Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com to download more hausa novels visits our site at www.NovelsHQ.com For feedback and support Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ Telegram : https://t.me/NovelsHQ [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "To sun ce ba sa jin barci ki rabu da su." Baffa ya shigar musu shi yasa ta ƙyale su, ta tafi ɗakin Baffa ta tafi da ruwan gora saboda yana shan ruwa da daddare. Ta bar su a falonta suna dasa sabuwar hira har da Baffa shima komawa ya yi ya zauna. Ammah ta sake dawowa ta gansu dirshan suna hira. "Yau wai meke damun ku? Baffa mu je ka kwanta ka ƙyale yara nan." Baffa ya amsa da to, Saddam ya kalli Abdurahim suka kalli juna suna kunshe dariya. "Munafukai." Ammah ta faɗa tana hararansu. Suka kwashe da dariya Baffa na mirmishi. "Ammah Baffa fa ba ya jin barci." "Ya faɗa maka? "To ga Baffan nan a tambaye shi? Baffa wai kana jin barci? Saddam ya juya yana tambayan Baffa. "To ko ban ji Saddam tunda Jamila ta ce ina jin barci ai haka ne gaskiyan magana." "Baffa kai fa mijin ta ce ne na lura." In ji Abdulrahim yana dariya. "A'a ba mijin ta ce ba ne shi, mijin kan ta ce ne." Saddam ya gyara masa, Ammah ta wurgesu da cussion ɗin kujera tana cewa su fitar mata a cikin ɗaki su kuma suna ta dariya. "Ammah gaskiya fa muka faɗa. Duk abin da kika ce Baffa ba ya iya miki gaddama." "Ku kuma kuna jin haushi.? "Aa kawai dai shima Baffa ya dinga nuna ƙwanjinsa." Baffa na ta dariya ita kanta Ammah dariyan take yi. Saddam da Abdulrahim shaƙiyan yara ne haka suke tasa su da zolaya. Baffa ne ke faɗa musu, su yi fatan samun mace irin Ammah dukkansu mijin kan ta ce za su zama. "Tana da kyakyawan hali misalin mace ta gari ce Jamila." "Awwww.." Suka haɗa baki wajen faɗa ganin Ammah na ta mirmirshi jin Baffa na yabon ta. "Su Baffa an iya kalamai." Saddam ya faɗa yana tsintsira dariya. "Ammah da kalaman nan ne Baffa ya sace zuciyarki? Ta wurga masa harara tana mirmishi. Baffa ne ba su labarin ai haɗa su aka yi kuma suna haɗuwa ganin farko suka aminta da juna. "Love at first sight kenan." Abdurrahim ya faɗa yana dariya. "Ammah ta ga farin bafillace ina za ta yi sakaci." "A'a itama ai fara ce, ni ne na yi sa'a." Baffa kenan yana ta wasa Ammah kunya ta ji ta bar musu falon su kuma su Saddam suna ta dariya. Da gaske yau hira suke ji domin har ɗaya saura na dare suna falon Ammah suna hira. Saddam kawai ya sako wata maganar wai yanzu sai Baban Hanan ya zo ya ce Hanan ɗiyar shi ce? "Haba ai da kunya. Shi da ya ce baya son cikin ? "Irin su ba su da kunya ina nan da kai zai iya dawowa ya ce ina abin da Auta ta haifa." "Ai ko da ya ci ubansa wallahi." Abdulrahim ya faɗa da iya gaskiyan shi. Baffa na gefe bai ce komai ba cigaba da magangansu suka yi Saddam na faɗin shi jiran ranar kawai yake yi ranar da Habib zai sako kafarsa a gidan nan sai ya tara matasa anguwa sun yi masa jina jina. Abdulrahim ya ce daga karshe mu haɗasa da jami'an tsaro. Ammah ta fito lokacin da suke auna irin iziyar da za su yi ma Habib duk ranar da tautsayi ya kawo shi gidan nan. "Ni na manta da shi, koma yana ina yanzu na tabbata Auta ta fi shi samun rayuwa mai inganci. Ai ba za ka yi zalunci ka sha ba sai Ubangiji ya yi sakkayya tun a duniya." "Ai Ammah yana can ma yana girban abin da ya shuƙa. Irin addu'o'in bala'in da na dinga auna ma wannan mutumin ai in dai Allah ya karɓi addu'o'i na to yana cikin iftila'i." Ammah ta ce har Umra ta je ta yi addu'an Ubangiji ya yi ma Auta sakayya kuma da ikon Allah yana can yana gani. "Kuma wai ko danginsa ba su sake neman ku ba Ammah.? Abdulrahim ya tambaya. Ammah tace ba wanda ya sake neman su, ai in shi Habib ya ce ba ya son cikin bai kamata su su juya baya ba tunda sun san jinin su ne. Sai a lokacin Baffa ya yi magana da cewa shi ya yanke alaqar daga farko. "A baya ɓacin rai da ganin halin da Auta ta shiga ya sa na ce na haramta ma Habibu da danginsa abin da Auta za ta haifa. Amma daga baya na fahimci na yi kuskure, Hannatu mace ce duk iya abin da za mu yi mata tana bukatar Uba da danginsa." Kallon Baffa kawai suke yi mamaki ya hana su magana. "Ko ba a ba shi y'arsa ba watarana ina da rai ko ba ni rai in har Habibu da danginsu suka waiwayi jininsu ku karɓesu ku kuma ba su dama" "Dama kuma Baffa? Wani irin dama kuma? Ammah ta tambaya cikin mamaki. Received at 09:09Reactions: ❤ 9, 👍 1, 😱 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Damar ya nemi afuwarku sannan ku ba shi dama ya haɗu da jininsa." "Cewa ya yi ya gane ya yi kuskure Baffa? Kuma cikin da ya ce ba ya so ne za ka ce a ba shi dama ya ga jininsa? "Ban sani ba amma ina ji a jikina lokacin ya kusa. Ko da ina rai ko ba ni da rai wasiyya ce Jamila. Hannatu mace ce wata rana za ta yi aure tana bukatar mahaifi da dangin shi in har Habib ya gane kuskuren shi ku karɓe shi ku yafe masa muma mutane ne muna yin laifi Ubangiji na yafe mana to babu laifi in ya yi laifi kuma ya gane kuskuren shi ya tuba." Da alamun maganganun Baffa sun sanyaya musu jiki har da Ammah ita kanta "Baffa ni ban gane maganganun ka ba, ka haɗu da Habibun ne ko ya kira ka a waya ne? "A'a ban sake ganin shi ba kuma da ya kira ni da na faɗa miki. Kawai tunasarwa ne domin na san ko a jima ko a daɗe Habibu zai dawo ya nemi Ummu Salma tare da bin kadin cikinta jikinta. Jininsa ne zai yi nadama ko kuma alhaki zai bibiye shi, alhakin ne kuma zai kawo shi nan kusa." "In har ya zo kar ku yi masa rashin ɗa'a. Ku yi masa kara sannan ku ba shi dama. Muma damar Ubangiji ke ba mu da babu wata damar da duk rayuwarmu ba ta kawo yau cikin farinciki ba." Shuru suka yi kowa na saƙa maganganun Baffa a zuciyarsa Ammah dai cewa ta yi Baffa na jin barci ya zo su kwanta sai ya miƙe yana faɗin kanshi ke ɗan ciwo ta duba masa panadol. Saddam da Abdulrahim suka miƙe suka fita tare da Baffa suna yi masa sallama. "Allah ya tashe mu lafiya." Suka amsa da Amin suka tafi bangaren su Baffa kuma ya shiga ɗakinsa tiolet ya shiga ya kama ruwa ya zo ya sauya kaya zuwa jallabiya ya kwanta Ammah ta shigo da maganin ta tashe shi ta bashi ya sha ya kora da ruwa ya koma ya kwanta. Ammah ta yi zuru tana kallon shi domin a cikin lokaci ƙalilan sai ta ga duk Baffa ya sauya ya yi wani sanyi da shi. Da ta tambaye shi sai ya ce ciwon kan ne ya ɗan dame shi. "Kuma shi ne tun ɗazu ba ka yi magana ba? Ko rashin barci ne Baffa? "A'a yanzu nan ne ciwon kan ya fara amma na san zuwa safe zai bari.' Ta yi masa Allah ya sauwaƙe Ta rufa masa bargo a kafafunsa sannan ta yi shirin barci itama ta kwanta bayan ta je ta rage hasken falonta ta rufe falon. Kofar turakan Baffan ma sakayawa ta yi, saboda ana sanyi ba ta kunna fanka ba. Itama ta gaji shi yasa tana kwanciya sai barci. Can cikin dare ta ji Baffa na kiran sunanta. Ta tashi cikin barci ta ji yana cewa ta kunna masa fanka zafi yake ji. Ta yaye bargon ta sauko daga kan gadon ta kunna hasken ɗakin Sai ta ga Baffa na ta zufa abin mamaki sanyi fa ake yi. Ba ta yi musu ba ta kunna masa fankar tana duba agogon bangon dake ɗakin Baffa uku saura na dare. Gefen Baffa ta zauna tana miƙa hannu tana share masa gumin da ya taru a saman goshinsa. "Baffa ciwon kan ne? Sai ya ɗan buɗe idanuwansa yana kallonta. "Na ga kana ta gumi ne! Ko akwai zazzaɓi a jikin ka ne? Ta faɗa lokaci ɗaya tana dafa goshinsa. Sai ta ji jikinsa ya ɗan yi ɗumi. "Baffa ina jin zazzabi ne zai kama ka jikin ka ya yi ɗumi." "Ba komai ki koma ki kwanta." Baffa ya faɗa a sanyaye muryansa ta yi wani iri. Ammah ta ji kawai gabanta na faɗuwa ko Baffa na ciwo bai saba yi mata magana da wannan muryan ba. Sai hankalinta ya tashi ta fara cewa ko ta ƙaro masa maganin ne ya yi mirmishi ya ce ciwo kan ya sauka kawai zafi ne yake ji ta koma ta kwanta. Ba ta yarda ba sai da ya rike hannunta duka biyu gam a cikin hannayensa. "Ki koma ki kwanta na ji sauƙi zafi ne kawai na ke ji kuma da kika kunna fankar ba ki ga na daina gumin ba." Ba ta kwanta ba zama ta yi da shi tana riƙe da hannayensa. Abin da ya ƙara tsorata ta ganin ga iskar fanka amma shi yana ta gumi ita ke share masa gumin ma da hannunta. Zuwa can kuma sai ya samu barci sai da ta ga yana mumfashi a hankali sannan ta koma ta kwanta a zuciyarta tana faɗin da sassafe za ta kira Baba ya zo su je asibiti da Baffa ba ta taɓa ganin ya yi irin haka ba. Bini bini ta juya tana kallon Baffa tana taba shi ta ga dai yana ta barcinsa. Itama barcin ne ɓarawo ya sake tafiya da ita. Received at 09:09Reactions: ❤ 13, 👎 1, 🥰 1, 🤔 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sai dai kamar a cikin barcin ta yi mafarkin Baffa na kiran sunanta ta farka a firgice. Sai tarin shi ta ji daman ba ta kashe hasken ɗakin ba ta yi kanshi cikin firgicewa Tari kawai Baffa yake yi har gadon da suke kwance yana jijjiga. Ɗago shi ta yi ya jingina da filo tana shafa masa bayansa lokaci ɗaya tana yi masa sannu. "Sannu Baffa me ya faru ne? "Tari ne kawai ya sarƙe ni." Ya amsa mata cikin rawam murya. Har a lokacin gumi yake yi ta sauko daga kan gadon ta fita tsakar gida zuwa kitchen ta kunna filitar kitchen ɗin ta dauko kofi ko da ta dawo tarin ya dawo ma Baffa jikinta ba in da ba ya rawa ta durƙusa ta tsiyaya masa ruwan a kofi ta zauna a gefen shi ta ɗago kan shi tana ba shi ruwa jikinta ya saki ne lokacin da ta ga ruwan da take ba ma Baffa yana dawowa ta gefen bakin shi sannsn tarin bai tsaya ba. Har yana hawaye wasu suna zuba wasu na sake tunkuɗowa. Ammah ta ruɗe hankali tashe take kiran sunan Baffa. Amma ba ya iya amsawa tarin ya sarƙeshi kamar wanda ya ci wani abu ya sarƙe shi. Idanuwansa sun yi jajir gwanin ban tsausayi. Amma ya miƙe tana faɗin bari ta je ta taso su Saddam su zo su tafi asibiti amma sai Baffa ya riƙo hannunta ta dawo ta zauna tana yi masa sannu. "Ka bari na je na taso su, ba ka da lafiya Baffa mu je asibitin tarin nan naka ya yi yawa." Bai saki hannun na ta ba, kan shi ya fara girgiza mata tarin ya ɗan lafa masa. "Ki yi haƙuri Jamila." Baffa ya faɗa cikin dashewar murya. Hawaye na zubo masa ta gefe da gefen kunnuwansa. Kamar an kwarara ma Ammah ruwan sanyi haka ta ji, ta kasa magana kawai ta kafe Baffa da idanuwana. "Ki yi haƙuri lokaci ya yi da za mu yi sallama da juna haka nan." Ya faɗa tarin na sake kama shi, Ammah ta durƙushe a ƙasa a gaban shi zuciyanta ke bugawa hannunta da jikinta babu in da ba ya rawa "Baffa me kake faɗa haka? Ina kuma za ka je? Bakinta na sarkewa saboda tashin hankali. Kuma ya riƙe hannunta gam yaƙi sakinta. Cewa ya yi ta zo ta zauna dole ta mije ta zauna a gefen gadon ya janyo jikinsa da ya saki ya ɗora kan shi a samam cinyarta suna masu kallon juna. "Ki yi haƙuri Jamila lokaci ya yi." Sai ga hawaye, yaushe ne rana na ƙarshe da ta ga kukan Baffa? Duk da yana da raunin zuciya amma ba kuka irin wannan ba. Ta san mutuwa tunda iyayenta sun rasu amma ba'a taɓa mata mutuwa ana ta zuru'an ba. Yadda Baffa ke yi kawai ya sa jikin Ammah ya saki gabaɗaya. Baffa ya gama kwanakin da aka diɓo a duniya yau ko tana so ko ba ta so lokaci ya yi da Baffa zai tafi ya barta. Yadda Baffa ke yi lokaci ne ya yi watakila ma mala'ikun ɗaukan rai suna cikin ɗakin. Tarin da yake yi na kiran ajali ne. Ba ta san a ina ta samun ƙwarin gwiwa ba amma jin bakinta kawai ta yi, tana maimaita ma Baffa kalmar shahada kuma sau ɗaya ta maimaita ya kama yana yi. Baffa ya cika idanuwansa kamar suna kallonta amma ba ita yake kallo ba idanuwansa sun yi sama ya rufe kalmar shi ta ƙarshe da la'ila ha illallahu muhammdun rasulillah.' A man cinyar Amma ya cika har a lokacin akwai danshi hawayensa a gefe da gefen kunnuwansa. Ammah ta kasa gane a wani yanayi take ciki. Ta ɗago idanuwanta tana kallon agogo Uku da mintina arba'in na daren ranar Litini Baffa ya koma ga Allah. Hannunta da ta ji ya sandare ta miƙa ta shafe idanuwan Baffa. Sannan ta yi jarumtar sauke kan shi a saman gado ita kuma ta sauko ƙasa ta durƙusa a gaban shi tana kallon shi. Me take ji? Wani abu ne ƙullutu mai girma ya yi mata tsaye cak a wajen zuciyarta shi bai wuce ba shi kuma bai faɗa mata ba. Baffa ne ya tafi ya barta? Ta kasa gasgasta abin da ya faru cikin mintina. Ga shi kwance kamar mai barci kamar ta kira shi ya amsa. Wai ba ɗazu nan nan ba daɗewa suka gama hira tare da su Saddam ba lafiyan shi ƙalau fa, cewa kawai ya yi kan shi na ciwo ashe na ajali ne. Hawaye ko kaɗan ba su kawo mata ba zuciyarta ta bushe, amma ta yi mata nauyi jikinta ya saki gabaɗaya. Received at 09:09Reactions: ❤ 12, 😭 6, 👍 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta miƙe tana jin kamar ba ita ba. Tana jin ta kamar falle takarda saboda yadda take jin kanta. Gyara ma Baffa kwanciya ta yi akwai zanin ta a gefe ta jawo shi ta yaga shi da ƙarfin tsiya da kanta ta duka ta haɗa babban yatsun kafafun Baffa ta kulle su kar kafin safe su sandare. Sannan ta fita ta koma ɗakinta ta buɗe wardrope ta ɗau zaninta sabo ko taɓa sa shi ba ta yi ba ta zo ta rufe Baffa ruf daga kafafunsa har kansa. Sannan ta shiga toilet ta ɗauro akwala ta zo ta shimfiɗa darduma ta fara sallla, ba ta san ko raka'a nawa ta yi ba ita kawai salla take yi da ta sallame ta sake miƙewa ga Baffa kwance a kan gado a matsayin gawa Ta kasa zama ko na minti ɗaya ballatana ta yi wani tunani ji take yi kamar za ta haukace kamar ƙarya ne sai dai ba ƙarya ba ne ga Baffa nan kwance babu rai a tare da shi. Ta yi salla har sai da kafafunta suka ga ji, har sai da ta ji an fara kiran sallar asuba a wasu masallatan da suke kusa da su. Sannan ta dakata ta zauna tana jan casbaha ta ƙura ma gawar Baffa idanuwanta amma ta kasa kuka ta rasa ma abin da take ji amma wani abu mai nauyi yana yi mata ɗaci ya tokare mata a maƙoshi ya kasa wucewa. Tana nan zaune har lokacin salla ya yi ba ta iya tashi ba Hasbunallahi wani'imal wakeel kawai take maimaitawa bakinta na motsi kamar ba ta cikin hayyacinta Daga tsakar gida ta ji muryan Saddam na kiran sunanta. Ƙofar dakin Baffa a buɗe take sannan akwai hasken wuta zumbur ta miƙe ba ta son ya shigo ya fahimci halin da ake ciki yanzu sai ta yi zaraf ta fito suka haɗu a tsakar gida. "Ina kwana Ammah" Bai fahimci yanayin ta ba ganin ta da hijabi bai kawo masa wani tunani ba. "Ina Baffa? Har wasu masalatan fa sun tayar da salla? "Ku je kawai, yau a gida Baffa zai yi salla ba ya jin daɗin jikinsa." Ya ce Subhanallah me ke damun shi ta ce zazzaɓi ne. Sai ya wuce yana faɗin to bari su je masallaci su dawo sai su shigo su duba shi ta amsa masa, bayan ficewarsa ta daɗe a tsaye Baffa ke fara tashi, ya tashe ta ya yi alwala sannan ya fita ya tayar da su Saddam ya tada su domin su tafi masallaci. Allahu akbar ga shi yau sun sun tashi amma Baffa bai tashi ba. Ɗakin ta koma ta tayar da salla. Sai da ta idar da salla sannan ta zo gaban gawan Baffa ta buɗe shi tana kallon shi kamar ta kira shi ya amsa. "Allah ya jiƙan ka da rahama Baffa. Allah ya haɗa ka da mala'ikun rahama Allah ya sa su yi murna da zuwanka. Ubangiji ya karɓi baƙunci ka." Ta kasa ƙarisawa tana jin wani irin abu na ta so mata. "Allah ya haɗamu a darussalam." Sannan ta miƙe ta ja zanin ta sake rufe shi. Fita ta yi zuwa falonta ta ɗauki wayarta sannan ta nemi gefen gado ta zauna ta kira wayar Abdulrahaman Lokacin baya gida ya je masallaci Ummu Sulaim kuma ba ta ji kiran ba wayar tana chaji ne kuma a silent take. Ganin bai ɗaga kiran ba sai ta kira Abdullahi Shi ta same shi, domin ya dawo daga masallaci kenan ya kwanta wayar ma tana hannun shi ne sai ga kiran Ammah gaban shi ya faɗi kiran waya wajen shidda na safe Allah ya sa lafiya. Sai ya ɗaga wayar da sallama amma kirjinsa na duka. "Baba." Ta kira shi kamar yadda ta saba kiran shi. Ya ji wani kaifi a muryanta da zai ce bai taɓa jin Amma ta kira shi da wannan muryan ba. "Na'am Ammah lafiya kuwa? "Lafiya ƙalau ka taho gida yanzu." "Amma me ya faru? Ya faɗa yana saukowa daga kan gado cikin ruɗewa jikinsa ya ba shi ba lafiya. "Na kira Abdulrahaman bai ɗauka ba, ka kira shi, shima ya taho gida yanzu." Ammah ta faɗa tana ƙokarin daidaita yanayinta. "Ammah wani abu ne ya faru? "Ku zo dai. Ku zo gida" Da sauri ta kashe wayar tana numfarfashi lokaci ɗaya ta dafe kanta tana kiran sunan Allah. Dai dai lokacin su Saddam suka dawo daga masallaci, hango Ammah suka yi a falonta ya sa suka shiga dakin suna gaisheta Ta mike da sauri ba ta son su haɗa idanuwana. "Ammah ya jikin Baffan? Mu je mu ga jikinsa na shi ko kuma kawai mu je asibiti ." Abdulrahim ya faɗa Saddam ya ce shima dai haka ya gani. "Yanzu haka maleria ce." "Ba ta wuce ita ɗin ce." Received [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ammah ta yi gaba suka bi bayanta har zuwa cikin ɗakin Baffa. Ta tsaya a gaban gawan Baffa su kuma suna bayanta tunda suka shigo ɗakin kamar an zare musu lakkan jiki ganin Baffa kwance rufe da zani ya sa suka fara kallon juna. "Ammah zazzaɓin ne ya yi zafi haka? Saddam ya faɗa yana fatan Ammah ta amsa da cewa zazzaɓin ne ya yi zafi Baffa ya rufa har saman kanshi amma abin da bai gane ba akwai bargo me ya sa Baffa zai rufa da zani? Abdulrahim ko ƙura ma Baffa idanuwana ya yi Baffa ba ya motsi, kirjinsa ya doka a rikice ya kalli Ammah. "Ammah Baf..f" Sai ya kasa ƙarisawa, domin da gudu Saddam ya durƙusa ya yaye zanin Baffa ga shi nan kwance idanuwansa a rufe daga sama har ƙasa suka sauke ganinsu a ƙafafunsa in da Ammah ta haɗa ta ɗaure. A tare kirjinsu ya doka, Abdulrahim shima ya yi ƙasa ya durkushe yana ganin duruduru. Ammah suka kalla da ta koma ta jingina da bango tana maimaita salati a cikin zuciyarta. "Baffa ya tafi ya bar mu, jiya ƙarfe uku na dare Ubangiji ya karɓi Baffa." Ammah ta sanar da su cikin wani irin murya. Saddam ya faɗa jikin Baffa kamar ba namjji ba ya wage murya yana kuka yana kiran sunan Baffa Shi ko Abdulrahim bakin shi ya danne da hannu bibbiyu kuka na son ƙwace masa da rarrafe ya fita daga ɗakin ya koma ƙofar ɗakin Baffa yana hawaye, hawaye masu ɗaci da zafi. Jiya fa har ɗaya saura na dare suna tare da Baffa suna hira ashe ciwon kan da ya ce yana ji na ajali ne. "Innalillahi wa'inna inna ilaihirraju'un." Haka Abdulrahim ya ke maimaita yana kuka mara sauti hawaye na zuba wasu na koran wasu Saddam daga cikin ɗakin Baffa ana jiyo kukansa. "Baffa " Haka yake kiran sunan shi yana kuka har da shessheƙa. Ammah ce ta yi ƙarfin halin daka masa tsawa. "Meye haka? Kai da za ka yi masa addu'a shi ne za ka tasa shi kana yi masa kukan wofi? "In kuka zaka yi, ka fita waje." Ta faɗa tana buɗe murya. Tashi ya yi da gudu ya fito waje, ya kusa ture Abdulrahim dake zaune dirshan a ƙofar ɗakin Baffa yana kuka. A tsakar gida shima ya baje yana kuka da duka muryansa. Hamma Abdullahi ya fara isowa gidan. Sun yi waya da Abdulrahim ya faɗa masa Ammah ta ce su zo gida shima ya ce ya ga kiranta hankalinshi tashe ya ce wani abu mara daɗi na faruwa duka sun ji a jikinsu. A waje Abdullahi ya yi parking ɗin motarsa Da sauri ya shigo gidan sai dai kukan da ya ji ne ya sa ya faɗo gidan da gudu jallabiyan jikinsa ma a bai bai ya saka ta saboda sauri. Ganin Saddam baje a tsakar gida yana kuka mai sauti ga Abdulrahim a ƙofar ɗakin Baffa yana hawaye tare da salati. "Me ya faru? Ya tambaya muryansa a buɗe. Ganin sa ya sa Saddam ya sake rushewa dakuka. "Hamma Baffa." Ya faɗa shessheka na hanasa magana. Abdullahi ya zaro idanuwana. "Me ya faru da Baffan? Zuciyarsa ne ta nemi tsayawa cak lokacin da Saddam cikin kuka yake faɗa masa Babu Baffa, Baffa ya tafi ya barsu. Abdullahi ya yu wurgi da takalmin kafarsa ya rumtuma ɗakin Baffa yana fatan ya ga ba gaskiya ba ne yana fatan ya ga Baffa zaune. Sai dai abin da Saddam ya faɗa masa gaskiya ne. Ya iske Baffa na kwance babu rai a jikinsa ga Ammah zaune a gefe tana jan carbi ko bai tambaya ba yasan yau sun wayi gari cikin wata jarabawa. Allahu akbar, duk cikin su yafi shaƙuwa da Baffa saboda tare suke kasuwanci daga shi sai Saddam da Abdulrahim tunda kodayaushe suna gida tare da shi. Ya durƙushe a gaban Baffa ya dafe kanshi hawaye suna shatata masa. A jere yake sauke numfashi na kukan zucci. "Ku daina masa kuka Baba, Baffa addu'an mu yake buƙata a yanzu." Ammah ta faɗa muryanta ta karye amma ta kasa kuka. Abdullahi ya juya yana hawaye yana kallon Ammah. "Ammah." Ya kirata muryansa na rawa bakinsa na rawa duk a lokaci ɗaya. "Baffa ne ya tafi ya bar mu? Ya faɗa kuka na taso mata, ya kwantar da kanshi a kirjin Baffa yana rera kukan zucci yana sharɓe majina. "Baffa Allah ya gafarta maka." "Ubangiji ya sadaka da rahamarsa." A lokacin Abdulrahaman ya shigo gidan shima ganin su Saddam a tsakar gida cikin wani yanayi, ga shi suna ta kuka kamar ba maza ba. [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Bai tsaya tambaya ba ya faɗa dakin Baffa shi ne kaɗai bai gani ba jikinsa ya ba shi wani abu ne ya faru da Baffa amma bai taɓa kawo ma Baffa mutuwa ba. Ko bai tambaya ba, ya san amsar. Ga Abdullahi durƙushe a gaban Baffa yana kuka. Ammah na gefe da Hijabi da casbaha ta sunkuyar da kanta. Tabbas Baffa ya amsa kiran mahallicinsa ashe zaman hiran da suka yi jiya na bakwana ne Baffa lokaci ya yi. Shima gefen Abdullahi ya duka shima yana kallon Baffa amma shi bai yi kuka ba zuciya ce ke suya kawai. Ya fara yi masa addu'a daga karshe ya ce" Allah ya gafarta maka Baffa" Shi ya janyo zanin ya sake rufe shi sannan ya tashi ya zo gaban Ammah ya duka yana kallonta. "Ammah ya haƙurin mu? "Mun gode ma Allah Abdulrrahaman." "Allah ya jiƙan Baffa, Ubangiji ya ba mu haƙurin rashin sa." Ta amsa da Amin kallon ta yake yi ba ta yi kuka ba amma Allah kaɗai ya san suyan dake cikin zuciyarta. "Rasuwar dare ce? "Ƙarfe uku na dare da wani abu ya cika." Ya jinjina kai cikin sanyin jiki da na zuciya. "Allahu akbar Ubangiji ya karɓi bakuncin Baffa." Ta amsa da Amin Amin "Ka kira sauran yan'uwanka, sannan ku sanar da Baffa Umaru." Ya miƙe yana amsa mata. Ya kalli Abdullahi ganin yadda yake hawaye da kuka har yana sauti. Ga su Saddam can a tsakar gida suna ta hawaye suma Kamo Abdullahin ya yi ya miƙar da shi "Haƙuri za mu yi Abdullahi. Lokacin Baffa ne ya yi ba mu da yadda za mu yi." Ya faɗa yana dafa kafaɗan shi alamun lallashi. Suka fita tsakar gida shima Abdullahi a yarin su Saddam ya bi ya yi zaman dirshan a tsakar gida yana dafe kansa lokaci ɗaya yana hawaye. Ya rasa ma wanda zai fara kira wayarsa ya zaro a cikin aljihu ya ga Ummu Sulaim ta kira shi ganin yadda ya fita hankali tashe shi ya sa ta damu. Bai kira ta ba, sai da ya kira wayar Baffa Umaru bai same shi ba sai ya kira na Baffa Salihu shi ya sama bayan sun gaisa tun kafin ma ya sanar da shi abin da ke faruwa ya ce ba lafiya tunda ya ga kiran shi da sassafe haka nan ya sanar da shi Baffa lokaci ya yi. Baffa Salihu ya ja salati ya dire. "Hadi ya rasu Abdulrrahaman? "Wallahi Baffa sa'i ya yi." "Allahu akbar., ciwo ya yi ne ba mu sani ba? "Ba ciwo Lafiyan shi kalau jiya har sha biyun dare muna tare da shi. Lokaci ne kawai ya yi " "Allahu akbar. Allah ya jikan Hadi Allah ya yi masa rahama." Ya amsa da Amin yana faɗa masa ya kira wayar Baffa Umaru bai same shi ba ya sanar da su Baffa lokaci ya yi Baffa Salihu ya ce yanzu kuwa tunda kuma rasuwar ta dare ce sai yanzu kowa zai sani a sanya jana'izar zuwa sha ɗaya na safe haka kafin nan kowa ya iso Hamma Abdurrahama ya amsa masa da to. Suna ma cikin wayar Ummu Sulain na ta sake kiran shi. Sai da suka gama wayar ya kira ta tana tambayan shi me ya faru ya ce kawai ta rufe gida ta ɗauko yara su samu adaidaita su taho gida. "Me ya faru? "Baffa ne Allah ya yi ma rasuwa.' Ta ja salati bai bari ta ƙarisa ba ya kashe wayarsa. Ya juya yana yi ma su Abdullahi nasihan su daina kuka addu'a kawai Baffa ke bukata. "Abdullahi ka yi haƙuri, yanzu mu tsara yadda za mu isar da Baffa gidansa na gaskiya." Cewa ya yi Abdulrahim ya je ya faɗa ma limamin masallacin da su Baffa ke salla nan kusa da su ne, ya tashi yana goge hawayensa ya zura takalmin shi ya fita Saddam dai ko motsi. Dakin Baffa suka koma dukkansu biyu suka durƙusa gaban Ammah. Abdulrahaman na faɗa mata ya samu Baffa Salihu a waya ya faɗa musu ya ce suna tafe yanzu. "Ku kira Fatima, kar ku faɗa mata kai tsaye ku yi magana da mijinta." Hamma Abdullahi ya ce bari ya kira Daddy. "Abdulrahaman ki kira su Balki ku faɗa musu, sannan ka kira Lamiɗo." Ta yi shuru tana saukar da numfashi. "Kar ku faɗa ma Auta tana da juna biyu, za ta iya shiga hatsari ku kira su Jibo su sanar da su, su taho da wuri a sallaci Baffa a sada shi da gidan shi na gaskiya" Ya amsa mata da to, tsakar gida ya fita ya fara kiran Hamma Jibo. Shi kuma Hamma Abdullahi ya kira Daddy ya sanar da shi ya ce yana Abuja amma zai kira Mami ya sa ta samu jirgin da za ta taho Adamawa cikin dubara ba tare da ta san abin da ya faru ba. Received at 09:09Reactions: [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Cikin lokaci kaɗan labarin rasuwar Baba ta zagaya kunnuwan dangi na kusa da na nesa. Ammah da kanta ta kira Ummin ikki ta faɗa mata Baffa lokaci ya yi. Su Adda Suwaiba ne kaɗai suka riga ta zuwa sai liman sai gata tare da su Baɗɗo da babansu. Ammah falonta ta koma aka bar ma mazan nan ɗakin Baffa. Su Hamma Jibo haka suka ji mutuwar Baffa kamar saukan aradu kowa ma sai ya ce wai ya yi ciwo ne.? A ce ba ciwo ajali ne ya yi kira. Su Umma Balki suma hankalinsu a tashe suka ce yanzu za su kamo hanya. Lamiɗo kuma Abdullahi ya kira shi bai same shi ba sai ya tura masa sako Kafin ya ga sakon Hamma Kabiru da ya ji labari ya kira shi shidda da mintina Hamsin na safe ya faɗa masa A lokacin ya dawo daga masallaci kenan ya kwanta gefen Ummu Salma da yake yau an yi wa'azi a masallacin ya tsaya ya saurara. Lokacin da Hamma Kabiru ke faɗa masa Babu Baffa sai da ya ji jiri ya kwashe shi. Tsam ya tashi daga kan gadon ya mike ya fita falo. Mutuwan ta girgiza shi Baffan da suka yi magana da shi jiya lafiyan shi ƙalau. Ammah kawai yake tunawa daga ita sai Ummu Salama sai Mami waɗanan ukun ya za su ji yau in suka tabbatar da Babu Baffa. Tashin hankalin shi yadda zai faɗa ma Ummu Salma babu Baffa. Ga ta da ciki tana da B.P. Kansa ya dafe yana kiran sunan Allah. Wayarsa ya shiga ya nema musu jirgi, har ya amince ma Ummu Salma za su fara biyawa ta Abuja kafin su sauka Adamawa. Sai ga shi komai ya sauya daman bai nema musu ticket ba. Nan take ya shiga ya nema musu jirgi kuma an yi sa'a akwai wanda zai tashi zuwa Adamawa takwas na safe Sai bayan ya yi booking sannan ya kira wayar Mai martaba bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka bayan gaisuwa ya shaida masa halin da ake ciki. "Allahu Akbar." Mai martaba ya ja kabbara sau uku. "Allah ya jiƙan Hadi. Ubangiji ya kyautata makwancinsa." Tambaya ya yi ƙarfe nawa ne za a yi janaizar? Ya ce sai ya kira ya tabbatar zai faɗa masa. Mai martaba ya ce to ya kira shi ya faɗa masa yanzu zai sa a shirya tagawa za su taho in sha Allahu. Mai martaba ne ya kira Fulani a waya ya sanar da ita tana ta salati nan ma Masarautar tuni labari ya kai ma kowa, Saleem kuma ya shiga group ɗinsu na iyalan Mai martaba ya sanar cewa kawun Yarima Yayar mahaifiyarsa kuma mariƙinsa sannan uban matarsa Allah ya yi masa rasuwa jiya da daddare. Gimbiya Hadiza ta fara kiran Bilkisu ta faɗa mata rasuwan Baffa ta ji mutuwan nan sosai domin wani abu bai taba shiga tsakaninta da Baffa ba sai alherinsa. Da ta kira Lamiɗo yana waya lokacin da Abdullahi yana jin lokacin da za a yi Jana'iza ya ce sun saka sha ɗaya na safe. Saboda yan nesa su ƙariso, ya ce Ummu Salma ta yi nesa da wayarta tunda duk sun fitar da sanarwan a kafafen sada zumunta Lamiɗo ya ba shi tabbacin zai hana ta ɗaukan wayarta har sai sun iso. Sai da suka gama waya ne ya kira Bilkisu Ta tambaye shi ya tabbatar mata. Nan take ta ce za ta nema musu ticket ita da yara itama za ta taho ya ce suma yanzu shiri za su yi jana'izar ƙarfe sha ɗaya na safe. "Ciwo ya yi ne Ranka ya daɗe? "Lafiyan ƙalau jiya ma mun yi magana da shi." "Allah ya jiƙan shi." Ya amsa da Amin suka yi shuru. "Ummu Salma ta sani? "Ban faɗa mata ba." "Kar ka faɗa mata akwai hatsari." Ya amsa da toh, ta na faɗa masa ya bari in sun je can kawai ya ce haka yake tunani. Ba su daɗe suna wayar ba suka yi sallama da cewa sai sun haɗu a can duk da ba ta son Ummu Salma amma Baffa bai yi mata komai ba ta ji mutuwarsa sannan ta tausaya ma Umma Salma ta san yadda take son Baffan nan na ta sosai. Mami kuma tana cikin barci wayar Daddy ya tashe ta. Tunda ta ji ya fara cewa za ta je Adamawa a yau yau ɗin nan da safe nan ta watsake. Ta san ba lafiya ta ce koma me ya faru kawai ya faɗa mata ita ba yarinya ba ce za ta iya kula da kanta. Lokacin da ya faɗa mata Baffa ne ya rasu ya yi mamakin ƙarfin halinta Mami ta yi shuru kamar a mafarki. "Allah ya jiƙan Baffa. Allah ya yi masa rahama." Tausayinta ya kama shi ya ji takaicin ba ya kusa. Nan take ya ce ta nemi mota su taho Abuja ya duba babu jirgin da zai taho Abuja zai nema musu jirgin da za su tafi Adamawa daga can Abujan. Ta ce shike nan bari su shirya. Received [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Zama ta yi a ɗaki ta sha kukanta tun shekaranjiya take jin jikinta ba daɗi ashe maraniya za ta zama jiya ne kawai ba su yi magana da Baffa a waya ba. Lafiyan shi lau bai yi ciwo ba amma ajali ya kira shi. Data ta buɗe tana ganin hotunan Baffa da R.I.P a jiki sai ta ji kawai ta sake fashewa da kuka. Status ɗin Hamma Abdulrrahaman ya fi karya mata zuciya. "Allah ya yi ma mahaifina Alhaji Hadi Baba Rasuwa a jiya da daddare za a yi jana'izar sa yau da misalin sha ɗaya na safiyar ranar talata a gidansa dake anguwan Zone3 a garin Jimeta Adamawa." "Ku yi masa addu'a. Ku nema ma mahaifina gafara." Ba hoto ya saka ba rubutu ne amma gabaɗaya jikinta ya saki. Tana kuka ta fita ta yi magana da Barira. Tare za su tafi tunda ba ta san yaushe za su dawo ba lokacin da Barira ta ji Baffa ne ya rasu itama ta yi kuka sosai, Islaam ma kuka share shere Faruk har yana birgima ko wanka ba su tsaya sun yi ba, ballatana maganar abinci. Mami ta kira Hajiya Falmata a waya ta faɗa mata. Ta tausaya mata domin ta san a duniya Mami ba ta da kowa sama da Baffa nan ta yi mata gaisuwa ta ce kafin a yi uku za ta taho. Rufe gidan suka yi karfe bakwai da wasu mintina Hamisu ya kwashe su a baƙar pradon ɗin Dadduy suka ɗau hanyar Abuja. Mami tana idanuwanta sun tasa muryanta har ta dishe ta umarci Hamisu da ya yi gudu sosai shi yasa cikin awa biyu da wani abu suka isa Abuja. Har suka isa Abuja Mami kuka take yi, a filin jirgin suka haɗu da Daddy ashe jirgi ɗaya za su hau zuwa Adamawa tare da Hamma Jibo da iyalansa. Jirgin karfe goma ne, A Airport Daddy ya rumgume Mami tana ta kuka yana lallashinta Hamma Jibo bai yi kuka ba amma duk ya yi zururu. Adda Nauwara ma da su Saudat ɗin kukan suke yi Allahu akbar rai baƙon duniya. Sai da jirginsu ya ɗaga sannan Hamisu ya baro Airport ɗin ya kama hanyar komawa Kaduna. * Ƙarfe goma da mintina arba'in da takwas su Mami suka iso Adamawa. Tashar Napep biyu suka yi zuwa gida. Tun daga farkon layin motoci ne sun cika ga jama'a. Mai martaba ya iso tun wajen goma tare da Tawagan wakilan Fada, da Saleem da Fulani tare kuma da Gimbiya Shahida da Gimbiya Amratu. Bilkisu ma ta iso tare da su Sultan da su Sabuwa. Hamma Mustpha ya iso haka ma Hamma Kabiru. Mutanen Mubi motoci uku sun iso, daman su Mami ne sai su Lamiɗo ba su taho ba. Tuni har an yi ma Baffa wanka an haɗa shi sannan an je makabarta an yi hakan kabari Baffa Umaru ne da su Hamma Mustapha da Hamma Abdulrrahanman da Abudullahi suka yi masa wanka. Cikin gida tun daga haraba har cikin ɗakuna cike yake da jama'a kama daga yan'uwa da mutanen anguwa. Ammah na zaune a falonta da Hijabi Ummin ikki na gefenta tare da su Umma Balki. Kowa da Hijabi a jikinsu masu kuka na yi masu share hawaye na yi. Zuwan Mami ya rikita falon domin zubewa ta yi a jikin Ammah tana gunjin kuka su Umma Balki ne ke ba ta baki. "Baffa ya tafi ya bar ni, ni ba marainiya ba ce a baya amma yanzu na zama marainiya." Har tsakar gida ana jin ihunta. Mai Martaba na cikin ɗakin Baffa tare da su Baffa Umaru da su Hamma Mustapha. Yau ga Mai martaba ga Batula sun haɗu bayan shafe shekaru sama da talatin amma haɗuwar ba ta zama mai daɗi ba. Yana kallonta cikin rawaninsa cikin tausayinta lokacin da ya yi mata gani na ƙarshe tana kuka yanzu ma da ya sake haɗuwa da ita cikin kuka ne Ƙirjinsa ya dinga suya, yana so ya lallasheta amma kuma ba shi da wannan hurumin yana gani Daddy ya riƙe mata kafaɗu yana lallashinta wanda suka shigo ɗakin tare da su Hamma Jibo. Gabaɗayansu sun zagaye gawan Baffa suna ta yi masa addu'a da fatan dacewa Allahu akbar ga Baffa kwance ba ya motsi. Jiya fa lafiyan shi ƙalau amma yau ba ya raye. Duniya zencen banza Ubangiji ya sa mu gama lafiya. Hamma Lamiɗo ake jira da Ummu Salma su kuma sun samu tsaikon jirgi ne sai ƙarfe goma sauran jirgin su ya tashi. Duk da Umma Salma ba ta sani ba. Amma ta ji a jikinta wani abu mara daɗi na faruwa tun da tashi da safe take jin ta wani iri kamar mara lafiya sukuku ba ta da kuzari. [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Barcin da ta koma bayan sallar asuba ta yi wani mafarki ta ga gidansu cike da jama'a ta ga kowa da kowa har mutanen Mubi amma ba ta ga Baffa ba kuma ta kasa faɗa ma Lamiɗo mafarkin da ta yi amma tunda ta farka zuciyarta duk ba daɗi hankalinta duk ya koma gida. Lamiɗo ya yi dubaran ya ɗauke wayarta ya kashe ba tare da ta sani ba, halin da take ciki ne ya sa ba ta ma nemi wayar ba, ba ta cikin yanayi mai daɗi Ko karyawa ba su tsaya sun yi ba ya ce in suka isa can za su karya. Da shi da Ummu Salma da Hanan da Harira. James da Baban Adila ya sallame su, rufe gidan za su yi suma su tafi garuruwansu hutun kirisimeti da sabuwar shekara. Ummu Salma ko a cikin jirgi sukuku take har Lamiɗo ya ji tsoron ko ta sani ne? Sai dai daga baya ya fahimci yanayin. Yanayin da mutum zai ji a jikinsa in ya rasa wani abu mai muhimmanci ko da ba a faɗa masa a lokacin ba zai ji a jikinsa. Da suka sauka a filin jirgi ta ga ba a zo ɗaukan su ba. Tun daga nan ta san wani abu na faruwa a gida. Hamma Lamiɗo shima wani iri take ganin shi ya ginsheƙe fuska ba ya son ma ta yi masa tambaya amma yana riƙe da hannunta kamar za ta gudun masa. Suma Napep ɗin suka yi tasha zuwa gida. Ta tabbatar da zarginta da yanayinta tun lokacin da suka doso anguwan su ta ga layin su cike da motoci. Tun daga lokacin ta san wani abu ya faru. "Hamma " Ta kira sunan shi cikin wani rauni tana mai kallon shi lokaci ɗaya tana rike hannuwansa. "Me ya faru ne? "Ya na ga mutane sun cika ƙofar gidanmu." Mutuwa aka yi haka zuciyarta ke faɗa mata? Domin taron mutane dalili biyu ke kawo su lokacin farinciki ko lokacin baƙin ciki. Na baƙin cikin take zargi domin in na farinciki ne za ta ji labari. Zuciyanta na rawa. Waye ya rasu? Har ta fara hawaye, me ya faru? Wa ye ya rasu. Ba ta son ta kawo lissafin ma waye ya rasu ɗin ji take yi kamar za ta haukace a lokacin saboda tashin hankali da fargaba. Rumgumeta kawai ya yi yana lallashinta Harira ma duk a firgice take tunda ta ga tarin mutane ta san ba lafiya suna sauka get ɗin a wangale yake haraban gidan ma ga mutane nan suna ta alwala. Sannan ta ga dogarai da masu kaki sun taso suna yi ma yarima barka da zuwa. Ta ga Hamma Saddam idanuwansa jajir shi da Hamma Abdulrahim. Fuskokin mutane take dubawa tana neman Baffa amma ba ta gan shi ba. Tana kokarin ƙwace hannunta Lamiɗo ya hana ta Harira na ɗauke da Hanan, daman ba su ɗauko kaya ba akwati ɗaya ne da jaka. Lamiɗo bai saki hannun Ummu Salma ba har cikin gida, Baɗɗo da su Adda Suwaiba duk suna tsakar gida zazzaune da Hijabai ita ce tana ganin su ta taso, ita ya miƙa ma Ummu Salma yana kallonta. "Ki yi haƙuri " "Allah ya jiƙan Baffa." Ya faɗa yana yana runtse hannun Ummu Salma cikin na shi. Sannan ya miƙa ma Baɗɗo hannun nata. "Please take care of her." Ko bai faɗa ma ta san Baffa ne ya rasu a cikin taron mutanen da ta gani tun daga waje ba ta ga Baffa, in kuma yana nan to da tabbas shi za ta fara gani a haraba tantama take yi shin da gaske Baffan ne ya rasu? ƙafafunta suka fara rawa ta damƙe hannayen Baɗɗo hawaye na yi mata ambaliya. Baffan ne ya rasu? To in ba Baffa ba waye zai rasun da kowa da kowa zai zo. Ina Ammah? Zuciyanta ta harba, ta yi tsalle ji take yi kamar ta buɗe idanuwana ta ga komai mafarki ne. Hamma Kabiru ne ya fito suka yi musabaha da Lamiɗo sannan suka nufi ɗakin da gawar Baffa ke ciki. Ganin sun nufi ɗakin Baffa ga takalma nan masu yawa a ƙofar ɗakin daga nan ta ji kafafunta na rinjayanta. Amma ta kasa bin unarninsu, ba ta ga Baffa ba sannan ba ta ga Ammah ba tabbas wani cikin su ne ya rasu yau. Ummu Salma ta kasa zama tuni ta saki jakar hannunta haka ma takalmin kafarta Adda Suwaiba ta tattara mata su duka ta rumgume suma kuka suke yi ba mai ba ma wani hakuri, suna tuna jiya fa har da shi a masu yi musu rakiya. Umnu Salma ba ta ma sanin in da take jefa kafafunta Baɗɗo na rike da ita, itama hawayen take yi. Falon Ammah ta shiga, tunda ta ga Ammah zaune gefenta su Umma Balki da Hijabai Ta kai kallonta kan yan'uwansu na Mubi matayen su Baffa Umaru suna ta kuka. Received at 09:16Reactions: ❤ 12, 😭 2, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta hango Mami a jikin Umma Balki tana ta kuka. Tabbas Baffa ya rasu ta yarda tunda ta ga Ammah ta ga kowa ban da Baffa. Ba domin Baɗɗo ba da faɗi za ta yi ita ce ta tare ta sai ta kasa shiga ɗakin ta juya Baɗɗo na rike ta suka fito tsarkar gida ba ta gani ma sosai ɗan cikinta ya dunƙule waje ɗaya jiri ma take gani ta zame nan samar tabarma ta zauna tana saka fuskanta a cikin tafukan hannayenta ta saki wani marayan kuka. Baɗɗo ta zauna a gefenta ta rumgumeta tana lallashinta itama kukan take yi. "Baɗɗo Baffa." "Baffa." Take faɗa tana wani gunjin kuka. Hankalin kowa ya koma kanta. "Ki daina kuka ki yi masa addu'a." "Jiya fa mu ka gama waya da shi." "Wayyo Allah Baffa." Kuka har da ƙaraji daidai lokacin da su Hamma Jibo suka fito shi ya shiga falon Ammah ya ce ita da Mami su taho su yi ma Baffa bankwana za a fita da shi a yi masa salla. Ammah ta miƙe Ummin ikki na rike da ita tare da Gimbiya Shahida da su Fulani. Umma Balki ta riƙe Mami tare da su Umma A'i. Suka fito Ummu Salma kuma Hamma Jibo da kanshi ya riketa ta miƙe suka tafi ɗakin Baɗɗo ta rufa masa baya. Su Baffa Umaru duk sun fito, wasu suna ta cewa za su shiga ana cewa in iyalansa sun gama sai su shiga su yi masa addu'a. Duka ya'yan Baffa har da Lamiɗo da Mai martaba da su Fulani sai Hamma Jibo ya leƙa yace su Adda Suwaiba su shigo tare da su Saudat masu hankali. Haka ya'ya da jikoki suka zagaye gawan Baffa. An fara koke koke liman ya tsawarta. Ya ce a yi masa addu'a babu kyau ka tasa mamaci kana yi masa kuka. Kowa kukan zucci wasu kukan na fidda sauti. Mami kuka har da majina ta kamkame Baffa tana kuka. "Baffa me ya sa ka tafi ka bar ni? "Lokacin da na rasa su Gwaggo ban yi kukan maraici ba saboda ina dakai, me ya sa za ka tafi ka bar ni? Duk wanda ke ɗakin nan ya tausaya ma Mami, da Umma Salma itama kamar za ta shiɗe sai da Lamiɗo ya riketa har Bilkisu tana ɗakin itama har hawaye sai dai ta yi ba mutuwar wani kake yi ma kuka ba, taka mutuwar kake yi ma kuka. Ammah ce ta ba ma kowa mamaki ba ta yi kuka ba. Amma har Hamma Jibo ya yi hawaye. Su Saddam kamar mata kuka share share. "Allah ya jiƙan ka Baffa. Tun zamana da kai ba ka taɓa mugunta mini ba. In ma ka yi a cikin kuskure na yafe maka, baƙin cikina ɗaya da ka koma ga Allah ban nemi gafaranka ba." "Allah ya jikanka. Ubangiji ya sada ka da rahamarsa. Allah ya haskaka makwancinka ayyukan ka na alheri ya bi ka har kabarin ka. Na gode Na gode Alhamdulillah." Daga nan kawai ta tashi ta fita, ta bar su Ummu Salma ta shesaheƙa. Sha ɗaya har ta gota da mintina sha biyar mutane na ta jira a waje. Lokacin da za a fita da gawar Baffa Mami ta ƙamƙame makaran har tsakar gida tana kuka. Ummu Salma kuma Gimbiya Shahida ta karɓeta daga Hannun Lamiɗo ta hana ta fita ta zaunar da ita ga ciki a jikinta kar ta miƙe ta faɗi. Dakyar aka samu aka ɓambare hannun Mami daga makara aka fita da Baffa daga gidan duk matan sun miƙe tsaye masu kuka na yi da masu hawaye. "Allah ya jikan ka." "Allah ya sada ka da mala'inkun rahama." Hamma Jibo ya dawo yana faɗin a cikin mata waɗanda za su yi jana'iza su yi alwala su fito. Anan ƙofar gida za a yi masa salla. Kowa ko ya tashi yana neman ruwa domin alwala wasu kuma daman da alwalansu. Sai ga shi yau Fulani ce ke ta lallashin Mami tana ba ta baki. Har ta daina kuka da murya sai hawaye. Ta ce in za ta iya ta yi akwala ta sallaci gawan ɗan'uwanta ta ce za ta iya. Ammah ko kowa mamakinta yake yi ta dake ta yi jarumta tuni har ta yi alwala ta fita tare da su Ummin ikki. Ummu Salma ma ta ce za ta iya. A ɗakin Ammah ta je ta yi alwala ta saka hijabi a saman doguwar rigar jikinta su Adda Suwaiba daman da alwalan su. Rabin matan dake gidan sun fita sun sallaci gawan Baffa. Maza na gaba da tazaran taku goma haka matan suka kafa sahu a bayan su. Baffa ya yi jama'a Ubangiji ya bamu irin tashi. Limamamin masallacin da Baffa ke salla me ya yi masa salla. Mutane maza da mata suka sallace shi, akwai Mai Martaba sarkin Daura tare da Waziri da Shamaki. Akwai wakilan Gwamman jahar Adamawa tunda tawagan Gwamnan ne suka zo filin jirgi suka ɗauke su. Ga zaratan yaran Baffa kaf ɗin su. Received at 09:16 11 people reacted with ❤ [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ga yan anguwa abokan kasuwanci da waɗanda ma ba a yi tunanin zuwan su ba. Cikin su kuwa har da Habib tsohon mijin Ummu Salma a cikin dubban mutanen da suka sallaci gawan Baffa. Makabarta da ɗan tafiya amma a ƙasa aka ɗau hanya. Shike nan an yi an gama. Mata suka koma cikin gida suna kuka Mami a haraba ta faɗi a sume aka ciccibeta zuwa cikin gida aka watsa mata ruwa ta farfaɗo tana ta kuka gwanin ban tausayi. Ammah na zaune kanta a sunkuye ta kasa kuka amma zuciyarta na ɗaci tana jin kamar itama za ta iya bin Baffa saboda halin da take ciii. Ummu Salma kuma Gimbiya Shahida da Baɗɗo na kafa kafa da ita, suna riƙe da ita kar su saketa ta faɗi domin sai layi take yi kamar ma ba ta iya tsayuwa da kafafunta hawaye kawai ke fita babu sautin kuka. Cikin gida suka koma a falon Ammah suka zaunar da ita. Gida ya cika danƙam da jama'a ana ta koke koke. Ubangiji ya sa mu yi kyakyawan ƙarshe. *Janafty* Received at 09:16Reactions: 😭 34, ❤ 8, 😢 7 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. Lokacin da za a sanya gawar Baffa a cikin Kabari aka ce ƴa'ƴansa su haɗa hannu wajen saka shi Hamma Abdullahi ƙasawa ya yi saboda hawaye da majina haka suke zuba masa, Saddam da Abdulrahim ma sun kasa suna dai tsaye suna kukan zucci da hawaye. Hamma Jibo ne da Hamma Mustapha sai Lamiɗo sai Hamma Kabiru da Hamma Abdulrahaman suka haɗa hannuwa suka zura shi a cikin kabarin shi. Allahu Akbar bawa ba a bakin komai yake ba, duk abin da ka mallaka in ka mutu daga kai sai farin likkafani za a zuraka a cikin ƙasa a toshe ko wata ƙafa. Ya illahi Ubangiji ka datar damu duniya da lahira. Wajen toshe kabarin da kasa ne har da Mai martaba ya saka hannu, suna ji suna gani aka rufe Baffa ruf sannan duk in da aka hango iska sai an toshe shi bayan an gama jera itace an rufe ko'ina sannan aka rufe shi da ƙasa. Kafin a watse a maƙabarta liman sai da ya yi nasiha ya jawo hankalin mutane a game da mutuwa. "Jama'a mu ji tsoron Allah a dukkan ayyukanmu mu dinga tunawa da cewa wata rana za mu mutu, mutuwa ba ta ƙwanƙwansa ƙofa ba ta neman izini kada mu shagala mu yi tunanin cewa ai muna da sauran lokaci ko mu yi tunanin tsoffafi ke mutuwa ni ina da ƙaruciya ba yanzu zan mutu ba ko mu dinga tunanin ina aikata zunubai amma kafin na mutu zan tuba to ya kamata mu farka mutuwa ba ta zaɓa da lokacin ka ya ƙare a duniya za ka tafi ko kana so ko ba ka so. Tana ɗaukan jariri ta bar uwa tana ɗaukan uwa ta bar jariri tana ɗaukan uba ta bar ɗa, tana ɗaukan uwa ta bar uba, tana ɗaukan tsoffi ta bar yara matasa sannan tana ɗaukan matasa ta bar tsoffin abin da zamu gane shi ne mutuwa tana tare damu aduk in da muke, wataƙila a cikin mu ɗin nan akwai wanda ba zai wayi gari ba, wani ma ba zai kai anjuma ba, duk wannan na Allah ne abin buƙata kawai mu dinga tuna mutuwa mu kuma ribanci kyakyawan ayyuka, ku duba wannan bawan Allah jiya har sallar isha'i tare da shi muka yi a masallaci yau da asuba da ɗan wajensa ya zo yana faɗa mini rasuwarsa kamar zan ce me ya sa me shi? Sai na tuna ajali ko ba ciwon in ya yi kira sai an tafi. Ƴaƴansa sun ba ni tabbacin har wajen sha biyun dare suna tare da shi suna hira sun koma gidajensu sun kwanta da asuba aka kira su, suna zuwa gida ba su same shi da rai ba. Abin lura anan jiya lafiyan shi lau a cikin iyalan shi bai san yau ba zai wayi gari ba Ajali ya yi kira Ubangiji ya yi ikonsa. Ina mai baku tabbacin Alhaji Hadi mutumin kirki ne salla akan lokaci ba ya wucesa tare da iyalansa. Sannan yana da daraja mutane da sannin haƙƙin zaman tare, Ubangiji Allah ya gafarta masa, tashi ta ƙare mu kaɗai ne yanzu muke da kaico, mun dai ga in da ake saka duk wanda ya rasu a cikin ƙasa daga kai sai halin ka, guzirin mu shi ne kyakyawan ayyuka da nisanta kanmu da aikata zunuban da Ubangiji ba ya so. Jama'a mu ji tsoron Allah mutuwa ta zame mana wa'azi." Kowa a makabarta jikinsa ya yi sanyi. "Mu tuba da wuri tun kafin lokaci ya kure mana. Ba mu san yaushe ne za mu mutu ba amma tabbas mutuwa tana tare damu, yau in ka raka abokinka watarana wasu ne za su rako ka, yau in ka raka babanka watarana wasu ne za su raka ka, haka rayuwar za ta tafi tun kana zuwa raka wasu kai ma watarana kai ne tun muna jin labarin mutuwar wasu muma watarana tamu mutuwar za a ji. Ubangiji ka sa mu yi kyakyawam ƙarshe." Aka amsa da Amin jikin kowa a sanyaye Nan ya ce za a yi addu'a. Ya yi addu'a sosai daga karshe ya rufe da cewa " Allah ya jiƙan Alhaji Hadi. Allah ya sada shi da mala'ikun rahama. Ubangiji ya haskaka kabarin shi ka ba shi ikon amsa tambayan kabari ka sanya shi cikin amimcinka. Allah ya yafe masa kurakuransa Allah ya ba mu sa'a gabaɗaya." Aka sake amsa da Amin Amin gabaɗaya. Received at 09:59Reactions: ❤ 4, 😭 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Kowa ka gani jiki a sanyaye wasu na kuka wasu na jimami a cikin masu jimanin har da Habib da yake