran mutane suka ci gaba da ingiza mai kantu ruwa kuma sai hakan ya kara armasa abin da zama ya gagare shi yanzu haka zancan da nake miki yana can chaina sai kura ta lafa zai dawo. Hajiya Talatu tace har na hango abinda zai faru tunda baya nan amma ni menene ladana idan na tsara miki yadda komai zai kasance?" Anty tace A daura mishi aure da Ma'u shine kawai, sai mu hada kai da ita mu sa mu biyan bukatar mu. Hajiya Talatu ta saki dariya tare da fadin na yarda da wannan Dan haka yanzu zan shirya in bar Zariya in nufo Kano kinsan ance shirin zaune ya fi na tsaye zamu tsara yadda za a sace ta a zubar da cikin Ko mu sake danna mata wani sharrin da zai kaita gidan Yari. Anty tace ina fatan ki Iso lafiya Sahiba ta. Hajiya Talatu ta saki dariya bayan ta kashe wayar tace lokaci ya yi da zan rama wukancin da aka yi min...... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [8/13, 17:12] Ummi Tandama😇: Anty ta kalli Hajiya talatu cike da mamaki tace Wallahi Sahiba nasan kin iya shirya tuggu amma ban yi tsammanin har haka ba, yanzun nan sai da kika lissafa min kala daidai har a shirin wanda duk wanda na dauka a ciki sai na yi nasara. Cikin alfahari Hajiya Talatu tace "Ai Sahiba in kika ga na bar mutum ni na so, mutum nawa ke gidan yari wanda na yi silar zuwan su.? Kinsan Allah abinda kika min kwanaki wallahi wani abu na duba daban kawai na kyale ki, mutuncin da kika min a farkon haduwar mu bana manta alkairi ko yaya yake,amma wallahi da badan haka ba, da sai na shirya miki abinda dangin ki ma sai sun tsane ki. Anty ta yi yar dariyar yake tace Sahiba kenan ai nima kawai dan na duba din ne amma wallahi danabi ta Malamin nan tuni zai batar da ke. Talatu ta saki dariya, tace "Ke matsalar ki tana da yawa wallahi. da kina duba mutunci bazaki sako dan kanin ki a gaba haka ba, duk abinda yake miki bakya gani kawai dai ki yarda ke muguwa ce ko ta ina." Anty tace naji yanzu dai mu koma kan maganar mu dan Allah na baki wuka da nama. Hajiya Talatu ta ja tsaki tare da fadin." Wai ba iya cikin kike son a zubar ba? " Anty ta amshe da faɗin Sai sakinta da nake son Halifa ya yi, wallahi da Adamu ne da tuni na sa shi ya sake ta, amma Halifa yana da taurin kai da muguwar zuciya, abinda ke bani haushi ya kasa kwada zuciyar akan yarinyar nan Sam. yanzu ma fa saboda damuwar ta ya bar gari ko kasar ma zan ce so nake kafin ya dawo na kammala ko mai sai kawai ya yi sabon Aure. Hajiya Talatu tace "Da Ma u na ba, "karamin alhaki ne wannan case din kawai zuwa zamuyi gidan nasu mu dauke ta zuwa Asibiti a kwakule abin banza a watsar mu maida ta mu dire. " Anty ta ce to wane Asibitin zamu kaita kinsan dai babu wani Asibitin da za su yarda su cire mana ciki haka siddan ko? Hajiya Talatu ta yi wa Anty wani irin kallon raini Sannan ta ja tsaki, tace." Karki fada min cewa baki da daurin gindi a garin nan? Kina nufin baki da likitoci kamar uku da zaki iya kira su miki abinda kike so nan take? Baki da Yan sanda kamar biyar da zaki kira su a take ayi miki yadda kike so? Baki da lauyoyi da alkalai a hannun ki? Ke har faraskiton kotu da gandiroba San ina da su sunfi guda nawa. Ke yan daba ma ina da su saboda tsaro. Kuma duk wadannan Umarni kawai zan basu. Ta sake jan tsaki gaskiya naji kunyar hada hanya dake ashe ke gaba daya ma gwara kifin rijiya dake. " Anty cike da muzanta tace Nifa bana rigima da kowa harda zan damu saina hada wannan gayyar ina zube musu kudi na. ke kuwa ai yar harkallace ko yaushe kin ari kudin wane kin cinye na wance. Hajiya Talatu tace" To yanzu wannan da zakiyi ya ci uwar harkalla, tunda kisan kai ki ke son a yi kuma Kaninki da ya yarda dake, ni kuma kinga ko wanda muke Uba daya bazan iya cuta ba bare cikin Ummana. Ta sauke numfashi. Kinga da kina da likita minti biyar ya yi yawa za a watsar da shi yabi sokawe. " Anty tace Menene abin yi dai yanzu? Hajiya Talatu tace yanzu muje yan magani mu sayi na zubda ciki muje gidan mu dauke ta mu kaita wani guri mu bata, ko kuma mu bata ma a gidan na su, in kuma zamu ja abin ya yi tsawo ka wai sai mu saka wani ya bata. Saboda karma a gane mu ne, amma fa zamu zama cikin zullumin na rashin tabbas. " Anty tace Allah na tuba tunda ba wasu masu hali bane Uwar ma kamar wata sakarya a gaban ta ma sai mu bata. Haka dai suka gama kulle kullen su suka tashi. Inna tana wanki na wankau da aka kawo mata, sai taji an doko sallama. a murya bibbiyu ta amsa tare da daga kai ta kalli su Anty duk da gabnata ya fadi amma sai ta dukar da kai ta ci gaba da wankinta bayan ta amsa sallamar a zuciyatar ta ci gaba da adduo'in neman tsarin Allah daga sharri su. Anty tace Ko da kika kallemu kika watsar muma ba zama muka zo ba, ina yar iskar yarki mai bin maza gurinta muka zo za ayi gwajin kwayar halitta dan musani ko cikin ba jinin mu bane. Inna bata tanka ba Hajiya Talatu ta fusata, tace "Ke baiwar Allah dake muke magana, kamar ke matsiyaciya har kin isa muna magana ki yi mana banza? Inna ta sake dago kai ta dube su tace, Wai me yasa Mutane suke hana kansu sukuni saboda son zuciya kuma su hana wani? Anty ta ce ba gurin ki muka zo ba, mun zo ne gurin yar iskar yar ki ta zo muje a yi gwaji dan mu rarrabe domin bazamu dauki dan wani a matsayin dan mu ba, yawwa. Inna tace ikon Allah to bari in fada muku babu inda Asiya zata kuma ciki dole ku karba duk sharri da tuggu da kike shirya wa yarinyar nan da wani kaita gidan boka ko ki bata guba duk na banza ne domin zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai ya yi ina son ki sani tsakanin dan Asiya da Halifa sai yazo Duniya kuma sai ya gaji abinda ki ke kwadayin mallakewa.!!! Kuma kina raye zaki ga haka!!! Ke!!! Anty ta daka mata tsawa. Taci gaba da fadin Ina son ki iya bakin ki ki kama kanki banda dalili ke kin isa ki fada min magana? Yar wanke wanke na tafi ki komai banza talaka matsiyaciya. Ga ki matsiyaciya kina gorin arziki jahila baki san cewa wanda yake rabon arzikin shine Ubangijin talaka ba, kuma hakan ba yana nufin ya manta dashi bane. Kije ki nemi ilmi. kuma ku fitar min a gida ta dauki ruwan dauda na wa kin data tsoma tsumman share ruwa ta nufi kansu da shi tana fadin babu wanda bai iya tijara ba sai in bai so ba!!! Ta sheka musu a jiki ta nufi ruwan zafi dake kan wuta tana dumamen tuwo,. Tace sai in kona ku ku kukazo har gida. Da sauri suka yi baya sai dai tuni Inna ta wanke su da ruwan datti kuma tana fadin Auzu billahi minnashaidanirrajim. Hajiya Talatu mamakin Inna ya cika ta, wai dama tana magana? Gashi ta wanke su da ruwan dattin ta kuma wawuro na kan murhu da gudu suka fita Anty tana sai na sa yan sanda sun rufe min ke.!! Inna tace na isa dauri muguwar mace wadda ke zalintar Dan Uwan ta to haka bakin ciki zai kashe ki insha Allah mutu ka raba Halifa da Asiya. Lamarin nan ya bataran Anty sosai ba a taba ci mata zarafi kamar haka ba tunda Uwar ta ta haife ta. Har suka kai gida bata ce komai ba tana saka abinda zata sa a yi wa Innar su Asiya ne kawai dan ta gane tazarar da ke tsakanin mai arziki da matsiyaci. Hajiya Talatu tace Ga abinda nake fada miki, yanzu in kina da yan sanda saidai ki bada Adireshi aje kawai a aje miki ita sai jibi zakije sai a lokacin zaki fadi abinda kike son a yi miki da ita. Idan nice fa wallahi matar nan sai taje gidan yari ko na kwana daya ne. Anty tace ko yanzu bazan barta haka ba. Bari mu canza kaya muje ofishin yan sanda. Suna zuwa Anty zata soma bayani ga dansanda dake kan teburin Hajiya Talatu ta jata gefe tace ke in kika biyo ta haka fa mune bamu da gaskiya tunda mu muka je gidan ta. Harkar girma kawai za ayi kinzo da kudi dai ko? Anty tace "A a sai dai ki Ara min." Hajiya Talatu taje muje ki ciro baza a rasa gurin POS a nan kusa ba, bani da kudin da zan aramiki ba biyana kike yi ba. Anty tace Au harda gori kuma har nawa zan ciro? Hajiya Talatu tace dubu Hamshin shima maleji za ayi dan na sanki da shegen son kudi bazaki iya fidda dari ba. Anty ta danyi shiru can tace "Ko dai share matar nan zanyi kawai in samu mu gama da yar tata? " Hajiya Talatu tace ai kinji matsalar ki duk da munyi wanka har yanzu ina jin tashin warin ruwan dattin talaucin da matar nan ta watsa mana kuma daga yau raini ya shiga tsakanin ku. Dan taci bulus Anty ta fusata ta fita zuwa zuwa POS. Tun a can Hajiya Talatu ta amshe kudin tare da fadin kawo ki gani ba a shiga irin gurin nan da kudi ttsirara. Suna komawa Hajiya Talatu tace D. P. O. yana ciki? Suka ce bai shigo ba,. Tace D. C. O fa suka ce yana hanya. Tace to ina son a dakko min wata ne a Fage ta ci mana zarafi daga kawai kaninmu yana auren Yarta, sai aka kama ta da wani shine mukaje gidan dan taje ayi gwajin Kwan halitta tunda tana dauke da ciki shima ta watsa mana ruwan dauda tare da zazzagi mu. Ta sa hannu a jaka ta tsakuro kudin ta mika shi gashi ku sha mai ku kawo mana ita nan sai gobe zamu dawo. Jiki na bari Shugaban su na gurin yace maza a dakko mota ta sake kawo dubu daidai ta ba yan gurin Shugaban kuma dubu biyar tace ku sha ruwa a hanya. Nan fa suka dauki mata biyu da maza da direban suka ce muje ina kuka aje motar ku? Hajiya Talatu da Anty suka kalli juna. Hajiya Talatu tace ai bamu zo da mota ba, me adaidaita ne gashi can motarmu mun aiki direba bai dawo ba. Dansandan yace Ku shige gaba muje ku nuna mana gidan sai ku tafi abinku. A cikin adaidaita Hajiya Talatu tace "Kawata wallahi yau naji kunya da Dansandan nan ya yi maganar mota ya kamata ace kina da mota taki ba wai ta Dady ko ta Halifa ko Adamu ba, sai zaki Je Unguwar sirri kina hawa adaidata sahu. Kin girmi haka wallahi ke ba tsohuwa ba amma baki jan mota da kanki. Yanda mata suke baza kafasitin nan da hawa manyan motoci suje Dubai da Umara akai akai, gaskiya Sahiba akwai bukatar yiwa rayuwar ki gyaranbawul. Anty ta sauke ajiyar zuciya tace kibari dai komai ya daidaita zaki sha mamaki yanzu ina sauran kudin ko duka kika ba su? Hajiya Talatu ta zage jakar ta tura sauran kudin a karamin zif sannan tace, "Har dubu ta da dari biyar ta shiga, kece bakuwar ba Yansanda kudi.... . [8/20, 22:26] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Suka aje mota a kofar gidan Inna suka tsai tsaya tare da tura matan ciki dan su kamo matar gidan. Sulaiman sun fito gidan su shi da Abban su zai tafi shago Abba za shi Unguwa sai kawai suka ga Yansanda a kofar gidan su Asiya. Abba da Sulaiman suka kalli juna dan neman karin bayani, amma kuma babu wanda ya san komai. Abba ya taka kofar gidan cike da al ajabi dan jin karin bayani daidai lokacin da Matan yansanda suka fito suna cewa matar gidan tana salla sai sun jira kadan. Sulaiman ya tako zuwa gurin wani matashi kamar sa a cikin yansanda yana tambayar sa ko lafiya? Ya kalli Sulaiman "Kai dan gidan ne? Kafin ya bashi amsa ya ji wanda Abban su ya tambaya yana cewa " Matar gidan zamu tafi da ita. Da sauri Sulaiman ya matsa kusa da su daidai lokacin da Abba yake cewa ina zaton dai kunyi kuskure ba matar gidan nan bace, domin babu wata matsala da zata saka har a dakko mata ku. Dansanda ya fusata bangane me kake nufi ba, kana son kace bamu San aikin mu ba? To tare da masu korafin muka zo suka nuna mana gidan suka wuce ka ga kuwa babu maganar kuskure. " Ina suke masu korafi? Abba ya katse shi. Malam Dan Allah ka tafi abinka ko ka jira in anje can ka bi kaji komai. Sulaiman ya tsoma baki da cewa babu inda zaku tafi da ita domin dai babu wani laifi da Inna zata yi wa wani. Sai ka hana inji wani ɗan sandan dake gefen sa dan baki kerere lebensa ya farfashe saboda shan taba. Ina takardar shedar kamun ta domin dai ku ba yansandan nan Unguwar bane. Abba ya furta yana Kallon babban su wanda ya ke kada kai cikin isa. Malam a Najeriya fa muke inba manyan mutane ba waye ake zuwa kamashi da waranti? Matar nan sai taje tunda ta ci zarafin Hajiya kawai dan tazo akan maganar auren kaninta bayan yarinyar ma an kamata da wani!! Abba ya ja tsaki tare da fadin Koma menene dai sai naga takardar shedar kamunta sannan zaku kamata. Wanda baisan kanshi ba shine ake zuwa a diba kara zube,ko da muke a Najeriya ba kowa bane lalatacce wanda bai san doka ba. Sulaiman wanda ya gano daga inda maganar ta taso ya shiga kiran layin Halifa yau dai kam ko shiga bata yi, ba kamar kwanaki ba da tana shiga amma ya ki dauka, har Sulaiman ya fusata ya daina kira, Kenan ma ya yi Blocking dina Sulaiman ya raya a ransa Takaici ya kama Sulaiman ya sa kai ya shiga gidan daidai da komawar matan yan sanda viki. . Suka ce mama munzo zamu tafi da ke office din mu. Sulaiman yace babu inda Inna zata je. Abba ya kira makotan su a waya ya sanar da su, wadanda ke kusa duk suka zo harda me Unguwar su. Take ya kira D. P. O na nan Unguwar ya tambaye shi cewa yarana ne suka zo kama matar marigayi makocin su. Take ya bincika ya Tabbatar cewa ba daga gurin su bane. Nan fa aka ce babu inda Inna zata dan ba su da hurumin kamata daga wata Unguwa ko daga sama ne sai an biyo ta kan yansanda Unguwa. Mutane suka cika matasa suka soma hayaniya tsageru suka soma jifan yansanda wanda haka ya tilasta musu fesa tiyagas sannan suka dauki motar su suka tafi. Inna wadda har ta saka hijabi tana cewa aje duk inda za a ta zauna tana kuka tana baiwa Babar su Sulaiman labarin abinda ya faru. Makota suka yi ta shigowa suna jajantawa Inna. Abban Su Sulaiman ya gama sauraron Inna yace ko sun dawo kar kije zalunci ne kawai irin na masu kudi, zan kira kawun shi wanda shine waliyinsa tunda abokina ne dan inji duk da sanin su ake ta wannan bada kalar, ke baki sanar dani me ake ciki ba, yanzu haka ma shi din bai san komai akai ba. Inna tace " Ba mamaki in bai sani din ba, amma abin ya bi gari ana ta cecekuce jiya zuwa yaune abin ya lafa." Yace Allah ya kyauta. Tayi masa godiya suka yi sallama. Anty ta zata Inna na kulle dan haka washe garin ma sai yamma sukaje ofishin yansanda sai dai wadanda suka samu jiya ba su ne yau a gurin ba, Hajiya Talatu tace ai ba matsala tunda dai mun san tana tsare bari mu nemi ganin D. P..O. Bayan sun gaisa suka sanar masa cewa sune mutanen da suka yi rigima da wata mata ta kwana a nan. D. P. O yace bai San zan can ba, daga ina ne aka kawo ta? Suka ce daga Fagge Yace " Gaskiya bamu da hurumin yi muku case a nan kuje can Fagen ku yi case din a can. Daya sa aka bincika sai ya gano yan Unguwar sun hana a kamo matar. Yace to dama dai ba hurumin mu bane kuje Fagen. Anty Wadda takaici ya hana magana har sai da suka zauna a Kekenapep ta ja tsaki ta ce Gaba daya kinsa na yi asarar dubu hamshin dina gashi babu wata nasara da aka samu shikenan matar nan ta ci galaba a kaina! Hajiya Talatu cikin sigar wanke kanta daga zargin Anty tace "Ko kadan kar kiga laifina. Ke kika kaimu na Unguwar ku kuma ko yanzu din na can Unguwar ta su Fagen zamuje ai ba barin case din zamuyi ba." Bazanje ba"! Anty ta katse ta, " Kin ga Talatu na sako ki cikin sabgar nan ne dan ki sama mun mafita badan ki kara min damuwa da takaici ba. dan haka in baza ki iya ba, ina rokon ki da ki hada komatsanki ki koma garin ku. Hajiya Hajiya Talatu ta saka dariya tare da fadin Dadina da ke sahibata, idan kika fusata sai ki rasa abin fada, shiyasa ko me zakice baya damuna. Anty ta ja tsaki Sannan tace sai ki fada min mafita dan wannan dai babu nasara. Hajiya Talatu tace mafita fa na fada miki kiyi duk abinda zaki yi amma ina son ki sani zakiyi komai ne kafin Halifa ya dawo domin ko yanzu bana tunanin zai ji dadin kiran yansanda da kika yi wa Inna. " Anty tace Hakane yanzu dai menene mafita? Hajiya Talatu tace dole fa mu fara ta kan cikin a zubda shi sannan abubuwa su biyo baya. Abban su Sulaiman ya kira Baffan Halifa a waya bayan sun gaisa sai yake tambayar Baffa da cewa Yaya anyi abu cikin mutunci da girmamawa yanzu kuma abu ya zo da cin zarafin Uwar yarinyar nan su Halifa za su kirawa yansanda. Baffa ya kasa gane kan zance kuma ya kasa hasko ma wace yarinya ake nufi. Sai da Abban su Sulaiman ya fayyace masa zance kamar dai yadda Inna ta sanar da shi. Baffa ya cika da mamaki yana shakku akan wai Aunty Halifa ce za ace duk ta kitsa wannan lamarin ko dai su binciki yarinyar nan yaran yanzu ka iya kulla abinda ba shi bane. Yace Kuma kuna da tabbaci akan abinda yarinyar nan ta fada? Saboda ni dai iya sanin na nayi wa Habiba mutuniyar kirki sbedar cewa ta na son Halifa kuma mu dangin Halifa na waje Uba, ta dauke mu kamar dangin ta, kuma ta bawa Halifa tarbiyya daidai gwargwado bana shakka akan haka. Sai dai kuma bari zan yi magana da Halifa idan ya dawo domin gaskiya baya nan ya yi tafiya, kuma dai ni bai sanar da ni komai ba. Abban su Sulaiman yace To Wallahi kamar yadda ka bada shedar matar nan haka zan baka shedar yarinyar nan da uwarta. Kusan sai ince maka kaf Unguwar nan tamu da kyar a samu mai hakuri da kirki Uwar yarinyar nan. Shi yasa muka hana yansanda su tafi da ita. amma ka bincika dai insha Allahu ai gaskiya zata yi halinta ko ba dade ko ba jima. Haka suka yi sallama kowa yana cike da yakinin shike da gaskiya. Anty ta tura Adamu Bros gidan wata kawarta wadda suka yanke shawarar hada yaran bayan fahimtar da ta yi cewa Mijin kawar ta ta ya samu kudi harma ya tsaya takardar dan majalisar jiha. Da ta share Hajiya Mairo bata ko daga kiranta bayan mijina ya samu karayar arziki, sai gashi harda kai mata ziyara daga jin labarin abin Duniya ya kara dawo musu. A nan ne tace "Kai najima banzo ba haka Huda ta girma gaskiya baki kyauta ba ko ita ai da kin turo min ta dan yi min kwana biyu anyi hutu Hafsa fa tana nan kinga ai da sun saba. Ta fadi hakane bayan Huda tazo ta gaida ita. Hajiya Mauro tace Kaji ki da kare kai keda kika watsar da mutane yaushe har zan turo miki ita? Anty tace hummm ni da zaku ba wannan yaron ita wallahi da nayi murna ga hankali masha Allah. Hajiya Mairo tace Da dai kafin ya yi aure ne gaskiya ba zata gidan Mijin wata ba. Adamu ai yaron kirki ne kawai dai bazan kai yarana gidan kishiya bane. Anty ta amshe da fadin "Wace kishiya kike ta fadine Adamu yanzu bashi da mata sun rabu, yarinyar da harni ta zazzaage a gaban sa nan take ya dan kara mata saki uku ya aunata gidan su." Hajiya Mairo tace Ko dai ke ce kika shiga shirgin su shiyasa har ta yi miki rashin kunya. "Haba Hajiya Mairo ashe baki ma san ni ba ko ince kin manta ni. Anty ta cafke maganar, taci gaba da fadin zan turo shi in har ya yi mata shikenan muyi tuwon mu manmu. Sun shirya cewa yaje a ranar Lahadi Dan haka ta kira Bros ya zo har gida ta kwatanta masa gidan Hajiya Mairo tare da bashi Umarnin lallai ya shiyar a ranar Lahadi ya tafi su hadu da Huda. Maman Nihal ce ta karfafa masa tare da tilasta masa cewar yaje din domin bashi da wata mafita dole ya yi biyayya ga mahaifiyarsa. Huda tana da kyau dukda ya kula tana da jin kanta sannan kuma ta aminta da shi. Ta gefensa dai kawai yace mata su yi tunani zuwa sati mai zuwa zai dawo in har sun ga ya dace su yi aure. Saidai kafin satin Huda ta fada da Bros ta matsa masa da kira da sako. A gurin Hajiya Mairo Anty ta ke samun labarin zuwa Bros da yadda Huda ta amince da shi. Anty ta kira Adamu ta yi masa tatas sakamakon baizo ya sanar da ita yadda suka yi da Huda ba. Kuma tace lallai da kanshi take son ya kawo kudin da za akai yaba Dadin su hannu da hannu, wanda za a kai gidan su Huda tace kuma ya bada kudi masu kauri domin tuwo girma dai miyarsa nama . Kafin zagayowar satin da yace su yi tunani Anty ta tilasta aka kai kudin auren har aka saka rana wata biyu. Halifa ji yake kamar karya dawo Nigeria domin ya samu nutsuwa zuciyar shi abu daya zai dawo danshi Asiya. Ya kasa samun ta balle labarin ta. Ya yanke shawarar yana dawowa zaije ya dakkota su koma sabon gidansu Koda Anty bata amince da hakan ba. Asiya kuwa tana shirin dawowa domin soyayya da kewar mijita sun hana ta kwanciyar hankali. Saiga Inna cike da tashin hankali take sanar da su Abinda Anty ta yi mata. Sannan ta kara da fadin cewa tana zargin cewar Halifa ya san komai tunda har baizo ba ko hakuri ya bata. Asiya ta sha kuka dan takaici gaskiya Halifa ya sani domin tana da Tabbaci Sulaiman ya kira shi ya fada masa ya kamata ya zo ya wanke kansa a gurin Inna. Dan haka ta kudure a ranta cewa duk wanda ya taba mutuncin Innarta zata iya hakura da shi da soyayyarsa. Saidai wani sashe na zuciyata ya ki yarda da cewa Halifa yana da masaniya. Ta dai yanke shawarar ci gaba da zama a Malumfashi har sai ta haifi dan cikin ta. *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [8/28, 10:09] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Hajiya Talatu ce ta binciko cewar Asiya tana garin su, ta hanyar yin amfani da wata makociyar su Inna. Kuma ta bata aikin cewar duk lokacin da Asiya ta dawo ga lambar ta nan Dan Allah ta sanar da ita, domin ita tana aiki ne da Hukumar kare hakkin dan Adam sannan taga Videon Asiya yana yawo wanda ta san cewa sharri akai mata. Makociya ta saki jiki tare da fadin tabbas sharri ne, domin Asiya yarinyar kirki ce zan sanar da Innar su kuma nasan in ta dawo zata sanar da ni. Haka kuwa makociya ta shiga gidan cike da murnar taimakon su Inna ta sanar da Inna komai. Inna tace to gaskiya dai ni bana ma son sai muje muna wata shara a ko wani maida zance. Allah dai na barwa komai Asiya zata dawo amma bansan rana ba wallahi. Makociya ta yi ta kokarin wayar wa da Inna kai amma Inna tace Allah ya zaba abinda yake mafi alkairi. Ko dan wannan tashin hankali na yan Biñdiga da suka soma kawo hari makotan kauyen nan Asiya dole ki koma gida tun da can komai ya lafa ko kuma ki zauna a kurna. Domin muma kaura zamu yi daga nan zamu tafi Kankiya Baba Tabawa take fadawa Asiya. Asiya tace "Nima na yi tunanin haka amma ji nake gaba daya an cire min Kano a raina sai dai inje dole." Tabawa tace Hakuri za ki yi saidai in zaki bimu hijirar sai mu tafi. Asiya tace haba dai, babu wani abu zuwa gobe sai in koma Kano. Makociya ta sanar da Hajiya Talatu bayan dawowar Asiya da kwana biyu dan haka suka soma shirya abinda za su aiwatar. Sulaiman Asiya ta sa Abba ya kira mata. Suka gaisa a soro. Tace kasan abinda ya sa na kira ka Yaya Sulaiman? Yace 'A' a. Tace Ina son inji ko kunyi magana da Abokin ka ne, bansan zaman da nake yi ba har yanzu gara ya bani takarda ta sannan in san matsayin dan ciki na. Ta kai karshen maganar da kuka. Sulaiman ya ce Kiyi Hakuri wallahi Halifa nima bai daga wayata ba tunda aka shiga wannan kwamacalar yanzu ma ina zaton ya yi Blocking dina ne dan bana samun shi, kawai, ina son Kiyi hakuri zanje har kasuwar su in same shi zuwa kamar karfe biyu. Duk yadda ake ciki zan sanar da ke zuwa magariba. Tace to Na gode ina son zuwa Asibiti ne amma sai naji inda muka kwana da zancen shi. Yace ba damuwa. Kamar yadda Sulaiman ya alkawarta haka ya yi. Yaje saidai yaran shagon sun tabbatar masa da cewa Halifa baya kasar kusan wata daya kenan amma suna sa ran dawowar shi cikin satin nan. Ya bukaci lambar da zai same shi. Suka ce ai ba a samun shi sai dai in shine ya kira. Haka Sulaiman ya sanar da Asiya lokacin da ya shiga gidan bayan magariba. Yace ki kara hakuri nima sai yanzu na huce dana fahimci ashe baya nan ne, kuma gaskiya ko can dama abotarmu bawai ta yi mugun karfin da duk inda zashi sai ya sanar da mu bane. Yana dai son mu ne gaskiya dan kafin mu nemeshi ya nememu ya yi mana alkairi kinga kenan baya nan Anty ta kawo wa Inna yansanda bana tunanin ya sani. Asiya ta sauke Ajiyar zuciya Sannan tace haka ka ke gani? Yace Gaskiya dai haka ne ma ance ya yi wata baya nan su kuma ai ba ayi wata ba. Sannan a iya sanina da Halifa Koda abinda ya faru da gaske ne ba zai sa a kama Inna ba. Asiya tace to Allah ya sa hakan ne. Sulaiman ya kawo kudi dubu goma ya ba Asiya ga wannan kije Asibitin inhar da wata damuwa ki sanar dani. Asiya zata ki amsa ya yi mata tsawa da cewa baya son haka. Ta amsa ta yi godiya. Inna ma ta yi masa godiya. Asiya ta na kwance tana tunani ko da ba gaskiya bane abinda Sulaiman ya fada ta ji sanyi da farin ciki. Allah ya sa su koma zaman su da mijinta tana sonshi sosai. Asiya da Sadiyan su Maman Annur suka tafi Asibiti tun a gida suke ta shawara suje Asibitin Unguwa ne ko kuwa suje Murtala. Karshe dai suka tafi wani Asibitin kudi amma ba shi da tsada wata mata da suka hau kekenapep ta basu shawara tace ga kula sosai.Sun isa Asibitin nan suka fada mata cewar dubu ishirin ne zata biya har ta haihu, saidai hoton ciki ko magani su siya zata yi. Tace zata fara ba su dubu goma kafin ta haihu sai ta cika, suka ce babu damuwa. An tabbatar mata ita da abinda ke cikin nata duk suna lafiya domin bugun zuciyar sa daidai, amma an bata takardar da zata yi hoto domin aga yanayi zaman sa. Sadiya ce ta bata kudin hoton domin anyi mata albashinta ba jimawa. Sunce cikin nata watan shi Hudu da sati uku kuma sun saka mata ranar haihuwa. Hajiya Talatu da Anty suka shiga duba katuna sun samu masu suna Asiya guda biyu saidai ba za su gane wacce ce ba saboda Anty bata san sunan Baban Asiya ba. Likitan yace ku duba shekarun mana, inhar baku gane nata shekarun ba sai ku bincika sunan Babanta. Sun samu Asiya daya shekaru Talatin dayar sha takwas, dan haka suka gano yar sha takwas din nan dai ita ce suka zo akan ta. Hajiya Talatu itace ta sanar da Likitan abinda suke bukata suna son a zubda cikin Asiya suna son ya fadi abinda za su bashi. Ya dan jima yana Nazari Sannan yace "To da farko dai ina mijinta domin bana son in shiga abinda zai bada matsala. Anty tace bata da miji sun rabu sakamakon kamata da ya yi tirmi da tabar ya da wani, to sai ta zo da wannan cikin tace nasa ne, nasan in anje kotun musulinci shi za a bawa cikin nan, ni kuma gaskiya bazan yarda a bashi ciki da ba nasa ba, shine kawai zamu raba gaddamar. Likitan yace to ba damuwa miliyan daya zaki bani. Anty ta mike tsaye a gigice haba dai kai kuwa milinyan fa da yawa gaskiya yace to baki duba girman laifin da kike son a aikata wadda ta saba da Dokar likitanci akan wannan aikin naki sai a rufe asibitin tare da kwace lasisin Asibitina, ya dan yi shiru gaskiya nama fasa domin aikin yana da hadari sosai. Hajiya Talatu tace "Kinji matsalar ki ke baki son fidda kudi kuma kina son ayi miki aikin kudi. " Anty tace ke bazaki gane bane, nifa ba nice me kudin ba Halifa ne me kudin rigar alfamar sa ce ke nuna ni ake min kallon kudi. Hajiya Talatu ta kyakyace da dariyar keta, sannan tace To sai ki ta shi mu tunda ba kudi. Anty ta danyi tsai tana tunanin inda zata samar da wannan kudin kai tsaye. In kawo miki mai sayen ragowar kayan Lefen nan ku karasar da su har akwatunan ki biya bukatar gabanki. Anty ta danyi shiru tana tunanin Anya kuwa Halifa zai yafe mata ta saida masa kayan masu tsada ta hanyar karyar da su kuma ta yi amfani da kudin gurin zubar masa da ciki dan sa. Ta saki murmushin mugunta tare da fadin hakuri zai yi kawai. Ta kalli Talatu shikenan zanje in nemo rabi aiki yana kammala zan cika maka saura. Asiya taga Anty da Hajiya Talatu sun biyo ta da gudu tana ta boyewa kuma a cikin Asibitin da taje awo. Ta labe a wani daki suna ta neman ta sai taga wani likita ya shigo yace karki damu zan boye ki biyoni. Bayan ta bishi ya boye ta sai kuma ta hango shi ta windor yana magana da su suna tuntsira dariya. Firgugit ta farka ta tashi zaune tana addu"a, tayi hamdala da ta ga mafarki ne, Asiya tana da girmama mafarki, bata yawan yin sa, amma kuma duk lokacin da zata yi shi sai ya zame mata kamar ishara ko nuni zuwa ga wani abu. Suna karyawa da safe tace wa Maman Annur nifa ina zargin kamar Anty tana bibiyata domin na yi wani mafarki da ya bani tsoro abin ya shafi cikin jikina domin harda Asibitin da mukaje. ta bata labarin mafarkin. "Karki baiwa mafarki muhimmanci. Da Yawan mafarkai shedan ne ki kyautata zato kiyi addua khairan insha Allah. Halifa ya sauka a filin jirgin sama na Kano da karfe shidda na safe, mota ya dauka kai tsaye ta kai shi gidan sa, sai da yayi bacci ya huta yunwa ta fito dashi, yaje gidan ci abinci ya ci sannan ya sake daukan mai a daidaita sahu zuwa gida. Kiran Baffan sa ya shigo wayarsa, mamaki ya kama shi tunda ya shigo ya maida layinsa yake jin saukar sakwanni tunda ya duba daya biyu babu na Asiya kawai ya fita sabgar su. Ba wanda ya kira shi dan bai fadawa kowa cewar ya dawo ba. Ya daga cike da girmamawa suka gaisa Baffa yace ashe ka dawo? Halifa yace na dawo tun sassafiya da yake gidana na wuce ko su Anty ba su san na dawo ba. Baffa yace to idan babu damuwa ina son kazo yanzu. To ganinan Insha Allah. Ya saka me a daidaita suka kama hanyar gidan Baffa. Cike da sake sake. Bayan sun gama gaisawa Baffa yace Ina son ka fada min abinda ke faruwa a gidanka da bakin ka. Domin na samu labarai marasa dadi daga bakuna daban daban. Nan dai Halifa ya zanyyane wa Baffa iya abinda ya faru na zuwan kwarto gidan sa abinda ya biyo baya na dorawa a waya. Baffa yace to kai ina matsayar ka da yarinyar domin kayi kuskuren rashin rike kwarton kuma kai baka shiga ba dan haka babu wani labari da zaka bada shara a ta karba. Sannan Antyn ka taje da ƴan sanda gidan su matar ka za a kama Uwar yarinyar yan Unguwa suka hana. Kasan da wannan? Tsaye Halifa ya mike,. Anty ce ta kira wa Inna yansanda to akan me? Baffa yace zauna ka kwantar da hankalin ka. Kamar yadda na fada maka munyi magana da abokina Baban Abokin ka. Gaba daya suna zargin Antynka da yunkurin kashe auren ku, ta hanyar kulla abubuwa. Dan sunce har guba ta bata da sauran zantuka su na mata. Ina son ka kwantar da hankalin ka ka sanar dani kai me ke ranka game da matar ka? Halifa yace gaskiya Baffa bana zargin matata har zuwa yanzu kawai naji haushi tafiyar da ta yi gida ne bayan na hana ta, kuma tafiyar ta ta ce ta bawa masu yada maganar damar bin diddigi da kuma kaga wasu zantuka, da tana gidanta karya ne wani dan jarida ko dan tiktok koma waye ya tinkare ni ko ita tunda dai irin wannan abin ace ya faru da gaske kuma muna tare ai bazai yiwu ba. To da ta tafi ma daga gidan su sai ta kuma tafiya kauyen su duk ba yarda ta. Dan haka sai na barta ta gama yin yadda take so. Amma game da aurena ko cikin ta wannan duk baani da wata damuwa. Sannan ni kaina ina zargin Antyna da wasu abubuwan saidai bana fata zargin ya zama gaskiya shiyasa nake ta gocewa kuma ina ta bata uzri. Domin idan har Anty zata cutar da ni to kuwa Mahaifiya zata cutar da danta. In Anty bata sona meyasa bata kashe ni tun ina tsumman goyo ba? In Anty tana son kashe ni me yasa ta tsaya ta bani tarbiyya da ilimi bata taba nuna min wani banbancin ba? Wace riba zata samu in ta hana ni zama da mata ta? Wadannan sune tambayoyina Baffa kuma inka duba zaka ga haka ne. Amma Na fadawa Allah ya kawo min mafita ya bayyana shedanin da ke son hanani zama lafiya da matata da kuma Anty na. Baffa yace to Allah ya bayyana gaskiya amma ka samu ka dawo da matar ka dakinta ita kuma Antyn taka ka bata hakuri matsalar iyali ba a sako jami an tsaro. Halifa yace Insha Allah zan tashi in koma can gidana ne kawai maganin fitinar Baffa yace haka ya yi. Halifa ya nufi gida. Anty ta kira mai sayen akwatuna ta zube su a falo suna ta ciniki Hajiya Talatu ma tana son biyu a ciki amma fa Anty tace sai ta zube mata kudi ko kuma idan taga alat sannan zata bada. Halifa ya yi sallama a kofar falo sannan ya shigo kai tsaye.... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [9/7, 11:02] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Kallo ya bisu da shi fuskarshi cike da alamun tambayoyi Anty ta diririce tamike tana fadin oyoyo Halifa Oyoyo Uban masu gida oyoyo uban masu kudi kinsan fa duk yan gidan su masu kudi ne. Har lokacin idanun shi suna kan akwatunan Anty cike da in ina tace "Am dama wannan ne ya wannan irin akwatunan ka ya kawo za a siya kasan baka nan an saka ranar danka Baban su Nihal shine ka ga ina wayata ma ko ina ya jefa ta, wallahi sai kiranta nake yi bai daga ba. Halifa ya kai kallon shi kan Hajiya Talatu wadda ta ke ta kokarin rufe wasu jajayen kayan bacci wadan da yasiye su a wata tafiya da ya yi Chaina lokacin yana kan hada lefe. Nuna wasu ta kalma da aka tura kasan kujera yace, "Harda wadan can takalaman da kayan baccin can duk zai saida? Ba jira amsa ba ya ci gaba da fadin Ni zuwa anjima zan amshi nawa akwatunan da kayan ciki zan kai su sabon gida." To ai suna ciki ko zaka dauka yanzu? Anty ta fada da sauri tare da share zufar data keto mata a goshi. Ta ci gaba da fadin ka zauna mana bari a kawo maka abinci ka sha hanya. Zata yi hanyar kicin Halifa ya ce " A koshe nake Anty karki manta bayan magriba zan kwashi kayan". Ya Juya ba tare da ya jira amsa ba. Kai kawo yake yi tunda ya shiga falon sa, ko kaffara ba zai yi ba wadannan kayan sa ne, kwanaki ta fada masa ta taba wani abu a kayan ransa ya baci amma ya nuna mata babu komai. Shine yanzu kuma zata sai da akwatu nan. A fili ya furta Allah ya sa dai ba duka kayan ta salwantar masa ba. Anty ta kalli Hajiya Talatu tace "Na shiga uku kinga wata masifa to yanzu ina zan samo sauran kayan ni Habiba, ko kuwa dai in kira Malam ya rufe min bakin sa. Hajiya Talatu ta ja tsaki" Dan Allah dubi yadda duk ki ka burkuce kika fita hayyacin ki kamar wani ubanki, dan bai samu kayan ba sai ya dake ki? Anty tace "Baza ki gane irin zuciyar da Halifa yake da ita ba, a haka ma dan na saka Malamai sun min aikin karya zuciyar ta sa, ke da dane ya samu kayan nan wallahi sai ya daga mana hankali a gurin nan ko ya kwashi kayan ya cinna musu wuta." Hajiya Talatu tace, to hakura zakiyi da wancan aikin kenan na Asibitin? Anty ta kalli mai sayen akwatunan tace Inaga kawai kaje. Yace To zan baki yadda kika ce da farko. Anty tace Kai kuma ana ga koshi kana ga kwanan yunwa, duk fa a gaban ka komai ya faru kuma da Hausa muke magana ba wai da wani yare ba. Me siya akwatuna yace Hajiya in kun canza shawara Dan Allah ku nemeni ta wannan lambar. Hajiya Talatu ta yi karaf tace ina ganin abinda za ayi kawai ka bamu kudi in kurar ta lafa kazo ka kwashi kaya. Anty tace "Tabbas domin na san ganin kayan ne ya sa yace zai dauka domin fa tabbas ya san kayan shi ne ba wai ya yarda da abinda na fada bane. Me Siyan kaya yace ina ce nan gidan ki ne? Anty tace. Ban gane ba, yace" "Ba dai nan ne gidan mijinki ba, ko kuwa zan ba ki kudi ne kawai dan tsoro? Hajiya Talatu tace gidan ta ne ka bamu miliyan daya daga baya sai muyi magana. Yace ai ba kayan miliyan zan siya ba, akwati catai in bada dari uku nake neman ragi. Hajiya Talatu tace ai zamu baka wasu kayan kalli gidan nan fa, ji kayan da ke falon nan miliyan din banza kawai dai wata bukata ce ta gaggawa. Yabi ko Ina da kallo a zuciyar sa yace zai so ma su ki bashi kayan ko kudinsa domin in har abin ya zama rigima sai ya ci ribar da ta linka abinda zai samu in aka yi sabgar lafiya lafiya. Ya Numfasa Yace to naji zan bada amma in na bada miliyan daya in kudin za a maido min miliyan da dari biyu da hamsin za a bani ko kuma a bani kayan kudi. Suka ce sun yarda nan take yace sai anyi rubutun yarjejeniya bayan sun gama yace Su bashi account number. Kamar wasa ya saka wa Anty miliyan daya kuma ya tafi. Halifa bai jima a gidan ba ya dauki motarsa ya kaita gurin wanki yana can ya kira Bros ya sanar da shi ya dawo anan yaake fada masa Maman Nihal ta haihu da namiji. Ya yi masa murna ya kuma tambaye shi batun aure da ya ji Anty tana fada, yace tabbas akwai batun ya sanar da shi komai. Halifa yace Kasan kayan lefen mata ta da Anty tace a jinkirta bata sune na gani sun tasa tare da wannan kawar ta ta suna cinikin su? Bros ya saki salati Sannan yace "Amma ka Karbi kayan ka ko?" Halifa yace Tace ba su bane amma dai na san borin kunya ne da dare zanje in ce ta bani wallahi Bros Anty bata taba bata min rai irin na yau ba, yau ne na yi tunanin dama ace mahaifiyata tana raye domin Uwa ce kawai ta san darajar duk wani abu na danta. na ga iyayen da sune ke hadawa yaran su lefe dan su rufa Asiri. Bros yace "Ina tabbatar maka cewa Anty ko ni din ne hakan zata aikata min dubi yadda ta korar min mata." Halifa yace ta yi haka ne dan tana zargin tun da ka auri maman Nihal kasuwancin ka ya tsaya kaga tana fada ne akan son ci gaban ka. Bros ya ce akan son ranta dai, ni mahaifiyata ce bani da yadda zanyi amma kai yar ka ce zaka iya neman hakkin ka ko nuna mata rashin jin dadin abinda ta yi maka. " Halifa ya sauke ajiyar zuciya yace. Na fada maka ne dan inji sanyi kar kaji haushin magana ta. Bros Yace ba wai bakar magana na fada maka ba Uncle wallahi haka shine gaskiya kaje ka ce mata ta baka kayan ka, bai dace abar mutum ya yi tafiya a cikin kuskure ba. Halifa yace zanga me zanyi. Asiya tace Inna gaskiya Na hakura da yin awon nan ina yawan mafarki da Asibiti wai kuma ga Anty abin dai na kasa fassara shi. Inna tace" Khairan insha Allah babu abinda zai samu ke da abinda ke cikin ki, Kiyi ta adduo'in neman tsarin nima kuma ina yi, kinsan dai Allah baya wofintar da adduo'in mahaifa akan yaransu. Insha Allah zaki sauka lafiya. Sadiya da ke gefe tace Ameen insha Allah. Ni Mijin nata ne ma ko da dai ance ya yi tafiya amma ya kamata ko a waya ya nemeki in dai ba wai yana zargin ki a gaske ba. Asiya tace Babu mamaki ya neme ni ai nâ kashe wayata. Inna tace shi dai ya sani nikam gara ma ya baki takardar ki in kin haihu lafiya kya samu wani mijin daidai ke. "Asiya tabi Inna da ido tana Kallon ta domin kalaman Inna sun soki zuciyar ta har ma ta rasa kalmar fadi. Sadiya tace muna daya Inna gara su rabu da a kashe ta a banza, dan matar nan ta shirya wa haka. Suka ci gaba da tattauna zancan a tsakanin Inna da Sadiya. Asiya dai bakinta dai ya yi nauyi zuciyar ta kuwa ta shiga zogi gaskiya bata jin zata iya rayuwa ba tare da Halifa ba, gaskiya tana son shi zata iya jure komai saboda shi, sai yanzu ta yi data sanin dawowarta gida da ta tsaya kamar yadda ya bukata. Inna tana da sauki amma in ta cije bata canzuwa ga ciwon ta ba sa son abinda zai bata mata rai. Ta share zufar da ta keto mata ta kuma sauke ajiyar zuciya lokaci guda. Inna ta kalleta lafiya ko dan ance bazaki koma gidansa ba? Asiya tace Ba haka bane kawai dai bari ya dawo muji ta bakinsa. Inna tace Ai ko ya dawo bazan iya gayyar rashin mutuncin ba abida kawai zaifi shine a rabu. Yansanda kamar anzo kama yan fashi banda Allah yasa muna zaune da yan Unguwa lafiya ba, ai da tuni sun tafi dani, Kasar nan ba a jin kunya a juya takarda a rubuta abinda ake so a kaiwa alkali ya jefa ka gidan Yari..Sadiya Tace nifa Har shi Halifa haushin sa nake ji, da ka yake zaune ace duk abubuwan da ta miki wai yace bai sani ba kuma bai fahimci komai akai ba?!! Asiya tace kar kice haka maman Annur kar ki ga laifin sa dan bai sani ba, Na farko baya yini a gidan sannan ya yarda da ita bata taba yi masa wata mugunta ba bare ya zarge ta. Kuma yadda naga yana shiga tashin hankali idan zuciyarsa ta hasaso ko ta zarge ta shine yasa ban fada masa komai ba. Kinga kuwa dole a yi masa uzri. Inna tace "Dama fa ba sanin su mukayi ba, dare daya yazo rabon dai wannan ciki. Ni mutum ko dan karuna ne ya zo dan kudi wallahi bazan dauki wulakanci ba. Asiya ta sunkuyar da kai. Lallai abin ya wuce yadda take tunani. Halifa ya shiga ciki falon Anty Hafsi tana waya yace ina Anty? Tace tana ciki ba ta da lafiya. Yace Allah ya sau wake, ki ce mata nazo zan dauki kaya. Hafsi ta ce To ka shiga mana Uncle ita da Hajiyan Zariya ne. Yace Shiyasa bazan shiga ba domin bana son ganin matar nan a gidan nan duk lokacin da ta zo abubuwa sai sun yi ta faruwa babu dadi. Hafsi ta taba baki "Ai kwadayi ke kawo ta dan ma Anty tana taka mata burki. Ya ja tsaki Sannan ya bi bayan Hafsi. Anty tana kwance ta rufa cikin bargo tana ta rawar sanyi Hajiya Talatu tana yi mata sannu. Ya kalli sashin akwatuna suna jere kamar yadda suke hatta rinbom din dake jikin akwatunan suna jiki. Ya dan taba baki shikam ya tabbatar wadannan din dai ya gani dazu. Ya dan matsa kusa da Anty yace Sannu Anty zazzabi ne. Hajiya Talatu ta ce Hawan jinin ta ne ya tashi ta samu kanta a bacin rai gidan su wannan matar taka da muka je neman sasanci Uwar ta ta zage mu tas ta zuba mana ruwan wanki har ta yi ikirarin kisan Antyn ka. "Shine dalilin kira mata ya sanda da kukayi? Halifa ya katse Hajiya Talatu. Tace Eh to ai dole dannan kaji yadda ta tara mutane tana shan alwashin kashe Antyn ka kuwa!!? Cike da tsana Halifa ya sake Kallon ta." Nasan ke zaki zuga ta kuje gidan ku yi mata rashin mutuncin kuma ko me ya faru dai ku kuka sameta har gidan ta. Anty wadda ke kwance tana makyarkyata ta tashi da sauri zaune cike da mamaki tana Kallon Halifa cike da Al ajabi yaron da in bata da lafiya ya fi kowa daga hankali yaron da in wani ya tabota sai inda karfin sa ya kare idan da ne ya samu bata da lafiya ba zai bari ta kara minti goma a gidan ba, zai tabbatar tana gadon Asibiti. Ta soma magana cikin kuka Halifa ni ka ke fadawa magana akan surukan ka shine har kake wadannan zantuka ko? Halifa Ya ce. "Menene karya ko laifi a magana ta Anty? Nace kuje neman sasanci ne da wa muka yi fada ni da mata ta ba fada muka yi ba, anyi mata sharri ne kuma ta yi fushi in kuma ta huce zata dawo to menene naku da zuwa gidan?Wallahi Anty kin bani mamaki kuma kin nuna min cewa lallai mahaifiyata ta mutu domin da tana raye wallahi baza ta dakkowa surukai na mutane muskunai masu rauni kamar su Inna yansanda ba. Kamar yadda ke ma nasan bazaki dakkowa iyayen matar Bros ba tunda danki ne. Yanzu kam Anty kukan gaske take rerawa ba kamar dazu ba da take kukan kissa da makirci ba. Hajiya Talatu wadda ta hangame baki ta kasa magana har sai da ya kai aya ta sauke ajiyar zuciya tace Amma dai dannan baka kyauta ba, Antyn ka bata cancanci irin wadannan kalamai daga bakin ka ba domin..... Ke da Allah yimin shiru ina wuya dake wallahi in kika kara magana sai nasa an rufe min ke, kuma ki tashi ki fita ki bar gidan nan yanzun.!! Anty mai rashin lafiya ta diro daga kan gado Tazo gaban Halifa ta sa hannu ta dauke shi da wani wawan mari, Ka fara shaye shaye ne a tafiyar da ka yi ko? Ta daga murya ni zaka ciwa zarafi wannan ne sakamako na ko Halifa!! Ta fashe da sabon kuka mai karfi wanda ya janyo hankali kowa na gidan inda suka nufo dakin. Halifa ya dafe kuncin sa ya cike da bacin rai a kofar fita suka ci karo da Dady zai shiga falon. Ganin yadda Halifa ya wuce ba tare da ya Kalle shi ba bare ya yi masa magana ba ya gane akwai matsala dan haka ya nufi ciki da sauri, kukan Anty da zantuka da take maimaitawa ne suka dira a kunnen shi. Tana fadin ni Halifa zai ciwa zarafi akan surukansa wallahi daga shi har su basu isa ba inna haihu cikin iyayena ko asiri suka yi masa sai na karya shi. Bai shiga dakin ba ya wuce nashi dakin sai da ya cire kayan jikinsa ya saka jallabiyya sannan ya fito ya nufi dakin Halifa dan jin ba"asi. Yana fitowa tsakar gida Halifa ya fita a motarsa da gudu daga gidan ya danyi shiru yana tunanin abinda zai yi, yana tsoron masifar Anty ne shiyasa bai ma shiga dakin ta ba. Ya yi ta maza ya tunkari dakin danjin meke faruwa. Ya kalli yaran da suka tasa su gaba suna kallo yace kai duk ku fice. Ya dubi Anty wadda ke ta kuka tana sharbe sam bataji dadin abinda Halifa ya fada mata ba har zuciyar ta. Hajiya Talatu tana fadin daga gani zugashi suka yi. Dady yace Wai me yake faruwa ne? Sabon kuka Anty ta dora tana rattafo mishi abinda Halifa ya fada mata. Dady yace Gaskiya fa ya fada miki kuma ya kamata ki zauna ki yi wa kanki tunani sosai domin kina shiga hurumin yaran nan, menene naki na kirawo musu yansanda kuma? "Dan Allah ka rufe min baki!! Anty ta katse shi, ai kai dama kullum nice mai lefi akan komai. To Bari kaji Halifa dai dan Uwa na ne in ka so kayi masa fada ya bini ko kuma ka sa mana ido. Cikin mamaki taji ya daka mata tsawa." Ke Habiba saurara kiji, na gaji da abinda ki ke yi a gidan nan ina kauda kai. Ina yi ne fa dan a zauna lafiya ba wai dan tsoron ki ko wani abu ba, ina son ki sani bazan iya ci gaba da wadannan munanan dabi un naki ba, dan haka ina son ki sani komai zai iya faruwa ya sa kai ya fice daga dakin. Sai lokacin ta samu damar magana ta kalli Talatu Ki dubi wannan mutumin fa, har yana da izzar yi min magana kenan? Ta mike rai bace ta nufi kofar dakin shi tace ka fito ka fada min abinda zai faru karkari dai ka ce ka sake ni ko? Kaga sai ka hada yan kayan ka ka yi gaba banda haka me zai faru!! A doke dai ba zan doku ba haka ma zage bazan zagu ba.. Ya fito da karamar waya a hannunsa yana sauraron labarai ya kalleta ya ja tsaki ya wuce.. Anty fa abin ya zame mata goma da I shirin tana mamakin Inda mijinta ya samo kwarin gwiwa. Hajiya Talatu ta ce, Alamu suna nuna ayyuka duk sun karye wadan da kika yi masa, dan haka gobe akwai sammakon gidan malamai sai kuma kin kwance bakin aljihu. Anty tace Kai Na shiga uku yanzu me yafi mahimmanci a guri na aikin Halifa ko na Asiya ko na Dady...... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [9/20, 15:40] Ummi Tandama😇: Asiya da Sadiya suna tafe fitina irin ta masu ciki ta sa Asiya ta nemi Sadiya da ta yi mata rakiya zuwa gidan wata tsohuwa da suke siyan magarya lokacin suna zuwa primary suna tafe Sadiya tana mitar nisan gidan tana fadin "Allah da ace ke daya ce ba domin cikin nan ba wallahi bazan kama doguwar tafiyar nan ba kila ma muje bamu samu ba. Asiya tace sai mu wuce bakin Asibiti muje rimi can kam zamu samu har a duwa. Sadiya tace saidai ki biya mana mu hau dan sahu kuma yanzu .ma dare ne bazamu samu ba. Cak Asiya ta tsaya tana waige waige. 'Lafiya?" Sadiya ta fada tare da dafa Asiya. Tace "Ina jin kamshin Turaren Yaya Halifa, duk yadda aka yi yana nan gurin. Sadiya ta saki baki tana bin Asiya da kallo. Sannan ta taba baki tare da fadin "Waye kuma Halifa?" Mijina Asiya ta fada tare da nufar shagon Sulaiman ta leka shi kanshi Sulaiman baya ciki,ta juya da sauri ta nufi gidan su ta ma manta da Sadiya. Sai biyo ta ta yi tana kwada mata kira. Ta duba ko ina a kofar gidan tana kalle kalle, bata ganshi ba ta shiga gidan Inna tana tsaye rike da wata farar takarda da sauri suka karasa Asiya tace Inna la.. Lafiya? Bata san me yasa ta faduwar gaba ba. Inna tace Takardar sakin ki ce Mijinki ya kawo. Maganar ta daki kirjin Asiya har ma da Sadiyar duk da ba ita aka saka ba. Da sauri Sadiya ta amshi takardar ta soma karantawa a fili. "Ni Halifa na saki Asiya saki uku kuma cikin jikinta ba nawa bane ta nemi ubansa,in kuma bata yarda ba zan shigar da kara kotu. Tun kafin ta kai karshe Asiya take fadin Amma kuwa Inna waye wanda ya kawo wannan takardar? Ta kai karshen tambayar cikin rawar jiki da rawar murya. Inna cike da bacin rai tace koma waye ya kawo ke dai ba ya sake ki ba,ni gara haka da a sabarta min ke,batun ciki kuwa dole ya amsa koda kuwa hakan zata kaimu har gaban alkali ne. Amma zamu fara ta kan waliyyan shi tukunna da safe zan yi magana da Abban su Sulaiman. Sadiya ta sauke gwauron numfashi sannan tace, "wannan zalunci ne aka yi wa Asiya gaba daya tun daga auren zuwa yanzu." Asiya tace Inna gaskiya ba zan taba yarda cewa Halifa ne ya kawo min ba, domin kalaman da ke rubuce a jikin takardar ba kalaman da Halifa zai yi amfani da su ba ne koda kuwa saki na zai yi, sannan in har Halifa zai sake ni ba zai min saki uku ba. Kuka ya kwace mata ta fada daki da gudu ta fada kan yar yaloluwar katifarta tana furta Innalillahi wa Inna ilaihirraji un. Sadiya ta zo ta zauna kusa da ita ta dafa ta cikin sigar lallahi tana cewa, kiyi hakuri Asiya Allah ubangiji shine mai sakayya zai bi miki hakkin ki. Asiya cikin kuka wiwi take fadin 'Ba zan iya tsayuwa gaban alkali muna shari'a da Halifa ba,ya fi karfin haka a gurina koda kuwa zai karyata cewa cikin ba nashi bane. Sadiya tace kaji Haukan ba,to wazai yarda da hakan? Inna daga tsakar gida take fadin cewa "Sam bata san illar da hakan zai ja mata ba, ni kuma matukar Ina raye ba zan bari karya ta hau kan gaskiya kuma ta zauna ba." Asiya ta sake fashewa da kuka tace, Inna , zuciyata har yanzu bata amince da cewa Halifa ne ya sake ni ba,Halifa wallahi ya yi min alkawura da dama yana sona Inna. Sadiya ta ja tsaki ta fita a dakin da ta shigo dan lallashin Asiya. Inna ma cike da jin haushi tace "To sai ki hada kayan ki ki koma gidan sa ki zauna tunda kin ce ba,zai iya sakin ki ba. Kuma ki rufe min bakin ki kafin ki tunzurani in hau kanki har ke har cikin dake jikin ki,bana son in sake jin muryar ki a gurin nan har ke har cikin naki. Asiya ta kwanta tana hadiyar zuciya nan take zazzabi da ciwon kai suka diro mata,bata taba sanin tsawon dare da ake fada ba sai a ranar, tufka take tana warwara zuciyarta tana fada mata cewa ba gaskiya bane akwai alkawura masu dama a tsakanin su.To amma ba shakka ta ji kamshin turaren shi a wannan lokacin . Sai taji wata sabuwar kauna da son Halifa a zuciyarta ita kam zataje ta yi idda a dakinta. Ta tashi ta kalli sadiya tana ta baccinta da yaranta.Da a ce mutuwa Halifa ya yi zai fiye mata akan ace yana raye ita ma tana raye amma basa tare, ina ma ace ta mutu, ta ayyana hakan Ta mike ta je gurin akwatin kayanta ta dinga daga su a hankali har ta ciro wayar ta. Bata yi mamakin ganinta babu chaji ba,domin iya tsawon lokacin da aka kawo mata bata sa a chaji ba, kuma bata zaton ta kashe kafin ta fita sabgar ta. Bazata tuna tsawon lokacin da gidan su ya dauka babu wutar lantarki ba tun farkon ciwon Babansu. Kenan ita da chaji sai dai gobe idan ta kai gurin chaji. A fili ta furta Innalillahi wa Inna ilaihirraji un. Hannu ta ji an dafa ta ta baya. Ko bata juya ba,ta san Sadiya ce. Tace "Haba mana Asiya ke da a ka yiwa shedar hakuri da kawaici ya kamata ko bakiji dadin abinda ya faru ba,ki daure ko dan Inna musamman ma da yake bata da ishashiyar lafiya. Asiya ta juyo ta kalli Sadiya. "Maman Annur dan Allah ke kunyi soyayya da Baban Annur kafin ya rasu?" Sadiya tace kin dai san ba auren dole aka yi min ba ko?" Asiya ta lumshe idanun ta, taci gaba da fadin Baki san soyayya ba domin da kin santa ba zaki yi min wannan maganar ba, in da soyayya kuke yi dashi na tabbata da daya mutu da sai kin bishi." Sadiya tace Kina nufin in kashe kaina duk da lokacin mutuwata bai zo ba? Asiya ta mike tana tangadi ta koma kan katifar bata taɓa zaton Sadiya zata fahimci abinda take nufi. Sadiya ta ci gaba da fadin ki sani bawai banji mutuwar mijina ba ne ko kuma bana son shi ko kusa, kawai dai tawakkali gare ni. "Baza ki gane ba.' Asiya ta fada tare da kwanciya rigingine ta ci gaba da fadin, ki kwanta kawai. A zuciyarta ita dai kawai zata koma gidan mijinta ta yi idda ko Allah ya sa ya maida ita. "Ya kamata ki nutsu sosai saki uku ya yi miki,ki kauda kanki daga gare shi karma ki nuna masa kin damu ko da mu kin nuna mana." Sadiya ta sake katsewa Asiya tunani, da magana kuma kamar ta san tunanin da take yi. Kan Asiya ya kuma sarawa ashe fa saki uku ne. A fili tace astagfurullah ba shakka akwai wani laifin da na aikata wa Ubangiji. Kafin gari ya waye Asiya bata iya gane banbancin 7 da 17 . Hankalin Inna da Sadiya ya tashi suka dauketa zuwa Asibiti, likitan ya yi fada sosai akan yadda suka bari jininta ya hau irin haka, ya bukaci ganin mijinta bayan ya ba su gado Inna ta ce shine sillar ciwon saki uku ya yi mata kuma yake da a war cikin ba nashi bane. Likitan ya fusata yace zai hada su da wani lauya mai rajin kare hakkin dan Adam kuma zai taimaka musu dan su kai shi kotu. Duk da halin da Asiya take ciki bata iya magana amma ta daga yatsa tana girgigizawa alamun baza ta iya tsayawa da Halifa a gaban kotu ba. Inna tace "Ai ba ta ita zamu yi ba in zamu bi mata hakkinta,makauniyar soyayya ta rufe mata ido. Likitan yace a kwai yarinta a kanta dan haka baza ku tsaya jin ta ba. Amma yanzu a bari a samu kanta tukunna. Anty suna tafe bayan sun sauka daga kan dan sahu, gida suka nufa, tun farar safiya suka fita sunje gidan malami ya kusa goma,duk damuwarta akan batun Halifa ne, tana cike da tsoron abinda ya aikata jiya,ta san shi da zuciya ta masifa kuma ta kashe kudi a shekarun baya gurin malamai da dama kafin ta samu aka karya masa zuciya sannan ta samu sassauci,domin in da ne ta yi masa wannan rainin hankalin da kaya samu zai yi ya cinnawa sauran wuta. Kuma ta sa a rufe mata bakin mutumin nan mai kudin da ta karba dan tijara. Hajiya Talatu tace karki damu gashi rabin kudin ma duk sun tafi a malamai, nasan tun yau zamu soma ganin karfin aiki domin mun saka malamai masu zafin hannu......... *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [9/21, 18:35] Ummi Tandama😇: Ta kalli motar Halifa da ke aje a gurin da yake aje ta, tace yana gida ma wallahi Sahiba har wata faduwar gaba naji kinsan bamu hadu ba tun jiya, bari inje gurin dakin sa inga me yake ciki. Talatu ta ja tsaki karya ki ke ashe ba tsoron haduwa da shi ki ke ba,in kuma ya fito fa. Cike da kuri Anty tace sai me? Ta tsaya inda ta saba yi masa labe, waya yake yi da alamu da lauyan shi yake yi. Taji yace Barrister mu bar Zaman zuwa ranar litinin. Halifa ya fada yana tari. Ya dan jima yana tarin kafin daga bisani yace Barrister zai fi kyau haka zan kira jimawa mu karasa. Bai saurari amsa ba ya kashe wayar. Cike da tashin hankali ta isa dakin ta. Ta samu Talatu har ta cire riga zata shiga wanka, Anty ta shigo tana fadin "Wata sabuwa na shiga uku Talatu cike da tashin hankali. Hajiya Talatu cike da fargaba tace 'Me aka yi ne Sahiba Anty tace Naji Halifa ya na waya wai za su zauna da lauyoyin sa ko dai zai amshe duk dukiyar shi ne ya koma yana sarrafa su, in kuwa haka ne yanzun ne daidai lokacin da zan mallake shi. Hajiya Talatu tace baki yi tunani akan ko zai kwace wannan gidan yace ku tashi ba? Ya amshe dukiyar sa ta hannun mijinki danki Adamu ?"Anty ta zabura tana kai komo. Ta gaigiza kai,ko a mafarki Halifa ba zai aikata haka ba. Yanzu kin kara jin maganar akwatunan...... maganar ta katse lokacin da idanunta suka sauka akan gurin da akwatunan suke, shakku ya dar su a zuciyarta. Ina akwatunan ta furta a fili Hajiya Talatu ta kalli gurin da sauri,tace "Lallai kam hankali shi ke gani,Talatu ta furta ta mike ta nufi gurin tana fadin Sam ban kula da ba wani abu a dakin nan ba. A gigice Anty ta fita ta nufi falo tana kira Hafsa. Hafsa ta fito a gigice tana fadin "Lafiya Anty? Tace Halifa yaushe ya kwashi akwatunan shi?Hafsi ta taɓe baki wallah har kin tsorata ni. Da rana ya kira su Anty Umma da su Maman Nana suka raba suka tafi." Anty ta kara zaro ido bai taba ba kannenta wani abu ba shawarar ta ba,bare abunda yake dakin ta. Anty tace "Lallai sabon abu to ba matsala nima na kwashi rabo na ,gara ma ace su ya ba da ya ba waccan shegiyar matar tashi ko da dai na gama da babinta fatana su fusata su kai shi kotu kafin ya motsa na saka lauyoyin da za su ji min da shari ar, ta dubi Talatu Ina alfahari da lamari da ke. Hajiya Talatu ta ce 'Ni kuma fargaba ne ya cika ni, barin in hada kayana asubahin fari zan dauki hanya in tafi gidana sauran bayani zamu yi a waya tunda na miki me wuyar.Hafsi ta ce "Gara kam ki tafi domin wani huci na ga yana yi yau din nan yana cewa Anty Umma ku raba kuma yan uwana ne,kuma daga yau kowa babbane a cikin ku duk mai son wani abu ya kirani kai tsaye duk daya ku ke da kowa." Anty ta zauna ragwaf a bakin gado, lalacewar tawa har ta kai haka a gurin Halifa? Tabbas sako ya bada kuma ya iso,zan kuma same shi har dakin sa. Ta mike fuuu ta nufi dakin Halifa amma sai ta hange su tsaye da Dady suna tattauna wasu zan tuka da zata so jin abinda suke cewa. Kai tsaye ta nufi gurin su,abinda ta iya ji shine insha Allahu Dady ranar litinin a office din Barrister Sani makoda. Sai Dady yace Ina fatan dai lafiya in kuma maganar kudi ne in taho da listening abinda ke guri na.Halifa yace ka yi hakan ma,domin maganar ta shafi hakan. Shima Bros na sanar da shi. Halifa Anty ta kwada masa kira cikin tashin hankali .Ya kalle ta duk da duhun magariba tana iya kallon yadda ya daure fuska yana kallon ta ba tare da yace kala ba. Tace "Gidan uban wa ka kai Akwatunan nan? Sannan mitin din uban me ka ke hadawa!!! Ya Kalli Dady sai kuma ya nufi motar sa ba tare da ya yi magana ba. Hakan ya bata kwarin gwaiwar karasawa kusa dashi cike da gadara ta ce Ni sa ar ka ce harda zaka wuce ina yi maka magana? Ya daga Murya "Kama kan ki Anty!! Karfa ki kure ni!! Dady ka fada mata karta fusata ni ba danta bane ni, bata da wani karfi na hani ko Umarni a kaina fa!!!!Ya bude motar ya shiga ya tashe ta ya fita da mugun gudu gudu. Anty ta yi tsaye cike da mamakin irin daga muryar da Halifa ya yi mata, har su Hafsi da Talatu sai da suka leko ta window. Dady ya sa kanshi ya wuce ya bar ta tsaye cike da mamaki da tsoro. Ta koma ta zauna bakin gado suka yi shiru dukkan su. Hajiya Talatu ta mike ta janyo jakarta, ta shiga linke kayanta dake bakin gado. Hafsi Tace "Anty shawarar da zan baki ki rage matsawa Uncle Halifa akwai matsala sosai. Hajiya Talatu ta ce "Kodai ya samu labarin...Anty ta daga mata hannu ba wannan bane, Halifa ne ya dawo asalin Halifansa, fatana malaman nan su dukufa aiki,domin akwai katuwar matsala. Abinda ya daure min kai nake son sani yanzu wane shiri ya ke yi da lauyoyin ? Zaman me zasu yi harda Dady da Adamu? Dukiyar sa yake shirin karbewa ? Ina son sanin wannan amsar. Hafsi tace to Anty kije ki tambayi Dady mana bazai rasa sanin wani abu ba. Zaraf ta mike kamar mai jiran madafa ta nufi dakin Dady. Yana waya daidai lokacin yana fadin To da zaki barsu a gidan ko zaki rufe su ta baya ne? Ya danyi jim sannan yace, ok tunda Shafa tana nan shike nan kuje sai ki min message zan tura miki kudin Allah ya bashi lafiya da safe in na fito masallaci zan zo inga jikin nashi. Yana kashe wayar ya dago kai suka yi ido hudu da Anty. Duk da faduwar gaban da Dady ya ji amma sai ya dake, maimakon ta tambayi a binda ya kawo ta sai ta bige da tambayar Da wa kake yin waya? " Baki sansu ba. Ya bata amsa a takaice .Ta danyi tsam kamar me nazari . Sannan ta taɓa baki tace Halifa ya ke nufi da yace Me Halifa yake nufi da yace ku hadu ku yi mitin? Me yasa baki tambaye shi ba? Ya fada cike da daure fuska. Tace Au me kake nufi wai kaima kulle ni zaka yi? Dady ya zauna bakin gado "Dan Allah kije bacci nake ji." Ta fita tana huci ta zauna bakin gado inda Hajiya Talatu da Hafsi ke jiran ta. Hafsi tace Anty karfa ki saka wa ranki damuwa ki zo ki kwanta ciwo. Amma me Dady yace? Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce wai ni kuwa Hafsi Babanku na da yan uwa ne a nan Unguwar? Hajiya Talatu tace kaji wata maganar kuma an tambayi wani abu kema kuma wai kina tambaya.. Anty tace Talatu Alhaji na samu yana wata waya wadda ta daura min kai,shine nake tambayar ko yana da wata yar uwa na manta. Hafsi ta kalle ta "Me yake cewa,da wata yake waya wai Bintu. Hafsi ta sa dariya Anty kin manta ne da matar Abokin shi marigayi Bintu matar Alhaji b Baita.? Anty ta taba baki. "Wallahi shaf na manta, yana taimaka musu, ni kinsa ko a matan abokai in har baza a kira ki ki amsa ba to hanyar jirgi daban da ta mota. Ta sauke ajiyar zuciya dan jin hasashenta bai tabbata ba. Tace Dadyn ma yaki fada. Halifa tafe yake ko ta kan shagon Sulaiman bai bi ba ya nufi gidan su Asiya yana son zuwa ranar litinin ta tare a sabon gidan shi insha Allah. Gidan nasu a rufe da wani dan karamin kwada hakan yana nufin basa nan. Ya kira wayar ta kamar kullum a kashe sai yaji zuciyar shi tana hasala dan haka sai ya juya ya dauki motarsa ya tafi. Kasuwa ya wuce rai babu dadi, saidai yana zuwa yaran shagon suka bashi wata takarda inji wani mutum yace daga Kotu. "Kotu! Ya furta cike da mamaki bashi da abokin rigima ko daya waye zai yi karar shi. *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [10/1, 10:07] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Halifa ya sha mamaki ganin wai Asiya ce ke karar shi, ya shiga shago ya zauna duk da sanyin A C hakan bai hanashi zufa ba. To me ya yi mata har da zafi haka zata yi kararsa? Bayan shi da ta yi wa laifi yace kar ta fita ta fita,kuma taki yarda su hadu,ta tafi wani gari duk bada izninsa ba, sannan ya nemeta a waya duk abin ya gagara yaje gidan ma basa nan,shine yanzu kuma zata tsaya da shi a gaban kotu, gaskiya shi kam ba zai tsaya da ita a kotu ba,sai dai ta fadi duk abinda take so alkali ya yi mata kawai ya hakura, dan kila saki take nema,sannan zai dauki nauyin cikinta amma a sani da ta haihu zai amshi dansa. Ko da ba su yi soyayya ba,tana da wani mahimmaci a gare shi,tana bai taba sanin mace ba sai a kanta,kuma ita ce kadai ta ganshi a wani yanayi da ba zai iya fassara shi ba. Ya mike ya fita a shagon yaje mota ya zauna sannan ya kira Bros a waya, ya sanar dashi abinda ya faru da kuma abinda ya yanke. Bros ya cika da mamaki, yace "Ka kira waliyinta mana babu mutunci fa kuje gaban Kotu ku tsaya,kuma dole ne fa in alkali ya kira ka kaje,amma in kun samu masalaha a gida sai ta janye batun Kotu. Halifa yace Zan fi son hakan saki take bukata zan bata. "Karka yi saurin yanke haka, ka fara kiran waliyyin nata sai muji yadda za a yi. Halifa ya ja tsaki kan mace Bros bazan dauki rainin hankali ba, babu wanda zai mutu dan baya tare da wani. Yarinyar nan fa ta wani gefen alfarma na yi mata,amma wai har ita ta kai mutum!! Adamu yace "Haka ne amma abi komai sannu. Kamar yadda Hajiya Talatu tace,tana idar da sallar asubahi ta kama shiri ta kalli Anty wadda ta idar da sallar tana kwance tana ta saka da mugu zare. Tace "To Sahiba nifa zakara zai bani sa a, zan zarga wa kare na igiya in yi gidana bazan bari wancan bomb din ya tashii da ni ba,dan kuwa dole zai tashi.sai dai in har ki ka kiyaye abinda zan fada miki to ba shakka asiri ba zai tonu ba, ke koda asirin nan ya tonu to zai tonu a kuraren lokacin da sai dai su yi da sun sani. Anty tace Hakan ma in yafaru ni ce da godiya. Hajiya Talatu ta yi kasa da murya tace 'Kamar yadda na fada miki,wannan takardar sakin in har su ba jahilai bane kotu za su nufa shi kuma bai san zance ba yaga sammaci a zuciya irin tasa da kike fada ba zai je ba,saidai ya tura lauya to ke kuma sai ki maza ki siye lauyan kiyi ta tsara masa abinda zai fada masa da kuma yadda zai yi a kotu.' Anty tace Kash ga bikin zuwa amma babu zanin daurawa. Bani da kudin da zan baiwa lauya kina dai kallon rigimar dana dakko ta kudin mutumin nan gashi saura dari da Talatin duk na Bawa malamai. Hajiya Talatu tace Sai a kuma tambayar sa ya karo wani abu,naga fa kamar wani wawa sai sanda kika samu kya bashi. Anty tace 'Tab wannan fa daga gani dan tijara ne, amma dai bari mu gani in har suka kai shi karar ko ina ne zan nemo kudin dan dai inga bayan su. Hajiya Talatu tace Da kinyi kyan kai,yanzu dai ki samo min kudin mota in sa kai. Anty tace ko kwabo,ke din da duk kudin da kike min kwange ,ina kudaden da kika yi ta amsha gurin malaman nan ki na cewa zaki yi musu Transfer banga kin tura komai ba."Zan tura musu a hanya,network ne jiyan nan,zanci musu kudi ne?" Haka dai suka rabu suna ta yi wa juna ba a,da cin fuska. Tana isa gurin Get Halifa ya shigo daga masallaci. A tsorace ta kauce ta yi gefe. Ya ja dogon tsaki. Asiya ta na zaune kan gadon Asibitn kuka take kuma ta ki ci ta ki sha,bakin cikinta an kai Halifa Kotu,sannan sun ki sauraron ta tana fada musu akwai alkawura da Halifa ya yi mata ciki harda alkawarin ba zai taba sakinta ba,dan haka ita bata yarda cewa shine yayi sakin ba. Sai likitan ya bada shawara cewa a kaita Dawanau,akwai alamun Depression a tare da ita. Halifa ya shiga cikin gida ya sauya riga ya fita zuwa gidan Baffan shi bayan sun gaisa sai Halifa ya sanar da Baffan sa halin da ake ciki na kararsa da Asiya ta yi, sannan ya nemi shawarar Baffan sa game da shi hukuncin da ya yanke, na bada takarda a kai kotu. Ko kuma ya aika mata da ita gida.Baffa ya yi salati daga bisani ya ba Halifa shawara cewa ya koma gida,insha Allah zai taka har gurin Waliyyin yarinyar su yi magana. Da ciwon kai ya koma gida. Yana ta kai kawo ga takarda da biro tun jiya ya kasa rubuta saki, sai yana ganin kamar ya karya alkawuran daya daukar mata. Wata zuciyar tana ta zuga shi akan ya sake ta kawai tunda ita har ta iya kai shi kotu. Washegari Hafsi ta kwankwasa dakin yace shigo ta turo kofar tare da fadin "Uncle ga break fast din ka." Tafi dashi banaci, daga yau karki kara kawo min abinci dan Allah !! Ya daka mata tsawa .A gigice Hafsi ta fita. Anty kam dama ta san haka ce zata faru,Ada ma lokacin da bai fara zuwa kasuwa ba in yana fushi ba zai ci abincin gidan ba, kafin tasa a raunata mata zuciyar sa. Tace yarinyar nan da za su koma zama iya fushi da bakar zuciyar nan ta Halifa ka dai zata koreta gidan su. Hafsi tace lokacin da zan shiga naji yana ta maimaita cewa wai ni Asiya zata kai kotu. Menene me zafi har haka? Anty ta tashi tsaye tana fadin anzo gurin bani wayata ta soma neman wayarta cike da murna. Hajiya Talatu tana dagawa ko gaisuwa bare ta tambayi ko har ta isa gida,abinda kawai ta ce Sahiba sun kawo masa sammaci. Hajiya Talatu cike dariya tace Alhamdulillah. Komai ya zo kamar yadda muka tsara,da sauki, kije ki lallaɓa shi kiji komai dan mugano bakin zaren muna bukatar samun lauyan, ta yadda zamu saye shi ya yi mana aiki." Anty tace wai ba yanzu ba, dan kuwa a fusace yake da kowa'zai iya komai in ya hau dokin zuciyar nan tashi. Zanbi a sannu in dinga samo labari ko ba ta gurin shi ba. Baffa ya samu Abban su Sulaiman a bakin wapa inda suka yi mahada,sun tattauna game da matsalolin kafin suka tsaida shawara cewa Abban su Sulaiman zai samu Inna da yarinyar kuma duk yadda ake ciki zai sanar da Baffa. Abban su Sulaiman ya Isa gidan su Asiya ya yi sallama, daga ciki Sadiya ta amsa dama ita da yaranta ne a ciki Inna tana Asibiti da Asiya Sadiya ta fada masa cewa suna Asibiti bayan ta gaishe shi, yace To amma Yaya baku fada ba ko ke ba sai ki shiga ki sanar da Umman su Sulaiman ba?Sadiya tace an fada musu Abba inaga dai sun shafa a ne basu sanar da kai ba. Ya tambayi Asibitin ta sanar da shi, ya yi addu'a ya ce yaje gobe da sassafe ko kuma bayan issha yau in ya samu sarari. Sannu a hankali Halifa ya gama kwashe kayan shi ya kai su sabon gidan shi duk ba tare da kowa ya sani ba. Abban su Sulaiman ya kira Baffan Halifa ya sanar da shi cewa ya yi hakuri yarinyar bata da lafiya tana Asibiti in ta samu sauki za su zauna. Shima da safe zaije ya ga jikin. Ya samu Asiya tana zaune Inna tana ta godo da ita akan tasha kunu amma taki. Yace" Ki amsa mana ki sha magani ai sai da abinci." Inna tace ka ganta nan tunda mijin ya aiko mata da takarda gaba daya ta haukace, sai zantuka take yi wai wallahi bashi bane ya mata alkawarin bazai sake ta ba,wai sai abarta taje ta tambaye shi. Taki ci ta ki sha, sunce ma zamu je dawanau ayi mata gwajin kwakwalwa. Ga hawan jini sai ya sauka ya kuma hawa,Wallahi Malam ina yin dana sani akan wannan aure na gaggawa da aka yi huce haushi kawai ya yi amma sam Halifa baya kaunar yarinyar shida yan uwansa har fa cewa ya yi shi ciki ba nasa bane. "Subahanallahi " Abban su Sulaiman ya fada, abin har ya yi tsamari haka? Ashe har ya aiko da saki,ni da na zo ne akan batun kotu waliyinsa ya fada min suna son a yi masalaha a gida." Inna tace "Masalaha yanzu ne suke son masalaha tunda su masu dashi ne suna jin kunyar tsayawa a gaban alkali masalaha daya ce ya karbi cikin shi domin ba zai yiwu ya tarwatsa mata yau sannan ya tarwatsa mata kuma goben ta ba. Ta tashi da dan da bashi da uba,wa zai aureta, shi kanshi dan an tarwatsa masa rayuwa fa kenan. Abba cikin rashin fahimta yace "Wai tsaya, kina nufin cewa ya yi ba dansa ba ne?" Haka yace a jikin takardar daya aiko mata ta saki har uku. Na ce ko daya ma ya yi mata dama ni ba bari zan yi ta koma ba cutar ta isa haka. Abba ya yi shiru ya rasa abin cewa. Ya kawo dubu biyu ya basu yace "To ni zan tafi,insha Allahu zanje har can gurin Baffan na shi in ji." Asiya ta dago ido tace Abba dan Allah ka ce su barni in koma gidan mijina wallah bai sake ni, sharri ne kawai, wallahi ko da zai sake ni ba irin kalaman da ke cikin takardar zai rubutaba na san Halifa kuma na san me zai aikata. Abba yace "Allah ya baki lafiya lallai kam da matsala" Gara kuje a duba kan nata." Asiya tace Abba dan Allah a maganganuna ina ne na yi maganar rashin hankali? Ya ce 'Babu Asiya " Tace to me yasa ake jifana da kalmar hauka? Shiya sa nake yin shiru. Haka dai Abba ya tafi cike da jimami na halin da yarinyar ta tsinci kanta. amma kanshi a daure,domin shi Baffa bai fada masa cewar anyi saki ba,hasali ma dai ya nuna masa sun kai kara ne akan a bata takardar ta. Halifa ya gama shiri tsaf zai fita sai ga kiran bros yace masa lafiya yanzu na shigo gidan na samu ana rigima Anty Umma ta zo kwasar kayan dakin ka Anty ta hana kuma tana ta kiran wayar ka amma ba ka daga ba. Halifa yace na ga ni Bros kawai dai ban daga bane saboda bana son in fadawa Anty abinda yafi wanda na fada mata ran nan. Ni na tashi a gidan gaba daya na bawa Anty Umma kayan tafi Anty bukatar su. Da yake a hands-free Bros ya saka duk suna ji su Antyn. Lamarin ya girgiza Anty har ta fasa kuka yau ita Halifa zai guda sabodar matar sa,to wallahi in zata yi yawo tsirara sai ta raba shi da ita. Bros ya ce Anty kar ki dauki wani alhakin mana.Ita kanta yanzu haka bata gidan amma kin dora alhakin a kanta maimakon ki yi tunanin ina ne ki ka masa ba daidai ba ya za ayi kuma a gyara!! ""Kai ka min shiru Halifa haihuwar sa ne kawai ban yi ba,kuma kafin ya auri wannan yarinyar lafiya lau muke kowa ya sani,dan haka bazan bar wannan ya tafi a banza ba. Ta nufi ciki tana kuka. Halifa kuwa dama ya na kai karshen maganar shi ya kashe waya,sai dai kuma kukan da ya ji Anty ta saka ya tsaya mishi a zuciya. Ya soma tuhumar kan shi, wai ma akan wane dalili ne ya yi irin wannan fushin haka? Saboda abin duniya kudi abin banza. Kayan lefen me? Ya dauki waya kamar ya kira Anty amma sai ya fasa,domin ya san halinta yana kiranta dan ya nuna mata ya yi kuskure zata hau dokin zuciya sai ya yi ta bata hakuri zai jira ta neme shi tukunna. *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Asiya Ta bude ido dakin kowa ya yi bacci Inna ma tana kan tabarmarta ta tada kai da da kullin kayan su wanda Inna ta hada da safe za su tafi Dawanau ganin likita. Asiya ta sauka a hankali ta fice daga dakin, Asibitin ya yi tsit wannan ke nuna dare ya yi nisa Ina zata ga Halifa yanzu tana son ta samu tabbaci akan sakin da ya yi mata. Bata da kudin mota amma haka ta ci gaba da tafiya kanta ma gaba daya ya juye bata san ina take saka kafarta ba. Kadan wani mai kekenapep ya bige ta, yace ke Malama ta shi a hanya mana? Tace dan Allah ina neman hanyar Gandune gandun sarki .Yace Kina kan hanya amma dai ba a kafa zaki ba ko? Tace to dan Allah ko zaka taimaka min wallahi daga Asibiti na ke. Yace can din gun wa zaki je? "Ta ce gidan mijina zani. Ya saki baki yana kallonta. Yarinya ce karama kuma gata wata iri amma kuma kamar mai ciki. Yace kinsan gidan kuma yana nan mijin na ki? Sai lokacin ta tuna in kuma yana can gidan su Anty fa? Amma saita ji zuciyarta ta yarda cewa zata same shi a sabon gidan. Ta dube shi,in Allah ya yarda yana nan. Yace To hau muje amma ni da har na tashi daga aiki wai nawa ma zaki bada? Tace ko nawa ka ce zai baka muje kawai ta fada cike da kwarin gwiwa. Sun fara tafiya sai yace "Wai to ki kira shi a waya mana. Tace wayata ta mutu ko kana da waya ka ara min ?' Yace kin rike number ne?' Tace Na rike. Ya dakko wayar ya bata. Ta saka lambobin gabanta yana faduwa. Tana kira ta fara ringing sai dai har ta katse ba a daga ba. Ta sake kira sai aka danna busy Tace Allah ka bashi ikon daga wa, wannan ce dama ta Allah ka ceci aure na. Me a daidaita ya ce ko baya daga wayar da bai sani ba? Asiya tace yana dagawa dan kasuwa ne fa. Ta sake kira cikin sa a ya daga tare da sallama. Jin muryar shi sai tsoro ya kamata ta kasa magana. Yace "Hello ka na jina kuwa?" Cike da rawar murya Asiya tace Yaya ni ce Asiya kana ina ne gani nan zuwa. Ya maimaita sunan Asiya yanzu da tsohon daren nan daga ina ki ke tace daga Asibiti. Nan take Halifa ya zabura ya mike dazu Baffa ke fada masa cewa Abban su Sulaiman ya fada masa bata da lafiya har ana maganar zuwa dawanau dan haka su aje maganar a gefe sai yarinyar ta samu sauki. Yanzu haka abinda ya hana shi bacci kenan yana tunanin wane irin ciwo ne sai anje dawanau? Zuciyar sa ta zuga shi akan kar yaje Asibitin domin yaji matukar bakin cikin sammacin da aka kawo mishi. Ya ce Asiya to kuna ina yanzu? Tace kana sabon gida ne can zamuje. Yace Ina can ke da waye? Tace Dan sahune yace bashi wayar." Ta mika mishi yana amsa Halifa ya ce kar ka tsaya ko ina ka wota nan Gandun Sarki ya yi masa kwatance. Bakin layin ya fito ya tsaya. Sai ga su a dan sahu. Halifa ya tsaya cike da mamaki yana kallon yadda kiwon sa ya lalace, yarinyar ta rame ta yi baki ta koje,sai ciki kwi kamar an kifa kwarya. tana zare idanu. Ta nufo shi tana kuka ta shige jikin sa,ji ya yi gaba daya tana wani irin tsami. Ya dago fuskarta yace Asiya hakan da ki ka yi kuma adalci ne a gare ni? Bata yi magana ba,ya kalli dan sahu 'Nawa ne kudin ka?" Ya tambaya bayan ya rungumeta gefe daya yana laluba aljihunsa.Dan sahu yace kawai ka bada Megida aikin ma na tashi kawai dai taimakonta na yi can waje Tukuntawa na ganta. Duk da Halifa bai zaci zai samu kudi ba domin jallabiya ce a jikin sa,sai ya ci sa'ar samun wasu sabbin yan dari biyu irin wadan da yakan je da su sallar Asubahi dan rabawa sadaka. Bai tsaya kirga su ba ya ce to Oga gashi ka yi hakuri da wannan na gode. Dan sahu ya amsa yana fadin "Nima na gode megida." Har ciki Asiya ta yi karkadaf da Halifa kamar tana tsoron kar ya kwace mata. Sai da suka shiga lafo ya sake tsorata da hasken fitila ya bayyana ta sosai, idanu sun yi jajir ya zaunar da ita kan kujera ya dakko ruwa mai sanyi daga firji ya bude ya bata. Ta amsa ta kama sha har sai da ya tsorata wata zuciyar tana fada masa ko dai tabuwar hankalin da gaske ne Baffa ya ce za su je Dawanau,ya yi sauri ya amshe ruwa har tana kware wa,cikin tari tace "Yaya zan kara.' Ya bata tare da fadin To kisha a hankali. Ta shanye ruwan tas,sannan ya zuba mata madara mai sanyi cikin kofi ta shanye sannan yace in kara miki? Ta gyada kai. alamun e,ya kuma zuba mata ta kafa kai karshe dai sai data shanye madarar da ya ke sawo wa su kwana biyu suna sha. Yace tashi kije kiyi wanka. Ta shiga bandaki yaje ya tsaya ya hada mata ruwan zafi a bahon wanka yace ta wanke jikinta sosai dan tana tsami sai ta kuma hada wani ruwan ta kara wanke wa. Ita dai kai kawai take dagawa, domin mugun ciwon kan da ke damunta yasa tana jin kan kamar ba a jikinta ba. Ya dawo yana dubawa ko zai ga kayan da zata iya sawa,amma babu kayanta a gidan sai wadanda ba a dinka ba duk dinkakkun ya kai mata.karshe ya dakko jallabiyar sa ya tafi bandakin dan yaji shiru. Turus ya tsaya bacci take a ruwan ta cuda jikin bata dauraye ba.A tsorace ya karasa ya girgiza ta ta bude ido luuu ta kuma lumshe su.Ya koma ya cire ya dawo daga shi sai gajeren wando,ya zage ya wanke ta tas ya dauraye ya nado abar sa a tawul. Ya kwantar da ita ya ja bargo ya rufe ta.Ya dan rage karfin Ac, ya zauna bakin gadon yana kallonta, fargaba ya cika zuciyar shi,ya rasa wa zai kira ya ce gata nan ta zo. Daga baya kuma sai ya yanke shawarar yin shiru da bakin shi haka zai taimaka ya san wasu abubuwan dake bibiyarta. Sai dai akwai bukatar likita.Nan take ya kira likitan da suke zuwa gurin sa ya fada masa yana da mara lafiya da yake son likitan ya taimaka ya zo ya duba masa. Likitan yace Har ya kwanta amma yana jin nauyin irin alkhairin da Halifa ya ke masa dan haka yace To ya kwatanta masa gidan zai zo. Kusan mintuna Talatin sai ga likitan ya zo Halifa ya zura mata jallabiyar sa sannan ya shigo da likitan Gwajin farko na hawan jini ya ga ya haura dari biyu,ya tsorata sosai ya ce wannan zai iya taba mata kwakwalwa tun yaushe take fama da ciwo? Halifa yace wallahi bai sani ba jiya ta zo daga gidan su. Likitan yace To zai mata allurar bacci tare da wasu allurai ya barta ta yi baccinta sosai ko ta kai rana bata farka ba kar ya tashe ta,sai ta tashi dan kashin kanta sai su zo Asibitin. Halifa yace Ranka ya dade ka yi hakuri ko nawa ne zan biya ka dinga zuwa kana dubata a gida. "Ba damuwa in ta farka sai ka sanar dani. Likitan ya fada da sauri.Halifa ya raka shi mota tare da fadin Yallabai katuro min da account. Dr yace Ina godiya Alhaji. Dr Yana jin dadin yadda Halifa yake girmamashi. Duk da ya kula haka dabi ar shi take yana da girmama kowa. Ya koma Shima ya kwanta ya zuba mata ido yana kallon ta bai yi wani bacciba sosai kadan kadan ya farka.. Ya dawo masallaci yana zaune a falo ya daga waya ya kira Baffa yana tambayar shi ko ya labarin jikin Asiya din yana son sanin inda magana ta kwana dan zai yi tafiya ne zuwa Dubai. Baffa yace bai sake tuntubar su ba,amma ya dan yi hakuri zuwa ta warware. Sannan yace ya daure yaje ya dubo ta. Halifa yace sai in ya dawo domin nan da awa daya jirgin su zai ta shi. Halifa ya yi haka ne dan kar ko cigiya ta biyo ta gurin Baffa ya kawo shi a ransa. Dan shine kadai ba zai iya yi wa karya ba.Ya kira Bros ya fada masa cewar ya tafi Dubai. Inna ta samu bacci domin yau babu koke koken Asiya da alama itama ta samu bacci.Wani ikon Allah bata kula babu Asiya a gadon ba har sai da ta idar da salla ta soma hada kaya dan da wuri zasu tafi Dawanau din dan ganin likita. Taje tashin Asiya ta yi salla sai ta ga gadon babu kowa,ta daga abin rufar da sauri ta yi bandaki kafin minti goma labarin bacewar Asiya ya baza Asibitin. Aka ce taje gida ta gani ko can taje,sai kuma ga Sadiya da kokon su na kari,tace Asiya bataje ba. Inna ta soma kuka Sadiya kuka. Likita yace shi dai tsoron shi kar ciwon ya yi karfin da zuciyarta zata dinga bata umarni mara kyau kuma ta na bi.hakan babban hadari ne in ba a kula ba sai taje ta fada wuta ko ruwa wanda zai halaka ta. Haka suka bazama neman ta ga shi su ba waya ba bare duk inda suke zaton cewa tana can su kira su ji . Nan fa Unguwar ta dauka Asiya ta bata a Asibiti wasu su ce ance ta haukace ne har mutane suka soma ba Inna shawara wai su bi bololi su duba. Haka Inna suka gama yawo har sha daya na dare suka fawwala wa Allah suka dawo gida suka zauna. Sai kuma gobe su ga ta inda za su fara. Asiya bata farka ba sai karfe biyu na rana. Halifa ya tsorata amma likitan ya ce masa babu komai da yake suna waya. Ta yi mika da salati ta bude ido, ashe dai ba a mafarki bane gidan Halifa ta ke, ta tashi da sauri ta zauna a tsakiyar gadon. Halifa ya fita ya karbo abinci a restaurant yana shigowa ya ganta a zaune. Da sauri ya kara so ya na fadin kin tashi babyna,baby na ya jikin naki? Asiya ta lumshe ido tana kallon abincin da ke hannun shi. Ya ce zaki ci? Ta daga kai alamun e. Ta kama abinci ta cinye a take away din ko plate bata bari an dakko ba,cikin mamaki yace ko a karo miki? Sai lokacin ta yi magana ",Na koshi. Yace Alhamdulillah tun jiya sai yanzu kika yi magana har na fara tsorata,yanzu me yake miki ciwo? Tace "Kai na ne ya ke yi kadan kadan kuma ya yi min nauyi sosai." Yace zai bari likita yana zuwa. Kiran likitan ya katse masa magana. Ya daga yace masa ya shigo. Likitan ya duba hawan jininta ya dan ragu akan jiya,yace Insha Allah zai sauka da sauri tunda bata kumbura ba saboda ciki hakan ba zai shafi abinda ke cikin ba. Saidai tana bukatar a kwantar mata da hankali,duk abinda zai daga mata hankali ko ya sata tunani a yi kokarin kauce masa. Yace shi kanshi likitan da ke kula da ita bai san aikin shi ba,tana da irin wannan hawan jinin bai sha kan matsalar ba kuma zai tura su wani Asibitin. Ya bada magunguna kuma zai ci gaba da zuwa duba ta har ta warke,sannan ya sake bada shawarar kar a barta cikin hayaniya. Halifa ya kudirci ba wanda zai san inda take. *Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [10/16, 10:31] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w Inna sun gama sarewa amma dai sun kai rahoto tare da hoton Asiya karkashin jagorancin Sulaiman. Sulaiman sun yi magana da Halifa ta chat cewa ba a ga Asiya ba. Halifa ya nuna wa Sulaiman damuwar sa musamman saboda cikin da Asiya take dauke da shi, yace yana Dubai amma zai dawo duk da bai gama abinda ya kai shi ba sannan Yace wa Sulaiman dan Allah ya yi iya kokari shi dan ganin an samu labarin Asiya. Labari ya riski Anty farin ciki kamar me bata boye ba sai ma tunaninta ya tsaya akan aikin da ta sa malaman ta ne ya ci Asiya. ,. Inna ta rasa wane irin tunani zata yi ta yi kuka ta yi addu'a tace dama Asiya mutuwa ta yi ta ga gawar a gaban ta da sai ya fiye mata wannan bakin cikin. Wasa gaske yau gashi har kwana uku,Inna ta gama debe tsammanin har wata gawa suka je suka duba da aka ce an tsinta a ruwan jima, su ka ga ba ita bace ta dawo gida ta ci gaba da addu'a amma a kasan zuciyar ta tana zargin wani abu. Cikin kwana uku Asiya ta dan murmure ta dawo ciki hankalin ta. Halifa ya siyo mata jallabiyoyi da riga da wanduna dan ta ke sakawa. Suka fita da dare suka tafi dan a wanke mata kai. Ta yi kyau matuka sosai, ga turaruka ya saya mata tana ta kamshi, ya kai hannu ya shimfida su akan nata da ta aje a gefen ta, ya dan murza yace Asiya har yanzu ina mamakin yadda ki ka iya share ni tsawon watanni baki tunanin halin da zan shiga ba ki kusa da ni ko bayan ke kinsan mijinki bashi da juriya? Sannan wai har ki ka iya kaini kara kotu Asiya ina mamakin ki fa. Asiya tace Yaya wallahi ba ni bace itama Inna taji haushin takardar sakin da ka aiko min ne.Bai san lokacin da ya taka birki ba, tare da fadin saki? Har ya rage kaɗan wata mota ta daki bayan su.Bai damu da me mutane suke fada ba, a gurin ganin yadda ya kusan hada hatsari. Tambayar Asiya ye ke yana maimaitawa . Saki fa ki ka ce,waye ya kawo takardar? Asiya tace "Kana nufin baka aiko min da saki ba?" Yace Haba Asiya ke yanzu sai ki yarda in aka ce miki na sake ki? Asiya tace dama ni banyarda ba tun da aka kawo sakin, saki uku kuma aka ce in nemi Uban dana kai ba cikinka bane. Takai karshen maganar tana kuka. Ya gungura motar gefen titi lokacin da ya fahimci mutane sun fara ce masa bari su tura masa ita ya tare hanya,a zaton su ta lalace ne. Asiya taci gaba da fadin "Nafadawa Inna ba kai bane baza ka sake ni ba munyi alkawarin hakan,kuma yadda nayi Imani cewa ban kawo namiji daki na ba,haka na yi Imani cewa kai ma sharri ne. Shi ne su Inna suka ce kaina ya tabu wai na haukace,Ina ji ina gani aka dora min hauka. Dole na karba domin sun fini hujja, wannan damuwar ce ta hanani bacci na kwanaki ta hana ni ci da sha,domin gara in mutu bani da wani amfani ina raye kana raye bama tare. Ban san so ba kai ka koya min,ban san namiji ba kai ka sanar da ni,kai ne ka sa nasan cewa ni din mace ce kuma mai dauke da wata daraja da ni'ima da Allah ya bani ta Yaya zan barka. Halifa ya rungumo Asiya cikin wani irin yanayi ya ce 'Muje gidan su Inna yanzu in tabbatar mata da sharri ne ake binmu da shi ba ni ne na sake ki ba, Asiya hakika lokacin da na aure ki wallahi fushin zuciya ne ba wai son zuciya bane,amma da na zauna da ke sai na gane ashe da sha awa da kyale kyale ke ɗiba na, ke nake yi wa asalin so da kauna yanzu. Dan Allah muje in fadakar da su." Asiya ta kai hannu ta shafi kumatun Halifa Kar muje yanzu domin Inna tana da matukar sauki amma kafin ta hau dokin naki,yanzu abu daya ne zai sa Inna ta yarda, shine aje mata da hujjar cewa baka sake ni ba,abin nufi sai ka nemo wanda ya shirya sakin iya maganar fatar baki baza ta wadatar ba. Sannan zaka iya yin abu daya,ka je a zuwan ka dawo daga tafiya kuma kaji labarin ɓata na, nasan maganar saki zata ta so sai ka fada mata ba kai bane,daga nan sai ta sanar da kai wanda ya kawo takardar ta haka zaka iya binciko ko wanene. Halifa yace Allah ya min baiwa da ya bani ke, kina da basira. Yanzu bari muje gida sai mu kara tattauna yadda zamu bullowa lamarin. Inna ta kalli Sadiya bayan sun dawo daga dan kara zagawa neman Asiya,tace nifa jikina yana bani Asiya ko gurin mijin nan nata ta gudu, ki leka shagon Sulaiman ki ce ina nemansa. Sadlya tace "Anya kuwa Inna, nafa tambayi Yaya Sulaiman din yace min ya yi tafiya amma bari na dubo miki shi. Bayan sun gaisa Sulaiman ya ce Inna an samu wani labari ne? Inna tace 'Ko kadan,kawai dai wani zargi na ke yi game da mijin Asiya, kamar tana gunsa bayan ya yi mata sakin nan har uku,kasan ance Allah yasa jarabtar su da son macen da suka yi wa saki uku.ko ya jarrabe su shi da ita.' Sulaiman yace Kai Inna ina shakka,domin a sanin da na yi wa Halifa ba zai yi hakan ba,shifa ba ma ya nan yana Dubai yace min dai zai dawo saboda faruwar wannan matsalar,kuma za a ganta insha Allahu zai kokarta. Inna tace To Allah ya sa a dace,dama wannan ne dalilin kiran. Saidai ya bar kokarin shi bana so,yaje ya samu wadda ta dace dashi zamu nemota da kan mu,indai addu'ar Mahaifiya tana aiki. Sulaiman yace Inna Allah dai ya sa mu dace. Yawan addu'a ya sa wa Inna dangana da kuma yan uwanta da suka zo jaje suka kwantar mata da hankali. Sai dai kukan zuci. Halifa yana kwance rigin gine Asiya ta tada kai da kirjin shi tana lallashin sa akan ya tashi ya tafi gidan su Inna dan ya gano mata halin da Inna ke ciki. Shi kuma yana cewa shima a yi masa alkawarin yau za a bashi hakkin shi tunda dai sauki ya samu kuma sun tambayi likita yace babu matsala za su iya yin mu amalar su ta aure. Tace to naji amma so daya.Yace Haba baby ko ba a dade haka ba kin san dai ya yi kadan. Wayar shi da ta hau ruri ce ta hanata magana. Yace Anty ke kira kinsan na bude wayar domin na nuna musu cewa na dawo. Ya daga da sallama. Tace "Halifa manyan gari, duk yadda na so in yi fushi da kai bana iyawa, amma kai yanzu ka ma tare a gidan ka ni ban isa ka sanar da ni ba saboda na taɓa maka abin duniya, to ba komai Halifa zan biya ka ka rubuta ko nawane in ma bansamu ba ya zama bashi ko na mutu yarana su dauki nauyi su biya ka....Takai karshen maganar tare da fashe wa da kuka. Hankalin Halifa ya tashi yace "Anty ai kinji ke matsalar ki komai kuka dan Allah ki yi hakuri ni na yafe kayan kin fi karfin su a gurina kawai naji haushin a bin ne amma ya wuce." Ta ce Ya kuma labarin yarinyar nan ashe ta bace ko? Halifa ya kai hannu ya shafi cikin Asiya sannan yace" Abinda ya dawo da ni kenan daga Dubai Anty ya za ace yarinya ta bata kamar wata kaza." Anty tace ni da zaka yarda wallahi da ka share su kar ka shiga zancan nan tunda kai ba a gidan ka ta bace ba, ai danake fada maka tana da ciwon hauka ai baka yarda ba,yanzu dai gashi yar fara ta nuna. .Halifa yace "Ta ya zan kyaleta da cikina a jikinta?"Anty dan Allah kar ki fadi wani abu da zanji babu dadi. Ta dan yi shiru sannan tace "Shike nan Halifa amma ka bi a hankali Allah ya bayyana ta,dama ni dan naga yanda yarinyar ta kawo mana kwar.... "Antyy" Ya katse ta da sauri, ya ci gaba da fadin, karki karasa wannan maganar bana bukatar ta.! Tace Na yi shiru kana sabon gidanka ne? Yace Hotel na sauka,anjima zan shiga gidana,zan shigo nan gidan ma zuwa dare ya katse wayar domin tuni idanunshi sun kada sunyi jajir. Mai siyan akwatuna ya Isa kofar gidan Anty da babbar mota,ya shiga yana sallama. Nihal ce to sanar da Anty ta yi bako. Gaban Anty ya fadi lokacin da ta yi ido biyu da shi. Ta daure fuska ta iso gabanshi. Lafiya malam da sasafen nan zaka diro min gida? Yace dole In diro kin ki daga min waya bayan yarjejeniyar mu ta cika shiyasa na shigo cikin biyu a yi daya a bani kudina ko kayan kudi ga mota can waje. Anty ta ce "In kuma babu fa?" Yace dole ma akwai. Hayaniyar su ta tada duk yan gidan. Dady ya tsaya kallon mutumin cike da takaici yace kai me ya kawo ka cikin gidan matar aure? Mutumin yace ita ta gayyato ni,ai ni na zata ma bata da miji. Dady yace "Ni ba abinda na tambaye ka kenan ba, abinda kawai nake son in sani me ya kawo ka yanzu?" Yace kudi na ta ara akan zata saida min akwatuna, miliyan daya, daga baya tace dama na kaninta ne kuma ya kwashe kayansa, amma kudin ta ara,na fada mata sati biyu zata dora min ribar dubu dari biyu da hamsin ta yarda,gashi yanzu an kusa wata bata daga kirana,yanzu dai kudina a gurin ta miliyan daya da rabi da dubu saba'in, dan kullum kwanan Duniya kudi na karuwa suke yi. Dady ya dubi Anty rai bace, yace ki bishi waje kuje ku yi case dinku a can dan Allah. Ku fita waje! Anty Ta dubi Dady cikin wulakanci tace sai dai kai in bazaka iya ji ba ka fita domin dai gidan ba naka bane kuma bana wanin ka ba. Dady yace "Ko sarkin gori,to albishirin ki, yanzu wannan gidan mallakina ne, Halifa ya mallaka min shi ya bani takardun sa haka wanda Adamu ke ciki ya mallaka masa ya bashi takardunsa!! Anty bata san lokacin da ta kai kasa ta zauna ba,sai da taji su Hafsa na fadin Anty kiyi a hankali.ta dafa ta. Ta kalli Dady Kasan Allah bazata sabu ba, kura da shan bugu gardi da kwashe kudi. "Kiji da ni dan Allah. "Mutumin ya katse ta,cike da bala'i tace kai bani da su bani da dalilin su ,haukatani za ku yi ? Ta fashe da wani irin kuka na tsananin takaici. Dady ya dube shi yace shigo ka duba duk abinda ya kai darajar kudin ka ka dauka amma kaima ka yi Don Allah. Ya koma ciki ya shirya zai fita lokacin suna fita da kujeru Ko kallon su bai yi ba ya wuce. Anty ta na kwance ta sa Hafsi ta kira mata layin Yayansu ya daga Anty ta karba ta ce kazo yanzun nan ina nemanka duk inda kake ko me kake ka bari kazo. Bros ya saki baki yana kallon Falon Anty ba komai ba kujeru bare firji ba TV Ya nufi dakin ta,turus ya yi da ya ganta a kan katifa ga shirgin kaya wandan da su ke cikin sif An tule su gefe. Cike da mamaki yace Anty lafiya? Ta dubeshi "Wato har na yi lalacewar da zaku hada kai da Dadynku da Halifa ya baku gida ya mallaka muku amma ban sani ba, kuma ban isa ayi shawara da ni ba ko?" Bros ya ce wallahi Halifa ne ya hana mu fada wai zai fada miki in lokacin hakan ya yi,amma ya ba Dady takardun gidan nan da ya amsa a hannun lauyoyin sa,sannan nima ya bani nawa gidan da nake ciki.Anty tace magana dai ta tabbata. Hummm lallai Halifa ya dauka da zafi daga taba kayan akwatin sa shine yake ta min irin wannan ramuwar gayyar!! Hafsa tace "Kema Anty na fada miki fushin fari ba naki bane ki kira shi a waya kiyi masa godiya karki nuna kinji haushin komai sai kiga ya baki naki rabon ki samu ko gado ki saya." Uban gado Anty ta katse Hafsa suma ba su wahala da shi ba ya basu gidaje bare ni da nai rainon sa? Adamu yace 'Haba Anty infa ya bamu tamkar ya baki ne, ke yanzu me zakiyi da gida? Burinki bai wuce ki barma gado ba,to mun yafe karki damu, kina karkashin Dady ne,shine cinki da komai,dun radda babu Dady mu gamu zamu rike ki.....'