can baya ya sunkuyar da kai har ƙwalla ya yi Ubangiji yana son shi da ya ba shi ikon tuba tun kafin ya mutu. Ko bai sunkuyar da kai ba, ba ma lalle ba ne ahalin Ummu Salma su gane shi ba saboda wahalan rayuwa sannan a halin da iyalan Baffa ke ciki ba ta kan shi za su bi ba. Yana cikin tawagan mutanen da suka bar maƙabarta iyalan Baffa kaɗai aka bari sai Mai Martaba da wakilan fada dare da sauran dogarai. Habib ya tafi yana waiwayan Lamiɗo, daga nesa ne kawai sai da ƙwarjininsa ya dake shi. Duka duka sau ɗaya ya taɓa ganin shi Zahiri  tun kafin auren su da Ummu Salma amma yana ganin shi a hoto in Hamma Kabiru ya saka shi Ummu Salma kan nuna masa. Duk da ya sauya kuɗi da mulki suna nuna kansu a ganin farko ma in ka yi masa. Ya tafi yana hawaye, hawayen nadama da tausayin kanshi, ruɗin duniya da sheɗan sun ruɗe shi ya rasa Ummu Salma rashi na har abada. A wajen makabarta ya haɗu da Sani suka gaisa ya yi masa godiya. Domin ya taimakesa da ya kira shi ya faɗa masa rasuwar Baffa ko ba komai ya samu jana'izarsa amma yana cikin jimamin har Baffa ya koma ga Allah bai nemi gafaran shi ba domin ya san cewa tabbas ya kuntata masa bisa ga abubuwan da ya yi ma Ummu Salma. Yana tafe a hanya yana istigafari da neman yafiyar Ubangiji. A can maƙabarta kuwa dukkansu suna duƙe a gaban kabarin Baffa da Hamma Jibo ya ɗan saka wani alama na katako a wajen yadda ko da watarana ziyara ya kama su za su iya gane kabarin Baffa. Duk da ana mutuwa sosai a lokacin ma kaburbura wajen biyu aka haƙa a gefen na Baffa. A rana ba wanda ya san adadin mutane nawa suke mutuwa. Addu'o'i suke ta yi ma Baffa domin a lokacin da sahun ƙarshe ya ɗaga kafarsa mala'inkun tambaya za su sauka fatan su Allah ya ba shi ikon amsa dukkan tambayoyi. Hamma Abdullahi ya kasa daina kuka hawayensa suna ɗiga a saman kabarin Baffa shi da Abdulrahim shi ko Saddam jiri ne ya ɗebe shi lokacin da ya miƙe sai da Hamma Abdulrahaman ya kama shi ya ce ya koma gefe tunda ba zai iya daurewa ba. Hamma Jibo da Hamma Mustpha sun yi jarumta sosai idanuwansu ne dai suka kaɗa suka yi jajir amma ba su yi kuka ba haka ma Hamma Kabiru da Hamma Abdulrrahaman, Lamiɗo ma ba a gane yanayinsa duk sune masu dauriyan. Baffa Umaru da Baffa Salihu  sun kasa daurewa suma hawayen suke yi haka ma Daddy sai da ya share hawayensa da wani farin hanky Mai martaba kuma ba a gane yanayinsa tunda yana cikin rawaninsa ne Saleem na gefe jikisa duk ya yi sanyi ga sauran yaran su Baffa Umaru maza da suka taho daga Mubi wasu na hawaye wasu na sharɓan kuka domin Baffa na kowa ne mai barkwanci ga zumunci da son ƴan'uwa. Sai da za su bar maƙabarta sannan Hamma Jibo ya juya ya kalli kabarin Baffa sannan hawaye suka kawo masa bai share su ba ya barsu suna ta faman zuba kamar famfo. "Allah ya jiƙan ka Baffa." "Allah ya gafarta maka Hadi. Allah ya sadaka da amincinsa." Baffa Umaru ya faɗa yana hawaye. "Sai mun zo Hadi Ubangiji ya karɓi baƙuncin ka." Baffa Salihu ya faɗa shima yana ɗauke hawayensa. Kamar ba za su tafi ba, sai dai ya zama dole suna tafe suna waige, shike nan an yi an gama sun tafi sun bar Baffa a in da yake a halin yanzu nan ne gidansa na gaskiya gidan kowa ma na gaskiya. Haka suke tafe tun daga maƙabatarta har gida ba wanda ya yi ma wani magana. Kowa na fama da raɗadin zucci. Hamma Saddam sai da Abdulrahim ya riƙe shi ya ce jiri ma yake gani hawaye suke yi har suka dawo gida. Cikin gida Hamma Jibo ya shiga yana maganar a ɗauko manya tabarmu da cafet saboda masu zaman gaisuwa a waje. Adda Suwaiba ce ta ɗauko manyan tabarmun Ammah guda biyu sai kuma cafet. Suna da shi a gidajen su, sai Hamma Abdulrahim ya je gidan shi ya ɗauko na su tabarmun da cafet duk aka ba za a haraban gidan aka zazzauna ana karɓan gaisuwa. Mata kuma in sun zo bayan sun yi gaisuwansu a waje cikin gida suke shiga su yi gaisuwan su. Received at 09:59Reactions: ❤ 8, 😭 4, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby A ɗakin Ammah, Mami take zaune tare da Ammah da su Ummin ikki tare da su Umma Balki, sai ga Fulani zaune a gefen Mami tana ta ba ta baki da lallashi domin tun bayan da ta farfaɗo take gunjin kuka mai ban tausayi Fulani na tunsar da ita da cewa ta daina kuka ta yi masa addu'a. Gimbiya Shahida kuma na gefen Ammah zaune tare da Ummin ikki sai Bilkisu. kowa mamakin Ammah yake yi ba ta kuka kuma duk wanda ya yi mata gaisuwa za ta amsa tana sanye da hijabi da casbaha a hannunta amma kallo ɗaya za ka yi mata ka jinjina ma raɗadin da ke ji a zuciyanta. Ummu Salma kuma da su Baɗɗo suna ɗakin Baffa tare da su Adda Suwaiba. Sauran mutanen Mubi kuma suna tsakar gida wasu daga cikin iyalan su Umma Balki da sai bayan an yi jana'iza suka iso suna cikin ɗakunan barcin Ammah da na Ummu Salma, wasu kuma suna cikin ɗakin tsakar gida. Ana zazzaune ana ta amsa gaisuwa an yi jugum jugum, kowa ka gani fuska a koɗe gwanin ban tsausayi. Baɗɗo na gefen Umma Salma ba ta barta ba, domin Gimbiya  Shahida ta ce a zauna tare da ita a kula da yanayinta. Tun bayan da aka fita da gawan Baffa Ummu Salma ta ji kanta ya yi wani irin sarawa, ta ji kamar an ɗora mata wani ƙaton dutse a saman kanta sara mata yake yi irin sarawar da ba ta taba jin irin shi ba. Ita dai tana biye da duk wanda ya riketa ne duk in da aka bi da ita can take zuwa. Tana zaune ne hawayenta sun ki tsayawa. Wani irin abu ne mai zafi da maƙaƙi ya tokare mata a zuciyarta da kirjinta ba ta taɓa jin abu mai zafi irin shi ba ko lokacin da Habib ya saketa ba ta ji irin haka ba wannan abun ya ninka abin da ta ji a wancan lokacin sau dubu Tantama take yi tana shakkun cewa wai yau ba Baffa? Jiya fa sun yi magana da shi ashe ashe Allah ya yanke ganawarsu gani take yi kamar a mafarki gani take yi kamar a ce ta farka ta ga komai bai faru ba. Ta ga lokacin da aka tafi da gawan Baffa daga lokacin ta ji komai ya tsaya mata duniyar ta tsaya mata cak ba ta jin daɗin komai bakinta ya yi wani takaf ɗaci daci ma take ji jikinta ya yi mata nauyi, cikin jikinta ya dunƙule a waje ɗaya maranta ya ɗaure haƙoranta na karo da junansu tana jin kamar jikinta na kamewa a waje ɗaya Baffa zai dawo wasa ne bai mutu ba haka take gani amma in aka shigo yi musu gaisuwa ta ji ana cewa Allah ya jikansa sai ta ji kukanta ya ƙaru da gasken kenan babu Baffa yanzu shike nan ya tafi ya bar su. Ta jima tana jin labarin irin raɗaɗin rashin wani na kusa dakai, ita da ta tashi uba ta rasa a lokacin da ba ta taɓa kawo masa mutuwa ba ko a mafarki ko a hasashe ta yi hasahen rasa Ammah ko Baffa sai zuciyarta ta ƙuntata ta ji labarin ɗacin mutuwa ita sai yau ta ɗanɗani wannan ɗacin ta sha jin waɗanda aka yi ma rashin irin ta uwa ko uba suna faɗin har abada ba za su taɓ mantawa ba yau itama wannan rashin ya risketa tana jin itama har ta koma ga Allah ba za ta daina kuka ba har abada ba za ta ƙara dariya ko wani farinciki ba tana ganin farincikinta ya ƙare tunda ta rasa Baffa. Baƙi suna ta zuwa maza da mata, wasu daga can Mubi ne wasu iyalan su Baffa Umari ne da su Umma Balki mata da maza dake can wasu garuruwan suna aiki sai gida ya sake kacamewa da koke koke ba yadda za a yi domin Baffa ya rasu ba kuma zai taɓa dawowa ba. Har bayan azahar ba wanda ya sha ko ruwa a cikin waɗanda mutuwa ta shafa sai dai wasu na can gefen da ba su damu da mutuwar ba, domin sun ma kafa dandalin hira ne ba ko nuna jimami ga waɗanda aka yi ma wannan rashib, wasu ma sun fara ƙorafin su yunwa suke ji wasu ma wayarsu suke dannawa. Shi gidan mutuwa kaɗan ne daga ciki ke cikin jimami da ka mutu an kai ka an binneka shike nan taka ta ƙare sai iyalanka ne za su jima suna kukan rashinka. Sai da duk aka yi salla sannan Ammah ta yi magana da Adda Nauwara tunda ita ce Babba ta ce su dafa abinci ko saboda yara. Su kansu sun san an yi mutuwa sun natsu a waje ɗaya. Harira na tare da su Sabuwa yaran kuma duk suna tare da su. Sultan da shi aka je makabarta tare da sauran yaran su Hamma Jibo suna can haraba tare da iyayensu wajen zaman gaisuwa. Received at 09:59Reactions: ❤ 13, 😭 4 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Adda Nauwara ta fito ta yi ma Adda Suwaiba magana suka tattara kansu surukan gidan suka yi maganar ɗora abinci , duk da ma daga maƙota duk an fara kawo abincin wasu har sun fara wawaso, wato yanzu gidan mutuwa ya koma gidan da ake ci a sha, barin ma in a ka ga gidan akwai maiƙo. Kayan abinci akwai su danƙam a store ɗin kitchen cefane ma akwai domin kwana uku da ya wuce Hamma Abdulrraham ya yi cefane. Suka ɗibo kayan miya suka gyara babban tukunyar Ammah mai lamba talatin suka ɗora a wani babban murhun gawayinta a tsakar gida gawayin ma akwai shi tunda lokacin bayan lokacin Ammah na amfani da shi. Wajen ukun rana suka gama abincin aka zuzzuba anan cikin gida sannan aka zuba aka fita da shi waje daman kuma an kawo katan katan na ruwan gora da lemu sama da katan hamsin a cikin gida bayan wanda aka sauke a waje an samu abin da ake so tuni gidan mutuwa ya koma gida cin abinci da kuma hira , ana ci ana hira ana korawa da lemun gora da ruwa. Yara dai duk an saka musu sun ci tunda su yara ne ba ma su san abin da ke faruwa ba. Waɗanda mutuwar ta shafa ko ruwa sun kasa kaiwa baki. Ko su Fulani ma sun kasa cin abinci ruwa kawai suka sha. Ammah ma ba ta ci ba, ba ma wanda ya yi mata magana ganin yanayinta Ummu Salma ce Baɗɗo ta matsa mata ta ci abinci sai dai kawai ta kalleta hawaye na kwaranyo mata. "Ba zan iya cin abinci ba Baɗɗo. Abinci ba zai wuce ba, bayan na san Baffa na cab cikin kabarinsa a yau ba zan iya ba." Ta sake fashewa da kuka, mutanen dake ɗakin suna ta ba ta baki amma ta kasa ci, wai ta ci saboda cikin jikinta ta ce ba za ta iya ba su ƙyaleta. Kukanta ya dawo saboda tana yi tana shessheƙa. Bayan la'asar Mai martaba za su koma tare da Fulani da Gimbiya Amratu za a bar Gimbiya Shahida da Saleem sai an yi addu'an uku za su koma Daura. Har cikin gida Mai martaba ya shigo sake yi ma Ammah gaisuwa da yin sallama. Hamma Jibo ne ya yi masa jagora. Mata suka dare sannan Mai martaba ya shigo tare da Waziri da shamaki dogarai suna dake a bakin ƙofar ɗakin Ammah ya shiga har ciki ya zauna a saman kujera. Ammah na gefe kanta na kasa su Umma Balki sun bar falon sai Mami ne kawai tare da su Gimbiya Shahida sai Ummin ikki da su Bilkisu Ya yi ma Ammah gaisuwa tare da ba ta haƙurin wannan rashin da suka yi gabaɗayansu tare da tausasan kalaman hakuri da cin wannan jarabawan "Allah ya jiƙan shi, Allah ya ba ku haƙurin rashi." "Amin ranka ya daɗe mun gode Ubangiji ya mayar daku gida lafiya." "Ammah Mai martaba ya ba da kuɗi masu yawa ya ce a siya kayan abinci da duk abin da za a nema a wajen zaman makokin nan" Hamma Jibo ya faɗa yana zaune daga gefen Ammah. "Allah ya ba da lada. Mun gode ranka ya daɗe." Bai amsa yana da cikin rawaninsa idanuwansa da wani farin gilashi ya kalli Mami da ta jingina da jikin kujera a rana ɗaya kawai ta wani faɗe kamar wacce wani cuta ya kamata. Kamar ma ba ta san abin da ke faruwa a falon ba hawayenta ne kawai ke zuba da motsin carbin hannunta. "Batula ya haƙurin mu? Mai martaba ya tambayeta yana mai kallonta ta cikin rawaninsa. Tana ji ashe ba ta ɗago ba amma bakinta ya yi motsi alamun ta amsa. "Allah ya jiƙan shi, Allah ya ba da haƙurin rashi." Ta amsa da Amin tana mai rufe bakinta da tafin hannunta guda ɗaya wani kuka ne ke ƙwace mata kawai sai ta kifa kanta a jikin kujera tana faman rerewa kukan da ya kashe ma duk wanda ke ɗakin jiki barin ma Mai martaba da ba ya son jin kukan Batula kukanta na tuna masa da shekaru talatin baya Ɗakin Ammah kawai suka shiga daganan suka fita ya ce sai ranar addu'an bakwai in ya samu dawowa in kuma bai dawo ba zai turo wakili shima nan da sati uku zai tafi ganin likita a ƙasar London. Tawagan wakilan Gwmnan Jahar Adamawa ne suka kwashe su zuwa fadar gwammati daga can za su wuce filin jirgi su koma Daura. Da gaske dai Baffa ya rasu, tun da ga shi har an yini an kwana Baffa ya yi kwanan kabari. Barci ko ɓarawo bai saci Ummu Salma ba haka Mami ma, kuka kawai take yi ba saurarawa. Ammah kuma kwana ta yi salla domon nema ma Baffa rahama da gafara a wajen ubangijinsa. Received at 09:59Reactions: ❤ 13, 😭 4 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Duk anan suka kwana har Bilkisu mazan kuma a can bangaren su Saddam da safen ne Hafiz da matarshi Salima suka iso ya ce a status ɗin Hamma Kabiru ya gani ashe ba rabon ganawarsu da Baffa a ranar ma mota biyu daga Mubi sun sake zuwa amma ba su kwana ba kama daga yan'uwan matan su Hamma Abdulrhaman tare da abokan ayyukansu duk sun taho gaisuwa gida ya sake cika danƙam Sannan abokan aikin su Hamma Jibo daga Abuja, Gombe Taraba duk sun taho gaisuwa. Kuma suna shigo da su cikin gida domin su yi ma su Ammah gaisuwa. Lamiɗo dai tun jiya bai sake shigowa ba gida cike da mata. Amma zuciyarsa da tunaninsa suna wajem Ummu Salma ne a daran ma ya kira Bilkisu a waya ya ce ta duba masa ita. Domin ya yi ta kiran wayarta ba a ɗauka ba ita ba ta nemi wayar ba tana cikin jakarta, jakar kuma Adda Suwaiba ta tusa mata a wadrope ɗin Ammah ta saka maƙulli ta rufe. Bilkisu ta ce masa tana tare da ƙawarta lafiyanta ƙalau shi ya sa hankalinshi ya ɗan kwanta amma ya san tana cikin damuwa sosai, su kan su dauriya ce irin ta maza amma rashin Baffa wani babban rashi ne a gare su gabaɗaya. A ranar ma su Gimbiya Maimuna da Gimbiya Hadiza tare da Hajiya Zainab suka zo gaisuwa daga Daura. Ba su jima ba, iyakarasu awa biyu suka juya. Mutane suna ta zuwa gaisuwa daga garuruwa dabam dabam. Wasu mota ne wasu kuma jirgi ne. Abinci ga shi nan ana kawowa wanda ake dafawa ma a cikin gida mai rai da lafiya ne sannan ga ruwa ga lemu, girkin ma da nama ake yin shi, shi ya sa gidan yake cika da mutane maƙil. A ranar ma Hajiya Falmata ta zo tare da wasu dangin Daddy daga zamfara su dai yan zamfara a ranar suka koma Hajiya Falmata ne ta ce sai an yi uku A ranar dakyar Mami ta iya cin abincin ba domin tana so ba Ammah kuma sai kunu aka dama mata ta sha kaɗan Ummu Salma kuma ta kasa cin abinci daƙyar ta sha tea shima sai da Gimbiya Shahida ta matsa mata tana gama sha kuma sai amai sai ga ta kwance jikinta ba karfi da za ta faɗi irin yadda kanta ke ciwo da sun tausaya mata tana kwance akan gadon Baffa tana ta hawaye da kukan zucci Har bayan mangariba ba ta saka komai a cikinta ba, kuma mai rai ba zai zauna bai ci wani abu ba. Sai Gimbiya Shahida ta kira Saleem a waya ta ce ya yi magana da Lamido ya shigo cikin gida ya lallashi Ummu Salma ko za ta ci abinci saboda yanayinta Yana faɗa masa bai tsaya ba tare da Saleem ɗin suka shiga cikin gida falon Ammah ya fara tsayawa ya yi musu gaisuwa. Ammah ya kalla a cikin kwana ɗaya duk ta zabge kamar ba ita ba. "Ammah kin ci abinci? Ya tambayeta lokaci ɗaya yana kallonta cikin tausayi da wani abu daga ƙasan zuciyarsa "Ta dai sha kunu amma abincin ya kasa ciyuwa Lamiɗo." Umma Balki ta amsa masa. Sannan ta cigaba da faɗa masa Fatima dakyar ta yi cokula ta ce ta ƙoshi sun kasa cin abinci "Kowa ya san an yi muku rashi amma hakuri za ku yi ku ci abinci saboda lafiyarku, ita Auta ma tea aka ce tasha ta amayar da shi tana can kwance tana kuka to gwara su sun samu sun yi kuka ita uwar taka ko hawaye ba ta yi ba. Na ce Jamila ki yi kuka in ba za ki a gaban mu ki kebe kanki ki koka domin abin kukan ne ya same ki , ta kasa yin kuka zuciyarta ne kawai ke cikin azaba ina tsoron kar zuciya ta kume mata itama wani abu ya same ta" Hankalin shi ya tashi, ko daga ganin yanayin Ammah zafin dake cikin zuciyarta ya wuce tunanin mai tunani. Gabanta ya sake matsowa ya durƙusa ya riƙo duka hannayenta ya sanya su a cikin na su ya ji sun yi ɗumi kuma suna ta rawa Ya kalleta idanuwansa har sun sauya launi Ba ya son ganin damuwarta, yanzu sai ya rikice "Ammah." Ya kira sunanta a cikin karaya domin shima ya karaya bai kuma san da wani kalamai zai yi amfani da shi wajen lallashinta ba. Rashi ne babba ya same su musamman ma ita, duk wanda ya zauna da Baffa da Ammah sai ya ji rayuwarsu ta birgeshi. "Na'am Lamiɗo." Ta amsa masa tana kallon shi. "Kar ku damu da ni, lafiya ta ƙalau na san Allah ne ya ɗauki ran Baffa, ni musulma ce na san kaddara na kuma karɓeta." Ta ɗan ja fasali kafin ta cigaba da faɗin "Ku je ka samu Auta ka duba ta, an ce tun jiya ba ta ci komai ba tana ta kuka ga lalura a tare da ita." Received at 09:59Reactions: ❤ 9, 😭 2 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta faɗa idanuwamta sun kawi ruwa amma ba ta barsu sun zubo ba. Kowa a falon su kawai yake kallo. "Ammah zan je, amma ke ma ki yi haƙuri." "Na yi Lamiɗo." "Baffanku ma maganarsa ta ƙarshe kafin kalmar shahada haƙurin ya ba ni." "Ammah to ki yi kuka. In wani abu ya same ki ina za mu saka kanmu." "Babu abin da zai same ni Lamiɗo. Baffa ya ce na yi haƙuri yana gangaran mutuwa sau uku yana ba ni haƙuri Lamiɗo me ya sa zan masa kuka. Aikina shi ne na dauwama ina yi masa addu'an rahama har nima ta Allah ta kasance a gare ni." Bakinta ne ya fara rawa daman hannayenta dake cikin na shi sun daɗe da kama rawa, bai san lokacin da ya durƙushe a gabanta ya jawota a ƙirjinsa ya rumgume ta yana mai lumshe idanuwana kamar shima ya fashe da kukan zuciyarsa ta yi wani dum kamar ba shi ba. Ammah jin ta a jikin Lamiɗo ya sa wasu hawaye masu zafi suka saukar mata wannan hawayen ji ta yi kamar saukar dalma, ta yi saurin goge su a jikin shaddar jikin Lamiɗo dakyar hawayen suka fita amma zafin su ya fi  zafin zaman su a zuciyarta tana hana kanta kuka ne saboda in ta yi kuka za ta iya mutuwa ko ta haukace saboda rashin sanin abin da za ta yi gwara ta bar komai a zuciyanta yafi mata sauƙi akan zafin fitan hawayen nata. Shi ya lallashi Ammah aka kawo tuwo miyar ganye ya takura mata ta ɗan ci kaɗan ba da yawa ba ta haɗa da ruwa. Kowa ya jinjina ma ƙaunar dake tsakanin Ammah da Lamiɗo. Ya sanyata ta ci Abinci kuma ta yi masa yadda yake so. Mami ma ya shiga wajenta tana cikin ɗakin Ammah zaune saman darduma in da ta yi salla da hijabi ta haɗa kai da gwiwa tana kuka. Ya daɗe da shigowa ɗakin ba ta sani ba sai da ya durƙusa a gabanta ya dafa kafaɗanta sannan ta dago fuskarta da idanuwanta jajir alamun dai ta sha kuka. Tare da Hajiya Falmata suke zaune a ɗakin shigowar Lamiɗo ya sa ta tashi ta fita ta ba su wuri. Ita kuma ta ɗauka ma Falmatan ne sai ta ga wanda ba ta yi tunani ba. Gaishe ta ya yi ta amsa tana ɗan kauda kai tana ɗauke hawayenta. "Mami ki yi haƙuri ki daina kuka haka nan." "Allah ne ya bamu Baffa kuma shi ya karɓesa daga hannunmu, muma mutuwar nan muke jira Mami, ki daure ki daina wannan kukan kar ki samu wata matsalan" Ya faɗa a sanyaye yana kallonta Kawai sai ta kalleshi ta girgiza kai lokaci ɗaya ta fashe da kuka. Daddy na nan bai koma ba yana tare da su Baffa Umaru sune manya masu karɓan gaisuwa. Kukanta ya sake raunana masa zuciya kuka take yi har da sauti "Lamiɗo na rasa Baffa kuma sai ka ce na daina kuka." "Baffa ne uwata Baffa ne ubana, shi ne dangina gabaɗaya ba ni da kowa sai shi. Yau babu shi Muhammadu yau na rasa Baffa ya zan yi in ban yi kuka ba? Take faɗa cikin gunjin kuka lokaci ɗaya tana riƙe hannayensa. "Baffa shi ne gata na, wallahi shi ne gata na, na rasa gata na." Take faɗa tana jijjiga hannayensa cikin gunjin kuka. Ya rasa yadda zai yi mata kukan ta ya fara yawa. "Ki yi haƙuri Mami ki daina kuka." "Lamiɗo yanzu shike nan Baffa ya tafi ya barmu? Sai ta sake fashewa da kuka. "Tun iyayenmu na da rai Baffa ke amsa matsayin Uba a wajena. Lokacin da Gwaggo ta rasu Baffa ya so ya riƙeni amma aka hana shi riƙona lokacin da na koma Daura duk abin da Baffa ya samu sai ya raba shi da ni ya aiko mini da nawa. Baffa ya damu da rayuwata ya tattaleni ya mini dukkan gata. Lokacin da mahaifinka ya sake ni da a ce ba ni da Baffa da yanzu na mutu da yanzu ka mutu Lamiɗo. Baffa ne ya ba ni bayan shi na jingina Ammah ta ba ni Hannunta na kama, suka rumgume mu tare suka cicinɗa rayuwarmu Lamiɗo, Baffa ne gata na, na rantse da wanda raina ke hannun shi Baffa kaɗai nake da shi a duniya ta ya ba zan yi kuka ba." Maganganun da take yi kamar ma ba a hayyacinta take yi ba jin ta kawai ta yi yi a cikin jikinsa ya rumgumeta. "Na rasa Baffa. Na rasa farincikina na rasa gata na." Take faɗa tana rumgume da shi cikin kuka. "A'a bayan Baffa Ammah nan nan muma muna nan za mu taɓa bari ku yi kukan maraicin Baffa ba." Yake faɗa yana ɗan tapping bayanta alamun lallashi. Amma Mami kuka take yi kamar ranta zai fita. Received at 09:59Reactions: 😭 5, ❤ 3, 👍 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Baffa ya sha ce mini Fatima ki yi haƙuri wata rana sai labari. Baffa ya sha ce mini Fatima duk abin da ya faru dake ki ɗauke shi kaddara watarana komai zai wuce komai ya wuce Baffa ya yi gaskiya amma me ya sa tare da shi komai zai wuce ɗin me ya sa? "Ubangiji ne ya fi mu son shi, shi ya sa ya ɗauke shi daga cikin mu." "Da ni mutuwan nan ta ɗauka da ta sani ta bar Baffa.." "Aa Mami kar ki yi saɓo don Allah." Da a ce zai iya yin kuka da ya koka. Amma shima ɗin ya kasa sai da tafafarsan zuciya. Yau ne rana ta farko da hankalin shi ya taɓa jin Mami a jikinsa. Ko hannun juna a matsayin uwa da ɗa ba su taɓa kamawa ba sai yau. Ita uwa ta dabam ne, wani irin yanayi ya ke ji yana lulluɓeshi, wani irin abu a ƙasan zuciyarsa yana motsi. Sun fi mintina biyar yana lallashin Mami tana ta kuka gwanin ban tausayi. Sannan ya ɗago ta ya share mata hawaye. "Ki yi hakuri Mami, bayan kin rasa Baffa kina damu in sha Allahu ba za ki yi kukan maraicin Baffa ba." Yana share mata hawaye wasu na taruwa. Amma ta rage sautin kukan na ta. "Tsakanin mu da Baffa alheri ne. Addu'a kawai za mu dauwama muna yi masa." "Allah ya jiƙan Baffa Allah ya gina masa gida a aljanna saboda yadda hidimta mini, Ubangiji ya albarkaci bayansa." Mami ta gama faɗa tana mai tsiyayan hawaye sannan ta saka gefen hijabinta ta share Lamiɗo na ta ya ta sharewa da hannayensa. Ta bi hannayensa na sa da kallo zuciyarta ta yi nauyi amma ta kasa magana. Fita falo ya yi ya ce a kawo ma Mami abinci sannan ya koma ciki bayan an kawo da kan shi ya zauna yana ba ta a baki kamar yadda ya yi ma Ammah tana karɓan abincin tana tsiyayan hawaye. Har sai da ta ce ya bar shi haka ta ƙoshi. Ya ba ta ruwa tasha, ta riƙe hannayensa. "Allah ya yi maka albarka Muhammad. ubangiji ya albarkaci zuru'anka. Na gode sosai." Take faɗa tana hawaye, yau dai ta faɗa ta sanya masa albarka a sarari Sai da ya yi mirmishi sannan ya amsa da Amin Amin a ƙalla dai yau ya ji Mami ta kalle shi ta yi masa godiya kuma ta sanya masa albarka. "Ka tashi ka tafi wajen Ɗiyata. An ce itama ba ta ci abinci ba." "Yanzu zan shiga wajenta Mami." Bai bar ɗakin ba sai da ya tabbatar ta daina kuka. Ya fita ta bishi da kallo sannan ta girgiza kanta. "Allah ya yi maka Rahama Baffa." Ta furta tana mai tsiyayan ƙwalla. Akwai mata a falon Ammah yan anguwa da suka shigo gaisuwa sai kawai ya fita. A tsakar gida ya ga Bilkisu kamar ta gama waya ne ta gaishe shi ya amsa. "Ya haƙurin mu? "Mun gode ma Allah." "Allah ya jiƙan shi" Ya amsa da Amin in da Umma Salma take ya tambayeta sai ta nuna masa ɗakin Baffa lokacin an yi mangariba amma gidan tunda akwai nepa ko'ina ya da wadatu da haske. Bilkisu ta bishi da kallo har ya shige ajiyar zuciya ta sauke, ita ko kallon fuskarta ma bai yi ba yafi damuwa da Umma Salma a kanta zuciyarta ta cika da kishi. Jibi za ta wuce Abuja daman bikin sai wannan satin ne tuni wasu daga cikin yan'uwanta yau sun tafi Abuja itama ba domin wannan rasuwar ba da yanzu tana can ta kasa komawa ciki saman tabarman dake tsakar gidan ta zauna hankalinta na kan kofar ɗakin Baffa kamar ta yi tsuntsuwa ta shiga ta ga abin da ke faruwa. Mutuwa dai an san da zafi amma sai take ganin kamar makirci ne ka ƙin cin abinci Ummu Salma sai an ta so kamar Lamiɗo ya zo yana lallasheta. Lokacin da ya kira ta a jiya ya ce ta duba masa Ummu Salma taƙaici kamar ya kasheta ba ta je ba kawai cewa ta yi to, can da ya sake kira ta ce ai taje lafiyan ta lau. Tana jin sa har numfashi ya sauke haushi da kishi suka sanya ta kashe wayarta ko sallama ba ta yi masa ba. Tana ganin yadda Gimbiya Shahida ke kafa kafa da Ummu Salma kar wani abu ya same ta. Ita ko kallo ma ba su isheta ba. Saboda kawai tana da ciki? Kafin Ummu Salma ta yi ciki ta haihu ita ta fara yin cikin Lamiɗo kuma ta haifa masa yara har biyu amma ta fahimci an fi murna da abin da ke cikin Umma Salma. Received at 09:59Reactions: ❤ 17, 😭 2 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Nadama take yi, nadaman me ya sa ta tun farko ba ta shiga ta fita ta raba Lamido da Ummu Salma ba, yanzu lokaci ya ƙure mata in ma ta ce za ta yi wani abun darajanta ne da ƙimanta zai yi kasa. Amma har abada ba za ta taɓa son Umma Salma ba, ba ta da maƙiyiya sama da ita. Domin duk macen da za ta yi tarraya da abin da take so ta zama maƙiyiyarta. Tana zaune tana hararan ɗakin barin ma da ta ga Baɗɗo ta fito kenan su kaɗai ne a ciki. kishi da baƙinciki sun mantar da ita rashi ne mai girma ya samu Ummu Salma tana buƙatar lallashi. * Lokacin da Lamiɗo ya yi sallama a ɗakin Baffa Baɗɗo ce kawai a ciki. Itama saboda kar a barta ita kaɗai ne su Adda Suwaiba suna waje suna wanke wanke n kwanukan da aka ɓata. Ta gaji ma da lallashinta ta haƙura ta ƙyaleta. Sai ga Lamiɗo ya shigo ta miƙe da sauri tana gaishe shi ya amsa sau ɗaya ba tare da ya kalleta ba. Ficewa ta yi domin ta ba su wuri ya zo a daidai domin daman tana tunanin ta aika can haraba a kira shi wataƙila in ya zo a samu Ummu Salma ta daina kuka ta ci abinci. Tsaye ya yi a saman kanta tana kwance a saman gadon Baffa ta juya baya ta dunƙule a waje daya kamar wata yarinya. Tausayinta na tsirga masa, mata uku mafi muhummanci a rayuwarsa yau suna cikin damuwa suna kuka, kukan da ba zai iya hana su ba tunda abin kuka ne ya same su Ya duƙa a gaban gadon yana kiran sunanta amma ba ta amsa ba. Ya sanya hannu ya juyo da ita tana fuskantar shi. Kuka take yi, irin kukan zucci nan mai tahowa da hawaye. Sai kawai ya miƙe ya hau gadon ya tarairayota daƙyar yana nishi domin ta saki jikinta ya ɗora ta a saman cinyarsa. "Why? "Ummu Salama Why? "Kin manta halin da kike ciki ne? Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya yana shafa cikin jikinta. Fashe masa da kuka ta yi domin ta rasa ma abin da za ta ce. Baffa ne fa ya rasu, ba ta tunawa da kanta ma a wannan halin da ta ke ciki. Rumgumeta ya yi ƙam ƙam a cikin jikinsa yana ɗan tapping ɗin bayanta alamun lalallashi bai hana ta ba ya ba ta lokaci duk ta ɓata masa shadda jikinsa da kuka da majina. "Shii is Okay." Sannan ya ɗago fuskarta ya tallabeta yana faman goge mata hawaye. "Ya isa ki daina kuka." "Hamma." Ta kira shi da muryanta da ba ta fita. "Hamma ya zan yi? Kaina kamar zai fashe." Ta gama faɗa tana kama kan na ta, da hannu bibbiyu. "Subhanallah kin ga abin da nake tsoro ko? Tun yaushe ya fara miki ciwo? "'jiya." Ta amsa mishi tana hawaye Wani irin yanayi take ji da ba ta taɓa jin irin shi ba Hamman ma dake gabanta ba ta iya ganin shi sosai ta ƙura masa idanuwana amma duru duru take iya ganinsa. "Hamma" "Yes" "Bana ganin ka sosai." Ta faɗa a daburce tana kallonsa. Ya kalleta cikin mamakin kalamanta, sai dai ganin numfashinnta na sarƙewa ne ya sa ya ruɗe. "Ummu Salama what wrong with you.? Hannunta ya riƙo sai ya ga hannun ya kumbura kuma a jiya da suka taho ba haka hannunta yake ba a ruɗe ya kai kallon shi kan kafafunta ya ga suma sun kumbura. Fuskarta ya bi da kallo ya ga tana ta fama da sarƙewa numfashi. Ya ruɗe yana ta kiran sunanta ta kasa amsawa tana so ta yi magana ta kasa. Tana irin jan numfashi da ƙarfi jikinta na shaking yadda yake kiranta da ƙarfi ne ya sa mutanen dake tsakar gida hankalinsu ya faɗa kansu, Baɗɗo na gaba wajen rumtumawa zuwa cikin ɗakin har da Bilkisu. Halin da suka ga Ummu Salma suma ya ba su tsaro. Bilkisu ta ƙarisa tana duba Ummu Salma. "Ta ce kanta na ciwo, sannan ta ce ba ta ganina yanzu kuma ta kasa numfashi." Yake faɗa cikin ruɗewa. Bilkisu ta ɗaga hannunta ta ga ya kumbura ga sarƙewan numfashi ga shi ta ce ba ta gani sannan tana wani kakkafewa jikinta na mimmiƙewa. A ruɗe ta kalli Lamiɗo yadda yake a firgice itama ta ɗan firgita. "Lamiɗo a tafi asibiti da gaggawa." "Eclampsia. Antepartum Eclampsia. Is accurs before delivery" Bai gane ma bayaninta ba ya sa ta sake kallon shi. "Tsinkau tsinkau in hausa. A tafi asibiti da gaggawa domin a cire abin da ke cikimta in ana so ta rayu." Received at 09:59 13 people reacted with ❤ [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ba ta ma gama rufe baki ba ya sunkunci Ummu Salma ya yi waje da ita ba takalmi a kafarsa haka ya fita da ita haraba. Baɗɗo ta ruga falon Ammh tana kuka tana faɗa musu abin da ke faruwa Mami na cikin ɗaki ta rumtuma ta fito tare da Gimbiya Shahida da su Umma Balki Ammah na zaune ba ta motsa ba. Haka suka bi bayan Lamiɗo har haraba tuni har ya saka ta a motar Abdulrahaman. Domin yadda ya fito a gigice ga Umma Salma a hannu kowa ya san ba lafiya. Hamma Kabiru ne ya yi saurin shiga bangaren tuki Abdullahi ya zauna a gefensa kafin su Mami da su Baɗɗo su ƙariso tuni har sun yi riverse da yake get ɗin a bude yake suka fice da gudu. Daddy ne ya ce ya kamata mata su bi bayan su. Adda Nauwara ce ta ce ba takalmi ma a kafar Lamiɗo Hamma Saddam ne ya shiga gida ya ɗauko masa. Mota biyu suka yi Hamma Jibo ya tuƙa su a motar Abdulrahim sai kuma shi Saddam ya tuƙa su a tashi motar. Mami da Hajiya Falmata ne sai Umma Balki sai Baɗɗo da Adda Nauwara sai Gimbiya Shahida da Abdulrahim da Saleem suka bi  bayan su ba ma su san asibitin da suka je ba sai da suka kira wayar Hamma Kabiru shi ya faɗa musu private hospital ne da sunan asibitin suna zuwa suka same su a bakin emargency haka kuma kafar Lamiɗo ba takalmi sai da Hamma Saddam ya miƙo masa takalmin sannan ya farga da babu takalmi ma a kafarsa. An shiga da Umma Salma ciki ba yadda take domin a lokacin ma har ta fara jijjiga. Ba ɗadewa likita ya fito ya ce ina mijinta Lamiɗo ya isa gare shi. "Matarka na ciki haɗari, Eclampsia ya kama ta sakamakon jininta ya haura sosai 270 ga ciki a jikinta in za mu ceto ta ya zama dole mu cire cikin dake jikinta. Ku sanya mana hannu a wannan takardan sannan kuje ku biya kuɗin aiki." Ba Lamiɗo kaɗai kowa a wajen nan ya firgita Hannunsa na rawa ya karɓa takardan ya zura hannu aljihunsa ya laluba ya ɗauko wallet ɗinsa tuni har Hamma Kabiru ya wuce wajen biya. "Hamma Kabiru ya tafi ya biya kuɗin ." Saddam ya faɗa cikin tashin hankali shekaranjiya ne Baffa ya rasu amma yau sun kara fuskantar wani tashin hankalin. "Cikin ya isa haihuwa ne? Hamma Jibo ke tambaya. "Wata bakwai ne da kwanaki." Mami ta amsa tana tsiyayan hawaye "Allah ya dube ki Ummu Salama." Kowa jikinsa a sanyaye, ana biyan kuɗin aka shirya yi ma Umma Salama tiyatar gaggawa. Suna asibtin nan har goma na dare. Sai dai mazan sun fita sun yi salla. Adda Nauwara ce ta ɗauko waya ita ta kira gida ta ce a sanya Auta a cikin addu'a tana cikin haɗari. Karfe goma da rabi aka gama yi mata tiyata. Likita ya fito ya sanar da su an ciro jariri amma an saka shi a kwalba saboda ya yi ƙanƙanta Ita kuma Umma Salma za a yi obsarving ɗinta 48hours daga lokacin ta farka lafiya lau in sha Allahu za ta fita daga cikin hatsari. Sun samu salama kaɗan da hamdala. Lamido ne kawai da Hamma Kabiru aka bar su, suka shiga ɗakin jariran nan suka ga mai sunan Baffa ɗan cukili da shi a cikin kwalba. Ummu Salma kuma tana cikin wani ɗaki na musamman sai ta farfaɗo sun tabbatar da ba ta cikin hatsari sannan za a kawo ta ɗakin da za ta huta har a samu ganinta. Sha biyu na dare suka bar asibitin Mami aka bari da Baɗɗo za su kwana tare da Umma Salma. Sauran kuma suka koma gida. Da asuba likita ya zo ya sanar da su jaririn da suka ciro ma Umma Salma Hadi Allah ya yi masa rasuwa. Mami tana hawaye tana ta kabbara daman jiyan ita da Baɗɗo ba su runtsa ba. Ana cikin wani rashin ga shi an sake yin musu wani da Baffa da mai sunan Baffa duka Ubangiji ya karbesu. "Allah ya sa mai sunan Baffa ya yi ceton mu ranar gobe ƙiyama. Umma Salma kuma Allah ya ba ki lafiya." Baɗɗo na amawa da Amin tana hawaye ta san yadda zuwan wannan yaron ya zama abin kirgawan kowa ashe ba mai zama ba ne jiya ya zo duniya yau kuma ya koma ga mahallincinsa Ba waya a hannunsu, sai da Mami ta karɓi ta wata nurse ta kira Daddy ta ce ya sanar da Lamiɗo jaririn Umma Salma ya koma cikin dare. Received at 09:59Reactions: ❤ 11, 🔥 1, 😁 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ranar yinin uku da rasuwar Baffa aka wayi gari da wannan rashin na jaririn Ummu Salma. Lamiɗo ya damu domin har damuwan ta bayyana a saman a fuskarsa. Sun gama tsara na su Ubangiji ya gama na shi tsarin. Da safen suka tafi asibitin duka mazan suka yi cike cike sannan aka ba su gawar jaririn sak Lamiɗo kamar ya yi kaki. Lamiɗo ya miƙa ma Mami shi a cikin zanin Ammah da suka taho da shi daga gidan ta kalli jaririn ta rumgume shi. "Allah ya sa ka cece mu" Aka amsa da Amin Baɗɗo ma ta leƙa shi ta ganshi tana hawayen tausayin ƙawarta sannan Hamma Kaburu ya karɓe shi ya ce za su je a yi masa wanka da salla tunda ya zo da rai. "Allah ya sa ya cece mu. Amma ku ɗau hotonsa saboda Ummu Salma." Mami ta faɗa tana sharan hawaye. Suka amsa da in sha Allahu Lamiɗo tuni ya fita ma haraban asibitin ya kasa ma tsayawa tunda ya ga jaririn komai ya kwance masa ga Ummu Salma da ake jiran farkawanta. Sun gode ma Allah kawai domin ya jarabesu a lokaci ɗaya da jarabawowi masu zafi da radaɗi. *Janafty* Received at 09:59 4 people reacted with ❤ [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. A ranar da aka yi addu'an rasuwar Baffa kwana uku a ranar aka sallaci jaririn Ummu Salma aka yi masa salla sannan aka kai shi maƙabartan da aka rufe Baffa shima aka rufe shi, sai dai ba ma a layi ɗaya ba ne bayan rasuwar Baffa mutanen da suka mutu aka zo aka binne su ba su da adadi jama'a ana mutuwa fa sai dai kawai fatan mu Allah ya sa mu yi kyakyawan ƙarshe. Zaman gaisuwan sai ya zama biyu, duk baƙin da suka zo daga baya sai dai su ji Umma Salma na asibiti ta haihu jaririn bai zo da rai ba. Mami da Baɗɗo na asibitin har yamma lokacin da ta farfaɗo ba kuma wanda suka bari ya sake ganinta sai da suka tabbatar da ta fita daga cikin haɗari sannan aka kawo ta ɗaki na musamman. Likita ya ce za su kula da ita saboda daidaitawar jininta eclampsia ya sake ta amma tana buƙatar kulawa ta musamman sannan ga mikin aiki a tare da ita. Sun shiga sun ganta tana barci domin likita ya ce tana buƙatar hutu sosai saboda jininta ya yi ƙasa sannan ba su son cikowar mutane saboda yanayin mai jinyar. Ummu Salma ta rame duk ta zabge Mami da hawaye ta fito haka ma Baɗɗo ita kawai tunanin ta yadda Ummu Salma za ta ji in har ta dawo hayyacinta aka ce jaririn cikinta ya koma. Ubangiji ne shi ne mai tsara gaskiya mu bayinsa duk ƙarya muke tsarawa duba da yadda duk aka gama shirin zuwa wannan jaririn duniya har suna an raɗa masa ashe ko yazo duniya shi ɗin ba mai zama ba ne. Ummu Salma ta tsallake rijiya da baya, eclampsia ce ta kamata ma'ana ciwon tsinkau tsinkau kamar yadda muka sani a hausan ce. Shi ciwon Eclampsia(Tsinkau-Tsinkau) cuta ne da ke da hatsari kuma hatsarinta shi ne tana kama masu juna biyu ne. Sanadinta kuma hauhawar jini in ya haye ƙwaƙwalwa shike nan sai mace mai juna biyu ta shiga cikin hatsari in ba a yi gaggawan kai ta asibiti ba za a iya rasa ta tare da abin da ke cikinta. Alamomin cutar Eclampsia su ne; Ciwon kai mai tsanani  kumburin kafafu ko hannuwa, sarƙewaan numfashi da ganin duru duru mafi hatsari shine  jijjiga ga mace. In ya faru da mace mai ciki to ana gaggawar fitar da abin da ke cikinta ne ko da bai isa haihuwa ba, saboda ceto ta daga hatsari, za a kula da lafiyanta na tsawon lokacin da jininta zai sauka ta fita daga hatsari. Rukunin cutar Eclampsia: Antepertum Eclampsia. Shi yana faruwa ne kafin mace ta haihu. Shi ne kuma irin Eclampsia da ya kama Ummu Salama. Intrapartum Eclampsia; shi ne ke faruwa a lokacin da mace ke naƙuda. Sai kuma Postpartum Eclampsia; shi yana faruwa ne bayan haihuwar mace within 48hours. Cutar Eclampsia cuta ce mai hatsari, ana iya rasa mace da cikin jikin nata gabaɗaya. Zuwa awo na da matukar amfani sannan da lura da yanayin hauhawar jinin mace mai ciki tunda jinin ne yake hayewa saman kwakwalwa sai cutar ta bayyana ga gangan jiki a kiyaye shiga damuwar masu juna biyu. Da kuma kula da blood pressure saboda shiga hatsari faruwan haka kuma a yi gaggawan zuwa asibiti domin samun taimakon gaggawa. * Ba a barin mutane masu yawa suna shiga in da Ummu Salma take, da safe da rana da yamma duk wanda ya zo gaisuwa sai dai ya tsaya can ya yi mata fatan samun lafiya. Amma da Hajiya Kilishi tare da Hajiya Zaliha suka taho gaisuwa da duba Umma Salma sun zo asibitin kuma an bar su sun shiga sun dubata. Da yake kowa ya ji labarin abin da ya faru domin a ranar Saleem ya faɗa a group na su na iyalan Mai martaba. Ƙannen Lamido ba wacce ba ta kira shi ta yi masa gaisuwa da jaje ba. Tana farke ma a lokacin  da su Hajiya Kilishi suka zo ranar kwana biyar da rasuwar Baffa domin tunda ta dawo hayyacinta ta ga ba ciki a jikinta sannan ɗinki ma a in da aka yi mata na haihuwan Hanan a wajen aka sake yi mata wannan ma sannan ta ga har kwana biyu ba a ce mata komai ba sannan ba a nuna mata abin da ta haifa ba ta cire rai da shi. Received at 10:00 8 people reacted with ❤ [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Saboda ko Lamiɗo kullun da safe zai zo asibitin ya duba ta amma bai taɓa mata maganar cikin ba sai dai kuma damuwar dake zuciyarsa wannan karon ta bayyana a saman fuskar shi ko bai faɗa ba ta saka ma ranta cewa yadda ta rasa Baffa shima mai sunan Baffa ta rasa shi. Sannan ko Mami da Baɗɗo da suke kwana da ita ba su taɓa mata maganar abin da ke cikin ta ba. Ita ba yarinya ba ce in abin da ke cikinta na da rai ai za ta gan shi amma tunda ta ji shuru ta saka ma zuciyarta cewa koma me ta haifa shima babu shi kamar Baffa ba ta yi kuka ba amma kuma raɗaɗin dake zuciyarta bawa bai isa ya kwantanta ba. Sannan ana gobe bakwai ɗin rasuwar Baffa ranar da aka buɗe wajen da aka yi mata C.S aka yi dressing ɗin wajen ba daɗewa Lamiɗo ya zo shi ya haɗa ta da Fulani a waya ta gaisheta. Ta yi ta tambayanta ba wata matsala dai ko? Ta ce babu sai ɗan abin da ba za a rasa ba. Asibitin babban asibiti ne tunda kuma asibitin kuɗi ne akwai ƙwarrarun ma'aikata  suna kula da majiyantan su sosai tun ballatana ita da take matsayin VIP. Ta faɗa ma Fulani kawai yanzu rashin karfin jiki ne sai kuma rashin daɗin bakinta an fara ba ta abinci amma ba ta jin taste ɗin komai. Sai kuma sai yawn ciwon kan da ta ke fama da shi ga ciwon mara, ga zafi daga in da aka yanka ta, ta yi ma likitan magana ya ce a hankali komai zai bari saboda C.S ɗin da aka yi mata ne. Ita a lokacin haihuwar Hanan an yi mata C.S amma duk ba ta fuskanci wannan matsalolin ba sai yanzu. Fulani ta yi ta lallashinta da kalamai masu daɗi da nuna mata komai ta ga ya faru da bawa mukaddari ne. Ta yi haƙuri Allah zai ba su wani rayayye tun kafin ta ji daga bakin kowa ta san shima mai sunan Baffa bai zo da rai ba, kuma duk da cikin wattaninsa bakwai ko da ana haihuwar bakwaini su rayu amma ƙarancin hakan ya fi yawa. Ta amsa ma da Fulani da cewa ba komai haka Allah ya so. Ita kuma Fulani ba ta san ma ba a faɗa ma Ummu Salman ba sai da Lamiɗo ya karbi wayar ya fita daga ɗakin yake faɗa mata ba su riga sun sanar da ita ba. "Lamiɗo Ummu Salma ta san cikin ta bai rayu ba. Ka faɗa mata ba domin ba ta sani ba sai domin ka lallasheta." Shi yana tamtama a ina ta ji? Tunda ba wanda ya faɗa mata. "Uwa ce fa, in da abin da ke cikinta na da rai da ta gan shi zuwa yanzu." Sai ya aminta da maganar Fulani bayan sun gama waya ya koma ɗakin sai ya ga Mami na zaune gefenta tana yi mata magana sannan ga wayar Mamin a hannunta alamun cewa hoton jaririn ta nuna mata Mami na ganin ya shigo ta mike tana faɗin"Na faɗa mata, ka zauna ka sake ba ta baki." Tana gama faɗin haka ta fice, Baɗɗo ta je gida ta dawo daga can za ta ɗauko ma Ummu Salma wasu kayan sawa duk da ba ta fara wanka ba sai dai su goge mata jiki tare da gasawa saboda ba a son ruwa ya taɓa wajen aikin kafin a kwance. In Baɗɗo ta dawo ita Mamin za ta koma gida ta yi wanka, Daddy ya koma Kaduna sai gobe addu'an bakwai zai dawo Hajiya Falmata ma kwanan ta biyu ta koma Kaduna. Su Gimbiya Shahida ma ana yin uku suka koma Daura. Bayan fitan Mami in da ta tashi ya koma ya zauna wata farar kujera dake gaban gadon da Ummu Salma ke kwance. Ya ƙura mata idanuwana yana so ya fahimci yanayinta. Hannunta da ba karin ruwa ta riƙe wayar da shi wayar ta ƙura ma idanuwa Lamiɗo ya kasa gane yanayin da ta ke ciki bai ga hawaye ba sannan bai ga tana kuka ba. Ɗayan hannunta ya kalla na dama in da ake yi mata karin ruwa. Ya ɗan kumbura domin akai akai ake zuwa duba ta tare da kayadde lokacin da za su yi mata allurai da saka mata ƙarin ruwa. Sannan sun fara ba ta kwayoyin maganin tunda ta fara cin abinci. Sannan suna yawan yi mata awon B.P jini akai akai da kuma awon fitsari tunda tana da B.P Sannan ga Eclampsian da ta yi fama da shi lokacin da aka kawo ta. Miƙa masa wayar ta yi ya karɓa yana kallon ta. "Kin gan shi? Ya tambayeta lokaci ɗaya yana ɗan rike hannunta mai ƙarin ruwan Received at 10:00 13 people reacted with ❤ [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta juyo ta kalle shi ta ɗan gyada masa kai, tunda ta farfaɗo ba ta cika yawan magana ba zai gaisheta za ta amsa amma kuma babu wata doguwar hira a tsakaninsu bai damu ya ɗauka shock ɗin abin da ya faru da ita ne ga kuma rasuwar Baffa a tunanin shi nan gaba kaɗan za ta warware. Abin da bai sani ba Ummu Salma komai na duniyar ne ya daina birgeta har shi kan shi ya daina birgeta yanzu gata nan ne kawai tana raye amma kamar ta mutu. Radaɗin dake zuciyarta kawai zai iya barazanar kashe ta a kwance a in da take. Sannan tunda ta farka take ganin duniyar ba daidai ba, ɗakin ma ganin shi take yi wani lokaci ƙarami, wani lokacin babba, daga nesa in ta ga abu sai ta ga ya canza mata gata nan ne kawai yanayinta gabaɗaya ya canza. "Ya zo da rai ya kwana ɗaya ya rasu." Ya faɗa yana sake kallon hoton daga wayar Mami. Hamma Kabiru ne ya ɗau hoton ranar da suka koma gida yana tunanin shi ya tura ma Mami. "Allah ya kaddara mai sunan Baffa shima zai zo kuma zai tafi ya bar mu kamar Baffa" Ya faɗa cikin sanyin murya amma a ƙasan zuciyarsa wani abu ke yi masa motsi rashin wannan jaririn ya dake shi, ba shi kaɗai ba da dukkan dangin su ba wanda bai ji ba daɗi ba. "Allah ya jikan su. Shi kuma Allah ya sa ya cece mu." Ummu Salma ta faɗa tana ɗan kauda kai. "Amin." Yana so su haɗa idanuwana amma ta ki ba shi damar haka. "I'm sorry." Ya gama faɗa yana matsa kafafunta da duka hannuwansa duka biyu. "Allah zai ba mu wani mai sunan baffa in sha Allahu." Kanta na can gefen ba ta yi magana ba shima shurun kawai ya yi yana ɗan matsa mata kafafuwa Kiran wayarsa ya katse sa daga abin da yake yi, sai ya ga Bilkisu ce ya ɗauka suka gaisa ƙasa ƙasa tana Abuja ranar kwana huɗu da rasuwar Baffa suka tafi tare da yara da su Hidaya amma kafin tafiyarta ta zo har asibiti ta duba Umma Salama lokacin tana barci. Yanzu ma cewa ta yi ya jikin Ummu Salma ya ce da sauƙi ga shi ma tare da ita. "How is she? Kun faɗa mata? "Ta sani." "How is she? "She is fine, ba ta tada hankalinta kamar yadda na yi tunani ba." "Allah ya ba ta lafiya." Bilkisu ta faɗa cikin wani yanayi, ba ta son ta amma ta ji tausayinta cutar Eclampsia tana da hatsari sannan ga shi ta rasa jaririnta ga shi ta rasa uba duk a lokaci ɗaya in dai kai musulmi ne za ka ji tausayi ko kaɗan ne. Wayar ta ce ya ba ma Ummu Salma ta gaishe ta. Sai ya miƙe ya isa ta wajen kunnenta ya ƙara mata a kunne yana faɗa mata Bilkisu za ta gaisheta. Ya riga ya saka mata wayar a kunne ta ji Bilkisu na yi mata sannu ta amsa a sanyaye "Babu wata matsala ko? Ta amsa mata da cewa babu "So ki cire damuwa a ranki, ana so jinin ki ya yi ƙasa sosai in kina so a sallameki ki koma gida" Ta ce mata toh kawai sannan ta ce Allah ya ƙara mata lafiya ta amsa da Amin Sultan da Beena suna kusa suna ta cewa a basu wayar sai ta ba su ɗaya bayan ɗaya suka gaishe da Ummu Salma sai a lokacin ta ɗan yi mirmishi kaɗan Bayan ta gama wayar shi ya karɓi wayar yana magana da yaran sai ga likita da wasu nurses sun zo duba ta sai ya fita waje ya ba su wuri suka fara checking ɗinta kamar yadda suka saba a koda yaushe. A wajen ɗakin ya samu Mami zaune saman wasu kujeren zama dake wajen, sai da suka yi sallama da Bilkisu sannan ya ƙarisa in da Mami ke zaune amma har ya zauna gefenta ba ta sani ba ta zurfafa a tunani. Sai da ya kira sunan ta sannan ta san da shi a gefenta. "Ya take? Ina fatan ba ta yi kuka ba? Wayarta ya miƙa mata ta karɓa. "Ba ta yi ba." Shuru suka yi dukkansu na wani lokaci. "Ka yi haƙuri kai ma. Allah zai ba ku wani in sha Allahu." Jinjina kai alamun gamsuwa. "Allah ya sa." Shuru ya sake wanzuwa a tsakanin su Mami ta kalle shi duk ya rame sai sumar fuska da ya tara daga gani ba shi da natsuwa sai ta dafa kafaɗan shi ya juyo yana kallon ta. "Kana cin abincin kuwa Muhammadu? "Ina ci." "Ka kwantar da hankalin ka, Ummu Salma za ta warke ku koma gidanku ku zauna, Allah zai sake ba ku wani rabon da ikon Allah sai kun haifi mai sunan Baffa" "In sha Allah." Received at 10:01Reactions: ❤ 8, 👍 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ya amsa mata cikin yaƙini da tabbatarwa. Suna cikin haka ne sai ga Baɗɗo ta dawo tare da Umma Balki. Zuwan su ya sa Mami ta bi Lamiɗo zuwa gida su kuma suka zauna a asibitin tare da Ummu Salma wacce ta koma barci. Haka aka yi addu'ar rasuwar Baffa kwana bakwai Ummu Salma na asibiti. A ranar kwananta biyar kenan a asibiti. Kuma ba su da niyar sallamanta domin a washegari mutanen Mubi da za su koma duk sun zo asibtin duba ta, da su Baffa Salihu shi Baffa Umaru sai an yi sati biyu. An barsu sun shiga amma mutum biyu biyu, sun duba ta da jiki, likita dai ya ce ba yanzu za su sallameta ba sai an kwance ɗinki sannan sai jininta ya daidaita. Ammah ce kawai ba ta zo duba ta ba, amma dai sun gaisa ta waya. Kowa dauriyan Ummu Salma yake gani ba ta yi kuka ba da aka ce jaririnta ya zo ba rai nan ko ba su san raɗaɗin dake cin ta a zuciya ba. Satin ta ɗaya a asibiti aka kwance ɗinki. Har a lokacin ba a wanka sun ce jikinta na da kyau ba ta da ƙwan jiki babu wata matsala sun kara mata kwana uku sai ta yi kwana goma sannan za ta fara wanka. Amma tana shiga ruwan ɗumi saboda tsarki da jini. Mami da Baɗɗo ne tsaye a kanta shi ya sa suke da wani matsayi mai girma a zuciyarta. Yayyenta ma suna zuwa duba ta tunda duk suna nan ba su koma ba. Tana asibitin ne amma hankalinta duk yana gida. Ita na ta zaman makokin a gadon asibiti ta yi shi. Sannan ta zama wata shuru shuru magana ma ba ta yi ban da ta amsa ya jiki shike nan. Ba wanda ya damu tunda tana cikin jinya ne ga rashi har sau biyu, ita ko ba su san abin da take hange ba gani take yi tunda ta rasa Baffa ba za ta sake rayuwa mai daɗi ba sannan ta zo ta rasa jaririnta tun daga lokacin ta ji duniyar ma ta fita kanta har cewa ta yi me ya sa ba ta mutu a wajen haihuwar ba! Da ta huta da wannan  raɗadin da duniyar ma gabaɗaya. Yanayinta ne kwata-kwata ba ta gane ba, tana jin ta kamar wata sabuwar hallita. Kwananta goma sha biyu a gadon asibiti suka sallameta jininta ya sauka ya koma 130 sannan sun yi dukkan gwaje gwaje babu wata matsala an kwancen ɗinki har ta fara wanka. Sun koma gida Baffa na da sati biyu da rasuwa kenan. Washegarin ranar da ta dawo gida Fulani da Gimbiya Shahida tare da Saleem da Hajiya Kilishi suka dawo gaisuwa suka kuma sake duba ta da jiki. Mai Martaba dai bai dawo ba amma ya sake turo wakilai ranar da aka yi bakwai. A ɗakinta dake cikin falon Ammah aka sauke ta, Baɗɗo har lolacin ba ta koma gida ba tana tare da Ummu Salma sai da ta dawo ne ta ga Harira baiwar Allah ita ce ke kula da yaran dake gidan Hanan ma ta zo wajenta tana surutun Mahma ban gan ki ba Papa ya ce kin yi tafiya sai ta amsa mata tana shafa kanta idanuwanta suka kawo ƙwalla Hanan kaɗai ta rage mata a yanzu a duniya. Ummu Balki da Umma A'i suna nan ba su koma ba. Amma Umma A'i za ta koma ita Umma Balki ce sai an yi arba'in za ta koma Mami na nan ba ta ma saka ranar tafiya ba Daddy ma ya dawo shi ya tafi da Barira za ta je can zamfara ta ga iyayenta kafin Mami ta dawo. Su Hamma Jibo duk suna nan tare da matayensu suma ba wanda ya saka ranar tafiya. Baffa ya rasu ranar talata 21 ga wata December, shi kuma jaririn Ummu Salma ranar 22 ya zo duniya ya kuma koma a ranar 24 ga watan december. Ga shi har an shiga sabuwar shekara. Makota da wasu da ba su samu zuwa gaisuwa ba suna ɗan shigowa yin gaisuwa. Ummu Salma ta koma ba ta uhm ba uhm, duk abin da aka ce za ta ce to kawai jinin haihuwanta kwana sha uku ya yi ya ɗauke amma tana shiga ruwan zafi sannan Mami na yi mata wankan jego na towel tana gasa mata jiki cikin dubara duk da mikin wajen da aka yi mata aiki yana ta warkewa yana haɗewa. Sannan sun rubuta magunguna an siya tana sha, dokar likita ce ta dinga cin abubuwan da za su gina mata jiki sannan ta dinga motsa jikinta sannan wannan haihuwar ta ɗan ajiye tumbi ba kamar na Hanan ba. Ita ba ta wannan take ba, jikinta ko wani gayun duniya ba ya gabanta yanzu Received at 10:01Reactions: ❤ 6, 👍 3 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby In ta tuna yau Baffa a duniyar nan sai ta ji ta rasa meke yi mata daɗi, sai da ta dawo gida aka ba ta wayarta. A status ta ga Hamma Saddam ya saka hoton jaririnta ta yi saving a ɓoye ta ɗauka tana kallo tana kuka haka ma hoton Baffa gani take yi kamar zai dawo gani take yi kamar a mafarki. Kwata kwata ba ta cikin natsuwarta amma dai tana bin shawaran likita tana kokarin yaki da abin da ke damunta amma dafin da radaɗin rashin Baffa wani abu ne da har ta koma ga Allah ba zai taɓa gushewa ba. Baffa mutum ne na gari ba domin yana matsayin uba gare ta, ta tuna ranar da ya rasu Hamma Jibo na tambayan ko ana bin shi bashi, tunda ana so kafin akai mamaci makawancinsa a biya masa bashi ko ya yi kwanciyar kabari cikin salama nan take Hamma Abdullahi ya ce Baffa ba ya cin bashi, tunda tare suke kasuwanci ya ce sai dai shi Baffan ne ke bin mutane bashi. * Ranar da Baffa yake da kwana da ashirin da biyu da rasuwa Umma A'i da Baffa Umaru suka koma Mubi, aka bar Umma Balki tare da Ammah sai Mami da matan su Hamma Jibo. Suna nan ba su koma ba, kowa ba ya son tafiya duk da duk sun koma bakin aiki amma suna tunanin acikin satin nan duk za su koma suna ma ta shiri ne. Lamiɗo ne kawai bai koma aiki ba yana ma shirin tafiya Daura ne. Mai martaba zai koma London ganin likita cikin satin nan. Mami ma tana nan ba ta ma saka rana ba, itama ba ta son tafiya duk dare haka suke taruwa suna tunawa da Baffa suna kuka, wato mutuwar Baffa rami ne a zukatansu da ba zai taɓa cikewa ba. Ga Ummin ikki da itama koda yaushe a gidan take yini. Baɗɗo kuma nan wajen Umma Salma ta tare saboda ta ɗebe mata kewa Duk ba wani hira suke yi ba. Amma mutum rahama ne. Ammah ko har yau ba wanda ya ga kukanta kuma ta na nan tsaye kan kafafunta. Daman Umma Balki ta sha cewa Ammah jaruma ce sai da rasuwar Baffa kowa ya ga tabbaci ko kuka ake yi yanzu za ta fara faɗa da cewa su daina yi ma Baffa kuka addu'a kawai take roƙo su yi masa kodayaushe tana cikin hijabi da casbaha tana cikin ibada da nema ma Baffa gafaran Ubangijinsa kowa jinjina ma dauriyarta yake yi ta yi jarumta matuƙa. Washegari kuma aka ce za a je maƙabarta ayi ma Baffa addu'a. Baffa Kabiru da Baffa Mustpaha gobe za su koma gidajen su. Hamma Lamiɗo ma a goben zai bi jirgi zuwa Katsina. Mami kuma ta ce sai sati na sama Daddy zai zo sai su koma. Hamma Jibo kuma ya ce sai karshen sati za su koma Abuja. Za a tafi gabaɗaya ne har da Mami da Ummu Salma duka gidan ma gabaɗaya. Bayan la'asar suka tafi Ummu Salma ma motar Hamma Jibo ta shiga Hamma Lamido kuma motar Amininsa. Sauran kuma suka shisshiga ta su Hamma Abdullahi. Harira kawai aka bari a gida sai Islam da yara. Har da su Adda Nauwara aka je maƙabartan. Maƙabatar ba nisa shi yasa suka isa da wuri. Sun yi magana da maigadin wajen tunda ana ziyara addini ya hallata amma ba wai mutum ya samu wajen zuwa a kodayaushe ba. Sunna ta yarje ma iyalan wanda ya rasu su ziyarce su domin su yi musu addu'a amma ba wai a mayar da abin kamar ibada ba. Alaman da suka sanya yana nan amma zuwa lokacin nan Baffa sun yi nisa a makabarta. Kafin shigarsu Hamma Jibo ya ce kowa ya yi addu'an da muka sani a cikin azkar na shiga makabarta. Kowa ya yi sannan daman suka shiga, a gaban kabarin Baffa Ammah ta dafa kasar tana yi ma Baffa addua'a. Sai a lokacin ta yi kuka hawayenta na ɗiga a saman hannunta da kasar kabarin Baffa. "Allah ya jiƙan ka Baffa. Haƙurin da ka ba ni kafin rasuwarka na yi, ban yi kuka ba. Na gode Baffa Ubangiji ya sanya kabarinka cikin salama Allah ya yalwata maka hasken shi. Mun yi kewarka Allah ya sada ka da rahamarsa." Sai a lokacin ta fashe da kuka Ummin ikki ta rumgumeta gefe tana lallashinta. Amma da Ummu Salma da su Mami suka fara kuka sai ta fara musu faɗan ba ta so. Hamma Abdullahi kuka Saddam kuka haka ma Abdulrahim Ummu Salma kam sai da Lamiɗo ya rumgumeta yana ta lallashi kuka har yana sauti. Received at 10:01Reactions: ❤ 11, 👍 2 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sai da kowa ya yi masa addu'a sannan suka bar wajen kamar kar su tafi kamar su ga Baffa ya fito daga kabarin sun tafi gida tare da shi. In da aka binne jaririn Ummu Salma ne ya ɓace ba su gane wajen ba. Shi ya sa ba su daɗe ba suka bar makabarta. Suka duba hagu da dama, gabas da yamma maƙabarta babba ce amma ta yi rabi da mutane. Jama'a mu dinga ziyartan maƙabararta za mu kara imani da tsoron Allah, za ka ga fa cewa kai ma wata rana nan ɗin ne gidan ka na gaskiya. Duk tarin arzikinka nan ne karshen ka, Sarki ma anan za a san ya shi haka ma Gwamna haka ma attajiri , haka ma talaka nan ɗin ne dai shine ƙarshe, za mu ƙara imani za mu ƙara jin cewa mu shirya ma muttuwa ko yau ko gobe ko anjuma tana tare damu. Ubangiji ya sa mu yi kyakyawan ƙarshe. Allah ya sa mu mutu cikin imani. Amin. Sun koma gida kuma sai mutuwa ta dawo sabuwa Suka haɗu suna ta kuka. Ammah tana ta faɗan ita ba ta son kukan nan. "Abdulrahim har da kai? Kai da za ka zama namiji mai lallashi " Umma Balki ke magana ganin har da shi cikin masu kuka. Mami kuma ɗakin Ammah ta shige tana ta kukanta. Haka ma Ummu Salma Baɗɗo na tare da ita. Mazan ne ke zaune a falo masu dauriyan daman su Hamma Kabiru ne da Hamma Lamiɗo da su Hamma Abdulrrahaman. Ammah dai yau ta yi kukan hawaye shaɓe shaɓe amma a hakan take ce ma wasu su daina kuka. Hamma Jibo na maganar bayan sallar isha'i za su zauna gabaɗaya su tattauna kafin tafiyar su. Suna cikin wannan maganar Sai ga sallaman baki mata. Mata huɗu ne, ɗaya tsohuwa ce ɗaya kuma ba yarinya ba ce sai yaran mata biyu. Suna shigowa mazan suka tashi suka fita kuma daman bakin sun ce suna da tare da maza ne a waje. Har baƙin suka zazzauna ana gaisawa Ammah ko su Ummin ikki dake falon ba su gane su ba. "Hajiya ba ki gane ni ba? Gwaggo ta faɗa tana kallon Ammah ganin ba ta gane ta ba. Ammah ta kalleta domin ga shi ta san kamar fuskar amma ba za ta iya tunawa ba. Duk da sun haɗu da Gwaggo lokacin da Umma Salma ta yi ɓarin cikinta na farko. "Ayya Ban gane ki ba wallahi ki yi hakuri ki yi mini bayani." Ammah ta faɗa murya a sanyaye. "Daman na yi tunanin haka, duka duka bai fi sau biyu muka ga juna ba" Gwaggo ta faɗa tana kallon Shamsiya da kanta ke kasa ta kasa ɗago kanta. Habiba kuma sai kalle kalle take yi tana taɓe baki daga ganinsu dai masu ragwamen gata ne "Ɗago kan ki Shamsiya." Gwaggo ta faɗa tana kallon Shamsiya. "Na san in ni ba ki gane ni ba wataƙila ki gane Shamsiya." Daidai lokacin Ummin ikki ta ƙura ma Gwaggo idanuwana sai a lokacin ta ganeta. Ita ta yi jinyar Ummu Salma asibitin a lokacin da ta yi ɓarin cikin Habib sannan wacce ke kusa da Gwaggo ma ta gane ta matar kanin baban Habibu ne, Hajiya Sahura. Da ɗago kan Shamsiya tare da maganar Ummin ikki da Ammah duk a lokaci ɗaya ne. "Shamsiya." Ammah ta kira sunanta cikin mamaki. "Wa nake gani kamar dangin Habibu." In ji Ummin ikki. "Mu ne ashe kin gane mu" Gwaggo ta faɗa cikin ɗan yake. Sai aka fara kallon kallo. Ammah mamaki ya kama ta. Ummin ikki kuma ta ma kasa magana. "Wai wani Habibun na ji kuna magana? "Ba dai wanman yaron tsohon mijin Auta ba? Mara mutumci mara albarka ba, ba dai dangin shi ba ne nan zaune a gaban mu? Umma Balki ta faɗa tana kallon su Ammah. "Su ne." Ummin ikki ta faɗa cikin gatse. "Me kuma ya kawo su ni Balki? "Shi muke son sani Umma Balki." Ummi ikki ta amsa tana kallon Gwaggo da suka kasa magana. "Lafiya me ke tafe da ku?  Naga tun bayan sakin wulakancin da ɗanku ya yi ma ɗiyarmu alaqar dake tsakanimmu ta yanke me kuma ya kawo ku? Ummin ikki ta tsare su da tambaya. "Alheri muka zo da shi Hajiya." Gwaggo ta faɗa, tana gyara zama. "Ku tashi ku koma da alherin ku, duk alherin da zai fito daga ɓarayin ku bama so." Ummin ikki ta faɗa a fusace. "Aa Hajiya ba za a yi haka. Ku tsaya dai ku saurare mu ku ji da abin da muke tafe." Hajiya Sahura ta faɗa cikin kwantar da kai daman ta san haka zai faru. Shi ya sa Alhaji Sheriff ya da ke ba zai zo ba, darajan Gwaggo ne da ita da ta sanya baki ya sa ya amince ya zo Shamsiya kuwa tana ta sharan hawayen kanta a ƙasa. "Wallahi ba da sharri muka zo ba alheri ne ya kawo mu" Received at 10:01Reactions: ❤ 12, 👍 2 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta sake faɗa cikin lalama. "Gaskiya ba za mu saurare ku ba. Ku tashi ku tafi kawai." Ummin ikki ce ke magana Ammah ta yi shuru kanta na kasa. Gwaggo da Hajiya Sahura na ta rokon a bar su su yi magana. Dai dai lokacin Baɗɗo ta fito falon daga ɗakin Umma ta zo ɗaukan ruwa. Ta ga mata a falo a cikin matan ta ga Shamsiya. Ta razana ta ja baya ta kwalalo idanuwana ta kira sunanta da karfi. "Shamsiya" "Baɗɗo." Ta amsa mata cikin hawaye "Ke ce? Baɗɗo ta tambaya saboda ganin kamar ba Shamsiya ba. Fuska duk kuraje ta yi baki ta rame ga wani hijabi a jikinta mai kama da tsumma. Mami ma maganar Baɗɗo ya fito da ita ganin Baɗɗo tsaye cirko cirko ya sa ta tsaya tana tambaya. Nan take faɗa mata Shamsiya ce da dangin Habibu domin ta gane har Gwaggo sauran ne ba ta san su ba. "Wani Habib ɗin? Mami ta tambaya tana yi musu kallon wulaƙanci. "Kuma suke zaune anan ba ku fatattake su ba." Ta gama rufe baki kenan Ummu Salma ta fito daga cikin ɗakin ita ce daman za ta sha ruwan Baɗɗo ta fito ta ɗauko mata sai ta ji shuru, daga baya sai ta ji kamar tashin maganganu a falo. Lokacin da ta fito ba ta ma lura da mutanen dake falon ba Jikinta da hijabin da suka fita da shi ba ta cire ba kafarta akwai safa. "Me ya fa.." Sai ƙarshen maganar ya maƙale daga bakinta. Lokacin da ta ga waɗanda ke zaune a kasan cafet a falo. Tana wurga idanuwanta tsakanin Gwaggo da Shamsiya. Ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, wani irin ɗaci da raɗaɗi ya dawo mata sabo. "Bestie" Shamsiya ta miƙe tsaye tana kiran Ummu Salma. "Ummu Salma." Gwaggo ma ta kira ta a muryanta akwai tausayi. Har idanuwanta na cikowa da kwalla. Ummu Salma ta kasa amsawa domin sai ta ji kanta ya sara ƙafafunta na rawa tare da jikinta. Ta damƙe hannun Baɗɗo kawai ta juya za ta koma ciki Ba za ta iya ganin su ba, ba ta kaunar ta sake ganin wani abu da ya dangancin Habib har abada. A lokacin kuma sai ga Hanan ta rugo da gudu Faruk ya biyo ta suna guje guje. Uwarta ta nufa sai jin ta kawai Umma Salma ta yi akan kafafunta ta rumgumeta. "Mahma Faruk zai kama ni." Take faɗa da muryanta na yara shi kuma Faruk na faɗin sai ya rama tsungilinshi ta yi Mami ce ta janye shi gefe. Jikin Ummu Salma ya fara rawa ba ta san ta juyo ba, sai kuma idanuwam su Gwaggo na kan Hanan suna kallonta itama ganin baki sai ta kura musu idanuwanta na yara har tana dariya. Tsoron Ummu Salma a yanzu rasa Hanan ba za ta iya jure wannan rashin ba. Ko ba a faɗa ba duk wanda ya ga Hanan ya ga Habib domin tun a jaririyarta kamar shi ta ɗauko bayan ta fara wayau sai kamanin ma suka sake bayyana. Da Shamsiya da Gwaggo zuciyarsu na bugawa a lokaci ɗaya suna ƙura ma Hanan ido. Haka ma Habiba da Hajiya Sahura. Wannan yarinyar jinin Habib ne tabbas Hajiya Sahura ta furta a zuciyarta Habiba kuma haushi ta ji me ya sa Maganar Habib ta tattaba ta? Jwalla suka ziraro ma Gwaggo ashe da rabon Habib zai ga gudan jininsa. Hannu ta miƙa ma Hanan tana faɗin" Zo nan y'an mata" Hanan dake tsaye da jan riga yar kanti a jikinta kanta ba ɗankwali an yi mata kitson shuko. Kamar ba za ta je ba haka ta nufe Gwaggo tana zuwa ta kamata ta rumgume. Kowa kuma a falon ya kasa magana ballatan motsi saboda mamaki. Gwaggo da tsufanta amma hawaye take yi. Ta ɗago Hanan tana kallonta. "Ya sunan ki." "My Name is Hanan." "Hanan Habib Jimeta" Gwaggo ta ce magana ta ƙare a zuciyarta Hannatu Habib wannan jinin Habibu ne. Shamsiya ta duƙa a gaban Hanan tana kuka tana riƙeta sai Hanan ta turje ganin ba ta san su ba kawai sai ta fara kuka kamar an buga ma Ummu Salma guduma a saman kanta ta dawo hayyacinta ta saki hannun Baɗɗo ta nufe su ta ture shamsiya sai da ta faɗi zaune ta janye Hanan. "Bestie" Shamsiya ta kirata cikin kuka. "Kar ki ƙara kirana da wannan sunan" Ummu Salma ta faɗa a fusace cikin ƙaraji. Sanman ta ja Hanan za su koma ciki. "To ki bar ni na rumgume Hanan" "Kar ki kuskura, kar ki kuskura ki matso kusa da yata." "A'a ba su da kunya ne " Mami ta faɗa tana tafa hannu mamaki duk ya ishe ta. "Ku fita kawai tun kafin rayukanmu su ɓaci." A lokacin Hamma Abdullahi ya shigo falon Ammah kamar an jeho shi. Received at 10:01Reactions: ❤ 12, 👍 2 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Ammah ki ji mini marasa kunyar mutane wai dangin wannan shegen yaron da shi kan shi ne da ya tozarta Ummu Salma sun zo suna mana maganar wai sun zo ba da hakuri duk abin da ɗansu ya yi a lokacin ba su san su ba da haƙuri ba sai yanzu." Ya faɗa yana huci idanuwansa sun rufe ko ta kan su Gwaggo bai bi ba. "Na ce a kore su kawai Hamma Jibo ya ce a'a, Ammah wallahi tallahi zan kira musu hukuma." "Shi Habibun ne ya zo don ba shi da kunya? Ummin ikki ta tambaya. "To ai daman an ce in ba ka da kunya ka yi abin da kake so, yana can zaune a koɗe mara mutumcin ba." "Ku kore su, ga ma sauran nan ku tarkata su bar mana gida." In ji Mami tana sake tafa hannuwa. Ummu Salma kuma tun da ta ji an ce har da Habib sai da ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya. "Nima dai ban ga amfanin zuwan su ba, tun a lokacin ba su zo ba sai yanzu." Umma Balki ta faɗa. "A'a ku ƙyale su." Sai a lokacin Ammah ta yi magana gabaɗaya suka kalleta "Ku ƙyale su. Ku shigo da su nan a yi maganar." "Su shigo fa kika ce Ammah? Hamma Abdullahi ya tambaya. Ta gyaɗa kanta cikin tabbatarwa. "Haka na ce, kuma ko Baffa na raye shima haka zai ce" Jin sunan Baffa ya sa kowa jikinsa ya yi sanyi. "Wasiyar Baffa ne, a daran da zai rasu tare da ni da su Saddam ya faɗa mana in sun zo mu saurare su in sun nemi gafara mu yi musu afuwa." Tunda ta ce wasiyar Baffa ne ba wanda ya kara magana Ummu Salma ta ja Hanan suka shige ciki Baɗɗo ta bi bayanta. Haushi take ji, me ya sa Ammah za ta ta ce a saurare su ta sha roƙon Allah kar ya sake haɗa ta da Habib ko Shamsiya. Ba ta ƙaunar su san ma abin da ta haifa balle ya zama yana da alaƙaa da su. Sai ga shi komai ya kwaɓe mata. Ba ta jin za ta iya yafe ma Habib da Shamsiya sun cutar da ita. Kulle ɗaki ta yi saboda Hanan na so ta fita. Ummu Salma kuka kawai take yi komai ya dawo mata sabo. Baɗɗo kuma mamaki kawai take yi na ganin Shamsiya a haka. "Tab rayuwa Sisna kin ga yadda Shamsiya ta koma?" Tana jin ta ba ta yi magana ba. Ba wannan ba ne a gabanta ita haɗuwa da su ne ba ta so. Fargabanta ma Hanan ne, za ta iya yin komai domin Hanan ba ta kasance tare da su ba har abada. *Janafty* Received at 10:01Reactions: ❤ 16, 👍 2, 🥰 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. Tunda har Ammah ta ce su shigo a ba su dama sannan a saurare su ba wanda zai yi musu da ita. Ko lokacin Baffa na raye ba ya musa ma umarnin Ammah balle kuma yau da ba ya raye maganar Ammah tana saman na kowa duk abin da ta ce shi za a yi. Balle kuma ta ce wasiyar Baffa ne. Hamma Abdullahi ya mayar da fusatar shi ya fita can haraba in da su Hamma Jibo ke tare da su Alhaji Sharif ya ɗan duka ta wajen kunnensa yana faɗa masa saƙon Ammah. Shi daman Hamma Jibo ɗan sauki ne ya ce a saurare su. Hamma Abdullahi ne da Hamma Abdulrahaman sune ke ta bala'i Allah ya sa ma tun a farko ba su gane su ba da ko gaisuwan da suka yi musu ba za su amsa ba. Su uku ne daga Alhaji Sherif sai Baba Usman sai Habib ɗin da yake ta raɓe raɓe yadda rayuwa ta mayar da shi ne da kuma daman ba wani sanin shi suka yi ba shi ya sa ba su gane shi ba gwara ma Saddam shi ya je gidan Ummu Salma ba adadi sun sha haɗuwa da Habib ɗin amma shi da farko bai gane shi ba sai daga baya ya fara masa kallon sani. Hamma Jibo kuma ya so ya gane Alhaji Sherif tunda sun taɓa zuwa da Baffa a wancan lokacin amma ya kasa kama suna ballatana ya tuna in da ya san shi. A tunaninsu kawai masu zuwa gaisuwa ne tunda har gobe kafa ba ta ɗauke ba. Amma sai suka ga bayan sun yi gaisuwan sun yi shuru. Hamma Abdullahi ya fusata ne lokacin da Alhaji Sherif ya gabatar da kan su a matsayin dangin Habib ɗin tare ma da Habib ɗin sai a lokacin ma suka gane shi. A lokacin Hamma Abdullahi ya ta shi a fusace ya shiga gidan yana sanar da Ammah abin da ke faruwa. Hamma Abdulrahaman ya ce su ba za su saurare su ba su ta shi su tafi kawai. Hamma Jibo ne ya ce su ɗan dakata tukunna. Habib kawai suke kallo lalle rayuwa juyi juyi na gaba ya koma baya. Tun daga kayan dake jikin Habib ba sai an faɗa musu ba sun san rayuwa ta juya masa baya. Kallon reni da wulaƙancin ya sha shi a wajen su Hamma Abdullahi. Lamiɗo ko kallo ɗaya ya yi masa bai ƙara ba wani abu na yi masa rawa a zuciya na haushi da kishi. Habib kuma ya kasa magana ya kasa haɗa idanuwa da su domin sun yi masa ƙwarjini ga kunya ga nadama sun taru sun natsar da shi a waje ɗaya ba domin Alhaji Sherif ba tabbas zai iya tunkara wannan gidan ba. "Ku yi hakuri don Allah, mun san abubuwa sun faru a baya mara sa daɗi. Ku ɗan ba mu lokaci ku saurare mu ku ji da abin da muke tafe da shi." Alhaji Sherif kenan yana sake roƙon su Hamma Jibo ganin ba su yi maraba da zuwan su ba. Ya san daman haka za ta faru shi ya sa ya ce shi ba zai zo ba. Darajan tsufan Gwaggo ya duba da kuma bakin da matarsa Hajiya Sahura ta saka sannan tare da nadamar Habibu shi ya sa kawai ya amince zai zo amma tabbas abin da ya faru a baya ba mai daɗi ba ne ko shi ne a matsayinsu abin da zai aikata wataƙila sai ya fi na su shi yasa ko kaɗan bai ji haushin su don sun ce su bar musu gida ba. "Ba komai. Mahaifiyarmu ta ce ku shiga ciki domin a zauna a yi magana." "Allah Sarki mun gode. Allah ya saka da alheri." Saddam aka tura cikin gida ya fara sanar da su Ammah shigowar maza. Daman falon daga Ammah ne sai Umma Balki da Ummin ikki. Sai Mami sai su Gwaggo da Shamsiya da suka zo daga baya. su Adda Nauwara suna dawowa daga makabarta suka bi su Adda Suwaiba gidajen su. Islam kuma tana ɗayan ɗakin tana ta fama da waya a hannunta. Ummu Salma kuma tana ciki ta rufe ƙofa ita da Baɗɗo da Hanan. Daman da hijabai a jikinsu sai kawai suka ce su shigo. Hamma Jibo ya yi ma su Alhaji Sherif jagora har falon Ammah shi dai a saman kujera ya zauna tare da Baba Usman amma Habib a ƙasa ya zauna daga can gefe ya takure ko idanuwana ya kasa ɗagowa. Ammah kallo ɗaya ta yi masa ta kauda kanta haushin shi take ji a baya amma a yanzu da mutuwar Baffa ta gama zare mata jin haushin kowa tausayin ma ta ji ganin yadda ya koma. Received at 11:37Reactions: ❤ 14, 🥰 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ummin ikki kan haka take hararan shi bai sani ba tunda kansa na duƙe ne, Mami dai fuskar nan ba fara'a ba domin an ce wasiyyar Baffa ba ne da itama ba za ta amince da zuwan waɗanan mutanen a gidan su ba. Su Hamma Jibo ma duk sun shigo sun zazzauna. Hamma Kabiru na kusa da Lamiɗo. Shi kuma yana fusƙarta ɗakin da Ummu Salma take ciki ne yana tunanin halin da take ciki wataƙila ma tana can tana kuka haka kurum zuciyarsa ta fara zafi yana jin ɓacin ran da bai san dalili ba. Bayan gaisuwa da kuma ta'azziya Alhaji Sherif ya kalli Hamma Jibo yana faɗin ina mahaifiyar ta su take anan? Hamma Jibo ya nuna masa Ammah dake zaune a ƙasan cafet da Hijabi. "Sannu Hajiya Allah ya gafarta masa Allah ya sa ya huta." Ammah ta amsa da Amin Amin. "Mun gode Allah ya ba da lada." Sai falon ya yi shuru, Shamsiya ce kawai ake jin ɗan jan majinanta na alamun tasha kuka. Alhaji Sherif ya juya kaf bai ga Ummu Salma ba ya san ta tunda lokacin in dai Habib zai zo gaishe shi tare suke zuwa kuma abin da suka zo da shi ya shafeta ya kamata duk abin da za a tattauna tana wajen, Habib ya ba shi tabbacin an ce duka suna gida saboda wannan rashin da aka yi musu balle ma ya ce ai ɗan gida take aure yanzu. "Na ce in ba damuwa ina son duk abin da za mu tattauna a nan wajen a ce ita wacce abin ya shafa tana wajen nan." Alhaji Sherif ya faɗa yana kallon fuskokin su Hamma Jibo. "In ba damuwa ina so ta fito itama domin abin da ya kawo mu saboda ita ne." Ammah ta ce ba komai, Mami ta yi ma magana akan ta kira Ummu Salma. Lamiɗo kamar ya ce ba sai ta fito ba sai kuma kawai ya fasa bai yi magana ba. Habib kuma tunda aka ce aka kira Ummu Salma kirjinsa ke duka. Shamsiya kanta na kasa tana tsiyayar hawaye ko daga ganin Ummu Salma ta san ta ga cigaba a rayuwarta sabanin su, to ko ba ta faɗa ba ita fa ɗan Sarki take aure wani jin daɗi ne ba ta cikin sa. Ita da suka cuta ne ita ce Ubangiji ya yi ma sakayya su kuma da suka cutar da ita sun girbi gwargwadon abin da suka shuka in da suka gode ma Allah sun yi saurin gane kurkurensu sun tuba ba sai lokaci ya ƙure musu ba. Sai da Mami ta yi knooking ƙofar sannan Baɗɗo ta tashi ta buɗe mata, duk da Umma Salma na mata tsawan kar ta buɗe ta yi banza da ita ta zo ta buɗe ƙofar sai ga Mami ta shigo cikin ɗakin Ta samu Ummu Salma na zaune gefen gado tana ta kuka ga Hanan ta saka kafafunta ta matse ta, ta hana yarinya kuka sai hawaye take yi, domin cewa ta yi in dai ta yi mata kuka sai ta yi mata duka shine Hanan ta kama bakinta amma tana ta hawaye tana son fita ne Ummu Salma ta hana ta. "Me ye haka? Mami ta faɗa tana jawo Hanan daga kafafun Ummu Salma. "Mami kin ga ni ko! Tun ɗazu nake yi mata magana tana ƙin kula ni." Baɗɗo ta gama faɗa cikin jin haushi. Ita fa ba zuwan su Habib take ji ma haushi ba sai Umma Salma meye na zama kina kuka a kan waɗanan mutanen? A yadda ta ga Shamsiya tun kafin ta ga Habib ta san haƙƙin Umma Salma bai bar su sun zauna lafiya ba. Mami ta hau share ma Hanan hawaye wacce ta yi lamo a jikinta tana sauke ajiyar zuciya. "Ba ki da hankali ne Ummu Salma.? Mami ta faɗa tana mai kallon ta. Sai kawai ta fashe da kuka har da sauti. "Mami me ya sa za ku saurare su? Take faɗa hawaye na kece mata wasu na zubowa wasu na sake tunkuɗowa. Zuciyanta na yi mata wani irin zafi. "To me zai rage mu in mun saurare su?. Su suka neme mu, ba mu ne muka je wajen su ba." "Mami bana son ganin su, bana son su zo kusa da ni ko kusa da y'ata. Bana so a a raba ni da Hanan." "To daman wa ya ce za a raba ku? Shi da ya ce ba ya son cikin ya kuma ce ya bar miki ai ba maganar kuma Hanan." "Mami da gaske kike yi? Ummu Salma ta tambayeta bayan ta ɗan dakata da kukanta. "In sha Allahu." "Nima fa abin da nake ta faɗa mata kenan tana ta kuka wai ba wanda ya isa ya ɗauki Hanan daga wajenta na ce in yana da kunya shi Habib ɗin ai ba zai ma fara wannan maganar ba." "Ko ma ya yi maganar ba shi da wannan hurumin Aisha. Ɗiya ta Ummu Salma ce har abada." Jin kalaman Mami sai kukan Ummu Salma ya ragu fargabanta daman a ce za a raba ta da Hanan zuciyarta ba za ta iya ɗauka ba. Received at 11:37Reactions: ❤ 13, 👏 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Shiga tiolet ki wanko fuskarki. Mu je falo ana magana dake." "Ni kuma Mami? "Ke sun ce suna son duk abin da za a tattauna kina wajen." Kokarin sake fashewa da wani kukan take yi Mami ta ce me ye haka? Magana ce kawai ba wani abu ba. "Kuma a yadda na ga shi Habib ɗin ai nadama ce fal a tare da shi duk ya lalace daga shi har maciyar amanar ƙawar taki." "Na gan ta Mami duk ta bushe. Shamsiya yar gayu ce amma ji beta kamar yar gudun hijara." Maganganun su Mami ya sa ta shiga toilet ta wanko fuskarta Hanan kuma har ta yi barci a jikin Mami sai ta kwantar da ita a saman gado Mami na gaba Ummu da Baɗɗo na bin bayanta har falo, Baɗɗo ce ke rike da hannun Ummu Salma wacce ke tafiya a hankali gabanta na faɗuwa ba ta son ko ganin Habib da Shamsiya domin sun yi sanadiyar samar da wani taɓo a cikin zuciyarta. Tunda suka shigo falon kallo ya dawo kan su, musamman ma Ummu Salma can gefen Ummu Balki Baɗɗo ta zauna a kasan cafet sannan Ummu Salma ta zauna a gefenta ba ta ɗago kai ba balle ta tantance mutanen dake falon amma tabbas ta ji duka idanuwa a kanta. Habib ta kasan idanuwa ya yi ta kallon Ummu Salma tun shigowanta wani abu na yin rassa a zuciyarsa. Ammah ta kalli Ummu Salma sannan ta juya tana ce ma Alhaji Sherif ga Ummu Salman nan ta fito. "Sannu baiwar Allah. Sannu ya ƙarin haƙuri? Ta ɗan ɗago ta kalle shi ta gane shi, mutumin kirki ne ta amsa masa da yauwa haƙuri da godiya cikin sanyin murya amma a ɗan shaƙe alamun ta sha kuka. Habiba na gefe tana ta kallon kowa ɗaya bayan ɗaya addu'a take yi Allah ya sa kar su yafe ma Habib domin tunda ya ƙi sakinta ba ta fatan ya samu salama daga shi har Shamsiya da ta fahimci tunda ya dawo da ita ya canza. "Na so a ce lokacin da muka zo mahaifinku na raye shima Habibu ya roƙe shi gafara, domin lokacin da abubuwa suka lalace zuciyarsa ta ɓaci matuka. Sai dai haka Allah ya so muna fatan Allah ya yi masa rahama." Gabaɗaya falon aka amsa da Amin Amin Ya ɗan yi shuru ya ja fasali sannan ya fara magana. "A baya ko na ce shekaru huɗu a baya ƴa'ƴanmu sun haɗa mu danganta a waje ɗaya ni ne nan da kaina na zo nan gidan muka haɗu da magabatan wannan yarinyar muka nema ma Habib auranta kuma aka bamu cikin darajawa da ƙimantawa, auren su ya sa alaja ta ƙullu a tsakanin mu, muna ta jin daɗi da fatan alheri kwatsam matsaloli suka dinga faruwa a tsakanin ma'auratan,  matsalan ciki da shi Habibu ya ce ba ya so sai an zubar ita kuma ta ce ba za ta zubar ba. Matsalan da muka kasa gyarawa har ta kai su ga rabuwar, rabuwar da ya yi sanadiyar yanke duk wata alaƙa dake tsakanin mu daku gabaɗaya." Alhaji Sherif ya yi shuru kansa na ƙasa. Kafin ya cigaba da faɗin. "Allah ne shaida na, ga Habibu nan zaune ga uwarsa nan a zaune ta san yadda na yi na yi da yaron nan akan ɗiyar ku amma bai saurare ni a wancan lokacin ba. Lokacin da ya saketa shi kaɗai ya yanke hukuncinsa ban sani ba lokacin da Mahaifinku Allah ya jiƙansa ya kirani yana faɗa mini abin da ya faru na ji takaici da bakin ciki dalilin haka yasa na ce na cire hannuna daga rayuwar Habibu tunda ba ya jin magana sannan ba ya jin shawara. Wallahi ɓacin rai ne da baƙinciki suka sanya tunda mahaifinku a wancan lokacin ya fusata ya ce sun yanke dukkan wata alaqa dake tsakanin ɗiyarsu da Habib kar ya sake neman su, nima na aminta da hukuncinsa. Daga lokacin na koma gefe ina jiran ranar da Habibu zai yi nadamar duk abubuwan da ya aikata wannan lokacin ya zo kuma nadamar tasa ne ma ya kawo mu gare ku" Falon ya yi shuru ana sauraran sa. "Da farko na ce ni ban zo ba saboda abin da Habibu ya aikata mai girma ne amma nadamarsa da roƙon mahaifiyarsa ya sa na amince na taho. Ga shi nan ya yi nadama duk abin da ya aikata ga ɗiyarku da gare ku gabaɗaya don Allah ku yi haƙuri ku yafe masa muma ku yafe mana gabaɗaya." Falon ya sake yin shuru. Alhaji Sherif ya cigaba da faɗa musu irin rayuwar da Habibu ke ciki a yanzu, ya fahimci cewa haƙkin Ummu Salma ne ke bibiyan shi, shi kuma ya matsa sai sun zo sun mara masa baya ya nemi gafaransu gabaɗaya. Received at 11:37Reactions: ❤ 7, 😁 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Lokacin sheɗan na jagorantan sa, yana ganin duk abin da ya yi daidai ne, ni sai daga baya ma nake ji a she ita matar da ya aura daga baya ƙawar ita yar wajen ku ne, ashe cin amana suka yi, to gabaɗayansu sun ga sakamakon su tunda itama ko wata biyu ba a yi da mayar da auren su ba. Ya sake ta sun rabu sama da shekaru biyu kuma duk hakan na cikin sakamakon cin amanar da suka yi ne." Baɗɗo ta kalli Ummu Salma itama ta kalleta, Baɗɗo har da mirmishin mugunta tabbas Ubangiji ya amshi addua'anta ya ɗanɗana ma Habib da Shamsiya guɗan su maciya amana ne Ummu Salma kuma ta kasa jin tana farinciki ne ko baƙinciki, domin zuciyarta a ƙuntace take. Gwaggo ce ta karɓi Alhaji Sherif tana sake ba da haƙuri tare da bayanin abubuwan da suka faru da Habib marasa daɗi. "Ya yi nadama ku duba tubansa ku yafe masa kurakuran sa." "Sai da ya rasa komai ne sannan ya san ya ma ƙanwarmu ba daidai ba ko kuwa tun yana da Habib ɗinsa mara mutumci ne ya gane ya yi kuskure? Hamma Abdullahi ya watsa musu tambaya domin shi duk ya fahimce su, shegen ya yi nadama ne lokacin da ya rasa duk abin da zai yi taƙama da shi. "Wannan kuma sai dai shi Habibun ya amsa, Kai Habibu matso kusa ka yi magana." Alhaji Sherif ya faɗa yana ya fito shi, ya janyo shi ciki ya ƙariso kusa da kafafuwan Alhaji Sherif. Jikinsa har rawa yake yi, ya ma kasa ɗagowa ballatana ya yi magana. "Ka buɗe baki ka yi magana wannan ita ce damar ka." Gwaggo ta yi masa magana ganin yana ta rawan baki  ya kasa magana. "Ku yi haƙuri, ku yi hakuri." Habib ya faɗa muryansa na rawa kamar zai fashe da kuka "Nadamar da na yi wallahi ta gaskiya ce. Duk abin da na yi ma Ummu Salma haƙƙinta ya bi bayana cikin da na ce bana so na wulajanta Ubangiji ya jarabceni da son yara amma bai sake ba ni ba. Domin ya nuna mini ya ba ni kyautar a baya na ce bana so yanzu kuma ina nema ya hana ni. Wallahi summa tallahi na yi nadama. Nauyin dake kirjina daman na nemi gafaranku ne sannan na memi yafiyar Ummu Salma in ba ta yafe mini ba rayuwata ba za ta ga dai-dai ba." Ya ƙarishe faɗa yana kuka har da sauti. Falon ya sake yin shuru. Kowa kallon Habib yake yi daman haka rayuwa take ga aikata alheri ko domin watarana. "Allah ya kyauta ba komai Allah ya yafe mana gabaɗaya." Hamma Jibo ya faɗa yana kallon Habib. "A lokacin da abin ya faru min ji ba daɗi amma tunda har komai ya wuce shike nan ka je ka cigaba da rayuwarka mun yafe maka." "Ko ba komai ya ga sakamakon abin da ya aikata." In ji Hamma Mustapha. "Ammah ki yi haƙuri ki yafe mini." Habib ya faɗa cikin rawan murya. "Ba komai Habib, Ubangiji ya yafe mana gabaɗaya." Ammah ta faɗa kanta na ƙasa tana jinjina ma rayuwar nan da komai cikinta sai tarin ƙalubale. Shamsiya ma tana kuka tana cewa Ammah ta yafe mata. "Ba komai Shamsiya Allah ya kiyaye na gaba." Ammah ta sake faɗa tana kallon ta, yadda duk ta lalace kamar da wacce ta sani a baya da wannan Shamsiyar akwai bambamci. Habib ya ɗaga idanuwana ya kalli Ummu Salma kanta na ƙasa ya kira sunanta Lamiɗo sai da ya runtse idanuwana. Me ya sa zai kira sunan ta? Yadda ya kira sunan na ta ne ya sa kawai ya ji yana fusata. Ummu Salma ta ɗago ta kalle shi amma ba ta amsa ba. Akalla dai ya girbi abin da ya shuƙa. Taji daɗi domin sun ɗanɗani abin da suka ɗanɗana mata aƙalla dai ko ba kai na ta ba suma sun rayu cikin ƙunci. "Ki yi haƙuri don Allah ki yafe mini." Ta yi shuru tana mai kauda kai. Wani abu na taso mata sun fama mata gyambonta. Hawaye suka kece mata amma ta kasa magana. "Ki yi hakuri don Allah ki yafe mini. Na yi nadamar duk abubuwan da na yi miki." Nan ma shuru sai hawaye, ji ta keyi kamar ba za ta iya yafe musu ba. Gwaggo ta saka ba ki tana faɗin. "An san an ɓata miki, amma don Allah ki yi hakuri ki yafe masa." Hajiya Sahura ma ta saka baki haka ma Alhaji Sherif amma ya ce ba za a tursasa mata ba. An yi mata ba daidai ba ta yafe wannan imani ne in ma ba ta yafe ba, ba wanda zai ga laifinta. Mami ta juya tana kallon Ummu Salma yadda take kuka ta kasa magana. Lamiɗo kuma ya kasa gane yanayinsa, me ya sa taki magana kawai ta ce ta yafe su bar gidan ba ya son ganin Habib kwata kwata. Received at 11:37Reactions: ❤ 9, 😁 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Shamsiya ce ta tashi daga in da take zaune ta ƙarisa gaban Ummu Salma ta durƙusa a gabanta. "Bestie." Ta faɗa muryanta na rawa Baɗɗo ta yi mata wani mugun kallo. "Sunan ta Ummu Salma, wannan sunan kin daɗe da cire shi a tsakanin ku." Baɗɗo ta amsa ma Shamsiya a fusace. "Ki yi haƙuri Aisha." "Ba komai Shamsiya. Ki yi hakuri kema amma ko tausayinku ban ji ba. Na ji ɗaɗi ma wataƙila kuma kun ɗanɗana irin zafin da muka ɗanɗana a zukatan mu a baya." Shamsiya ta kasa magana sai kuka. Ta janyo hannuun Ummu Salma tana riƙewa a cikin nata hannun da sauri ta janye hannunta Sai Shamsiya ta kece da kuka tana ba ta hakuri lokaci ɗaya ta tsinke da ba ta labarin duk abin da ya faru. "Ni na ba ma Habib shawaran ya zubar da cikin jikin ki, sai ga shi ni da nake son na haihu da shi Ubangiji ya hana ni sau uku ina samun ciki yana zubewa, likitoci sun ce ina da raunin mahaifa, zai yi wahala mahaifana ya iya rike ciki, wannan ba alhakin ki ba ne? Habib ɗin dana ke so na raba ki da shi ni na aure shi, daga baya nima ya guje ni, ya sake ni lokacin da na ke bukatarsa na koma gida cikin halin baƙin ciki na rasa karatuna a lokacin na kuma rasa mahafina. Ummu Salma na shiga jarabawa mai tsanani amma da wuri na gane kurakuraina na gyara, na daɗe ina tunanin hanyar da zan same ki, domin na nemi gafaranki ban samu ba, kunya kuma ta sa na kasa neman gidan nan. Ubangiji ya jarabeceni da Soyayyar Habib da duk abin da ya yi mini na kasa cire shi a raina shi na yi ta jira yana dawowa da nadamarsa na ƙarbe shi, ni da shi mu muka faro komai dole tare za mu karkare shi, fatanmu mu haɗu dake mu ba ki hakuri Habib ya samu labarin kin yi aure kina auran ɗan uwanki ɗan Sarkin Daura daga nan muka san kin yi mana nisa, wani matashi ne a anguwan nan Habib ya sa ya saka masa ido duk ranar da ya ganki ya faɗa masa domin mu samu damar neman gafaran ki, sai kawai ya kira sa yana faɗa masa Baffa ya rasu da shi aka yi jana'izar Baffa sannan aka raka shi har gidan sa na gaskiya. Mun bari ne sai zukata sun sanyaya sannan muka zo, ki yi hakuri ki yafe mana wallahi Habib ya yi nadama kuma duk abin da ya yi miki da shawarata in akwai wanda za ki fi ganin laifin sa ne ni ce Ummu Salma ni ce silan komai." Ta ƙarishe faɗa cikin kuka, kowa a falon jikinsa ya yi sanyi. Shamsiya kuka take yi kamar ranta zai fita amma Umma Salma ta kasa magana itama hawayen take yi. Ammah ce ta juya tana kallon Umma Salma. "Ki yi hakuri ki yafe musu, a daran da Baffa zai rasu ya yi mana wannan tunasarwa ya ce muma muna laifi amma Ubangiji ya yafe mana sannan ya ce mu zama masu afuwa da yafiya domin Allah na tare da masu hakuri." Umna Balki ta jinjina kai tana faɗin gaskiya ne ita da Ummin ikki. Ummu Salma ta runtse ido ta buɗe, tun da aka ce Allah sannan aka kira sunan Baffa an gama magana Za ta yafe musu amma ba ta son wata alaka ta sake haɗa su har abada. Murya a shaƙe ta ce komai ya wuce ta yafe. "Mun gode Ummu Salma Allah ya saka da alheri." Ta amsa da Amin tana kallon Shamsiya. Shamsiya ce ta koma haka? Lalle rayuwa kenan ta tuna a baya ba ta da ƙawar da ta fita sai Baɗɗo amma yau an wayi gari Shamsiya ta ba da gudummuwa wajen jefa rayuwarta cikin baƙinciki. Shamsiya ta riƙe hannuwan Ummu Salma da karfi domin kar ta ƙwace. "Mun gode sosai Ubangiji ya cigaba da dauwamar da rayuwarki cikin farinciki, kin ga yadda rayuwa ta yi danmu ko? Na kasa haihuwa Umma Salma itama Habiba ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba tunda Habib ya aure ta." Ta gama fada tana juyawa sannan ta nuna Habiba. "Ɗiyar Baba Usman ce ita ya aura bayan mun rabu." Ummu Salma ta bi ta da kallo, sai da Shamsiya ta yi magana sannan ta gane ta. Ta san ta tabbas ɗiyar Baba Usman ce suka kalli juna Ummu Salma ta kauda kanta kawai, rai suka wulaƙanta kuma wannan haƙƙin sai ya tambaye su amma ko Habib zai mutu bai haihu ba ne, ba za ta ba shi Hanan ba Kowa ya ɗauka za su yi maganar Hanan amma ba su yi ba sai godiya da suke yi suna shirin tafiya. Ammah ta ce su dakata sannan ta kalli Ummu Salma wacce tunda ta ce su dakata gabanta ke zikiri. "Ina ɗiyar su? Received at 11:37Reactions: ❤ 8, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ba Ummu Salma ba hatta su Hamma Jibo sun sha mamaki, sun ɗauka daga neman gafara shike nan cikin nan cewa ya yi baya so, suma kunya ce ai ta hana su tambayan labarin cikin Lamiɗo ya ji maganar Ammah a zuciyarsa amma ko a fuska bai nuna wani alamu ba. "Ammah ba fa ɗiyarsu ba domin cewa ya yi baya so ya bar ma Auta wannan cikin halak malak." Hamma Abdullahi ya sake maimaitawa. Sai Alhaji Sherif ya kalli Baba Usman, shima ya kalle shi cikin mamaki domin ba su gane kan maganar ba. Habib kuma  jin sa yake yi wani iri yana ganin a kamar mafarki daman kunya ce da nauyi ya sa bai tambayi cikin jikin Umma Salma ba amma abin na ran shi cewa ya yi ba zai taɓa tambaya ba. "Alhaji cikin da Umma Salma ta fita da shi ta haife shi, mace ce sunan ta Hannatu kamar Habibu ne yana ƙarami " Gwaggo ta faɗa ma Alhaji Sherif tana dariya lokaci ɗaya da hawaye. Shamsiya kusa da Habib ta koma tana faɗa masa Umma Salma ta haifa masa yarinya mai kama da shi Ya kasa magana bakin shi da jikinsa ma rawa suke yi. "Na sani, amma Baffa ya ce ko bayan ran shi mu haɗa Hannnatu da mahafinta tare da ahalinsa." "Why Baffa? "Me ya sa? Su Hamma Abdulrahaman ke tambayan kan su. Su Hamma Jibo kuma sun yi shuru domin ta wani fannin sun hango manufar Baffa Ammah ta kalli Baɗɗo sannan ta ce ta ɗauko Hannan ta kawo musu itama duk jikinta ya yi sanyi. "Barci fa take yi Ammah." Mami ta faɗa domin itama a ɗauko musu Hanan din bai yi mata daɗi ba "Ku taso ta." Ammah ta faɗa kai tsaye. Sai kowa ya kasa motsi barin ma Ummu Salma da ta ji kamar numfashinta zai ɗauke me Ammah take nufi? A ɗauko Hanan a bawa Habib ina ba zai saɓu ba yau ko duniya za ta haɗe ba za ta bari Habib ya ga Hanan ba, ballatana har ya taɓa jikinta. Baɗɗo ta miƙe ta wuce ɗaki ta ɗauko Hanan dake barci, tana ɗauko ta kuma kamar ta sani ta farka tana mutsike idanuwana. Ummu Salma ta ji kamar an zare mata lakka, lokacin da Ammah ta ce wai Baɗɗo ta miƙa Hanan ga su Habib. Ba ta san ina ta samu wannan karfin ba, ganin ta kawai ta yi a gaban Baɗɗo ta warce Hannan ta ƙanƙameta a jikinta. "Ba zai taɓa mini ƴa ba, shi ya ce ba ya so ya bar mini. Saboda haka har abada ta haramta a matsayin jininsa." Take faɗa tana kuka, Mami ta miƙe tana yi mata magana ta matsa baya ta fashe da kuka. "Mami har da ke! Raba ni da ƴa ta za su yi wallahi ƙwace ta za su yi" Tana wani irin gunjin kuka. Nan fa su Alhaji Sherif suma suka mimmiƙe cikin tashin hankali. "Ba wanda zai kwace miki ƴa' ai tunda ya ce ba ya so ya bar miki ta ki ce har abada.' Alhaji Sherif ke faɗa cikin sigan lallashi amma Ummu Salma ta kamkame Hanan ta hana su, su ganta Hamma Jibo ya yi magana ta sake fashe masa da kuka har tana ya taimake ta. Ko zafin jikinta ba ta ji yadda take jijjiga ga kuka. "Ki saki yarinyar nan Ummu Salma, ba ki ji me na ce ba ne?. Ammah ta sake magana amma Ummu Salma ba ta amince ba da gudu ta nufi Hamma Lamiɗo ta duka a gaban shi. "Hamma ka saka baki, ka faɗa ma Ammah kai ne Baban Hanan, ka hana ta ba su ita." Take faɗa tana wani irin kuka mai ban tausayi Baya son kukanta shima hukuncin Ammah bai yi masa ba amma tunda umarninta ne ba zai ja da ita ba. "Is okay amma dai yanzu ki yi abin da ta ce, miƙa ma Aisha Hanan ɗin." Ya faɗa yana kallonta lokaci ɗaya da ƙokarin riƙe ta, wani kallo take yi masa na kaima har da kai za a raba ni da farincikina kawai sai ta tashi ta manta akwai mikin ɗinki a jikinta bai gama warkewa ba ta juya ta saka Hanan a baya wacce ta yi zuru zuru har ta fara kuka ganin abin da ke faruwa. Habib na tsaye amma kafafunsa rawa suke yi. Shamsiya ta duka a gaban Ummu Salma. "Ba ƙwace ta za mu yi ba Ummu Salma ganin ta kawai za mu yi." "Ba za ku ganta ba. Ba ke kika ce a zubar da cikin ba shi kuma ya bi abin da kike so ba, ya so Hanan ba ta rayu ba Ubangiji ne ya fisa wallahi ba za ku taɓa ƴata ba ku je na yafe muku amma har abada kar ku sake tunkaran in da nake " Nufinta ta gudu ɗaki ta rufe Ammah ta miƙe tana sake daka matsa tsawa. "Kar ki matsa daga in da kike." Received at 11:37Reactions: ❤ 8, 👍 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Maganar Ammah ya hana ta motsi amma ba ta daina gunjin kuka ba Mami tausayi ya kamata sai hawaye haka ma Baɗdo da Ummin ikki. "Jamila bi ta a hankali." In ji Umma Balki cikin tausayawa. "Ai a hankali na bi ta da farko na ga za ta yi mana hauka " Ammah ta faɗa,sannan ta ƙarisa kusa da Umma Salma. "Ba ki da hankali ne daga cewa za su ga yarinya sai ki fara ma mutane hauka? Ba ni ita." Ammah ta gama faɗa tana mija mata hannu. Amma ina Umma Salma ta kasa. "Ba za ki sauke ta ba? "Ammah." "Na ce ki sauke ta kar in mare ki anan wajen" Ammah ta fusata ranta ya ɓaci, kan ta farau haihuwa ji wani haukar da take yi. "Kan ki farau haihuwa ko nan duk ba mu haihu ba ne sai ke? Daga cewa a kawo yarinya su ganta sai ki fara mana hauka in aka barki da ita za ki iya ba ta sunan Uba ne? Koma me ya faru shi ne mahaifinta mun sani kin sani suma sun sa ni." "Ammah Hamma Lamiɗo ne mahaifinta." Ummu Salma ta faɗa cikin gunjin kuka kuma ba ta sauke Hanan ɗin daga bayanta ba. "Na ji shima mahaifinta ne amma kowa ya san ba shi ya haife ta ba. Cewa fa kawai na yi za su ganta ba tafiya da ita na ce za su yi ba amma tunda na ga abin da kika yi na ma fasa." Ammah ta juya tana kallon Baɗɗo. "Aisha shiga ciki ki haɗa kayan Hannatu ki ba ma mahaifinta su tafi da ita ta kwanan musu biyu." "Ammah." Ummu Salma ta kira sunanta da karfi tana kuka. "Ammah don Allah ki yi haƙuri." "Wallahi sai sun tafi da ita, in ta ga dama ta mutu saboda haka, shanshanci kawai kika rasa ma uba kika dangana balle wata ƴa? Yadda Ammah ke faɗa kowa yasan ranta ya baci shi ya sa ko su Hamma Jibo ba su yi gaddama ba. Gwaggo ne da Alhaji Sherif ke ba da hakuri. Baɗɗo ko ta shiga cikin ɗaki a wata ƙaramar jaka ta haɗa ma Hanan kaya kala biyar da komai da komai ta zage ta fito, tun kafin ta miƙa ma Shamsiya ta yi saurin karɓan kayan Hanan kuma Ammah ta sauke ta daga bayan Ummu Salma, tana kuka Hanan na kuka ta tura ta Shamsiya ta ɗauketa itama tana kuka tana dariya. "Mun gode Ammah, za mu dawo da ita in sha Allahu." Habib kuma yana kallon Hanan yana kuka, daga karshe ma fita ya yi daga falon daga gidan gabaɗaya ya fita waje ya je can yana kuka shi kaɗai. Nadama ta kara kama shi yanzu cikin da ya so ya salwantar da karfin tsiya ita ce Hanan da ya ke gani mai kama da shi. A cikin falon Ammah kuwa Gwaggo na faɗin ba sai an yi haka ba. A bar Hanan kawai in an kwana biyu sai ta je kowa ya ganta amma yanzu tunda uwar babu daɗi ta zauna tare da mahaifiyarta shima Alhaji Sherif haka ya ce. "A'a ku je da ita, itama ba daɗewa za su yi ba za ta bi mijinta su koma Lagos. Wannan kukan da take yi na jaririn da ta haifa ba rai ne kwana biyu da rasuwan Baffa." Ammah ta faɗa musu, domin ita a ganin ta shi ya sanya Ummu Salma shiga wannan halin nan Gwaggo ta dinga addu'an Allah ya kawo mai tsayawa Shamsiya kuma tuni ta yi waje ɗauke da Hanan da take ta kuka har tana faɗin ta daina kuka nima maman ki ce, Baɗɗo ta dinga hararanta kamar idanuwanta za su faɗo ƙasa. Habiba ta bi bayanta, ita tausayin Umma Salma ta ji bai kamata a ji tausayin Habib ba. Fitar Shamsiya da Hanan tana kuka ya fito da su Adda Safina da Islam da Harira. Suka ga wata ta fita da Hanan suka shigo falon Ammah nan suka ga Umma Salma ta faɗi a tsakiyar falon Ammah tana gunjin kuka. "Wayyo Allah na an cuce ni." Haka take faɗa kamar ta zare, a lokacin kukan rashin Baffa take yi, da kukan rashin jaririnta yanzu a ce kuma an raba ta da Hanan "Ba ma wanda ke sona sai Baffa wayyo Baffa, Allah ya jiƙan ka da kana nan da ba ka bari an cuce ni ba." Take faɗa tana birgima tana kuka Mami na yi mata maganar ta tashi, ta manta akwai miki a jikinta amma ba ta ji ba. Har Hamma Jibo ya yi mata magana Hamma Kabiru har tsawa ya yi mata amma ba ta ji ba. Ran