.Kai Adamu sa idonka cikin nawa. Anty ta fadi tare da Mikewa zumbur. Kana nufin ni yanzu na tsufa bani da sauran lokacin da zanyi wata rayuwa mai dadi?In yi gayu in hau mota in fita kasashe inga gari..... ✍🏻 *HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [10/27, 09:26] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt Adamu yace Haha Anty ya kamata ki daina zafafa al amura,kina dagawa kanki hankali ko masu yawo kasashen da kike magana da yawa dalili ke kai su daga kasuwanci sai ciwo masu yawan shakatawar a wannan karnin ba su da yawa. Amma in kin yadda,ki yi zamanki kiyi istigfari in Allah ya kawo hajji ko Umra sai ki je kiyi adda"a kema ki huta da damuwa. Anty ta girgiza kai tare da fadin "Bashakka,dole ka fadi haka tunda kun rufe min alkhairin da dan uwana ya yi muku, amma ba komai. Yanzu sai ka fada min dalilin da ka daina zuwa gidan su yarinyar can." Ya dan yi jim sannan ya ce Anty In fada miki gaskiya ko kuwa in yi miki karya? Ta dube shi menene ribar karya,kawai ka fada min gaskiya. Yace kiyi hakuri Anty wallahi bana son yarinyar nan ne. "Kayi kadan ta katse shi ,ciki. daga murya ta ci gaba indai ni ce na haife ka wallahi sai ka aureta....Jiri ne ya debeta sai gata wanwar ta fadi kasa ba tare da kowa ya ankara ba. Agigice suka kama ta suna mata sannu.Adamu yace muje Asibiti Anty ta dafe kai tana fadin kaina ciwo yake min. Aka kwashe ta zuwa Asibiti Bayan gwaji likita ya gano cewa Anty jininta ya hau dan haka ya kamata ta kwanta a Asibiti . Anty ta buga kafa tace ita fa baza ta kwanta ba, gida zata koma dan tana da abubuwa a gabanta. Hafsi tace to Anty gida kuma akan me zaki kwanta ba gado ba kujera. Sai suka ga Anty ta saka kuka. Abinda ke bawa Adamu haushi duk wannan halin da Anty ke ciki babu wata nadama a tare da ita. Badan ta so ba ta kwanta. Adamu ne ya kira Halifa ya sanar da shi cewa Anty tana Asibiti. Sai dare yaje tare suke da Asiya sai ya barta a mota. Ya kalli Anty duk ta rame, yace "Anty wallahi ki daina damun kanki game da wa su lamura da basu shafe ki ba. Yanzu me likitan yace? Tace "Ni kawai ka ce masa ya sallame ni zan sha magani a gida ina da sabgogi da yawa a gaba na, wannan kwanciyar zata kawo min cikas. Wane irin sabgogi kenan kike magana? Halifa ya katse ta. Hafsi tace Uncle ko ta koma gida fa wani mutum ya zo da mota ya kwashe kayan gidan duka. ,"Kamar Yaya? Halifa ya tambaya. Kafin Hafsi ta amsa Anty ta fara wani irin nishi da kuka ,dole suka maida hankali a kanta. Kuma ta yi haka ne dan kar ta fadawa Halifa maganar. Halifa dai ya fada wa likita lallai kar a sallameta sannan duka abinda take bukata a yi mata. Da suka bar Asibiti kai tsaye unguwar su Asiya sukaje ya aje motar Inda ya saba ajewa sannan ya tafi gidan su ya bar Asiya amotar yace ta jira shi kar ta fito. Ya kira Sulaiman suka tafi gurin Inna. Tana zaune tsakar gida ta zabga tagumi Sulaiman ya shiga ya sanar mata zuwan Halifa. Inna tace To kuma me ya zo ya yi min bayan ya yi min silar diyar tawa. .Sulaiman yace Inna duk ba wannan bane ki saurare shi muji abinda ya kawo shi, domin shima yana cikin tashin hankali yau din nan ya dawo daga Dubai ya kasa hakura gari ya waye ya taho kuma kin san bai fa gama abinda ya kai shi ba ya dawo. Inna tace "Ummm Ai sai ya shigo din muji kuma wace karyar zai yi min. Asiya ta ce kai a zo har Unguwar nan in tafi banga Inna ba,kai gaskiya dai da sake, ta duba lokar mota ta dakko face marks ta saka ta fita tunda kayan jikinta irin rigar nan ce wadda ke hade da mayafi ta san ba wanda ya san ta da kayan. Unguwar su ce ta san duk wani langu mara haske dan haka ta sakada ta isa kofar gidan su har ta ci karo da Abba suna fada da wani yaro yaki kamar ta raba su sai kuma ta tuna, ya sheko da gudu ya bige ta ya waigo yana fadin yi hakuri,ta ki kallon shi amma shi sai ya tsaya yana kallonta ta dan waigo ta ga ya tsaya kamar yana son ya gane ta sai kawai ta wuce gidan ta yanke wani lungu ta tsaya, ta dan leko sai taga shima ya biyo zai leko lungun sai kawai ta ci gaba da tafiya.Taji ya daga murya yace "Asiya! Asiya!!! Kai gaskiya sun yi kama ashe ba ita bace." Ya fada tare da juyawa. sai da ta tabbatar ya fita a lungun ta fito ta fada gidan su ta makale a soro. Tana jiyo yadda Halifa ke yi wa Inna rantsuwa da abinda zai kashe shi cewa bashi da wata masaniya akan sakin. Inna kuma ta dage akan cewa gaskiya dai Asiya ta saku duk ranar da Allah ya bayyana ta to gaskiya dai ba matar shi bace. Cikin dai in ka yarda na ka ne to ba maganar kotu. Halifa yace Inna "Dana ne kuma mata ta ce, Asiya Allah shine ya tsare ni da ganin ranar da zan furta kalmar saki ga Asiya, me ma zata yimin har haka,wallahi Inna makircine kawai na wadan da ke bibiyar mu.Abinda kawai za ayi shine in har zaki gane Yaron da ki kace ya kawo sakon to abin zai zo da sauki zan gano wanda ya rubuta wannan takardar. Inna ta ce "Zai wuce Antyn taka ce ta ke aikatawa,domin dai bata kaunar yarinyar nan,har gidan nan ta zo ta fada min, kai ni ai ko bakai ka yi sakin nan ba, dole ka hakura da yarinyar nan,dan bazan jure ba sam." Halifa yace To Inna yanzu dai ki kwantar da hankalin ki zan yi bincike tare da kokarin gano inda Asiya ta ke, daga nan kuma ko mai zai warware dan Allah Inna kiyi hakuri insha Allah zan nemo Asiya. Tace "Allahu ya bayyana ta. Sai dai fa kamar yadda nace hakuri dai za ayi ko ka ganta yadda yan uwanka basa sonta. Da sauri Asiya ta fita ta koma gurin mota domin kar Halifa ya fito. Tana cikin motar tana kallon dawowar shi,Halifa namiji ne kamar irin na littafan nan da zaka ji ana fada, kowace mace zata so ace Halifa mijin tane ya kai namiji ko ta ina. Yana ta dorawa yara tare da Abba kayan abincin da ya sai musu ita bata san ma ya siya ba. Ya rungumo ta bayan ya shiga motar, yace kyakykyawata insha Allah Inna zata hakura amma ba da gaggawa ba, sai dai munbi mun gano kowaye ke aikata wannan sharrin .Asiya tace "To Allah ya tona shi. Ya sake ta suka kama hanya duk sun yi shiru kowa yana tunani. Halifa ya katse shirun da fadin, "Baby, shin akwai wani wanda ki ke zargi ne ke? Asiya ta dan yi dim sannan tace "Anya kuwa?" Yace Inna ta fada min wasu abubuwa da Anty ta yi miki wanda ni bansan da su ba,kai tsaye Inna tana zargin Anty ce ke shirya duk wadannan abubuwan. Asiya tace "Gaskiyar magana Yaya ka yi hakuri amma ka binciki Anty sai dai ina rokon ka kabi a hankali kuma ni abinda ya sa kaga ina ta rufe maka komai saboda na ga irin tashin hankalin da ka ke shiga ne game da lamarin Anty. Halifa ya numfasa ya ce Asiya kamar yadda ki ke so da kaunar Inna haka nake son Anty,bansan Uwata ba ita na sani, duk wata Soyayya da da zai yi wa Uwa ita nake yi wa Anty. Amma a wayi gari tana yimin irn wadannan abubuwan kice bazan shiga tashin hankali ba. Ya kai karshen maganar da kai duka jikin sitiyari tare da rishin kuka. Asiya cike da tashin hankali tace Yaya to ka tsaya muyi magana yi fakin. Bai saurare ta ba ya ci gaba da tafiya cikin wani mugun gudu har gida. Ko kashe motar bai yiba yafita ya nufi cikin gida. Asiya ta rasa yadda zata yi ta kashe motar cike da tsoro Allah ya sa ta murda makullin sai kuwa motar ta mutu. Ta nufi ciki sai dai wani abin tsoro ta same shi ya yi fashe fashe ya yi jifa da abubuwa a falo yana dada kai wa bango duka yana cewa yanzu da wa kuma zan yarda in har uwa zata cutar da danta. Hannuwan shi suna zubar da jini. Da gudu ta je ta kwakume shi ta baya tana fadin haba Yaya sai kace ba musulmi ba, hankade ta ya yi, ta fadi cikin kirsa ta ce wayyo Allah cikina. Da sauri ya nufo ta cike da tsoro yana cewa Baby ya daga ta cak zuwa kan gado ya kwantar kin gani ko shiyasa bana son in raina ya baci a zo kusa dani, me nene tashi babyna kinji ciwo? Ina waya ta bari in kira likita. Baiga wayar ba dan kuwa can ya baro ta mota. Tashi in kai ki Asibiti. Asiya cikin nishi ta kama hannun shi ba zan iya ba ka bari cikin ya dan lafa sai muje. Ya zauna yana mata sannu ta ja ji ki ta dora kanta a cinyar sa yana shafa mata kai tana nishi har dai ta gaji sai ta yi lamo kamar ta yi bacci, shi kuma yana zaune ya zuba mata ido wai baya son ya motsa kar ta tashi. Kusan minti goma sai ta dan motsa ta tashi zaune ya kai hannu ya shafa cikin ta Yaya kinji sauki. Ta tura baki,na ji sauki, Yaya ashe zaka iya duka na?" Yace "kiyi hakuri in raina ya baci ne ban iya fushi ba, ki daina zuwa in kinga na fusata. Asiya Ta ce "To yanzu sai ka tashi kaje a wanke maka hannun ka ko? Yace ai ya daina zuba zan gyarashi yanzu akwai akwatin gaggawa. Kwanan Anty uku a Asibiti kullum Halifa yana zuwa kuma shine ya biya kudin Asibiti. Bai nuna wa Anty komai ba. Yanzu abinda Anty ta gane yin amfani da rashin lafiya dan ta tursasa su. Saboda likita yace kar a dinga bata mata rai . Halifa ya sake sai mata gado da kujeru yace Bros ya sai mata TV da sauran su. Haka kuma ta uzzura batun auran Bros babu dama ya yi gaddama dan tsoron kar ciwo ya ta shi su ke yi ,dan abu kadan sai ta soma jirin karya kamar zata fadi sai an kamata an zaunar. Cikin Asiya yana ta girma sauran wata daya ta haihu tuni duk wani abu da ake bukata Halifa ya siyo musu shi. A na tsaka da bikin Bros wanda Anty ta matsa sai anyi, ta tilasta ya gyara gidan da Halifa ya bashi nan zasu zauna da amarya. Bros bai halarci komai na bikin ba,yana gida tare da matar shi yana lallashin ta,kukan ta daya ita dai kar ya canja mata. Ya kuma daukar mata alkawarin kar ta tashi hankalinta ita kadai yake so. Asiya tana kwance jikin Halifa tana mishi mitar ita dai kar yace zai kara aure dan ita wallahi baza ta zauna da kishiya ba. Halifa yace bazan miki alkawari ba, Mahaifina matan shi hudu,ance har ya rasu hudu ne suka yi masa takaba,kuma ance ko wata ta mutu ko ta fita baya jimawa yake maye gurbin ta. Ya dago fuskarta suna kallon juna yace nima kuma akwai alamar haka Baby in har zaki kula za ki min adalci ga yadda nake damun ki,da akwai wata yadda cikin nan na ki ya girma ai da kyale ki zan yi sai kin haihu. Asiya ta turo baki tace "Amma ka fadi tsakani da Allah na taba raki ko in hana ka hakkin ka, ko so nawa ka bukata bana nuna gajiyawata." Halifa yace na sani kina kokari,amma ki sani in kika haihu dole mu hakura. Sam Asiya bata san tana da irin wanna kishin ba, ji ta yi wani abu Yama mata tukuki a kirji,ta soma kuka,kamar wasa sai ciwon baya,sai mara. Duk basu san haihuwa bace, dan sun ga wai EDD dinta da saura yana ta lallahi yana fadin wasa ne amma abu sai ta azzara ya ke ga dare Halifa ya kira likita yace ya kaita Asibiti shima yana gurin zai yi wa wata tiyata ne. Asiya ta ji ciwon da bata taba jin irin sa ba, dan haka ta shiga neman yafiyar Halifa da kuma bada sako zuwa ga Inna........... *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [10/30, 22:19] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt Ganin yadda ta ke shan wahala likitan ya bada shawarar kawai ayi mata aiki ya kara da cewa dama ta yi karama kwarai da haihuwa kawai dai ya bari ya ga ko zata iya haihuwa ne da kanta. Take Halifa ya sa hannu aka soma yi mata shirin shiga tiyata. Ana yunkurin saka mata ledar fitsari sai wani nishi yazo mata kafin su yi wani yunkuri haihuwa ta zo. Halifa yana ta kai kawo yana ta addu'a Allah ya sa a yi aikin cikin nasara. Gashi ba bu dama ya kira kowa kar a san inda take. Aka fito masa da jariri nade cikin tawul ya sha kayan sanyi likitan da kanshi ya miko masa ɗan yaro namiji .kyakykyawa yana fadin na taya ka murna. Cike da farin ciki da kuma rawar jiki Halifa ya amshi gudan jininsa hannunsa na rawa dan shi ba ya iya daukar jarirai. Yace "Yanzu wannan da na ne? To ita kuma Mamansa din fa tana ina ne? Likitan yace tana cike da koshin lafiya ina yi maka albishir da cewa ta haihu ne da kanta. Yanzu nurse za su gyara ta. Halifa ya ce "Alhamdulillah " To bari mu zauna mu jirata,goron albishirin ka kuma sai mun samu nutsuwa. Likita yace sai a kira wayar a sanar da yan uwa da abokan arziki. Halifa yace zan sanar da su. Bayan likitan ya koma ciki Halifa ya shiga tunanin yanzu shikuwa ya zai yi gurin kula da ita da kuma jariri ita kanta bata san ma ya zata kula da kanta ba bare Yaron. Ko ya kira Inna? Kai Inna zata raba su ne.Anty kuma bai gama binciken da yake yi ba,Allah ya rufa asirin su kuma har yanzun ba a san suna tare ba. Ya tashi da sauri ya nufi office din likitan yana rungume da dan a kirjin sa. Likitan ya taso yana cewa a kwai wani abu ne? Halifa yace a a, Ina son ka ba ni wata nurse da zata kulamin da su a gida kamar yadda zata kula da jikinta da kuma shi yaron nata. Likitan ya dan yi mamaki har ya kasa shiru, yace amma wannan mai sauki ne da ka sanar da dangin ka,ko nata. Halifa yace "Ka san kowa da irin nasa tsarin ni kuma dai haka nawa ya ke. Likitan yace To wannan ba zai zama matsala ba, za a duba nurse guda daya da kuma dattijuwa ko a cikin masu kula da tsaftar mu ne sai mu baka suna zuwa suna duba su. Asiya kamar ba ita ce ta haihu ba, tana zaune a mota rungume da danta ta kafa mishi ido tana jin wata kaunar sa, suka nufi gida. Halifa yana tuki a hankali kamar ya dakko kwai. Asiya ta kalle shi cike da murmushi tace yana kama da ni fa. Halifa yace "Ko dai da ni, ki kalli fuskar shi sosai ki kalli hancin. "Asiya tace da kuwa anyi kyakykyawan yaro Allah dai ya yi masa albarka. Halifa ya sa hannu ya shafi kuma tunta Ameen Babyna. Kwanciya ta yi dama likita yace ta ci abinci ta sha magani ta kwanta ta huta tunda Halifa ya matsa kan cewa su tafi gida..Halifan ne ya hado mata shayi zafin ruwa baya baya ta sha ta kwanta. Shi kuma dama Halifa ya kwana gadin su sai bayan ya yi sallar asuba sanna ya kwanta. Kuka Yaron ya tada Asiya bata san ya zata masa ba.gashi tana tausayin Halifa ya samu bacci. Ta dauki wayar sa ta fita falo ta duba lambar likitan ta kira shi,bayan sun gaisa ta ke sanar da shi yaron ya ta shi yana kuka. Yace ina baban tace yana bacci, Likitan yace yunwa ce kawai ke damun baby zan masa text na madara sai ya siyo yanzu kafin ruwan nono ya zo,ki ci abinci ki sha shayi sosai da kunun kanwa dan ki samu ruwan nono da wuri, kar yaron ki ya rame. Asiya tace to tayi godiya. Kukan yaron ya farkar da Halifa,ya ce "Ya baki tashe ni ba?" Ta fada masa yadda suka yi da likitan yace To bari in je neman madarar ya dauki makullin mota da sauri ya fita yana kiran wayar likitan yana fada masa abinda zai siyo wanda maijego da jariri ke bukata a yanzu. Ya dawo ya samu yaron yayi bacci. Ba jimawa Nurse Anty Amina da gyatuma Wadda tace Hajjo ake ce mata, suka iso. Anty Amina tana tsaye Hajjo ta wanke yaro tas sannan ta yi wa Asiya wanka ta gasa mata jiki. Ta ci abinci ta fito fes. Anty Amina ce ta nuna wa Asiya yadda zata hada mishi madara da kuma yadda zata bashi, sannan ta gargadeta akan cewa da tasamu ruwan nono to fa ta aje madarar nan nonon Uwa shine abu mafi amfani a gurin jariri. Ta dubi Halifa tace Ranka ya dade ai ni ba sai nazo kullum ba jifa jifa zan ke zuwa, amma ita Hajjo sai ta zo kullum sai dai ku samu mai aikin gida kuma kafin matar gidan ta yi kwari. Halifa ya yi godiya tare da bata kyautar kudi. Hajjo tace akwai wata jikarta ta zo daga maiduguri in suna so sai take zuwa tana ta ya Asiya girki da kuma shara. Halifa ya ce ba damuwa su rinƙa zuwa. Kwana biyu Halifa ya kwashe bai leka kasuwa ba, ga abin fadi babu dama shi ya yi wa dan sa huduba da sunan mahaifinsa wanda shima shine sunan sa wato Umar. Halifa ya samu Sulaiman ya ce, Dan Allah zan baka wani aiki ne, na fara shi ni kadai amma naga bazai yiwu ni kadai ba. Tun lokacin da aka yi posting din video wanda ya shiga dakin mata ta, na ke bi comments na mutane duk posting din da na gani lokacin na dauki lambar wani wanda yace shege Mansur kayi nayi yau Kaine kuma da kwartanci. Na bibiyi wanda ya yi wannan rubutun ta hanyar number sa da ke a kan shafin sa, na ga cewa tela ne shi,dan haka na bukaci zan kai masa Dinkin mata ta. To abinda nake son ka min guda daya ne,zan baka kaya ka kai masa a kofar ruwa yake,sai ka ce masa kai ne kuka yi chatin da shi,ka kira shi da lambar ka,kace masa shine daya layin ka. Sannan ina son ka tambaye shi Mansur kayi nayi,cikin hikima na san dai ka san me zaka yi,sai muji ta inda zamu same shi. Sulaiman yace "Ka yi dabara,amma kuma ba abin ya wuce ba?" Zai dai wuce insha Allahu iya shi in na kama zuciyata zata samu saukin domin zai fito min da duk wanda ke da hannu akan komai. "Haka ne Sulaiman ya fada cike da kwarin gwiwa. "Zan kokarta in ga na yi maka wannan insha Allahu za mu samu nasara. Bros bayan amarya ta tare ba yabo ba fallasa tana ta kokarin farantawa ango dan haka ya zubar da komai ya kula ta aka sha amarci, sai dai tun safe yake barin gida sai kuma dare, can yake tafiya gurin maman Nihal ya yi wanka ya yi shirin kasuwa, da ya ke su maza yayan Baban su ne,sai yake nuna mata bai yi komai da amaryar ba,ita kuma tana ta lallashi wai ya kula ta saboda hakkinta da Allah ya dora masa. Zuwan Anty uku gidan bata samun shi amarya kuma ta tabbatar wa da Anty cewar gida yake kwana sai dai yana fita da wuri dan wani lokacin ma a gidan wanka na kasuwar ya ke yin wanka ya canza kaya. Anty tace "gi Gidan wanka kuma duk bandakunan da ke gidan nan amma ace sai ya yi wanka a kasuwa? " To rigima kuke yi tace a a lafiya lau muke.To yana cin abinci ko baki soma girkin ba?" Amarya tace Gaskiyar magana bai tabacin abinci na ba. Fitar wuri yake yi, in ya dawo kuma sai ya zo da nama ko kaza. Anty tace "Kuma ke hakan ya miki?Amarya ta fara jin haushin tambayoyin Anty dan haka tace Umm.Anty ta fahimta yarinyar bata son maganar tace Nifa kamar Uwarki ce shiyasa ki ka ga ina tambayar ki domin in ya miki ba daidai ba in taka masa birki,amma tunda ke kin ce ba matsala shike nan . Ta mike tana fadin ni zan tafi. To ki gaida gida. Har ta kai bakin kofa ta tsaya, ke kuma haka ki ke yi wa bakin duk wanda ya zo ba dan cincin ba lemo ko tayi ruwa zuwana uku fa. Amarya tace "Na ga ai an kai muku na ku ne cincin din da sauran kayan gara,nawa na baki ne,ke kuma Anty ai ba bakuwa bace. To ruwan kuma fa shima bazaki iya bani ba. " Dan ruwa sai in baki mana ruwa dai Allah na tuba dawo ki sha."Amarya ta fada tana yatsina baki. Anty tace Allah ya amfana,na yi miki magana ne kar wani ya zo bare a yi masa haka ni ai ta gida ce. Amarya ta yi yar dariya. Anty dama ai dan ke ce shiyasa nima na yi haka. Maganar ta doki Anty ta dawo ta tsaya, kina nufin idan Uwarki ta zo gidan nan itama haka zaki yi mata? Amarya tace "Anty ina tabbatar miki daga nan har in shekara ba lalai uwata ta zo gidan nan ba matsawar lafiya lau,ita kuma haka Allah ya yi ta da kamun kai zan ce ko kawaici,bare har ta doko sammako,to kin san Allah Anty gidan Yayanmu shekara biyu matarsa ta haihu sai lokacin ta taka gidan ta yi musu barka,in anyi maganar bata je ba sai ta ce me zakaje gidan yaro ka yo masa, indai suna lafiya haka ake so,ni bana wannan gayyar sa idon da kwakwafi, da kalan nema raini gurin yara. Anty ta gama gane yarinyar nan ta fake da Guzuma ne take harbin Karsana. "Wato ni ki ke yada wa magana baki san ni ba ko? Kiyi a hankali kar ki dakko irin wannan ta kun tsakanin mu, an bini ma ya aka cika bare kuma Anja da ni. Amarya ta ce kiyi hakuri Anty yadda ki ke zato ba haka nake nifi ba.Anty taa wuce fuuu a fusace. Amarya ta raka ta da harara tana fadin nima din ba sani na ki ka yi ba. Kafin kwana hudu Asiya ta yi shar da ita, ta gyagije, abinda ke ta damunta ba taron suna. Halifa yace kar ki damu zamu yi sunan mu kuma idan Allah ya yarda muka warware komai sai mu yi wa jama a na su. Ana gobe suna Halifa ya kawo wa Asiya kaya akwati uku da ya sa aka dinka mata, sarka takalma mayafai harda kayan ciki dangin pant. Ya kawo raguna guda biyu da asuba aka rada sunan a masallacin unguwar su. Sai lokacin makota suka san da mace a gidan har ta haihu, da suka koma gida suka sanar da matan su, kuma sun zo suna, Hajjo da jikarta Fati sune suka yi girki, tunda ba mai yawa bane. Gidan dai gaba daya ko mutum goma ba a kai ba. Halifa ya kira mai hoto inda ya dauke su kala kala shida Asiya da Jariri mai sunan Ubanshi da kakan shi. Hajjo ce ta samo wata 'yarta suka yi aikin raguna. Asiya ta basu da yawa ta ɗibi na cin su sauran ta ce su sa a cikin mai. Hajjo tana zato aiki ya kawo su Asiya Kano dan haka ba su da kowa. Tun ranar farko da Fati jikar Hajjo ta dora ido akan Halifa sai ta kasa sukuni bata taba ganin namijin da ya kwanta mata kamar Halifa ba,gashi matashi mai aji ga kudi ga kyan siffa,tana ta mamaki yadda akayi ya auri Asiya wata lange lange da ita kamar kara, duk da daular da ke gidan amma gata nan ita ba wata kyakykyawa ba. Ta sha alwashin sai wannan gidan ya zama na ta. Haka take sakawa kullum in tana zagaya gidan ko tana aiki a kicin. Asiy tana zaune a falo a na ta gwagwagwa da shan nono har yanzu baya iya kamawa saboda irin mara kunyan nono nan gare ta wanda ke tsaye car dole sai dai ayi sama da dan ita kuma hannuwanta gajiya suke sai Hajjo ta tallafe sannan in ya samu ya kama yana fara tsotso gaba daya sai zafi ya isheta. Halifa ya fito yana rike da kugu yana murmushi yana kallon ta, birge shi hakan ke yi, ta dube shi cike da shagwaba ta ce Yaya kawai a dakko mishi wannan abin tsotson ko a hada mishi madara, zafi nake ji. Yace Baby kin fiye raki kema haka kika yi wa Inna. Hajjo ta yi yar dariya tare da fadin a haka zata saba Maman nata ne ba masu sakkowa ba shiyasa dole sai a hankali. Halifa ya matso ya sa yatsa ya lakuci kumatun yaron tare da fadin Babana ayi wa Momy a hankali ka ji ko? Suka sa dariya. Fati dake can gefe tana goge goge ta shagala da kallon Halifa a jikin shi ya ji kamar ana kallon shi ta gefe TV ya kalli gurin ta yi saurin dauke kai tana kara kakkabe gurin. Ya lura da irin kallon da yarinyar take mishi ba tun yau ba. Yace Baby ni zan fita tace Kadan jira mana Yaya mu raka ka? Yace na yafe baki ne da ni yau yan Niger za su dauki kaya. Su sun fi son su ganni. Asiya tace To Yaya sai mun yi waya Allah ya bada sa a da rabo mai amfani.Yace Ameen ya wuce. Ji ya yi an ce Sannu Alhaji ya waiwaya ya kalli gurin yarinyar nan ce, tace ina kwana "Lafiya" ya amsa yana mai ci gaba da tafiya.Sai da ya shiga mota sannan ya kallo gurin har yanzu yarinyar tana tsaye a gurin tana kallon motar. Ya dan taba baki ya fice. Sulaiman ya hadu da Tela bayan ya kwatanta masa inda yake ya bashi dinkuna Tela yace "Ina gwajin kayanta?" Kash Inji Sulaiman bari zan turo maka, na shafa a,yace "To ba matsala. Tela yace bari a kawo maka lemo ka sha tafiya gashi duk da bamu da nisa da titi sai gashi ka wahala." Sulaiman yace ruwa zaka bani, Nifa zuwa na daya nan Unguwar lokacin da wani abokina Mansur kayi nayi.Tela yace Kayi nayi dai wanda na sani dan gidan Dala?Sulaiman yace shi mana wani baki haka. Tela yace shine kuwa ai yana gidan yari ka san kwanaki an kama shi da wata matar aure,shine ina ga dalilin zuwanshi,ance yana gauron dutse.Sulaiman yace Allah ya kyauta Shi kuwa Mansur me ya kai shi irin wannan danye aikin. "Son zuciya mana,da Sana arka da komai kasan pop yake yi ya iya aiki kuma yana samu. Sulaiman yace azal din kenan. Tela ya kawo wa Sulaiman ruwa suka yi sallama bayan ya sha. *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [11/6, 08:25] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt Halifa ya yi murna da Sulaiman ya sanar mishi amma duk da haka sai yace ina son ka samo min cikakken sunan da zan same shi idan naje gidan yari. Sulaiman ya sake kiran Tela ya tura masa gwajin dinki da kuma kudin da suka daidaita,sannan yace masa ko yasan cikaken sunan Mansur dan zai kai masa ziyara can gidan yari din. Tela Yace Ai gaskiya kayi nayi kamar sunan mahaifinsa Garba Dala,kasan tsohon dan canji ne. Sulaiman yace To hakan ma ya yi Insha Allahu zaije.Ya sanar da Halifa, komai. Fati ta kalli Kakarta suna cikin Keke napep tace, Ni kuwa Hajjo kin kula yarinyar nan da muke yi wa aiki kamar wata wawuya ko? Hajjo tace kamar Yaya me ki ka ga ta yi? Fati ta ce, kawai dai haka nake ganin Hajjo tace ina kula da yadda ki ke kallon mai gidan nan wallahi ba ruwana kar ki ja abinda za a kore mu. Fati ta ce ai ni da zan samu lambar sa..... bari dai zan dauki wayar ta in dauki lambarsa.Hajjo ki yi tunani ace jikar ki ce a cikin wannan gidan da sai dai in ware miki wannan falon da su ke cewa na baki in samo miki masu aiki,ki saka goma ki tsoma biyar. Hajjo ta saki dariya ki ce sabuwar Duniya,da dai cewa yai yana sonki shine sai in murtsike ido na in goya miki baya, amma yanzu ki ce zaki sa kanki in yaki fa? Fati tace ai nayi mafarki munyi aure da shi. Hajjo tace "Tabdi to wallahi ki bi a hankali na fada miki. Asiya ta sha wanka tana sanye cikin dogowar rigar atamfa ta yi kyau sosai tana dauke da ɗanta a kafaɗa. Ta fito Halifa yana zaune yana kallon TV Ta zauna tana fadin har Fati ta zo kenan naji kamshi ya cika gidan. Yau ba tare suke da Hajjo ba ga maigidanta yana jiran wanka Halifa Yace "Ke kam yanzu ai kin iya wankan ko?Tace tun yaushe na sati daya tayi min. Ya kai hannu ya sagalo wuyanta, kyakykyawata wallahi na takura fa, wai dole sai kinyi wata arba'in ne? Dama ance mai mace daya aminin gwawro,tace Kamar yaya? Yayi dariya Yace To nima dai yanzu ai daidai muke da wanda ba shi da ita. Fin sati biyu saidai a bani shayi da lemon tsami. In ta lashe yawu,kin ga da ku biyu ne shike nan.... Asiya ta yi saurin saka hannu ta dafe bakin Halifa cike da shagaba ta ce, Ka ce Allah katuba, dan gaskiya bana son zancan nan ko da wasa, kana son in mutune? To na ji matsalarka zanji da ita insha Allahu. Amma ka yi min alkawarin cewa ka daina tunanin cuso wata tsakaninmu. Ina fa da kishi Yaya akan ka ba zan iya yin kisa ba,amma ni za ka ga na yi fut na mutu. Kafin ya yi magana sallamar Fati ce dauke da tiren kayan karin kumallo,ta gaishe su sannan ta nufi Dinning ta shirya ta kuma zuwa ta kwaso sauran. Sannan ta dan matso gurin su kamshin humrar da ta shafa ta bude su,tace Anty an gama shirya karin kumallo. Asiya tace Fati wannan turaren na ki yana da kamshi kina sai da humra ne? Tace "A a daga gida na zo da shi." Amma kin iya hadawa ko?" Fati tace " Ban iya ba wallahi." Asiya tace Kina Maidugurin? Fati a ranta tace ai bazan hada miki bane, a fili tace "Kinsan ba kowa ya iya ba. " Asiya tace OK Baba Hajjo fa bata iso ba ne? Fati ta kalli Halifa wanda ke danna waya kamar baya jin su,ta ce "Zata dauraye kayanta ne,shi yasa, amma yanzu zata karaso. Bari in gyara dakin ku kafin ku gama." Asiya tace to. Tana wuce wa Halifa yace gaskiya turaren da kamshi ki tambayi Hajjo din ko za a samu masu saidawa. Asiya ta kafa mai ido tana kallon shi ta kasa magana. Har sai da yace, Aƙwai kuskure a magana ta? Cike da gatse ta ce babu. Tashi muje ka karya. Fati ta na gyaran daki tana ayyana yadda nan da lokaci kalilan zata mallaki wannan kyakykyawan daki da kuma mai dakin. Ta dauki jallabiyar Halifa da ke kan gado ta rungume tana fadin I love you so much. Idan taga abin Asiya sai ta yi tsaki kafin ta gyara. Tana ganin ta fi Asiya wayewa kuma ta girme mata bata zaton zata sha wata wahala gurin karbe mata miji,gashi ita ba ta da kowa bare wata ta bata shawara,ta fada kan gadon tana manne da rigar Halifa a kirji tana ta sumbatar ta. Kunun gyada ta yi musu da kosai kamar yadda Asiya ta fada mata tun jiya,sai dai ta kara da farfesun kayan ciki wanda Halifa ya samu ya yi ta sha da alamu ya yi masa dadi. Domin magana ta gaskiya ya yi dadin kuma Fati ta iya girki. Haka ranar da ta yi miyar kubewa Halifa bai boye santin shi ba. Sannan ko shayi mara madara sai yace kisa yarinyar nan ta dafo min shayi. Asiya ta fara jin haushin Fati to amma sai ta lallashi zuciyar ta domin kuwa fushin fari ba nata bane. Za dai ta dauki mataki ne. Fati ta fito bayan ta gama gyara dakin har lokacin suna kan Dining yana fada mata zai je gidan yarine ziyarar wani dan kasuwar su. Asiya ta daga murya ta kira Fati. Fati ta zo gurin tana satar kallon Halifa wanda ya ki dago kai,yana danna waya. Asiya tace Fati da Allah in zaki zo gidan nan daga yau kar ki kara saka wannan turaren. Cike da mamaki Fati ta kalleta "Saboda me Anty?" Asiya ta kalli Halifa, saboda Yaya yace baya son kamshin yana tada masa zuciya. Fati tace To insha Allah ba zan sake sakawa ba,ta kalli Halifa wanda kunya da mamaki suka hana shi ya dago kai. Tace "Alhaji a gafarce ni bazan sake ba. Halifa ya dago ya dube ta, kar ki damu. Abinda ya iya furtawa ke nan ta juya ya bita da kallo,reshen zuciyar sa yana kawata masa surarta, sai ya sunkuyar da kai. Tana fita Hajjo na sallama. Suka mike a tare Asiya ta saba Danta a kafada suka nufi falon Hajjo ta amshe shi suna gaisawa. Halifa ya nufi daki bayan sun gaisa Asiya ma ta nufi dakin dan dakko wa Jariri kayan da za a sa masa in anyi wanka. Halifa yana bakin gado yace "Ke zonan ki fada min yaushe kika soma karya da kulla sharri? Asiya tace bari in bawa Hajjo kaya inzo in fada maka. Ta maida kofa ta kulle sannan ta zo ta same shi, ta zauna a cinyarsa. Da me kake tambaya? Ya kama kunnenta ya matsa har ta yi dan kara,yaushe ki ka soma karya? Tace yau na fara, kuma akan ka bazan daina ba. Ta haye kirjin shi bayan ta tura shi ya kwanta ta rike masa kunne tana fadin kar ka sake ka kara cewa turaren wata da dadi, nawa kadai zaka yaba kaji ko? Yace "Ai ban fada mata ba fa ke na fadawa." Tace shine saukin ai. Ta soma yi masa wasu wasanni da ya fara neman rasa nutsuwar shi, yace Kar ki haukata ni Baby ke gashi kina cikin wani yanayi da sai hakuri. Tace Ai tunda ka fara kwadayin aure ka daina fita ba nutsuwa. Zan gwada maka banbancin mai mace daya da gwauron da ka ke fada. Haka kuwa da wasanni saida ta sa shi ya nutsu, yace lallai yarinya ashe kinsan yadda zaki yi dani in kina fashin salla amma kike kyale ni ? Tana ta dariya, sannan ya yi wanka ya fita zuwa Gidan Yari. Anty ta kira Hajiya Talatu yafi a kirga bata same ta ba, layinta ma baya shiga,tun ranar da tijararren nan ya kwashe mata kaya. Amma yau sai ga kiran Hajiya Talatu, cike da mamaki Anty ta daga, ta soma zazzaga masifa Lallai Talatu kin nuna min ke cinnaka ce baki san na gida ba. Ni zaki cuta shiyasa ina ta kiran ki amma ki ka ki daga min waya. "Ba haka bane wallahi." Hajiya Talatu ta katse Anty, Ma u bata fada miki bane, Ina gidan yari a Kaduna, yau din nan na fito ke na fara kira Sahiba yanzu haka kin gani a gida ko ruwan gidan ban kai ga shaba. Ina tun ranar da na baro gidan ki,to tun ranar ina dira Zariya ko minti talatin ban yi ba a gida, wasu mutane suka kamani suka danna a mota na zata ko yan kidinafin ne, kai tsaye muka tsaya bakin wata kotu a Kaduna aka amshi wata takarda aka kaini aka jefa ni gidan yari ba tare da nasan abinda na yi ba.kuma har zuwa yau da aka je aka kira sunana akace in fito za akaini kotu sai aka tsaya a hanya aka ba wani mai mashin ni aka ce ya kaini tasha ya sa ni a motar Zariya kin ganni nan dirata kenan. Anty ta cika da mamaki,tace "Ke to da waye ba kya ga maciji ne har haka? Hajiya Talatu tace Wallahi Sahiba ba na ce ba, nasan dai akwai masu jin haushina da yawa, wanda ba su da yadda za su yi dani,dan haka dole sai na nutsu zan gane waye, duk ba yadda ban yi ba amma ko damar yin magana da wani ban samu ba. Anty tace "Tabdi, to Allah ya kyauta ki ce dai kina cikin matsala ni dai nan damuwar da sauki Asiya ta haukace ta ma bace ba a kara ganin ta ba. Kuma anyi bikin Wannan dan naki, sai dai kuma kamar fa na debo ruwan dafa kaina ne, amma zanji da ita. Kije ku huta ki kuma samo bakin zaren matsalar ki sai ki zo mu san ta kwatanci. Haka dai suka yi sallama. Da Sulaiman sukaje da kuma lauyan shi, Dan haka kai tsaye suka shiga suka bada suna,an dan samu jinkiri kafin aka gano Kayi nayi. Yana ganin Halifa ya gane shi,nan take hantar cikin shi ta kada. Bayan sun zauna kayi nayi ya soma fadin mai gida dan Allah ka taimaka min wallahi ni ba kwarto bane wallahi san kudi ne zan kai kudin aure gidan su budurwata gashi son zuciya na kare a nan. Kuma yarinyar nan nasan na rasa ta "ka shirya fadin gaskiya kenan ko? " Zan fada megida, domin na gane cewa Allah daya ne kuma bashi da abokin tarayya. Lauya yace ka bamu labarin yadda aka yi kaje dakin matarsa,daga nan sai mugani me ya kamata ayi? Mansur kayi nayi. Yace To ni dai wani malami ne zan kira shi ko boka,naje gurinsa da neman taimako akan sana'ata abubuwan basa tafiya yadda ake so, sai yace ga aikin kudi in zanyi,nace zanyi indai ba sata bane. Yace min zan shiga dakin wata mata ne a wani gida in yi kamar minti talatin, sai in fito za a bani dubu dari kawai dai in yi kamar naje kwartanci. Gaskiya farko na tsorata nace kar mijinta ya dake ni, sai yace Za a bani kudin magani daban. Na ce sai nayi tunani,bayan kwana biyu sai suka sake cewa sun kara min dubu hamsin to daga nan fa sai na yarda tunda sun min alkawarin baza su bari a kamani ba. Ranar da na yarda matar ta zo har gidanmu ita da kawarta tace bazata bari a tabani ba,dan a gidanta zan yi aikin. Halifa ya katse shi, Kace ta ce a gidan ta? Yace kwarai kuwa. Lauya ya Dakatar da Halifa yace "Ka bari ya gama sai ka tambaye shi abinda ka ke son sani. Mansur ya ci gaba da fadin, nace amma kar a yi min Video tace sun yarda. Naje gidan na yi komai kamar yadda suka ce, amma sai gashi an dake ni, da kyar na gudu ta gurin da ta nuna min,kuma bayan kwana kadan aka kamani aka kai ni gidan yari ba tare da an kaini kotu ba, yanzu haka bansan zaman da nake yi ba, domin so daya mukaje kotu ko gaban alkali ba a kaini ba aka amso wata takarda aka kawo nan. Halifa ya numfasa yace "Me kasani game da takardar saki da aka rubutawa mata ta? " Kayi nayi yace Megida wallahi bansan wannan ba, iya bayanin nan wallahi su na sani. Kuma wallahi ni ko ganin matarka ban yi ba har sai da ta fito ,ina shiga kicin na shige na boye har sai da suka kira wayata suka ce in fito, kuma duk maganganun da na fada mata na cewa tana zuwa guna wallahi sharri ne ku yafe min. Halifa ya yi murmushin takaici, yace Kasan cewa sanadiyar abinda ka yi yanzu matar ta bace ana zaton ma ta haukace ko?" Kayi nayi ya dauki salati yana fadin ya shiga uku. Halifa yace "Abinda ke bata min rai yadda gaba daya abin ke nuna cewa Anty ce ta hada shi." Kayi nayi yace Yawwa ita ce duk Anty ce ta hada komai wallahi. Da wata kawarta. Halifa suka fita suna tattauna wa akan abinda ya kamata ayi, Sulaiman yace zuwa za ayi a samu Anty a nuna mata ansan komai ina mai tabbatar maka sakin ma ita ce ta hada shi ba wani ba. Lauya yace "Ita ce mana, ai babu dogon bincike kai yanzu Halifa ya ka ke ganin za ayi, musa yansanda su kamota ne ayi case ko me kake gani? Halifa wanda idanun sa suka yi ja,zuciyar sa ta yi zafi a fusace yake ya daki gilashin motarsa na gefen da yake tsaye take ya fashe, suka rike shi suna fadin Haba haba wannan ai ba dabi'a bace. Halifa yace Me kuke son inyi ku fada min. Ya yi maganar murya a sama, har mutane suka fara tahowa,nan suka tura shi mota suna kwantar masa da hankali, Yace "Kamar kaine Barrister mahaifiyar ka ta yi maka haka, Yaya zaka mata ka fadamin?" Duk suka cika da mamaki,yace wai mahaifiyar ka ce? Halifa yace haihuwata ne kawai bata yi ba,amma tun ina tsumma itace ta raine ni.Uwarmu daya.Barrister yace To zamu tattauna yadda za a bullo wa abin. Bayan su sauke Sulaiman sai Barrister yace Kasan ni na aje wannan yaron a gidan nan tun lokacin da ka turo min Video na abinda ya faru,kawar Anty ku din ma ni na saka aka aje min ita a Kaduna sai jiya na sa aka sake ta, da ka sanar dani halin da ake ciki, amma dole zamu sake dakko ta zuwa nan Kano din, sannan zamu kawo ta nan ayi case din in kuma baza ka yi case da suba,to dole mu hada su guri daya mu warware matsala,sannan shi yaron mu sa ya yi video ya wanke matar ka. *✍🏻✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [11/15, 17:31] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt Koda Halifa ya shigo gida Asiya bata gane kansa ba,yana cikin bacin rai sosai, suna falo da Hajjo ya wuce daki, ta aje dan ta bishi da sauri ya jingina da sif ya dafe fuskar shi da tafin hannun sa. Taje ta shige jikin sa ta rungume tana fadin Allahumma ajirni fiimusibati. Yaya me ya faru,dan Allah kar ka daga hankalin ka, zo mu zauna ka fada min ko da banyi maka maganin abin ba za muyi shawara kaji Yayana. Kamar rakumi ya bita domin ta yi maganar cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Suka zauna bakin gado, Ya kalleta Asiya duk abinan da ke faruwa ya tabbata Anty ce ke hada shi, me na yi mata haka da take shirya min makirci kala kala, in kece matsalar ta ta fito fili tace min bata sonki, shike nan ni ina son ki sai kawai in muku tsakani ta yadda ko ganin ki bazata yi ba,ba sai ta yi ta wannan wasan kwaikwayon ba,harda yunkurin kashe ki, wai ma me kika yi mata?Hawaye suka soma zubo masa. Asiya ta saka hannu tana share masa hawaye, Haba Yayana bana son kana hawaye zuciyata zafi take yi, karka damu jarrabawa ce komai zai warware kamar ba a yi ba. Zata gane kuskuren ta kuma ni na yafe mata saboda kai. Yace "Ni bazan yafe ba, zan bi miki dukan wani hakki na ki har sai ta yarda ta cutar da ke. Asiya ta tashi ta je ta bude karamin firjin da ke dakin ta ta dakko ruwa ta tsiyaya a kofi ta bashi ka sha. Ya karba ya shanye sannan ya bata labarin dukkan abinda ya faru. Asiya ta cika da mamaki amma sai ta boye mamakinta da damuwar dan kada ya kara shiga damuwa. Ta samu ta kwantar masa da hankali. Ya fada mata abinda lauya yace. Tace kar kayi shara'a da ita,ta ci albarkacin zumunci da kuma 'ya'yanta, ka samu Bros ka fada masa dan kaji ta bakin sa, sannan ka tara duk wata hujjar ka sanan ka tara manyanku dan su san me yafaru, sannan saboda mu warware matsalar mu da Inna ita ma ta zo gurin. Halifa yace kema kin kawo shawara amma zan duba. Asiya tace saboda ni damuwata yanzu bai wuce Inna ta gano gaskiya ba, sai nafi sakata in walwala. Halifa yace kar ki damu fa, in yi miki ta wani mawaki da yace ko mutuwa baza ta rabamu ba,in tazo tare zata dauke mu. Asiya ta saka dariya. Dama kana jin waka? Yace fisha ba. Sulaiman ya samu Inna da hantsi ta idar da sallar walaha tana zaune tana Jan carbi, bayan sun gaisa yace, Inna dan Allah ki daure ki sanar dani wani abu daya, kila ta haka zamu samu bakin zaren warware matsalar Asiya. Inna Tace "An samu labarin Asiya din ne? A a ba a samu ba, bincike ne dai duk akan abinda ya shafi sakin ta,muna sa ran gano bakin zaren. Inna tace wannan yaron dan gidan Fatsuma mai dashi ne ya kawo takardar yace wai Inji Halifa.Kuma da na bi bayan shi na na leka na hange shi, yana tafiya, Sulaiman yace Dan gidan Malam Danyaro kenan? Shi kuwa inji Inna Sulaiman yace to ba komai zan samu yaron inji wanda ya bashi sakon takardar saboda gaskiya Inna ba Halifa ba ne. Inna ta ce ni dai Allah ya bayyana min yata,yan zu nasan cikinta ya isa haihuwa, matsawar tana raye, ko akan bola ko wasu su taimaka mata,Allah yasa ta fada hannu na gari, kullum addu'a ta kenan. Hawaye suka zubo mata. Sulaiman ya bata baki tare da kwantar mata da hankali. Kafin ya fita a gidan. Anty ta fito zata fita sai ta ga a nata fenti a gefe da Halifa ya tashi, ta tsaya ta cika da mamaki ashe har anzo lokacin da za a dinga yin abu ba shawarar ta kuma babu sanin ta,to Halifa ne ko kuwa Dady ne wanda aka ba wa gidan? Ta isa gurin masu aiki,tace kai waye ya saka ku wannan aiki? Babban su yace "Sannu da fitowa Hajiya, Alhaji ne me gidan." Tace Tofa! Lallai kuwa mai gidan. Ta wuce tana danna waya. Ta kira shi ya daga, ko sallama babu tace Wai me kake nufi ne?Dan Halifa ya baka gidan shike nan sai ka dinga yin wasu abubuwa gaba gadi ban isa ka fada min ba ko? Ya yi yar dariya "Habiba kikan so saka kanki a matsala meye abin daga hankali gyara ne na saka a yi mutane ne za su dawo ciki da zama." Mutane kuma! Ta katse shi wadanne mutane ina fatan dai ba dangin ka zaka rakito min ba? Dan wallahi sai in karbe gidan inga ta fadi. Dady yace kinga ba zancan waya bane inna dawo ma yi. Anty tana mamakin yadda Dady ke yi mata musu dole sai ta sake bazama akan shi gaba daya asiran da ta yi sun karye a lokaci guda haka. Dady ya shigo gida cike da kwarin gwaiwar sa, ya samu kuwa shi Anty ke jira har daki ta bishi babu ko sallama bare gaisuwa ta saka shi gaba sai ya fada mata su waye zai saka a gurin. Yace Bintu ce zata dawo gidan nan, tace wace ce Bintu din nan da kake ta magana? Yace Matar Abokina da ya mutu ya bar amanar su a hannu na, kin tsane su saboda su ba masu shi bane ba zaki iya hulda da su ba baki taba zuwa gurin su ba tun mijinta yana raye, da ya mutu da kyar ki ka je gaisuwa, ai bazaki san su ba. Anty tace OK to menene matsala ta da su? Bayan haka kuma me yasa za su dawo nan bata da dangi ne?" Dady yace tsawon shekarun nan bakwai ni ke biyan haya yanzu kuwa tunda Allah ya sa ina da gida su zo su ci arziki kamar yadda nima arziki ya sa aka bani. Dan haka bai zama dole sai na fada miki ko inyi shawara da ke ba, gargadin da zan yi miki ba ruwanki da Bintu kar ki sake ki ce zaki takura mata domin komai zai iya faruwa. Anty ta sake fusata, kana nufin zaka kore ni ka zauna da ita,kokuma zaka sake ni ka aureta? Ya ja tsaki ya shige bandaki ya barta tana fadin. Da kuwa ka ji haushi wallahi , wannan kucakar matar wallahi ko a yar wanke wanke ni bata min ba bare kuma kishiya,ai kana aurarta ni kuma zan san ta kwatanci domin ba hauka ake yi ba. Wani takaici ya kara turnike Anty da ta danganta ta da kishiya, tace kai wallahi ma baka isa ta tare a gidan nan ba, tunda ba gidan ubanta bane. Daga bandaki Dady cikin takaici yace ke ai gidan naki Uban ne. Anty ta shiga salati tana ihu tana fadin yau ni ka zaga saboda wata shegiya har zaka zagi ubana, kai kan ka yau sai ka bar gidan nan ba ma wai ka shigo min da wata ba. Ke naki uban hoto ne ko kalanda ce da baza a zage shi ba, Ina zaton uba baifi uba ba. Ta fito a dakin ta tsaya tsakiyar falo ta na fadin Hafsa zo ku ji min Babanku wai yau ni yake zagi. Hafsy Ta fito da sauran yara, suka yi cirko cirko. Zagi kuma Anty kamar Yaya? Anty ta fashe da kuka tana fadin zagi dai da ki ka sani wai Ubana, akan wata banzar mata da ya ke ikirarin zai taimaka mata ta dawo gidan nan da zama. Kuma dai na yi rantsuwa saidai ya zaba ko dai ni ko ita. Hafsi tace Anty dan Allah ki daina cewa ko ke ko ita, akwai wadda ta isa ta shigo gidan nan ba ke kika kawo ta ba, kije kawai ki kwanta shima Dady ya fada ne kawai dan ya daga miki hankali a banz...... Saukar wani wawa mari Hafsi ta ji a kuncinta. Kafin ta fahimci ko waye ya sake sauke mata a daya gefen. Dady yace "Yanzun rashin kunyar ki har ta kai ki kutso kai cikin magana ta da mahaifiyar ki kuma har kina nema ki zage ni?" Dukan su suka cika da mamaki suka juya suna kallon Dady kamar wani TV. Hafsi ta fashe da kuka tana kallon Anty dan neman ta yi wani abu. Dady ya sake nufarta yana fadin bari in zane miki jikin ki in ya so sai kiyi kukan mai dalili. Ta fada dakin su ta kullo kofa tana ta rusa kuka. Anty tace Lallai abin naka da gaske ka ke yi to kuwa ba zai yiwu ba ko asiri aka yi maka sai na karya shi. Ta nufi wayarta ta dauka ta shiga neman number Adamu Ya daga yana gidan amarya lokacin ya shiga wanka. Amarya ta daga wayar Anty cike da bacin rai tace Ina mai wayar bashi maza . Amarya tace ya shiga wanka. To yana fitowa ki ce ina neman sa maza yanzu yanzu a gida Amarya tace haba Anty yanzu fa ya dawo kwana biyu ba ya gari, gaskiya sai da safe zai zo koma meye abarwa safiya. Anty ta kara zuwa iya wuya, tace "Ke zan dura miki ashar ina wasa da ke ne dan uwarki,Ina kiran dana ki na fada min cewa sai gobe zai amsa kiran!!" Sa ar uwarki ce ni?" Katse wayar ta yi sannan ta goge kiran ta kuma kulle layin Anty data Hafsi ko sun kira zasuji yana amfani da wayar. Dan haka babu abinda ya fahimta da ya fito, sai ma ciwon cikin da ta hau murkusu, tun yana mata sannu abin babu sauki har dai ya ce ta tashi suje Asibiti. Ta yi ne shima dan su fice ta san Anty zata iya zuwa gidan. Ta kira Halifa ya dauka, tana kuka take fada masa cewa Dady ya na wulakan ta ta akan wannan gidan daya bashi dan haka ita tana neman su yanzu. Halifa wanda ke cike da jin haushin ta yace gaskiya ba zai iya zuwa yanzu ba sai da safe, tace Halifa ni ke kiran ka kana fada min sai da safe? Yace "To Anty kin san uzrina ne? Jiki ba kwari tace a a, yace" To a barwa safiyar. Anty ta furta cewa lallai ta kare min, me ya rage min na kima yanzu, ta fashe da kukan gaske ba kamar na dazu na wasan kwaikwayo ba. Washe gari tun safe masu kawo kayan Bintu suka shigo da sabon gado wanda Dady ne ya siya da kujeru sai sauran tarkacen ta na akin da kayan sawa. Yan gidan su sun zo da yake yan gwale ne, suna taya ta gyaran gurin Dady ma yana tsaye a gurin yana sabe da Ahmad a kafadarsa. Halifa ne ya shigo gidan bayan ya yi fakin din motarsa, suka gaisa da Dady ya tambaye shi ko anyi baki ne a gidan ya ga yaro. Dady yace Bintu ce ta dawo gidan, dama ina son magana da ku na kira Adamu ma yana hanyar zuwa. "Wacece Bintu?" Halifa ya tambaya. Matar marigayi abokina wadda ka ke ba su zakka. Oho to madallah. To bari in shiga ciki, Dady ya ce to. Jim kadan sai ga Bros shima ya shigo. Ya tambayi Dady su waye ke tarewa a gidan? Yace muje ciki akan magnar ne na kira ku.. Anty tana ganin Halifa ta dora sabon kuka, shi kuwa Baice kala ba haushin Anty ma yake ji in ya tuna abubuwan da ta yi masa.a haka tana ta rattafawa Halifa zance har su Bros suka shigo lokacin tana fadin wai ya kama Hafsa yana ta duka. Halifa yace "Dady baya duka gaskiya abinda ya saka Dady ya daki Hafsi to ba karami bane." Dady ya cafke maganar da fadin Wai Yarinyar nan ta bude baki tana neman zagina a gabanta gata nan. "Zagi!!!" Halifa da Bros suka hada baki. Gata nan Ai a gabanta aka yi. Dady ya fada yana nuna Anty. Bros yace "Dady ai da ka yi ma shegiya dukan da zata suma, kyashi Dady ta fito da miji ko kuma a samo ko waye a dangi a tura masa ta karata mara hankalin banza kawai. Dady yace Nima na yi tunanin haka amma bari mu gama da abinda ya tara mu. Anty ta kalli Bros Dan uban ka kai har kana da bakin magana, jiya in kira ka har sau nawa matarka ta daga tace bazaka zo ba dare ya yi ta kashe min waya ?Bros yace wace matar a ciki? Har nawa ne matan naka? Anty ta katse shi. Gabanshi ya fadi ya yi katobara,sai ya wayance da fadin To abin ne da mamaki Anty kin ce mata tace bazan zo, ba, to tama isa ta daga min waya ne,ki dai duba kinyi kuskuren kira ne amma jiya da dare ina gida. Anty tace 'E ai bansan lambar ka ba kuma kowa ya sani wallahi babu wanda zai yi wa Hafsa auren dole wallahi garama ku sake shawara,sannan dole Dady ya janye batun dawo da wacan matar nan gidan dan kuwa sai dai ya zaba ko zamanta ko nawa,dan kuwa bana son ganinta a gidan nan. Dady ya kalli Halifa da Adamu yace ku bani hankalin ku kuma ina son ku fahimce ni sosai game da Zaman matar can a gidan nan.Acan inda take ni ke biyan haya kuma ni ke ci dasu,nan kuwa in tadawo na huta. Anty tace shi bata yarda ba. Bros yace To ke Anty menene matsalar ki da haka kowa da gefen ta? Tace haka kawai,nan gaba kuma sai yace zai aureta, ni ba damuna zai yi ba dan ya aureta amma abin kunya ne ace na hada miji da ita. Halifa ya ja tsaki yace duk kishi ne banda abin Anty tunda shine da gidan sa kuma kema karkashin sa ki ke ya yi yadda yake so da gidan sa. Anty tace "Haka ka fada to ni na hakura da gidan nasa ya bani takarda ta zan kama haya. Dady yace To bari kiji cikakkiyar Magana sai dai karki zauna amma Bintu mata ta ce,na aure ta shekaru hudu da suka wuce muna da yara biyu Ahmad da Nasir yanzu kuma tana da wani cikin... *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [11/25, 17:05] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302* Tamkar mafarki Anty ta ji kalaman Dady wan da ke magana babu alamun wasa bare tsoro kokuma shakka . Ba iya Anty ba Bros da Halifa sun girgiza da jin wadannan kalamai na Dady, dakin ya yi shiru kowa da abinda yake tunani, Lallai wata damuwar tafi karfin kuka, domin Anty da a banza ne da yanzu ta fadi tana farfarin mutuwa,amma yanzu gata zaune ta zubawa Dady ido wanda ke sauraro ko wani zai furta wata magana amma duk anyi shiru. Ya yi gyaran murya babu mai abin fadi, in babu to kuna iya tafiya dama na sanar da ku ne dan naji Habiba tana ikrarin yi mata wani abu, karta sake ta soma,ku ne dai yanzu wadanda dole ku fada mata gaskiya. Cikin wata irin murya wadda da kyar Anty ta tattara yawun bakinta ta soma magana, "Yanzu kana ganin ka yi daidai kenan wannan cin amanar da ka yi min? Halifa ku du ba fa, kuji zancen nan shekaru hudu baya ya yi aure ban sani ba, ku baku sani ba,yanzu kana bashi gida har ya kawo matar,kuka ya kufcewa Anty Halifa in har ni yar uwar ka ce kuma na isa da kai ina son ka janye wannan kyautar Gidan da ka bashi." Ta ci gaba da rusa kuka. Dady yace ki godewa Allah da ya tsaya a kishiya kawai, in dan ta halinki ne ba sai mutum ya kama bin matan banza a waje ba, me kika sani na kula da miji? Abinci saidai ki aiko yara su kawo min, shinfidata zaki iya tuna rabonki da kakkabe min bare ki kwanta akai? In na matsu da bukata ta sai dai na zo dakin ki inkin gama wulakantani da min ba a da gori da kira na jarababbe sannan in naci sa a ki bani hakina shima kina yi kina ke inyi sauri kina jan tsaki. A haka na rayu da ke, yanzu kuwa in azuminan ya zo shekara guda kenan rabon da ki bani abinda ya shafi hakki na kwanciya. Ya kalli Bros wanda ya sunkuyar da kai,zantukan sun yi wa kunnuwanshi nauyi, Dady ya ci gaba da fadin dukkan ku ba yara bane yanzu, kowannen ku ya san yanayin da nake magana a kai, idan na yi aure dan in tsare mutuncina da na iyalina akwai laifi a ciki? Suka girgiza kai alamun babu. Anty ta katse shi da fadin Wallahi gara ace ga ka can an kama ka da wata akan wannan ranar ta yau ni a guri na. Bros Yace "Au'zubillahi minna shshaidani rajim,Allah ya tsare mu da mugunji da mugun gani, Anty infa rai ya baci hankali baya bata,ko mu da muke matasa bama fatan a samu haka a garemu bare mahaifinmu Dady Allah ya kara rufun asiri,in hali ya samu ka kara mata biyu Allah ne ya yarje maka, zan tafi dan bazan jure jin wadannan zantukan ba. Bai jira amsa ba ya wuce cike da bacin rai. Halifa ya dago ya kalli Dady zuciyar shi tana fada mishi cewa kenan wata rana Asiya zata iya yi mishi fatan ya yi zina idan har Anty a matsayin uwa kuma kaka tana kauracewa mijinta tare kuma da mishi wannan fatan kila duk haka mata suke domin dai ba a haka suka yi aure ba. Halifa ya sauke ajiyar zuciya,Yace "Dady lokacin da zaka auri Anty amma tilasta mata aka yi ko? Cikin sanyin murya ya yi maganar. Dady yace inji wa? Tana sona ina sonta aka yi mana aure, mun dai samu yar tangarda kafin bikin da yake muna tare da ita tun tana primary lokacin mahaifinsu yana raye, bayan rasuwar shi lokacin ina dako a singa ni na ci gaba da daukar nauyin karatun ta da kananan bukatu har zuwa lokacin da mahaifiyar ku ta auri mahaifin ka. Ganin sun koma gidan masu hali tunda shi mai kudi ne. Sai ta tsiro min da matsaloli da bukatun da suka fi karfina,nace na hakura shine mahaifiyar ku tace bata isa ba, kawai ma ayi auren mahaifinka shine ya yi mata komai kuma da zai yi auren yayansa ya hada da namu bai fi sati daya ko biyu da auren ba mahaifin ka ya rasu lokacin da cikin ka. A haihuwarka Allah ya yi wa mahaifiyar ka rasuwa lokacin ni na bata shawara aka ta amso ka mu rike ka.Da kyar baffan ka ya yarda domin yace bamu taba haihuwa ba baza mu iya kula da yaro ba. Ni na dage muka amso ka, haka duk yadda za ayi ta samu ruwa nono na yi amma abin ya faskara sai dai madara na dinga saye duk sati wannan abokin nawa mijin Bintu ya sai madara ba sau daya ba Na kawo an baka. Ai gata zaune tace karya ne in ta isa. Lokacin da ta samu cikin Adamu renon ka gurina ya dawo, da kyar nake fita a gidan nan in kana kuka sai ka bini. Lokacin da ta haifi nata dan haka ta juya maka baya Lokacin na mata uzri dama ba kowace uwa bace zata fifita dan wani akan nata. Amma sai ta zo ta soma nuna kishi akan ka wai nafi kula da kai na fi sonka. Anty ta Katse shi "Au har sharri zaka hada min da shi?" Dady yace Ki rantse baki taba yin yaji kince in zauna gani ga Halifa ba, ai Babarku tana raye bata mutu ba. Sai da kika yi yaji akan na saka Halifa makarantar kudi wadda kike korafin nawa nake samu da zan saka shi, in bari danki ya isa makaranta shi a saka shi naki. Duk kayan wasan da nake kawo wa Halifa ba boye wa danki ki ka yi ba? Keke nan da na sai wa Halifa kwacewa ki ka yi,duk sharri ne na yi miki? Halifa ya tuna maganar Keke lokacin da tace wai tana tsoro kar yaje mota ta takashi amma tabbas daga baya Bros yana hawa keken. Ya tuna wannan lokacin yana da wayo. Ya yi murmushin takaici, yace Dady ka share min tantamata da kuma mamakina akan abubuwa da Anty ta yi min ko take kan yi min zan tafi amma ka sani nima ina goyon bayan ka dawo da matarka nan kuma suma yaranta zan dauki nauyin karatun su kamar dai na yan uwansu. Sannan nima zan kira irin zaman nan nan da lokaci kadan. Anty tace "Halifa zo kaji karfa ya hada mu duk abin da yake fada son zuciyar sa ce kawai. Halifa yana tuki yana tuna zantukan Dady ba shakka bai yi kuskuren ba wa Dady gida ba, duk da tarihin da Dady ya bashi ya dame shi amma fa babu kamar waccan kalma da Anty ta furta ta cewa gara ace ga Dady can an kama shi da wata yana zina da ace ya kara aure, duk mata haka suke? Wata rana Asiya zata iya fada masa haka dama yanzu ma ta nuna kishin ta mai karfi. Cikin wannan tunanin ya iso gida, Asiya tana kichin ta tasa Fati suna yin miyar nan margi special. Bata san ya shigo ba sai da suka gama ta nufi daki dan ta yi wanka sai kawai ta ga mutum kwance. Da sauri ta nufe shi ta zauna bakin gado ta kamo hannunshi ta saka a cikin nata tana tambayar shi, Yaya lafiya dai? Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya maida kallon shi gare ta yana tunanin abinda zai faru gaba. Tsoro ya kama Asiya tace Yaya kamin magana baka da lafiya ne? Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya tashi zaune, ya "Asiya zan tambaye ki wani abu." Asiya ta danji dim domin duk lokacin da zai yi magana yace Asiya ba shakka magana ce mai muhimmanci. Cike da tsoro da kasala tace to Yaya ina jinka. Yace Zan baki zabi daya a cikin biyu. Gabanta ya fadi ba dai zai ce ta tafi gida ba, ko maganar saki. "Kina ji?" Ya katse ta. In inajinka Yaya ta fada da in'ina, Yace Nan gaba in Allah ya amince ina son kara aure,in kuma ba haka ba to zaki lamun ce min in nemi mata banza a waje kinga ba ruwanki da kawo miki kishiya." Asiya ta mike tsaye da sauri tana fadin Au'zubillahi minna shshaidani rajim. Allah karka kama shi da wani laifi mai kama da wannan. Allah kar ka sa mala'iku su amsa wanna magana.Ta kalle shi, Yaya daga ina ka ke? Taje ta kama fuskarshi ta kai hancin ta gurin bakinshi ta shaka. Tace Yaya duk da bansan wari kayan maye ba banji alamun kasha wani abu ba, nasan baka sha kuma ba su ka shaba. Menene ya kawo wannan tunanin a zuciyar ka? Me zai sa ka ce zaka nemi mata a waje. Ta fashe da kuka, ta durkusa a gaban shi Yaya wallahi na yarda ka sake ni ka auri mata hudu in baka bukata ta, da ace ga uban dana yana bin matan banza gara a ce ka auri mata hudu. In har maganar da na yi maka ce dana ce bana son ka kara aure ta kawo wannan tunanin Yaya ka yafe min wallahi bazan sake ba. Ka yi auren ka ko yanzu ka ke so Allah ne ya baka dama kar ka damu da kishina. Ta fashe da sabon kuka. Halifa ya tashi cike da tausayin Asiya ya kamota ya rungumeta yace ki daina kuka wani abu ne na gani ya rudani dan Allah ki yafe min Baby. Asiya tace Yaya Allah ya yafe maka da ka ayyana kan ka da aikata zina,dan Allah kar ka sake, Ina son ka min alkawarin yadda baka aikata zina ba kana samartaka yanzu ma baza ka yi ba. Yace na miki alkawari Baby. Suka zauna tace Yaya ina ga dai da zarar jini ya dauke min zan dawo maka rashin samun kulawata sosai ne ya saka ka soma saka da mugun zare ko? Yace " Anty ce ta firgitani naga cewa idan har Anty da girmanta a matsayin ta na uwa kuma kaka zata yi fatan da Dady ya yi aure gara a kamashi da mace to ke kuma da kike karama sai Yaya kenan? Asiya ta zuba ido cike da mamaki tana kallon Halifa kamar shine ya fada, tace amma kaji da kyau kuwa? Halifa yace Ba ni kadai bane bare ince kunne na ya yi tsatsa. Asiya tace Allah ya kyauta abin dai ba dadin ji. Ya bata labarin duk abinda ya faru. Ta sha mamakin Dady ya yi aure ya boye ma matarshi tsawon shekaru. Ga Maman Nihal ita ma Bros ya boye ta. Ta kalli Halifa Yaya Dan Allah zan nemi wata alfarma in zaka yi aure wallahi ba zan taba hanawa ba, kawai ka fada min karka damu da kishi na, kar ka boye mace saboda ni. Ta kama hannuwan shi ta matse cikin nata. Ni da kai wallahi abu daya ne. Ya sunkuyar da kai cikin rashin Walwala Baby sai dai kar a kuma ni ma dai na boye mace kuma har ta haihu. Asiya ta zabura ta mike tana fadin Innalillahi wa Inna ilaihirraji un. Tun wane lokacin ka yi haka? Ya Kalli yadda ta firgita ya kamo hannun ta yace ke ce ai wadda na boye, ya saki dariya yanzu wa yasan muna tare? Ta sauke ajiyar zuciya Yaya ka tsorata ni walllahi dan Allah kar ka boye min komai. Ya kamota ya zaunar da ita a cinyar sa. Asiya wallahi na rantse miki da Allah a yanzu gani nake bani da wani wanda ya kai ki zama jini na, ke ce komai nawa, na baki amanar kaina Asiya wallahi da gaske nake yi, ki sani komai zan yi ki hanani zan hanu amma banda abinda ya shiga hurumin Allah. Asiya ta rungume shi, nima haka Yaya kuma insha Allah bazaka taba yin danasanin bani amanar kanka ba. Sulaiman ya taso yaro da yamma zuwa gaban Inna, ta tabbatar masa da cewa shine ya kawo takardar a gaban Inna ya tambayi yaron yaron yace 'Ni dai wasu mata ne suka bani suka ce ince inji ko wa ma nace da nazo na manta sunan har suka bani dari biyar. Sulaiman yace To kinji dai Inna da kunnan ki, wallah sharri ne kawai, Inna tace kayya to yanzu ina ma Asiyar take,ta fada cikin yanayin tausayi. Sulaiman yace Allah zai dawo da ita lafiya kuma wallahi mijinta bai zauna ba, yana can yana neman matar sa. Sulaiman ya kira Halifa ya fada masa halin da a ke ciki Inna ta fahimta fata dai Allah ya bayyana Asiya. Halifa ya ji dadi kuma ya yi godiya. Yace dan Allah zai neme shi akan ya kawo Inna akwai zama da za ayi Sulaiman yace Insha Allahu ba damuwa. Kafin Asiya ta yi arba'in sai da ta tabbatar ta koyi duk wani salon girki da Fati ke yi,ta kau da kai daga duk wani kini bibi da Fati ke yi idan taga Halifa. Ta kuma sa ta yawo da hijabi a gidan da ta kula takan fizgi hankalin Halifa in tana kai kawo. Bangare Hajjo ma Asiya ta ko yi wankan yaro dan haka bata da matsala da wannan. Ranar da zata cika arba'in ta sa su Hajjo suka zo mata da me lalle aka zuba shi ta yi mata kitso gurin mai kitso ta sai wasu magunguna duk da dai ta yi amfani da abubuwan da ta samu a soshiyal midiya na gyaran jiki ga masu jego. Da yamma ta zuba wanka ta yi kyau kamar amarya. Halifa ya yi ta kallon ta yana mamakin bayan fitar shi duk ta yi wannan gyaran kasa cin abincin ya yi dan doki, ya shiga nuna mata zalamar shi . Da safe ya tashi cikin yanayi mai dadi da farin ciki ya laluba gefe bata nan. Kichin ya same ta tana hada abin kari. Yace zomuje ki bari su Fati su yi. Ta kalle shi, ai na sallami su Fati tun jiya. Gaban shi ya fadi, cikin in'ina yace "To me suka yi miki? " Ta yi murmushi babu komai, aikin su ya kare tunda na yi arba'in. Ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin ok na fahimta. Amma ai baza ki iya kula da gidan nan ba,ga yaro tace Zan gwada in na kasa sai mu samu mafita. Sai dai yadda Halifa ya yi ne ya sa taji kamar akwai wani abu. Ya fita da sauri bata bi bayan shi ba sai da ta dauki tiren abin kari ta fita. Baya falo kamar yadda ta zata dan haka sai ta gama hada komai sannan ta nufi dakin, karaf ya aje wayarsa da sauri bayan ta murda kofar ta shigo, ya kama fadin kin kin gama hada break fast din ne da wanka zan yi, Asiya ta yi saurin kauda shakkun ta tace yanzu muje in maka wanka sai ka zo mu karya din ko? Yace muje dai mu fara karyawa bari in yi brush. Ya kuma daukar wayar sa ya saka aljihun jallabiyar sa. Murmushin takaici Asiya ta yi sannan tace ina jiran ka a can. Ta kalli danta yana bacci a gadon sa sannan ta wuce. *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302* *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [12/4, 12:12] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt Inna bata gamsu da abinda Sulaiman ya fada ba,dan haka ta taka da kanta ta je har gidan su yaron ta same shi ta fadawa uwarsa komai, tace ita tana son yaro ya fadi gaskiya game da abinda ya sani na aiko shi da aka yi,kamar yadda ya fada haka ya maimaita Inna tace wa uwar dan Allah su lallaba mata shi ko zai fadi gaskiya. Ta kama hanya ta tafi. Yaro kuwa ya yi ta rantsuwa akan cewar iyakacin Gaskiyar shi kenan dan haka suka shedawa Inna halin da ake ciki Inna dai zuciyarta ta kasa yarda amma bata da wani zabin ko tunanin face ita dai aga ƴarta. Anty tana zaune ta zabga tagumi abin duniya ya ishe ta,wai yau duk takamar ta isarta da ikonta da juya Dady da take yi ita ya yi wa kishiya da wata mara aji. Matar da bata fi ta yi mata wanke wanke ba. Halifa da take hankoron yadda zata mallaki abinda ya mallaka ta juya ta yi sabuwar rayuwa, abinda ta gina a zuciyarta tsawon shekarun da ta rike Halifa Dady ya rusa komai ya hada ta dashi hatta danta da ta Haifa ya tsane ta. Ta farajin Duniyar ta isheta gara ma ta mutu ta huta. Katsam sai ga kiran Hajiya Talatu, bata ji wani daɗi ba,domin zuwa yanzu tana jin kunyar faɗin wai an mata kishiya. Talatu tace Sahiba me yake faruwa ne haka ba kya ɗaga waya ta. Anty tace Talatu ina cikin masifa ba karama ba, Me kuma ya faru? Ki bari kawai Me gidan nan ne ya munafurce ni ya yi aure, ta fada mata halin da ta ke ciki. Talatu ta ce "Ba ki makara ba kawata, kishiya dai dama ki saka mata date na barin gidan ki dan haka kar ma ki sata a gabanki, shi kuwa Halifa har yanzu ba shi da mata bare ɗa, kuma duk a ciki ƙoƙarin ki ne haka ta faru,aikin ki ya sa ta haukace ta bi Duniya kin ga ko hakan ma ai nasara ce, ki koma ga malamai ki ki sa a haɗa Halifa da Aljana ta aure shi bazata taɓa bari ya yi aure ba bare ya haihu, sannan ki dage ki mallake shi, farraƙa Dady da matar nan ba wani dogon aiki bane, abin kunya ne su Hajiya Gaji su ji wannan yadda suke gulmarki cewa kin tare gaba kin tare baya." Anty ta ja tsaki Bana son wannan mafitar.domin sabga ce ta cin kudi kuma bani da su. "Habiba kina da hanyar samun kudi tun kwanaki na fada miki, kin ki ne da yanzu ba wannan magnar ake yi ba. Tsaki Anty ta ja dan ta tuna abinda Hajiya Talatu ta yi ta bata shawara a kai. Tace dan Allah ki bar wannan maganar domin yanzu ko da mun hada baki yan bundiga sun dauke ni ba wanda zai damu sai su Hafsy ƙilama Dady murna zai yi ya rabu dani. "Ga Halifa? "Hajiya Talatu ta katseta. Anty tace tab ai Halifa yanzu ya fi kowa tsanata. Kwabon shi ba zai bayar ba dan fansa ta, ni dai kawai zan taho wajen ki in dan huta, dan naji Halifa yana fadin zai kira zama ina tsoron ma ko ya gano wani abu ne. Hajiya Talatu tace "Dan wannan ba damuwa zan turo miki kudi sai ki zo mana da shinkafa,kinsan Kano tafi sauki. " Anty ta fusa ta, tace Au kina fada min inzo da abincin da zanci ke nan ko? Ni da kike zuwa gidana ko sanar dani zuwanki ba kya yi sai dai ki diro min fa?" Hajiya Talatu tace "Wallahi Sahiba ba haka bane maida wukas Allah ya kawo ki lafiya." Anty tace na fasa zuwa ma ta kashe wayar. Hajiya Talatu ta sa dariya ta ce shegiya dadina da ita saurin gano inda mutum ya dosa,kar ta zo da shinkafar aikuwa ta kwashi faten tsaki. Asiya ta kula da yadda Halifa sam baya son ta kusanci wayar sa, ba kamar da ba in ankira zai ce miko min watarana ma har in yaga wani abu a tiktor zai ce zo ki gani, hatta lambobin sirrin shi ta sani, amma yanzu sai taka tsantsan. Alamu sun gama nunawa akwai abinda yake boyewa dan haka sai ta fara tunanin abinda ya kamata ta yi, dan ta dakile abin da take zargi.Abu dai mai muhimmanci shine ta hadu da Innar ta kafin komai dan haka bari ya dawo. Abinda ya daure mata kai shine yadda Halifa yau shine har karfe shabiyun dare bai dawo gida ba, mutumin da sai ya dawo gida ma sannan ya fita sallar magriba, ta kira wayar shi yafi sau hamsin amma bai daga ba, kuma ta mai text tana tambayar ko lafiya, amma babu amsa,dan haka ta sawa zuciyarta cewa tabbas Halifa ko dai ya fara neman matan da yace, ko kuma yaje gidan su Fati. Ta yi kuka har ta godewa Allah abinda ya bata mamaki da ya shigo ya ganta zaune a falo. Wai sai yace "Lafiya ba ki yi bacci ba har yanzu? Ta danne komai ta tausasa murya, ina fa lafiya baka dawo ba,yaushe zan iya kwanciya Yaya ta nufe shi da nufin rungumewa. Sai ya dakatar da ita tare da faɗin muje ciki bari inyi wanka. Kuma sai ya yi gaba ya barta turus a tsaye. A sanyaye ta bishi ciki tini har ya shige ban daki, ta kalli wayar shi akan madubi zuciyar ta tace kul karki taba masa waya baki san me zaki gano a ciki ba.Wata zuciyar tace ki duba kila ta haka zaki gano matsalar har ki san ta yadda zaki dauki mataki. Abin mamaki Halifa ya canza lambobin sa na sirri. Ko iya haka hujja ce,ta fada cike da tashin hankali. Tana canza kaya zuwa na bacci ya fito ta sani yanzu kam in komai bai kawo shi ba jarabar shi zata kawo shi tunda wani sa in ko kwaurin kafar ta ya gani ko ya yi shirin fita zai iya sake wanka. Amma abin alajabi ko kula hakan bai yi ba ya tada salla ya yi magariba da Isha 'I. Asiya tana zaune bakin gado tana kallon shi har ya idar ya isa gadon Jariri ya sunbace shi sannan ya yi masa addu'a. Asiya jiki ba kwari tace abinci fa? Ya zauna kusa da ita ya dafo kafadarta, shayi kawai zan iya sha.Ta mike zuciyar ta tana fada mata cewa tabbas Halifa ya tara da wata domin ga hujjoji, ya zo da janaba, ya yi wanka hatta sallama hadawa ya yi ke nan tun kafin magariba suke tare, wata zuciyar tace in haka ne me zai hana ya yi wanka acan inda ya yi abin? Halifa yana da kyankyami ba zai iya wanka a kowane irin bandaki ba. Daya zuciyar ta fada mata. Sannan shayi kawai yake sha bayan ya gama nutsuwa a duk dare in ya kwanta da ita. Da waɗannan tunanin Asiya ta hado shayin ta kawo masa ya karba tare da fadin "Allah ya yi miki albarka. Ta kwanta ta yi lamo. Ya gama shan shayin sa, ya kwanta ya kawo hannu ya janyo ta zuwa jikin shi, sai taji kamar tana kyankyamin shi dan haka sai ta saɓule. Yace Baby wai kina fushi ne dan na jima a waje ? Bata yi magana ba, yace To kiyi hakuri ni namiji ne, kinsan dole wani lokacin ana iya samun haka. Asiya tace "La ba komai Yaya tunda ka dawo lafiya Alhamdulillah. Dama nima wata magana nake son mu yi. Ta mecece? Ya tambaya da sauri tare da kara matsowa kusa da ita, kamar yana tsoron ta fadi wani abu da yake boyewa. Ta yi dan murmushi mai sauti na takaici, ta ce "Ba wani abu bane ina ganin gobe zanje gurin Inna kawai domin bana son alhakinta ya taba ni,tana can tana tunanin na banda ta yi tawakkali ciwonta baya son ta shin hankali. Halifa ya tashi zaune yana kallon Asiya "Na miki wani abu ne? Ya tambaye ta cikin tsoro, itama ta tashi zaune tana kallon shi. "Me zakamin Yaya kuwa? To me zai sa kice zakije gurin Inna ki bari na gama hada hujjojina ina tsoro kar ta rike ki tace na sake ki. Asiya tace In bata yarda in dawo ba,in ka hada hujjojin sai ka kawo mata shike nan sai mu dawo. Halifa ya tsorata sosai ya sauka daga kan gadon ya na Fadin kinga Baby kar ki min haka ki yi hakuri mana. tare dan Allah kar ki yi min irin wannan hukuncin, wallah rashin ki komai zai iya faruwa da ni. Ta kafe shi da ido. Ka wai ka yi hakuri Yaya. Ya soma fusata saboda ƙin jin maganar sa da ta yi, Ya kama kafadunta yace "Asiya ban yarda ki taka nan da can ba, idan har ni ne mijin ki, ina fatan kin jini ko?!!! Ta tsorata da yadda ya riƙe mata kafaɗu idanun shi sun kada sun yi jajir dan haka ta kwanta ta yi lamo,shi kuma ya koma falo yana kai kawo. Tana jiyo shi yana ta ɓari. Bai kwana dakin ba, sai dai ko da Asiya bata fita duba ina ya kwanta ba, sam bata yi bacci ba sai gefen Asbahi dan haka ta makara salla. Tana idarwa ta dauki ɗanta dake kuka tana bashi nono. Tambayar kanta ta ke wai dama haka rayuwar aure take cike da kalubale ko kuwa dai nata ce ta zo a haka? Tun da ta yi aure daga wannan sai wannan Hasashen da ta ke yi a cikin aure ashe abin ba haka bane ance ana yin aure dan a huta ita dai har yanzu baza ta dorar da komai ba,to yanzu wane mataki ya kamata ta dauka, tana bukatar me bata shawara amma waye? Ta gaji da yin shawara da zuciyarta. A lokacin kuwa zuciyar ta faɗa mata cewa kawai ki tafi gurin Innar ki, dubi yaje gurin wata kilama wani abin suka aikata ya dawo kuma zai hau wani fushi. kawai ki gama shirin ki kiyi wucewar ki duk abinda zai faru ya faru. Ta kwantar da yaron ta fita falo zuwa kitchen. Yana zaune akan kujera yana jan carbi sai dai kayan da ta gani a zube a kasa duk an watso su wasu ma sun fashe shine a fushin jiya ya yi wannan aikin baya iya zama bai yi barna ba in ya fusata fushin sa baya sarrafuwa ta daɗi, kamar ta wuce sai wata zuciyar tace Asiya ki gaida shi mana. Dan haka ta dube shi tace ina kwana Yaya? Ya kalle ta ya kuma kalli inda yake zaune ta gane me yake nufi wai ta kusan to shi,amma sai ta kasa kusanto shi tana jin tsoro gashi bai yi magana ba, bare ta gane ina ya saka gabanshi. Yana cikin fushi ko ya sauka. Ki wuce kawai ai Allah ya gani kin gaishe shi. Zuciyarta ta rada mata. Dan haka sai ta wuce zuwa kicin. Tana kokarin hada karin kumallo yayin da wata zuciya ke faɗa mata cewa ba fa ta kyauta ba, Lalai ta koma ta kusance shi ta gaidashi kamar yadda suka saba. Ji tayi an rungume ta ta baya, a kunne yake rada mata cewa Baby da gaske tafiya za kiyi ki barni? Kece fa komai nawa kece rayuwata bani da kowa sai ke sai danki. Asiya ta juyo ta rungume shi, " Ba iya son ka kawai nake ba Yaya Ina kaunar ka sosai Yaya dan Allah kar ka kawo ruɗani a zaman mu wallahi bazan jure ba. Ya sauke ajiyar zuciya ya dago fuskarta hawaye suna sauka akan kumatun ta, Baby Wallahi bazaki taba danasani na aure na ba. Ki kwantar da hankalin ki, cikin satin nan zaku ga Inna ta dauki Babana ta yi masa addu'a cikin farin ciki, in kinje yanzu ba wani bayani kin fini sanin wacece Inna. Asiya ta sauke ajiyar zuciya miji da mata sai Allah wanda ya shiga zai ji kunya Asiya ta sauka kuma ta hakura da zuwa gurin Inna saidai ta kara jaddada masa lallai ya sada ta da Inna nan kusa. Ya yi mata alkawarin haka. Wayar shi ta shiga ruri ya sake ta ya ciro wayar ta kai duba fuskar wayar ko zata ga sunan waye, ta dai ga wasu haruffa ya yi saurin fita a kicin din ya bar falon ma can harabar gidan ya fita tana kallon shi ta window yana kai kawo duk da bata iya jiyo me yake fada ta tabbatar da mace yake wayar domin tana iya hangen hakan a fuskarsa. Hawaye suka zubo mata a fili tace wannan kuma wace irin masifa ce? Gaskiya ina bukatar mai bani shawara akwai bukatar in sanar da wani damuwata ko zan samu sauki. *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [12/4/2025, 12:12] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt Inna bata gamsu da abinda Sulaiman ya fada ba,dan haka ta taka da kanta ta je har gidan su yaron ta same shi ta fadawa uwarsa komai, tace ita tana son yaro ya fadi gaskiya game da abinda ya sani na aiko shi da aka yi,kamar yadda ya fada haka ya maimaita Inna tace wa uwar dan Allah su lallaba mata shi ko zai fadi gaskiya. Ta kama hanya ta tafi. Yaro kuwa ya yi ta rantsuwa akan cewar iyakacin Gaskiyar shi kenan dan haka suka shedawa Inna halin da ake ciki Inna dai zuciyarta ta kasa yarda amma bata da wani zabin ko tunanin face ita dai aga ƴarta. Anty tana zaune ta zabga tagumi abin duniya ya ishe ta,wai yau duk takamar ta isarta da ikonta da juya Dady da take yi ita ya yi wa kishiya da wata mara aji. Matar da bata fi ta yi mata wanke wanke ba. Halifa da take hankoron yadda zata mallaki abinda ya mallaka ta juya ta yi sabuwar rayuwa, abinda ta gina a zuciyarta tsawon shekarun da ta rike Halifa Dady ya rusa komai ya hada ta dashi hatta danta da ta Haifa ya tsane ta. Ta farajin Duniyar ta isheta gara ma ta mutu ta huta. Katsam sai ga kiran Hajiya Talatu, bata ji wani daɗi ba,domin zuwa yanzu tana jin kunyar faɗin wai an mata kishiya. Talatu tace Sahiba me yake faruwa ne haka ba kya ɗaga waya ta. Anty tace Talatu ina cikin masifa ba karama ba, Me kuma ya faru? Ki bari kawai Me gidan nan ne ya munafurce ni ya yi aure, ta fada mata halin da ta ke ciki. Talatu ta ce "Ba ki makara ba kawata, kishiya dai dama ki saka mata date na barin gidan ki dan haka kar ma ki sata a gabanki, shi kuwa Halifa har yanzu ba shi da mata bare ɗa, kuma duk a ciki ƙoƙarin ki ne haka ta faru,aikin ki ya sa ta haukace ta bi Duniya kin ga ko hakan ma ai nasara ce, ki koma ga malamai ki ki sa a haɗa Halifa da Aljana ta aure shi bazata taɓa bari ya yi aure ba bare ya haihu, sannan ki dage ki mallake shi, farraƙa Dady da matar nan ba wani dogon aiki bane, abin kunya ne su Hajiya Gaji su ji wannan yadda suke gulmarki cewa kin tare gaba kin tare baya." Anty ta ja tsaki Bana son wannan mafitar.domin sabga ce ta cin kudi kuma bani da su. "Habiba kina da hanyar samun kudi tun kwanaki na fada miki, kin ki ne da yanzu ba wannan magnar ake yi ba. Tsaki Anty ta ja dan ta tuna abinda Hajiya Talatu ta yi ta bata shawara a kai. Tace dan Allah ki bar wannan maganar domin yanzu ko da mun hada baki yan bundiga sun dauke ni ba wanda zai damu sai su Hafsy ƙilama Dady murna zai yi ya rabu dani. "Ga Halifa? "Hajiya Talatu ta katseta. Anty tace tab ai Halifa yanzu ya fi kowa tsanata. Kwabon shi ba zai bayar ba dan fansa ta, ni dai kawai zan taho wajen ki in dan huta, dan naji Halifa yana fadin zai kira zama ina tsoron ma ko ya gano wani abu ne. Hajiya Talatu tace "Dan wannan ba damuwa zan turo miki kudi sai ki zo mana da shinkafa,kinsan Kano tafi sauki. " Anty ta fusa ta, tace Au kina fada min inzo da abincin da zanci ke nan ko? Ni da kike zuwa gidana ko sanar dani zuwanki ba kya yi sai dai ki diro min fa?" Hajiya Talatu tace "Wallahi Sahiba ba haka bane maida wukas Allah ya kawo ki lafiya." Anty tace na fasa zuwa ma ta kashe wayar. Hajiya Talatu ta sa dariya ta ce shegiya dadina da ita saurin gano inda mutum ya dosa,kar ta zo da shinkafar aikuwa ta kwashi faten tsaki. Asiya ta kula da yadda Halifa sam baya son ta kusanci wayar sa, ba kamar da ba in ankira zai ce miko min watarana ma har in yaga wani abu a tiktor zai ce zo ki gani, hatta lambobin sirrin shi ta sani, amma yanzu sai taka tsantsan. Alamu sun gama nunawa akwai abinda yake boyewa dan haka sai ta fara tunanin abinda ya kamata ta yi, dan ta dakile abin da take zargi.Abu dai mai muhimmanci shine ta hadu da Innar ta kafin komai dan haka bari ya dawo. Abinda ya daure mata kai shine yadda Halifa yau shine har karfe shabiyun dare bai dawo gida ba, mutumin da sai ya dawo gida ma sannan ya fita sallar magriba, ta kira wayar shi yafi sau hamsin amma bai daga ba, kuma ta mai text tana tambayar ko lafiya, amma babu amsa,dan haka ta sawa zuciyarta cewa tabbas Halifa ko dai ya fara neman matan da yace, ko kuma yaje gidan su Fati. Ta yi kuka har ta godewa Allah abinda ya bata mamaki da ya shigo ya ganta zaune a falo. Wai sai yace "Lafiya ba ki yi bacci ba har yanzu? Ta danne komai ta tausasa murya, ina fa lafiya baka dawo ba,yaushe zan iya kwanciya Yaya ta nufe shi da nufin rungumewa. Sai ya dakatar da ita tare da faɗin muje ciki bari inyi wanka. Kuma sai ya yi gaba ya barta turus a tsaye. A sanyaye ta bishi ciki tini har ya shige ban daki, ta kalli wayar shi akan madubi zuciyar ta tace kul karki taba masa waya baki san me zaki gano a ciki ba.Wata zuciyar tace ki duba kila ta haka zaki gano matsalar har ki san ta yadda zaki dauki mataki. Abin mamaki Halifa ya canza lambobin sa na sirri. Ko iya haka hujja ce,ta fada cike da tashin hankali. Tana canza kaya zuwa na bacci ya fito ta sani yanzu kam in komai bai kawo shi ba jarabar shi zata kawo shi tunda wani sa in ko kwaurin kafar ta ya gani ko ya yi shirin fita zai iya sake wanka. Amma abin alajabi ko kula hakan bai yi ba ya tada salla ya yi magariba da Isha 'I. Asiya tana zaune bakin gado tana kallon shi har ya idar ya isa gadon Jariri ya sunbace shi sannan ya yi masa addu'a. Asiya jiki ba kwari tace abinci fa? Ya zauna kusa da ita ya dafo kafadarta, shayi kawai zan iya sha.Ta mike zuciyar ta tana fada mata cewa tabbas Halifa ya tara da wata domin ga hujjoji, ya zo da janaba, ya yi wanka hatta sallama hadawa ya yi ke nan tun kafin magariba suke tare, wata zuciyar tace in haka ne me zai hana ya yi wanka acan inda ya yi abin? Halifa yana da kyankyami ba zai iya wanka a kowane irin bandaki ba. Daya zuciyar ta fada mata. Sannan shayi kawai yake sha bayan ya gama nutsuwa a duk dare in ya kwanta da ita. Da waɗannan tunanin Asiya ta hado shayin ta kawo masa ya karba tare da fadin "Allah ya yi miki albarka. Ta kwanta ta yi lamo. Ya gama shan shayin sa, ya kwanta ya kawo hannu ya janyo ta zuwa jikin shi, sai taji kamar tana kyankyamin shi dan haka sai ta saɓule. Yace Baby wai kina fushi ne dan na jima a waje ? Bata yi magana ba, yace To kiyi hakuri ni namiji ne, kinsan dole wani lokacin ana iya samun haka. Asiya tace "La ba komai Yaya tunda ka dawo lafiya Alhamdulillah. Dama nima wata magana nake son mu yi. Ta mecece? Ya tambaya da sauri tare da kara matsowa kusa da ita, kamar yana tsoron ta fadi wani abu da yake boyewa. Ta yi dan murmushi mai sauti na takaici, ta ce "Ba wani abu bane ina ganin gobe zanje gurin Inna kawai domin bana son alhakinta ya taba ni,tana can tana tunanin na banda ta yi tawakkali ciwonta baya son ta shin hankali. Halifa ya tashi zaune yana kallon Asiya "Na miki wani abu ne? Ya tambaye ta cikin tsoro, itama ta tashi zaune tana kallon shi. "Me zakamin Yaya kuwa? To me zai sa kice zakije gurin Inna ki bari na gama hada hujjojina ina tsoro kar ta rike ki tace na sake ki. Asiya tace In bata yarda in dawo ba,in ka hada hujjojin sai ka kawo mata shike nan sai mu dawo. Halifa ya tsorata sosai ya sauka daga kan gadon ya na Fadin kinga Baby kar ki min haka ki yi hakuri mana. tare dan Allah kar ki yi min irin wannan hukuncin, wallah rashin ki komai zai iya faruwa da ni. Ta kafe shi da ido. Ka wai ka yi hakuri Yaya. Ya soma fusata saboda ƙin jin maganar sa da ta yi, Ya kama kafadunta yace "Asiya ban yarda ki taka nan da can ba, idan har ni ne mijin ki, ina fatan kin jini ko?!!! Ta tsorata da yadda ya riƙe mata kafaɗu idanun shi sun kada sun yi jajir dan haka ta kwanta ta yi lamo,shi kuma ya koma falo yana kai kawo. Tana jiyo shi yana ta ɓari. Bai kwana dakin ba, sai dai ko da Asiya bata fita duba ina ya kwanta ba, sam bata yi bacci ba sai gefen Asbahi dan haka ta makara salla. Tana idarwa ta dauki ɗanta dake kuka tana bashi nono. Tambayar kanta ta ke wai dama haka rayuwar aure take cike da kalubale ko kuwa dai nata ce ta zo a haka? Tun da ta yi aure daga wannan sai wannan Hasashen da ta ke yi a cikin aure ashe abin ba haka bane ance ana yin aure dan a huta ita dai har yanzu baza ta dorar da komai ba,to yanzu wane mataki ya kamata ta dauka, tana bukatar me bata shawara amma waye? Ta gaji da yin shawara da zuciyarta. A lokacin kuwa zuciyar ta faɗa mata cewa kawai ki tafi gurin Innar ki, dubi yaje gurin wata kilama wani abin suka aikata ya dawo kuma zai hau wani fushi. kawai ki gama shirin ki kiyi wucewar ki duk abinda zai faru ya faru. Ta kwantar da yaron ta fita falo zuwa kitchen. Yana zaune akan kujera yana jan carbi sai dai kayan da ta gani a zube a kasa duk an watso su wasu ma sun fashe shine a fushin jiya ya yi wannan aikin baya iya zama bai yi barna ba in ya fusata fushin sa baya sarrafuwa ta daɗi, kamar ta wuce sai wata zuciyar tace Asiya ki gaida shi mana. Dan haka ta dube shi tace ina kwana Yaya? Ya kalle ta ya kuma kalli inda yake zaune ta gane me yake nufi wai ta kusan to shi,amma sai ta kasa kusanto shi tana jin tsoro gashi bai yi magana ba, bare ta gane ina ya saka gabanshi. Yana cikin fushi ko ya sauka. Ki wuce kawai ai Allah ya gani kin gaishe shi. Zuciyarta ta rada mata. Dan haka sai ta wuce zuwa kicin. Tana kokarin hada karin kumallo yayin da wata zuciya ke faɗa mata cewa ba fa ta kyauta ba, Lalai ta koma ta kusance shi ta gaidashi kamar yadda suka saba. Ji tayi an rungume ta ta baya, a kunne yake rada mata cewa Baby da gaske tafiya za kiyi ki barni? Kece fa komai nawa kece rayuwata bani da kowa sai ke sai danki. Asiya ta juyo ta rungume shi, " Ba iya son ka kawai nake ba Yaya Ina kaunar ka sosai Yaya dan Allah kar ka kawo ruɗani a zaman mu wallahi bazan jure ba. Ya sauke ajiyar zuciya ya dago fuskarta hawaye suna sauka akan kumatun ta, Baby Wallahi bazaki taba danasani na aure na ba. Ki kwantar da hankalin ki, cikin satin nan zaku ga Inna ta dauki Babana ta yi masa addu'a cikin farin ciki, in kinje yanzu ba wani bayani kin fini sanin wacece Inna. Asiya ta sauke ajiyar zuciya miji da mata sai Allah wanda ya shiga zai ji kunya Asiya ta sauka kuma ta hakura da zuwa gurin Inna saidai ta kara jaddada masa lallai ya sada ta da Inna nan kusa. Ya yi mata alkawarin haka. Wayar shi ta shiga ruri ya sake ta ya ciro wayar ta kai duba fuskar wayar ko zata ga sunan waye, ta dai ga wasu haruffa ya yi saurin fita a kicin din ya bar falon ma can harabar gidan ya fita tana kallon shi ta window yana kai kawo duk da bata iya jiyo me yake fada ta tabbatar da mace yake wayar domin tana iya hangen hakan a fuskarsa. Hawaye suka zubo mata a fili tace wannan kuma wace irin masifa ce? Gaskiya ina bukatar mai bani shawara akwai bukatar in sanar da wani damuwata ko zan samu sauki. *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [12/8/2025, 09:11] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302* Ta na gama jera abinci akan Dining ya fito wanka, yana gama shiryawa ya same ta akan Dining ɗin tana haɗa masa shayi, bai zauna ba ya karɓa kafin ya kurɓi shayin daga tsaye, ya ɗora da fadin ana jirana Baby ba zan iya zama ba, akwai wani baƙo yana jira na kwastoma ne daga nesa yake, ki kula sosai kar fa kije ko ina. Bata amsa ba tana kallon shi yana magana yana satar kallon ta, yana in'ina, shi dai mara gaskiya ko aruwa sai ya yi zufa ta ɗarsa haka a zuciyarta. Ya matso ya shafi kumatun ta, kina bukatar wani abu ne? Wayar shi ta sake rigin ya kalle ta da sauri bayan ya kalli fuskar wayar, ya daga minti biyar kacal dan Allah gani nan yanzu. Ya katse, yasake dubanta zan kawo wani abu ne? Ta girgiza kai, To kimin addu'a mana ya fada kamar dai mara gaskiya. Ta danne zuciyar ta, ta ja dogon numfashi, a hankali ta furta Allah ya tsare. Na gode ya fada da sauri. Gudu gudu ya fita. Wata zuciyar tace dama ki bishi ki ga ina zashi haka, ya zuba kaya masu kyau yana ta kamshi, da ka ganshi kaga matashin mai kudi, ko karyawa ya kasa. Ta tashi a gurin ta koma falo domin ita ma baza ta iya cin komai ba. Ta shiga zirga zirga da tunanin mafita,wayar ta ta tuna lokacin da Hajjo suke nan suna sauraron shirin rai dangin goro ta ji Labarin Hamshakiyar Uwa tun bata sauraro in suna ji har itama tazo tana ji, Fati ce ta bata lambar marubuciyar da niyyar zata sai littafin tun da bataji farkon labarin ba, bata ma samu ta siya din ba, amma dai zata kira marubuciyar dan ta nemi shawara tana kyauta ta mata zato. Ta kira layin sau biyu duk ba a daga ba, tace Ummm dama fa ana cewa irin wadanan suna da wulakanci bari dai in sake tunanin wa zan kira. Doni in rage wannan damuwar ta hanyar fada wa wani halin da nake ciki.Kukan danta ta jiyo dan haka ta nufi dakin da sauri,tana daukar shi wayarta ta soma ringing. Ta kalla Number da ta kira ce, da sauri ta daga tana Sallama marubuciyar ta amsa amma sai ta jiyo kukan jariri, sai tace a kula da me kukan nan tukunna. Asiya tace "To Anty zan kira ki anjima kadan. Anty Halima tace ba damuwa. Sai taji kamar matsalar ta ta yaye, kamar ta gama samun mafita,ba shakka Anty Halima zata bata shawara. Sai da ta gama dashi tsaf ya sha wanka ya koma bacci sai ta koma falo ta zauna ta sake kiran Anty Halima. Bayan sun gaisa Asiya tace To Anty ni bansan yadda zan yi miki bayani ba, ni dai na kasance ina karanta littafin ki kuma ina da shawara da nake nema. Anty Halima tace babu damuwa ina sauraron ki ki yi magana kamar kina tare da mahaifiyar ki ko wata yayarki ta jini. Asiya ta sake samun nutsuwa ta kwashe dukkan labarinta har zuwa inda ake yanzu ta sanar da Anty Halima.lokacin katin Asiya ya kare, tana kokarin cin bashin kati sai ga shi Anty Halima ta kira, . Asiya ta daga tace bari in saka kati Anty Halima tace babu damuwa ci gaba. Asiya tace Yanzu dai haka kinga ya fita yau ko karyawa bai yi ba, kuma ina zargin wata ce ta kira shi. Sai ta fashe da kuka. Anty Halima tace Yi hakuri ki saurara da kukan haka, kina jina, ki nutsu, kuma yadda baki masa magana ba ina baki shawara karki yi masa maganar, domin shiru hanyace ta dafa mutum a ruwan sanyi musamman abokin zama, kuma ki daure ki daina nuna masa wata alama da ke nuna kina zarginsa. Abu na farko ki rage bacci ki fadawa Allah duk wata damuwar ki cikin dare, sannan ki daina saka ido akan wayarsa karma ki sake dauka,domin zaki iya ganin abinda zai kawo karshen zama lafiyar ku har na nan gaba. Asiya tace Allah ya sa in iya zan gwada. Sai abu na gaba maganar Mahaifiyar ki tun da abin da zai faru ya riga ya faru, to kawai ki saurari lokacin da ya ce ki bashi din, domin tafiyarki ke kadai kuma kina cikin damuwa zai iya haifar da komai tunda kina son mijinki ko kuwa? Asiya tace haka ne. Ni yanzu abinda yafi daga min hankali Anty Halima guda ɗaya ne ya fita gurin wata zuciya ta wallahi tana cike da kunci. Kina da tabbacin gurin wata ya fita? Anty Halima ta katse ta. Asiya ta soma kuka Ina da tabbaci Anty, boye boyen da yake yi min fa? Kuma ai ko me aiki na ya nuna damuwa da na sallame su. Ina zargin ma ko ita yake bi. Assha!! Inji Anty Halima, ta katseta, kar ki yanke hukuncin da iya hasashe ba lallai ya zama gaskiya ba, amma ki daure ki kau da kanki, kinsan fa zargi in ya yi yawa yana bata aure. Ki yi masa addu'a ko ya dawo kar ki nuna masa, cin amana bata dorewa a cikin aure, kuma yana bukatar ki kusa da shi tunda shi ba mai abokai bane barkatai yawan shige masa da bashi shawara za su taimaka miki gurin maido shi hanya,karki nuna kyankyami a gare shi ko da ta tabbata cewa kin kamashi dumu dumu na abinda ki ke hasashe. Hakan zai ba matan wajen damar samun shi, kin fada min cewa shi mutum ne mabukaci ga kudi ga lafiya dan haka ki ja abinki a jiki, Mata da ki ke gani a wannan zamanin su ne ke neman mazan da kansu Dan haka ki kula sosai amma addu'a tafi komai muhimmanci kar ki manta. Asiya ta yi godiya suka yi sallama duk da ta samu kwanciyar hankali kadan sai dai fa bata yarda wai ta kauda kai ba. Ina zata samu labarin su Fati, tana son sani ko fati ya ke so. Ta tuna da nurse wadda ta ke kula da baby, ta daga waya ta kira ta suka gaisa, ta tambayi yaro tace ko anyi masa allurar wata ta farko da ake yi? Ta ga ya wuce sati shida. Asiya tace ba ayi ba, ai su basu san anayi ba. Nurse tace ya kamata ku kai shi yau ko gobe, Asiya tace insha Allahu. Sannan tace yawwa wai kuwa kinsan wannan Hajjo din da suka min aiki Ina nufin Unguwar su. Nurse tace kinsan tana aikin shara ne a Asibitin mu,na dai san kamar a Darmanawa aka ce take amma bansan gidan ta ba. Asiya tace Allah sarki Dan Allah ko zaki iya samo min lambarta sai dai dan Allah karki ce ni ce, ina son ne in ziyarce ta, na bazata, ta yi min mutunci kamar yarta ko jikarta muka zauna. Nurse tace "Ki tambayi megidanki mana ai kamar ba zai rasa ba. Asiya tace bashi da ita gaskiya, domin dashi mukayi maganar yace in tambaye ki. Nurse tace to in naganta zan karba miki, in kuma bata bayarba shike nan.Sai bayan sun yi sallama zuciyar ta ke ce mata wai me kike son aikatawa ne Asiya. Cikin sa a ba a jima ba,lambar ta shigo. Asiya kuwa ta kira Hajjo suka gaisa da ta tabbatar Hajjo bata gane ta ba, sai tace wai ita kawar Fati ce daga Maiduguri ta kira lambar Fati bata samu ba shine ta ke son a hada su. Hajjo tace Allah sarki ga shi kuwa Fati yau tun safe suka fita ni ma na kira layin nata ma baya shiga ko bata da caji ne. Gaban Asiya ya fadi, zufa ta karyo mata kenan dai suna tare, tace na shiga uku.ta darsa a zuciyarta ta. To dan Allah ko zaki tura min lambar ta wannan da nake ta kira din kamar tsohon layinta ne Intel ko shine har yanzu? Hajjo tace A a wannan MTN ne bari zan turo miki sai ki gwada,amma yau ko kunu bata sha ba ta fice tana sauri. Asiya tace Allah sarki ko ta samu aikin ne da tace min tana nema? Hajjo tace gurin wani ma ta tafi da zai saka sunan ta a aikin poliyo zan turo miki lambar yanzu sai anjima. Asiya ta yi shiru tana nazari kenan karya Fati ta yi wa Hajjo dan ta fita da Halifa maganar aure suke yi kokuwa dai sakarcin su za su yi? Kuka Asiya ta zauna tana rerawa, zuciyar ta tana tafasa wata zuciyar ta faɗa mata cewa kuka fa bazai zame mata mafita ba. Ta kira layin Halifa bai daga ba sai a kashi na uku, ya daga kafin ta yi magana ya rigata,muryarsa can kasa kasa, gashi sai taji gurin yana amsawa. Yace "Baby Yaya akwai damuwa ne? Ta ce dama Nurse ce muka yi waya tace min ya kamata a kai yaron nan allurar sati shidda yau ko zaka zo yanzu ka kai mu? Yace Baby tace dole sai yau ba za a bari gobe ba? Inda nake yanzu ba zan iya fitowa ba gaskiya. Gaban Asiya ya kuma yanke wa ya fadi, kenan wata ta fi su muhimmanci. Kin san ya za ayi?" Ya katse mata tunani. "Ki samu dan Adaidaita sahu sai ki hada ni da shi muyi magana,amma ki kula kar ki fita ba tare da kin rufe fuskar ki ba, kar ki hadu da wani. Asiya ta kuma hadiye fushinta tace Yaya ba kudi a gurina. Yace "Ki bude Sif din nan karama zan turo miki lambar da zaki saka ki bude yanzu sai ki dauki dubu goma in na zama free zan kira ki kinji, ki kula da kanki. Bai jira amsarta ba kawai ya kashe wayar. Hakan ya tabbatar miki da cewa suna tare da wata Zuciyar ta ta fada mata. Ta soma hasaso su shi da Fati da abubuwan da suke aikatawa. Karar shigowar sako taji a wayar ta, lambobin da zata buda ma adanar kudin ce. Tana kuka ta bude, kudi ta gani kaloli na kasashen waje ta kirgi dubu goma ta kudinmu na Najeriya ta mayar ta rufe. Ta saka face marks amma bata kira shiba lokacin da ta samu me dan sahu. Taje Asibitin ta kira Nurse aka yi musu allurar ta tambayi. Nurse ko sunyi waya Nurse ta ce mata a a bai kira ba, har ta tambayi Asiya ko lafiya ta ganta duk a Hargitse Asiya tace ba komai bari ta tafi. Zuciyarta tace kawai ta wuce gurin Inna dan haka ta samu dan sahu dan ya kaita Fage, sai dai suna kaiwa kwari tace da me Adaidaita dan Allah ka kai ni Hotel. Ya juyo ya dube ta da sauri,"Hotel kuma baiwar Allah?" Tace wata kawata zan duba. Yace To wane Hotel din aciki? Asiya ta dan yi shiru ta manta ashe fa Hotel din da yawa. Can tace wanda haka maza ke zuwa da mata ni na manta sunan shi, kai baka san wani Hotel haka ba wanda maza ke kai mata ka kaini in duba ta sai ka maida ni Gandun sarki zan biya ka. Dan sahu ya yi yar dariya wannan kuwa tasan adadin Hotel din garin nan? Sannan ya juya kan Adaidaita ya nufi hanyar Nasarawa yace zan kai ki dai inda mutane suka fi dabdala Tahir ko kuma Ni'i ma sai ki duba.Tace To gaban ta ya kara tsanan ta faduwa, Daidai rawul din gidan Gwamna kawai ta hangi motar Halifa ta daya hannun suna fitowa daga titin da za su hau, da sauri tace wa mai keken Juya ka bi waccan bakar motar ga su can. Ya yi ganganci ya yanke ya fasa shaga titin ya sha rawul suka bisu. Duk da danja ta tsaida su bayan wucewar motar su Halifa shima mai dan sahu ya bisu bai tsaya ba,. Yace mata wannan ai kasuwar Farmcenter ya nufa, tace muje dai. Kafin su same su har sun bar gurin sun dai samu motar, a gurin paking na kasuwar. Asiya ta kalli lokaci a wayarta, karfe uku tun safe. Ta dubi me a daidaitar tace hanyar Hotel din ne suka fito ko? Yace e nan ne. Tace shike nan kaini Gandun Sarki. *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [12/11/2025, 08:53] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302* Bintu tana girki a kicin ta ji an banko kofar falo ta fito Hafsi ce ta shigo. Bintu tace Au ke ce ? Hafsi ta amsa cike da rashin kunya wallahi fa sai kin bar gidan nan tunda ba gidanku bane. Bintu tace ki fada wa wanda ya kawo mu mana sai ya zo ya fitar da mu. Ta dungure kan Ahmad tana fadin kai dena kallo na mummunan banza. Bintu tace Ko zaki mutu ki dawo dai kanin ki ne shi ba yadda zaki yi. Fitar min daga nan. "Bazan fita ba. 