Ammah ya kai kololuwa wajen ɓaci, har Umma Balki sai da ta yi magana Umma Salma ta duƙa tana kokarin tayar da ita amma ba ta ji ba sai ma fizge jikinta da ta yi tana cigaba da kuka. Ammah ta kalleta wasu hawaye suka ziraro mata. "Yau da ko wata Baffa bai yi da rasuwa ba har za ki fara tona mini asiri Ummu Salama? Ni ce na cucen ki kenan? Received at 11:37Reactions: ❤ 8, 😱 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Ammah kin cuce ni, Hanan kaɗai gare ni kika raba ni da ita." "Are you Mad? "Will you keep quiet." A tare ya yi magana cikin tsawa lokaci ɗaya yana miƙewa. Sai da ta yi ɗif da kukanta domin tsawan Hamma Lamiɗo mai razanarwa ce. Tun ɗazu yake ganin abin da take yi ya ɗauke kan shi, duk da shima hukuncin Ammah ya yi masa tsauri amma ba zai iya gaddama da ita ba. Kowa ya yi mata magana amma ba ta ji ba, har tana cewa wai Ammah ce ta cuce ta. Me take so a yi mata? Ko can gidan take son komawa saboda an tafi Hanan. "Yauwa gwara ka yi mata  magana tunda mu ta ƙi jin namu." In ji Ummin ikki itama ranta ya ɓaci. Haba Ummu Salma kuma ta fara fita daga hayyacinta. "Sakarci ne kawai ku yi mata dai a hankali." Umma Balki take faɗa domin tausayi Ummu Salman ke ba ta. Ammah kuma kuka ta fashe da shi ta koma ta zauna "Allah ya jiƙan ka Baffa, ka tafi ka bar ni yau ga shi Auta na cewa na cuce ta." Kukan da Ammah take yi ya ɗaga musu hankali. Ummu Balki na faɗin ta daina kuka wannan ba wani abu ba ne, ita Umma Salma duk cikin rashin da aka yi mata ne ta faɗi haka amma ba cikin hayyacinta take ba Mami kuma ta duka tana ba ma Umma baki da hakurin kan ta tashi. Hamma Kabiru ya ce su ƙyaleta gwara ma da Ammah ta yi haka ko gabaɗaya ma za su karɓi Hanan ɗin sai ta mutu don ubanta. "Ummu Salma me ke damun ki? Wannan ai sakarci ne" In ji Hamma Jibo yana mata faɗa. Lamiɗo kuma yana tsaye kawai yana huci ga cewar da ta yi Ammah ta cuce ta sannan ga abin da take yi sai kawai zuciyarsa ta haska masa Habib ɗin take so, da za a ba ta zaɓi shi za ta zaɓa saboda Hanan. Ganin Mami da Baɗɗo suna ta lallashinta amma ta ki yin shuru ya sa Lamiɗo ya ce duk su ƙyaleta. Cewa ya yi ta miƙe ta zauna. Ta ƙi tashi ya sake daka mata tsawa da sauri ta miƙe tana rufe idanuwanta hawaye na sake kece mata. "Ka yi mata a hankali mana." Mami ta faɗa ganin ya harzuƙa Ummu Salma kuma tana cikin wani halin da za a tausaya mata. "Mami Ammah ce fa ta yi magana, ta yi mata gaddama a gaban mutane ta kyauta abin da ta yi? Ya faɗa yana nuna ta da yatsa hannunshi na hagu. "Ko ba ta so hukuncin ba tunda Ammah ta yi mata umarni me ya sa ta yi gaddama is she is ok? Bayan kuma ta kunyata ta a gaban mutane yanzu kuma look at her.? Kina ji fa ta ce wai Ammah ta cuce ta! Ammah ce za ta cuce ta? Yanayin yadda yake magana ya sa kowa ya san a fusace yake. "Ba ta kyauta ba. Amma a yi haƙuri." In ji Umma Balki, Mami kuma cewa ta yi ya yi shuru kawai tunda dai ya faru kuma ba cikin hayyacinta ta yi ba. "Ga zafin rasuwar Baffa ga na rasa jaririnta rana tsaka kuma ga Hanan dole za ta rikice." "To ta tashi ta bi su can, tunda Ammah ta cuce ta. Ta bi su can if she want to stay with her Daughter sai na sake ta ta je ta aure shi sai ta samu daman zama tare da Hanan sosai." Cak kukan Umma Salma ya tsaya. Ta ɗago da jajayen idanuwanta tana kallon Lamiɗo cikin ido, yau ba kallon soyayya yake yi mata ba wani irin kallo ne da ya kusa sanyata bugun zuciya ta ɗauka shi zai fi kowa fahimtarta ta ɗauka zai fi kowa sanin yanayinta baƙincikinta ɗaya yadda ya kasa gane halin da take ciki Ammah ma sai da ta tsaya da kukan Mami da Umma Balki har suna haɗa baki wajen kiran sunan shi a firgice. "Ƙul kar na sake jin wannan maganar a bakin ka." Mami Ta faɗa cikin ƙaushin murya. Hamma Jibo ya ce abu bai yi daɗi ba tunda ran Lamiɗo ya ɓaci sai ya ce Kabiru ya janye su fita waje "Gaskiya ya faɗa abin da ta nuna kenan sai ya sake ta, ta je can ta ƙara ta." Ammah ta faɗa da iya gaskiyanta. "Haba Ammah." Hamma Abdulrahim ya faɗa, da tunda aka zauna bai ce komai ba sai yanzu. Hamma Kabiru ya ja hannun Lamiɗo yana faɗin ya zo su fita. "Ba ta kyauta ba, Amini kar ka biye mata." Ummu Salma ta ga tunda ta rasa Baffa sai me don ta rasa Lamiɗo? Tunda ya iya cewa zai iya sakinta ai ya yi rugurugu da yardan dake tsakanin su. Sai kawai ta miƙe tana kuka. "Sai me in ka sake ni? Ka sake ni mana ai ba zan mutu ba, na rasa ma Baffa ban mutu sai me don na rasa ka? A baya ma an sake ni kuma ban mutu ba yanzu ba.." Ba ta kai ƙarshen maganar ba Mami ta buge mata baki. Received at 11:37Reactions: ❤ 9, 👍 2 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Rufe mini baki, ba ki da kunya ne? "Umma Salma kin yi hauka ne? In ji Hamma Jibo. "Sisna.." Baɗɗo ta kira sunan ta a zafafe domin ta fahimci ta fara zarewa. Lamiɗo kuma cak ya tsaya ya juyo suka kalli juna. Ya ga duk abin da take faɗa a cikin idanuwanta kenan da gaske ne zarginsa ta fi son Habib akan shi. Da gudu ta ruga ta shige ɗaki ta kulle kanta ta kwanta a saman cafet tana wani irin kuka mai cin rai da ƙuna ga gunji. Tana jin mikin ta na aiki na yi mata zafi amma ba ta jikinta take yi ba kuncin dake cikin zuciyarta ne ya fi raunin da ke waje zafi. A falo kuwa Lamiɗo bai sake magana ba ya fita lokacin ma har an fara kiraye kirayen sallar mangariba. Suma sauran mazan fita suka yi domin ɗaura alwala suwa masallaci. Ammah kuma ɗakinta ta shige. Mami ta zauna tana faɗa ma su Umma Balki Umma Salma na cikin damuwa su yi mata uziri. Ga shi a gaban su Islam aka yi duk sun yi wiƙi wiƙi. Umma Salma kuma ta ƙi buɗe ƙofa Baɗɗo ta yi ta magana shuru. Daga karshe ma Ummin ikki tabi suka koma gida Ammah kuma kamar an yi mata fami ta shige cikin ɗaki tana ta kuka haka su Adda Nauwara suka dawo gidan duk a rikice Adda Safina ce ta kora musu abin da ya faru suma jikina su duk ya yi sanyi. Lamiɗo kuma bai dawo cikin gida ba sai da safe a gidan shi ma ya je ya kwana tunda Hamma Saddam ya zo ya karɓi key ɗin bangaren Bilkisu a daran. Da safe kuma jirgin karfe goma ya bi zuwa Katsina Ya shigo ya yi ma Ammah da su Mami Sallama. Mami ta bi shi har haraba in da Hamma Abdullahi ke jiran shi zai kai shi filin jirgi Wai kar ya biye ma maganganun Umma Salma tana cikin halin tausaya mata ne. Shi mai zai ce ban da ya ce to kawai. Mamin na faɗa masa sai da safen nan Ummu Salma ta buɗe kofa ta damu kar wani abu ya same ta. Ko a fuska bai nuna ga yanayin da yake ciki ba, amma tabbas kalaman Umma Salma sun dake shi matuƙa. Shi na shi maganar ya faɗa ne cikin ɓacin ran abin da ta yi, amma ita ba cikin bacin rai ta furta na ta kalaman ba, har a zuciyarta ne. Zai yi mata abin da take so, tunda ya fahimci ta fi son zama da Habib ɗin sama da shi. Bayan tafiyan shi Baffa Kabiru da iyalansa suka ɗau hanya, kusan lokaci ɗaya suka wuce da Hamma Mustapha. Zaman da suka ce ma za su yi kafin tafiyarsu abin da ya faru ya sa bai yuyu ba. Kowa ya yi banza da Umma Salma Mami ce kawai ke shiga wajenta. Umma Balki ma ta ce abin da ta yi rashin kunya ne. Su Adda Safina duk sun shiga sun yi mata sallama tana kwance idanuwanta har sun kumbura saboda kuka. Ba nadamar maganganunta na jiya take yi ba. Tunanin yau Hanan ta kwana can tare da mutumin da ta yi alƙwarin har abada ba zai kusanci ƴarta ba. Me ya sa ita ba za a ga damuwarta ba? Ai itama tana da haƙƙi me ya sa ba za a bari a ji ta bakinta ba. Duniyar ne gabaɗaya ba ta mata daɗi, abinci ma Mami ce ta matsa mata ta karya saboda shan mangunguna amma yadda ta ji rayuwar ma ta fita kanta ba ta ƙi ta mutu ba. Baƙinciki take ji yadda duk yadda ta sadaukar da zuciyarta ga Hamma Lamiɗo ya kasa fahimtarta. A wannan halin da ta ke ciki ta ɗauka zai fi kowa fahimtarta. Rashi ta yi na uba da jaririnta amma bai damu da wanman ba har yana faɗin zai sake ta, shi ne zai kalleta ya ce zai sake ta in ta tuna da kalamansa sai ta ji ba ta ma son ganin shi, tunda dai shi ya kasa fahimtarta to kowa ma in bai fahimceta ba ba za ta damu ba. Ya sake ta ɗin ai ba mutuwa za ta yi ba. Ita tunda ta rasa uba ma da jaririnta in ta ƙara rasa wani ai ba mutuwa za ta yi ba. *Janafty* Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Hanan kuma tunda Shamsiya ta fita da ita take kuka, kuka har da hawaye da majina. A cikin mota ma kukan take yi duk ko da yadda Shamsiya da Gwaggo suke lallashinta ba ta yi shuru ba, su ɗin baki ne a gare ta in ta juya ta sake juyawa ta ga ba wanda ta sani sai ta sake fashewa da kuka. A motar Alhaji Sherif suka zo daman. Su matan suna baya gaba kuma Alhajin na tuƙi Habib da Baba Usman suna mazaunin gaba. Kukan take yi amma in Gwaggo ta miƙa hannu domin ta ƙarbeta sai taƙi yarda da ita har gwara ma Shamsiyan ta ƙamƙameta amma ba ta daina kuka ba. Habib ya kasa motsi idanuwansa sun yi jajir ta madubin gaban motan yake kallon Hanan kukanta ma daɗi yake yi masa zuciyarsa ta yi wani irin ɗumi ya rasa yanayin da yake ciki na farinciki ne ko na ɗimaucewa da sanin abin daman hasashe ne da yaƙini kawai amma ba shi da tabbas ɗin Ummu Salma ta haifi wannan cikin. In ya kalli Hanan sai Fargar jaji ya sake kama shi, lalle da ya zama cikin masu asara da ya yi sanadiyar zubewar cikin nan, da haƙƙin Hanan ba zai taɓa barin shi ya sake rayuwa cikin sukuni ba. Hajiya Sahura tana ta cewa Ubangiji mai yadda ya so, ashe dai cikin nan sai da ya zo duniya. Gwaggo na amsa mata da cewa Allah ya ce zai rayu ai bawa bai isa ya hana ba. Habiba na gefe tana ta taɓe baki tana hararan Shamsiya ganin yadda take wani zakewa a zuciyarta ta ce ai daɗin abin ma ba yarta ba ce, takaicinta ɗaya da ya kasance Yaƙinin Habib ya zama gaskiya ta so har abada kar ya samu abin da yake so. Gidan Gwaggo suka sauka gabaɗaya nan Gwaggo ta dinga kiran kannen Habib a waya tana faɗa musu su zo gida su ga ɗiyar Habib. An tasa Hanan a gaba ana kallo cikin birgewa da sha'awa ita kuma tana ta kuka. Shamsiya ce ta ɗauketa ta goyata da zani tana faman lallashinta. A ɗakin Gwaggo ana ta mayar da magana Baba Usman na faɗin bai taɓa zaton ahalin Ummu Salma suna da sauƙin kai haka ba. "Ai mahaifinta dattijon arziƙi ne. Mutumin kirki ne Allah ya yi masa rahama." Alhaji Sherif ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin" Ni da man na san cewa ba za su zubar da cikin ba, Habibu ka ga ikon Allah ko? Ka ƙara gode ma Ubangiji na son ka." Ya gama faɗa yana kallon Habibu da ya sunkuyar da kansa ya kasa magana domin wani farincikin ma ba a iya magana. "Nima haka na ce, Allah yana son shi da Rahama." In ji Gwaggo, dukkansu kuma suna mai sake yi ma Habib ɗin nasiha da kuma cewa ya lura da rayuwa, ga shi dai yana ganin abubuwan da suka faru "Ni uwar ce ma ta ba ni tausayi tana ta kuka." Hajiya Sahura ta faɗa domin da gaske Ummu Salma ta ba ta tausayi. "Nima sai da na yi mata ƙwalla, ga rasuwar uba ga shi kin ji an ce ta haihu ba rai, abubuwan ne suka yi mata yawa, sannan abin ne ya zo a lokaci ɗaya ni kaina ban taɓa tunanin za su kawo maganarka ba, tunda muna zuwa yarinyar ta shigo ko ba a faɗa ba ga kama nan da Habibu, shima kuma ya ki magana tunda yana ganin tunda shi ya ce ba ya so ba shi da ikon tambaya sai ga shi uwar ta ce a ɗauko ma na Hannatun. Sun yi mana karamci Ubangiji suma ya karrama su ranar gobe ƙiyama." Gabaɗaya suka amsa adduar Gwaggo da Amin Amin. "Tunda sun yi mana kara muma mu yi musu, ta yi kwana biyu kowa ya zo ya ganta ku mayar da ita wajen mahaifiyarta " Alhaji Sherif ya faɗa yana kallon Gwaggo ta amsa da in sha Allahu. "Ai ka ji mahaifiyar Ummu Salman ta ce a can Lagos suke zaune komawa za su yi." "Can uwar ke aure? Hajiya Sahura ta tambaya. "Ina jin can take aure, ai ɗan'uwanta take aure yaron sarkin Daura ne." "Ɗan Sarki? Hajiya Sahura ta sake faɗa da sigar tambaya. "E, ai shi Sarkin Daura ya taɓa auren ƙanwar ita mahaifin Ummu Salma ta haihu da shi suka rabu tun kafin ya zama sarkin ma, ni lokacin na sani tunda Habibu ya faɗa mini , yanzu kuma an ce shi take aure ban dai sani ba ko yana cikin mazan da muka gani a gidan" "Yana nan" Habib ya amsa a sanyaye "Yana nan wani fari dogo baya magana, domin har muka tafi ban ji ya yi magana ba." Received at 11:37Reactions: ❤ 3, 🥰 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Gwaggo ta ce ba ta kula da shi ba, Hajiya Sahura ta ce ai duk kusan yaran farare ne suna kama da junan su. Alhaji Sherif da Hajiya Sahura ba su jima ba suka tafi tunda mangariba ta yi Gwaggo na ta yi musu godiya. Baba Usman ma gida ya tafi amma Habiba na nan so take yi ta ga abin da zai faru a gidan sai ta ce ma Gwaggo anan za ta kwana sai da safe za ta koma gidanta Ai ko ta sha kallo, domin haka yan'uwa Habib ke tururuwan zuwa ganin Hanan washegari Hanan ta gaji ta daina kuka, Shamsiya ta yi mata wanka ta kuma dafa mata indomie da safe, amma har cikin dare ta tashi da rigima tana kiran sunan Mahma da Mami Shamsiyar ta goyata a daran ta kwana jijjiga Habib kuma bai yi barci ba, farincikin da yake ciki ya hana shi barci kwana ya yi yana kallon Hanan yana hawaye, yana cewa yanzu wannan yarinyar ɗiyarsa ce! Ya yi ma Allah godiya a fili da sarari bai san iyaka ba, bai ɗauketa ba domin sai ya ji ya kasa amma saboda kallo har ya haddace kamaninta Hanan ta sha ɗauka, ta shiga hannun wannan ta fita ta koma hannun wannan Kowa sha'awarta yake yi, kuma kowa in ya zo sai ya ba ta kuɗi ko wani abu, tun tana ƙiyuwa har ta dawo ta daina sai dai bin mutane da kallo, kowa mamaki yake yi ashe cikin da Ummu Salma ta fita da shi ta haife shi, ga Hanan sun gani a matsayin shaida. Hanan ta fara sabawa da Shamsiya tunda ita ke wahala da ita, sannan in Gwaggo za ta ɗauketa ba ta ƙiyuwa yanzu Habib kuma sai dai ya tasa ta kawai yana kallo Habiba ta gaji da ganin takaici ta koma gida ranar a wajenta Habib ya kwana ko tarin ta bai ji ba, ta saba ta dinga masa habaici da tijara amma ranar tunda ta shige ciki sai da safe ya ganta da alamun dai jikinta ya yi sanyi, ko kuma ba haka ta so ya faru ba. * BAYAN KWANA HUƊU. Ranar asabar misalin ƙarfe goma na safe Hamma Jibo ne da iyalansa ke ta haraman komawa Abuja. Gabaɗaya suna falon Ammah har su Hamma Abdullahi duk sun taho domin yin sallama dashi duk da jiya har wajen sha ɗaya na dare da shi da Hamma Abdulrahaman duk suna gidan. Ummu Salma na cikin ɗakinta duk hayaniyar da ake yi ba ta fito ba. Tun bayan abin da ya faru ta daina ma kowa magana ta daina hira ta daina dariya ko falo ba ta fitowa tana cikin ɗaki abinci sai dai Harira ko Mami su shigar mata da shi. A gidan ma su kaɗai ne ke shigowa in da take, Ammah ko ɓarayin ɗakin ba ta sake kallo ba, ballatana Umma Balki da ta ce ba ta da kunya itama ta fita bayanta kan abin da ta yi Mami ce kawai ba ta taɓa juya mata baya ba sai Hamma Saddam da shi Abdulrahim suma ɗin ta ji haushin su domin suna bayan Lamiɗo kuma duka maganarsu ta kira Lamiɗo ta ba shi haƙuri ne ita an kasa gane yanayin ta shi ne mai gaskiya ita ce mai laifi. Hamma Abdulrahaman kuma a gabanta jiya da Hamma Jibo ya kira ta da daddare yana yi mata faɗa ya ce ya so ne ma Lamiɗo ya kikkifa mata mari saboda ta yi rashin kunya. Duk a cikin abin da ya faru abu ɗaya ne ta yi nadamar shi maganganun da ta faɗa ma Ammah sune ta yi nadama kuma har haƙuri Hamma Jibo ya saka ta duƙa ta ba ma Ammah a jiyan Daga yanayin yadda Ammah ta amsa mata itama haushin ta take ji. "Ni ba ki yi mini komai ba Ummu Salama, kukana ɗaya ko wata ɗaya ba a yi da kasa ta shafe idanuwan Baffa ba amma har kin fara yi mini gaddama da nuna cewa ban isa dake da abin da kika haifa ba." Kowa laifinta yake gani an kasa samun mutum ɗaya da zai fahimci raunin ta? Sun manta itama mai rai ce tana da zuciya a kirjinta uba fa ta rasa a tsakani kwana biyu ta rasa jaririnta me ya sa ba za ta damu don za a raba ta da ɗiyarta ba a matsayinta na uwa bai dace a ji ta bakin ta ba? Sai kawai a yanke ma rayuwarta hukunci don ta ce ba ta amince ba sai kowa ya koma yana ganin laifinta. Kuka kawai take yi in ta tuna da rashin da Baffa yau da yana raye da duk haka ba ta faru ba ko da zai yanke hukunci ba zai yi kai tsaye ba sai da amincewarta ba zai yi mata dole ko tursasa ta ba. Har yau da Baffa da ke da kwana ashirin da biyar da rasuwa ta kasa gasgata mutuwarsa gani take yi kamar mafarki ne kamar tafiya ya yi zai dawo nan ba da jimawa ba Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 👍 1, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Duk da yadda yan'uwanta suka gasa fahimtar ta ya yi mata zafi, amma duk bai kai kwatankwancin abin da Hamma Lamiɗo ya yi mata. Ga kewar Hanan da ya yi mata rami a zuciya gani take yi kamar za ta rasa ta ne alhalin a lokacin ita kaɗai gare ta. Yadda suke da shi ta ɗauka zai fi kowa fahimtar halin da ta ke ciki. Ta rasa mahaifinta ta rasa jaririnta duk a lokaci ɗaya shin ba ta cancanci tausayawa ba ne? Abin da ya yi mata ya fi rashin Hanan zafi a zuciyanta. Shi ne fa ya buɗe baki a gaban mutane ya ce wai zai sake ta, ta koma wajen Habib in ta tuna ma da kalamansa sai ta ji kamar ta kurma ihu, komai zai faru tsakaninsu ba ta ɗauka a tsakanin ita da shi ma zai iya kallonta ya faɗa mata zai iya sakinta ba, ballatana a bainar nasi gaban kowa da kowa. Abin takaicin ma wai ta koma ma Habib, mutumin da ta tsana. Ai tunda ya gama da ita, itama ta gama da shi har gaban abada. Gwara ta mutu ba ta sake aure ba, in ta kama Hanan ɗin ta koma wajensa ko son yarinyar zai kasheta ta gwammace ta yafe ta har abada. Abubuwa biyun nan suka sake raunana zuciyarta suka tafiyar da sauran fatan ta ga cigaba da rayuwar farinciki. A daran ranar sai asuba barci ya kwasheta, kuka kawai take yi ga tunanin Hanan ta na can wani wajen za ta kwana ba ta san sau adadin nawa ta yi addu'an da Allah ya nesanta Hanan da Habib da zuru'an shi na har abada ba. Shi ya ce ba ya son cikin nan kuma akan shi ya yi mata wulaƙanci ya saketa sannan ya ce ta je da cikin baya so me ya sa Ammah za ta tusa masa abin da ya ce ba ya so ya bar mata? Don ya yi nadama ba ya nufin cewa ta sadaukar da Hanan ga nadamarsa in kuma wasiyya Baffa ce ta tabbata da shi ne ba haka zai yi ba duk abin da zai aikata ko zai yanke akan rayuwarta sai ya tuntuɓeta sai ya tabbatar da ta gamsu da niyyarsa amma daga Ammah har su Hamma Jibo ba wanda ya tsaya ya fahimceta kowa ita yake ganin laifinta. Sannan ga baƙincikin kalaman Hamma Lamiɗo da suka zame mata dalma, saboda haka ya sa ko sunan shi ba ta son tunawa, mutumin da a baya ko sunan shi ta ji sai zuciyanta ta yi rawa amma ban da yanzu da tuna sunan shi ma kaɗai na kara sanyata jin haushin shi mai tsanani ya kama hanya ya yi tafiyarsa bai yi mata sallama ba, bai kuma sake nemanta ba ko a waya haushinta ɗaya wato shi ma a ganin shi bai yi laifi ba ita ce ta yi masa laifi don ya ce zai saketa ta ce sai me? Ita ce yake jira ta kira shi tana ba shi haƙuri ita kuma a yadda ta ke jin zuciyarta ko za su dauwama a haka ba za ta ce ya yi haƙuri ba domin shi ya fara rusa yarda da amincin dake tsakaninsu. Gani ake yi kamar in ya rabu da ita wani abu ne, a yadda take jin kanta da yadda duniyar ta fita kanta ba za ta taba damuwa don Hamma Lamiɗo ya sake ta ba. Haushin shi da take ji yasa ta ji ba ta son shi yanzu, ko ya sake ta babu abin da za ta rasa domin ita an gama yi mata rashi a duniya. Har jiya da aka zauna zaman meeting din da Hamma Jibo ya haɗa a daran an kira Hamma Kabiru a waya aka saka a amsa kuwwa tana ji yana faɗin ya so Lamiɗo ya sake ta da gaske ya ga yadda za ta ƙare. Cikin izza yake faɗin ba za ta samu wanda yake ƙasa da shi ba kamar ma kuma ya yi mata nisa ta yi kuka sosai hawayenta har da majina kowa ita yake gani a matsayin mai laifi shi da ya fara furta kalaman shi bai yi laifi ba sai ita da ya mayar ma martani, ba zununci ba ko menene sai da ya lalace za ta nuna ma kowa Lamiɗo ba don shi aka haife ta ba, shima ba don ita ya zo duniya ba kowa ma zai iya rayuwa ba ɗan'uwansa kuma ya zauna lafiya. Hamma Jibo ya yi maganganu sosai barin ma ita ya yi mata nasiha haƙuri sannan daga ƙarshe shima ya ce ta kira Hamma Lamiɗo ta ba shi hakuri haka ma su Hamma Abdullahi duk suka ce har da Mami, su suna ganin ita ce ba akan gaskiya ba jin su kawai take yi ba za ta ba shi hakuri ba domin ba ita ta fara maganar ba shi ya fara. An yi maganar in Baffa ya yi kwana arba'in da rasuwa Umma Balki za ta koma gida, wa zai zauna da Ammah? Tunda zaman shurun ba daɗi, ita cewa ma take yi za ta iya zama ita kaɗai. Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Umma Balki ta ce bayan arba'in ɗin za ta je ta duba gida sai Umma A'i ta zo, ta yi ko da sati biyu ne ita kuma sai ta dawo su dinga karɓa karba kafin Ammah ta fita takaba, sannan ga Ummin ikki ma da kullum tana zuwa. Maganar girki kuma Hamma Jibo ya ce za a ɗauki yar aiki Umma Balki ta ce ba sai an ɗauka ba, za ta iya yin komai da kanta. Hamma Abdullahi ma ya ce matayensu da yaransu za su dinga leƙowa akai akai saboda kar gida ya yi shuru. Daga karshe aka tsaya da sai Ammah ta fita takaba za a yi maganar raba gado. Da gaske kenan Baffa ya rasu! Tunda ga shi ana maganar rabon gado. Mutuwar Baffa mutuwa ce mai zafi ga iyalansa amma a wajen Umma Salma ba a taba mata wani abu da ya daketa da zafi irin mutuwar Baffa ba, ko lokacin da Habib ya saketa ashe abin da ta ji a lokacin wasa ne yanzu ne ta ke jin raɗadin abin da hausawa ke faɗin wasa farin girki. * Ta yi niyar ba za ta fito ba, ba ta san ma wani ya yi mata magana amma kudirinta bai cika ba twins Hassan da Hussaini da su Ammi suka shigo suna yi mata sallama. Sai ga Saudat itama ta shigo tana faɗin Anty Ummu za mu tafi. Ba a son ranta ba, yaran suka sanya ta fitowa sai ga shi sun haɗe da Adda Nauwara a falo tana ganin ta ta hau yi mata tsiyan ta ɗauka har su tafi ba za ta fito su yi sallama ba. Ummi ikki ta gani ashe ta zo, ta gaisheta ta amsa tana kallonta. "Kullun fuska a kumbure Ummu Salma, ko uwar taki ba ta gasa ki da ruwan zafin ne? Ummu Salma ta yi shuru ba ta yi magana ba. Kanta na kasa tana wasa da Hannun Isma'il da ya riƙe ta. Tana sanye da hijabinta dogo har da safa tunda Mami ta hana ta zama ba safa hijabi kuma tun dawowarta asibiti take yini da shi barci ne kawai ke raba ta da shi. Ammah da Mami tare da Umma Balki duk suna falo, mazan ne suna tsakar gida. "Ba dole ki ga fuskarta kullum a sumtume ba, ba ta da aiki sai shigewa ɗaki tana kuka, kin ga ko ai yanzu idanuwana da fuska suka fara kumbura in dai kuka ta mayar abin yin ta." Umma Balki ta faɗa tana hararanta, ba ta kuma yi magana ba Mami ce ke amsa mata da cewa ta fa daina kuka. "Kar ma ta daina yarinya daga faɗa mata gaskiya, sai rashin kunya sai fushe fushe. Kin ba ni kunya Ummu Salma ban za ci haka kike da taurin kai ba, to shi Lamiɗon ma ya yi fushi ya yi tafiyarsa gidansu ki ci kan ki." Umma Balki ke ta faɗa ta in da take shiga ba ta nan take fita ba. Mami na tare mata aka haɗa da ita. "Auta ki daina haka kin ji ko? Ba ki kyauta ba, Ki kira shi ki ba shi hakuri, har yar'uwan ta ki ma ta yi fushi dake yau ma na ce ta zo mu je ta ce ba za ta je ba." Ummu Salma ta kalli Ummin ikki amma ba ta yi magana ba. Wai har da Baɗɗo a masu jin haushinta. Kar ta zo ta je itama ta yi ta fushin tunda itama ta kasa fahimtar yanayinta. Shi ya sa ba ta son fitowa saboda ba ta son magana, ranta baci ma yake yi. Sai da su Hamma Jibon za su tafi ne ta fita tsakar gida Harira da Islam sune masu ɗaukan kaya zuwa haraba Hamma Abdullahi ne zai kai su filin jirgi. Faruk take kallo yana ta bin bayan Islam da gudu yana rigiman sai ta ba shi wata karamar akwatin da ta ɗauka Hanan kawai ke yi mata gizo yau kwana huɗu ba su dawo da ita ba. Ita abubuwa da dama ma gizo suke yi mata tunda ta dawo daga asibiti, sai ta ga abu kamar wani abu dabam, ranar fulas ɗin ruwa zafi ganin shi ta yi kamar tunkuya abubuwa dai suna sauya mata a idanuwanta tun bayan fardaɗowanta daga asibiti kuma ta kasa faɗama kowa to waye ma zai saurare ta? Kowa na jin haushin ta wanda ta ke zaune domin shi bai damu da ita ba cewa ma ya yi zai sake ta. Gabanta faɗuwa yake yi in ta tuna cewa wataƙila gidan su Habib su ƙi dawowa da Hannan da ko mai zai faru sai dai ya faru amma sai ta karɓo yarta ba za ta bar musu ita ba har abada. A tsakar gida ta tsaya da rakiyar ta yi komawarta cikin ɗaki bayan Hamma Jibo ya jadadda mata ta kira Hamma Lamiɗo ta ba shi haƙuri ta amsa da to amma a zuciyan ta ce shi ya kamata ya ba ni hakuri ba ni ce zan kira shi ina ba shi hakuri ba. Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Baɗɗo ma ta daɗe ba ta yi fushin ba itama ba ta ga laifin da ta yi mata ba, akan gaskiyanta take ai ta san fushi ta yi domin tun ranar ba ta dawo kuma ba ta kira ta a waya ba, itama ba ta kira ta ba. Tunda Baffa ya rasu ta rasa jarrinta taurin zuciyarta ya karu ba ta jin taushi taushi, ta san tana da taurin kai a baya amma yanzu ya yi ƙamari tana ji ko za a yi tashin ƙiyama ne ba ta yarda a ce ita ce ke da laifi ba shi ya sa ko kaɗan zuciyarta ba ta rusuna ba. Wanda zai yi fushi da ita ya daɗe bai yi ba. Tafiyar Hamma Jibo da iyalansa sai gida ya yi shuru. Hamma Abdullahi daga kai su filin jirgi ma bai dawo ba, Saddam kuma ya fita Hamma Abdulrahim ne kawai muka yana bangaren su. Harira ta shigo ta gaisheta tana tambayanta ko akwai abin da za ta yi mata, yan zannuwanta da take sawa da dogayen riguna ta ce ta kwashe ta ɗan wanke mata. Bayan fitan Hariran ne Mami ta shigo ɗakin ta ba ta waya Daddy ne ya yi mata ya jiki suka gaisa shi yake faɗa mata ba zai samu zuwa ba tafiya ta kama shi zuwa Lagos amma gobe Mami da su Islam za su bi jirgi su koma Kaduna tunda duk sun koma makaranta. Bayan sun gama wayar ne ta miƙa ma Mami wayarta. Ta karɓa tana kallon ta kur kamar tana nazarinta, ita kuma tana kwance ne daman lokacin da Mami ta shigo sai ta ɗan zauna a saman gadon ta cire hijabin jikinta doguwar rigar atamfar dake jikinta ta bayyana kanta akwai hula amma ana ganin gashin ta, a tsefe yake ta so ne in suka zo nan a yi mata kitso to ba kwanciyar hankali, ga rasuwar Baffa ga abin da ya same ta, gashin duk ya yi biji biji. Mami ta faɗa mata cutar da ya kamata, har goggle ta yi na cutar ta yi daga nan ta san tana da sauran kwana a gaba ne, amma cutar tana da hatsari ga mata masu ciki. "Yaushe ne za ki koma ganin likita? Mami ta katse shurun da ya gifta a tsakanin su, itama yanzu Ummu Salma ba ta mata hira in ba ita ce ta tsare ta da magana ba. "Ranar monday ne jibi." "Kuma ga shi gobe za mu tafi, ke da wa za ku je? "Ni kaɗai, Harira za ta raka ni." "Baɗɗo fa ko kuma Umma Balki ta raka ki." Mami ta faɗa tana kallonta. "To." Kawai ta ce tana kauda kanta. Ba haushin Mami take ji ba kawai itama ta san tana bayan masu cewa ba ta kyauta ba. E ta san maganganun da ta faɗa ma Ammah ba ta kyauta ba, wannan ta yarda ta kuma karɓi kuskuranta amma a kan maganar Lamiɗo tana da ja akan masu cewa ita ce ta yi masa laifi. "Ummu Salma." Mami ta kira sunan ta lokaci ɗaya tana matsawa kusa da ita har tana riƙo hannuwanta. "Ɗago ki kalle ni nan." Ta ɗago idanuwanta tana mai kallon Mami. "Ki yi haƙuri ki daina damuwa. Baffa addu'a za mu yi ta masa, maganar Hanan kuma ki kwantar da hankali babu wanda ya isa ya karɓe ta daga hannun ki." Idanuwan Umma Salma suka kawo ƙwalla suka kece mata a saman kumatunta. "Mami yau kwana huɗu amma ba su dawo da Hanan ba." "Za su dawo da ita, in ma ba su dawo da ita za a je a ɗauko ta." Mami ke share mata hawaye da tafin hannunta. "Ke da za ku koma Lagos da zaran Muhammadu ya dawo, tare da ɗiyar ku za ku koma in sha Allahu.'" Hankalinta ya ɗan kwanta ta tabbata koma me zai faru Mami tana tare da ita. Ba za ta koma Lagos ba sai Hamma Lamiɗo ya janye kalamansa in kuma bai janye ba ta rantse da wanda ranta ke hannun shi ba za ta bi shi ta koma ba. Mami ta sake lallashinta da cewa ta sake zuwa ta samu Ammah ta sake ba ta haƙuri. "Ko ɗazu da safe ma na shiga na gaisheta dakyar ta amsa gaisuwa ta Mami." "Ki sake zuwa ki ba ta haƙuri abin ne ya dame ta." "Mami nima fa ba a kyauta mini ba." "An ji ke ma ba a kyauta miki ba, amma ke ce ƙarama ke ce ba ki da gaskiya." Sai kawai ta yi shuru. "Uwa ce ita, duk wanda zai so ki da cigaban ki bayan ita ne." "Haka ne." "To ki sake zuwa ki same ta daga ke sai ita, ki sake ba ta haƙuri." Ta amsa da to za ta je. "Shi Lamiɗon kin kira shi? "E bai ɗauka ba." Ta yi ma Mamin ƙarya domin ita dai ba za ta kira ba. Kawai sai Mami ta ɗau wayarta tana cewa bari ta kira shi. Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ummu Salma na zaune ko fargaba ba ta yi domin ta san halin shi ba zai taɓa cewa ba ta kira shi ba a e ɗin shima zai tafi. Wayar a amsa kuwwa Mami ta saka tana fara ringing ya danna mata busy har tana tunanin ko yana cikin mutane ne sai ga kiran shi ya shigo ta ɗaga. Muryan shi tarai, muryan da kan sanya Ummu Salama kasala da shauƙi a baya ban da yanzu. Suka gaisa da Mami da tambayan mutanen gida. "Yaushe za ka dawo? "Da zarar Mai martaba ya ta shi zuwa London' Ya amsa mata cikin yanayin maganarsa. Mami ta tambaya da cewa daman bai tafi ba? Sai ya ce sun samu tsaikon Visa ne ta yi fatan alheri. Suka yi shuru dukkansu ba wanda ya yi magana. Shi da man ba gwanin ɗago magana ba ne ko da akwai maganganun a bakin shi. "Ɗiyata ta ce ta kira ka, ba ka ɗauka ba? Sai ya yi shuru kamar bai ji ba sai da Mami ta sake maimaitawa. "Ban lura da kiran na ta ba Mami." Ya amsa kai tsaye amma a ƙasan zuciyarsa yana tunanin ko lokacin haihuwar nan Ummu Salama ta samu natsala ne? Shi dai yana ganin she is not okay. "To ta kira ka ne ta ba ka hakuri kowa a gida ya ce ba ta kyauta ba. Amma kai ma ba zan fasa faɗa maka ba ka kyauta ba koma me ya faru ai ka duba yanayinta lallashi take buƙata ba faɗa ba." "Mami." Ya kira sunanta ta amsa. "Ni cikin ɓacin rai na yi maganar da na yi, amma Mami Ummu Salama ta kyauta mganganun da ta faɗa ma Ammah? Ta kyauta abin da ta yi? Ya faɗa a jere daga ji yana ƙokarin sarrafa fushinsa ne "Ba ta kyauta ba, kowa ma ya faɗa mata kuma ta karɓi laifinta kuma har ta ba ta hakuri ma." Ya yi shuru kawai bai yi magana ba. "Kai ma sai ka yi haƙuri, kai ne babba. Ka lallasheta domin tana bukatar hakan." "I will." "Amma ni ma mganganun da ta faɗa mini ta kyauta? "Ba ta kyauta ba, za ta ba ka hakuri." "Better." Ummu Salma na zaune haushi duk ya isheta har wani better ya ke faɗi tunda an ce za ta ba shi haƙuri to ya cigaba da jira. Maganar komawarta asibiti Mami ta yi masa ya ce zai kira Ummu Salman za su yi magana ya tambayi ko an dawo da Hanan? "Ba su dawo da ita ba, in ba su dawo ba za a je a karɓota ai kana dawowa za ku koma Lagos ɗin ko? Ya amsa da in sha Alllahu ya kara da cewa shima hutunsa ya kare ga yara ma sun koma makaranta. "Bilkisun fa? "Tana nan tare da ni." Ya amsa ma Mami, sannan ya cigaba da faɗa mata daman bayan sun gama biki a garin Abuja Kano ta koma, daga Kanon ne jiya ta zo Daura ta same shi gabaɗayansu tare za su taho nan Adamawa. Yanzu akwai sakin jiki tsakanin Lamiɗo da Mami, sai su ɗau lokaci suna magana a waya ma ba su sani ba. Ummu Salma kuma haushi ya turniƙeta, wato ma matarshi na can tare da shi, ita ce ya gasa ma maganganu ya yi tafiyarsa. Ta ɗauka Mami za ta yanke wayarta ne amma kawai sai ta ga ta miƙa mata tana ce masa ga Ummu Salma ma su yi magana ta karɓa saboda Mami ce, a gabanta ta yi masa sallama ya amsa a ginshiƙe kamar ba zai yi magana ba. Allah ya taimaketa Mami ta ba su waje, tana fita ko ta yi zaraf ta kashe wayar, saboda ma an ce za ta ba shi hakuri dakyar yake amsa sallamanta. Ya sake kiran wayar Mami ta ƙi ɗauka baya nan itama ya kirata sau biyu a wayarta ma ba ta ɗauka ba sai hararan wayar take yi tana sakin tsaki ita kaɗai. Can ba jimawa sai ga saƙon shi. "Umma Salama." "Pick the Call." Ko buɗe sakon ba ta yi ba ta sreen ɗin wayarta ta hango shi kuma ba ta ɗauka ba ko da ya sake kira sau ɗaya daga nan kuma bai ƙara kira ba. Mami na dawowa ta miƙa mata wayarta ta yi mata ya ce zai kira wayarta su yi magana. "Yauwa ko ke fa, yanzu maganar kayan gyara za mu yi bari na kira Hajiya Falmata na ji yadda za mu yi" Da za ta iya da ta ce ma Mami kar ta ba kanta wahala. Ita ta daina yi ma namiji wannan rawan jikin duk ba yan goyo ba ne halin su saya. Nan jaririn Hamma Lamiɗo ne a cikinta wajen haihuwansa ta kusa mutuwa amma bai damu da ita ba har a yanayin yake cewa zai sake ta maza yan kutumar uba ne, ta yadda da maganar hausawa da suke cewa namiji ƙañin ajali. Namiji hankaka gabansa fari bayansa baki, namiji dafin shi ya fi dafin kunama namiji kuma ba ɗan goyo ba ne. Received at 11:37Reactions: ❤ 7, 👎 1, 👏 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Lokacin da ta auri Habib tana ganin za ta goya namiji, sai ga shi da ta goyasa ga tozarcin da ya biyo baya, a lokacin tana ganin ta gama bama wani namiji yarda amma Hamma Lamiɗo ya mantar da ita wannan har take ganin namiji ɗan goyo ne sai da ya yi mata wannan abin ta fahimci shegu duk halin su ɗaya ta ɗauko ko a cikin maye ba zai iya cewa zai sake ta ba. Kalamansa sun munana a wajenta, tunda kuma ya furta an ce magana zarar buni ce ta fita ba halin ta koma. Tunda maganar nan ta fito daga bakinsa shike nan take ganin baƙin sa. Tana jin Mami ta kira Hajiya Falmata suka gama magana. Tana faɗa mata za ta siya mata babban package na maganin sanyi, da na haɗin maijgo a wajen Surayya Halin yau 080322773332 Bojuwa zuwa jibi sako zai iso ta fara amfani da shi kafin su koma Lagos, ta cinye kaza da ciccibinta anan da kayan sanyi, na garin kuma ta tafi da su. Ta amsa da to kawai, amma a zuciyarta ta ce ba za ta ci ba ko da an kawo. Domin ita a yadda take jin zuciyarta ba za ta iya yin wani abu da sunan wani gyara ba. Lafiyanta take nema da tunanin ma za ta sake ɗaukan cikin? Ko kuma a wannan karon za ta haihuwa lafiya?ga shi dai an yankata sau biyu a waje ɗaya bawa bai isa ya guje ma kaddaransa ba. Tana tunanin haka sai wata zuciyar ta ce kin manta kin ce ba za ki koma ba? Sai kuma ta amsa ma da kanta za ta koma in dai ya fara yin nadaman kalamansa ya bata haƙuri kuma ya janye su za ta iya yi masa afuwa ta bi shi su koma tare amma in dai bai yi haka ba sai dai kowa ya ga baƙinta ba za ta koma ba. Ba ta furta ma kowa abin da ke zuciyarta ba. Amma za ta aiwatar da kudrinta sai dai a kore ta a gidan tunda ta fahimci kowa Hamma Lamiɗo yake goyon baya. Washegari ma kafin tafiyarsu Mami haka ta yi ta mata faɗa, ta daina damuwa saboda halin da take ciki ta ce za ta daina. Tafiyar Mami sai ya kara sa gidan ya zama shuru ba Faruk ba Islam. Duk da Mamin ta ce za ta dawo nan ba da jimawa ba. Mami na tafiya ko sauka ma ba su yi baa direba ya kirata tana da saƙo daga Kano. Ta san saƙon maganin nan ne sai kawai ta tura masa lambar Saddam, ta ce Direban ya kira shi zai karban mata saƙon in sun shigo gari. Da yamma da Saddam ya shigo gidan yake tambayanta tana da sako ne daga Kano am kira shi ta ce e na ta ne. Gida ya yi tsit Allahu Akbar babu Baffa ba ta ma san fita tsakar gida saboda sai ta ga kamar za ta gan shi ya fito daga cikin ɗakin shi, ɗakin ma yana kulle ne Ammah ma ba ta son shiga, wataƙila yana tuna mata da Baffa ne. Ba su da matsalan komai, kayan abinci a store sai ya shekara, kafin tafiyan su Hamma sun ajiye komai, ko ruwa katan katan ne ba adadi ga lemu, sun yi cefane ga kudi masu yawa da suka bari har gobe ma kuɗin da Masarautar Daura ta ba da ko rabi ba a taɓa ba Daddy ma ya ba da kuɗi mai yawa, haka ma Mami da za ta tafi. Baffa ne kaɗai suka yi rashi amma komai na rayuwa babu abin da babu shi a gidan nan amma gidan kowa ka gani babu karsashi. Harira ita ke taimaka ma Umma Balki da wasu ayyuka tunda tana da ƙokari sosai. Ranar monday da safe ita da Harira suka tafi asibiti. Hamma Saddam ya kai su, Hamma Abdulrahim ya tafi wajen aiki. An yi mata cheekup, babu wata matsala mikin ta ma yana warkewa B.P ɗinta ne dai ya yi sama likita na ba ta shawaran ta daina tunani sannan ta dinga samun ishashen barci, kuma da gaske ne a kwanakin ba ta samun barci sosai ya sake rubuta wasu magungunar suka siya a cikin asibitin kafin su tafi, da ATM ɗin ta, ta yi amfani na Hamma Lamido ba ta taho da shi ba, ba shi kan shi ba duk abin da ya danganceta haushin shi take ji. Daga asibitin ma tasha Saddam ya wuce suka karɓo saƙo kaya ne mai yawa har na mota Mami ta biya. Baiwar Allah tana son ta, so mara algus Ubangiji ne kawai zai saka mata. Sai da suka koma gida ta kira Mami a waya ta faɗa mata saƙon ya iso. "To sai ki fara amfani da shi ai na san jinin ya ɗauke ko? Mamin ta san jinin ya ɗauke tun sati biyu da haihuwar, amma take sake tambayata ta ji kunya ta kasa amsa mata. "Kina da lambar mai mganin ko? Ki yi mata bayanin ke ce mai wannan saƙon ta yi miki bayanin yadda zaki yi amfanin da komai." Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 👍 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta amsa da to, domin ba za ta yi gaddama ba. Amma yadda Harira ta shigo da ledan ta tura ta can bayan gado ba ta ƙara ma kallon su ba, ballatana ta yi tunanin cire su daga cikin ledan. Ita abin da ke gabanta ta ga ɗiyarta ta dawo ga shi yau sati amma shuru har wajen yamma ba su dawo da ita ba. * Ta damu matuƙa ta ga kuma ba wanda ya damu a gidan Ammah ce da Umma Balki ta san tana yi musu magana sai faɗa ya dawo sabo daman daƙyar ta samu Ammah ta fara amsa gaisuwanta cikin sakewa. Bayan ta sake ba ta haƙuri ta nuna nadamarta. Itama dai daga karshe cewa ta yi ta kira ɗan gold ta ba shi haƙuri ta yanka ƙarya ta ce tuni sun yi magana ma an wuce wajen ahalin tunda ya kira ta ba ta ɗauka ba. Bai sake kiran wayarta ba, itama daman ba niyar nemansa a zuciyarta Har bayan mangariba shuru haƙurinta ya gama ƙarewa za ta fita ta je har gidan su Habib ai ta san gidan a anguwan Doubeli ne, ko mai zai faru in dai ta dawo da Hanan sai ya faru daga baya. Ta yi tunanin tafiya ita kaɗai sai ta ga ba mafita ba ne. Ta kira Baɗɗo ita ta ma manta wai suna fushi da juna ne, kamar Baɗɗo ma ba za ta amsa wayar ba sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga wayar tana amsa mata magana a ciki a ciki. Tana kan darduma ne daman bayan ta idar da sallar mangariba "Baɗɗo za ki iya zuwa gida yanzu? "Me zan yi miki? Ta amsa mata a yangance "Raka ni za ki yi wani waje." "Ina kenan? "Gidan su Habib, zan je na dawo da Hanan ne yau sati ɗaya ba su dawo da ita ba kuma na ga ba wanda ya damu ballanta ya yi magana." "Mtsewww Ba zan je ba, ki je ke kaɗai." Daga haka Baɗɗo ta katse wayar ta bar Ummu Salma bakinta a buɗe sai a lokacin ta tuna sun rabu ba daɗi yau sati ɗaya kenan, idanuwanta ya rufe ta ma manta da wannan da ta tuna ba za ta kira ta ba "Ai zan iya zuwa ni kaɗai." Ta faɗa a fili tana mikewa tsaye darduman da ta yi salla ta ninke, ta ɗau karamar jakarta a saman madubi ta ɗauki kuɗi duk wanda ya tambayeta za ta faɗa masa in da za ta je ba amfanin kuma ɓoye ɓoye. Hijabin jikinta take sauyawa, ta ɗauko gogagge a cikin wardrope. Ta ji ana amsa gaisuwa a falo kamar wasa ta ji Ammah na kira sunan Hanan itama ta ji karaɗin muryanta. Da sauri ta nufi falon, tana zuwa ko ta ga Hanan a jikin Ammah sanye da doguwar riga na atamfa ba ma cikin kayanta ba ne har sabon kitso an yi mata ga wata leda a hannunta sannan ga wata teedy na wasa a ɗayan hannun nata. Umma Balki na ta cewa maraba da Hannatu. Shamsiya na zaune a ƙasa da hijabi a jikinta gabanta kuma jakar kayan Hanan ɗin ne da suka tafi da ita. "Hanan. " Ta kira sunan ta da wani irin farinciki, a muryanta. Hanan ta juya ganin uwarta, da gudu ta tashi daga jikin Ammah ta nufe ta, da murnan ganinta. Tana zuwa Ummu Salma ta duka ta ɗaga ta sama. "Hanan sai yau? Ummu Salma ta tambayeta tana dariyan farinciki dariyan da tun tafiyan Hanan ba ta yi irin shi ba. Ammah da Umma Balki na bin ta da kallo har da Shamsiya dake ta mirmishi. "Mahma Anty ta kai ni kiso " Ta ke faɗa tana nuna mata kanta, ta sha cuko duk an bishi da duwatsun yara. "Abba ya siya mini Baby." Ta sake faɗa tana mata Teddy dake hannunta. "Anty ta siya mini sweet." Wannan karon sai da ta nuna Shamsiya sannan ta ciro sweet da yawa daga cikin ledan hannunta. Haushi ya kama Ummu Salma Anty, Shamsiyar ce Anty kenan Habib Abba. Takaici ne kawai ke murkurkusanta amma ganin Hanan sai kamar ana rage mata zafin zuciya. Cewa kawai ta yi ta gani da fatan ta ce musu ta gode ta ɗaga kanta. Sauketa ta yi ta nufi Ammah tana nuna mata sweet ɗin hannunta ta ba ta, Umma Balki ta ce itama a ba ta nata sai ta ɗibo biyu ta ba ta. "Son kai, na kakarki ya fi nawa yawa." Ta faɗa tana dungure ma Hanan din kai ta ko maƙale kafaɗa kamar ta san abin da ake yi. Ammah na mirmishi, Umma Balki na fadin yarinyar nan akwai wayau. "Sosai kowa fa mamakin wayaun ta yake yi ga zence a bakinta haka Babanta ya ce wayanta ya girmi shekarunta." Shamsiya ta amsa tana mirmishi. Ammah ta amsa da cewa Hannan ai akwai magana. Ummu Salma na tsaye tana jin Shamsiya na ba da haƙurin ba su dawo da Hanan da wuri ba Received at 11:37 4 people reacted with ❤ [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "A yi haƙuri babanta ne ya ce a ɗan tsaya ya samu kuɗi ya yi mata y'an siyayya." Kallon ta kawai Umma Salma ke yi in ta ce babanta sai ta ji zuciyarta ta yunkuro. "Ba komai, ai da yake ma baban nata na nan bai dawo ba. Sai ya dawo ne za su tafi." Umma Balki ce ke bayar da amsa. Shamsiya ta ce sun gode sosai Habib ya na kofar gida ya ce a miƙa masa godiyar sosai. Ammah da Umma Balki suka ce ba komai "Da yake a can Lagos ɗin take makaranta amma in sun samu hutu su ka zo za a dinga kawo ta in sha Allahu." Bakin Shamsiyar har kunne tana ta godiya. Hanan kuma har ta fita tsakar gida in da Harira ke zaune a saman tabarma. Ummu Salma ta juya za ta shiga ciki sai Shamsiya ta miƙe ta ce tana son za ta yi magana da ita. Ko amsa ta ba ta yi ba, ta wuce ciki yanzu kam hankalinta ya kwanta magana kuma babu sauran wata magana a tsakaninsu a yanzu. "Bita ciki mana." Umma Balki ta yi ma Shamsiya magana sai ta ɗaga kafa ta bi bayan Ummu Salma har zuwa cikin ɗakin da ta san na Umma Salma ne tun tana budurwa ɗakin da ta kan zo su yini suna hira. Amma yau ɗakin ya zama baƙon ta. Lokacin da ta shiga Ummu Salma na tsaye a gaban madubi kuɗi ta mayar a cikin jakarta sannan ta koma ta zauna a gefen gado ko kallon Shamsiya ba ta yi ba. Ita kuma a ɗarare take, ta kasa zama tana tsaye daga jikin ƙofar ɗakin. "Umma Salma." Ta kira sunanta a sanyaye. Ta kalleta amma ba ta amsa ba. "Daman ina so na sake ba ki haƙuri kan abubuwan da suka faru a baya ne." Sai ta ɗan dakata ta jan fasali tare da kallon yanayin Ummu Salman. "Don Allah ki yi haƙuri ki manta baya, Hanan ta riga ta haɗa mu ba yadda muka iya." Wani kallo Ummu Salma ta watsa mata amma ba ta yi magana ba. "Ba don ni ba don Allah, ki yi ma Hanan kara ki ba ni lambar wayarki " "Saboda mene? Na ce na yafe ba buƙatar haka." Ummu Salma ta faɗa tana kallon ta. "Akwai bukata mana, saboda mu dinga gaisuwa da ke da Hanan gabaɗaya." "Don Allah." Yadda take yi mata magiya ya sa taka sa musa mata. Ta fara karanto mata lambar Shamsiya na lodawa a cikin wayarta. "Na gode sosai." Ta faɗa hawaye na taruwa a cikin kwarmin idanuwanta. "Ko da ba za mu koma da amintar mu ba. Don Allah ki daina jin haushina." Ta kalleta amma ba ta yi magana ba. "Zaman Hanan tare da mu na kwana bakwai kamar shekara bakwai ne a wajen mu, ta wanzar mana da farinciki sosai yan'uwa sun ganta kowa ya yi murna. Habib na son yara an jarabesa nima ina son na haihu ga shi da kamar wuya tunda ko na samu cikin baya kai labari yake ɓarewa." Ta gama faɗa tana sharan kwalla. "Don girma Allah kar ki yi mana katanga tsakanimmu da Hanan, har abada taki ce ba wanda zai raba ki da ita. Amma muma ki yi mana alfarman aron ta na wani lokaci duk sadda damar haka ya zo" Ummu Salma ta kalleta yadda take hawaye sai ta ba ta tausayi. Ta san ya zafin ka ɗauki ciki ka rasa shi yake. "Ba damuwa." Yadda Shamsiya ke yi mata godiya kamar ta ba ta duniya. Nan take ta kira ta a waya sai ga lambar Shamsiyar ta fito ita ce dai lambarta tun na baya tana ganin lambobin ta gane sun yi amimta har ya sa ta haddace lambar Shamsiyar a lokacin baya. "Ga lambata nan ki yi saving don Allah." Ummu Salma ta ce za ta yi, Shamsiya ta yi mata sallama da cewa za ta tafi Habib na can kofar gida yana jiran ta. "Ki gaida gida." Kawai Ummu Salma ta iya cewa. Sai Shamsiya ta ɗan waiwaya tana kallonta. "Habib ya ce na sake ba ki haƙuru." "Ya wuce" "Mun gode sosai." Har ta juya za ta fita Ummu Salma ta kira sunanta. Ta juyo tana amsawa. "Ke ma Allah ya ba ki haihuwa" "Amin na gode sosai." Ta amsa hawaye na kace mata. Da a ce baya za ta dawo da watakila suna nan da ƙawancen su da Ummu Salama amma yanzu abubuwa sun sauya har abada ba za su taɓa komawa kamar baya ba Haka ta fita falo ta yi ma su Ammah Sallama a tsakar gida ta ga Hanan ta yi mata Bye bye ta ga Harira sai ba ta damu da Shamsiyar don za ta tafi ba haka ta fita tana waigen Hanan kamar ta sake ɗaukanta su koma tare A ƙofar gida ta ga Habib jikin get ɗin in da ta bar shi yana jiran ta. "Na fito" Received at 11:37 8 people reacted with ❤ [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta faɗa tana yin gaba ba ta so ya ga tana kuka shi kuma ya riga ya gani. Bayanta kawai ya bi, shima yana ji kamar ya koma ya ɗauko Hanan amma babu daman haka, kwaannta bakwai tare da su amma kamar shekaru haka yake kallon kwanki nan. Kwana bakwai kawai ta shiga ransa yarinyar nan da zai iya ba da komai saboda ya kasance da ita rayuwarsa a cikin kwana bakwai ta yi sauyi mai yawa a cikin kwana bakwai kawai ya tsinci kansa cikin tsananin farinciki. Hanan ga hira sannan Bakuntar kwana ɗaya zuwa biyu ta yi musu daga nan ta saki jikinta. Shamsiya tana son Hanan ta shiga ranta sai ya ji da yana da iko da ya ba ta rijon Hanan na har abada amma ina ya rasa wannan damar na shi a matsayin shi na uba tun lokacin da ya furta baya son cikin nan yanzu kuma bayan an haifi ciki ba shi hurumin yanke wani hukunci sun gode ma da aka ba su damar sanin akwai Hanan da ba su damar zaman da ta yi da su har na tsawon kwana bakwai amma ji yake yi kamar jiya ne ta zo yau za ta koma ƙunci yake ji a zuciyarsa na kewar Hanan Haka ma Shamsiya, har suka hau adaidaita ba ta daina kuka ba Bai ce mata komai ba sai da suka koma gida ta shiga ɗaki ta kwanta a saman gado tana ta kuka. "Cewa suka yi ba za su sake kawo mana ita ba? "Aa Ammah ta ce in dai suka samu hutu suka zo garin za su kawo ta." Ta faɗa tana share hawayenta. "To kuma mene ne na kuka? Hakuri za mu yi gabaɗaya." Ya faɗa yana zama a gefen gadon. "Kukan nadama nake yi, da a ce ban ci amanar ƙawata ba da kaddaran rayuwata bai fara ba. Da kana tare da matarka da Hanan har ma da wasu yaran cikin farin ciki. Nima da watakila na yi aurena ina tare da mijina da ya'yana cikin farinciki." Sai ta ba shi tausayi ya dafa hannunta yana faɗin. "Haka Allah ya so, sai mu yi hakuri mu ce mun gode." Hawayenta sun ƙi tsayawa shi ke share mata yana lallashinta. Ce mata yake yi ai mun tuba, tubar mu zai saka Ubangiji ya ba mu abin da muke so Hanan kuma tana tare damu har abada. *Janafty* Received at 11:37Reactions: ❤ 5, 👍 2 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Baɗɗo ma ta daɗe ba ta yi fushin ba itama ba ta ga laifin da ta yi mata ba, akan gaskiyanta take ai ta san fushi ta yi domin tun ranar ba ta dawo kuma ba ta kira ta a waya ba, itama ba ta kira ta ba. Tunda Baffa ya rasu ta rasa jarrinta taurin zuciyarta ya karu ba ta jin taushi taushi, ta san tana da taurin kai a baya amma yanzu ya yi ƙamari tana ji ko za a yi tashin ƙiyama ne ba ta yarda a ce ita ce ke da laifi ba shi ya sa ko kaɗan zuciyarta ba ta rusuna ba. Wanda zai yi fushi da ita ya daɗe bai yi ba. Tafiyar Hamma Jibo da iyalansa sai gida ya yi shuru. Hamma Abdullahi daga kai su filin jirgi ma bai dawo ba, Saddam kuma ya fita Hamma Abdulrahim ne kawai muka yana bangaren su. Harira ta shigo ta gaisheta tana tambayanta ko akwai abin da za ta yi mata, yan zannuwanta da take sawa da dogayen riguna ta ce ta kwashe ta ɗan wanke mata. Bayan fitan Hariran ne Mami ta shigo ɗakin ta ba ta waya Daddy ne ya yi mata ya jiki suka gaisa shi yake faɗa mata ba zai samu zuwa ba tafiya ta kama shi zuwa Lagos amma gobe Mami da su Islam za su bi jirgi su koma Kaduna tunda duk sun koma makaranta. Bayan sun gama wayar ne ta miƙa ma Mami wayarta. Ta karɓa tana kallon ta kur kamar tana nazarinta, ita kuma tana kwance ne daman lokacin da Mami ta shigo sai ta ɗan zauna a saman gadon ta cire hijabin jikinta doguwar rigar atamfar dake jikinta ta bayyana kanta akwai hula amma ana ganin gashin ta, a tsefe yake ta so ne in suka zo nan a yi mata kitso to ba kwanciyar hankali, ga rasuwar Baffa ga abin da ya same ta, gashin duk ya yi biji biji. Mami ta faɗa mata cutar da ya kamata, har goggle ta yi na cutar ta yi daga nan ta san tana da sauran kwana a gaba ne, amma cutar tana da hatsari ga mata masu ciki. "Yaushe ne za ki koma ganin likita? Mami ta katse shurun da ya gifta a tsakanin su, itama yanzu Ummu Salma ba ta mata hira in ba ita ce ta tsare ta da magana ba. "Ranar monday ne jibi." "Kuma ga shi gobe za mu tafi, ke da wa za ku je? "Ni kaɗai, Harira za ta raka ni." "Baɗɗo fa ko kuma Umma Balki ta raka ki." Mami ta faɗa tana kallonta. "To." Kawai ta ce tana kauda kanta. Ba haushin Mami take ji ba kawai itama ta san tana bayan masu cewa ba ta kyauta ba. E ta san maganganun da ta faɗa ma Ammah ba ta kyauta ba, wannan ta yarda ta kuma karɓi kuskuranta amma a kan maganar Lamiɗo tana da ja akan masu cewa ita ce ta yi masa laifi. "Ummu Salma." Mami ta kira sunan ta lokaci ɗaya tana matsawa kusa da ita har tana riƙo hannuwanta. "Ɗago ki kalle ni nan." Ta ɗago idanuwanta tana mai kallon Mami. "Ki yi haƙuri ki daina damuwa. Baffa addu'a za mu yi ta masa, maganar Hanan kuma ki kwantar da hankali babu wanda ya isa ya karɓe ta daga hannun ki." Idanuwan Umma Salma suka kawo ƙwalla suka kece mata a saman kumatunta. "Mami yau kwana huɗu amma ba su dawo da Hanan ba." "Za su dawo da ita, in ma ba su dawo da ita za a je a ɗauko ta." Mami ke share mata hawaye da tafin hannunta. "Ke da za ku koma Lagos da zaran Muhammadu ya dawo, tare da ɗiyar ku za ku koma in sha Allahu.'" Hankalinta ya ɗan kwanta ta tabbata koma me zai faru Mami tana tare da ita. Ba za ta koma Lagos ba sai Hamma Lamiɗo ya janye kalamansa in kuma bai janye ba ta rantse da wanda ranta ke hannun shi ba za ta bi shi ta koma ba. Mami ta sake lallashinta da cewa ta sake zuwa ta samu Ammah ta sake ba ta haƙuri. "Ko ɗazu da safe ma na shiga na gaisheta dakyar ta amsa gaisuwa ta Mami." "Ki sake zuwa ki ba ta haƙuri abin ne ya dame ta." "Mami nima fa ba a kyauta mini ba." "An ji ke ma ba a kyauta miki ba, amma ke ce ƙarama ke ce ba ki da gaskiya." Sai kawai ta yi shuru. "Uwa ce ita, duk wanda zai so ki da cigaban ki bayan ita ne." "Haka ne." "To ki sake zuwa ki same ta daga ke sai ita, ki sake ba ta haƙuri." Ta amsa da to za ta je. "Shi Lamiɗon kin kira shi? "E bai ɗauka ba." Ta yi ma Mamin ƙarya domin ita dai ba za ta kira ba. Kawai sai Mami ta ɗau wayarta tana cewa bari ta kira shi. Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. Tunda Hanan ta dawo ranar cikin salama da aminci Ummu Salma ta yi barci har da makara. Tashin hankalinta daman a ce yau za a raba ta da Hanan amma tunda ta dawo gare ta, sai fargabanta ya ragu abin da ke gabanta kawai Hamma Lamiɗo ya dawo su yi ta ta ƙare. Ba ta ma san a ranar za su dawo ba sai da suka yi waya da Fulani ta kira ta, domin ta gaisheta da jiki daman lokaci bayan lokaci tana kiran ta a waya. Ita ke faɗa mata Hamma Lamiɗon da Bilkisu suna tafe yau, bayan kuma sun gama wayar wajen bayan azahar Hamma Abdullahi ya zo ya karɓi key din bangaren Bilkisu a hannun Ammah ya ce Lamiɗo ya ce ya karɓi yana jin a gida za su fara sauka. Tana falo ne a lokacin ta zo ɗaukan ruwa ta ji Hamma Abdullahin ya shigo suna magana da Ammah Ɗaki ta koma abin ta, gwara ya dawo domin ta san matsayin ta. Ko ya janye kalamanshi ko kuma ya cika abin da ya faɗa. Gidan shi suka wuce domin sai yamma suka zo gidan abin da ya kara baƙanta ma Ummu Salma zuciya bai neme ta ba tana jin shi a falo tare da su Ammah amma bai leƙo in da take ba. Itama ta yi kudirin ba za ta fita ta gaishe shi ba sannan ba za ta neme shi ba. Sai Bilkisu ce ta shigo tare da su Sultan sai ta ga kamar ma Bilkisun dariya take yi mata lokacin da ta shigo ta ganta ta fito wanka ne ɗaure da towel tana yin wanka da safe da Yamma da ruwan zafi sosai Mami ta ce ta dinga yi har sai ta yi arba'in amma ba ruwan zafi sosai ba Ta ga tana mata kallom sama da ƙasa tana dariyan fatan baki. Sai take tunanin me take yi ma dariya? Sai da ta fita ta kalli kanta a madubi ta fahimci abin da Bilkisu take yi ma dariya. Duk ta lalace fuskarta ta yi baƙi gashin kanta ya yi biji biji, ga tumbi da ta ga wannan haihuwar ya yi mata kumbiyu a jikinta. Hawaye suka cika kwarmin idanuwanta, duk a dalilin wa ta koma haka! A dalilin wanda ya ce zai iya sakinta bai damu da halin da take ciki ba. Dole kishiya ta zo tana yi mata dariya. Baƙinciki da kishi suka rufe mata jin ta da ganinta sai da ta yi kuka ta samu salama. Har kuma suka bar gidan bai neme ta ba Hanan ma bin su ta yi domin da ta fito ta ga ba ta gan ta ba Umma Balki ta ce ta bi babanta zuwa gida. A tunaninnta in ya zo washegari zai neme ta amma ta ji shuru. Ya zo gidan da yamma sannan suka fita da su Hamma Abdulrrahaman zuciyarta ba ta ƙara zafi ba sai da Umma Balki ta leƙo ɗakin da take tana ce mata ya ba ta ga tana shiri ba ne. "Shirin me ne Umma Balki? "Shirin tafiya mana, ko ba da ke za a koma Lagos ɗin a goben ba ne? Kenan gobe za su tafi amma bai faɗa mata ba, kuma a tunanin shi ta shirya ta bisa bayan ya gama tozarta ta, ya ja mata dariyan kishiya. Amsa ma Umma Balki ta yi da cewa kayanta a haɗe suke. Harira za ta haɗa mata sauran. Amma baƙincikin ya yi mata hawa hawa a zuciya. Ba za ta bari sai goben ba a yau koma mai zai faru zai zo ƙarshe. Ƙarshen renin hankali ya gama yi mata. Wato tunda shi yana da ya'ya ba zai damu don ta rasa jaririnta ba tuna haka kawai in ta yi kuka yake sakata yankata fa aka yi amma ba ta samu kulawa daga wajen wanda take tunanin ya fi kowa son ta ba. Tana idar da salla ta jawo wayarta ta tura masa saƙo. Tun wannan kiran da ya yi mata ba ta ɗauka ba, bai sake neman ta ba. Shima kiran saboda Mami ne bai yi ra'ayi ba. Kenan har gobe yana nan akan bakan shi ita ce mai laifi shi kalaman da ya faɗa daidai ya yi. "Hamma ka ce za ka sake ni amma na ji shuru." Sakon ya tafi da wajen mintina goma bai dawo mata da amsa ba. "Abin da ka nuna na rashin damuwa da ni ya fayyace mini nufin ka a kaina. Kar ka damu ko ka sake ni ba zan tagyayara ba" "Ina jiran ka, domin ba zan bi ka ko'ina ba." Ta jira amsar shi shuru shuru har takwas ta gota sai ta tashi ta kabbarta sallar isha'i. Tana cikin sallar wayarta ta yi haske tana idarwa gabanta na faɗuwa ta jawo wayar ta duba shi ne. "Okay." "Ki zo ki karɓa abin da kike so ɗin" Abin da ya ce mata kenan da sauri ta tura masa tambaya. "A ina? "Bangaren su Saddam." Received at 07:52Reactions: ❤ 6, 😁 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ko fita daga kan saƙon shi ba ta yi ta miƙe da Hijabin da ta yi salla ta fice. Umma Balki ce kawai a falo tana salla Ammah na ciki, tana jin Umma Balki na uhm uhm da gyaran murya ta zura takalmin silafas ɗin dake ƙofar ɗakin Harira na kitchen tana wanke wanke sai da ta leƙo. "Ranki ya daɗe ina za ki je? Sai ta juya tana kallonta "Hamma ke magana da ni a waje." Sai ta jinjina mata kanta ko tsaya ma sauraranta ba ta yi ba ta wuce Zuciya ce ke tura ta gwara ta san matsayinta. A hanya ta haɗu da Saddam da Abdulrahim za su shiga cikin gida. Ta tambaye su ina Hamma Lamiɗo? "Yana bangaren mu." Ba ta ma tsaya jin ƙarshen maganar ba ta wuce da sauri. Suka bi ta da kallo ganin saurin da take yi cikin gida suka nufa ita kuma har tana haɗawa da gudu da gudu. Akwai haske a bangaren tunda akwai nepa a lokacin. Tana shiga falon shuru kamar ba kowa amma ta ji ƙamshin turaren shi tana ɗago idanuwa suka haɗu da na shi kallon mai kassara sauran kuzarinta. Yana hakimce a saman kujera, sanye yake da ƙananun kaya wando baki rigar fara mai layi layin baki sannan tana da dogon hannu. Kafa ɗaya kan ɗaya. Ta daɗe ba ta gan shi ba, tun ranar da kalamansa suka ɓata komai. Ta ga ya ƙara yi mata wani kyau da ƙwarjini ne Cak ta tsaya ta kasa ƙarisawa domin mutuwar jiki ne ya same ta duk ƙarfin gwiwan da ta zo da shi ganinsa kawai da ta yi yana neman ya ruguza shirinta. Saurin kauda kai ta yi idanuwanta na tara ƙwalla amma ba ta bari sun zu bo ba. Shi kuma a hankali ya miƙe yana takun nan na sa na ƙasaita har zuwa gaban ta. Ya tsaya lokaci ɗaya yana tusa hannuwansa a cikin aljihun wandon jikinsa. Kafe ta da idanuwana ya yi yana kallonta kuma tana jin kallon a cikin jikinta. Amma ta ƙi yarda su haɗa ido, kar ya yaudare ta da kallon shi ta ji kawai ta bar maganar ba tare da ta bi kadin wulakancin da ya yi mata ba. Shi kuma Lamiɗo ƙura mata idanuwa yake yi sosai so yake yi ya fahimci ko tana da wata matsala ne! Domin abin da take yi ya yi kama da na wanda bai da lafiya Abin da ta yi ma Ammah ya yi masa ciwo sosai, maganar da ya yi ɓacin rai ne da kishi amma har a zuciyansa ba haka ba ne ko giya ya sha ba zai iya sakin Ummu Salma ba. A lokacin dai ya ji in har ta fi son wani akan shi zai iya sakinta sai da ya tafi Daura tunaninta ya hana shi sakat daga nan ya gane ba zai iya rayuwa babu ita ba. Ya fahimceta amma abin da ta yi ne ba ta kyauta ba amma ta kasa gane laifinta. A zuciyarsa kawai in ya tuna da kalamanta sai ya ji yana fushi wai ita ke cewa ya sake ta ɗin mana sai me? Bai taɓa tunanin haka daga gare ta ba. Da farko ya yi fushi amma daga baya ya sauka ya yarda da maganar Mami tana bukatar kulawa saboda yanayin da take ciki. Ya ɗauka da gaske ta yi nadama za su daidaita kan su, Sai ga shi ita ba haka take so ba tun a ranar da Mami ta ba ta wayar ya son rigima take ji ta ƙi magana sannan ta kashe wayar, ya kira wayarta kuma ya san tana gani ba ta ɗauka ba. Shi kuma ya ba ta lokaci ne ba ya so yadda take cikin ɓacin rai ya sake nemanta a tunanin shi in suka koma can gidansu sai su zauna su daidaita kan su, ya dawo idanuwansa na kewar ganinta amma ba ta fitowa, yana da dalilin da ya sa bai neme ta ba ai shine a gaba da ita. Ita ya kamata ta fara neman shi a matsayin shi na namiji kuma mijinta. Duk da haka ya sauke komai na shi ya yi niyyar a daran nan zai bita ya lallasheta ya ɗauketa su koma gida da safe kuma su bi jirgi zuwa Lagos. Amma sai ga saƙonnin ta masu rikitarwa. "Why Ummu Salama" Yake faɗa a zuciyarsa duk da ranshi ya ɓaci ba zai biye mata ba. Gaskiya Mami ta faɗa tana bukatar lallashi duba da yanayinta. Duk da har Ammah cewa suka yi ya fita batun ta, ba zai iya ba ne duk mulkinsa da komai na shi zai rusuna mata in dai za ta haƙura. "Ina saƙon? Ya ji ta faɗa kai tsaye, sai ya ɗaga idanuwana yana kallon ta. Har tana miƙa masa hannu. "A takarda ka rubuta ko a baki za ka faɗa mini? Mirmishi ya yi ta kasa ma kallon fuskar shi ashe ƙaryan rashin kunya take yi. "Ba anan zan ba ki ba." Received at 07:52Reactions: ❤ 6, 😁 1 [6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ya fada yana ɗan lumshe idanuwana sannan ya sake buɗewa a kanta sai da ta ɗan yi baya ta daburce. Matsota ya fara yi ta jingina da bango "Hamma ka tsaya fa." Take faɗa tana kare shi da hannayenta. Ko kusa da ita ma bai yi ba. Giransa ya sosa yana ɗan mirmishi. "Ni ba taɓa ki zan yi ba." "Mu je ciki ki karɓa saƙon na ki." Ya faɗa yana wucewa, ɗakin farko na jerin ɗakunan ukun dake falon ya nufa ya shiga, kafafunta suka lamkwashe saƙon me? Sakin na ta ya yi da gaske? Ƙirjinta ya buga wani hadari ya ruguzo mata a saman kanta. Ta kasa gaba ballatana baya domin kafafunta har sun yi wani gara gara. "Ki zo ki karɓa mana? Ya leƙo yana kallonta. "Ko ba ki so ne? Ya faɗa yana shafa sumar kansa. Daƙyar ta ja kafafunta ta bi bayan shi. Ita ce ta ce ya yi abin da ya furta amma barazana ce ba ta taɓa tunanin zai iya sakinta da gaske ba. Wata zuciyar ta ce to sai me in ya sake ki? Kamar ta farka daga barci sai ga ta bi shi cikin ɗakin tana shiga ashe yana ta baya wajen kofa ganin ba shi a ɗakin tana shirin juyowa ta ji ya rumgumeta ta baya ƙamƙam ya hana ta ma juyawa. Ta fara mutsu mutsun ƙwacewa amma bai ba ta dama ba ya kanannayeta sosai ya sagalo hannayensa ta wajen cikinta ya nitsata a cikin jikinsa kansa na wajen wuyanta yana sake tusawa gabaɗaya duk ya kashe mata jiki, har jikinta ya fara rawa. "Ina..ina saƙon? "Ga shi nan" Ya faɗa yana sumbatar wuyanta. "Ke a tunanin ki sai na iya sakin ki? "Why Umma Salma? Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakinta sannan ya juyo ta suna kallon juna. "Kin yi mini laifi amma ni kike horawa? Ƙureta da idanuwansa ya yi, da ya sa ta kasa jurewan kallon shi. "Kai ne ka ce za ka sake ni da bakin ka a gaban kowa da kowa." Sai hawaye suka kece mata sharr. "Menene laifina da za ka tozarta ni Hamma? Don kawai na ce kar a tafin mini da ƴa ta? Sai kuka wiwi har da sauti ya yi shuru yana sauraranta. "Na san na yi laifi maganganun da na faɗa ma Ammah ɓacin rai ne bana cikin yanayi mai daɗi amma kai abin da ka faɗa mini ya yi daidai? "I'm sorry." Ya faɗa a hankali yana riƙe hannuwanta duka biyun "In kowa bai duba yanayina ba, kai fa? Ka manta Baffa fa na rasa sannan na rasa jaririna ko tausayina ba ka ji ba? "Sorry." Ya sake ba ta haƙuri, domin duk ya amsa laifinsa maganar ta wuce. "Ka tafi ba ka sake nema na ba, ka manta da ni, ka manta da halin da nake ciki." "Yiyiyiyi..." Sautin kukanta, har da majina tana faɗa zafin abin na sake dawo mata sabo. "Sorry, kina raina na kuma damu da halin da kike ciki." "Ba ka damu ba, da ka damu da ka nuna kulawar ka a kaina." "Haushi na ji, haushin maganganun da kika faɗa ma Ammah." "Ai na ba ta hakuri." Ta faɗa cikin kuka. "Kuma nima ai ba a kyauta mini ba, ba a kyauta mini ba." Kukan da take yi har ya yi yawa da sauri ya jawo ta jikinsa ya rumgumeta yana lallashinta da hannun rigarsa ya dinga share mata hawaye "I'm sorry, ki yi mini afuwa." "Sai ka janye kalaman ka na cewa za ka iya sakina." "Na janye." "A gaban kowa da kowa za ka faɗa." "Done." Ya faɗa yana sake shigar da ita jikinsa ya samu dai maganar ta wuce. Daga lallashi ya zarce da sumbata, ba ta wani ba shi haɗin kai ba sai ma ture shi da take yi amma ya nane mata sai ga su a saman katifar ɗakin Saddam sun baje, a nan komai ya wakana ba wani daɗewa tunda ba ta bada dama ba sosai. Wanka ya shiga ya bar ta nan tana kuka, ya fito ya mayar da kayan jikinsa har lokacin ba ta daina kuka ba. Ya ce ta tashi ta yi wanka cikin masifa ta ce ba za ta yi anan ba. Sai ya ce to ta tashi ta saka kayanta sai ta je cikin gida ta yi wankan a can. Ko a jikinsa da kukan da take yi. Sai ma wayarsa da ake kira ya ɗaga yanayin wayar kawai ta gane Bilkisu ce falo ma ya fita ya barta kishi ya tirniƙeta ta tashi ta mayar da kayan jikinta tana yi tana kuka ta zura hijabin ta kenan ya shigo ɗakin Ganin yadda take yi ya sa dariya ta kama shi har tana sauti. Zuciya ta ciyo ta, ta kalle shi cikin hawaye tana faɗin "Dole ka yi dariya mana dole na zama abin dariya." Sai kuka wiwi, kamar ƙaramar yarinya. "Na zama abin dariya haka ma matarka ta zo tana kallona tana dariya." Received at 07:52Reactions: ❤ 7, 👍 1, 🥰 1, 😁 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sai ya yi shuru kawai yana kallonta amma ya daina dariyan ganin da gaske take yi. "Ai dalilinka ne na koma haka, kana gani ina kuka amma ka kasa lallashina sai ma fita ka yi kana waya da matarka ko ajikin ka." Ta karishe faɗa hawaye na kece mata a saman kumatu. "Ummu Salama." "Na ce miki sorry, na lallashe ki da baki da aikace amma kin ƙi yin shuru" "Me zan yi miki? Kin ce duk ni ne da laifi na amince. Kin ce na janye i do, kin ce a gaban mutane zan faɗa na ce done? Amma ba ki daina kuka ba." "To ya kike so na yi miki? Ya faɗa yana ɗan sassauta maganarsa Ba ya son ranshi ya ɓaci amma kuma Ummu Salama na son sai ta ɓata masa rai. "Haka za ka ce ko? Ta ke faɗa tana nuna shi. "Ai daman ba za ka san raɗaɗin dake zuciyata ba." Cikin idanuwana ta kalle shi. "Saboda ba ka yi rashin da na yi ba. Jaririn da muka rasa a wajenka rashin ba shi da ciwo tunda kana da wasu ya'yan da matar." Ya yi mata ƙuri yana kallonta zuciyarsa na ɗaukan zafi yana ƙankance idanuwansa cikin mamakin kalamanta "Sannan ba ka yi rashin mahaifi ba shi ya sa ba za ka san zafi da raɗaɗin dake zuciyata ba dole.." "Ummu Salamaaa" Ya kira sunanta a ƙausashe. Cikin tsawa da sai da ta dakata da maganarta. A irin kallon da yake yi mata ne ya sa ta dawo hayyacinta ta tuna abin da ta ce. Sai ta koma ta rufe bakinta ba ta san maganar ta fito ba, ba ta san ma aka yi ta faɗi haka ba. "Gori ki ke yi mini? "Faɗa mini kike yi Baffa ba shi ne ya haife ni ba? Ya faɗa yana kallonta kallon mamakin ke ce zaki ce mini haka. Nan da nan ta gano ɓarnan da ta yi da sauri ta buɗe baki za ta yi magana. "Get out" Ya faɗa a tsawa ce. "Hamma..." "I said get out." Ta tsaya kawai tana rawan jiki. Wallahi sheɗan ne ya tunzurata ta faɗi haka amma ba haka ta so faɗa ba. Ganin ba za ta fita ba shi ya bar mata ɗakin yana banko mata ƙofa ta kwashi gudu ta bi shi har falo key ɗin motarsa ya ɗauka a saman kujera ya wuce ta ko kallonta bai yi ba. Ta kwashi gudu ta bi shi tana faɗin. "Hamma ka yi haƙuri don Allah." Take faɗa tana kuka, ita ce ta ce yau za a yi ta ƙare ashe ita ce komai zai ƙare a kanta mai ya kai ta faɗin wannan maganar! Ɓacin rai ne da kishi wallahi tallahi ba ta san bakinta ya subuce ta furta waɗanan kalaman ba. Tana bin shi tana kiran sunan shi ko waiwaye bai yi ba sai ga su a haraba. Motarsa ya nufa ya buɗe ta ya shiga sai ta tsaya cak ta kasa ƙarisawa gare shi. Me za ta faɗa masa? Ba ta kuma da abin da za ta faɗa masa ita ce yau take yi masa gorin Baffa ba mahaifinsa ba ne. Bakinta ta rufe da tafin hannunta hawaye na gangaro mata kunyar kanta na kamata, ita ce yau in ta ji wani na faɗin haka sai in da karfinta ya ƙare amma a ce yau da bakin ta take faɗin Hamma Lamiɗo bai san zafin rashin uba? Ta manta ko ita tasowa ta yi ta gan shi ƙarkashin tarbiyan Ammah da Baffa. Me ya same ta! Kishi ne da takaicin dariyan da yake yi mata ko wauta ne duk ba ta san ma me ya shiga kanta ba. A lokacin da ta furta a lokacin kuma fargar jaji ya kamata. Amma ina magana ai zarar bunu ce ta riga ta fitar kuma ya ji ba ta kuma da sauran kalaman da za ta iya kare kanta da su. Kunyar ma haɗa ido take yi da shi, kunyar kanta da kanta na kamataa jikinta ya yi matukar sanyi da tana ji tana gani ya fice daga gidan da gudu a mota Sai kawai ta duke kan kafafunta tana kiran sunan Allah kukanta yaƙi tsayawa. Ta ɗora hannuwa bisa kai tana kiran sunan Allah. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un" Take maimaitawa hawaye na kece mata wasu na zuba wasu na tunkuɗowa. Ta jima a wajen kafin ta tashi tana jan kafafunta da suka yi sanyi zuwa cikin gida sai da ta tsaya a haraba ta goge hawayenta sannan ta karisa. Amma da Umma Balki da su Saddam suna falon ta wuce su sum sum ba ta yi musu magana ba. Umma Balki ce ma ta ke tambayanta Lamiɗon ya tafi ne ko juyowa ba ta yi ba ta ce ya wuce ɗakinta ta shiga har tana rufo ƙofa tare da Harita suke kwana yanzu har ta yi shimfiɗa ta kwanta ta fara barci. Received at 07:52Reactions: ❤ 8, 👍 1, 👏 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Gefen gado ta zauna tana zabga tagumi da hannayenta biyu, in har wannan abin da ta faɗa ya je kunnen Ammah ba ta san me za ta yi mata ba, ba ma ita ba kowa ya ji sai ya tsine mata ita kanta tana jin haushin kanta sosai subul da baka ne ba ta san kalaman sun fito da zafi haka ba. Zaman ne ta ga ba zai kawo mata mafita ba sai ta jawo wayarta ta buɗe ta daga key tana kan sakon shi ne ma ba ta fita ba, sai ta fita ta je bangaren kira ta lalubo lambarsa ta fara kiran shi. Kiran da ta yi masa ya fi goma bai ɗauka ba. Ta koma tana ta tura masa sakon ban hakuri sama da goma amma bai kira ba, bai kuma amsa saƙon ta ko ɗaya ba. Daga karshe ma da ta sake kira sai dai ta ji ɗi ɗi sai kiran ya yanke. Kamar ma ya rufe ta ne kwata-kwata. Tana hawaye kace kace, har da majina ta dafe kanta cikin tashin hankali da nadama. Nadama mara amfani. Me ya sa ma ta je ta same shi? Da ta san haka abubuwa za su lalace da ba za ta je ba. Haushi ta ji haushin yadda ya yi banza da ita ta je da nufin ta bi kadin abin da ya yi mata kuma ya bige da ribatanta har ta ba shi dama a kanta, dariyan da yake yi mata ne ya tunzarata. Ba ta ma san mganganun dake bakinta ba kenan ita dai a harzuƙe take a lokacin shi ya sa aka ce in rai ɓaci hankali ke neman shi magana kuma dafi ne kaifin dafin ta yafi kaifin takobi. Ita dai maganganunta kaifin dafin sun soki Hamma Lamiɗo sokewar da bai taɓa tunani ba. "Na shiga uku ni Ummu Salama." Ita kaɗai take maganarta tana kuka, ta rasa wa za ta kira akan wannan matsalan duk in ta je ta faɗa to ita ce a kasa, ta yi tunanin kiran Baɗɗo sai ta tuna yadda suke ba daɗi ma, yanzu tana faɗa mata abin da ta yi abubuwa ne za su ƙara lalacewa. Ta koma tana sake tura masa sakon ban hakuri. "Ka yi hakuri Hamma suɓul da baka ne. Wallahi na yi nadama kuma na janye kalamai na" "i'm Sorry ba zan ƙara ba." Amma da alamun ma bai san tana yi ba, ta kasa barci ta yi kuka kamar me, daman a kwanaki nan ta ƙulla abota da kuka nadamar abin da ta faɗa kawai take yi. Ta yi wankan tsarkin najasan dake jikinta sannan ta yi shirin kwanciya ta kwanta amma ta kasa barci a daran kuma ba ta san sau adadin nawa ta kira lambar Hamma Lamiɗo ba amma kuma ya yi rufe ta da alamun ba za ta same shi ba. Ga ta kwance kawai amma ta kasa barci sai tsiyayan hawaye. Tana mai ganin laifin kanta da ta yi hakurin da kowa ya ce ta yi da yanzu ba ta cikin nadama shima ya ba ta hakuri amma taurin kai da kafiya suka hana ta ganin hakurin da ya ba ta, sai ga shi da kalaman bakinta cikin mintina ƙalilan ta bata komai Juye-juye kawai take yi da ta kasa barci dole ta miƙe ta shiga tiolet ta ɗauro alwala. Dole ne abubuwa su rikice mata ta manta da Ubangijinta. Tunda abubuwa nan suka faru da ita sai dai ta zauna tana koke koke ba ta tunawa da keɓe kanta ta faɗa ma Allah kukanta. Shi ya sa ta zama sai a hankali sai fama da zafin zuciya da fushi. Salla ta fara yi raka'a shidda ta yi sannan ta rufe da shafa'i da wutiri. Ta ɗaga hannuwana sama tana kuka tana neman ma Baffa gafara tare da fatan Allah ya sanya jaririnta da ta rasa ya zama mai ceton su ranar gobe ƙiyama sauran addu'o'in nata duk akan Hamma Lamiɗo Allah take roko ya sassauta zuciyarsa akan ta, Allah ya yi ramgwame a cikin fushin sa zuwa gare ta. Ita dai ba ta da sauran kalaman kare kanta duk abin da za ta faɗa ta riga ta gama ɓata komai tun daga farko. Sai uku da rabi na dare ta koma ta kwanta, tana kallon rufin ɗakin kafin barci ya kwasheta ta share hawaye ba ta san iyaka ba. * A bangaren Lamiɗo kuwa yadda ya fita a cikin fushi ba ƙaramin ƙokarin iya sarrafa fushin sa ya yi har Allah ya kai shi gida lafiya ba. Kalaman Ummu Salma na zuwa da dawowa a cikin kunnuwansa, shi bai damu da cewar da ta yi bai damu da rasa jaririnsu ba, amma cewar da ta yi bai san zafin da ta ke ji a zuciyarta ba, tunda shi bai rasa uba ba. Maganar ta zo masa cikin bazata ne, bai taɓa tunanin haka daga Ummu Salama ba. Da gaske ne ba ta da kunya duk ya shanye rashin kunyarta ya ɗau ƙankanta ya bar mata girman don a zauna lafiya amma duk bai isheta ba sai da ta yi masa gorin ba Baffa ne ya haife shi ba. Received at 07:52Reactions: ❤ 7, 👍 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ba domin ita ba ce, da wani ne da yau sai ya gane kuskuran shi. Amma duk da haka itama zai koya mata hankali, in taƙamarta rashin kunya da rashin iya magana to zai koya mata yadda za ta iya magana da shi, yadda anan gaba duk abin da za ta faɗa masa sai ta tauna shi ta tantance shi kafin ta faɗe shi. Haka ya shiga bangaren Bilkisu a fusace yara duk suna falo har da Hanan suna ganin shi suka nufe shi suna kiran sunan shi da Papa Amma duk yadda yake son yara bai tsaya kallon su ba. Bilkisu na yi masa sannu da zuwa bai juyo ba ya shige daki ya banko kofa ya saka key, baya son kowa a kusa da shi saboda yana cikin fushi shi kuma in ranshi ya ɓaci ya fi son zaman shi kaɗai fiye da komai Gefen gado ya zauna yana dafe kan shi da ya ji yana sara masa. Ta ce ta rasa jaririnta amma bai damu ba saboda yana da wasu yaran? Ta manta shi ne uban jaririn, ta manta irin soyayyar da yake yi ma cikin nan tun kafin ya zama gudan jini Shi fa namiji ne ta ya zai zauna yana nuna mata rauninsa alhalin tana mace, zai iya rantsuwa abin da ya ke ji akan rashin jaririn su ita ba ta ji irin shi ba, ko don bai faɗa mata ba? Ko saboda bai zauna ya yi mata kuka ba? Wani abin ba ka sanin zurfin shi. Wani ciwon ba ya iya bayyanuwa a fatar baki zuciya kaɗai ke iya riƙewa. A lokacin da ta faɗi maganar ta zo masa da zafi sosai, yana shirin ya dakatar da ita sai ta ɓata komai. Har Baffa ya koma ga Allah bai taɓa jin sa ba a matsayin mahaifinsa ba. Rashin Baffa gibi ne shima a rayuwarsa domin shi ya fara sani a uba kafin Mai martaba. Yau shi Umma Salma ke yi ma gorin bai san zafin mutuwar uba. Ya runtse idanuwana ya buɗe bai san adadi ba, ya nutsa hannayensa cikin sumar kansa ba adadi huci da fitar da numfashi kamar zai shiɗe sai da ya ta shi ya shiga tiolet ya sakar ma kansa ruwa sannan ya ɗan samu sauƙi sauƙi. Wayarsa tana silent ne sai da ya fito ya ga kiran Ummu Salma rututu, bai ma san yadda ya ke ji a zuciyarsa ba. Amma for now ba ya son ganin ta ko jin muryanta ta bar shi ya samu nisa da ita ko zuciyarsa za ta huce. Blooking ɗin ta ya yi, ba ya son ma ya ga sunan ta tana kiran shi saƙon ta kuma ko ɗaya bai buɗe ba. Ba ta kuma da sauran abin da za ta faɗa masa. Maganganunta suna neman goge duk wani alherinta a gare shi. A hankali a hankali ya ke jin kamar ta saka katanga ta katange duk wani hangen shi da zumuɗin shi a kanta, wannan soyayyar da kaunar da suka faro ta, tun daga farko yana jin tana yi masa nisa wannan kalmomin na ta sun sanya tazara mai yawa a tsakaninsu tazaran da suke tunanin sun daɗe da haɗe shi. Bilkisu tunda ta ga yanayin shi ba ta neme shi ba, shima kuma daman haka yake so ya fi son ya kaɗaice shi kaɗai Ba ya son ya ganta ballatana ya ji kalaman bakinta gani yake yi yanzu duk abin da za ta faɗa ba zai zama mai daɗi daga gare shi ba. A daran ya siya musu tiket ɗin zuwa Lagos. Tsarin shi ya ruguje kalaman Ummu Salma sun yi nisa da abin da ya shirya. Da ita ya so su koma a tare a sabon gida da ita domin su gina kyakyawan rayuwa a can har su mayar da jaririn da suka rasa amma a dare ɗaya ta ruguza wannan yaƙinin na shi akanta. Ba zai iya tafiya da ita ba, ko ta je can ba zai taɓa sauraranta ba yana bukatar lokaci mai tsawon da zai yi tunani amma shi ba zai sake yarda da ita ba, sai ta goge waɗanan munanan kalaman nata zuwa gare shi, kuma goge kalamanta abu ne da ba zai taɓa yuyuwa ba magana zarar bunu ce tunda ta fita ba za ta koma ciki ba. A daran ya canza duka tsarin shi da ita. Ba yanzu ba wataƙika sai ya huce ko zai iya sauraranta amma yanzu ta zauna a gida hakan shi ne mafitarsu gabaɗaya. Jirgin goma sha ɗaya na safe za su bi zuwa Lagos. Bayan ya dawo daga masallacin Jumma'a ya shiga ɗakin Bilkisu ya sanar da ita akan su shirya akan lokaci. Bai yi mata wata magana ba, kuma ba faɗa mata aka yi ba a jikinta take jin koma me ya ɓata masa rai to Umma Salma ne, zuciyarta kamar farar takarda tana ta addu'an Allah ya sa ba da ita za su tafi ba. Received at 07:52Reactions: ❤ 14, 👍 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta fahimci tunda Baffa ya rasu ta kuma haihu ba ɗa shi kenan ta ga ta ɗan yi sanyi ta rage tsiwa da yi ma mutane kallon reni da ta je ta ganta shekaranjiya duk ta fita kammaninta sai da ta yi dariya ta tabbata a haka babu kuma abin da za ta birge Lamiɗo da shi. Ba ta tambaye shi ba, ta san in ma ba tare da Umma Salma za su tafi ba za ta ga ni in lokacin tafiyar ta yi. Da wuri suka shirya jikinta ya yi sanyi da ta ji ya ce tare da Hanan za su tafi to za a tafi da ɗiya ne a bar uwarta anan sai murnan ta ya koma ciki. Amma suna zuwa gidan Ammah ta samu amsar tambayanta. Ammah ce da kanta take tambayan shi, shi ya ce Ummu Salma ta zauna anan sai ta sake warwarewa? Kai tsaye ya amsa da shi ya ce ta zauna ta sake warwarewa daga baya sai ta biyo su. Bilkisu murna kamar me, tana ta mirmishi ita kaɗai duk da bai faɗa ba, ta san wani abu ne ya faru a tsskaninsu da ya hana tafiyar Ummu Salma addu'a take yi a zuciyanta da Allah ya sa daga nan auren ya kare kowa ya huta. Ita kadai za ta dinga juyi a wannan ƙaton gidan da daman baƙin cikinta ɗaya yadda za ta juya a sabon gida itama Umma Salma za ta juya gani take yi ai ba matsayinsu ɗaya ba ma. Tafiya da Hanan kuma sai yanzu ta fahimci saboda makaranta ne. Ba ta damu ba in dai Umma Salma ta fara barin mata mijinta ita ma Hanan ɗin ba daɗewa za ta bi bayan uwarta. Kayanta ma Harira aka ce ta haɗa, sannan ko a gilmawa ba ta ga Ummu Salma ba kuma Lamiɗo bai neme ta ba. Daɗi ya yi kusa kasheta tana zaune tana girgiza kafa tana faman mirmishi. Duk maganganun da aka yi a falo Ummu Salma na laɓe daga ƙofar ɗakinta tana ji. Ita kaɗai ta yanke ma kanta hukunci, hukuncin da take da yaƙinin shi Hamma Lamiɗo zai yanke, daman ita ta ce ba za ta bi shi ba ta faɗa gaban yan amin, yadda ya ki ɗaukan wayanta ya rufe ma hanyar da za ta same shi ta samar ma kanta mafita. Bayan ta idar da salla asuba ta samu Ammah har ɗakinta ta yi mata karyan ita anan za ta zauna in ji Lamiɗo Ammah ta ce in ya zo za ta yi magana da shi ta ji. Tunda ta ji hayaniyarsu ta laɓe, ba za ta iya fitowa ba, ba ta yi mamakin cewar da ya yi ta zauna ba daman ta yi tunanin haka. Itama kunya ba zai barta ta bi su ba, sannan kuma ita ce ta ce daman ba za ta bi shi ba, shi ya sa ba ta shirya ma tafiyan ba. Gwara su tafi daga baya sai ta bi su in ta tabbatar da ya koma bakin aiki sai ta koma zuwa lokacin da zai dawo ya wuce, sai ta tattaro duka kalaman bakinta ta sake bashi hakuri. Amma yanzu ita kanta kunyar abin da ta faɗa masa take ji. Ta san kuma ba zai taɓa shigowa yi mata sallama ba, itama ba ta san da wani idanuwa za ta kalle shi ba. Tana zaune gefen gado Harira ta shigo tana ce mata Ammah ta ce a haɗa kayan Hanan ta amsa mata. Tana sake ganin girman Hamma Lamiɗo da kuma nadamarta duk abin da ta yi masa bai bambanta Hanan da su Sultan ba, kuma bai fasa amsa sunan uba a gare ta ba. Harira ke tambayan ta su ba tare za su tafi ba? Ta ce mata sai daga baya sai ta koma ganin likita. Ashe da ba ta ga Hidaya da Sabuwa suna Lagos Bilkisu ta tura su kafin ta wuce Daura suna can sabon gida suna kimtse kimtse ma'aikatan ma sun dawo bakin aiki har su Debora su kaɗai ne masu gidan ba su dawo ba. Tana jin Harira ne kawai na magana amma ita tunanin ta ya yi nisa, sai da Harira ta gama haɗa kayan a ƙaramar akwati ne, kamar za ta yi magana ganin har da wasu kayan da aka ɗinka mata a can gidan su Habibu, watsar da kayan ma ta so yi daga farko daga baya kuma sai ta fasa. Tana zaune har Harira ta fice ta yi tagumi kawai, tana jin hayaniya a falo sai da suka yi breakfast itama an shigo mata da nata amma ta kasa ci a lokacin ma ta sake kiran wayar Hamma Lamiɗo ba ta shiga. Tun da ta ji zuwan Hamma Abdullahi ta san tafiya ta tashi tunda shi zai kai su filin jirgi. Ta maƙale a jikin kofa tana leƙe. Ta hango Hamma Lamiɗo a durkushe a gaban Ammah ya rike hannunta yana mata magana a hankali ko kana kusa ba lalle ka ji abin da ya ke cewa ba, ballatana ita da take leƙe daga cikin ɗaki. Bilkisu da yaran sun fita Harira ta ɗaukan musu jakunkuna, Hanan ko nemanta ba ta yi ba, ballatana su yi sallama itama ba ita ce a gabanta ba yanzu. Received at 07:52Reactions: ❤ 12, 👍 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Tana gani ya saka ma Ammah farar evelope jikinta. Tana jin muryan Ammah na godiya da saka albarka. Umma Balki har da ita a masu fita rakiya lokacin da ya miƙe sai ya ɗan waiwayo kamar zai kalli ɗakin da Umma Salma ke ciki sai ta yi saurin yin baya tana dafe kirji kar ya kamata tana leƙensa. Bakin yadi ne a jikinsa ɗinkin zamani da bakar hula mai gashi gashi. Juya baya ta yi tana dafe ƙirjinta dake bugawa. Ba ta taɓa tunanin zai shigo ba sai ji kawai ta yi an buɗe kofa. Da juyawarta da shaƙam ƙamshin turaran shi duk a lokaci daya ne. Sun haɗa idanuwana amma shi ya yi saurin kauda kan shi. Baya son kallonta ita kuma tana ganin shi wani irin nadama abin da ta aikata ya ruguzo mata. Ta yi narai narai har kwarmin idanuwanta ya cika da ƙwalla. Kafafunta suka shiga rawa ganin yadda ya haɗe fuska ya fito a sak Yarima Daura ko Lamiɗon da ta sani a can baya. Wanzuwarsa a ɗakin sai ta ji kamar ta matsu, kamar babu wajen iska ƙwarjinsa ya babbake ko'ina da ya sa ta kasa ma numfashi mai ƙarfi. Duk nacin kallon shi da take yi bai yarda ya kalleta ba a cikin aljihun wandon sa ya fito da farin evelope mai tudu ya ajiye mata a gefen gado. Ya juya zai fita ba tare da ko hawa da saukan numfashin sa ba ta ji ba. "Hamma." Ta kira shi cikin karyewan sauti sai hawaye shar. "Ka yi haƙuri don Allah.." Ya tsaya amma bai juyo ba. "Na tuba ba zan ƙara ba." Kukan har yana sauti ya lumshe idanuwana ya buɗe. "Take care of yourself" "Ummu Salaama" Yana gama faɗin haka ya buɗe ƙofa ya fita ya barta tana durƙushewa a ƙasan cafet tana kuka yana jin ta amma ba zai bari kukanta ya yi masa tasiri ba. Daga shi har ita suna bukatar lokaci. Gwara ta zauna tare da Ammah a kula da lafiyanta ta samu natsuwa shima gwara ya yi nisa da ita ko zai samu zuciyarsa ta yi sauƙi. Amma zencen gaskiya yana buƙatar lokaci sannan ko zai saurare ta ba yanzu ba. Yana jin kalamanta har yanzu yana tunanin kuma zai daɗe yana jin maimaicinsu a cikin kan shi, Ummu Salma ta ruguza komai, in ya ce komai yana nufin komai amma soyayyarta dake cikin zuciyarsa ba ta samu rauni ko tawaya ba sai dai hakan ba shi zai hana ya nuna mata kuskuran abin da ta yi ba. Daman ya yi niyar ya shiga ya yi mata sallama. Ya fuskanci uzirinta ta bangaren halin da take ciki amma ba shi zai sa ta riƙe a matsayin makamin da za ta kwatsa masa wannan maganar ba. Ba ta da lafiya har yanzu tana kan dokokin likita ne, ya bar mata kuɗi masu yawa domin nauyin ta yana wuyan sa ne ta kula da kanta har zuwa lokacin da zukata za su huce. Yana jin kukanta amma bai juya ba haka ya fita, Ammah ba ta fita ba amma ta bi shi da fatan alheri mai yawa. A motarsa Hamma Abdullahi ya tuƙa su zuwa filin jirgi a ranar da Baffa ke cika kwana talatin da ɗaya a ƙasa. Sai da jirgin su ya tashi ya tashi sannan Hamma Abdullahi ya dawo gida da motar ya ba ma Ammah key ɗin motar da na bangaren Bilkisu. Ummu Salma kuma ba ma wanda ya sake bi ta kanta. Tun da Hamma Abdullahi ya tambaya ganin ya ga ba da ita aka tafi ba Umma Balki ta ce Lamiɗon ya ce ta zauna daga baya sai ta bi su. Ko su Hamma Saddam da suka dawo aka ce ta na nan ba ta tafi ba ganin Harira ba wanda ya damu da ya shigo ya duba ta. Tun a yau ta fara nadama, da a ce ta ji haƙurin da ake bata da tuni tana gidan mijinta. Ga shi tana gidan amma ba ma wanda ya damu da ita. Baɗɗo kuma ta yi fushi da ita ta daina zuwa ta daina nemanta. Zaman gidan ma sai ya zame mata kamar a gidan yari kwata kwata ba ta jin daɗi. Ga shi tun da Hamma Lamiɗo ya tafi sama da sati bai taɓa kiranta ba ko ta kira shi ba ta samu sannan tana jin suna waya da Ammah daga baya ma a bakinta take jin ya koma wajen aikinsa. Ga kewa duk ya sake surkukuta ta, ba wanda ya lura tana ta ramewa. Mami ma da suka yi waya ba ta san kwanan zencen ba har tana faɗin sai ta yi gyaran jikinta a tsanake, kayan da tunda aka kawo su ba ta duba su ba Sai ranar ta saka Harira ta buɗe tunda a leda suke ciccibi da kazar sababi sun ɗan fara lalacewa sai kawai ta ce Harira ta zubar garin magunganur kawai ta bari sai maganin sanyi. Abin ta aikata ne ya zo yana damunta ga shi ta kasa faɗa ma kowa. Received at 07:52Reactions: ❤ 9, 👍 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Baɗɗo ce abokiyar cin mushenta ta kira ta domin ta nemi sulhu ta ce za ta zo amma ba ta zo ba. Shamsiya sau biyu tana kiranta na farko ta ɗauka. Na biyun kuma ba ta ɗauka ba, ba ta ga amfaniin kiran wayar ba. Ta faɗa mata Hanan na Lagos ita tana Adamawa. Har abada ba ta buƙatar Shamsiya a rayuwarta yanzu, ita ta zama past tense a cikin rayuwarta ne. Daƙyar Baɗɗo ta hakura ta zo ranar Hamma Lamiɗo ya yi sati biyu da ta tafiya da ta zo ta ga Ummu Salma sai da ta yi magana. "Sisna kin ga yadda kika rame kika lalace? Mirmishi kawai tayi ba dole ta rame ta lalace ba. Rayuwarta ta yi juyin waina daga sama zuwa ƙasa. Tunda ta haihu ba ta gyara jikinta ba ita kanta ta san duk ta fita hayyacinta. "Har da Tumbi kika bari ya zauna miki, fuskarki ta yanƙwane jikin ki ya yi kamar ba na ki ba fuskarki ta sauya kin yi baƙi me ke damun ki? Da za ta iya da ta faɗa mata amma kuma ba za ta iya ba. Abin da ke damunta zaman da take yi ba rashin dalili. Ba ta san a wani babi Hamma lamiɗo ya jingine ta ba. Baɗɗo ta yi ta mata faɗan ta bar jikinta duk ya lalace. Gaskiya ya kamata ta gyara sannan zaman me take yi anan gwara ta shirya ta koma gidanta in ba za ta koma Lagos ɗin ba yanzu. Sai kuma da Baɗɗo ta faɗa ta yi tunanin haka. Tana son komawa Lagos amma ba ta son ta koma a haka a firgice sai ta yi gyara ta ɗan dawo hayyacinta. Sai ta ce za ta koma asibiti jibi in ta dawo daga can kawai sai ta wuce gidanta. Maganar kayan gyara kuma ta ce Mami ta siya mata ga su can za ta fara amfani da su. Tumbi kuma daman ba da yawa ba ne rashin kula ne ma yasa har yanzu bai tafi ba amma za ta miƙe domin ta gyara jikinta amma ita kanta ta san ta fita hayyacinta. Baɗɗo ta yini tare da ita sai yamma ta koma gida. A daran ta tura mata dubu dari biyar son da ta yi alƙwarin za ta tura mata ta kafa jari. Baɗɗo har da kuka saboda farinciki. "Ba zan iya biyan ki ba Sis na, wannan kawai kyautatawa ne daga cikin irin kyautatawarki a gare ni." Tabbas ba za ta iya biyan Baɗɗo tarin alherin da ta yi mata ba sai dai ta kamanta in tana da shi babu abin da ba za a ta mallaka mata ba. Sun yi maganar har sabaya za ta haɗa da kanta ta fara sha tunda har nonuwanta sun fara yamutsewa ita dai abubuwa da dama sun yi mata ruku'a a cikin rayuwarta. Ga abincin mai gina jiki amma ba ta ma sakin jiki ta ci, ta saka tunani da kwazzaba a zuciyanta duk ta bushe dole kishiya ta yi mata dariya. Ana gobe za ta koma asibiti ta dama garin haƙkin daka na cikin kayan Surayya Dee tunda da safen ta yi mata magana ta turo mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi. Maganin sanyi ta fara sha da safe da yamma ne ta dama na garin ta sha, sai dai bai ko gama zama a cikin ta bai yi ba, ta fara amai kamar hanjin cikinta zai zazzago. Cikinta da maranta suka dinga murɗawa a daran ko abinci ta kasa ci bakinta babu daɗi haka ta kwana cikin kasala da tsikewar miyau Da safiyar litini da ta kama kwanan Lamiɗo goma sha bakwai da tafiya ita da Harira suka koma asibiti Yanayin da take ji ta yi ma likitan bayani a can ma asibitin tana shan ruwa sai amai Jininta aka diɓa suka sanya mata drip tunda sun ce jikinta ya yi yaushi sannam ba abinci a cikinta suka yi mata alluran barci Hamma Saddam ne ya kawo su daga nan ya wuce wajen aiki. Harira ce ta kira Ammah ta faɗa mata sun rike Ummu Salma a asibitin. Ammah ta ce Umma Balki ta bi bayan su ta gani. Ko da ta je Umma Salma na barci, ba daɗewa likita ya kawo sakamako. Ciki ne a jikin Umma Salma kimaniin sati biyu da kwana biyu Kwanakinsa kwana sha bakwai kenan a cikin jininta suka gano cikin. Umma Balki ta yi ta mamaki, likitoci kawai a bar musu kayansu wajen bin kwaf yanzu cikin ma na sati biyu sun iya gano shi. Sai yamma suka gama saka ma Ummu Salma ruwa, ta samu kwarin jiki, an dakatar da ita daga shan ko wani magani saboda cikin dake jikinta. Sai ta ji abin kamar a mafarki da ta kirga kwanaki cikin ranar da suka kaɗaice da Hamma ne a bangaren su Saddam a ranar ta samu wannan cikin. Sai ta rasa me za ta yi, farinciki take ji ko mene ne, gata nan dai ta kasa gane kanta. Ashe rabo ne ya kirata shi ya kai ta wajensa har komai ya shiga tsakaninsu. Received at 07:52Reactions: ❤ 8, 😁 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sun koma gida da tarin dokar likita ta dinga cin abinci sannan ta daina tunanin jininta ya sauka amma kuma zai iya hawa ga ciki a jikinta ƙarami sannan tana da tarihin hawan jini da cutar Eclaampsia sai ta lura sosai wajen kiyaye lafiyanta. Umma Balki suna komawa gida ta fasa maganar cikin Umma Salma. "Daman ko haihuwa mace ta yi ɗa ba rai ko ta yi bari za ki ga da wuri take samun wanin cikin." Ammah dai ta yi fatan Allah ya kara lafiya. "Ki kula da kanki, tunda yanzu kin ga ba ke kaɗai ba ce." Abin da Ammah ta faɗa mata kenan. Umma Balki kuma na faɗin sai ta kira Lamiɗo ta faɗa masa ta amsa da to, amma ta san ba samun shi za ta yi ba. Ta neme sa ba ta same shi sai ta adana takardan gwajin cikin duk lokacin da ya sauko ya saurareta sai ta sanar da shi. Da kanta ta kira Baɗɗo ta faɗa mata ta dinga tsalle a waya sai ga shi ta taho. Ba ta fasa komawa gidan ta ba, sati ɗaya ta kara a gida saboda yanayin laulayin da take fama da shi sannan ita da Harira su koma can gidan Hamma Lamiɗo ta buɗe shashenta ta share ta zauna tana jiran Hamma duk lokacin da zuciyarsa ta huce da kan shi zai neme ta. Ta dage da addu'a ba dare ba rana akan Allah ya sassauta zuciyar Hamma Lamiɗo zuwa gare ta. Kuma tana da tabbacin ita ce kawai ba ya kira amma yana kira Ammah da su Hamma Abdullahi, ya san halin da take ciki tunda tana dawowa gidan Hamma Abdullahi ya kawo cefane kenan ya san da halin da take ciki kuma ya san a in da take. Na cikin ne tana da tabbacin bai sani ba. Ammah ce za ta faɗa masa kuma kunyarta ba zai barta ta faɗa ba. Mami kuma a tunanin ya sa ni shi ya sa ba za ta yi tunanin sanar da shi ba. Su Hamma Abdullahi kuma wannan ba damuwar su ba ce ita ta dai ta dage da kula da kanta. Wannan karon ba ta so ta rasa jaririnta. Tana cin abinci amma tana laulayi mai zafi komai ta ci sai amai, ga miyau. Amma duk da haka tana daurewa ta ci abincin ko da za ta yi aman ne. Magungunar wajen Surayya Halin yau kuma tattarawa ta yi ta miƙa ma Baɗɗo ta ce ta ba ma su Iklima su yi amfani da shi, ita ai ta gama amfani da shi sai in Allah ya sauketa lafiya. Amma ba laifi ta fara mayar da jikinta wannan ramar ta ragu. Ta fara kula da jikinta tumbin ma ya ragu yana ta bajewa a hankali a hankali. *Janafty* Received at 07:52Reactions: ❤ 10, 🥰 1, 🤩 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby BAYAN WATA BIYU. JIMETA. Wattani biyu sun shuɗe kamar kiftawar idanuwana, a halin yanzu cikin Ummu Salma watannin shi biyu da wasu satittuka amma bai kai uku ba. Ammah kuma takaba ya gangara Baffa na cikin wattani uku da rasuwa za ta fita Takaba cikin azumi tunda azumin ya kusa bai fi wata ɗaya da wasu kwanaki ba. A cikin waɗanan wattani biyun Ummu Salma tana cikin laulayi ne mai zafin gaske irin laulayin da ba ta taɓa yin irin shi ba, ashe cikin mai sunan Baffa kamar kyauta ne ubangiji ya ba ta, ba ta san da haka ba sai da ta samu wannan cikin kuma da alamun haka za ta yi ta shan wahala har sai ta haife shi tunda tun cikin na sati biyu ta fara shan wahalan shi har kuma yanzu tana kan wahala ne. Duk kuma wannan wahalan da take sha Lamiɗo bai sani ba, tun rabuwarsu bai neme ta ba, itama ba ta sake neman shi ba ta kudirta a zuciyarta ko wani tsawon lokaci ne za ta jira shi tana kuma da yaƙinin in zuciyarsa ta yi sanyi zai neme ta. Ko a chart ba ta masa magana sai dai ta yi ta kallon hoton su tare tana hawaye, adadin kwanakin da ya ƙaurace mata adadin lissafin kaifin maganar da ta faɗa masa tabbas maganar ta cancanci a yi mata wannan hukuncin maganar tana da zafi da kaifi. Addu'anta kullum in ta yi salla Allah ya sausauta zuciyarsa a kanta ya yi mata afuwa. Ko da ba ya kiran ta a waya ta san yana neman lafiyanta a wajen makusanta ta. Su kuma daman ba su san wani abu ya faru ba kowa a tunaninsa tana zaune ne in Lamiɗo ya zo za su koma tare. Hamma Abdullahi na zuwa lokaci bayan lokaci yana duba ta, zai tambayeta in tana da matsala? sai ta ce babu. Laulayi ne kuma shi ba shi da magani. Sannan Baɗɗo ma zuwa lokaci bayan lokaci ta fara kasuwacin siyar da takalma mayafai turarukan wuta da na jiki. Gida kuma lokaci bayan lokaci za ta shirya ita da Harira su je can su yini har wani lokacin ma har su kwana kowa tausayinta yake ji har Ammah, saboda cikin mai amai ne komai ta ci sai ta yi amai haka nan za ta sake ci abin da ya tsaya shi ne rabon ta wanda ya fita kuma shike nan ga shi cikin rama yake sakata ko ta fara mayar da jikinta cikin lokaci sai ta koma ta bushe. Da Mami ta dawo ta je ta ganta ta ce cikinta mai laulayi ne sannan ba zai saka ta kiba ba, bushewa kawai za ta dinga yi sai kuma in ta haihu, sannan abu ɗaya take ci ya zauna a cikinta tuwo shima ɗin gaya, ko kuma in an shanya shi ya bushe sai a daka mata ta dinga cin sa da ƙulii, tuwo ko gaya yana kwana huɗu a firizanta tana cin sa, sannan ba ta son kamshin komai in ta shaƙa ko wani ƙamshi yini za ta yi amai ba zaman lafiya shi ya sa gidanta na nan dum Harira tuni ta daina saka turaran wuta itama Ummu Salmaan ta daina amfani da duk wani nau'in turare abu ɗaya ne ta ke son ƙamshin shi ƙamshin ƙasan anguwan su Ammah shi ake ɗibo mata a leda ta jiƙa shi da ruwa ƙamshin ƙasan take shinshina tana jin daɗi in kasar ta daina ƙamshi ta zubar ko Hamma Saddam ko Hamma Abdulrahim cikin su duk wanda ya samu dama shi ke diɓo mata ya kawo mata da yawa a baƙar leda ta zauna ta jiƙa shi da ruwa to yana gefen ta duk in da za ta zauna ko za ta kwanta tana shaƙa tana jin daɗi ta rage yawan yin miyau amma kuma yana taruwa a bakinta sai dai ba sosai ba. Ta koma asibiti sau biyu saboda yanayin cikin da ya zo da laulauyi an auna BF ɗin ta sun ce ba matsala. Duk kuma lokacin da za ta je sai sun riƙeta sun ƙara mata ruwa saboda yanayin yaushin jikinta sannan da dokar ta dinga cin abinci tana shan ruwa akai akai, to gwara ruwan tana sha wannan cikin ma mai sanyi yake iya karɓa don sai ya yi ƙanƙara ma take iya sha in ya huce ba za ta iya shan shi ba. Gata nan dai ta tsuge sai hanci wuyanta sai kasusuwa kowa tunanin shi laulayi ne ba su san har da kewar mijinta ba. Ta azabatu da kalaman bakinta, domin wannan horon ya yi mata nauyi sosai wataƙila yana tare da ita, da ba za ta wahala kamar haka ba. Ta yi magana da Hanan sau wajen uku bayan tafiyar su ta wayar Harira tana da Lambar Hidaya suna magana. Received at 07:54Reactions: ❤ 9, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Hanan ko a jikinta ba ta damu da rashin uwarta ba in dai suka yi magana sai dai ta ce Mahma yaushe za ki zo? A bakinta ta ji cewa Hamma Lamiɗo ya dawo har ya koma. Kenan da gaske yake yi har a yanzu bai gama hucewa da ita ba. Ba ta damu da Hanan ba ta san za ta samu dukkan kulawa wajen su Anitha. Bilkisu daman ba ita ke kula da yaran ba, ba su da lambar juna ba waya suke yi ba. Amma tana da tabbacin Bilkisu murna take yi da rahin dawowarta domin ita daman ba za ta so ta koma ba tunda ba ta son ta da mijinta. Sai dai ta yi hakuri domin tunda ta shiga ba za ta fita ba. Hidaya na turo ma Harira hotunan su Hanan ta WhatsApp tunda tana yi ga su nan duk sun kara mata girma a idanuwa a cikin wattanin da ba ta gan su ba, ga sabon gida nan fa sun manta sun tsufa a cikin shi. Shamsiya ko sai da ta daina ɗaukan wayanta in Hanan ne ai ta faɗa mata ba sa tare, amma sai ta dinga damunta da waya. Wata alaja ce ba ta fatan ya sake haɗa su an yi na farko kuma ya zama na ƙarshe kenan har gaban abada. Shi ya sa tana ganin kiran ta ba ta ɗagawa lambar ma ba ta yi saving ba amma da yake tun a baya ta san lambarta shi yasa da ta kira take gane ita ce. Kwanaki har saƙo ban hakuri ta turo mata wai ta yi hakuri tana damunta ne daman suna son tambayan lafiyan Hanan ne ko amsa Ummu Salma ba ta mayar mata ba ta goge saƙon ba su san da lafiyar Hanan ba sai yanzu? Lafiya ke sa a ji shuru in da ba lafiya da sun ji labari. Ta kyaleta da damuwar dake damunta. Ga kewar miji ga kewar Baffa. Tana da tabbacin rashin Baffa sai an daɗe kafin ya zame mata jiki gani take yi kamar Baffa zai dawo ta kasa gasgata mutuwarsa, gani take yi kamar zai dawo wata yar tafiya ya yi. Duk da babu abin da ta nema ta rasa kayan abinci ne ga su nan tsibiri guda a store sai kuma cefane duk wata Hamma Abdullahi zai kawo, su kifi su nama duk da ba ta ci sai dai Harira ta ci ko ta saka ta soya ko ta yi ferfesu ta kai ma su Ammah, wacce yanzu karɓa karba suke yi Umma Balki ta koma yanzu Umma A'i ke zaune da ita, suma ɗin babu abin da ba su da shi naman ne kifin ne sai abin da suka ga dama za su ci. Kuɗi kuma tun wanda Hamma Lamiɗo ya bar mata da zai tafi ko rabi ba ta taɓa ba, sai in Harira za ta je kasuwa ta ba ta sakon kayan marmari da su aya da goriba tana cin su, a asibiti ma likita ya ce ta yawaita shan kayan marmari saboda za su ƙara mata kuzari wani lokacin ta sha ta zauna lafiya wani lokacin kuma ta yini tana amai sai dai godiya kawai. Kewar mijinta har ya bayyana a idanuwanta da jikinta daurewa kawai take yi. Amma tana buƙatarsa ga shi ya yi mata nisa amma tana ji a jikinta nisan na ɗan lokaci ne koma mene ne ya kusa dawowa zuwa gare ta. Za ta duƙa har kasa ta ba shi hakurin laifinta kuma bakinta ya yi limzami har abada ba za ta ƙara gangancin furta irin waɗanan kalaman ba, ta yi ganganci ta yi kuskure ta yi kuma nadama tun a lokacin sai dai kuma nadamar ne mara amfani. * LAGOS. MARINE ROAD. THURSDAY, 12:00PM. Barcin sa ya yi nisa, hasken da ya dinga kashe masa idanuwa shi ya farkar da shi daga nannauyan barcin da ya kwashe shi tun bayan dawowarsa salla asuba. Kare fuskar shi ya yi da hannun daman shi yana ɗan yamutsa fuska. Dariyan ta ya ji, daman ya san ita ce. "Ranka ya daɗe pass 12, ka tashi ka yi wanka mu yi breakfast." Lumsssun idanuwansa da suka shige ciki saboda barci ya buɗe yana ɗan muskutawa sannan ya ɗan tashi zaune yana jinginar da kansa jikin masagalin gadon da yake kwance. Sannan lokaci ɗaya yana yaye bargon dake jikinsa. Sanye yake da dogon wando baƙi, amma wandon bai rufe masagalin kafafunsa ba, ana iya ganin ƙaurin kafafunsa ga ƙananun gargasa nan kwance luf a zararan dogayen ƙafafunsa. "Yara suna ta jiran ka, suma yau tare da Papa za su yi breakfast" Bilkisu ta sake faɗa lokaci ɗaya tana zama a gefen shi. Ta ci kwalliya cikin ado mai burgewa na riga da wando yan kanti ta naɗa wani mayafi mai santsi a saman kanta. In da ta buɗe labulen ya kalla rana ta fito sosai, wajen wani glass ne wanda in ka fita za ka samu wajen shan iska ga kujeru a wajen. "Good morning Papa." Received at 07:54Reactions: ❤ 6, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Hanan ko a jikinta ba ta damu da rashin uwarta ba in dai suka yi magana sai dai ta ce Mahma yaushe za ki zo? A bakinta ta ji cewa Hamma Lamiɗo ya dawo har ya koma. Kenan da gaske yake yi har a yanzu bai gama hucewa da ita ba. Ba ta damu da Hanan ba ta san za ta samu dukkan kulawa wajen su Anitha. Bilkisu daman ba ita ke kula da yaran ba, ba su da lambar juna ba waya suke yi ba. Amma tana da tabbacin Bilkisu murna take yi da rahin dawowarta domin ita daman ba za ta so ta koma ba tunda ba ta son ta da mijinta. Sai dai ta yi hakuri domin tunda ta shiga ba za ta fita ba. Hidaya na turo ma Harira hotunan su Hanan ta WhatsApp tunda tana yi ga su nan duk sun kara mata girma a idanuwa a cikin wattanin da ba ta gan su ba, ga sabon gida nan fa sun manta sun tsufa a cikin shi. Shamsiya ko sai da ta daina ɗaukan wayanta in Hanan ne ai ta faɗa mata ba sa tare, amma sai ta dinga damunta da waya. Wata alaja ce ba ta fatan ya sake haɗa su an yi na farko kuma ya zama na ƙarshe kenan har gaban abada. Shi ya sa tana ganin kiran ta ba ta ɗagawa lambar ma ba ta yi saving ba amma da yake tun a baya ta san lambarta shi yasa da ta kira take gane ita ce. Kwanaki har saƙo ban hakuri ta turo mata wai ta yi hakuri tana damunta ne daman suna son tambayan lafiyan Hanan ne ko amsa Ummu Salma ba ta mayar mata ba ta goge saƙon ba su san da lafiyar Hanan ba sai yanzu? Lafiya ke sa a ji shuru in da ba lafiya da sun ji labari. Ta kyaleta da damuwar dake damunta. Ga kewar miji ga kewar Baffa. Tana da tabbacin rashin Baffa sai an daɗe kafin ya zame mata jiki gani take yi kamar Baffa zai dawo ta kasa gasgata mutuwarsa, gani take yi kamar zai dawo wata yar tafiya ya yi. Duk da babu abin da ta nema ta rasa kayan abinci ne ga su nan tsibiri guda a store sai kuma cefane duk wata Hamma Abdullahi zai kawo, su kifi su nama duk da ba ta ci sai dai Harira ta ci ko ta saka ta soya ko ta yi ferfesu ta kai ma su Ammah, wacce yanzu karɓa karba suke yi Umma Balki ta koma yanzu Umma A'i ke zaune da ita, suma ɗin babu abin da ba su da shi naman ne kifin ne sai abin da suka ga dama za su ci. Kuɗi kuma tun wanda Hamma Lamiɗo ya bar mata da zai tafi ko rabi ba ta taɓa ba, sai in Harira za ta je kasuwa ta ba ta sakon kayan marmari da su aya da goriba tana cin su, a asibiti ma likita ya ce ta yawaita shan kayan marmari saboda za su ƙara mata kuzari wani lokacin ta sha ta zauna lafiya wani lokacin kuma ta yini tana amai sai dai godiya kawai. Kewar mijinta har ya bayyana a idanuwanta da jikinta daurewa kawai take yi. Amma tana buƙatarsa ga shi ya yi mata nisa amma tana ji a jikinta nisan na ɗan lokaci ne koma mene ne ya kusa dawowa zuwa gare ta. Za ta duƙa har kasa ta ba shi hakurin laifinta kuma bakinta ya yi limzami har abada ba za ta ƙara gangancin furta irin waɗanan kalaman ba, ta yi ganganci ta yi kuskure ta yi kuma nadama tun a lokacin sai dai kuma nadamar ne mara amfani. * LAGOS. MARINE ROAD. THURSDAY, 12:00PM. Barcin sa ya yi nisa, hasken da ya dinga kashe masa idanuwa shi ya farkar da shi daga nannauyan barcin da ya kwashe shi tun bayan dawowarsa salla asuba. Kare fuskar shi ya yi da hannun daman shi yana ɗan yamutsa fuska. Dariyan ta ya ji, daman ya san ita ce. "Ranka ya daɗe pass 12, ka tashi ka yi wanka mu yi breakfast." Lumsssun idanuwansa da suka shige ciki saboda barci ya buɗe yana ɗan muskutawa sannan ya ɗan tashi zaune yana jinginar da kansa jikin masagalin gadon da yake kwance. Sannan lokaci ɗaya yana yaye bargon dake jikinsa. Sanye yake da dogon wando baƙi, amma wandon bai rufe masagalin kafafunsa ba, ana iya ganin ƙaurin kafafunsa ga ƙananun gargasa nan kwance luf a zararan dogayen ƙafafunsa. "Yara suna ta jiran ka, suma yau tare da Papa za su yi breakfast" Bilkisu ta sake faɗa lokaci ɗaya tana zama a gefen shi. Ta ci kwalliya cikin ado mai burgewa na riga da wando yan kanti ta naɗa wani mayafi mai santsi a saman kanta. In da ta buɗe labulen ya kalla rana ta fito sosai, wajen wani glass ne wanda in ka fita za ka samu wajen shan iska ga kujeru a wajen. "Good morning Papa." Received at 07:54Reactions: ❤ 6, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta faɗa lokaci ɗaya tana rumgume shi. Shima sai ya ɗan rumgumota yana amsawa. "How was your night? "Am fine." Ta amsa shi tana masa mirmishi, goshinta ya sumbata ita kuma sai ta sumbaci leɓen shi suna kallon juna cikin mirmishi. Wanka ya ce zai yi, suka miƙe a tare tana jikinsa tana faɗa masa ta yi kewarsa sosai. "I'm with you." Ya amsa mata lokaci ɗaya yana sake sumbatar gefen kumatun ta. Tambayata yake yi yau ba za ta je asibiti ne ta ce za ta je sai after 1 za ta fita Sakin ta yi ya wuce tiolet ta bi shi da kallo kamar ta kamo shi ta lashe shi da gaske ta yi kewar sosai. Jiya da yamma ya dawo a gajiye yake shi ya sa daga ita har yaran bai wani zauna da su ba da wuri ma ya kwanta a bangaren shi ita kuma sai ta bar shi ya huta ta koma bangaren ta, ta kwana da safe ma daya ya dawo masallaci barcin ya koma. Yanzu ma ganin sha biyu ta gota shi ya sa ta zo ta she shi. Ta san in har aka yi azahar zai yi mata faɗan me ya sa ba ta tashe shi ba. Lamido zai iya asaran komai bai damu ba amma ban da asaran salla a cikin jam'i. Bargon ta ɗan janye tana gyaran gadon, baya so su Hidaya na shigar masa bangaren shi tun suna ma wancan gida ba wannan ba. Shi yasa in dai yana nan za ta ɗan gyara amma fa in baya nan Hidayar ke gyarawa ba za ta iya ba. Bayan ta ɗan ninke bargo ta ajiyesa a gefen gado ita ta koma ta zauna wayarsa dake saman side drower ta ɗauka wayarsa babu tsaro shi ya sa ta samu damar duba abin da take nema. Kwata'kwata babu sunan Umma Salma a call long ɗin shi. Ta duba bangaren sakonni ba ta ga wani sabon sako ba tun wanda ta gani ne wancan dawowar da ya yi ne anan ne ta tabbatar da zarginta wani laifi ne mai girma Ummu Salma ta aikata masa, zuciyarta ta yi mata tsalle lokacin da ta ga saƙon Ummu Salma na ya sake ta ranar dakyar ta iya barci saboda farinciki ta fara zargin ya yi sakin amma ba tare da kowa ya sani ba ko kuma an sani an rufe maganar ne saboda ba al'adar gidan Sarauta ba ne sakin mata. Tun wancan dawowar ta bincike wayar nan tas, nan ta gano rikita shin Umma Salma ke yi a baya da hotuna da videos tare da chart na kalaman soyayya ai dole ya rikice akanta amma ta duba date wajen wata biyu kenan ba su ƙara magana da juna ba, ba waya ba saƙo kenan zarginta ya zama gaskiya. Saurin ijiye masa wayar ta yi tana ɗan yarfa hannuwanta sama alamun murna, Allah ya ga zuciyarta ya kawo mata masalaha a cikin sauƙi, duk a wancan dawowar na shi ma ta yi ta dukan ruwan ciknsa ta ji wani magana game da Umma Salman bai faɗa mata ba daman ta san ba zai taɓa faɗa ba. Miƙewa ta yi, tana juyi a cikin bedroom ɗinsa mai kama da ɗakin turawa komai cikn tsari. Wannan gidan ya fi wancan girma sai biyu ma. Ga dai shashen Umma Salma can a rufe amma ba za ta dawo mata gida ba. Tunda suka dawo ta yi sallama da damuwa da tashin hankali ta mayar da jikinta kamar ba ita ba. Ganin Umma Salma kawai a gidan ta, tana giftawa barazana ne ga zaman lafiyanta amma yanzu ita shar, Hanan ce kawai ta rage kuma Ya Hadiza ta ce ta ƙyaleta kawai me yarinya ta sani? Ba ma haka ba Lamiɗo ba zai taɓa yarda ya mayar da Hanan ba duk da a surutun yarinyar ta ji tana faɗin Abba da Anty sai ta yi tunanin wataƙila yarinyar ta haɗu da ubanta na gaskiya ne sai ta kira Ammah daman tana kiran ta bayan ko wani kwana biyu suna gaisawa shi ne ta ɗan kawo mata zencen Hanan ɗin nan ko Ammah ta kwashe komai ta faɗa mata amma ba ta faɗa mata hatsaniyar da Umma Salma ta yi ba nan ta tabbatar da wataƙila nan gaba kaɗan Hanan ɗin ma za ta bar mata gidanta da mijinta da yaranta ta koma gidan su. Saboda son jin kwaf irin na Bilkisu har tambayan Ammah take yi ya wajen su Ummu Salma? Sai Ammah ta ce suna lafiya lau da yake Ammah na da kunyar fulani, ba ta faɗa mata zencen cikin Umma Salma ba, ballatana ta ji labarin cikin sai kawai ta cigaba da zama cikin yaƙinin ta cewa Lamiɗo ya saki Umma Salma ba, ko a can Masarauta Ya Hadiza ta ce ba ta ji wani labari ba kenan suna ɓoyewa ne aamma duka alamomin sun tabbatar da wani abu ya faru. Received at 07:54Reactions: ❤ 6, 👍 1, 🤗 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Duk da ta fahimci su Sultan sun shaƙu da Hanan ɗin ba ma su har Lamiɗon da su Hidaya kowa Hanan saboda kazar kazar ɗinta kuma zamanta a tare da Beena ya sake saka ma Beena himma sosai, ba ita ke kula da yaran ba amma dai tana duba su lokaci bayan lokaci ta fahimci Hanan tana da ƙokari kuma sannan bayan dawowarsu an yi Parents day ta je musu anan ne headteacher ɗin su Hanan ta ke cewa yarinyar na da ƙokari suna tunanin yi mata jumping zuwa nursery 2 ajin su Beena ta ce a barta a in da take ba ta so daga zuwan yarinya ta zo ta fi yaranta ƙokari shi ya sa ta faɗa ma Anitha ta dake ma da Beena ta daina wasa da karatu ba ta son a fita sannan ba ta son a fi yaranta gwara ma Sultan shi ba ta jinsa. Amma Hanan irin masu kaifin kwaƙwalwar nan ne sau daya za a yi mata karatu ta ɗauke shi ko a Qur'ani duk ta iya ƙananun surorin nan ga shi ta iya salla ta iya azkar ta ce Mami ta koya mata daman ai Mami ba ta da wasa. Har Safina matar Kabiru Bilkisu ta kira ta ji ko da gasken Lamiɗo ya saki Umma Salma amma ba ta ji wata magana ba. Ba saba waya suka yi ba shiya sa suna gama gaisawa da tambayan yara suka yi shuru Bilkisu kuma ego ɗin ta ya hana ta tambaya dole suka yi sallama. Murna kawai take yi farinciki ya cikata. Tana nan tsaye har ya fito daga tiolet sanye da rigar wanka. Ta juya tana kallon shi cikin wani shauƙi, Ummu Salma ta zo ta yi mata aiki kuma ta tafi ta bar mata mijinta da gidanta. Ta yi mata aikin dawo da Lamiɗo irin yadda take so, Lamiɗon da ba zai sanya wani hijabi a tsakaninsu ba. In a baya ne ba zai taɓa tsayawa a gabanta kirjinsa a buɗe ba sai ga shi yanzu komai ya sauya. Har wanka suna yi tare su kwanta fatar jikinsu na gogan na juna. Yanzu ɗin ma ita ta shafa masa lotion ta yi masa cumbing ɗin gashin kansa sannan ya shiga clotset ya zaɓo riga da wando, wando baki ne amma rigar milk colour ce duk ita ta siya masa, ganin yanzu ya daina zaɓan kalololi, itama ta zage in dai ta fita Shopping sai ta siya masa jin daɗin ta kuma yana saka kayan. Tare suka fito daga bangaren na shi suna masu rike da hannun juna. Har zuwa main falon, wani babban falo mai ɗauke da saitin kujeru wajen uku a falon. Sannan ga wata faskekiyar plasma mai kama da bango guda in kana kallo kamar mutane za su fito tsabar girma. Duka bangaren suna jikin juna ne, falt ne suna haɗe ne a waje ɗaya. Saboda Lamiɗo ba ya so na wanda ke rabe, wani ma za ka ga sai an samu tazara tsakanin wannan shashen da wannan amma shi ya fi son mai gabaɗaya. Bangaren Bilkisu ne a farko mai falo da bedroom uku da kitchen amma kafin bangarenta akwai korido da ƙofa da ya raba tsakanin bangarenta da na maigidan. Sai na Lamiɗo mai falo da bedroom 2, shima kafin na Umma Salma akwai dogon korido da ƙofa mai falo da 3 bedroom sai kitchen komai suna da shi a duka bangarorin su. Sannan daga can gefe ɗakin yara akwai falo sai ɗaki ɗaya babba in da gadajensu yake falo kuma Tv ne da kujeru sai kayan wasan su, jikin shi kuma bangaren su Sabuwa sun samu babban falo da ɗakunan barci guda biyu. Gidan ga haraban mai girma da motoci sama da goma za su samu wajen zama. Ga fulawowi masu kyau da Lamiɗo ya sanya James ya siyo aka cuka ana kula da su. Suma a waje akwai ɗaki ciki da falo wajen kwanan Baban Adila da James. Wancan gidan yana rufe ne kuma har yanzu ma akwai sauran kayan sawan su a gidan tun da ba siyarwa za a yi ba, shi ya sa ba su damu ba sannan ma kayan sawan ne sun yi musu yawa. A main falo akwai bangaren Dinning wanda duk wanda ya fito in ba wajen ya zo ba, ba zai gan su ba. Bangaren Dinning ne sai kitchen daga gefen shi babban ne. Debora ta gama shirya komai an jera shi cikin tsari. Su suka fara zama akan dinning ɗin sannan Bilkisu ta je ta zo da yaran suna falon su. Sultan ke wasa da bindigarsa ta roba yana harba ma su Hannan suna buya sun yi kaca kaca da falon. Sun yi wankan su tas da su kamar yaran turawa. Suna ganinta suka nufeta suna gaisheta har da Hanan kan yaranta kawai ta shafa ban da Hanan ta ce su je Dinning Papa na jiran su, ba ta nuna ma Hanan tsana amma ba ta sakin ma yarinyar fuska ba ta iya munafunci ba. Received at 07:54 11 people reacted with ❤ [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Duk da yarinya ce amma an ce ko mahaukaci ya san mai son shi. Hanan ta san Bilkisu ba ta son ta shiya sa itama ba ta shige mata. In ka ganta da Lamiɗo sai ka yi tunanin shi ne mahaifinta suna da shaƙuwa sosai yana son yarinya kamar yadda yake son uwarta. Sannan Anitha ma tana son Hanan saboda kwazon yarinyar da daɗin zama har su Hidaya ma in tana magana sukan ce kamar Umma Salma. Wacce ba ta dawo ba kuma ba halin tambayan Bilkisu amma da suka yi waya da Harira ta ce za su dawo in har Yarima ya je Adamawa. Yaran suna zuwa ɗaya bayan ɗaya Lamiɗo ya ɗauke su Suna ba shi peck a gefen kumatu suna gaishe shi ya amsa cikin farinciki yana shafa kawunansu. Daya bayan ɗaya yana kiran sunan su. "Sultan how are you? Ya amsa da I'm doing fine Papa. "Princesss Beena do you miss me? "Yes Papa. I miss you" Ta faɗa tana shigewa jikinsa. Ya rumgumeta yana shafa kanta. Hanan ta ja gefen rigan shi ya juya yana kallon ta. "Papa." "My Hanan." Takaicin Bilkisu yadda ya sauke Beena ya ɗauki Hanan tana yi masa zence da cancan muryanta ɗin nan Tana kan cinyarsa har ta gama serving ɗin su, sannan ta ce Hanan ɗin ta baro jikin Papa ta zauna su ci abinci. Sun fara cin abincin wajen ya yi shuru. Bilkisu ke kusa da Lamiɗo a layi ɗaya. Yaran kuma suna layi ɗaya Sultan na tsakiya Beena da Hanan a gefen shi. Kamar an suɓuto da maganar daga bakin Hanan ta kalli Lamiɗo tana faɗin yaushe zai kai ta wajen Mahma? Ya kalleta yana juya cokalin hannunsa da yake shan romon ferfesun kayan ciki. Kamar ba zai amsa ba sai can kuma ya ce sai sun yi hutun makaranta tana dariya ta ce har da wajen Mami da Daddy da Islam da Faruk da Barira ya ce duk za a kaita. Sultan da Beena ma suka ce za su je Lamiɗo ya ce gabaɗaya za su tafi. Bilkisu ta kasa ta tsare tana son ta ji wata magana bai yi wata alama da za ta fahimci wani abu ba. Ferfesun kayan ciki kawai ya ci da buredi sai tea ya ta shi ya shiga ciki su kuma ya bar su anan. Komawa ɗakinsa ya yi ya zauna a gefen gado ya janyo wayarsa bai taɓa boye wani abu ba sai akan Ummu Salma. Ma'ajiyar hotunan ta ne waɗanda take tura masa a baya wasu hotunan shi kaɗai ya dace ya kalla shi ya sa ya tarkasu zuwa wani folder ya yi hidden na su sauran ne masu mutumcin ya bar su da kowa zai iya gani. Wani hoto ne da ta yi masa ta saka wata shimi, lokacin cikin mai sunan Baffa har ya ɗan fara hudowa. Ana ganin shatin kirjinta ta cika ta yi fari ta yi kiba tana dariya a gaban madubi ta yi masa hoton ta tura masa. Hotunan ta sune ke deɓe maasa kewarta in ya taso masa. Ba ƙaramin dauriya ya yi a cikin wattanin ba. Ratan da ya gina a tsakaninsu saboda ya samu natsuwar zuciyarsa ne da kuma lokacin da zai yi tunani. Kuma bukatar shi ta biya domin ya samu lokaci sosai ya yi tunani kuma ya samu mafita a wattanin biyun da ya hana kan shi kiran Umma Salma da zuwa wajenta ya yi mata afuwa sama da sau goma, ya fahimci rauninta ya fahimci halin da take ciki ya fahimci a lokacin tana cikin wani hali, tana buƙatar lallashi zuciyarta ba daɗi ya fahimci maganar da ta faɗa masa ba da gangan ba ne, wani abu ne da ya fito daga zuciyarta. A lokacin kuma tana cikin rauni wataƙila ba ta ma san ta faɗi maganar ba sai da ta fita. Ya yi mata uziri sannan ya yafe mata. Wattanin biyun da bai neme ta ba horo ne na laifin da ta aikata masa a lokacin da ya taho da ita ya fusata ba zai saurareta ba wataƙila da zukatansu ba su samu natsuwan da za su gano kuskuren junan su da yin afuwa ba. Amma yanzu ya fahimci a kadamin da take a wancan lokacin, sannan ya yi mata uziri ba ƙaramin dauriya ya yi ba amma ya yi kewar Umma Salma kewar da ke kassara kuzarinsa ba shi da aiki sai kallon hotunan ta ko video ɗin ta bibiyan chart din su kawai yana saka shi jin daɗi ya daɗe da cire ta daga in da ya kai ta amma kuma ba ta kira shi ba, shi kuma ba ya son su tattauna komai ta waya sai ya je ga ta ga shi. Shi ya sa a wannan dawowar ya yanke shawaran zai je can Adamawa saboda Umma Salma sannan ya duba Ammah. Received at 07:54Reactions: ❤ 10, 👍 1, 👏 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Duk da yana sanin halin da suke cikibyana waya da Ammah itama Umma Salma yana jin labarinta a wajen su Hamma Abdullahi. A cikin su kuma ba wanda ya taɓa katarin faɗa masa Umma Salma na da ciki kowa a tunanin shi ya sani ne. Mami ma farkon tafiyan shi da suka yi magana har wata magana ta faɗa masa ya kasa gane kan maganar kuma bai tambaya ba. Cewa ta yi Allah ya ga hakurin su ga shi nan ya sake ba su wani rabon. Bai tambaya ba sannan bai damu da bin kadin maganar ba ballatana ya fahimci in da ta dosa. A tunanin kowa a bakin matarsa zai fara ji shi ya sa ba wanda ya yi tunanin bai sani ba. Yana kallon hoton yana mirmishi ya saka tafin hannunsa ya shafa screen ɗin wayar daidai bakinta. Ya yi kewar komai na ta surutunta, hirarta kiran shi Hamma shagwaɓarta komai na ta, all ya yi missing. Kewarta na murƙuƙusan shi. kewar kasancewa da ita ya sha yin mafarkin sun kaɗaice da juna ya yi mata horo amma shi ne ya hora kan shi komai mene ta yi laifi kuma ya horata, ya yafe mata zai je su haɗu ya ba ta hakuri domin shima ya yi mata laifi, wani abu da ya ji ta ƙara burgeshi shi ne bata faɗa ma kowa halin da suke ciki ba personal life ɗinsu ne su zauna su warware shi. Ranar lahadi zai tafi Adamawa hutunsa na kwana goma ne kaɗai zai koma bakin aikinsa. Zai je ya taho da ita, domin rashinta a gidan ma duk ba daɗi. Yana nan zaune har lokacin salla ya yi sai ya fita daga kan hoton ya shiga tiolet ya yi alwala. Sannan ya fito ya saka jallabiya ya saka hula zai fita kenan sai ga Bilkisu nan suka yi sallama domin ta ce kafin ya dawo za ta tafi asibiti. Yana fita haraba ya ga motar Ummu Salma lullube a cikin tamfol, ɗan kaɗa kai kawai ya yi ya wuce tunani ma ya manta bai nemi Sultan ba shi kaɗai ya tafi masallacin yana dawowa ya iske Bilkisu ta tafi sai su Sultan ya tambaya sun yi salla suka ce aa nan ya tara su zuwa ɗakinsu, suka yi alwala suka yi salla a gaban shi sannan ya ce kowa ya ɗauko littafan makarantan shi wanda ya fi ƙokari za a yi masa kyauta. Suna rige rige, nan ɗakin yaran ya zauna har La'asar yana tare da su yana biye ma surutunsu. * JIMETA. Yau ta kama lahadi ne, weekend kusan duka ma'aikata suna gida. Tun safe Umma Salma ke doka ma Hamma Saddam waya ba ya ɗauka ta kira Hamma Abdulrahim shima bai ɗaga wayarta ba. Kasarta ta daina ƙamshi tun jiya ta yi ma Hamma Saddam magana a chart ya ce yau da safe zai ɗibo ya kawo mata amma kuma ta ji shuru, ƙarfe goma na safe har ta gota kuma in ba ta shaki kamshin wannan kasar ba yau ba zaman lafiya. Har ƙasan waje Harira ta fito ta ɗibo mata ta jiƙa ta shinshina amma ba ta ji irin ƙamshin da na anguwan su Ammah ke yi ba ta ce ba ta so amai ma ƙamshin ƙasan ya saka ta. Ta kasa cin komai tunda garin Allah ya waye. Sai ta shaƙi ƙamshin wannan ƙasan sannan za ta samu sukuni da zaman lafiya. Daman ba ta aiki Harira ke yin komai a gidan. Sai ɗan abin da ba za a rasa ba kamar gyara ɗakinta girki ma ba ta yi saboda ba ta son shaƙan ko wani ƙamshi in abinci ya tafasa ta shaƙi kamshi yini za ta yi amai sannan ba ta son wari maggi ɗunkule in abinci ne za ta iya ci amma ba ta son ƙamshin shi, shi ya sa in dai Harira za ta yi girki sai ta kulle kitchen ɗin yadda ƙamshin abincin ba zai fito ba. Kamshin ƙasan nan ta anguwan su Ammah kaɗai take so. Tana zaune falo ne, daga ita sai riga doguwar riga bubu ce mai sakewa, ba ta da nauyi cikin rigunan da Baɗɗo ta saro ne ta siya wajen kala huɗu ta siya ma Harira ma su take sawa tana jin daɗin su domin yanzu ba ta son saka kaya saboda zafi. Wannan cikin iska yake so da A.C ma take kwana ta yi ma likita ƙorafi zuwanta na ƙarshe ya ce saboda da cikin ne sannan da BP. masu hawan jini ba sa shiri da zafi. Harira ta gama gyaran falon tana kitchen tana wanke-wanke. Ita fa ko warin moneyfresh ba ta so, sabulun wanka ma da na wanki take amfani da shi mara ƙamshi, duk ta tattara showe gel ɗinta da sabulanta ta ajiyesu gefe. Lotion na shafawa ma a jiki yanzu ta daina shafawa, saboda ƙamshi. Received at 07:54Reactions: ❤ 9, 🔥 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ko wani mai yana da ƙamshi har mankaɗe Ammah ta aiko mata ta dinga shafawa sau daya ta shafa ba ta kara ba wari warin ya dinga tashin zuciyarta. Yanzu haka nan take wanka ba ta shafa mai ya fiye mata zaman lafiya. Gajiya ta yi da zaman sai ta sauko ta zauna a saman cafet sannan ta miƙe kafafunta Tv na kunne a tashar arewa24 hankalinta ba shi a wajen yana wajen wayarta da ke hannunta tana cigaba da kiran su Saddam amma ba su ɗauka ba. "Suna can suna ta barci" Ta faɗa a sarari kafin ta ɗan ja tsaki. Ita fa in ba ta shaƙi wannan ƙamshin ba akwai matsala. TV Ta ƙura ma idanuwana suna haska wani hausa film wai tarko. Ita yanzu ta rage ma wannan kalle kallen, tun rasuwar Baffa kamar an sauyata. Bayan dawowarsu gidan sun daɗe ba sa kunna kallo. Gabaɗaya komai ya fita kanta na waɗanda take ɗan bi a ma Tiktok ko Youtube duk ta daina bin su, girke-girken ma ta watsar da komai yanzu ta kanta take yi. Rasuwar Baffa ta sanyata cikin ƙunci sannan ga rashin jaririnta ga abin da ya faru tsakaninta da Hamma daga karshe ga cikin da ta samu duk sai rayuwarta ta zama kamar an juya ta daga sama zuwa ƙasa. Gwara ma littafan hausa da Baɗɗo ta matsa mata ta fara ji a youtube a tashar tsakar gida, na Mai sanyi ta fara sauraran wani littafi Ɗingishi kwaɗo na marubuciya Surayya Dee mai bojuwa, ta fahimci dai Baɗɗo na yin matan nan tunda har littafanta take matsa mata ta saurara. Kuma ba laifi da ta fara sauraran ya fara mata daɗi, tunda karatun yanzu wahala zai zame mata. Ko Ep13 ba ta kai ba ta watsar sai tana cikin ji sai kawai tunani su yi mata yawa sai can in ta dawo ta ga karatu ya yi nisa baya ba ta fahimci komai ba. Tunda kuma ta watsar ba ta sake bi ta kan shi ba sam ba ta da natsuwa. Kanta da ba ɗankwali ta sosa kalaba ne ya fi sati uku Baɗɗo ce ta zo ta yi mata shi. Ya tsufa shi ya sa yake ta ƙaiƙayi. Da ta ga sun ƙi ɗaga wayarta sai kawai ta kira wayar Ammah ba ta jima tana ringing ba ta ɗaga wayar suka gaisa. "Ammah ina tazuran samarin ki? "Suna bangarensu suna barcin tunda suka shigo nan bayan sun dawo masallaci ban ƙara ganin su ba, ga abin karyawansu ma can a kitchen ba su ga dama sun tashi ba." "Ammah ina ta kiran su ne ba su ɗauka ba." Ta faɗa kamar za ta yi kuka. "Na ce miki suna can suna barci ba yau lahadi ba." "To Ammah ya zan yi? "Na me kenan? Ammah ta amsa mata. "Kasar ne ta daina ƙamshin Hamma Saddam ya ce yau zai ɗibo mini da safe har yanzu shuru." "Ai fa shurun ne, to ki yi haƙuri in sun ta shi sai ya kawo miki." "Ammah ina son in shaƙi kamshin ne, ba ki ji zuciya ta ba." A shagwaɓe take magana "Harira to ta ɗibo miki nan kofar gida mana " "Ta ɗibo ba irin na ku ba, ba ta ƙamshi kamar na kofar gidan mu." "To" Ammah ta faɗa a fili a zuciyarta tana faɗin wannan cikin akwai tsirfa. A kullum addu'arta Allah ya sauki Auta lafiya. "Ammah in ban shaƙa ba ji nake yi kamar sheɗata za ta ɗauke kuma ba zan iya cin abinci ba." "To ai sai dai ki yi haƙuri su tashi barcin." Kamar za ta yi kuka tana tambayan Ammah ba wanda zai kawo mata. "Babu sai ni ko Ummarki A'i." Baƙa Ammah ta mayar mata ya sa ta fara dariya. "Ki fara gwada cin ko goro ne. Saboda tashin zuciya." "To Ammah ki ba ma Hamma Saddam ya kawo mini." "Ba ni da shi, zan ce ya biya kasuwa ya siyo miki mai yawa ki gwada ki gani." Ta amsa da yauwa, Umma A'i ce ta karɓi wayar tana mata faɗan ta rage shan kankarar nan da ta ga tana sha, cewa kawai ta yi to domin in za ta kwana tana bayani ba za ta gane ba wannan cikin na dabam ne wahala kawai yake ba ta. Bayan sun gama wayar har shaƙuwa ma ta fara yi tana jin zuciyarta wani iri kofofin hancinta na buɗewa ƙamshin da take son shaka ba ta samu ba. Ta ga dai su Hamma Saddam jiran su ma ɓata lokaci ne watakila ma sai yamma. Sai kawai ta jwala ma Harira kira sai ga shi ta fito tana goge ruwan hannunta a zanin jikinta "Gani ranki ya daɗe kina bukatar wani abu ne? Ta faɗa tana duƙawa a gefen in da take zaune "Harira ni fa na ce ki daina ce mini wani ranki ya daɗe, ki ce mini Anty kawai." Ta gama faɗa tana hararan Hariran da ta sadda kai ƙasa tana ɗan mirmishu. Received at 07:54Reactions: ❤ 9, 👍 1, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Aa ranki ya daɗe ai girman ki ne, na saba ne ba zan cewa Antyn ba ne.' "Ke kika sani dai." Ummu Salma ta faɗa tana ɗan muskutawa "Gida za ki zo ki je, ba ma sai kin shiga ba ki yi tashar adaidaita ya tsaya ki samu ƙatuwar leda ki ɗibo mini kasa yadda zan daɗe ina amfani da ita." "To ranki ya daɗe." "Kin gama wanke-wanken? "Saura kaɗan." "To karisa sai ki zo ki tafi Harira wallahi wani iri nake ji kin san in ba kasar nan yau ba zaman lafiya Hamma Saddam kuma da na dogara da shi ina ta kiran wayarsa ba ya ɗagawa." Harira ta miƙe tana faɗin bari ta ƙarisa da hanzari. Ba daɗewa kuma ta gama ta dawo, tana zuwa Ummu Salma ta toshe hanci. "Harira kina ƙamshin sabulun nan na wanke wanke." Harira ta shinshina hannunta kuma ƙamshin take yi, shi daman yana da ƙamshi sosai. Sai ta yi baya tana faɗin "Kuma na wanke hannu." "Shiga ɗakina a drower gefen gado ta hannun dama za ki ga kuɗi a farar takarda ki ɗauko dubu biyu" Ta gama faɗa tana sake toshe hancinta zuciyarta har ta fara tashi da sauri Harira ta amsa ta shiga ɗakin Umma Salma ta ɗauko sakon Harira Amintaciya ce a wajenta ta sha gwadata akan kuɗi ba ta taɓa kama ta da laifin sata ba, tana son Harira domin duk abin da take so kafin ma ta yi magana ta aiwatar. Shi yasa itama take kyautata mata, tuni ta saka Hamma Saddam ya buɗe ma Harira Opay a wayarta tana tura mata kuɗi ta tura can wajen danginta sannan tana saka mata kati wanda za ta siya data Harira ta yi karatu kawai ba ta gama sakandiri ba ne ta faɗa aikin bauta. Amma tana da burin nan gaba ta ba ma Harira jari da za ta tsayu da kafafunta wata rana in har ta samu miji ita da Hamma Lamiɗo za su aurar da ita. Harira ta sanyo hijabinta ta fita Ummu Salma na cewa ta yi sauri karma ta shiga gida ta ce to. Ta bar Umma Salma ita kaɗai TV na ɓaɓatun shi. Fitan Harira ko minti talatin ba ta yi ba sai gata ta dawo, ta ce ta manta ba ta ɗau leda ba tunda suna da ledojin na cefanen da ake kawo musu, a hanya ta tsaya ta siya bakko ta kusa yin rabin ta da ƙasa. Jikin Umma Salma har yana rawa ta dinga shinshinawa. "Kai Harira aikin ki na kyau ta wajena." Tana shinshina ƙasar har tana sauke ajiyar Zuciya. Nan ta ce Harira ta ɗauko mata leda ta ɗiba ta jika mata shi da ruwa. "Ba ki dai shiga gida ba ko? "Ai kin ce kar na shiga ranki ya daɗe. Mutane ne dai na ta kallona sun ga ina ta ɗiban ƙasa." Ummu Salma ta yi dariya kafin ta ce. "Ai sai ki ce lalura ce ba da gangan ba ne." Harira ta amsa da ba su mini magana ba amma mamaki suke yi na me zan yi da ƙasa haka, mai adaidaitan da yakai ni ma ya jirani sai da ya tambaya na ce masa na mai ciki ne ya ce wallahi shima matarsa ƙamshin yashi take so. "Gwara da kika faɗa masa kar ya ce na asiri ne." Dukkansu suka yi dariya. Sannan Harira ta tafi kitchen ta ɗauko mata roban gwangwanin madara da ya ƙare ta ce bari kawai a zuba a ciki ta huta da leda "Kuma fa hakane, to zuba da sauri ki jiƙa mini, wannan kuma ki ɓoye mini a cikin kitchen" Harira ta aiwatar da duka umarninta. Lokacin da ta kai hancinta tana shaƙan kamshin har jikinta sai da ta ji ya samu natsuwa cikinta kuma ta ji kamar ya juya. Shike nan ta samu zaman lafiya Hamma Saddam kuma sai wajen sha biyu da rabi ya kira ta haushi ya sa ba ta ɗaga wayarsa ba. Ba amfanin da zai yi mata kuma a yanzu ga ƙasarta a hannunta tana shinshina kamar wata mage. Sallar azahar ya sa ta bar falo ta koma ciki ta yi salla. Ta kwanta tana ta barci saboda likita ya ce ta dinga samun barci sosai wajen uku na rana yunwa ya tashe ta, ta je kitchen ta nemo sauran tuwonta tun na shekaranjiya da Harira ta yi mata da miyar kuka ta ciro a firiza ta kunna gas ta ɗumama miyar ba manja ba maggi dunƙule sai gishiri shima kaɗan sai farin maggi, ba ta son ko wani ƙamshi. Kodayaushe ta zo kunna gas sai ta tuna da wani abu ya faru farkon dawowarsu kawai ta shigo kitchen ta rasa abin da za ta yi, kawai sai ta kunna gas ta ɗora tukunya ta manta kawai ta koma ɗaki ta kwanta, Allah ya taimaka Harira ta zo kitchen ɗin ta ji ƙauri, da sauri ta kashe gas ɗin ta sauke tukunyar har ta fara ƙonewa da Harira ke faɗa mata shuru kawai ta yi ba ta san ta yi ba Received at 07:54Reactions: ❤ 15, 👍 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby abubuwa suna yi mata wani irin tun bayan abin da ya same ta na rasa jarirnta, sannan tana zaune kawai sai ta dinga jin wani ƙara a cikin kanta, ƙaran mai yawa yana barazanar fasa kunnuwanta, chanje-chanje da dama take fuskata da ta koma asibiti ta yi musu bayanin likitan ya ba ta tabbacin alamomin cutar Eclampsia da ta yi fama da shi ne lokacin da ta haihu, amma ta gode ma Allah ta fita daga haɗari suma canje canje a hankali za ta daina fuskartarsu. Kullum ta yi salla sai ta yi ma Allah godiya da ya tsare ta da wannan cutar, domin tana da haɗari itama za ta iya ba da labarin haɗarin ta. A kitchen ɗin ta ci tuwon nan ta wanke hannunta sannan ta koma ɗaki Harira na cikin ɗakinta wataƙila ta kwanta ne. Da ta koma ɗaki ba ta kwanta ba sai ta fara gyara kayanta wajen kwana huɗu kenan mai wanki ya kawo su da sauran ƙananun da Harira ta wanke mata ita kuma ta ce ta bar mata za ta gyara su amma ta kasa. Sai da ta gama tas ta jera a wardrope sannan ta shiga tiolet ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito ba shafa mai take yi ba doguwar rigarta kawai ta material ta saka akwai tattara ta ƙasa sai aka sake ta. Akwai zanen baƙi a cikin material ɗin sai ta saka hula baka ta rufe kitsonta da ya tsufa. Falo ta fito ta zauna a saman kujera tana canza tasha zuwa Saira movies ta ga suna maimaicin shirin gidan Sarauta. Ba daɗewa sai ga Harira ta fito, tana tambayan abin da za a dafa. "Harira ni fa ba cin abincin nan zan yi ba kullum sai kin tambaya ne? Harira ta sunkuyar da kai ba ta yi magana ba. "Ki je ki dafa duk abin da kike so Harira nan fa gidanmu ne." "To ranki ya dade" Har ta wuce sai ta dawo. "Ba za a yi miki wani abu ba? "Tuwo ne kuma ina ɗan da sauran shi, bari da safe sai ki yi mini wani" Harira ta wuce kitchen tana faɗin Allah ya kaimu. Ta bar Ummu Salma na kallo. Ta mayar da hankalinta kan kallo amma ba ta jin nishaɗin da take ji a da in tana kallo gata nan dai zaune kawai. Adaidai lokacin da agogon bangon dake falo ya harba 4:30pm na yamma daidai ta ji ana buga ƙofa an yi knooking na farko ba ta tashi ba, ta ɗauka ma Saddam ne har tana tura baki. To tun ɗazu ta so zuwansa bai zo ba sai yanzu. Ta ji daɗin zaman kamar kar ta tashi sannan ga Harira na kitchen akwai ba da wahala ta ce ta baro kitchen ta zo ta buɗe ƙofa. Sai biyu aka yi knooking sannan ta iya miƙewa ta isa ga ƙofar ta buɗe Tana buɗe ƙofar ta juya ko kallon wanda ke tsaye ma ba ta yi ba. "Sai yanzu? Ai Sai ɗan cikina ya bare da na tsaya jiran ka." Ta faɗa tana komawa ta zauna a in da ta tashi. Abin da ya ba ta mamaki jin shuru ba ta ji motsi ko surutun Hamma Saddam ba, shi da tun kafin ya shigo ake fara jin karaɗinsa. Sai ta juya a hankali wanda ta yi arba da shi ne ya sa gudun zuciyarta tsayawa na wani lokaci. Kasala da wani irin sanyi ya lulluɓeta a lokaci ɗaya nauyin jikinta sai ya ƙaru. Ya shigo falon sannan ya saka hannu rufe ƙofar falon Lokacin da ya fara takowa a tsakiyar falon ƙirjinta ya fara bugawa fat! Fat! Ta kafe shi da idanuwana ba kiftawa shima ita yake kallo da yanayin kallon nan na shi mai sanyata kasala. *Janafty* Received at 07:54Reactions: ❤ 19, 🥰 1, 😁 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Duk takun zai yi domin matsowa zuwa gareta, tare yake da tsinkewar zuciyarta. Ita ta fara ɗauke idanuwanta a kan shi domin ba za ta iya juran kallon shi ba tana jin wani iri kaifaffun idanuwansa da kuma ƙwarjinsa sun cika falon ga ƙofofin hancinta na shaƙo mata sanyayyan ƙamshin shi wanda a baya yake sanyata cikin shauƙi da soyayya amma yau zuciyarta ne ta fara tsinkewa tana jin kamar za ta yi amai tunda ya shigo falon ƙamshin gabaɗaya ya gauraye falon. Kanta na ƙasa tana wasa da zoben azurfan da Mai martaba ya yi mata kyautar shi tana jin a jikinta da zuciyanta Hamma Lamiɗo bai daina kallonta ba sannan yana ƙara kusantowa zuwa gare ta ne. Jikinta har rawa ya fara saboda fargaba, duk da ta daɗe tana shirya maganganun da za ta kare kanta duk ranar da Hamma ya waiwayota amma kuma ganin shi a gabanta bagatatan ya wargaje duka shirinta, ta kasa ko iya kallon shi ta kasa miƙewa saboda yadda jikinta ya yi mata nauyi. "Ummu Salama." Ta ji ya kira sunanta a hankali da wannan muryan na shi cikin amo. Sai idanuwanta suka cika da ƙwalla ta yi kewar kiran sunanta da yake yi shi kaɗai ne ke kiranta da Ummu Salama. Ta ɗago suka sake haɗa idanuwana wannan karon har ya ƙariso gabda yana tsaye hannunsa guda ɗaya a cikin aljihun bakin yadin dake jikinsa ɗinkin riga da wando har da babban riga. Amma babban rigan tana hannun shi na dama, kafafuna sanye da budaɗɗen takalmi na fata baƙi kansa kuma ya saka baƙar hula gashin sa ya fito ta gefe da gefen hulan sannan fuskarsa ta yi fayau tunda ya rage gashin gemu sa da sajensa gabaɗaya. Kallon shi take yi tana ji kamar ba Hamma Lamiɗon da ta sani a shekara ɗaya da wani abu baya ba. Kamar Hamma Lamiɗo da ta sani dai a shekarun baya ne. Ta kasa iya motsi ballatana ta iya amsa kiran sunanta da ya yi ko ta yi masa sannu da zuwa ba komai ya ƙwace mata kanta ta mayar ƙasa tana jin tafin kafafunta na ɗaukan ɗumi sosai. Wattani biyu ta yi ba ta gan shi ba amma ji take yi kamar shekara ce. Shi ko kallonta yake yi da dukkan zuciyarsa. Me ya same ta? Ya ga ta rame wuyanta sun faɗa idanuwanta sun ƙanƙance komai na ta ya sauya ba kamar yadda ya tafi ya barta ba. Wani abu ne ya faru da ita ne? "What wrong with you? "Are you sick? Tambayoyin duk a tare ya jera mata su, ita kuma lokacin zuciyarta ne ke cigaba da tsinkewa tana jin kamar za ta yi amai shi ya sa ta miƙe dakyar tana jin kamar jikinta ya yi ma kafafunta nauyi. "Sannu da zuwa." Ta faɗa cikin sanyin murya amma ta ki bari su sake haɗa ido. Ya amsa da yauwa a iya fatar bakinsa. "Na ce ba ki da lafiya ne? Ya sake tambaya yana mai ƙureta da idanuwansa. Yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa? Me ya sa ba a faɗa masa ba? Kuma dalilin da ya sa ya ke turo Abdullahi kenan amma sai ya ba shi tabbacin lafiyanta lau, me ya sa ta rame? Gabaɗaya ta sauya masa ta yi baƙi kamar ba Ummu Salama ba. "I'm asking you. Ba ki da lafiya ne? Ya sake maimata tambayar wannan karon muryansa ta ɗan buɗe. Ba ta so hawayen da suka kawo mata su zubo, hancinta kuma ya gaji da shaƙar iskar ƙamshin turarensa zuciyanta na yunƙurin amai kawai sai ta juya baya daidai lokacin da hawayen suka taho mata. "Lafiya ta ƙalau Hamma." Ta amsa shi da raunin murya kafin ta kwashi sauri tana mai rufe baki zuwa ɗakinta amai ne ya taho mata take saurin isa tiolet kafin ta sake shi anan shi kuma tunanin shi ko ta gudu ne sai ya taka ya bi bayanta. Yau ba gudu ba duk wani rashin fahimta dake tsakaninsu za su warware shi. Yana shiga ɗakinta ya ji ƙakarin amai a tiolet da sauri ya ajiye rigar hannun shi a saman gado ya buɗe ƙofar tiolet ya shiga tana durjushe a tiolet ɗin tana ta kwarara amai duk tuwon da ta ci ne shi ne take amayarwa daman ya sani ba ta da lafiya yana ganinta ya fahimci haka kamar ba jini a jikinta. Bai damu da kar ta ɓata shi ba, bai damu da warin amai ba, haka ya shiga tiolet ɗin ya riƙeta lokaci ɗaya yana rankwafawa yana yi mata sannu. Received at 17:28 8 people reacted with ❤ [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta ba shi tausayi yadda take amai, kamar hanjin cikinta zai zazzage daga ƙarshe ma sai ruwa kawai ke fitowa, shi bai san shi ne ciwon ta ba ƙamshin jikinsa da take shaƙa shi ke ƙara saka mata hararwa ta rasa kuma yadda za ta yi masa bayani ya fahimta. Jikinta sai rawa yake yi, tana mayar da numfashi sama sama in ta yunƙura ta yi aman ba ya zuwa sai wahala take sha, shi kuma yana ta faman yi mata sannu. Ta jingina da bango tana mayar da numfashi. "Sannu." Ya faɗa yanan mikewa tsaye. "Ki tashi ki wanke jikin ki, mu je asibiti." Ta kalleshi hawaye suka kece mata a saman fuskarta. "Hamma." Ta kira shi cikin raunin murya. "Na'am." Ya amsa yana kiran nata na ratsa duka jikinsa da zuciyarsa "Ciwo na yanzu ba shi da magani." Ta faɗa tana yi masa mirmishi. Ji take yi kamar za ta yi amai amma ba komai a cikinta ba ta son ƙamshin nan tana so ta ce ya fita ta kasa. "What? Akwai ciwon da ba shi da magani ne? "Akwai." Sai kawai ya zura mata idanuwana yana kallonta kirjinsa na duka, ta ga fargaba da tsoro a kallon da yake yi mata. "Hamma." Ta sauke numfashi. "Ka je waje, zan yi wanka ne." Ta gama faɗa tana yunƙurawa kamar wani aman zai fito amma kuma babu komai. Ya kalleta sai ta gyaɗa masa kai shi kuma sai ya fara nannaɗe hannun rigan shi wai zai taimaka mata ta gyara jikinta. "Aa." "Zan iya da kaina." Ganin kamar ba ta so sai ya ƙyaleta ya fito ya janyo mata kofa, yana fita ta rarrafa ta yi floshing ɗin aman da ta yi ya wuce rigar jikinta ma duk ta ɓaci da amai cire kayan da ta yi ta watsa ma jikinta ruwan sanyi. Ta fito ɗaure da towel har lokacin yana ɗakin zaune bakin gado yana jiranta. Bedroom din na ta ma ya gauraye da ƙamshin sa Da hanzari ya taso ya nufe ta, sai ta yi baya da sauri tana toshe hanci wallahi kamar za ta mutu haka take ji shi kuma mamaki ya sa kawai ya tsaya yana kallonta ya kasa magana. Dube-dube take yi ina ta baro ƙasanta shi kawai za ta shaka ta zauna lafiya. Sai ta tuna yana falo da gudu ta fita shima sai ya bi bayanta yana tunanin ko bayan baya nan aljanu sun shafeta ne Ya tsaya kawai yana kallonta ganin ta ɗauko gwangwanin madara ta buɗe ta kafa kai tana shaƙa har wani lumshe idanuwa take yi. Ya ɗauka ma madaran ne a ciki take so ta sha har hankalinsa ya kwanta amma sai ya lura koma mene shaƙan shi take yi ba sha za ta yi ba Ita ba ma ta shi take yi ba shakan ƙamshin ƙasan take yi kamar da zuciyarta. Har wani daɗi daɗi take ji. Harira ce ta fito daga kitchen sai ta yi kiciɓis da Yarima ta yi ƙasa da sauri tana yi masa sannu da zuwa Ya juya ya kalleta sau ɗaya ya amsa. Ya koma ya kalli Ummu Salama ya fara tunanin akwai abin da ke faruwa da ita wanda shi bai sani ba. Kamar zai tambayi Harira sai kuma ya fasa itama ta tashi ta koma kitchen ƙarisawa ya yi kusa da Ummu Salma ba ta ma sani sai ganin kan shi kawai ta yi ya leka gwangwanin hannun ta. "Ƙasa.? Ya faɗa a saman leɓen shi cikin mamaki. Ita kuma matsowan shi kusa da ita yasa ta yi tsalle ta koma gefe har towel ɗin jikinta na neman faɗuwa ta tare shi da hannu ɗaya. "Hamma." "Ka tsaya anan" Idanuwansa a kanta innalillahi tabbas wani abu ya same ta wanda bai sani ba. Me ta ke yi da ƙasa kuma? Ko Depression ne ya kamata ko wani cuta a ƙwakwalwarta amma in ba haka ba me ya sa za ta yi ta shinshinar ƙasa sannan ta hana shi ya matso kusa da ita. Tausayin ta ya lulluɓeta koma mene ne ya faru duk shi ne sila da ace tana tare da shi da ba ta samu wannan laluran ba. Ya yi tsaye kawai yana ganin ta tana ta shinshinar ƙasa. "Me kike yi haka? "Kasa ne fa" Ya faɗa muryansa na yin ƙasa. "Ina