'Bintu tace OK jira,ta dauki waya karki fita dama ai ba wannan ne zuwanki na farko ko na biyu kina min rashin kunya ba, bari in sanar da Ubanki sai ya taka miki birki. Har lokacin da Dady ya daga yana jiyo muryar Hafsi tana zazzagawa Bintu rashin kunya. Ta ce Abban Ahmad Yarinyar nan ba yaune na farko ta zo ta ci mutunci na ba, ta dinga dukan yaran nan, in ba dama gara ka sama min wani gurin. Dady yace "Kiyi hakuri Bintu karki da mu kar ki kulata uwarta ke turo ta, zan yi maganin abin idan na dawo. Tace To.a Hands free ne Hafsi ta ji komai. Dan haka ta saki dariya,wai Abban Ahmad duk mu ba Abban mu bane to sai kun jira daga ke harsu akwai wasu a gaban ku. Ta yi ball da wani filet na tangaran dake kusa da ita ta wuce. Tana fita Bintu ta maida kofa ta rufe ta lallashi yaranta. Da dare Dady ya samu Hafsi a dakin Anty dama tun da taji dawowarshi ta shige dakin. Yace ke dama wato zuwa ki ke kina cimin zarafin mata kina dukar min yara ko? To wallahi na gargade ki duk san da kika kara taba min su sai na rama masu, sannan kuma zuwa ranar asabar in saurayin ki bai fito ba ranar Lahadi zan saka ranar auran ki da duk wanda na ga zai rike ki,wanda in iyashege ki ke ji ya fiki, ya fice abinsa. Anty ta kalleta, Wai bana ce ki daina shiga harkar matar nan ba ne? Kinsan dai Dady tunda ya furta maganar aure kuma ya samu goyon bayan su Halifa ki bishi a hankali. Ni yanzu kinga ina kula shi ne? Hafsi tace Wallahi Anty kamar in kashe matar nan da yaranta na ke ji na tsane su,tsana me tsanani. Ke kuma sai ki zuba musu ido su zauna lafiya a gidan nan? Anty tace 'To fada min yadda zan yi tunda kin ce i na saka musu ido,, fada min. Kina kallon yadda na koma abin Duniya ya ishe ni, ba wanda na isa in fadawa ya ji, shi kanshi Dadynku da yake matukar shakkata yanzu tsoron shi nake yi, tun da abinda na yi ya karye. Hafsi tace to ki sake yi mana Anty ki dawo da izzarki kin fi kwarjini dubi yadda kika koma yanzu ko su Nihal ba tsoron ki suke ji ba. wallahi. Anty ta ja tsaki tare da faɗin Ana baki kina kin karɓa. Ni dai yanzu kinji abinda ya fada ki turo min Hafizun inyi magana da shi wannan kwane kwane da yake yi fa ya isa haka. Hafsi ta dan yi shiru can tace "Anty wai kawun sa dake Abuja ne ya tafi Ummara sai ya dawo tukunna. Anty tace ai ki fada masa kawai ya zo ina son ganin sa. Kema na ga nema ki ke ki sa min ciwon zuciya bayan na hawan jini da suka sa min. Hafsi ta fita tana kunkunai. Bros ya shigo dakin da sallama ta daga kai ta kalle shi tun ranar da aka yi wannan hatsaniyar rabon shi da gidan. Fuskarshi babu walwala ya gaida Anty ta amsa ita ma fuskar ta a dake, tana ganin bai kyauta mata ba,tunda ya zabi Babanshi. Ta Katse shiru da faɗin "Ai na zaci baza ka kuma zuwa inda nake ba tunda na fadawa ubanka magana bayan ni baku kalli girma zunubin da ya aikata min ba. Bros yace Anty ni ba wannan ya kawo ni ba, na zo ne in fada miki in su Nihal sun taso daga makaranta zan zo da dare zan tafi dasu su koma gida. Ta kankance ido tana kallon shi, me kake nufi gurin wannan shashashar matar ta ka zaka kai su? To ban yarda ba, in har ina raye baza a kai su ba makira ce ba yarinyar arziƙi bace. Bros yace ita ma kuma makira ce, to aike kika zaba min ita saboda kin yarda da ingancinta. Kuma dai zuwa yanzu banace ga laifinta ba. Anty tace "Kara da kiyashi ne daukar marasani na yi. Ya gyara zama, gurin uwarsu ma zan kai su, akwai abinda ban fada miki ba, Ya kalli Anty wadda ta zaro ido tana kallon shi so yake ya maida matar shi ke nan, aiko ba zai yiwu ba. Kinsan na maida mamansu. Ya katse mata tunani." Ka maida wa ka ce?" Wannan mai kashin tsiyar ka maida wadda ka shiga matsala saboda farar kafarta, ai kuwa zaka kuma sakinta domin ba zai yiwu ba. In ko ba haka ba,gara in tsine maka gaba daya. Bros yace "Anty na maida matata tun a satin da kika sa na sake ta, mun zauna a Hotel kafin na kama haya, yanzu haka ta haihu muna da yaro wanda na yi wa Dady takwara da shi, har ma ya fara tafiya, dan haka babu wata farar kafa da mata ta take da shi, domin duk abinda na samu yanzu ina tare da ita na samu dan haka sai dai ki tsine min din in kina son hakan amma babu hujja, babu kwakwkwaran dalili sannan ina me neman gafarar ki idan abinda na aikata ya bata miki to ki yafe min, zan dawo anjima in dauke su su koma gurin maman su. Saboda tsanani mamaki Anty bata iya furta ko kalma daya ba, har Bros ya fice,ta yi mutuwar zaune. Wane irin wasan kwaikwayo ne ake yinsa a gidanta haka? Da farko mijinta ya zo da mace da yara biyu ya yi aure a boye, yanzu kuma Babban danta ya zo wai ya maida matar da ta tsana, kuma har sun haihu, bayan ta bibiya an fada mata cewa matar nan ta yi aure a wani gari. Wai tana ina duk haka ta faru, bacci ko me? Zufa ta soma karyo mata me yasa abubuwa yanzu suke ta zuwa mata bai bai? Me ta yi ba daidai ba a rayuwar ta. Kuka ta ke son yi amma ta kasa. Tabbas inta mike zata faɗi a zaunen ma jiri take gani dan haka ta jingina bayanta da bango. Ta lumshe ido da kyar ta samu wasu hawaye suka soma ziraro mata ta gefen ido. *** *** *** Asiya ta shiga gida cike da bakin ciki, ga dai gida har gida haka kuma ga ababen more rayuwa amma babu farin ciki a cikin shi bare kwanciyar hankali. Asiya ta darsa haka a cikin zuciyar ta lokacin da take bin ko ina na gidan da kallo. Ta zauna a kujera ta sauke danta wanda ke ta kuka saboda allurar da aka yi masa dama an fada mata zai ta rigima. Wai haka rayuwar take ne babu wani sauki a cikinta? Asiya ta tambayi kanta a fili. Ta sa yaron a kafada tana jijjiga shi, tana kai komo a tsakiyar falo gashi tun abin kari bata ci ba komai,yau ko gado bata gyara ba bare kuma gidan, kuma bata jin zata iya yin wani abu. Motar baƙin gilashi gareta hakan ya hana ta ga ko wacece a ciki, bata da tabbacin cewa Fati ce shine ya hana ta dauki mataki akan ta. Cikin yanayin ta yini ba ci ba sha salla kawai ta ke yi sai jijjiga ɗanta da yake ta kuka, sai kuwa kukan ita ma da take sha. A haka goma ta wuce sha daya ta kawo jiki na dare. Ta ji shigowar motar sa, tana ta shawara akan abinda zata yi masa ko zata ji sanyi Tana ga kamar ta tunkare shi da zancan. Zantukan marubuciyar suka fado mata, anya zata bi wadannan shawarin sun mata tsauri addu'a dai zata ta shi ta yi dan ta san bazata iya bacci ba ma, amma ta kauda kai kar ta nuna ko alamar ta na zargin sa abu ne mawuyaci. Bata san ya shigo ba, tana kai kawo a falon ɗa na kuka. Sai Murya shi taji yana tambayar me ya same shi? Tare da kai hannu zai dauke shi, ta ja da baya cikin sauri kamar wadda taga abin tsoro fuskatar ta ta yi suntum da kuka, yace "Ya Subahanallah, Kema taya shi kukan kika yi? Ta kau da kai,kowa da nashi dalilin kuka. Yace To kawo shi sai ki fadamin naki ga mai share miki hawaye Allah ya dawo da shi lafiya.faɗa min dalilin domin shi na san nashi, munyi waya da Nurse ta fada min cewa zai yi kuka kuma kar ayi masa wankan yamma, saboda allurar nan, na yi ta kiran ki in fada miki baki daga ba. Ta kalli wayar dake gefe sanna tace banga kiran ba. Yace ki dai duba kafin ki musa, kawo shi. Ta sake kallon shi cikin ido, ka yi wanka tukunna. Ya matso ya karbe shi ba tare da jira ta miko shi ba. 'Ki huta kema ai kin sha aikin jijjiga ga shi da alamu yau gidan bai samu gyara ba,komai yana nan yadda na barshi. Dole fa sai an sama miki mai aiki gaskiya zata taimaka miki mussaman irin wannan lokacin kina fama da yaro, ko ba yaro gidan nan Baby ya yi miki girma da aikin gyaranshi kullum. To ka dawo da su Fatin mana tunda dama na ga bakaji dadin tafiyar su ba. Ta fada cikin gatse. Sai lokacin ya fuskanci abinda take nufi. Allah ya baki hakuri, ni shawara nake badawa Gida dai na ki ne Baby ki yi yadda ki ke so dashi su Fati tunda kika sallme su na kara magana? Kuɗin su ma sai daga baya na ba su.. Su Fati kuma ai sun zama tarihi a gidan nan. Ya nufi daki, turus yayi yana kallon ko ina ba a gyara ba. Ya fito ya same ta zaune ta dora sabon kuka,ya tsaya cike da mamaki da fargaba yana cewa wai me aka yi ne,ki fada min mana? Ta yi masa banza ga yaro na kuka, ya koma ciki ya kira Nurse ya tambaye ta ko akwai wani abu da aka gani na rashin lafiya game da yaron tace babu, ya fada mata yaron ya yini kuka jikinshi ya dauki zafi. Tace "An kuwa bashi maganin da aka bata na zazzabi? Yace bari ya tambaya, ya fada mata yanzu ya dawo ya samu Uwar da dan suna ta kuka. Tace akan samu haka a haihuwar fari, sukan taya yaran kuka in sun rasa yadda za su rerrashe su. A bashi magani. Ya dawo ya same ta ya zauna kusa da ita, kiyi shiru shike nan ina maganin na shi kin kuwa bashi? Kai ta girgiza alamun a a. Ya bashi maganin ya yi ta jijjiga ta zuba tagumi tana kallon su, gaskiya Halifa namiji ne da kowace mace zata so shi. Ta darsa hakan a ranta. har ya yi bacci. Ya je ya shimfide shi ya yi masa addu'a ya dawo ya zauna ya rungumo ta, Babyna sannu da kokari kiyi hakuri haka iyayen mu suka yi ta fama har muka zama mutane, kwana kadan kema zaki saba da komai, ai kina kokari Allah ya saka miki da Aljana. Asiya ta sauke ajiyar zuciya. To yanzu me ya kamata ta ce masa? Ta dube shi. Kana son ka kara aure ne? Ta jeho masa tambayar. Ya kalle ta. "Me kuma ya kawo wannan tunanin Baby?" Kawai amsa zaka bani. Ta katse shi. "A a " Ya amsa a takaice. Wata ce muka hadu a Asibiti na ganta a tashin hankali sai na tambaye ta ko lafiya, shine ta ke fada min ta ga mijinta a Hotel da wata. Ya dubi Asiya da sauri, "To ita me taje yi Hotel ita ma gurin wani taje kenan? " Asiya Tace ita ta ce min zargi ta yi sai ta ke bibiyar shi. Halifa yace Ta kuwa sa kanta a wahala, Ai be kamata ta yi haka ba ita ma Addu'a zata yi masa kawai. Asiya ta zuba mishi ido, ya kalle ta, ko a kwai wanda ke shiryawa banda Allah? Tace Babu amma shi ba zai ji kunyar Allah ba, sai yaje yana bin mata kuma bata kasa biya mishi bukatar shi ba. Ya dan yi tsam, kamar tana jefa mishi magnar ne. Amma sai yace Allah ya kyauta ta shi ki gyara mana gurin kwanciya. Ya wuce ciki. Yana bandaki ta shigo. Ta zuba ma wayar shi ido. Ta dauka tana juya ta dan bata san Sabuwar lambar sirrin sa ba. Sako ya shigo ta sama a whatsapp hotuna ne suka shigo amma ta kasa shiga domin shima whatsapp din a kulle yake. Bata ji fitowar shiba sai dai taji yace Me ki ke nema kuma a wayata? Ta dan firgita ta mika mishi tana fadin sako naji ya shigo kuma sai na yi mamakin ka saka sabon Security a wayar. Ya fizgi wayar, saboda irin ku ne ake saka Security a waya, na taba daukar wayar ki na duba? Me ki ke son ki gani? Ko nima bincike ne zaki fara min. Lallai zamu samu matsala in har zaki taba min waya.Ya bata rai sosai kar ki sake ko da wasa ki sake daukar min waya da sunan bincike baki da wannan hurumin na faɗa miki, na kula kwanakin nan fitina kawai ki ke so bana son in nuna miki rashin hakuri na, kar kuma ki bari ki kai ni bango. Ya yi tsammanin ta bashi hakuri,kawai sai yaga ta bata rai ta shiga gyaran gado. Tsaki ya ja ya dauki filo ya fice. Asiya ta yi shiru tana mamaki, a yi maka laifi kuma a fika fada, daga ganin yadda ya haukace an taba masa waya wallahi bashi da gaskiya ko kadan.Ta fada a fili. *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [12/17/2025, 19:26] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302* Da safe Halifa bai bi ta kan Asiya ba, ya shiga ya yi wanka ya shirya hatta ɗan sa bai kula ba, ya fice abinsa. Hakan ya daga mata hankali kodai sai ta fito masa a mutum ne ta nuna masa tasan me yake aikatawa a fili sannan zai haɗa hankalin sa, kila jikin sa zai yi sanyi ya shiga faɗin ta yi hakuri. Laifin nan ya bayyana karara koda yake wani nuna mata yaji haushin abinda Anty ta fada duk munafirci ne. Abin duniya ya ishi Asiya dole ta nemo hujjar da zata nuna masa tasan me yake yi. Karshe ta yanke shawarar kiran Fati akwai bukatar ta yi magana da ita. Tana ringing Fati ta daga,, Asiya tace Kingane mai magana ? Fati tace .Na gane ki, Asiya ce me miji,. Asiya kanta ya daure, tace bangane Asiya me miji ba Maman Umar ce fa daga Gandun Sarki. Fati tace ke dai nake nufi nima. Asiya tace To ai naji kin kirani da wani suna ne wai Asiya me miji. Fati tace ina dai jinki faɗi abinda ya sa kika kira ni. Asiya ta rasa me zata ce tunda Fati ta Faɗi wannan sunan. Kiyi magana ko in kashe tunda yanzu dai ba a gidanki nake ba bare ki yimin iko.Asiya tace Shikenan na fasa maganar da zan yi miki sai anjima. Fati tace mu jima da yawa, mijine dai kuma nima yanzu sai dai in banso auren shi ba, amma ya zo hannu. Gaban Asiya ya faɗi tace saidai ki nemi naki mijin amma ba nawa ba me zai yi da ke? Fati ta cafke da faɗin duk abinda ya yi da ke shi zai yi da ni.Koda kika kore mu ya zo har gida kuma yana ci gaba da zuwa in kina son ki sheda zance na,ki zo anjima ki ganewa idon ki,in baki bari mun shigo ba, mu zamu zame miki kishiyoyin waje. Asiya tace Allah ya kiyaye ni mijina ba dan iska bane, babu abinda zai yi dake. Fati ta sa dariya, sai dai kar a kuma ke ma din ai ya fada min ki gudo ne kin dawo gidansa bayan Mahaifiyar ki tana zargin cewa ya sake ki, dan haka kika haihu ba dangin iya bare na Baba munzo mu taimaka miki kuma shine harda cewa mu shirya kin sallame mu, ke ga matar gida. To mun ƙaru ba shakka amma kin bar baya da kura ko ince kin kashe maciji baki sare kan ba.. Git Asiya ta kashe wayarta. Ta zauna cike da bakin cikin abinda Fati ta fada mata, wato dai ta tabbata Halifa yana nema Fati hakan bai isheshi ba har sai ya hada da tona mata asiri. Duk zantukan Fati ba karya a ina zata ji in bai faɗa mata ba.Wata zuciyar tace ki tafi gidan ku kawai ki bar masa gidan sa. Asiya ta shiga hada kayanta da na ɗanta. Babu shakka ta hakura da Halifa in ba haka ba zuciyar ta zata buga. Ta gama komai bata da kudin mota, ko a kafa gara ki tafi. Wata zuciyar ta faɗa mata. Tana kaiwa bakin gate Motar Halifa tana isowa kofar gidan da alamun mantuwa ya yi ya dawo dauka. Cike da mamaki yake kallon Asiya da akwati tana ja. Ta kalle shi rai bace,zantukan Fati suka yi ta zuwa mata. Baice kala ba,ya wuce cikin gidan ta miƙi layin tana tafiya. Ya dakko abinda ya manta ya dawo ya wuceta ya tafi. Asiya cike da mamaki tace kenan ko kallo bata ishe shi ba, bare yace mata ina zata a zaton ta zai tsaya ya yi mata magana daga fara neman matanshi har daraja da kimarta ta zube a idon shi haka?. Ta tsaya tana tunanin inda zata samu kudin mota domin tasan karya ne taje Fage da kafarta ga goyo ga kaya. Ta karasa gurin wani mai P.O.S dake kan titi tace dan Allah in baka wayata ka bani dubu daya zan kawo maka sai in karba jakar kudin nawa na yarda. Ta sheka masa karya. Wani dake kirga kudi a gefe ya ciro dubu daya ya bata yace je da wayar ki ga wannan saboda Allah. Asiya ta karba ta yi godiya ta kama hanya tana tare mai Adaidaita. Ta fi minti Talatin kafin ta samu wani da mata biyu a ciki zashi Kurna tace ya sauke ta Kano Gest in. Tun kafin ta shiga taji matar ciki tana yiwa diyarta faɗa. Tana faɗin na fada miki tun ba yau ba ki kauda kai daga abinda Baban su baby yake yi ki yi masa addu'a kika taurare ke bazaki zauna ba yana neman mata, kika dawo gida kika bar masa gidan to gashi in da yana dibansu zuwa Hotel ne yanzu kam kin hutar da shi, tunda makota sun fada miki yana kawo mata gidan aurenki ai gashi zaki koma babu shiri. Inda kina gidan karyarshi ya kawo mace gidan. An fada miki shifa namiji in yana boye miki abu ko kin gane karki nuna kimarki ta sa hakan to gashi dai tun yana zuwa lallashi kinƙi ki koma gashi yanzu zaki koma bayan ya watsar da ke. Asiya taji kamar wani karatu ake yi mata, kenan shima Halifa zai iya kawo su gidan hankalin sa kwance motarsa da gilashi baƙi ya wuce da mace ya fito da ita ba tare da an sani ba. Kuma babu tabbacin zai biyota ko ya gyara kuskuren sa,tunda gashi a gabanta ya wuce ko ajikin shi,ran nan da tace zata tafi ai lallashinta ya yi da ban baki, amma yau dubi yadda ya watsar da ita. Ba shakka ance in ka rasa uwar da zata yi maka fada,to ka saurari faɗan da wata uwar zata yi wa ɗanta sai ka dauka kai ya yi maka amfani. Wadda ake yi wa faɗan tace "Ni wallahi dan Baba ya ki ne, da kawai takarda ta ya bani yanzu gashi duk makota sunsan abinda ya aikata.Uwar tace ki fada min waye ya ja? Kece nan tun farko me ya kaiki bincike da saka masa ido. Allah ya hana bin diddigi.Kika kwafe ki duba masa waya ki bibiye shi har sai da kika ga no tashin hankali tun lokacin har zuwa yau wace ribar kika ci? Bayan da kuna zaune lafiya abin shi awa. Me a daidaita ya karbe zancen da faɗin Babata in saka muku baki? " Ya ci gaba kanwata baki san me yake faruwa ba a wannan zamanin mu da muke jan Adaidaita mun san komai, mata ne suke neman maza yanzu, in har kika yi sakwasakwa da mijinki wata ce kawai zata samu ta yi ta masa abinda ke bazaki iya yi masa ba,wasu fa harda kuɗi suke kashewa maza,wasu malamai suke shiga. Shaiɗan fa da kika gani babu abunda yake so irin ya girgide auren sunna,dan haka ki koma gidan ki ki rike mijinki kici gaba da addu'a. Ki fita batun yan unguwa su aka san me mazan su ke aikatawa sanin na Allah ai sai Allah ko malami karyar sa yace miki ga na Allah Sam Asiya bata san anzo Kano Gest ba sai da mai Adaidaita ya dakata yace munzo Ta sauka ta bashi dari biyar ta tsallaka ta kuma tare wata ta hau zuwa gandun Sarki. Domin dai ta wadatu da faɗan da aka yiwa yarinyar nan. Ta dawo ta bude gidanta ta shiga. Ta kwantar da ɗanta a kujera sannan ta koma gefe ta zabga tagumi dole ta sake kiran Anty Halima da alamu dai shawarar nan ta ta itace mafita. Take ta kira bayan sun gaisa ta zayyana mata dukkan abinda ya faru a tsakanin su. Dariya ta ji Anty Halima tana yi.Haushi ya kamata kamar ta kashe amma saita share ta ci gaba da fadin Anty abin dariya aka yi? E mana abin dariya ne, ace wai kin tafi kuma kin dawo.Na faɗa miki fa,duk abinda zai yi karki nuna kin gane,baki ga abinda Baby ta cikin Hamshakiyar uwa ta yi ba? Ki karanta littafin zaki samu Illimin zama da miji me neman mata, naki mijin sabon shiga ne,kuma ke kike kara rura wutar dan haka ki nutsu in ya dawo ki bashi hakuri karma ki nuna kinyi waya da wannan yarinyar karki masa zanceta sam sam. Ki daure kishi da zafi musamman da matar waje amma Allah yana saurin amsar addu'ar wanda ke cikin damuwa. Asiya ta yi wanka ta gyara jikinta sosai ta yi kwalliya tsaf. Zan tukan Fati suna ɓata mata rai in ta tuna. Saidai kuma Halifa bai dawo ba sai sha biyu saura. Ran Asiya ya sosu amma ta dake ta zauna a falo. Ya sa makulli ya bude kofar falon dan bai zaci tana nan ba. Ya shigo yana waya abinda taji kawai shine, dadin baki kawai ki ke yi min, domin yaushe rabon da ki nemeni amma ni yau gashi na kiraki da..... Maganar ta tsaya cak ganin Asiya ta zuba masa ido. Cikin yanayi irin na mara gaskiya yace zan kira ki da safe, barista zan kira. Bai jira me zata faɗa ba, ya kashe wayar. Asiya ta daure ta kalle shi sannu da zuwa. Ya dube ta da in ina ya ce yaw wa, ya sa kai ciki, ta bishi yana cire kayan jikin shi ta iso dab dashi,in ka yi wanka akwai abinci. Ta fada tana kokarin ƙaƙaro fara a. "A koshe na ke, ya karkace wai dan kar ya taɓa jikinta ya nufi banɗaki. Asiya ta rumtse idon ta zuciyar ta ta soma tuna mata da maganarsu da Fati, ina ma ace ta yi recoding din ta yana fitowa ta kunna masa ya san ta san komai. Zuciyar ta tace ki hakura kawai. Wata zuciyar tace, kar ki hakura ki faɗa masa komai da zaran ya fito ki kunyata shi. Tana zaune bakin gado. Ya fito yana shafa turare ya yi wanka.Yana mata kwarjini ne amma ta daure tace Yaya ina son magana da kai. 'Bisimillahi " Ya faɗa lokacin da ya dauki filo zai fita kenan. Yaya dan Allah ban hana ka soyayya da kowa ba amma dan Allah kar ka kara faɗawa wata sirrina. Ga mamakin ta sai taji yace 'To' ya sa kai zai fita. Tace Yaya amma me yasa ka rasa wadda zaka nema sai Fati me mana aiki? Har ya kama kofa zai murda sai ya tsaya cak bai waiwayo ba, ganin ta fara kama shi sai ta ci gaba da faɗin kuma neman na na lalacewa har kai ne zaka dauki mace Yaya zuwa Hotel dan ka..... *✍🏻 HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [1/12, 17:34] Ummi Tandama😇: *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302* Saukar mari da Asiya ta ji shine ya katse mata maganar ta,ta kalle shi sai tsuma yake "me yasa ne ki ke son in yi losing ɗin temper?" Kafin ta fahimci abin da yake faɗa ya kuma kifa mata wani marin ya jefa ta kan kujera,a tsorace ta ɗago hancinta yana zubar da jini, kamar dai ya haukace, ya kuma nifo ta, ta ruga ɗakin da ke kusa da ita ta faɗa ta rufo ƙofa jikinta yana ta ɓari tana jiyo shi gaba ɗaya ya haukace yana ta fashe-fashe yana cewa ki fito ki faɗamin ko saki nawa kike buƙata?. Ya faɗa ɗakin su ya ɗakko takarda da biro "ki faɗi adadin sakin da ki ke so in yi miki yanzun nan na fara jin cewa na tsane ki. In har tsanar ki ta yiwa zuciya ta tasiri ko a hanya ba zan so ganin ki ba Asiya. Ta leƙo ta window tana kallon shi. Baki da wani tunani sai na zargina mata mata dai in neme su mana ba kuɗina bane ko kabarin mu ɗaya? Kina da wuta ne ko kina da aljanna? Haba kin hanani zaman lafiya, me ma ya hana ki tafiya gidan naku ɗazun da kika fita? Ki fito ki tafi da hujjarki a hannu in huta nima. Asiya ta firgita ta manta da dukan da ya yi mata ta isa bakin ƙofa ta buɗe a gigice ta zo gaban shi ta fisge takardar. "Yaya bana son ka sake ni don Allah" ta faɗa jikinshi ta rungume shi kam tana kuka tana faɗin "wallahi na daina zargin ka sherrin shaiɗan ne Yaya na tuba ka yi haƙuri. Jikinshi sai rawa yake kamar wanda ake kaɗawa gangi.... kamar minti uku ya ya kice ta ya jefar ita da biron ya fice daga falon ya shiga ɗaki ya fito ya fice Asiya tana kuka ta ji tashin motar sa ya fice daga gidan. Ta nufi banɗaki ta wanke jinin, zuciyar ta ta rasa wane irin tunani zata yi,borin kunya yasa ya dake ta ko kuwa zafin ƙazafin da tayi masa ne? Borin kunya ne zuciyar ta ta faɗa mata,ki zauna tunda ya fara dukanki ki zama jaka, yanzu ma ya fice zai je ya samu wadda ya kira ɗazu su ƙwana tare, gara fa kin koma gaban uwarki ki haƙura da talaucin ku yafi dukiya babu ƙwanciyar hankali. In ba haka ba wataran sai ya kashe ki kuma babu abin da za ayi. Da sauri ta tashi fuska kumbure ta kuma janyo aƙwati ta loda kaya lokacin karfe ɗaya ta wuce na dare,bazata ƙara ƙwana a wannan gidan ba tafa a fili. Tana kici kicin fito da aƙwati ta ji shigowar motar shi tace ai ko motar shi bazan hau ba gara in kwana a hanya cak ta tsaya a farfajiyar gidan tana kallon su sun nufo ta Inna da Sulaiman. Asiya!! Inna ta furta da ƙarfi, Asiya ta saki akwati ta ruga ta rungume Inna ta ma manta wai tana da goyo sai kuka ita da Inna. Sun ɗauki mintuna Halifa ya ce ya isa Inna ku shigo. Asiya ta ce Inna mu tafi kawai ni bazan kuma shiga gidan nan ba, tunda na ganki ƙafar ki ƙafata. Inna ta ce ina zaki da tsohon daren nan,bani ɗan naki in ganshi. Asiya tace gurin ki zan je, kullum sai na yi yunƙurin tafiya. Halifa ya kalle ta fuska a ɗaure ya kau da kai. Inna tace "me kuma ya samu fuskar ki haka?" Asiya tace faɗuwa na yi a banɗaki. Halifa ya yi karaf yace "marinta na yi Inna." Ina ganin kawai ku tafi tare da ita zata fi samun nutsuwar zuciyarta. Sulaiman zai yi magana Halifa ya ɗaga masa hannu tare da miƙa masa makullin mota. Kuna iya tafiya za mu yi waya kawai. Asiya ta yi gaba Inna ta bita a baya dan Sulaiman ya ɗauki akwatin,sai da suka fice a gidan Halifa ya dawo ya shige ɗaki *** **** *** Bros ya kalli Maman Nihal "ki daina wata faɗuwar gaba ita fa Anty yanzu tayi nadama,dan Allah kar ki nuna komai game da abinda ya faru a baya." Amarya dake riƙe da jaririn Maman Nihal mai sunan Dady tace Anty dan Allah ki daina wata fargaba. Suka shiga su ukun domin ɗakko Nihal da Nur. Anty tana zaune a falo tana kallon T.V sai dai sam hankalin ta baya kan abin da ake yi tana can cikin tunanikanta mafarkan ta da har yanzu babu wanda ya zama gaskiya,sai zuwa yaushe zata samu nasara? komai ta shirya sai ya lalace. Bata ji sallamar su ba sai da Bros ya ce Anty! Da ƙarfi sannan ta firgigit ta ɗauki sakwanni sannan ta fahimci su waye a gabanta. Ta ɗaure fuska tare da kau da kai. Maman Nihal ta durƙusa ina yini Anty? Bata amsa ba amarya ta je ta ɗora mata yaron a cinya ga mijin ki nan. Ta yi kamar zata ture shi da taga zai faɗi kuma babu wanda ya yinƙuro dan kamashi sai ta yi saurin riƙe shi. Bros ya yi murmushi ya yin da amarya ta saki dariya tare da faɗin ashe dai ana so. Anty ta dubi amarya "ke bana son rashin kunya zanyi maganin ki wallahi in zaki kawo min raini,bana wasa da yara." Allah ya baki haƙuri ta faɗa tana dariya "bari in nemo su Nihal" amarya ta faɗa tare da nufar ciki. Anty ta kalli Maman Nihal ta taɓe baki, Maman Nihal ta sunkuyar da kai cike da tausayin Anty,duk ta yi baƙi ta rame. Anty ta katse mata tunani da faɗin "wannan yarinyar makira ce,naga take taken ta sai kinyi da gaske. Cike da mamaki Maman Nihal tace "to Anty zan kula." Bros yace amma kuma ni banga wani aibunta ba,tana girmama mu. Anty tace "in kai baka gane abin da nike nufi ba ita matarka ta gane" ta kalli ɗan dake cinyar ta tace "sai ya tuna min kai kana yaro sak haka kake." Cike da jin daɗi suka yi yar dariya. Maman Nihal tace Anty shima bai yi rigima ba ke nan dan shi wannan bashi da rigima sai kirin kirin ba zai nutsu guri guda ba. Haka dai uban yake. Amarya ta dawo da su Nihal cike da murna suka faɗa jikin uwar su abin tausayi Nihal tace Momy Baba ya faɗa mana kin haifa mana Baby boy shine wannan a gurin Anty? Ungo kayanku Anty ta faɗa tana miƙa ma Nihal shi. Nur kuwa ta kasa sauka daga jikin Mamansu domin ita dai baza ta sake yarda ta tafi ta barta ba. Amarya ta ce Anty naga Hafsa tana kuka kuma bata faɗa min abinda ke damunta ba. Duk suka kalli Anty. Ta dubi Bros ita da Dadynku ne,ya ce ya saka mata ranar aure sati shidda bata san waye mijin ba." Maman Nihal tace Allah sarki amma ai da Dady ya bata dama ta fito da wanda take so tukunna. Bros ya ce "ya fa bata,ai munyi maganar da shi,banga laifin sa ba amma bari inga Hafsar shegiya sai dai ka shiga lamarin ta amma ba domin halinta ba." Ya nufi ɗakin. Ganin shigowar shi yasa Hafsi da ke ƙwance tashi zaune,Bros yace "kinga sakamakon mugun hali tun yanzu ko? Hafsi tace don Allah ka bawa Dady haƙuri wallahi ba zan sake shiga harkar matarsa ba. Bros yace "mafita ɗaya ce ina shi wannan saurayin naki bani number ɗin shi inyi magana dashi, amma Dady wannan ranar da ya saka miki ta aure bazai taɓa ɗage ta ba." Cikin sauri ta tashi ta ɗakko waya ta fito da number ta miƙa wa Bros tana cewa nayi nayi dashi ya zo Anty tana kiranshi yaƙi zuwa yanzu ma baya ɗaga kirana. Bros yace zanga ya zanyi da shi. Ya koma wajen su Anty suka ƙwashe ƴaƴansu,Bros ya kawo kuɗi ya ba Anty suka tafi. Anty har labulen window ta ɗaga tana leƙensu wai ashe aƙwai ranar da zata zo tana ganin Maman Nihal su jera da ɗanta a gabanta kuma har ta furta ku gaida gida. Batasan hujjar da zata bayar a matsayin dalilin hawayenta ba, abinda kawai ta sani shine bata yi nasara akan ta ba. Akan wa kika yi nasara ma? Zuciyar ta ta tambaye ta. A fili tace akan Asiya matar Halifa na kashe kuɗi na wahala nayi asarori, amma ban faɗi ba, na yi nasara tunda Yanzun ta Haukace ta shiga Duniya ba shakka wannan nasara ce. *✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [1/31, 12:32] Ummi Tandama😇: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302* Inna ranta ya kasa kwanciya da kalmar da Halifa ya furta a gabanta cewar ya mari Asiya. Dan haka Inna tace to ke me kika yi masa har ya yi miki wannan mari haka? Nifa bana son aure da dole wallahi sai na samu kaina a sabon tashin hankalin da naji kamar ina ma banganki ba? Sulaiman ya yi gyaran murya sannan yace Inna kar ki yi saurin yanke hukunci ki jira muje gida sannan da zai yiwu karki saurari me Asiya zata fada gobe zanzo da motar sa in dauke shi muje gata gashi a yi musu ba cuta ba cutarwa. Inna tace shike nan a yi hakan abin babu dadi Sam. Wa ya sani ko akan tace sai ta zo gurina ne? Inna ta fada ta na Kallon Asiya wadda take tunani anya zata iya tona asirin Uban ɗanta kuwa? Inna ki bari mu nutsu Zan fada miki komai. Asiya ta furta cike da son a bar maganar. Ta ci gaba da fa ɗin Ina Abba da Su Annur Maman Annur tana zuwa gidan aikin ta kuwa? Inna tace Tana zuwa kullum dai ita ma tana cikin damuwa da kewa amma ta kusa daina aikin ma. Abba kuma jiya muka dawo daga Asibiti. ‘Bashi da lafiya ne? Sadiya ta katse Inna. Sulaiman ya yi karaf ya ce ai ya samu sauki ma. Asiya ta yi shiru tana tunanin kamar akwai wata matsala game da Abba.Har suka isa gida. Sulaiman ya kira Inna gefe yace kar ki yi mata zancan Abba tun da dai shi bai fada mata ba. Kinsan dai tana da ruɗewa Inna tace shike nan. Ya kira Asiya itama yace, kar ki fada wa Inna matsalar mijinki kin san dai har yanzu ba a warware wata matsalar ba sannan ban da haka kuma Inna tana da wuyar fahimta . Asiya tace shike nan. Ga mamakin Asiya sai ta ga sun zo wani gida wanda ba gidan su ba, dan madaidaici mai kyau ba ginin kasa ba kamar na su. Ta cika da mamaki tana kallon Inna, “Nan kuka dawo Inna?” Tace Nan muka dawo bamu jima ba.Sadiya taji tsaiwar mota ta bude gidan ta fito da gudu tana fadin Asiya ! Asiya tace Maman Annur Suka rungume Juna Sadiya tana murna ta amshi jariri tana kallo ranar har ukun dare suna hira kafin kowa ya kwanta. Inna ta sauka a ɗan gadon ta tace ki kwanta ke da ɗan na ki. Asiya tace a a Inna shima ya kwanta a ƙasan dan ya saba. Inna ta amshe shi tana fadin kawo shi mu kwanta in ya farka kya tashi ki bashi ya sha. Asiya cike da farin ciki ta kwanta iyaye daban ne ta ayyana a zuciyarta. Sai dai fa kogin tunani ta fada maimakon bacci rayuwa baza ta yiwu mata ba babu Halifa ba haka kuma akan kunnen ta aka kira salla dan haka ta tashi ta fita ta tayo alwala tabi gidan da kallo ko ya akayi su Inna suka dawo nan gidan Mai kyau ga tayas ko ina ga ruwa daki uku ne da Siti rum da safe dai taji yadda aka samu gidan. Ta zo tana nafila, motsinta ya tada Inna ta ce baki tashe ni ba na makara koda yake bamu kwanta da wuri ba Asiya tace shiyasa na barki amma ba'a shiga salla ba har zakiyi raka atanil fijir. Inna ta fita tana fadin Asiya dan naki bashi da rigima. Tana idar da salla bacci mai nauyi ya dauke ta Kuka ɗanta ya tashe ta, taga Inna ta rufo kofa tana mishi wanka. Ta bisu da kallo cikin farin ciki tace “Inna a ina kuka samo robar wanka? Inna tace a makota na aika aka karbo min. Asiya ta gaida Inna ta tashi ta nufi tsakar gida ta wanke baki Sadiya tana hada abin kari kunu da dumamen shinkafa. Asiya tace maman Annur sai ga ku a sabon gida, wai ya akayi ne? Sadiya tace Hummm wallahi kuwa tun daga abin Abba Halifa ya dawo da mu nan ko bai fada miki ba? Asiya cike da rashin fahimta tace ban gane ba. Inna ta kwaɗawa Asiya kira ta amshi ɗanta yana ta ragsa kuka. Inna tana faɗin zauna ki bashi ai yana da hakuri tun jiya bai farka ba. Ta zauna tana bashi, tace ai bai cika tashin dare ba, . Inna tace. Wai kuwa me ya hada ku da Mijin naki har ya mare ki? Lamarin fa ya tsaya min a rai. Bana son auren duka. Asiya ta yi shiru tana tunani ta ina zata dakko maganar. Inna tace “Ban tsanan ta sai kin fada min ba amma aure da duka Asiya ba zai yiwu ba dan haka shi yasa tun jiyan bance komai ba da yace mu taho. Sallamar Sadiya ce ta dakatar da Inna , ta kawo musu abin kari, Abba ya shigo yana gaida su Asiya ta bishi da kallo ya dashe ya rame cike da mamaki Asiya tace Inna “Me ya samu Abba haka?” Sadiya cike da mamaki tace wai baki sani ba? Asiya tace “Maman Annur in har na sani bazan tambaye ki ba. Inna tace Wai kina mufin shi Halifa bai sanar da ke komai ba? Sallamar Sulaiman ce ta katse su.Ya shigo Halifa yana bayan sa. Sadiya ta yi musu shinfida suka zauna Halifa ya gaida Inna ko inda Asiya take bai kalla ba bare ɗanta. Ya amsa gaisuwar Sadiya. Sadiya ta miko musu ɗan sai Sulaiman ne ya amshe shi Halifa dai a fusace yake har Wannan lokacin Asiya ta dake domin zuciyar ta ta fada mata cewa ta dake kawai Yanzu lokaci ne na kwatar yanci kodai ya tuba nan gaban Inna akan bazai ƙara ba, kokuma ta haƙura da shi domin sai ta fallasa shi. Halifa ya katse ma Asiya tunani da faɗin Inna kamar yadda na fada jiya na mari Asiya har ture ta na yi domin har sai da ta yi habo wannan tabbas na aikata shi. To amma ko zata iya fada miki abinda ya jawo hakan? Asiya ta kalle shi cike da mamaki wannan yana nufin baima damu ba da abinda ya aikata. Yanzu har ya kai ba zai iya boye zunubin shi ba.Ya katse mata tunani bance ki rufamin asiri ba fa, nan gurin babu bakon ki mahaifiyar ki ce da yar ki, Sulaiman ma kamar wane a gareki dan haka karma ki tsaya boye komai. Kawai ki tona shi zuciyar ta ta faɗa mata haka. Asiya ta kalli Inna wadda yanayinta ya canza tunda Halifa ya ambaci cewa ya dake ta. Ko mutuwa ance tana jin kunyar idon mahaifi amma Halifa kamar yana gadara da ya dake ta. Tace ‘Inna ki yi hakuri ki yafe min har da alhakin ki na gudu na tafi Gurin Halifa ashe ban sani ba ya canza daga Halifan da na sani. Da na haihu ya kawo min wata Dattijuwa mai suna Hajjo ita da jikarta sai jikar ta fara nuna tana son shi, sai kuma wai ya biye mata. Har na kore su shine kuma ya ci gaba da kulata. Ya ma kama fa kulakulen mata shine har dayan dare sha biyu ba zai dawo gida ba gashi bani da sirri gurin matan Duk ya fada musu wai na gudo ne na dawo gurin sa. Ta kai karshen maganar da fashewa da kuka. Cikin kuka taci gaba da fadin wai dan na masa maganar ya daina jiya shine ya dake ni wai kuma zai sake ni. Idanun Halifa suka kada suka yi ja ya kalli Inna bazai iya fassara me take tunani ba. Dakin ya yi tsit sai kuka Asiya. “In kare kai na ko kawai Inna ta yanke hukunci? Halifa ya tambaya cike da bacin rai. Sadiya ta yi saurin fadin Ka kare kanka shine adalci Sulaiman yace Ka yi maganar ka aboki na. Halifa yace “Lokacin da na fahimci cewa Sulaiman ya gama yi min kokari Inna ta gane gaskiya ba ni ne na saki yarinyar nan ba, sai na fara kokarin yadda zan kawo ainihin wadda ta yi laifin ta fada a gaban Inna da kanta kuma in yi musu ba zata daga Antyn nawa har Inna wato in kawo musu Asiya da ɗanta su san tana cikin koshin lafiya. Katsam sai wani tashin hankalin ya samu Anty an mata kishiya a boye,dan haka na jinkirta, nan ita kuma wannan yarinyar naga ta soma damuwa da harkar masu mata aiki tana bay yana kishinta har da korar su. Duk ban damu ba har gida naje na basu hakuri na kuma biya su hakkin su,gata nan ko faɗa ban mata ba tunda nasan ina da fushi Sosai. Ranar da da na lura ta soma bata rai game da gida ta damu da son ganin ku sai na yanke shawarar in zo in sanar da Inna Asiya tana gurina kuma in tafi da su Innar can gurinta. Sai da na fara duba Sulaiman a shago baya nan sannan na nufo gidan ni daya, tun daga nesa na hango mutane cike a layin sai na yi tunani in juya domin gaskiya bana zuwa inda duk ake fada. Muryar Sulaiman na jiyo yana cewa ba zai yiwu a bashi hakuri ba, dan yana ganin ba su da wanda zai tsaya musu. Kawai sai na koma ashe rigimar a gidan su Inna ce. Naje na dafa Sulaiman ina tambayar shi, abinda ke faruwa sai na ji Yayi hamdala yana fadin ga me tsaya musu ya zo. Na tambaye shi abinda ke faruwa sai ya nuna wani mutum yana tsaye sanye da jallabiyya fara yace “Ga wanda ya dake su kuma wai kar su yi kuka, ya samu yara ya lalata su kuma Abba da ya tona asiri bayan ya haike masa shine ya zo yana fuffka zai kai kara. Na kalle shi cike da mamaki ban gane ya haike musu ba su da ba mata ba. Halifa yace mazan fa kuma yara kanana kowa ya sani a layin nan an kasa yi masa magana dan yana da abin hannu. Bansan lokacin da na zabga wa uwar sa zagi ba, nace za a kai yaro Asibiti in ya tabbata wallahi sai kaje gidan yari. Saboda ƙarfin hali wai ya taso zai mare ni, ni kuwa na dinga jibgarsa sai da naga baya motsi sannan na kyale shi. Muna Asibiti aka tabbatar an haike wa Abba Sai da aka yi masa karamar tiyata. Yan sanda suka zo suka same ni a Asibiti suka tafi dani wai ana za ton Mutumin ya mutu ne. Na kira Yaya Bashir Babanmu daya shine mataimakin Kwamishina na faɗa mishi halin da ake ciki take ya kira DPO yace ni kanin sane ya na son case din ya koma hannun sa dan haka akai ni can yanzu. Lokacin karfe tara sun ta shi aiki tuni amma ba su tafi ba. Muna zuwa ya fara min faɗa bana neman shi kaza kaza na bashi hakuri domin gaskiya dai ban saba da su ba, amma mukan hadu a gida lokacin duk da za ayi wani shi ani Ina zuwa, da Ina karami ne Anty bata cika kai ni ba. Amma dana girma Dady ne yake fada min in bi yan uwana mu yi zumunci. Sai sha biyu suka fito ya sauke ni a gida yace da sassafe in same sh office nace to. Shine ranar da na kai sha buyun da take magana sai wani irin kallo take yi min dana dawo na shiga wanka dan ina ta jin kyan kyamin jikina tunda an sakani a sell Gurin ƴan sanda kafin muje Bamfai. Ga gajiya na ki fada mata ne dan bana son ta tada hankalinta Babu abin da ke daga min hankali sama da in ga Asiya a damuwa. Dan ina ganin yanzu ita ce komai nawa kuma na fada mata hakan gata nan Tana jina. Abinda ya bani mamaki muna dawo wa daga Bomfai Washe garin ranar ni da lauyana wai kawai sai na ganta a dan sahu bayan Asibiti tace min zata je kuma ba hanyar bane. Har mun wuce sai na juya nace masa kamar naga wani da nake son haduwa da shi a Keke Napep Na yi haka ne kawai dan ta ga mota ta. Cikin sa a ta ganni ta sa mai keke ya bini. Na sauke lauya na a kasuwa ya dauki motar sa dama nan ya barta muka hau tawa. Ina zaune a motar ina mamaki kenan yarinyar nan bibiyata take yi tana zargina. To halin da nake ciki bana bukatar wani tashin hankali a gida domin mutumin da na buga har lokacin baya gane kowa duk da ya farka. Sannan nima na shigar da ƙara akan abinda ya yi wa yaran nan bani da ishshen lokacin da zan zauna ko abinci in ci, kasuwa ma bana samun zama sam daga gurin yansanda zuwa Asibiti kuma ni na bada jini da aka yi wa Abba aiki amma matar nan tana ta zargina har da cewa ina tona asirinta a gurin matan da nake nema . Ta tashi dan hauka ta tafi gidan su Fati me aikin ta dan wulakanta kai da zubar da aji . Hajjo ta kira ni ta faɗa min har lambar da ta sa aka turo mata duk babu abinda ban sani ba. Na shanye to wai kuma jiya na shigo gida Ina waya zan kira Barista ka wai kiran ya tafi ashe wayar Bilkisu na kira yarinyar da zan aura a da, gudun kar ya zama kamar na wulaƙanta ta sai na tsaya muna gaisawa sannan na shigo gida da kwarin ta kai tsaye tunda nasan bata nan kuma Ina da kwarin gwiwar cewa yanzu suna tare da Inna taji komai dan haka na shigo Ina wayata kai tsaye, ganinta zaune yasa naji na dan kadu domin dama ga halin da nake ciki game da ita kuma gashi taji ina waya. Yadda na tsargu shine ya bata damar fada min magana wai ina kai mata Hotel. Raina ya sake ɓaci sakamakon tuna batun cikin fushi yace aure baya yi wuwa da zargi dan haka na fada mata wallahi ta fara dusashewa daga raina ta zabi abinda take so wallahi zan mata in gaba ɗaya take son sakinta zan bata, sai inje in yi sharholiya ta yadda nake so,. Ya mike bayan ya kai ƙarshen bayanin shi, Inna wadda duk jikinta ya yi sanyi tace to aiba tafiya zaka yi ba,, ka tsaya a warware maganar . Sulaiman ya ce Inna kiyi hakuri zamu dawo wallahi dama da kyar na sha kansa ya zo. Shima ya fice. Asiya wadda kunya da bakin ciki suka hana ta dago kai sai da ta tabbata Halifa ya fice. Ta mike tsaye tana fadin Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Inna wallahi nayi kuskure na zargi yaya Halifa cike da jahilci. Inna tace Nan fa shine ya tsaya mana kare wa ma wannan gidan shi ya saya mana yace mu bar unguwar saboda abinda aka yi wa Abba. Ya kawo kayan abinci ya jibge mana hatta Sadiya yace ta daina zuwa aikin nan dan kuɗin makarantar yara zai biya musu dan dai matar da ta ke yi wa aikin taje Umara ne amma da ta dawo zata daina zuwa. Sadiya tace to wai ke Asiya duk wa ya zuga ki kika dinga wannan shirme babu lissafi? Dan gaskiya da ba haka ki ke ba, wallahi gaba ɗaya duk kin sa kunya ta rife ni, na kasa magana. Asiya tace sharrin zuciya ne wallahi sai ta yi ta raya min ni kuma inta hasashe cewa fa ga shi can kuma bugu da kari Fati me aikina da ta fada min cewa yace na gudo ne. Asiya tace aikin banza kila ma jinku ta yi ba kince a gidan sauke yini ba? A kwai wanda ya kai masu aiki gulma da bin diddigin masu gida ne aka fada miki? Gidan aikina gashi nan ina gani a gurin sauran masu aikin har labe suna yi. Asiya tace Ita wannan shegiyar zata iya aikata wa . Inna tace Ni na ma rasa ta inda za bullo wa lamarin shi yana nan yana kare miki mutunci iyaye da kanin ki ya kuma kasa faɗa miki dan kar hakalin ki ya ta shi ke kuma kina can ki nai masa cin zarafi. Asiya tace to wai ni ku fada min ta inada zan fara. Sadiya tace ki kira shi a waya ki ba Inna ta bashi haƙuri ko kuwa? Asiya tace dan yi shiru bari in gwada bashi hakurin ni da kai na mugani. Asiya ta firgita da ganin yadda ta yi masa kira goma sha biyu bai ɗaga ba. Tace lamari fa ya baci ta kira Sulaiman yace ai ko ɗazu kafin na fito har ya tafi kuma nima bai daga kirana ba. Yace Asiya kema baki kyauta ba abin fa da ciwo ya zama iyalinka kuma basu yarda da kai ba. Asiya tace Na yarda Yaya Sulaiman na yi laifi hakuri zan bashi. Yace ki masa Message sai ki jira zuwa gobe ya huce. Bata da zaɓin da ya wuce hakan. Sai dai wasa wasa yau sati daya ba wani ci gaba ta masa sako ya fi dari amma ba amsa kira kuwa da ya gaji ya saka layin a DNA. Har kasuwa Sulaiman ya je yaran shagon suka ce ya yi tafiya. Hakurin Asiya ya kare ga fargaba kar fa Halifa yace zai sake ta. Ta shiga yi wa Inna kuka har ta ba Inna haushi Tace zata saba mata in dai bata nutsu ba wani yace ta yi laifin tunda ta san halinsa. Sadiya dai sai lallashi Su tufka wannan shawara su kwance. Daga karshe ta sake kiran Anty K mashi bata boye mata komai ba. K mashi tace “Abinda ya faru dai ya riga ya faru, yanzu shawara daya ce waye kika sani guda daya wanda ba zai musa maganar sa ba? Asiya tace sai dai Baffan shi, K mashi tace to ki sanar da Inna cewa zaki je gurin Baffa din domin ya bashi hakuri ita rayuwa akwai yanayin da baka tsayawa ga mace musamman miji ya diga miki alama ta cewa kin fara fita ransa har kuma ya maimaita hakan a gaban mahaifiyar ki. To ki aje wani batun wani aji ki sunkuyar da kai . Asiya tace “Yanzu ma kuwa zan tashi in kama hanya . Ta sanar da Inna komai Inna tace Ni da zaki bi tawa ki jira shi ya huce ya kawo kanshi hakan akwai daraja kuwa? Asiya tace “Inna Ni nasan halin kaya na, Yaya da ki ke gani sai ya shafe labarina daga yadda ya bar wadda suka dade suna soyayya ya aure ni ya ishe ni misali. Inna tace To ku tafi tare da Sadiya. Kuma dan Allah kar ki kuma tafiya ba da izini na ba. Asiya tace kar ki damu Inna bazan sake yin wannan kuskuren ba. Asiya da Sadiya suna zaune a gaban Baffa ta sanar da shi ko ita din wacece dan ba zai gane ta ba Baffa ya sha Mamaki wai dama an ganta . Tace ita dama gidansa ta tafi, ta zayyana wa Baffa komai . Baffa ya yi mata faɗa sosai sannan ya dauki waya ya kira Halifa yace Yace duk inda yake ya zo yanzun nan yana neman sa. Halifa bai kawo Asiya cikin dalilin kiran ba, domin ai ba su san anganta ba. Sai dai abin mamaki yana shiga Falon Baffa sai ya ya ga Asiya zaune ita da Sadiya shi kuma yana rungume da jariri yana ta yi musu nasiha. Halifa ya daure fuska yana kallon Asiya. Ta sun kuyar da kai, ya shigo ya zauna ya gaida Baffa . Asiya da Sadiya suka gaida shi, ya ƙi amsawa Yace Baffa ga ni. Jikin Asiya ya yi sanyi amma ta saka aranta duk abinda zai faru sai dai ya faru domin kuwa tunda har ya zo sai ta sha kanshi. Baffa ya Katse mata tunani da faɗin. Matar ka ce ta zo kuma ta min bayani komai, ba tare da an maimaita zance ba ina son ka dauke ta ku tafi gida. Ka yi hakuri. Halifa ya sunkuyar da kai “Baffa Umarni ne ka bani?” Baffa Yace A a shawara ce kawai. Halifa ya mike Tare da faɗin Baffa ka yi hakuri ba zan iya yafe wannan zargin ba, na so in yi hakan na kasa, Baffa ban taba aikata zina ba ko da ina saurayi Allah shine shaida ta, amma ace matar ka wadda ka auro ka aje a gida ita ce zata dinga bin al amuran ka dan kawai ta gano wani laifin ka.Baffa yace Ka yi hakuri Su mata haka suke. Halifa yace Anya ta fada maka abinda ta aikata kuwa ka ke bani hakuri ? Ta fada inji Baffa. Halifa yace in kuwa haka mata suke to su sha zaman su na hakura. Asiya bata san lokacin da ta mike ba ta isa gaban Halifa ta zube tana fadin Dan girma Allah dan soyayyarka da manzo Allah dan darajar maihaifan ka da suke kasa dan kimar Baffa da muke gaban shi ka yafe min. Wallahi ba zan sake ko kawo hakan a raina ba, na tuba. Ta soma kuka, in kuma na sake ka dauki dukkan mataki a kaina. Baffa ka zama sheda. Halifa ya yi shiru domin dai Asiya ta gama daure shi ta hada shi da kokoluwar abinda za a hada kowane dan Adam da shi ya saduda. Baffa bai ce kala ba domin in har Halifa bai duba kalaman Asiya ya ba su kima ba, to ido zai zuba. Dakin ya yi tsit sai kukan Asiya da take yi na debe tsammani domin wadannan sune kalaman da kaɗai take da su in yaƙi sai dai ta koma gida ta rungumi kaddara. Ya sabule kafar shi ya nufi fita. Sadiya da Baffa suka bishi da kallo ya yin da Asiya ta saki sabon kuka. Dafda zai fita ya furta Ki koma gidan ku zanzo. Baijira Jin komai ba ya fice. Baffa ya ce zashi tunda yace za shi, amma dan Allah ki kiyaye gaba dan Allah Asiya tace Insha Allah. “Ya ce Allah ya shi muku albarka . Bayan sun dawo gida suka sanar da Inna komai tace To Allah ya kawo shi lafiya. Sai dai ya zo yau ya zo gobe Asiya har da yin kitso aka yi lalle ana jiran zuwan miji amma shiru.Sai ranar Juma a daidai da cikar su kwanaki takwas da zuwa gidan Baffa Asiya tana kwance a tsakar daki ta yi nisa cikin tunanin mafita. Kamar daga sama taji Inna tana fadin sannu da zuwa Halifa kai ne da rana haka? Yace Nine Inna kafin Asiya ta tashi ta kimtsa har ya iso dakin kofar ta yi masa shinfida cike da rawar jiki tana yi masa sannu da zuwa.Ya amsa fuska ba annuri Suna gama gaisa wa da Inna yace Inna idan ta shirya ta same ni a waje kuma ta hanzarta. Inna tace ai gata nan tana jinka. Yana fita Inna tace Anya Asiya kya koma gidan Halifa kuwa? Dubi yadda ko ta danki baya yi bare ke. Asiya tace Inna ya kike fadin haka? Ta tashi tana tattara Yan shirginta tana fadin Ance miji da mata sai Allah zamu shirya abinmu Inna ke dai ki yi mana addu a. Sadiya ta fitar mata da akwati ya bata leda da kayan sha yi da danyan Kwai. Asiya ta yi sallama da Inna Abba da Sadiya suka rakota tana ce musu sai sun zo. Asiya tana ta satar kallon Halifa wanda yake tuki yana waya da abokan kasuwanci sa, ya sa Bluetooth a kunne Ko da ya gama har suka isa gida kala bai hada su da shi ba.. Ya dakko mata kaya har cikin daki. Ya aje ya fita. Ta kwantar da yaron yana bacci a kan gado ta fada ban ɗaki dama bata yi wanka a gida ba, tana faɗin dakin kai da dadi ya ke ba wai batun talauci bane komai karfin iyayenka dakin kai Duniya ne. Ta fesa wanka ta zata zata same shi a dakin Sai da taje daukar kaya ta lura ba komai nashi a dakin. Jikinta ya yi sanyi ta zura doguwar riga ta fita. Rataye da jaka wadda yake zuba wayoyi wani lokacin ya fito daga ɗaya dakin. “Kasuwa zaka? Ta furta a hankali batare da ya dube ta ba yace A a Hotel zani. Ya kulle kofar tare da cire makullin ya zura a aljihu. Asiya gabanta ya fadi sabon canji ta darsa a zuciyar ta. “To ka yi hakuri Yaya Allah ya tsare me za a dafa da dare? Ta fada jiki a sanyaye. Abinda duk ranki yake so ya furta tare da ficewa. Asiya ta zo kan kujera ta zauna. Ga dai gida na dawo amma kuma gidan ya jagwale. Ke kika dawo ke kika yi biko dole ki ga cin kashi da bakaken magana da kin share shi sai kin samu wanda ya fishi. Zuciyar ta ta faɗa. Asiya girgiza kai, a fili tace. “Na dai na sauraro dukkan abinda zaki fada sheɗaniyar zuciyar nan kina yi min mugayen Hasashe ga inda kika jefani. Da dare Asiya ta fesa wanka ta yi kyau sosai cikin kayan bacci bayan ta yi wa ɗanta wanka yana bacci . Ta ji tsaiwar motar Halifa ta aje yaron akan kujera ta je tana yi masa sannu da zuwa zata amshi jakar yace No barta. Ta bi bayanshi zuwa ɗakin . Tabi ɗakin da kallo ya canza masa tsari ya saka duk wani abu da yake buƙata . Ya camza kayan shi zuwa jallabiya Aisiya tace ga abinci can tuwo na yi da miyar kubewa na kuma yi maka farfesu na kan sa dinnan. Ba tare da ya kalle ta ba yace ‘ sannu da kokari amma ni yau doya nake son ci na siyo tana mota bari ma na dakko. Ya fita ya bar Asiya baki bude. Kan Dining ta same shi ya zuba a plate ya ture abincin da ta jere a gefe. Ya dube ta Ki zuba ki ci in kina so. Asiya ta danne wani kululun bakin ciki ta ce ni tuwon zan ci amma bari na rage maka kayan ta kwashe ta maida kicin ta share ɗan hawaye sannan ta dawo. Yana ta cin doyar shi da wani kunun gyada da ya siyo. Sai da ya gama ya du be ta ba wata walwala Ina kika bar ɗan naki? Ta ɗan yi shiru ta na maimaita ɗan ta a zuciya. Ta ɗan ƙago yaƙe ta ce yana falo in ɗakko maka shine? Yace a a barshi ma haɗu da safe amma kije ki maida shi ma kwancinsa . Asiya Ta ɗan yi dim kenan yana nufin ba zai kwana da su ba. Dan ta tabbatar tace. Yayi kewar Dadyn sa,dan yau gunsa zai kwana. Halifa ya mike yana fadin ya kwana da Maman sa Allah ya bamu alkhairi. Asiya ta yi ta juyi a gado ita kam tana bukatar mijinta bare shi da tasan bashi da hakuri. Wasa wasa sai gashi sun shafe kwana uku Halifa ko hannun Asiya bai yi shauƙin tabawa ba. Kamar ba gaske ba haka take kallon abin. Ranar Asabar da dare tana daki zaune wayarta ta yi ringin ta kalla Halifa ne ya ce ki same ni a falo Yayi kyau cikin shadda mai ruwan kasa, gashi yanzu kara wani kyau da kwar jini yake yi. Ta gaida shi ya amsa. Yace ki shirya nan da minti goma zan dawo zamuje Unguwa. Gaba daya ta sadakar gida zai kaita baya cin abicinta baya kwana da ita baya daukar ɗanta sakin fuska ma babu a ranta tace Ta gaji wannan karon matsawar ya kaita gida ta hakura da shi. Ta dawo ta saka jallabiya da mayafin ta ta fito sabe da ɗanta ya kalleta in baki da kaya masu kyau to kawai ki zauna a gida. Tace bari in canza . Yace Shima wannan yaron asa mishi kaya masu kyau. Ta gane fita zasuyi dan haka ta saka kayan fitar sunan ɗanta shima ta saka masa sabbi .Suna ta kamshi Halifa sarkin son gayu sai satar kallon Asiya ya ke yi. Bata san ina zasuje ba kuma bata tambaya ba. Sai ga su a layin gidan su Anty Gaban Asiya ya fadi ta kalle shi tana tuna rabonta da gidan tun lokacin da aka yi mata sharri. Muryar tana rawa tace Yaya dan Allah….. Kar ki damu ya katse ta gani nan tare da ku. *✍🏻 HALIMA ABDULLAHI K MASHI* [2/10, 11:24] Ummi Tandama😇: *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302* Asiya ta dubi Halifa naga kamar gidan da jama a me ake yi? Gajen hakuri ya ke saka unguwarzoma tambayar me aka samu? Ba shiga za kiyi ba? Ya fada yana gyara paking . Suka fito Asiya ta tsaya tana hasaso abinda ya faru. Ko ma dai menene shi a ni ne gaskiya. Dan ta ga su Nihal cikin sabbin Kaya. Baban Nihal ne yake fitowa daga cikin gidan ya nufo su cike da fara a Yaba Halifa hannu suka tafa, ya na fadin “Afwan Halifa na ga ka fusata shekaran jiya . Halifa yace dole in fusata ace auren Hafsi sai Ana jibi zanji dan ina fushi da Anty ko menene ai ba a ki sanar min ba. Bros yace. Kasan bikin ne babu shiri kuma ba tabbaci akan za a yi shiga rigingimu, kasan yaron nan ne da ke zuwa gunta tuntuni Dady yace ya fito tunda bata da aiki sai daga wa matarsa da yayanta hankali, yaron yaki zuwa shi kuma Dady ya sakamata ranar aure, aka ce yaron ya zo yaki zuwa. Nan munzo da Maman Nihal kasan na kawo ta gurin Anty dan na gaji da boyeta . shine fa na amshi lambar yaron gurin Hafsi nace ya zo ya ki, na sa aka dakko min shi mukaje Hisba. A can aka nemo iyaye shi suka zo wani abin takaici ashe ko sana a bashi da ita. Da kyar suka hado dubu Hamsin shine kudin aure da sadaki. Ba lefe bare wani abu na al ada. Gurin zama kuwa gidan iyayensa za su zauna. Asiya da ke gefe wadda ta tabbatar Bros bai kula da ita ba sai da ta ji karshen zancen sannan tace “Ina yini.” Ya kalleta sosai Halifa dama an ganta ne? Halifa ya amshi Yaron ya mika masa ga Babana. Ya fada yana fara ‘a. Bros ya amshe shi baki bude wai tama haihu duk bamu sani ba haba Halifa ashe dai ni zaka iya boye min wani abu. Halifa yace Wai da gaske kake yi ban fada maka ba? Ni fa na dauka na fada maka ka tuna Bros ya ja tsaki a ina ka fada min ɗin kawai dai baka kyauta min ba, dan bana boye maka komai ka sani. Ayimin afwa. Dama ba ɓata ta yi ba tana gurina a sabon gida. Bros ya ja tsaki shine dan rashin kirki muka yi ta nemanta har da kai ana saka addu o i, akwai guraren da nasa ayi min sauka Allah ya bayyana ta kusan guri uku batare da ka sani ba. Halifa cikin dariya yace Gata ai yau Allah ya bayyan ta har da ɗanta. Bros ya yi dariya yace Allah ya yafe maka. Suka dunguma cikin gidan falon cike taf da dangi nan suka yo kan Halifa da murna, sai kuma suka lura cewa da Asiya suke tare, dan haka suka cika da mamaki da kuma tambayoyi akan yau she aka ganta. Sai kuma Bros ya ce ai ga dan Halifa nan fa sabon farin ciki ya tashi maman Nihal da bata taba ganin Asiya ba sai ranar taji kawai Asiya ta kwanta mata a rai. Ita kuma Asiya sai raba ido take ko zata hango Anty gaba ɗaya a tsorace ta ke tana yake tana kallon ta ina Anty zata fito. Hayaniyar ta yi yawa Anty ta tashi daga kwance zata fito. Baba tace Likita ya haramta miki fita cikin hayaniyar nan dan haka ki kwanta. Anty tace yanzu Zan dawo Ina ga kamar wasu bakin aka yi. Hajiya Talatu ta shigo suka ci karo tace ga Halifa nan da matarsa kawata har da dan su saurayi da shi. A tsakiyar kai Anty ta ji maganar dan haka ta fita da sauri dan tabbatar da abinda ta gani. Ta daga yatsanta dan manuni tana nuna Asiya abinda kawai ta iya furtawa kenan? Ta zube a kasa tana wani irirn abu kamar farfadiya. Asiya ta makale a bayan Halifa tana faɗin mu tafi gida. Bai ce mata Kala ba kuma bai je gurin Anty ba wadda dangi suka zagaye ta suna kuka. Bros ya dauki Anty cak sai mota. Suka wuce Asibiti Asiya sai kuka take. Ta ji tausayin Anty ganin yadda ta rame ta kare duk tsufa ya bayyana a gare ta. Halifa ya dakawa Asiya tsawa ki rufe min baki dan Allah kina ta kukan nan tun a gidan kin fi kowa tausayi ne ko me? Asiya tace Nice sila data ganni ne ta fadi da lafiyarta kalau. Yace Ke kika ture ta ko kinje kusa da ita. Alhakin kine ya ka mata da kunya. In ta ci Sa a bata mutu ba ta nemi gafarar ki. Asiya tace Ni fa tuntuni na yafe wa Anty komai ya wuce a gurina. Muje Asibitin. Baza a ba Halifa ya furta a fusace. Tsoro ya darsu a zuciyar Asiya ta yi shiru. Bayan sun isa gida Halifa ya kasa zaune da tsaye. Can Asiya ta jiyo shi yana tambayar Bros cewa wane Asibitin su ke? Ya dauki mota ya fita. Ance hannun ka baya rube wa ka yanke ka yar.Domin sai ga Halifa ya tasa Anty yana kuka likita ya tabbatar masu rabin jikinta ya shanye Tana kallonshi tana hawaye wanda bai san ko na menene ba, sai dai yafi kama da hawayen nadama in ya yi la akari da yadda kwayar idon ta take nuna rauni. Halifa ya shiga dakin Asiya tana zaune ta rasa wane irin tunani ma zata yi game da yadda rayuwarta ke tafiya a harɗe. Ya zauna kusa da ita, Asiya ta dube shi cike da sa ran zai hantare ta kamar yadda ya saba. Tace ya mai jikin kuwa. Yace ta nakasa Asiya Anty ta koma abin tausayi Ina son in Allah yasa ta fara magana zan kai ki ki yafe mata. Cike da tausayi Asiya tace Insha Allah dama na yafe mata. Ya kama hannun Asiya Ina son ki yi min wani alkawari mana dan Allah karki kara zargina nima kuma na daina boye miki koma menene tunda abinda ya kawo duk wannan matsalolin kenan har ga Allah na yi haka ne dan bana son ki shiga damuwa Asiya ina son ki fa irin wanda bakya tsammani sannan na tabbatar kina sona . Kirike a ranki ko wata na aura sai dai don jin dadi da nishadi ko kinyi sakaci da wani gurbi in kawo wata ta cike amma ba dan so ba,shi so guda daya ne tak kuma ke nake yi wa. Asiya tace Insha Allah tana rungume Halifa ya matse ta gam kamar ya maidata cikin sa dan kauna. Tace ka Sa a ranka in har ni ce zan baka matsala to ka yi bankwana da matala kishinka ne da son ka suka min yawa. Yaya ina alfahari da wani abu wanda ke da wahalar samu a zamanin nan. Kai ka fara sanina a ‘ya mace, ni na fara saninka a ɗa namiji Katuna yadda muka yi ta fama a daren farkon mu? Har yanzu kalamai da sambatun ka suna nan a zuciyata. In furta maka su? Ya dora tafin hannunshi kan lebunan ta.Nima ban manta da sunayen wadanda kika yi ta kira su kawo miki dauki ba. Suka sa dariya tare da rungume juna. Hafsi ce ke jinyar Anty lokacin da Asiya suka shiga dakin sun dawo daga gashin ƙashi kenan. Dakin cike Bros da matan shi, ga Dady da matar sa Bintu. Gaban Asiya sai faduwa yake kar ganinta ya sake rikita Anty. Idanu Anty ta zuba kan Asiya tana ta kallonta ba tsammani sai aka ji Anty ta yi wani gwaranci wanda da bata taba magana ba. Gaba daya aka maida hankali gurinta Hafsi tana cewa me kike so Anty? Ta maimaita sau uku kafin aka gano tana fadin Asiya ki yafe min. Yadda Anty ke hawayen shine ke bayyana tsantsar nadamar ta Asiya ta kama hannun ta tana fadin Anty nayafe miki komai cikin kuka Asiya sarkin tausayi. Anty tace a bata takarda da biro dan tana son yin magana amma ba a gane me take faɗa sai da kyar. Da hagu ta rubuta shima da kyar. “Na cutar da Asiya da yawa ni na mata sharrin kwarto. Ni na bata guba ni na yaɗa ta a Duniya. Halifa ne ya fara Karantawa ya jefar da takadar dar ya kama hannun Anty yace duk ta yafe miki Anty Allah ya baki lafiya. A mota za su gida Asiya tace shi kuma wannan yaron ko yana Ina yanzu oho. Halifa yace ban jima da sa wa a sake shiba kurkuku muka aje shi tuntuni ai ni na san komai. Asiya tace rayuwar nan abin tsoro ce dubi yadda Anty ta dawo abin tausayi .Halifa yace Hafsi ma rayuwa ta nuna ta tun yanzu aure mara daraja yanzu ma wane aure tunda dole ta yi jinyar Anty. Asiya tace dan Allah ku samo mai jinya ita kuma sai ta tare a gidan ta . Bayan sallamo Anty aka yi tarewar Hafsi sai dai fa kowa yaƙe ya ke abin gwanin tausayawa Hafsi zama da iyayen miji gida daya daki ciki daya sai maida Kaya aka yi gida. Saukin ta ma Halifa yace Bros ya samu inda zai saka mijin nata a kwari ya koyi kasuwa to in har ya riƙe amana akwai yiwuwar su duba lamarinsa. Asiya suna kwance da Halifa da rana tace Yaya ka ya kice wannan soyayyar ta rana tsaka zuwa yanzu dai duk na biyaka bashin da na ci maka ga azumi yana zuwa saura baifi sati daya ba. Ya ƙara matse ta ai karki damu ibada zamuyi sosai da azumi kamar ba gobe. Ya daga filon da ya tada kai,kin gani dakko passport Kaf azumin mu a Umara zamu yi shi. Farin ciki Asiya ta dira kasa tana ta rawa ta manta ma tinɓir take Halifa sai dariya yake tana sake birge shi.Ya sauka ya kama ta ya rungume kin sake mai dani ruwa wannan rawar ta birkitani Baby. Asiya tace dole in nuna godiyata a gareka amma Ina zan bar yaro na? Yace dashi zamu tafi. Bayan fitar Halifa Asiya ta dinga kiran dangi tana sanar da su. Ta fita tsakar gida tana ƙarewa gidan kallo tana godewa Allah da kyautar miji kamar Halifa da ya bata. Zuwa yanzu ta iya da fushin sa kuma tana kauce wa duk abinda zai janyo hakan. Alhamdulilah ƙarshen littafin HASASHE kenan Allah yasa muyi amfani da darasin dake cikin labarin. Downloaded from NovelsHQ.com This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com to download more hausa novels visits our site at www.Novels.Com For feedback and support Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ.com Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ.com Telegram : https://t.me/NovelsHQ.com