so ne." Ta amsa mishi, sannan ta kalle shi tana yi masa mirmishi. "Come here." Ya faɗa yana ya fito ta da hannunsa guda ɗaya. "Hamma." "Ƙamshin turarankaa ne ke saka ni amai da tashin zuciya." Ya sake yin sakayau kawai yana kallonta. Ya kasa gane abin da ke faruwa. "Meke damun ki? "Ciki gare ni." Ta ba shi amsa kai tsaye sannan ta bi ta bayan kujera ta wuce. "Ka jira ni anan." Received at 17:28 15 people reacted with ❤ [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ba ta so ya biyo ta ɗakin, kamar daman umarninta yake bi ya yi tsaye yana kallonta har ta shige ɗakin, shi ba ma wannan ba sai ya ji kamar da ya tambayeta abin da ke damunta ta ce ciki gare ta amma sai wata zuciyar ke tunanin bai ji daidai ba ne Yana nan tsaye ta fito ɗauke da wata farar takarda a ninke ta zo ta ajiye a saman kujera. "Hamma ka yi hakuri ka duba wannan sai mu yi magana." Tana gama faɗin haka ta koma ɗaki sai da ta bubbuɗe window amma duk da haka ƙamshin na nan Allah yasa ga kasarta a gefe tana ta shaƙa shi ne ya saukaka mata. Shi ko takardan ya ƙarisa ya ɗauka tsoro har ya bayyana a saman fuskar shi. Yana buɗewa ya bi rubutun dake ciki daki daki kafin ya gama karantawa ya ji hannunsa na rawa Ummu Salama tana da ciki, ashe abin da ya ji ta faɗa gaskiya ne. Date ɗin ya duba tun tafiyar shi ne ba daɗewa. Ko bai yi lissafi ba ya san ranar da suka samu matsalan nan ne ashe akwai rabo mai nauyi a tsakaninsu idanuwansa suka ƙankance da hanzari ya shiga ɗakin nata har ta saka kaya doguwar rigar Abaya. "Why? Ta juya tana kallon shi. "Me ya sa ba ki faɗa mini ba? "Ba wanda ya faɗa mini kina da ciki Umma Salama." Ya gama faɗa kamar zai yi kuka. Ba ta yi tsammani ba kawai sai ganin shi ta yi a gabanta tana kallon shi da idanuwanta masu ruwan hawaye. "A ina zan faɗa maka? "Ka rufe ni ko na kira ka bana samun ka." Ta gama faɗa hawayen na kece mata da kuka. Sai kawai ya rumgumota a cikin jikinsa ƙamƙam tare da takardan a hannunsa kamar tana jira ta saki kukanta mai sauti wannan kukan da kewar wattani biyun da ba ta samu kafaɗan da za ta yi kuka ba, yau shi take yi duk da ƙamshin turaransa na tsinke mata zuciya ba ta damu ba, tana bukatar kafaɗan da za ta yi kuka a lallasheta. "Hamma.." "Ka yi hakuri." "Shii." Ya faɗa yana ɗan bubbuga bayanta alaman lallashi ita kuma tana ƙara shigewa jikinsa tana rirrikeshi lokaci ɗaya tana kuka. "Na yi kewarka, na yi kukan rashin ka." "Wallahi na yi nadaman kalaman da na faɗa maka tun a ranar." "Na yi nadama." Take faɗa tana gunjin kuka. "Is Ok." "I'm Sorry." "Na barki ke kaɗai. Am sorry bana tare dake a lokacin da kike buƙata ta." "I'm Sorry Ummu Salama. I'm sorry." Shima yake faɗa kamar ya yi kukan haka yake ji, Ummu Salma ta yi ta kuka kukan dake fitowa daga ƙarkashin zuciyanta bai hanata ba ya barta ta yi kukanta har sai kukan ya dawo shessheƙa. Ya ɗago fuskarta yana share mata hawaye da gefen hannun rigansa. "I'm sorry." Ya sake faɗa, ta ƙamƙame hannuwan shi. "Hamma." "Yes" "Ka yafe mini." "Komai ya wuce Umma Salama." "Ka yafe mini? "Na daɗe da yafe miki." Ya faɗa yana kallon cikin idanuwanta. Wasu hawayen suka sake kece mata. "Shi ne ba ka nemi ni ba! Ba kira ni ba? "Am sorry." "Im here ba zan sake tafiya na bar ki ba." "Ka tabbata? "Na tabbata." Sai ta fara mirmishi tana hawaye, yana share mata. "I miss you. I miss everthing about you expecially wannan craying face ɗin na ki." Ya gama faɗa yana jan hancinta amai ta ji ya taso mata sai ta bar jikinsa ta rarumi gwangwaninta tana shakan ƙamshin ƙasan ta. "Warin turare na ne ba ki so? Ya tambaya cikin kulawa. Sai ta ɗaga masa kai "To bari na yi wanka ko na sauya kayan ne? "Ko ka yi wanka zan ji ƙamshin." "Bana son kamshin komai yana sani amai ƙamshin wannan ƙasar kaɗai nake so." Ya zura mata idanuwa a zuciyarsa yana faɗin dankari . "Sai dai ka zo ka yi wanka da sabuluna mara ƙamshi, ba za ka shafa mai ba sannan ba za ka fesa turare ba" "Ba matsala? Ya tambayeta domin shi gani yake ka yi ta shaƙan kamshin kasa ai akwai damuwa "Hamma." "Baby ke so fa ka gane." Ta gama faɗa cikin shagwaɓa. "Oh na gane." Bai gane ba kawai dai ya ce ya gane ne amma ya saboda ciki kawai sai mutum ya ce ba ya son kamshin komai sai na kasa. Shi ɗakinsa ya ce zai je ya yi wanka ta ce yana da mayuka da sabulan wanka ma su ƙamshi ba ta so haka nan ya shiga wanka a ɗakinta Received at 17:28Reactions: ❤ 12, 😁 2 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sabulu ne bai taɓa ganin irin shi ba ko kumfa ba ya yi, ba ƙamshin ko kaɗan daga karshe ma ruwa kawai ya watsa ya fito tuni ta kwashe kayan da ya cire ta tura cikin wadrope wai suna ƙamshi, ta fito masa da riga da wando, babu kamshi a jikinsu domin tunda ta dawo gidan ba ta yi amfani da turare ba yana ji yana gani aka hana shi shafa mai wai zai yi ƙamshi ba ta so dole ya hakura. Ga wani jidali duk in da za ta je tana tafe da gwangwanin kasanta abinci ta ce mai Harira za ta dafa masa? "Ke nake so ki yi mini girki." Ya faɗa mata lokacin yana gaban madubi yana tashe sumar kansa. Sai da ya duba ya ga ba komai duk ta kwashe duk wani mai ƙamshi ta ɓoye wannan cikin na gaske ne. "Bana iya girki Hamma bana son ƙamshi girki" Ta cikin madubin ya hangeta ta zauna a tsakiyar gado ta tankwashe kafa kawai tana ta shakan ƙasan hannunta "Cikin nan ya saka ki rama." "Na sha wahala ne Hamma." Ta amsa mishi kafin ta fara ba shi labarin irin wahalan da ta sha tana ma kan sha. "Tun cikin na 2week ya fara bani wahala." Ya gama abin da yake yi ya taho zuwa gare ta. Shima ya hayo gadon ya zauna sannan ya janyota jikinsa tana ta shinshina shi. "Wari nake yi ko? Ta kalle shi ba ta yi magana ba. "Wai da sabulunan kike wanka? Ta gyaɗa masa kai. "Tab dole ki yi baki, sabulu ne? Kamar ƙasa ko kumfa ba ya yi." Ta fara dariya tana faɗa masa Umma Balki ta aiko mata da shi ta ce a can shiyar sokoto ake samun shi ba shi da ƙamshi ko kaɗan. "Ummu Salama." Ta kalle shi, shima ita yake kallo. "I'm Sorry." "Na barki, kina ta wahala ke kaɗai" "Ba ni kaɗai ba ne, kowa na tare da ni kai kaɗai ne na yi missing" Ya jawo jikinsa ya rumgume. Yana faɗin ya yi mamakin da ba wanda ya faɗa masa halin da take ciki. "Abdullahi kodayaushe sai ya ce mini kina lafiya. Ammah ma ba ta taba faɗa mini wani abu ba. Gwara ma Mami tafiyata ba daɗewa mun yi waya ta ce ga shi nan Allah ya bamu wani rabon." "Lokacin ban gane me take nufi ba sai yanzu." Ya gama faɗa yana kallonta. "Ammah ba za ta faɗa maka ba kunya take ji saboda ni. Hamma Abdullahi kuma ba zai yi tunanin ba ka sani ba. Kowa ma har Mamin za su yi tunanin ka sani na faɗa maka tunda ban taba faɗa ma kowa abin da ke faruwa a tsakanin mu ba." "Good, personal life ɗin mu ne ba sai kowa ya ji ba." Ya amsa mata. "Ba ni labarin abubuwan da suka faru lokacin da bana nan" Ta ce ba zai ci abinci ba? ya ce sai anjuma. Nan ta lafe a jikinsa ta shiga ba shi labarin wahalan da ta sha tana yi tana shaƙan kasanta daga karshe ma shi yake miƙo mata gwangwanin yana hannun shi. Ya ji tausayinta sosai yana ta bata hakuri ita in ta ce ya yi hakuri sai ya ce "Kar ki kara tuna wannan maganar. Na manta da ita har gaban abada." Amma shi haƙuri yake bata na yadda ya yi dogon fushi da ita a lokacin da ya kamata ya kasance a kusa da ita, ta ce komai ya wuce tana jin kamar ma komai bai taɓa faruwa na faɗa a tsakaninsu ba wannan tazaran da Lamiɗo ke tunanin akwai tuni ya amince da cewa babu ita a tsakanin shi da Umma Salma har abada. Suna cikin ɗakin nan manne da juna kiran sallar mangariba ne kawai ya tashe su. Shi daman a Airport ya tsaya ya yi sallar la'asar ba wanda ya san ya dawo mashin ya hawo zuwa gida. Da ya fita salla mangariba sai da aka yi isha:i ya dawo lokacin har Umma Salma ta sake wanka ta sauya kaya wani riga da wando masu taushi. Abinci kuma Harira ta saka ta dafa masa ruwan tea da ya ji kayan kamshi daman ta yi farar shinkafa da miya da nama sai ta ce ta zufa masa har da salat. Lokacin da ya dawo ɗakin shi ya shiga ya yi waya da Bilkisu yana ta mamakin ta wannan karon har da murnanta da ya ce mata zai taho Adamawa ya zauna ya yi tunanin dalilin murnan nata ne bai samu lokaci ba. Abinci shi kaɗai ya ci a dinning tunda Ummu Salma ba ta son ƙamshi ita kuma sauran tuwonta aka ɗumama mata. Shi ko iya kallon tuwon ya kasa yi da bakar miyar nan zai je ya yi magana da Ammah me ya sa za ta dinga cin wannan abincin? Sannan shi ba ya son tana shaƙan ƙasan nan kar wani cuta ya kamaata ga dariya ga tausayi lokacin da take faɗa masa wai kasar kofar gidan Baffa ne kaɗai take ƙamshi, na anguwan nan Harira ta Received at 17:28Reactions: ❤ 16, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby ɗibo mata babu ƙamshi. A daran Saddam ya zo ya kawo mata goro da ƙasar sai ya ga Lamiɗo. Kasar ma kamar ta roƙa a wata leda ce ƙarama ta ce ya mayar kawai ita da take da shi da yawa. Har tana sa Harira na ɗauko masa ya gani yana dariya Hamma Lamiɗo na dariya kasa ne rabin buhun baggo ina lafiya. Anan ya ci abinci kafin ya tafi Hamma Lamiɗo ya ce sai gobe da safe za shigo ya gaishe da su Ammah ya amsa da to zai faɗa musu. Da wuri suka yi shirin kwanciya saboda wannan sabulun ko wanka bai sake marmarin yi ba. Kayan barci ma sai da aka zabo waɗanda ba sa ƙamshi bayan an gama shinshinawa aka ba shi ya saka. Halin da take ciki ya sa bai nuna yana son kaɗaicewa dai ita ba, duk da yana muradin haka. Sai ita ce suna kwance maƙale da juna hiran na ta ya ƙare shuru na wani lokaci hannunsa dai na kan cikinta yana shafawa. "In sha Allahu wannan karon za mu samu mai sunan Baffa.' "In mace ce fa? "Ki zaɓa mata suna. Gaba in mun samu namijin mai sunan Baffa ne." "Allah ya jiƙan Baffa." Ya faɗa cikin wani irin amo. "Amin Ya Allah." Shuru ya sake wanzuwa da ta fahimci ba zai taƙaleta ba. Sai ta ƙara shigewa jikinsa tanakiran sunan shi. "Hamma." 'uhm" "Ka taƙale ni" "Ba matsala ? "Ko Baby shima ba ya so.." Ba ta bari ya ƙarisa ba ta fara sumbatar bakin shi, shima sai ya mara mata baya Ya ɗauka shima baby baya son wannan taƙalen ne sai ga shi ya fahimci yana so sosai ma, domin ta nuna masa hakan kuma ya gani dukkansu sun yi kewar junansu domin gangar jikinsu ta tona musu asiri. Sai da suka yi wanka suka samu tsarki sannan suka koma suka kwanta. "Hamma." "Uhm" "Ba ka jin ƙamshi a jikina ko? "I don't care " "Wari nake yi ? "Ki bari. Bana so." A kausashe ya faɗa shi yasa ta san da gaske baya so. Hannun shi na saman cikinta suka yi barci amma ta yi ta tashi cikin dare tana shaƙan kasanta da asuba ma sai da ta yi amai abincin da ta ci amma tunda ta ɗan gutsiri goron da Ammah ta aiko mata da shi ta ɗan samu saukin tashin zuciyar. Da safe kasa cin komai ta yi, ta ce Harira ta yi zamanta ba sai ta yi mata tuwon ba za ta je gida kila su Ammah sun tara mata kanzo daman suke shanya mata ya bushe Ammah daga zaune ta daka mata a ƙaramin turmin ƙarfe. Shi ne kawai ya sha tea, karfe goma da rabi suka bar gida key ɗin duka motocinsa yana hannun Umma Salma ne, Hamma Abdullahi ya kawo mata. A toyota ɗin suka fita suka bar Harira a gidan. Daman tun jiya Saddam ya sanar da su Ammah zuwan Lamiɗo zuwansa bai yi musu ba zata ba. Gidan ba kowa Saddam da Abdulrahim duk suna wajen aiki. Sai Ammah kaɗai da Umma A'i sai Ummin ikki sun shigo ba daɗewa sai ga ta tazo gidan Kanzo nan ko Umma A'i ta daka ma Ummu Salma ta saka mata gishiri da farin magi ta ɗan yayyafa mata ruwa ya yi taushi shi ta ci abu kamar magani amma ita ya yi mata daɗi. Lamiɗo na zaune mamaki kawai yake yi Bilkisu ta haihu sau biyu amma bai ga wannan matsalan tare da ita ba. Cikin farko ma bai kai wannan cikin wahalar da Umma Salama ba. Sai da ya yi ma Umma A'i mgana wai kar ta zo ta samu wani cuta ba ta cin abinci mai gina jiki ga shinshinar ƙasa. "Ko wani ciki da na shi salon Lamiɗo. Auta da tunda ta samu cikin nan take wahala kuma in ka ga irin haka wataƙila har ta haife shi tana laulayi nan." Ya zaro ido irin abin ya ba shi mamaki Ammah na gefe tana dariya ba ta yi magana ba. "Ba komai duk abin da ka ga tana ci shi ne zaman lafiyanta tunda shi take so. Ba kuma abin da zai sameta da yardan Allah." Ummin ikki ta amsa mishi. Su Ammah suka amsa da in sha Allahu. "Haihuwar ce nake fatan Allah ya ba ta da sauƙi. Allah ya sa wannan karon ta haihu da kanta ba sai an farka ta ba." Umma A'i ta faɗa Ummin ikki na amsawa da Allah ya sa. "Ai ba anan ƙasar za ta haihu ba. In sha Allahu a Egpyt za ta haihu kusa da kwarrarun likotoci." tana cin kanzon ta sai da ta kalle shi ya gyaɗa mata kai daman a wancan cikin a can ya tsara za ta haihu shi da Mami sai Allah ya yi ikon sa kafin ma cikin ya isa haihuwa. Umma A'i ta ce hakan ma ya yi, tunda dai tana da matsaloli a wajen haihuwar gwara aje kusa da ƙwarrarun. Received at 17:28Reactions: ❤ 12, 👏 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sun bar wannan hiran sun koma hiran Mai martaba Ammah na tambayan yanayin jikinsa. "Da sauki Ammah har yanzu dai yana kan shan magani." A tare suka yi fatan Allah ya ƙara lafiya. Ya ce yana so zai je ko bai kwana ba ya dawo a ranar nan da kwana biyu shi da Umma Salama za su koma Lagos. Ummu Salma ta yi zaraf ta ce za ta je Daura. Ya ce ba za ta je ba saboda yanayinta ta bari da salla, sannan akwai wata tafiyar a gaban su tunda kuma ya ce ba za ta je ba da gaske yake yi. A gidan suka yini har dare barin ma da su Saddam suka dawo ga su Hamma Abdullahi kusan duk dare suna gidan saboda ɗebe ma Ammah kewa sai wajen goma na dare suka koma gida Harira ta sha zama ita kaɗai. Washegari a gida suka yini ba su fita ko'ina ba Baɗɗo ce ta zo ta kawo mata garin goriba da aya daman ita ta ce ta siyo mata lokacin Lamiɗo na barci ba ta wani daɗe ba ta tafi ba zama yanzu tunda ta zama yar kasuwa. Ranar Laraba jirgin safe Lamiɗo ya bi zuwa Katsina ya kwana ɗaya ya dawo alhamis da safe. Ya ce kuma a gobe za su wuce Ummu Salma ta ɗauki ƙalilan abin da za ta buƙata. Sai gashi tana faɗa masa za ta yi guzirin kasa a jirgi kallonta kawai yake yi ya ma kasa magana. Tunda ya dawo daga Daura ta ganshi sai a hankali ya shge ɗaki ya fi awa huɗu ta ɗauka ma barci yake yi sai da shiga ta same shi idanuwansa biyu. Gefensa ta zauna tana kiran sunan shi ya ɗan muskuta yana kwance ne daga shi sai bakin dogon wando jikinsa ba riga. "Meke damun ka? Tunda ka dawo ba ka da walwala! Ko wani abun ne ya faru? Ki jikin Mai martaban ne? Duk a jere ta yi masa tambayoyin tambayar ta ƙarshe na da alaƙa da damuwarsa amma ba zai iya faɗa mata ba. Kawai sai ya jawo ta jikinsa ya ce ta zo su kwanta. Lokacin wajen biyu ne na rana. Ba ta yi musu ba ta lafe a jikinsa yana so hankalin shi ya ɗauke daga tunanin tattaunawar da suka yi da Mai martaba a daran jiya ne. Shi yasa ya ce ta yi masa hira ko wani iri ne, sai ta fara ba shi labarin littafin da ta fara saurara daga tashar tsakar gida na Ɗingishin kwaɗo. "Yanzu kuma an daina kallo an koma jin littafin? "Kallon ne duk baya mini daɗi yanzu." Mirmishi kawai ya yi, ya tuna a baya yadda har wani shauƙi Umma Salma ke jin in tana kallo ita ta koya masa anma sai yana tare da ita in ba sa tare baya ma tunawa da wani kallo ba shi ke gaban shi ba. Labarin take ba shi, amma ba ita yake saurarawa ba. Ya tafi tunani ne, tunanin maganganun Mai martaba kamar na wasiyayya kamar na jaddadawa kamar na umarni. Sun daɗe ba su yi wannan maganar ba sai jiya ya ɗago masa. "Muhammadu ina maganarnmu ta kwana? Da gaske nake yi ina so ka gaji wannan karagar, a yan'uwana babu namiji duka mata ne kuma mace ba ta mulki, ɗan mace ba zai yi mulki ba in dai akwai ɗan namiji. A cikin ya'yana kai ne Babba kuma kai ne nake ganin yafi dacewa da ya gaje ni. Bana so sarautar gidan Shitu ta suɓuce mana, ka je ka sake yin tunani wannan shine magana ta ƙarshe. Zan yanke hukunci kuma duk abin da na yanke za ka bi umarnina ne." Kalaman Mai martaba suna nufin ya ajiye mafarkinsa da burinsa ya zo ya yi sarauta. Ba zai iya ba, kuma ba zai iya faɗa ma Mai martaba ba zai iya ba ɗin amma ya shiga damuwa bai san dalili ba yana ji kamar Mai martaba zai iya aiwatar da abin da ya faɗa. Maganar ya ce daga shi ne sai Ubangijinsu ko Fulani ba ta san sun tattauna wannan maganar ba ya je ya yi tunanin in ya sake kiran shi Umarni kawai zai bi. Addu'a yake yi Allah ya ƙara ma mai Martaba lafiya ya yi tsawon ran da zai yi ta mulkin jama'ar garin Daura. Washegari Jumma'a da za su tafi, Ummu Salma sun je asibiti tare da Lamiɗo ta yi ma likitan bayanin za ta koma Lagos can za ta cigaba da ganin likita ya yi mata rubutu a wata takarda ya ce duk asibitin da ta za ta koma tana ba su wannan takardan za su san matsalolinta su dora daga in da suka tsaya. Ba su ɗauki kaya da yawa ba akwati ɗaya ne sai ƙaramar jaka na Harira Ƙaasarta kuwa dakyar Lamiɗo ya lallaɓata bata ɗauka ba ya ce wa zai barta ta shiga jirgi da ƙasa ta bari zai sa ko Hamma Abdullahi ya sako ƙasar a mota a kawo mata har Lagos sannan ta haƙura. Received at 17:29Reactions: ❤ 17, 🔥 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Shima dai ya faɗa mata ne amma wayau kawai ya yi mata. Sun koma gidan sun yi musu sallama kanzonta an dake mata shi sai ta ɗauka ta saka cikin kaya Shi ya tuƙa su zuwa filin jirgi a can ya bar motar Hamma Abdullahi zai je ya ɗauka daga baya. Jirgin karshe 12:30pm suka bi zuwa Lagos. * Sun sauka a Lagos bayan azahar ƙarfe ɗaya da wasu mintina. James ne ya zo ya ɗauke su daga filin jirgi zuwa gida. Sai ga su a sabon gida. Daman ai sun zo gidn tun lokacin da za su duba gabaɗayansu. Da aka saka funitures ne lokacin sun taho Adamawa James da Baban adila suna gaisheta cikin girmamawa suma sun ji daɗin ganin ta. Yara suna gida ba makaranta sun shigowa falon suna kallo ai suna ganinsu yaran suka rumtuma wajen Umma Salma sai da Lamiɗo ya janye Sultan yana faɗin su yi mata a hankali ba ta da lafiya. Hanan ta san uwarta sai murnan ganinta take yi tana kiran sunanta Mahma. Hayaniyar yaran ya fito da su Sabuwa gabaɗayan su. Suka duƙa suna yi ma Umma Salama sannu da zuwa ita da Lamiɗo. Bilkisu bata nan tana wajen aikinta. "Welcome back second Madam." In ji Debora, haka Anitha ma ta yi ma sannu da zuwa Harira suka rumgume ita da Hidaya daman ta su ta fi zuwa ɗaya. Lamiɗo bangarenshi ya wuce ya ce Sabuwa ta raka Umma Salma bangarenta. Sai kallo gidan take yi, wato funitures ɗin da aka saka masu kyau yan waje duk haɗuwar wancan gidan da ta fara ruɗewa ranar da ta gan shi sai da wannan ya fi mata haɗuwa. Key ɗin bangarenta na jikin kofar korodin ɗin da zai kai ta cikin bangarenta buɗewa kawai suka yi suka shiga. Falon ta ya yi kyau kalan blue ne kujerun da fentin ma irin na zamani ne irin waɗanda take gani a fina finan turawa. Falon ba shi da wani girma amma ya tsaru ga faskekiyar plasma ta shiga duba bedroom ɗin su masha Allahu babu abin da babu, kitchen ɗin ya fi birgeta. Har da store ga kayan abinci sai ka ga dama za ka fita can main falo. Ta zaɓi ɗakinta ta ce Harira ma ta zaɓi ɗaya ta shiga. Na kusa da ita ta shiga ta ajiye kayanta. Salla suka yi sannan aka gabatar musu da abinci Ummu Salma ta ce ba ta ci, kanzonta da ta yi guziri ta ce da yamma za ta jiƙa ta ci. Barci Umma Salma ta kwanta sai la'asar ta tashi shima ɗin Hamma Lamiɗo ne ya shigo har ɗakin sai ji ta yi ana yi mata tafiyar tsutsa a kafarta tana buɗe idanuwa ta gan shi da shirin shi na tafiya masallaci ya ce ta tashi ta yi salla. Bayan ya fita ta miƙe ta faɗa tiolet Allah ya sa bangarenta ba a taɓa amfani da shi ba. Ba ƙamshin komai sai na sabin kaya. Bayan ta idar da salla ta dauko kanzonta ta fito, ta jira Harira a falo ta ba ta, ta ce ta jiƙa mata da maggi kawai da gishiri. Shi ta samu ta saka ma cikinta tana cikin cin ne ma sai ga su Sultan sun shigo Beena da Hanan suka saka rigiman sai sun ci sun ɗauka wani kayan gabas ne tana ba su, cin farko suka fara shirin dawo mata da shi. "Ai sai kun ci shi." Take faɗa tana musu dariya. Hanan ta zubar da na bakinta. Beena ta bi bayanta suna yamutsa fuska. "Karyan tsiya kuke yi, kun san ba za ku ci ba kuka ce za ku ci? Kamar za su yi kuka suka yi tsuru-tsuru sai ta koma tana yi musu dariya Sultan na taya ta. Sai suma suka fara dariyan Harira ce ta gyara in da suka zuzzubar. Yaran suka ɗebe mata kewa. Da yake duk an haɗa musu tasoshin ta kunna musu Tv a tashar Mbc3 ana cartoon. Suna ta bidirinsu a falo, ita kuma sai ta shiga ciki ta dauki wayarta ta kira Mami suka gaisa take faɗa mata Hamman ya taho har yau sun dawo Lagos. Bayan ita ta kira Baɗɗo sun yi magana da yake ba ta faɗa mata za ta zo Lagos ba. Tana ɗakin ma suka biyo ta ciki dole ta tarkata su zuwa falo nan suka sha zamansu itama tana biye musu. Har mangariba sannan ta ce a tashi a yi salla. Sai ga Hamma Lamiɗo ma ya shigo ya ce Sultan ya zo su tafi massllaci. Su Hanan kuma tare suka yi na su salla a falo. Bayan sun idar ta ce su karanta azkar suka fara rerawa tana ɗan yi musu gyara kaɗan. Har bayan isha'i suna bangaren Ummu Salma Bilkisu ta dawo tun bayan la'asar Sabuwa ta faɗa mata Yarima ya dawo amma ba ta faɗa mata dawowar Ummu Salma ba ganin ba huruminta ba ne. Received at 17:29Reactions: ❤ 10, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Wanka kawai ta yi a bangarenta ta je bangaren Lamiɗo shima kuma bai faɗa mata ba, ita kuma ta sakankance da cewa ya saki Ummu Salma tafiyar da ya yi wannan karon shi yasa ba ta damu ba. Yara kuma da ta ga ba ta ji motsin su ba, ta dauka suna bangarensu ne ba ta neme su ba. Sai da za su yi dinner ta ga Sultan a falo babu Hanan ba Beena ba ta yi magana ba ta ɗauka suna ciki ne. Lamiɗo ya yi wanka sannan ya fito sanye da dogon wando da riga mai gajeren hannu. Ya zauna a saman dinning Debora ta jera abincin cikin birgewa. "Sultan ina Beena? Bilkisu ta tambaya tana serving ɗin Lamiɗo. "Suna wajen Anty Umma." Kaɗan ya rage cokalin hannunta bai faɗi kasa ba tsabar yadda ta razana. Ta zaro ma Sultan idanuwana amma ta kasa magana. "Go and call them" Lamiɗo ya faɗa yana kallon Sultan yaron ya mike har zai tafi sai ya dawo. "Papa Anty Umma? har da ita? "No." Ya tuna ba ta son ƙamshin komai. "Ba ta son ƙamshi." Ya samu kanshi da ba ma Sultan amsa. Sultan yaro ne bai fahimta ba sai ya yi wucewarsa kawai. Bilkisu ta kasa iya motsa hannunta tsabar firgici. Wata Anty Umma? ba dai Ummu Salma ba. Kafafunta suka fara rawa, da hannunta ta kasa cigaba da abinda take yi. Ba ya saketa ba? Me ya dawo da ita? "Akwai matsala ne? Ya faɗa yana kallonta ganin ta tsaye ta kasa cigaba da abin da take yi. Lokacin ne ta farga ta yi saurin zuba masa ta tura masa filet ɗin faten dankalin turawan gabansa. Ta koma ta zauna tana jin zufa duk da sanyin A.C dake wajen. "Is she back? Ta faɗa tana kallon shi, idanuwanta har sun tara ƙwalla zuciyarta na wani irin rawa. Ya kalleta amma bai yi magana ba. Sai da ya fara cin abinci har ta cire rai da zai yi magana. "She is." Kaɗan ya rage zuciyarta ba ta buga a lokacin ba. Ta yi masa zuru da idanuwana kawai tana kallon shi. "Bilkisu." Ya kira sunanta. "Ummu Salama." Sai ta ga ya yi mirmishi har gefe da gefen bakin shi ya motsa. "She is pregnant." Kirjinta ya buga dam!. "Ciki? "Ba ka sake ta ba? Maganar ta fito ne daga zuciyarta ba tare da ta sani ba. Sai da ya tsaya da cin abinci yana kallonta. Sai ta yi saurin cewa. "A'a na ɗauka kun rabu ne." "Na ga ita ta ce ka sake ta." Ta faɗa ne domin ta kare kanta. Ba ta san ta sake kwaɓa komai ba ne Lamiɗo ya kalli Bilkisu kafin ya kauda kai ya cigaba da cin abincinsa tana so ta yi magana ta kasa bakinta ya yi nauyi ga zuciyarta na rawa, tana tunanin Ummu Salma ta bar mata mijinta ashe zaune ba ta kare ba ciki ma gare ta. Dowawar su Sultan ya dakatar da ita daga kan maganar da ta yi niyar yi, kanta ta dafe ta bata komai kishi ya sa ta furta abinda ke cikin zuciyarta. Sultan ne ke ba da labarin yadda su Beena suka ce za su ci abincin Anty Umma da yadda suka zubar da na bakin su. Lamiɗo har yana murmusawa wa zai iya cin wannan abincin na Umma Salma ai sai ita. Bilkisu na zaune kamar ba ta wajen ta kasa cin abinci tana ta wasa da cokalin hannunta Lamiɗo kuma kallo ɗaya bai sake yi ma Bilkisu ba. Abinci ma bai ci da yawa ba ya tashi. Ya bar Bilkisu anan ya wuce bangaren Ummu Salma. Har ta yi shirin kwanciya Harira kuma tana bangaren su Sabuwa. Gefen gado ya zauna ya janyota kan cinyarsa ta zauna yana shafa cikinta. "Kin ci abincin ki? "Uhm" Ta faɗa tana toshe hanci domin ya yi wanka da sabulu mai kamshi kayan jikinsa ma suna ta ƙamshi. Fuska ya kwaɓe kamar zai yi kuka. "Wari nake yi? "Ni yanzu ba a son ƙamshi na." Yadda ya yi da fuska ne yasa ta fara masa dariya shi kuma yana ɗan mirmishi. Sakinta ya yi tunda ta ce kar ya saka ta amai. "Hamma to yaushe za a aiko mini da saƙon? Ya kalleta domin shi ya ma manta da wayaun da ya yi mata. "Kasar da ka ce kar na ɗauko." "Oh na tuna." Ya faɗa yana dafe kansa. "Kasar nan fa babu sai dai a samo miki anan" Ummu Salma ta fara kallon shi kamar za ta yi kuka. "James zai samo miki mai ƙamshi." Ya faɗa yana jan karan hancinta. Sannan ya sumbaci goshinta. Cewa ya yi ta kwanta ba gaddama ta koma ta kwanta ya rufa mata bargo. Ya rike tafin hannunta yana mata wani irin kallo. "Good night Sweetheart." "Good night Darling." Ya yi dariya mai sauti. "Ni Hamma Darling" Received at 17:29Reactions: ❤ 19, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ya gama faɗa yana dariya. "Ni ƙanwa ni Sweetheart." A tare suka yi dariya sannan ya saki hannunta. Ya yi mata bye itama ta yi masa hasken wutar ya kashe mata ya kunna mata A.C tunda yanzu tana son sanyi sosai. Yana fita falo ya haɗu da Harira ta shigo ta duka ta gaishe ya amsa. Ya kalleta sau ɗaya ya kauda kansa. "Me sunan ki ma? In da amana ya kamata ya haddace sunan nan saboda yadda Ummu Salma ke jadadda masa "Sunana Harira. Harira ranka ya daɗe." Ta faɗa kanta na ƙasa cikin ladabi "Umma Salama." "Ki kula da ita" "In sha Allahu ranka ya daɗe." Ya wuce ya fita sannan Harira ta ƙarisa ɗakin Umma Salma ta leka ta ga har ta kwanta sai kawai ta rufe mata ƙofa ta shiga na ta ɗakin. * Bilkisu ta kasa zuwa bangaren Lamiɗo ko bai yi mata magana ba. Kallon da zai yi mata kaɗai zai kassara sauran ɗan kuzarinta. Ta firgice da dawowar Ummu Salma, ba ta taɓa tunanin za ta dawo ba. Ta ɗauka ta bar mata mijinta kenan har abada. Abincin ma ta kasa ci Lamiɗo na ta shi itama ta tashi ta shige bangarenta. Yaran ma Sabuwa ta kira ta ce in sun gama a kai su ɗakinsu a yi musu shirin kwanciya. Tana cikin wannan fargaban ne sai ga kiran Lamiɗo ya ce ta zo, jikinta ya kama rawa ta riga ta yi ɓaramɓarama, ta furta abin da ke cikin zuciyarta. Jikinta a sanyaye ta tafi bangaren shi. Ta same shi tsaye hannayensa harɗe a bayan shi. Tana shigowa ya juyo yana kallon ta. "Ranka ya daɗe." Ta faɗa tana kakaro mirmishi. Lokaci ɗaya tana gyara zaman rigar barcin dake jikinta. Hannayenta ta ɗora a saman kafaɗan shi sannan ta sumbaci bakin shi. Bai mayar mata da martani ba sai sunanta da ya kira. Tana jin yanayin kiran sunan jikinta ya sake saki. Kamar zai yi mata magana sai kuma ya fasa Maganganunta ya sa ya fahimci bincike ta yi masa a waya ta karanta saƙonnin Ummu Salama, ya goge ma dukasaƙo sannan ya yi abin da bai saba ba ya saka ma wayarsa password. Bilkisu tana da wani hali da ya fahimta, son shiga rayuwar shi da Umma Salama ahalin ita Umma Salama ba ruwanta da wannan. Yana so ya ce ta bari ba ya so sai kuma kawai ya ƙyaleta. Tambayarta ba ta bukatar amsa tunda ga Umma Salma har da ciki Cikinta ya ɗuri ruwa ta ɗauka zai yi mata fada ne sai ta ji shuru. Cikin farinciki ma suka kwana. Washegari asabar yana gida bai fita ba yara kuma sun tafi makaranta. Ummu Salma ta fara rigiman ita fa a samo mata ƙasa James ya yi magana ya ce ya shiga cikin gari ya diɓo kasa kala kala ya kawo masa. An kawo mata duk wanda ta shinshina sai ta ce ba ta ƙamshi James wajen sau uku yana fita. Shi kan shi mamaki ya kama shi mai oga zai yi da ƙasa? Bilkisu na bangarenta ba ta san ma abin da ke faruwa ba tunda yau tana gida ba ta je aiki ba. Ba ta son ma fitowa ballatana su haɗu da Umma Salma itama Umman Salman ko fitowa ba ta yi daga bangarenta ba tun jiya. Ƙasa dai karshen ta na wajen flowers na cikin gida aka samo mata tace tana so yana ƙamshi. Saboda da safe lokacin da James ke ba ma wajen ruwa ta ji ƙamshin ƙasar. Harira ta samo mata wata roba mai murfi ta jiƙa mata sannan ta kara jiƙa mata da ruwa. Sai goro da ta ce tana so ya hana ta tashin zuciya shima James aka tura kasuwa ya siyo mata. Abinci kuma Harira ta yi mata irin tuwonta da miya daga kuka sai gishiri da farin maggi ba wanda ya sani tunda a kitchen ɗin bangaren Ummu Salma ta yi girki. Sai litini da safe Ummu Salma da Bilkisu suka haɗu a main falo. Lokacin da za su yi ma Lamiɗo rakiya zai koma wajen aikinsa. Ummu Salma ta gaishe ta ta amsa tana kallonta. Ko ba a faɗa ba ga cikin nan a tare da Ummu Salma. Tun kuma da Lamiɗo ya tafi sai su yi kwanaki ba su ga juna ba kowa na bangaren shi yara kuma yawanci a bangaren Ummu Salma suke duduma. Suna waya da Mutanen jimeta, sannan suna waya da Lamiɗo maganar asibiti da ya ce ko za ta je in da Bilkisu ke aiki ne kamar na farko? sai ta ce aa, shi kuma bai matsa mata ba ta ce za ta samu wani asibitin ta je. Received at 17:29Reactions: ❤ 16, 👏 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sai da ta yi sati ɗaya da dawowa sannan ta fita. Motarta an kai wanki an saka ƙamshin nan da masu car wash ke sakawa sai da ta bari ƙamshin ya fita sannan ta fara fita da ita. Ta nemi wani asibitin kuɗi anan anguwan Apapa ta je ta ga likita ta nuna masa takardan da aka bata a asibitin Jimeta. Nan da nan suka buɗe mata fayel aka ɗora ta kan kulawa. Magani dai daga na karin jini sai na cin abinci kawai suka bata cikinta ya kusa shiga wata uku in ya yi wata uku za ta fara awo saboda conditioon din da take ciki, sun ce ta dinga cin abinci sosai ta ce ci amma tana amai sosai likitan ya ce ta ci ko da za ta yi aman ne. Sannan ta dinga cin kayan marmari to gwara su tana son su musamman ayaba su Debora ta aika kasuwa suka siyo mata ayaba da yawa da su kankana ta saka a firizanta tana diɓa kaɗan kaɗan tana ci. Zuwanta Lagos ya sa ta ɗan fara kiba ba kamar lokacin tana Jimeta ba. Hakan kuma nasaba ne da ta samu kwanciyar hankali. Damuwarta guda ɗaya ne yanzu rashin Baffa wanda ta kasa daina kukan mutuwarsa ga azumi bai fi saura kwana ashirin ba. Tabbacin Ammah ta kusa fita takaba. A group ɗin Ammah da Baffa ta ga Hamma Jibo ya ce za su taho da salla. In an yi salla an gama za a zauna a yi maganar rabon gado. Tabbacin da gaske Baffa ya tafi ya bar su. Ubangiji ya yi masa rahama amma har abada ba za ta manta da rashin Baffa ba. *Janafty* Received at 17:29Reactions: ❤ 16, 👎 1, 😢 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. Tunda Lamiɗo ya tafi sai da ya yi kwana ashirin sannan ya dawo. Dawowarshi ya sa zuciyar Bilkisu ya kusa bugawa saboda kishi da baƙinciki. Tunda ya tafi sai su yi kwanaki ba su haɗu da juna da Ummu Salma ba, Bilkisu na zuwa wajen aiki in kuma ta dawo tana bangarenta. Yayin da Umma Salma ke yini a bangarenta ba abin da ke fito da ita duk abin da take so akwai shi a bangarenta. Yara ma nan suke dudumarsu in sun dawo makaranta in ma suna gida yanzu sun fi zama a bangaren Ummu Salma. Su yi karatu tare, ta koya musu Qur'ani tana kuma koya musu azkar domin yadda za su tsare kansu sannan ta zaunar da su ta yi ta basu tarihin Annabawa. Zamansu da Bilkisu kamar yadda faro ne haka ya cigaba da wanzuwa. Har Lamiɗo ya dawo ko sau ɗaya a cikin kwana ashirin ɗin nan wata ba ta ga wata ba. Sai da ya dawo ne suka haɗu da juna. Abin da ya fara baƙanta ma Bilkisu rai shi ne Lamiɗo da kan shi yake bin Ummu Salma bangarenta ko ita ke da girki ko ba ita ba ce, ba ya jira shi da kansa yake bin ta har bangarenta. In ranar girkinta ne kuma a bangarenta yake kwana. Ta so ta share kar ta yi magana amma ta ga ba za ta iya ba. A matsayin Lamiɗo na Yariman Daura bai da ce yan aiki na gidan nan su gan shi yana kara kaina a bangaren Ummu Salma ba, sannan ga wani ririta da yake yi, ko cikinta na farko albarka na yanzu kam ko ƙoda in da yana da dama ba zai bari ya taɓa ta ba. Kishi ya dinga murkukusanta daman ranar da zai tafi a ɗakinta yake da ya dawo sai ya sauka a wajen Ummu Salma sai da ta bari ya dawo ɗakinta ranar ma ita ce ta same shi a bangaren shi. Sau tari ita ke samunsa a bangaren shi ba ta jiran shi saboda shi shugaba ne, ta amince ita ce za ta bi shi, amma yarinya ƙarama daga zuwanta ta na neman ƙwace mata matsayinta sannan duk ta sauya mata miji a lokaci ɗaya. Sai da ta bari sun kwanta sannan ta yi masa maganar. "Ranka ya daɗe, ina so na yi wani gyara." "I hope babu matsala ko? Tana kwance a kan jikinsa ne, bai yi magana ba ta san kuma ba zai ce komai ɗin ba shurunsa na nufin yana sauraranta. "Gyara zan yi maka. A matsayinka na Yariman Daura ko ba a matsayin miji ba. Kai Shugaba ne a gare mu bai dace a ce kai ne za ka dinga bin Ummu Salma bangarenta ba. Ba mu kaɗai ba ne a gidan nan Hadimai suna nan kuma suna ganin duk shige da ficen ka, koma mene ne ita ya kamata ta dinga biyo ka." Ta ɗan yi shuru tana sauraran shi, amma ya yi shuru kamar ma ba ya wajen Sai ta ɗago tana kallon shi a ɗan hasken dumlight ɗin dake ɗakin ta ga idanuwansa biyu kuma yana sauraranta ya kuma ji duk abin da ta faɗa. "I'm sorry in na yi shisshigi amma na ga kamar bai dace ba ne." "In kana son magana da ita. You can call her sai ta zo bangarenka ta same ka." "Amma ka yi hakuri in ba ka ji ɗadin magana ta ba" Shuru na wasu mintina kamar ba zai yi magana ba. Ta sake ɗagowa tana kallon shi. Gashin ƙirjinsa take shafawa tunda ba riga a jikinsa. "Ni na yi magana ne saboda matsayinka. Sannan bai dace ba ta kiran ka da girmamawa ba. Ya kamata ta dinga sakaya sunan ka a gaban mutane kai shugabanta ne." "Ba ta da lafiya ne." "Ba ta son ƙamshin komai." Ya ba ta amsa sannan ya ɗan matseta a ƙirjinsa. "Ba ta son ƙamshi? Ta faɗa da sigan tambaya, domin daman ta ga ko yana gari ba ya kiran ta cin abinci sai ta fara zargin akwai wani abu. "Cikin ne ba ya so ƙamshi." "Tana yin amai." Wani malolan abu ya tsaya ma Bilkisu a maƙoshi ya kasa wucewa. "Tana buƙatar kulawa. Ke ma in bana nan ki kula da ita." "Zan ji daɗin haka." Sai ta kasa ma magana ita ai ta yi cikin nan har sau biyu ta haihu amma ba ta son wannan tsirfan ba. "Maganar girmamawa kuma." "Hamma take kira na." "Hamma in fullanci means Yaya." Ya gama faɗa har gefe da gefen bakin shi na motsi. "I love the name." "Ranka ya daɗe da kike kira na kin sa kanki ne. Bilkisu ni mijinki ne, ke matata ce ba baiwata ba. Girmamanin da za ki yi na ibadar aure ne amma wannan girmamawan na tushe kuma na dabam yake." Received at 08:42Reactions: ❤ 10, 😁 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "A wajen mutane nake Yarima amma a wajen iyalaina da iyayena I'm still Muhammad Lamiɗo." "So ni wannan bai dame ni ba. Ke ma you can start call me whatever you want. Ba ki da matsala." Sai da ta yi nadamar yi masa maganar yadda ya dinga jera mata maganganu. Ta ɗan daure dai tana yi masa yar shagwaɓa ta ce ai ita ba ya zuwa bangarenta sosai. "Zan zo." "In kina so." "Ina so Papa." "Nima ina so na sake samun ciki." Ta faɗa masa abin da ke zuciyarta. Ta ji tana son itama ta sake samun ciki duk da ita ta tsayar da haihuwanta da kanta "As you wish. Zan yi farinciki da haka." Ta gama tsayar da shawaran za ta je a cire mata abin da aka sanya mata. Itama za ta samu cikin ba za ta zauna tana ji tana gani ana ririta wata macen saboda ciki ba. Duk a tunaninta ya za a yi wata macen da ba ta isa ba ta zo ta fita. Ta gaji da kiran Ya Hadiza tana ba ta hakuri. Kowa gani yake yi kishi ke damunta ba su hango abin da ke faruwa ba. Ta ya ya Lamiɗo zai ba ma wata macen muhimmanci sama da ita, a ganinta babban ci baya ne a gareta. Shi ya sa ta kasa bari zuciyanta ya zauna lafiya Kwana biyar Lamiɗo ya yi ya koma da zai tafi ya ce ma Bilkisu ta kula da Ummu Salma. Ta amsa masa ne kawai amma a zuciyanta ta ce ba za ta yi ba. Yarinyar da ba ta san darajan mutane ba, itama Ummu Salman da ya ce mata Bilkisu za ta dinga kula da ita a gida ba ta yi masa gaddama ba amma a zuciyanta ta ce bata bujata za ta iya kula da kanta. Yana kuma tafiya kowa ya kama harkan gaban shi. Tafiyarsa da kwana shidda aka fara azumin watan ramadana. Ummu Salma ta ce ba za ta sha azumi ba duk da Lamiɗo ya ce ba ta da lafiya ta huta haka ma Mami ta ce mata ita kuma tunda ta gwada ta ga za ta yi ta ce ba za ta yarda ta sha azumi ko ɗaya ba. Ga shi dai azumi ne amma ba sa sahur tare ballatana buɗe baki tare. Ummu Salma buɗe bakinta daman kayan marmari ne gwara yanzu ma tana ɗan cin wani abincin bayan tuwo sannan tana shan tea. Bilkisu kuma ko damuwa da wata Umma Salma ba ta yi, yaran ma tunda ta ga sun koma shashenta ta yi ma Anitha magana tare da yaranta take buɗe baki Hanan kuma da rigima ta saba da su Sultan sai ta je duk da Bilkisu ba ta so. Shi kuma yaro bai son ana so ko ba a so ba. Sai da aka yi azumi ashirin sannan Lamiɗo ya dawo. Ummu Salma ko ɗaya ba ta sha azumi ba. A ɓoye take yi ba ta bari Lamiɗo ya sani ba in suka yi waya sai ta ce ba ta ɗauka ba sai da ya dawo ne ya fahimci tana azumi bai yi mata faɗa ba ya ce tunda ta tabbatar da tana lafiya shike nan. Yanzu an samu sauƙi tana shakan ƙamshin abinci ta zauna lafiya amma har gobe ba ta daina shinshinar ƙasa ba. Suna yin sahur tare a dinning haka ma Buɗe baki tare da yaran gabaɗaya. Tunda Lamiɗo na nan dole in ya kira su, su fito su haɗu gabaɗaya. Kayan salla daman yana dawowa suka fita shopping, suka yi siyayya ɗinki kuma Bilkisu ta kira telan dake yi mata ɗinki a wani plaza ne ya zo gida ya karɓa harda na Ummu Salma tunda Lamiɗo ya na nan kuma ya saka baki. Ma'aikata kuma kuɗi ya ba su kowanne ya je ya siya abin da yake so. Harira ta ba ma Ummu Salma nata ta adana mata Daman kuma ta kira Baɗɗo ta je can wajen Ammah ta karɓi key ɗin gida ta je ta buɗe akwatinta ta ɗauko atamfa guda uku da leshi ta kai mata ɗinki na ta biyu na Harira biyu. Kayan salla su Ammah kuma kamar yadda aka saba Lamiɗo ya tura ma Hamma Abdullahi shi kuma Adda Suwaiba da ta saba siyowa ta siyo aka raba ma kowa. Wannan karon har da mutanen Mubi, Mami da iyalanta gabaɗaya. Ummin ikki da yaranta kamar yadda aka saba kowani shekara. Amma ta fita takaba ranar azumi ashirin da biyu. Kowa ya kirata a waya ranar sai ta zama kamar ranar ne Baffa ya rasu. Ummu Salma daman tun a ranar tunda ta tashi sukuku take, ta sha kuka idanuwanta sun kumbura Lamiɗo ne ya dinga lallashinta. Mutuwar Baffa gibi ne ba ta tunanin za ta manta da wannan rashin. Ba ta taɓa tunanin za ta yi dariya bayan rasuwar Baffa ba, sai ga shi tana yi amma kuma rashin shi ba zai goge daga zuciyarta ba. Received at 08:42Reactions: ❤ 12, 😢 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Wannan karon daga Lagos Daura suka sauka, tunda ba su taho da wuri ba ranar da aka ɗau azumi na ashirin da bakwai. Sun yi salla a Masarautar Daura kamar yadda suka saba lokacin cikin Umma Salma yana cikin wattani na biyar har ya fito. Ta rage laulayi amma har yanzu tana yin amai in ta ci abin da cikinta bai karba ba. Mai martaba ya samu sauƙi sosai tunda yana zuwa ganin likita lokaci bayan lokaci Fulani ne ma ke fama da kafafu. Kowa ya ga Ummu Salma da ciki sai ya ce Allah ya kawo rabo da wuri haka Hajiya Kilishi da Hajiya Zaliha suka yi ta faɗa da addu'an Allah ya sa a sauke lafiya. Mai Martaba ma ana gobe za su tafi Adamawa a daran sun daɗe suna hira da shi da ta je gaishe shi. Ya na bata labarin halin kirki irin na mahaifinta tana jin daɗi, ta tuna lokacin da ta rasa jaririnta ya kira wayarta ya daɗe yana yi mata nasiha da jan hankali akan hakuri da kaddara. A lokacin kuma ta ji daɗin maganganunsa sosai. Yana da hikima da hangen nesa. Adali ne na gaske ta tabbatar da haka ta ga kuma in da Lamiɗo ya ɗauko karamci da yakana. Bayan salla da kwana uku suka baro Daura zuwa Adamawa. Daman da azumi Shamsiya ta ddame ta da kira sai da ta haɗa ta da Hanan har Habib ɗin ma an ba shi ya yi magana da Hanan ɗin. Shamsiyar ta tambaye ta ko za su zo da salla ta ce a Daura za su yi salla. Ko sun zo Adamawa ba za su daɗe ba zaman da za a yi na rabon gadon Baffa ne ma zai tsayar da su Lokacin da suka isa sun iske Baffa Umaru da Baffa Salisu duk sun iso Hamma Jibo ma da Hamma Mustpha suna nan. Hamma Kabiru sai washegari da safe zai taho. Sai aka ce a bari zuwa da safe in kowa ya iso sai a yi zaman. Umma A'i daman na nan Umma Balki ce suka taho tare da su Baffa Umaru. Mami kuma sai a gobe za ta biyo jirgin safe ta taho. Su Umma Salma na zuwa Ammah ta ce ta kira Shamsiya su zo su tafi da Hanan. Anan ne ma Ammah ke faɗa mata da salla Shamsiyar da Habib ɗin sun zo gaishe ta har waina ma Shamsiyar ta kawo mata. Ta ce tana ta kiran wayar Ummu Salman ba ta ɗauka ba. "Auta da ace Ubangiji ba ya mana rahama da ba mu kawo yanzu ba. Ya kamata ki manta baya ki saki daga ƙullatan Shamsiya da kika yi a zuciyarki. Shi kuma Habib kun rabu Ubangiji kuma ya yi miki canji na alheri. Amma kuma akwai alaƙa tunda ga Hanan ya kama ta ki manta da duk abin da ya faru. Duniyar ma nawa take? in mune yau gobe ba mu ba ne! Yau ina Baffa? Yana can ƙasa ta rufe masa idanuwana" Nasihan Ammah suka sanyaya ma Ummu Salma jiki. duk abin da ta faɗa gaskiya ne. Da Ubangiji ba ya mana afuwa da tuni an kife duniyar ta yafe amma alaƙa ce ba ta son ta ɗaure. Maganar Ammah na cewa an rabu amma ba a rabu ba gaskiya ne tunda akwai Hanan a tsakani. Ko tana so ko ba ta so alaƙa ta haɗu ba ta da yadda za ta yi. Ammah ta yi ma Lamiɗo maganar cewa Hanan za ta je dangin babanta ta kwana biyu kafin su tafi. Ya ce ba komai, shima ta yi masa faɗan ba ya faɗa ma Umma Salma gaskiya. Ya dinga yi mata faɗa ta dinga haƙuri da rayuwa ya ce zai dinga yi mata in sha Allahu. Ummu Salma da kira lambar Shamsiya ta ce ta zo su tafi da Hanan ta kwana biyu ba daɗewa za su za su yi ba za su koma Lagos. Shamsiya ta ji kamar a mafarki da Ummu Salma ta kira ta daman ta ce ba za ta gaji ba. Wata rana Ummu Salma za ta sauko ta amince da nadamarta. Habib baya nan yana wajen Habiba ne ta kira shi a waya tana murna ta faɗa masa nan take ya taho ta shirya a daran suka zo suka tafi da Hanan. Habib ɗin bai shigo ba a waje ya tsaya Shamsiyar ta shigo ta shiga har cikin ɗakin Umma Salma suka gaisa. Ta ga Ummu Salma da ciki ta kalleta sai da hawaye suka kawo mata. "Allah ya raba ku lafiya Umma Salma." Ta amsa mata da Amin Saboda Nasihan Ammah ya sa ta ɗan saurari Shamsiyar. "Ke har yanzu shuru dai? Ummu Salma ta tambaya "Shuru ko ma na samu cikin ba zama zai yi ba. Habiba kuma ta ce ba za ta iya haihu da Habib ba." Sai hawaye sharr, Ummu Salma ta kalleta sai kuma ta ba ta tausayi. "Allah zai kawo mafita in sha Allahu." Ta amsa da Amin tana mirmishi. "Amin na gode Ummu Salma. Na gode." Received at 08:42Reactions: ❤ 14, 🔥 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Tana faɗa tana sharan ƙwalla suna cikin haka ne sai ga Baɗɗo ta shigo. Zuwanta kenan ta kawo ma Ummu Salma ɗinkunan ta, tunda sun yi waya ta ce suna gidan Ammah. Bilkisu tana gida tare da su Sabuwa suna sauka ta ce gida za ta je ta huta. Ummu Salma ne kawai sai Lamiɗo da su Sultan a gidan. Shamsiya ta kalli Baɗɗo wacce ta yi kamar ba ta ganta ba. Ta haɗu da Habib a waje ta yi kamar ba ta gan shi ba sai da ya gaisheta ta amsa adaƙune. Nan ma Shamsiya ce ta gaishe ta. Ta amsa sau ɗaya ta haɗe rai ita fa ba ta ga abin da zai saka Ummu Salma ta cigaba da mu'amala da Shamsiya ba. Shamsiyar ma ganin ba fuska sai ta yi musu sallama. Tuni Harira ta haɗa ma Hanan yar jaka na tafiya Shamsiya ta ɗauke ta Hanan dai wannan karon ba ta yi rigima ba Beena ce dai ta yi rigiman ganin za a tafi da Hanan a barta sai da Ammah ta rumgumeta tana ta lallashinta. Bayan fitan Shamsiya Baɗɗo ta dinga faɗa wai me ya sa take kula Shamsiya. "Nadamar dole ce shegu sun ga uwar bari " "Nima ba mu'amala nake son yi da ita ba. Ammah ce ma tayi mini faɗa shi ya sa kika ga na tsaya na saurare ta. Amma ni ko wayata ta kira bana ɗagawa." "Wallahi na tsane su daga ita har Habib maciya Amana kawai." "Na yafe musu kema ki yafe. Ni yanzu Ubangiji ya gama yi mini komai Baɗɗo." Baɗɗo dai ba ta yi magana ba. Alaman dai ko ta yafen to ba ta faɗa ba. Saboda haushi ma ba ta daɗe ba Hamma Saddam zai fita ta ce ya sauketa a gida. Ta kawo mata ɗinkunan da ta ba da, sannan ta haɗo mata da wasu wanduba plazo guda huɗu da Baɗɗo ke siyarwa da ta ce tana so. Nan gida Ummu Salma ta kwana Lamiɗo ne ya koma gida tare da Sultan, Beena ma wajen Ammah ta kwana. Washegari tun goma na safe Hamma Kabiru ya iso, Mami kuma sai sha ɗaya da wani abu ta iso daman su kaɗai ake jira. Har Liman an kira tunda shi ne zai yi rabon gadon. A falon Ammah aka tattaru kaf yaran Baffa mazan da cikon su Ummu Salma. Sai Baffa Umaru da Baffa Salihu wakilan Baffa sai wakilan Ammah kuma Umma A'i da Umma Balki. An buɗe taro da addu'a tare da nema ma Baffa gafara a wajen Allah sannan aka fara gudanar da abin da ya tara su. An fito takardun filayen da Baffa ya bari da na gida. Sannan daman lokacin da ya rasu Hamma Abdullahi ya ce ba a bin shi ba shi sai ma shi ne ke bin wasu, to duk sun dawo da kuɗin tunda shi ne suke kasuwanci da Baffa ya samu tattara kudaɗen da ya mutu ya rabi kudaɗe dai tsaba miliyan takwas ne sai gidan nan da suke ciki sai filaye guda huɗu sai mota sai kuma gadon shi dake can mubi na gida da gona. An raba gadon cikin tsarin kamar yadda Ubangiji ya raba gado a cikin suratul Nisa'i. A shari'a namiji ke da kaso biyu mace kuma na da kaso rabi daga abin da namiji ya samu. Matar da mamaci ya mutu ya bari tana da kashi ɗaya a cikin takwas. Tunda yana da yara maza, yan'uwansa maza ba su shigo gadon Baffa ba. Daga ya'yansa sai matarshi da a ce mahaifiyar Baffa na raye za ta shigo ciki a matsayin ɗaya bisa shidda amma tunda ta riga Baffa rasuwa babu lissafin ta a rabon gado. Gida kuma tare aka raba kowa da kowa har da Ummu Salma kuɗi ma aka yi kasafi aka raba komai kamar yadda addini ya tsara. Ana rabon Ummu Salma na sharan ƙwalla, shike nan Baffa ya rasu da gaske ne ba mafarki ba. Kowa ka gani jikinsa duk a sanyaye. Shike nan fa an yi an gama. Sai dai fatan Ubangiji ya sa mu gama da duniya lafiya. Sai gidan ya dawo kamar yau aka yi mutuwa. Ammah ta yi kuka irin wanda ko a lokacin rasuwar ba ta yi ba. Hamma Lamiɗo ne ke ta lallashinta Mami ma kuka har da sauti Liman ya zauna yana ta nasiha tare da ba ma su Hamma Jibo shawaran su haɗa kansu ko bayan ran Baffa su kasance ƴaƴa nagari a gare shi. Hamma Abdullahi sai share hawaye yake yi shi da su Hamma Saddam. Mutuwar Baffa babban gibi ce da har abada ba za su taɓa mantawa da shi ba. Bayan an gama koke koken kowa ya share hawayensa. Bayan Liman ya tafi su Hamma Jibo sun je sun raka shi sun dawo. Sai aka sake wani zaman saboda tunanin wanda za a samu da zai zauna da Ammah saboda ɗebe kewa. Ammah kuma na faɗin ita su ƙyaleta za ta iya zama ita kaɗai. Umma Balki ta ce ba zai yuyu ba ko yaya ne a samu wacce za ta taya ta zama. Received at 08:42Reactions: ❤ 11, 👎 2 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ita Ammah na faɗin ba matsala ga Ummin ikki a kusa da ita ga matan su Hamma Abdullahi suna zuwa akai akai ba ta da matsala. Umma Balki ta ce Umma A'i ya kamata ta ɗan zauna na wani lokaci saboda ita ce ba ta da kowa a gabanta. Ta amince za ta kara ko da wata ɗaya ne kafin ta koma. Hamma Jibo ya ce shawara kawai cikin Saddam ko Abdulrahim wani ya zo ya yi aure. A gyara gida ya saka matar shi a kusa da Ammah. Kowa kuma ya aminta da shawaransa. "Ni fa ba yanzu zan yi aure ba, ban kama aiki mai girma ba sannan ina karatu." Hamma Saddam ya yi saurin faɗa. "Kuma ni ai ƙarami ne Abdurahim ne ya dace ya yi aure, kuma shi ai ya gama karatu har ya kama aiki." "Kuma yana gaba da ni." Ya faɗa har yana marairaicwa. Umma Balki ta ce ai ya isa auren shima "Umma Balki ban isa aure ba fa." Tana cewa ya isa yana cewa bai isa ba diramansu ta ba ma kowa dariya. "Ai na ce ka turo mini CV ɗinka zan tura ma Maimartaba za ka fara aiki in sha Allahu " Lamiɗo ya faɗa yana kallon Saddam nan da nan ya washe baki ya ce ya sha'afa ne amma zai tura maasa daman ko aikin Abdulrahim daga Masarautar Daura aka samar masa. Abdulrahim da aka tuntuɓe shi ko yana da budurwa karaf Ummu Salma ta ce yana da shi. "A Abuja take anguwar su Hamma Jibo " "Tabbas haka ne, suna ma raba dare suna waya a kwanaki can amma yanzu na ga kamar ba sa waya." Hamma Saddam ya karɓe maganar. Abdulrahim na ta hararan shi. "To kai Abdulrahim ya ake ciki ne? Hamma Mustpha ya tambaye shi yana dariya. "Ko an ka sa ka ne? Hamma Abdulrahaman ya faɗa yana dariya. "Kamar ka sani, ba ni da kuɗi ta bar ni ta auri wani mai kuɗi bayan rasuwar Baffa ta yi aure." "Subhanallah." "Abu bai yi daɗi ba." "Sannu Allah ya mayar kaffara ne" Har da Hamma Kabiru a masu yi masa jaje. Mami na yi masa tsiyan ko bai iya soyayya ba ne ya ce ya iya mana ana ta dariya. Ammah na mirmishi kafin ta ce" Ita ce ta tafka asara ka ji, yanzu dai ka yi haƙuri ka zo ina da matar da zan ba ka kuma na san za ka ji daɗin ta." Kowa ya zura mata ido yana jiran ya ji sunan da za ta kira. Umma Salma ta yi jagale daman tunda ta ji Abdurahim ya ce budurwansa ta yi aure take wani tunani. Sai kuma ga maganar Ammah. "Wace ce? Abdulrahim ya tambaya yana addu'an Allah ya sa ba a ƙauye ba ne. "Aisha ce." "Aisha? Kusan duk falon suka tambaya a tare. "Aisha yar wajen Aminiya." "Baɗɗo tawa? Ummu Salma ta faɗa tana zaro idanuwa har tana dafa kafafun Hamma Lamiɗo domin tana kusa da wajen kafafunsa ne a zaune "Ita, ni da mahaifiyarta aminai ne, ka je ka neme ta in kun daidaita ina maraba in kuma ba ku daidaita ba, ba tilastawa." "Gaskiya tana da hankali Aisha." Saddam ya faɗa yana dariya. Abdulrahim ya ture shi da kafar shi ya koma gefe yana dariya. Hamma Abdullahi ya ce shi ya ɗauka ma soyayya suke yi da Saddam "A'a ni wallahi ba soyayya muke yi ba. Ni fa bana son farar mace." Ya faɗa da iya gaskiyarsa "Ka yi mata yaro da yawa ma." Ummu Salma ta shigar ma ƙawarta tana hararan shi. "Ke ni ne yaron? "Yaro ne mana ai gwara Hamma Abbdulrahim muma kai ba ajin mu ba ne " Ya taso yana jijiyar wuya ana ta dariya. "Ammah kamar kin shiga zuciyata. Ina ta so Baɗɗo ta samu miji cikin yayyena ni da har Hamma Abdulrrahaman na yi ma sha'awarta ma" Da ya ballo mata wata harara sai da ta sunne kanta kafafun mijinta tana dariya. Mami ta ce ai ta samu mijinta Abulrahim ƙin kowa ƙin wanda ya rasa shi dai ya yi shuru ya kasa magana kowa na tofa albarkashin bakin shi. Su Hamma Jibo duk sun ce zaɓin Ammah ya yi har da su Baffa Umaru ma. Umma Balki ta ce da tana da yar auta mace da ta ba ma Saddam yana tura baki ya ce ba ya so "Kai ka sani irin su Saddam ne, in ka ga matansu sai ka juya baya ka ɗauka yan aikin su ne saboda shigen zaɓe zaɓe." Aka saka dariya gabaɗaya shi kuma yana kumfar bakin cewa za a ga matar da zai aura kaf surukan Ammah ba kamarta. "Ba kamarta kam." Hamma Abdullahi ya faɗa yana dariya Saddam ya kasa magana. "Hamma wallahi ka amsa za ka ji daɗin Aisha sosai tana da kunya ga hankali ga natsuwa." "Uhm kina yi ma ƙawarki yaki ne? Received at 08:42Reactions: ❤ 7, 😁 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Hamma Abdullahi ya faɗa Ummu Salma ta fara dariya tana faɗin ba yaƙi ne ba ne sai gaskiya Hamma Lamiɗo ta kalla tana faɗin bai ce komai ba. "Me zan ce? "Ka faɗa ma Hamma Abdulrahim sa'ar da ya yi na samun Aisha a matsayin matarsa." Ya yi shuru bai yi magana ba yana kallonta. Sai ta marairaice fuska kamar za ta yi masa kuka. "Hamma ka yi magana mana." Har tana rumgume kafafunsa ta manta ma a inda suke ta ɗauka suna gidansu ne shi kuma da sauri kamar jani talau ya ce to sannan ya juya yana kallon Abdulrahim da duk aka saki baki ana kallon su. "Abdulrahin ka ji ko? Aisha is a good girl ka yi abin da Ammah ta ce kawai.' "Ko abin da Ummu Salma ta ce ba." In ji Hamma Kabiru yana kallon shi Aka kwashe da dariya a falon har Ammah sai da ta murmusa sai a lokacin da Ummu Salma ta san abinds ta yi da sauri ta saki kafafun Hamma Lamiɗo ta koma tana sunne kai a jikin Mami. "Ɗan Ammah dai ya shiga hannu " Mami ta faɗa tana dariya. "Ai ya zama jani talau kuma laifin Fatima ne." Umma Balki ta faɗa tana dariya. Haka ma Hamma Jibo ya ce nan duk ana magana bai saka baki ba amma Auta na marairaicewa ya bi umarninta yana jin su kawai mirmishi yake yi bai yi magana ba. "Amini ai ya canza sosai ni yanzu ma ina tsoron yin hira da shi kar ya kwashe ya faɗa ma yarinyar nan ta dinga mini kallon biri ni kuma ina yi mata na ayaba." "Wallahi ka kiyaye " In ji Hamma Abdulrrahaman Falon sai dariya ake yi shi kuma gogan bai yi magana ba illa Hamma Kabiru da ya kalla ya ce. "Bana faɗa mata komai fa." "Ban yarda da kai ba." "Wallahi Hamma ba ya faɗa mini hiran ku, hiran mu kawai muke yi ko Hamma? " Ummu Salma tana kallon Hamma Lamiɗo har tana yi masa fari da gaske ne ba ta sanin komai kai in dai wajen zurfin ciki ne da riƙe magana ba ta ga kamar Hamma Lamiɗo ba. "Tell him." Lamiɗo ya faɗa yana kallon Hamma Kabiru. "Kai dai ka kiyaye kawai tsakanin miji da mata.." Su Hamma Abdullahi suka ƙarisa da sai Allah ana ta dariya. "Auta ta nuna mana capacity ɗin ta yau." Hamma Saddam ya faɗa yana kallonta sannan ya dunkule hannu yana yi mata jinjina "Allah ya taimake ki ranki ya daɗe. Ai ke ce ma Yariman gabaɗaya." Gabaɗaya aka kwashe da dariya. Ammah na ta duƙar dakai tana share ƙwalla ta tuna da Baffa na raye da yanzu yana cikin nan ana hira da shi ana raha. Ummu Salma ma haka take tunani a zuciyarta. "Allah ya jiƙan ka Baffa " Sai da ta ji duk sun amsa da Amin sannan ta gane a sarari ta yi maganar. hawaye suka kece mata a saman kumatunta sai kawai ta kife kanta a kafafun mijinta ta fashe da kuka, shi kuma sai ya dora tafin hannun shi a saman kanta yana ta ɗan tapping alamun lallashi. "Ya isa Okay." "Kin san condition ɗin ki so please ki daina kuka nan ya isa." Ta ɗago fuskarta shi kuma ya rankwafo yana share mata hawaye "Ya isa kin ji ko? Ba ga ni ba! Ba za ki taɓa kukan wani abu ba in dai ina raye." "I promise to love you, support you care for you. I promise to give you everthing matuƙar za ki yi farinciki." "Hammaaaa...' Ta faɗa tana gunjin kuka saboda kewan Baffa da kuma kalamamsa da suka tsuma mata zuciya. "Na ce ya isa." Yake faɗa yana goge mata hawaye ganin kamar sun manta da kowa ne ya sa Hamma Kabiru ya yi gyaran murya. "What? Hamma Lamiɗo ya juya yana tambayansa. Sai yakasa magana lalle Lamiɗo ya canza shi ne zai iya kama mace a gaban mutane bai damu ba. "A'a bakomai ci gaba." Sai kuma ya ga ya koma ya ci gaba da lallashin Ummu Salma amma hannunta kawai ya riƙe sai dai kanta na saman kafafunsa. Allah ya sa Baffa Umaru da Babba Salisu sun fita waje da an yi abin kunya. Ammah ta dukar da kai tana yi ma Allah godiya. Tsam ta ta shi ta bar falon Umma Balki da Umma A'i suka bi bayanta Mami ta juyar da kai tana hamdala burinta ya cika Itama falon ta bari tana mai tsananin farinciki. Sauran kuma sai mirmishi kawai suke yi na farinciki. "Ina ga nima zan yi auren nan." Hamma Saddam ya faɗa yana kallon su yana mirmishi sai a lokacin kunya ta kama Umma Salma ganin yadda aka zura musu idanuwa sai ta sunne kanta a jikin kafafun Hamma Lamiɗo tana dariya. "Auta da gulma sai yanzu ne kika san kina jin kunyar mu? Received at 08:42Reactions: ❤ 8, 👍 2, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Hamma Jibo ya faɗa yana dariya ai sai ta tashi da gudu ta bar falon ta bar Hamma Lamiɗo na faɗin ta bi a sannu. Kallon shi kawai suke yi suna ganin sabon mutum "Lamiɗo ka canza fa da gaske." Hamma Jibo ya faɗa yana dariya "Ƙanwar ka ce ta susuta shi fa." Hamma Mustpha ya ba shi amsa suna ta dariya. Shi dai kawai mimishi yake yi bai yi magana ba shi kuma daman Hamma Abdulrahim tunda aka yi maganar Baɗɗo ya ɗauke wuta. Ranar gidan ya yini cikin farinciki da yamma su Adda Suwaiba suka zo tare da kawo abinci. Ummu Salma ce kawai ta saka Harira ta dafa mata dankalin hausa da ta ga su Ammah na da shi ta ci gaya ya yi mata daɗi sosai. Ranar gida Ummu Salma ta koma tunda a wajen ta Hamma Lamiɗo zai kwana ta yi ta yi ya barta ya ce Nahi da yaren indiyanci kuma babu abin da ya shiga tsakaninsu sun dai yi hiran su na ma'aurata sannan suka kwanta manne da juna. Washegari su Hamma Jibo duk suka koma har Hamma Kabiru. Su Baffa Umaru sun koma tun safe tare da Umma A'i, Umma Balki za ta zauna har Umma A'i ta je gida ta dawo nan da sati biyu. Mami kuma sai jibi za ta koma su Umma Salma kuma gobe da safe. Ummu Salma ba ta yi ma Baɗɗo maganar Abdulrahim ba amma ta yi ƙudiri niyyar za ta yi ta yi ma Abdulrahim maganar har sai ya ji ya amince tunda ba dole Ammah ta yi masa ba. Saboda shi ma ta zo gidan da wuri amma baya nan yana wajen aiki. Sai yamma ya dawo ta bi shi har bangaren su tana sake yi masa maganar ya ce zai yi tunani akan haka. "Wallahi Hamma Baɗɗo ba ta da matsala, mace ce mai alheri da sanin ya kamata sannan mace ta gari ce abar alfaharin kowa ni namiji." Shi dai ya ce zai yi nazari sannan zai yi addu'an in zuciyarsa ta kwanta da ita zai amince amma ba wai ya ce Aisha ba ta cancanta ba ne kawai abin ne ya zo masa a baza ta bai taɓa tunanin haka ba. Tunda kuma ya ce zai yi addu'a sai ta ƙyale shi, itama za ta yi addu'an alheri, domin tana son Baɗɗo ta auri ɗaya daga cikin yayyenta saboda alherin Aisha ga rayuwarta. Har Lamiɗo ta samu da maganar wai cikin hikima ya nuna ma Abdulrahim muhimmamcin wannan zaɓin na Ammah. Tana kuma faɗa masa shi Abdulrahim ɗin ya ce zai yi nazari sannan zai yi addu'a amma tana ce masa wai ya je ya yi masa magana cikin hikima. "Ki kwantar da hankalin ki, ba ya ce zai yi nazari da addu'a ba to mu ba shi lokaci." "Aure fa ya wuce wasa Ummu Salama. Ki bari ya zaɓar ma kansa abin da zai dauwama da shi har abada." Daƙyar ya lallasheta ta samu natsuwa ganin ta damu kanta. "Ke ma ki yi addu'a. In Ubangiji ya so za a yi." Sai ta aminta da shawaransa ta miƙa ma Ubangiji lamarin. A ranar aka dawo da Hanna ƙanin Habib Maharazu ne ya kawo ta da kayan ciye ciye sannan sun yi mata kayan salla wajen kala huɗu har da kuɗi. Sai murna take yi tana nuna ma su Sultan da yake sun zo gidan lokacin da aka dawo da ita. Sallama suka zo yi ma Ammah. Washegari kuma suka bi jirgin zuwa Lagos. Bayan Lamiɗo ya cika store ɗin gidan Ammah da kayan abinci sannan ya bar mata kuɗaɗe masu yawa. Tana ta saka albarka har tana hawaye. * Tunda suka koma gida Ummu Salma take ta addu'an Allah ya sa alheri ne a tsakanin Abdulrahim da Baɗɗo ga shi har a lokacin bai kira ta ba ya ce bai gama nazarin shi ba. Tana zuwa asibiti tunda har ta fara awo, sosai take kula da lafiyanta, tsakaninta da Bilkisu kuma ba ta canza zani ba. Gwara ma haka kowa ya yi harkan gaban shi tunda kowa da na bangaren shi. Amma dai in sun haɗu Ummu Salma na gaishe ta saboda haƙkin musulunci sun koma Lagos da sati Biyu Lamiɗo baya nan aka yi ma su Bilkisu rasuwa. Matar Mai martaba ta uku ce Allah ya yi ma rasuwa. Ummu Salma ba ta sani ba a waya ta gani ana ta sawa shi ne ta shiga har bangaren Bilkisun ta yi mata gaisuwa. Ashe kawai yayarsu dake aure a Turkiya ita ta jira a daran jirgi ya sauke ta a Lagos nan ta kwana Ummu Salma ta je itama har ɗaki ta yi mata sannu da zuwa da gaisuwa tana da fara'a ba kamar Bilkisu ba. Da safe suka wuce Kano tare. Ba ta je da yara ba tunda suna da makaranta da Sabuwa kuma kaɗai ta tafi sauran suna gida. Received at 08:42Reactions: ❤ 9, 👍 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Kuma sai da aka yi bakwai ta dawo, shima har bangarenta Ummu Salma ta bi ta, ta sake yi mata gaisuwa ta amsa. Da Lamiɗo ya dawo ya shirye sun je gaisuwa shi da Bilkisu suka kwana ɗaya a kano suka wuce Daura suka kwana ɗaya sun sake duba Mai martaba tunda jikinsa na shi ya rikice a satin ma za su koma London in da yake ganin likita sauƙin ta ma Saleem ya gama karatu yana gida ne shi ke kula da wasu abubuwan. Ummu Salma ta so ta bi su Lamiɗo ya ce aa saboda yanayinta. Shi fa yanzu taka tsantsan yake yi ba ya so su sake yin wani rashin a karo na biyu. Allah ya amshi roƙon Ummu Salma, kawai sai ga Baɗɗo ta kira ta tana faɗa mata cewa Hamma Abdulrahim ya zo wajenta da maganar aure. Ummu Salma ta saka ihun murna. "Wani amsa kika ba shi? "Na ce zan yi shawara." "Dilla banza wani shawara ki amince mu sha biki " Baɗɗo na dariya ta ce sai ta ja ajinta. "Ki tsaya garin jan aji, ajin na ki ya tsinke." Baɗɗo ta ce in ya tsinke shike nan. Ita kanta tana cikin farinciki kuma nan da nan ta ba da kai bori ya hau Saddam ya fito group yana faɗa ma su Hamma Jibo suka ce shikenan suna gama daidaitawa sai maganar aure. A wannan maganar ba wanda yakai Umma Salma farinciki ta gama lissafin abubuwan da za ta yi da bikin Baɗɗo burinta kenan ta rama mata alherin da ta jima tana yi mata. Abu kamar wasa sai ga magana ta miƙa. Kowa ya sani har can dangin Ummin ikki da dangin mahaifin Baɗɗo. Kowa ya ji sai ya ce tuwona maina. Soyayya ake sha tsakanin Baɗɗo da Hamma Abdulrahim ba sauƙi kamar daman can sun daɗe suna son juna. Sai aka tsayar da maganar cewa in su Hamma Jibo suka zo babbar salla za a yi maganar auren a saka rana a yi bikin cikin lokaci kowa ya huta. Haka kuma ya faru kaf ɗin su tare da iyalansu a gida suka yi babban salla. Su Umma Salma kuma kamar yadda aka saba a Daura suka yi salla. Wannan sallar da ta gayyaci Baɗɗo zuwa sai ta ce ba za ta je ba wai in ta tafi ta bar Sweety ɗinta shi kaɗai. Ummu Salma ta saki baki ta kasa magana saboda mamaki. Baɗɗo kuma na ta dariya. A wannan salla har Baffa an yi ma layya da fatan Allah ya kai masa ladan kabarinsa aka raba ma maƙota naman gabaɗaya. Karshenta dai tare da Islam suka tafi Daura salla ta haɗe da su Amira. Hafsat ma ta fara karatu a jami'ar Abuja. Lokacin cikinta na wattani shi shidda saura kaɗan ya faɗa wattaninsa bakwai an yi scan an ce mace za ta haifa wannan karon. Da yake ta samu sauƙin laulayi yanzu har girki tana yi lafiya lau. Ta yi ma Mai martaba abinci da kanta ta kai masa har fadar shi na cikin gidaa. Ya zauna ya ci ya saka mata albarka. Ranar har labarin Mami sai da ya ba ta Batula ikon Allah, yana ba ta labarin darun Mami Ummu Salma na dariya duk kuma abin da ya faɗa gaskiya ne Mami ba ta canza ba. Da za ta tafi ya ba ta kyautar doki ya ce duk ranar da ta shirya ta saka Lamiɗo ya ɗaurata saman doki tana ta masa godiya. Sai da suka gama salla a Daura sannan suka je Adamawa. A lokacin aka sanya ranar bikin Baɗɗo cikin ikon Allah wata biyu ma su zuwa aka sanya saboda komai yayyensa sun ce za su yi komai su za su haɗa karfi su gyara gida a fitar masa da bangarensa ya fara zama kafin ya mallaki na shi. Lefe kuma ango ya ce shi zai haɗa abin shi sai dai abin da za a ɗan taimaka masa. Hamma Lamiɗo ya ce zai shiga ciki. Baɗɗo za ta zama amarya nan da wata biyu. Farincikin Ummu Salma ya kasa ɓoyuwa, wannan zuwan ma na su Hanan ta je gidan su Habib ta kwana huɗu sannan suka dawo da ita. Tunda suka koma Umma Salma shirin biki kawai take yi ba ta taɓa kuɗin gadonta ba su akwai abin da za ta yi da su. Kuɗin hannunta dai take ta tanadin bikin Baɗɗo da su. Kuɗaɗen dake bankinta ta lissafa za su isa ta siya ma Baɗɗo fridge da Tv sai ga shi ma Hamma Lamiɗo ya ba ta miliyan biyu ya ce ta ƙara farinciki kamar za ta suma, Bilkisu ko kamar za ta mutu domin lokacin da ya ce zai ba da guddumuwarsa suna cin abinci ne a saman dinning tana ji tana gani, Ummu Salma na juyi yadda take so Lamiɗo na take mata baya. Received at 08:42 9 people reacted with ❤ [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Miliyan biyun nan duka ta tura ma Baɗɗo ta ce su ƙara wajen siyayya. Ita kuma nata ta ce sai ta zo amma ta ce kar su siya fridge da Tv da gas sai ta zo. Baɗɗo da iyayenta babu abin da za su ce ma Ammah da ahalinta sai godiya. Ammah ma miliyan ɗaya ta ba ma Ummin ikki, Mami ma 500k abincin da za a ci a duka gidajen kuma su Hamma Jibo suka ɗau nauyin komai. Lefe kuma rabin shi Hamma Lamiɗo ya saki bakin aljihu Adda Suwaiba ta haɗa akwatina takws shake da kaya sanna tuni an fara gyaran gida An bige ɗakin Baffa an bige kitchen ɗin Ammah an sake sabon tsari. Itama ɗakin na ta an kashe bedroon ɗinta zai shiga cikin bangaren Baɗdo ita kuma Ammah sai aka haɗe mata da wannan ɗayan ɗakin na waje. Cikin lokaci aka fitar da flat ɗin Hamma Abdulrahaman mai falo da bedroom biyu da kitchen. An sake yin wani kitchen a tsakar gida amma Ammah ma an yi mata wani kitchen ɗin a cikin bangarenta. An sake sabon fenti gida ya dawo kamar sabo fes. Lokacin da bikin ya ƙarato cikin Umma Salma wattani takwas kaɗan ya rage bai shiga watannin tara ba Lamiɗo ma ya fara nema musu Visa, shi da ita da Mami tare da Harira za su tafi can Egypt ɗin tuni har asibitin da Ummu Salma za ta haihu a can Egypt ɗin mai suna EL NADA HOSPITAL CAIRO, EGYPT Lamiɗo ya nemi bayanan su ta goggle. Asibiti ne mai kyau na maternity in da ake bawa mata masu haihuwa kulawa da yaransu asibitin kuɗi ne mai kyau. Hamma Lamiɗo ne ya yi musu email ya tura musu duka bayanan Ummu Salma da asibitin da take zuwa awo suka rubuta ya riga ya yi musu booking ɗin komai jiran su kawai ake yi. Amma sai an gama bikin Baɗɗo sannan za su tafi. Bai kyautu a ce a yi bikin Baɗɗo Ummu Salma ba ta nan ba duk tsaka tsantsan ɗin Hamma Lamiɗo shi kan shi ya sara ma wannan amintar dake tsakanin matarsa da Baɗɗo. Tun ana sauran sati ɗaya ta taho Adamawa tare da Harira. Bilkisu kuma sai ana gobe biki za ta taho tare da yara da Hamma Lamiɗo. Tunda ta sauka garin ba su zauna ba ita ce babbar ƙawa komai ita ce akan gaba. A can gidansu Baɗɗo ma ta sauka ta ce a can za ta yi bikinta. Hamma Saddam ke ɗawainiya da su a mota a washegarin ranar da ta iso suka je kasuwa ta siya ma Baɗɗo Tv babba da gas cooker mai shidda da frige. Baɗɗo ta yi hawaye ta rumgume Ummu Salma sai suka kama kukan a tare haka da suka dawo yan'uwan Ummin ikki da su iklima suna sake yaba karamcin Ammah da iyalanta. An yi ankon leshi da atamfa duk da ba biki za a yi sosai ba tunda Baffa ko shekara bai yi da rasuwa ba. Su Adda Safina tun ana saura kwana huɗu suka iso. Da su ake ta shirye shirye. An kai lefe tun wuri saboda Amarya ta samu bayar da ɗinkuna. Sun yi gayya amma daga maƙota sai yan'uwa kawai gidan Ammah ma cike da mutanen Mubi ango kuma abokansa sun zo har da waɗanda suka yi karatu daga kasar waje ya sauke su a hotel. Ummu Salma ta kira Shamsiya ta gayyaceta ta yi mata alƙawarin za su zo. Ranar Jumma'a, da yamma Hamma Lamiɗo da Bilkisu da yara suka iso tare da su Sabuwa. Ummu Salma bata ma gidan suna wajen saloon ita da Baɗdo da su Kaltume. Sai da suka dawo suka sauka a gidan Amarya kuma ta wuce gida. Ummu Salma ta yi ƙunshi ja ta yi kyau ga cikinta da ya girma sai ya sakata ta wani fashewa ta yi kiba. Lamiɗo in bai samu zuwa ɗaurin anan ba sai Ummu Salma sai yi fushi da shi, da ya ce ba zai samu zuwa ba ta fara rigima. Dole ya samu lokaci, sai kuma ya ci sa'a a satin ya dawo yana da cikakken lokaci. Shi dai faɗan shi Umma Salma ta bi a hankali har a samu matsala ta ce masa tana kula da kanta. Bilkisu tana gefe tana kallon kowa ɗaya ɗaya. Amma takaici da kishi sun hanata farinciki ganin yadda Ummu Salma ta zama tauraruwa. Mami ta iso tare da su Islam har da Barira. Hanan na ganinta ta maƙale mata. Washegari Asabar 25 ga watan october aka ɗaura auran Aisha Salisu da Dr Abdulrahim Hadi Baba, Baffa Umaru shine waliyin ango kamar yadda aka saba Baɗɗo kuma kanin mahafinta ne. Ɗaurin auren ya samu hallata mutane dabam dabam ciki har da Waziri da shamaki da suka wakilci Mai martaba. Mata kuma Gimbiya Shahida ce ta zo da Gimbiya Amratu sai Hajiya Zaliha A ƙofar gidan su Baɗɗo aka ɗaura auren. Received at 08:42Reactions: ❤ 7, 🔥 1, 🤗 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Bayan an ɗaura ango da abokansa suka shiga cikin gida aka yi hotuna da Amarya sannan suka tafi can gidan Ango. Ummu Salma ma Hamma Saddam ne ya zo ya ɗauketa za su ɗau hoton tarihi gabaɗayan su. Sun ɗauka gabaɗaya yaran har da Lamiɗo da Mami. Ummu Salma kusa da mijinta har tana kwantar da kanta a saman kafaɗarsa. Tana mirmishi Bilkisu ta kasa tsayawa a wajen saboda kishi. Ga shi Ummu Salma ta yi kyau ta saka wani farin leshi kamar ita ce amaryan. Duk in ta bi ta zama abin kallo. Ga Harira na biye da ita kamar jela. Gidan su Baɗɗo ta koma domin ta ce ita can take bikinta sai sun kawo Amarya. Shamsiya ta cika alƙawari ta zo tare da Habiba dake ta taunan cigham tana wani kallon kowa ɗaya bayan ɗaya. Shamsiya ta san gidansu Baɗɗo shi ya sa ba su wahala ba duk da an sami canje-canje amma gidan su Baɗɗo ba zai ɓace mata ba. Baɗɗo ma duk da haushin Shamsiya da take ji ta sakar mata fuska. Ummu Salma ta karrama su an ba su abinci da abin sha da za su tafi an ba su abin raba wa sannan Shamsiyar ta ce ma Ummu Salma za su je su gaida Ammah a can gida daga nan suka yi sallama suna fita gidan Ammah suka je Shamsiya ta yi mata Allah ya sanya alheri. Har suka ga Hanan ta sha gayu da leshi iri ɗaya da na Beena da Ummu Salma Tana ganinta ta ganeta ta nufeta tana cewa Anty. Habiba daman ba saninta ta yi amma ita kanta yarinyar sha'awa take bata to ba ta san talauci ba. Ta taso cikin gata yarinya ƙarama ga turanci ga larabci a bakinta. Sun fito har haraba tare da Hanan tana ganin su Lamiɗo ta saki hannun Shamsiya ta nufe shi tana kiran Papa. Da Shamsiya ta gan shi ko ba a faɗa mata ba ta san shi ne mijin Salma ballatana ta san shi a hoton tun a wancan lokacin da suke ƙawance da Ummu Salma. Ƙwarjininsa ya sa har Habiba sai da ta gaishe shi ya amsa sau ɗaya domin Hanan ta faɗa masa Anty ne, kuma a kaf a danginsu bai san su ba shi ya sa ya fahimci ko su waye sau ɗaya ya amsa ya yi wucewarsa wajan su Hamma Kabiru dake zaune saman darduma a haraban gidan suna hira. Sum sum Shamsiya da Habiba suka bar gida. Shamsiya ta sake samun tabbacin Ummu Salma ta yi ma rayuwarsu nisa har abada. Haka ta je ta ba ma Habib labarin mijin Ummu Salma. "Ke wannan mijin miji ne, nima wataƙila rabon Hanan ne ya sa muka yi aure amma in ana maganar mazaje irin su Lamiɗo na layi mu ba mu isa ma mu zo wajen ba." Habib ya ba ta amsa yana jinjina kai. Har gobe yana son Umma Salma, amma yana ƙokarin cire ta daga zuciyarsa ya tabbata yau ko mutuwa Lamiɗo ya yi Ummu Salma tafi ƙarfin shi har gaban abada. *Janafty* Received at 08:42Reactions: ❤ 8, 😁 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. Bayan sallar isha'i da misalin karfe takwas na dare abokan Hamma Abdulrahim suka zo ɗaukan Amarya. Har da su Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrrahaman a cikin su. An kai Baɗɗo wajen dangin mahaifinta sun yi mata nasiha, sannan Ummin ikki ma ta yi mata. Da cewa in da za ta je ba baƙon ta ba ne, Ammah ba uwar miji ba ce uwa ce a gare ta. Ta yi biyayya iya iyawarta domin bautar aure ne ya kaita. In ta ji ko da sau ɗaya ta yi ma Ammah wani kallo ba ta yafe mata ba. Baɗɗo ta sha kukan rabuwa da gida, Ummu Salma na gefenta duk da ta gaji ciwon kai na damunta kafafunta suna ta ciwo amma ba ta bar gefen Baɗɗo a matsayin ta na babbar ƙawa kuma ƴar'uwa ba duk da akwai wasu ƙawayen ƴa'ƴan yan'uwan Ummin ikki daga Mubi da wasu yanmata a dangin babansu Baɗɗo. Ga kuma maƙota har da mai yi ma Ummu Salma kitso Maijida da Bilkisu ke yi mata ƙunshi in tana gari. Sannan akwai yan makarantar su Baɗɗo da suka yi karatu tare, duk sun zo kuma sun yi mata kara sosai. An kawo motoci masu yawa shi ya sa kowa ya tafi. Ammah aka damƙa ma Amarya tare da cewa daman ɗiyar ta ce dawo mata da ita kawai suka yi. Ammah ta ce ta karɓa ta yi kuma alƙwarin zama da Baɗɗo ba a matsayin suruka ba, sai a matsayin ɗiya a gare ta. Aka yi addu'a da fatan alheri sun ba ma Ammah turmin atamfa na uwar miji da botikan cincin da dublan na Ammah da danginta daman kuma an riga an yi jere Ammah da kanta ta shigar da Amarya har kan gadonta bayan ta yi addu'an da ko wata amarya ke yi a lokacin da za ta shiga ɗakin auren ta. Ɗaki ya yi kyau sosai sai fatan alheri kawai mutane ke yi da fatan zaman lafiya. Gado biyu aka yi mata kuma masu kyau da quality. Mutane suna gama ganin ɗaki bayan sun ci abinci tunda su Adda Suwaiba sun yi abinci mai rai da lafiya na tarban Amarya, suka yi fatan alheri duk aka mayar da su gida. Baɗɗo kawai aka bari sai Umma Salma dake tare da ita, sai wata ɗiyar yayar Ummin ikki Mubeena sai Islam su kaɗai a tare da Baɗɗon. Nan suka kwana tare da ita tunda ba kowa a wajenta. Ummu Salma ta yi waya da Hamma Lamiɗo shi gida suka kwana tare da Bilkisu da yara har da Hanan ita kuma sai ta tsaya a wajen Amarya. Da safe kuma aka yi musu abin ƙaryawa mai rai da lafiya aikin su Adda Suwaiba ne. Suka kuma shigo dukkansu suna ta tsokanar Baɗɗo. Sai dai ta sunkuyar da kanta ta kasa magana bakinta ya mutu Ummu Salma ce ke tare mata. A ranar lahadin ma an yi biki sosai a gidan Ammah tunda an kawo Amarya. Shagali sai ya dawo sabo gida ya sake cika aka ci aka sha' babu abin da babu nama da naman kaza ko har ana ragewa a saman abinci Alhamdulillah kawai Ammah za ta ce, daga Masarautar Daura ma kuɗi ne masu yawa daga Mai martaba da Fulani, a ranar su Gimbiya Shahida suka koma ba su kwana ba. biki ne na yan gayu na masu kuɗi ba a yi wani shagali ba sosai saboda mutuwar Baffa amma dai an haɗu an yi zumunci an yi wasa an yi dariya. A ranar ma sun  sake yin hoto gabaɗayansu har da surukai da jikoki Baffa ne kaɗai ba shi a cikin wannan hoton an yi na tarihi ne domin sai a daɗe ba a sake haɗuwa ba ballatana a yi hoton. Har da Bilkisu tunda itama ai surukar gidan ce. Zuwa dare gida ya watse sai bakin nesa da ba su koma ba. Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim sun koma gidajensu da yaran su. Adda Nauwara ne da Adda Aisha sai Adda Safina ke gidan. Sai Ummu Salma da su Islam da su Mami tare da su Umma Balki har da Bilkisu da sauran yaran. Ummu Salma da Islam tare da su Adda Safina suna bangaren Amarya suna ɗan yi mata gyare gyare tunda yau ango zai shigo ɗaki. Su Mami ne ke can falon Ammah suna ta hiran su, da Bilkisu da ta hakimce cikin manya ana magana tana kallon bakin kowa ɗaya bayan ɗaya. Ummu Salma na zaune saboda ba za ta iya wani aiki ba, jikinta ciwo yake yi ga bayanta. Sannan kafafunta sun tasa aikin ma su Harira ne, ita ke shara Hidaya na mopping Sabuwa na tare da Bilkisu. Daman su Anitha suna can Lagos aka bar su tare da su James suna tsaron gida. Received at 08:43Reactions: ❤ 7, 👏 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Adda Safina na ta yi ma Baɗɗo shaƙiyanci da cewa Amarya ta ango yau dai Abdulrahim zai shiga ɗakin Amarya. "Ko kunya haka zai wuce bangaren Ammah ya shigo nan ko? In ji Adda Nauwara aka kwashe da dariya. Adda Safina na faɗin ga Abdulrahim da kunya dama Saddam ne mai ido a tsakar ka, ita dai Baɗɗo ba ta magana sai dai mirmishi. Ummu Salma na gefenta ita ce ke shigar mata. Baɗɗo kafafun Ummun Salma ta kalla da ta miƙar da su a saman cafet ɗin dake falon. Ta ga yadda suka kumbura suna sheƙi. "Kafafun ki sun kumbura fa Sisna? Ta faɗa tana kallon Ummu Salma. "Zirga zirga ne ya sa suka ɗan haye sosai" "Ko jinin ki ya hau ne? "E ya ɗan hau zuwa asibitin da na yi na ƙarshe likita ya ce jinina ya ɗan yi sama." "Allah ya sauwake. Ubangiji ya raba lafiya, yaushe ne tafiyar ta ku? "Visa muke jira, tana fitowa za mu tafi." "Allah ya kai ku lafiya. Allah ya sa a rabu lafiya cikin Aminci." Ummu Salma ta amsa da Amin Amin. Sai da suka gyara mata ko'ina suka turara shi da turaran ƙamshi ko'ina ya yi ƙal gwanin sha'awa. Sallama suka yi ma Baɗɗo suka koma bangaren Ammah tunda ga tashin muryoyin maza nan a can bangaren. Baɗɗo ta roƙi Ummu Salma ta zauna da ita kafin Hamma Abdulrahim ya shigo. "Na gaji Sisna, zan je na yi wanka  ga Islam ta zauna dake." Dole aka bar Islam da Baɗɗo. A bangaren Ammah kuma mazan suna nan gabaɗaya ango ne kawai da Saddam ba su a wajen suna can tare da abokan ango lokacin da Ummu Salma ta shigo tana tura ciki a gaba sai da Umma Balki ta yi mata maganar kumburun kafafunta. "Ki huta yar nan, nauyi ne a tare dake fa." In ji Umma A'i Mami ta ce itama tun safe ta ga kafafun Ummu Salman sun ɗan kumbura Lamiɗo na gefen Hamma Kabiru yana kallon Umma Salma dake tsaye a gefen Mami shima ya ga kumburin kafafun nata. "Zirga zirga ne fa ba wani abu." Ummu Salma ta faɗa sannan ta ce za ta shiga ta yi wanka bayanta ma na ciwo. Umma Balki ta ce ko tana kan gwiwa ne. Mami ta amsa mata da cewa akwai saura EDD ɗin ta farkon watan November ne. "To ina ruwan Allah da abin da bature ya ce? Ko yanzu Haihuwa ta zo ɗa zai fita fes." Umma Balki ta faɗa har tana tafa hannu, Umma A'i na cewa ƙwarai kuma yadda cikin Ummu Salman ma ya yi ƙasa daga gani ya kusa fitowa duniya. Mami ta karɓe da cewa da ikon Allah sai sun isa Egpyt sannan Ummu Salma za ta haihu a hannun ƙwararrun likitoci aka amsa da in sha Allahu. Bilkisu ta na zaune ta ji maganar kamar daga sama. Ta kalli Lamiɗo zuciyanta ta rufe saboda kishi ashe a Misra Ummu Salma za ta haihu bai faɗa mata ba. Ta kalle shi amma shi hankalin shi ma ba ya kan kowa sai Ummu Salma, Hamma Kabiru ma na yi masa magana kunnensa ne kawai ke ji amma hankalin shi na kan Ummu Salma da suke magana da Mami. Har duhu take gani saboda kishi da baƙin ciki. Ta daɗe tana tunanin Lamiɗo ya fi son Ummu Salma akanta sai yanzu take sake samun tabbacin haka. Ita duk haihuwanta a Nigeria take haihuwa na Sultan ma a wani babban asibitin kuɗi ta haihu a Abuja na Beena ta haihu a Lagos. Kuma ita daman ba ta da ra'ayin fita kasar waje ta haihu tunda duka haihuwanta ba ta samu matsala ba, ko ƙaruwa da mata ke yi wajen haihuwa Allah ya ba ta da sauƙi ba ta taɓa samun wata matsalar ba. Kallon kowa kawai take yi a falon cikin jin haushi. Domin ta fahinci ma da wannan bikin ko Ammah ba ta bi ta kanta ba. Kowa ya koma ma Ummu Salma, babban baƙin cikin Bilkisu a ce tana waje amma har tauraruwarta ta dishe sai Ummu Salma kaɗai ake gani, sannan har ana shirye-shiryen fita da ita kasar Cairo ta haihu amma Lamiɗo bai taba faɗa mata ba. Idanuwanta sun cika da ƙwalla ta yi ƙokarin ɓoyewa, ta jima tana fahimtar Lamido ya fi son Ummu Salma a kanta ko daga ganin yadda yarinyar nan ke juya shi, sai abin ta ce shi yake yi. Wani turiri ne ke tasowa daga ƙasan zuciyanta so take yi ta samu kaɗaici ko za ta yi kuka ta ji sauki. Received at 08:43Reactions: ❤ 7, 😁 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Kamar ta a ce Ummu Salma ta ƙere mata. Ita ta yi nasara ita kuma ta faɗi. Tun tana ƙarama ba ta taɓa yarda wata mace ta fita ba. Nadama take yi nadamar raina Ummu Salma tun farko ga shi ta raina ta, ta zo ta zame mata ciwon ido da damuwa kuncin dake zuciyanta Ummu Salma ce sila domin ta tsani ganinta kusa da mijinta. Jikinta ba in da ba ya rawa saboda damuwa da kishi. Shi yasa ta tura ma Lamiɗo sako a waya da cewa tana son ta koma gida ta gaji za ta huta. Sai ya ce okay, su shirya sai su tafi lokacin Ummu Salma ta shiga ciki. Ta miƙe tana yi ma Sabuwa magana da ta tattara yaran za su tafi. Daidai Ango na shigowa tare da Saddam ba aboki ko ɗaya Saddam ya ce duk sun koma yau. Ammah ta yi nasiha su Hamma Jibo ma duk sun yi masa nasiha da sake tunasar da shi nauyin da ya hau kansa sai ya yi haƙuri a matsayinsa na namiji kuma shugaba. Lamiɗo ma ya ce yanzu ya zama babban mutum ya yi duk abin da zai yi ya daraja wannan auren da matarshi tare da iyayen shi gabaɗaya. Ba wanda ya yi masa rakiya ɗakin Amarya sai Saddam dauke da ledojin Kaji da lemuka. Adda Safina na ta cewa Ummu Salma ta fito ta je ta yi siyan baki, ta ƙi fitowa ga gajiya sannan ga sallar mangariba da isha'i a kanta. Tana fitowa wanka ta fara yi sallar mangariba a zaune take yin sallar saboda bayanta ya riƙe kafafunta ma na ta ciwo suna tauna. Tana zaune bayan ta idar da sallar isha'i ta miƙe kafar kenan ta ji an buɗe ƙofa an shigo ta ɗauka ma Mami ce tana juyawa sai ta ga Gogan ta ne Ta sakar masa mirmishi ya mayar mata da martani. "Hamma na." Ta faɗa cikin shagwaɓa kamar za ta yi kuka tana ware masa hannuwanta daga zaune. Ya tako har gabanta ya duƙa suka rumgume juna. "Na yi missing ɗin Hamma." "Na yi missing ɗin ƙanwata" Ya amsa mata kansa na tsakanin wuyanta da kafaɗanta, lokaci ɗaya hannunsa guda ɗaya na saman cikinta yana shafawa. "How is my girl doing? "Yau sai tokari na take yi" Ummu Salma ta amsa masa cikin shagwaba Tana cigaba da faɗa masa bayanta da kafafunta na ta ciwo. Bai ce komai ba illa sakinta da ya yi ya koma yana matsa mata kafafun yana faɗin suna ciwo ne ta ce babu ciwo. "Ɗan zirga zirgan da na yi ne kawai fa Hamma." "To wa ya ce ki yi zirgan zirgan? Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Kanta ta miƙa masa, ya saka hannu ya cire mata hijabin jikinta. Daga ita sai wata yar shimi rabin cinyoyinta duk a waje ga cikinta da ya yi tsini. "Hamma bikin Baɗɗo ne fa. Dole na yi zirga zirga." "Baɗɗo ta wuce tunanin ka a wajena." Duk yasan da wannan labarin kamar sake maimaita masa take yi, tana faɗa masa komai na ta Baɗɗo ce akan gaba. Duk abin da ya sameta na farinciki ko na baƙinciki ita ke tare da ita. Shi dai matsa mata kafafunta yake yi bai yi magana ba. Domin sake tusa masa abin da ya sani kawai take yi. Ya ɗan jima a wajenta yana yi mata maganar ya za a yi da maganar tafiyarsu Shi yana tunanin za su koma Lagos tare da Bilkisu. Ita kuma Umma Salma sai ta ce ya bar ta anan sai Visar su ta fito tukunnah. Ya ce ba ta da matsala za ta iya zama. Bai bar ɗakin ba sai da Bilkisu ta kira shi awaya suna ta jiran shi ta shaƙa ta kusa fashewa daga cewa yana zuwa ya shanya su ta kuma san wajen Umma Salma ya je ya yi zamansa. Ko da ya fito ya yi ma su Ammah sallama tuni Bilkisu da su Sabuwa suna haraba suna jiran shi a bakin mota. Bilkisu ta kasa ko da dariya. Kishin ta ya kasa ɓoyuwa daman kuma ita abin da ke damunta ba ta iya ɓoye shi yana bayyana har a saman  fuskarta. Har suka isa gida ba ta yi magana ba duk da ko Lamiɗon ya yi mata magana ta kalle shi kallon tara saura kwata zuciyanta na zafi ta kauda kai. Tunda ya ga haka sai ya ƙyaleta ba daga Bilkisun har Ummu Salama ba wacce bai san halinta ba ya san halin Ummu Salma ciki da waje ya san kuma halin Bilkisu. Kawai shi dai mutum ne da ba ya son yana takura ma mutane, yana nuna kamar bai san komai ba ne amma babu abin da bai ankara da shi ba. Received at 08:43Reactions: ❤ 8, 🥰 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ya san Ummu Salma da Bilkisu ba sa shiri amma tunda ba faɗa suke yi ba no need ya shiga ciki. In dai za su daraja junan su to zaman su a haka bai zama illa a gare shi ba. Ya san Bilkisu tana da zafin kishi ba ta ɓoye kishin Ummu Salma saɓanin ita Umma Salma da ba ta taɓa nuna masa tana kishin Bilkisu ba, kuma ya san tana yi kawai ba ta nunawa ne. Yau ɗin ma abin da ta yi masa ya san kishi ne saboda ya tsaya wajen Ummu Salma. Ba ya son fitina ko kuma shi na shi ran ya ɓaci shi ya sa kawai ya ƙyaleta. Da suka koma gidan ma ɗakinta ta shige ta rufe ƙofa shima sai bai neme ta. Duk da ba aiki zai koma wannan satin ba amma yana buƙatar su koma gida ya huta sosai kafin visar su ta fito. Sai dai kafin su tafi zai je Daura. Shi yasa washegari da safe ya bi jirgi zuwa Katsina daga can aka zo aka ɗauke sa zuwa Daura. Yana zuwa Daura akai akai saboda jikin Mai martaba duk ya sasaabe duk da ba kwantar da shi cutar ta yi ba amma ta jima a jikinsa kafin ta bayyana. Amma yanzu likitocin dake duba sa a kasar London sun tabbatar da Lever ɗinsa ta taɓu 50% amma tunda ana kan magani akwai yuyuwar ba za ta cigaba ba. Daman yana ta fargaban kar Mai martaba ya ɗauko masa wancan maganar. Sai kuma aka ci sa'a Mai martaba bai yi masa zencen ba. Sun dai jima suna hira suna tattaunawa game da sha'anin mulki da sarkaƙaƙiyar dake cikin ko wace masarauta. Fulani ma ta ji sauƙi amma itama suna shiryen shiryen suwa Saudiya  itama a can take ganin likita tare da Hajiya Kilishi da Hajiya Zeenatu za su tafi. Washegari da Safe ya dawo Adamawa. Ya nema musu ticket, a ranar da karfe shidda na yamma suka koma Lagos shi da Bilkisu da yaran gabaɗaya. Sun zo gida sun yi ma su Ammah sallama Bilkisu ta yi kamar ta yi bindiga lokacin da Ummu Salma ta yi musu rakiya har tana riƙe hannun Lamiɗo kuma bai hana ta ba. A masu rakiyar har da Amarya Baɗɗo Hamma Abdullahi ne ya kai su filin jirgi washegari suma su Hamma Jibo duk suka koma garuruwansu da ilyalansu gida ya rage daga Ammah sai Ummu Salma da Mami, Umma Balki da Umma A'i ma sun koma Mubi Sai Amarya Baɗɗo da angonta sai Hamma Saddam. Amarya da ango suna ta cin amarcin su. Suna bangarensu amma ko wani safiya Baɗɗo za ta shigo ta gaishe da Ammah da Mami ba ta fara girki ba Adda Suwaiba na aiko mata da abinci. Haka ma Adda Ummu Suleim nan gida kuma Harira tare da Barira suke girkawa wani zubin kuma Mami ko Islam tunda ta iya girkin itama. Sai Ummu Salma da kan shiga wajen Baɗɗo in Abdulrahim na bangaren Ammah su sha hira. Washegari Daddy ya zo, bai samu zuwa ɗaurin auren ba domin ba ya ƙasar. Bai kwana ba a ranar ya koma tare da Islam da Faruk Barira kuma za ta zauna tare da Ammah kafin su Mamin su dawo daga Cairo. * LAGOS. BAYAN KWANA HUƊU. Tunda suka dawo Bilkisu ta canza masa. Ba ta sakin masa fuska, ba ta zama da shi ko a dinning suka zauna cin abinci haka za su zauna su ta shi amma ba wani hira ko sakin jiki ya fahimci tun suna Adamawa ne ta canza masa. Ba ta kwana a bangaren shi ya ɗauka tana buƙatar lokaci ne sai da aka kwana huɗu sai ya fahimci sai sun zauna sun yi magana wata kila akwai rashin fahimta. Shi ya sa ya yanke shawaran zai yi magana da ita domin su fahimci juna. Ba ta nan ta je asibiti, ya yi niyar cewa zai faɗa mata har maganar tafiyar su Egypt to da yamma ma kafin ta dawo ma aka tura masa sako Visar su ta yi ready, za su tashi nan da kwana uku. Tunda kamfanin da ya nemi Visa package ne gabaɗaya har da kuɗin jirgi da komai da komai. Ya tura ma Ummu Salma saƙo tunda ya kira ta bai same ta a waya ba. Ya kamata zuwa gobe su taho Lagos tunda ta nan jirgin su zai ta shi. Ya samu Mami a waya sun daɗe suna tattaunawa. Sun rabu da cewa zai neme musu Ticket gobe su taho Lagos jibi sai wuce gabaɗaya. Lamiɗo bai taɓa tunanin har da maganar tafiyar su Cairo a cikin abin da ya ɓata mata Bilkisu rai ba sai da ta dawo da daddare da kan shi  ya bita bangarenta. Ya fara da tambayanta ko akwai wani abu dake damun ta ne? Tana gaban madubi tana gyara gashin ta, ta yi shirin barci ma lokacin da ya shigo. Received at 08:43Reactions: ❤ 8, 👍 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta yi masa banza kamar ba ta ji shi ba. Haushin shi na sake kamata. Kishi mai zafi na murkukusanta. Tunda har ya fifita wata mace a sama da ita shima haushin shi take ji, ta nuna fushinta tunda suka dawo amma sai yau ne ya neme ta, ba ta da muhimmanci a wajensa shi ya sa bai damu da fushinta ba. Ya sake maimaita tambayarsa sai a lokacin ta amsa shi da cewa bakomai. Ya yi shuru kawai yana kallonta. Ya san da komai ɗin shi ya sa ya tambaya. Dole shi ya ƙariso kusa da ita ya rakwafa fuskokinsu na bayyana a cikin madubin yana sanye da kayan barci ne masu taushi riga da wando ita ma rigar barcin ce a jikinta mai santsi rigar tana da leshi- leshi a saman wuya. Ya daɗe yana kallonta ta cikin madubin ita kuma ta ƙi yarda su hada ido. Habarta ya ɗago yana kiran sunanta. Ta goce habarta daga hannunsa ta miƙe har tana ture shi. Domin kuka ne ke son ƙwace mata, kwanaki nan kwana take yi kuka kishi na neman zautar da ita jininta har hawa ya yi, yau sai da aka yi mata gwaji. Ta so ta je ta yi kwanciyarta ne sai ya tokare ta da jikinsa ta sake juyawa ya yi saurin riƙota ta baya ya rumgumeta. Ta fara mutsu-mutsun ƙwace kanta amma ya matse ta sosai a cikin jikinsa ba ta da yadda za ta yi kawai sai ta saki hannunta kukan da take riƙewa ya ƙwace mata ta kece da kuka mai sauti da ƙara. Bai hana ta ba, ya bar ta yi kukan ta ko ta samu sauƙi. Juyowa da ita ya yi ya matse ta a saman ƙirjinsa yana bubbuga bayanta alamun lallashi ta yi kuka da sauti ta koma shessheƙa hawayenta duk ya ɓata masa gaban rigar barcin jikinsa Kusan mintina goma suna tsaye kafin ya ja ta zuwa bakin gado ya zaunar da ita. Ya durƙusa a gabanta ya sanya hannayensa yana share mata hawauye Ta yi masa zuru tana kallon shi. Ko alama ba ta ji son shi ya ragu a zuciyarta ba. Tana son shi kuma har abada tana son shi. Ba ta son ta yi sharing ɗin sa da kowa shi yasa zuciyanta ke ciwo. Hannunsa ta riƙe tana kallon shi. "I love you Lamiɗo. Ina son ka, bana son wata mace a kusa dakai. Ji nake yi kamar zan mutu." Take faɗa hawaye na sake kece mata. Dole ya miƙe ya zauna a gefenta ya ɗagota  zuwa saman jikinsa Ta sake rikice masa da kuka shi kuma ya na ta lallashinta da ƙyar ya samu ta daina kukan ta koma ta lafe a jikinsa tana sauke tagwayen  ajiyar zuciya. Ya sake ɗago fuskarta yana share mata hawaye. "Is okay! na ce ya isa." "What wrong with you? Ni ne na yi miki laifi? "Ki faɗa mini, zan ba ki hakuri bana son wannan shuru.' "Shuru ba ya kawo mafita a relationship, ballantamu da muke Ma'aurata. Juzt in ma wani abu ne da na yi miki ba ki ji daɗi ba you can feel free ki yi mini magana mu tattauna mu samu fahimtar juna." Ta yi shuru tana kallon shi kawai ta kasa magana yana nufin bai san laifin shi ba. Laifin shi ɗaya me ya sa ya auri wata macen ya fifitata a sama da ita. "Uhm tell me what happen? "Why? Ta tambaye shi muryanta a shaƙe. Ya zura mata ido yana kallonta. "Why? Me ya sa ka aureta? "Me ya sa ka auri Ummu Salma.? Daman ya san matsalan kenan ya ɗauka ta fahimci kaddara tun daga fari ashe tana buƙatar ƙarin bayani. "Why me ya sa? Kasan yadda na ke ji a zuciyata in na ganta tare da kai? "Ji nake yi kamar zan mutu kamar zan yi hauka." "Ina sonka, ni kaɗai na ke so na mallake ka. Me ya sa ka aure ta? Ya ɗan lumshe idanuwana ya buɗe a saman fuskarta yana kallonta. "Kaddara." Sai ya ɗan yi shuru kafin ya ɗan gyara mata zaman ta a saman cinyarsa. "Tun a littafin zanen kaddarata. Ubangjina ya zana zan aure ki da farko ke Bilkisu daga baya zan auri Ummu Salma. Kuma ba wanda ya isa ya goge wannan zanen a cikin littafin kaddarata. Domin Ubangiji ne ya zana hakan kuma dole ya faru." Ya dakata yana fahimtar yadda ta karɓi maganar. Sai hawaye shar suka zubo mata a saman kumatunta. "Amma hakan ba ya na nufin na yi hurting feeling ɗin ki ba ne. I'm sorry." Sai kawai ta sake fashewa da kuka. Cikin kukan take faɗin" Me ya sa to sai ita ba ka auri wata ba? "Saboda ita Ubangiji ya rubuta mini." "Kana son ta? "Yes i do" Ta runtse idanuwana wasu hawayen na sake kece mata. "Ka fi sonta a kaina. Kafi son ta." Take faɗa cikin gunjin kuka. Received at 08:43Reactions: ❤ 7, 😁 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "A'a ba gaskiya ba ne " Ya yi saurin katse ta saboda shi dai ya san ba gaskiya ba ne. "Gaskiya ne mana komai ita ce abubuwa da dama a tare da kai ta canza ka, me ya sa? Saboda kana son ta ne ka ba ta damar ta canza ka, amma ni ba ka bani damar haka ba." "Na ba ki dukkan dama Bilkisu." Ya faɗa yana kallomta lokaci ɗaya yana share mata hawaye. "Ban taɓa takura miki ba, duk abin da kike so ina son shi. Saboda na ba ki damar samun auren ki cikin farinciki. Duk wani baƙon abin da kika ga ina yi Ummu Salma ke so, ta nuna tana so sai na yi mata ke kuma ba ki taɓa nuna kina son abu ban yi miki ba. Ni kuma ina gudun yin wani abun da ba ki so, bana so na ɓata miki rai bana so na ɓata ma duk wani wanda nake zaune da shi rai. Ina girmama ra'ayin duk wanda zama ya haɗa da ni da shi Bilkisu." "Ai ko ban faɗa ba ka san na daɗe ina son mu dinga wanka tare amma ba ka taɓa ba ni damar haka ba? "Ba ki ce kina so ba, kawai saboda ni bana so sai ba ki damu ba. Ita kuma tana so ta damu shi yasa na yi mata abin da take so." Tana kallon shi zuciyanta na sake ɗaukan zafi da ɗumi. "Am sorry." Ya faɗa yana sake riƙeta a jikinsa. "Ban taɓa hana ki abin da kike so ba. Kin sani." "Ka fi son ta ne kawai ka yarda da magana." Kukanta yaƙi tsayawa saboda kishi. "Na ce miki ba gaskiya ba ne ." "To mene gaskiyan? Yanzu ma ƙasar za ku bari ba ka faɗa mini ba. Ni yaushe na samu damar yin tafiya da kai!? Lokacin da na haifi Sultan ne kaɗai muka je Maroco shima ba mu daɗe ba muka dawo amma ita fa? Tare za ku tafi wataƙila ma sai ta haihu za ka dawo,  kana ji da ita a gaban kowa kake nuna tsananin kulawarka a kanta me ya sa ba zan ce ka fi son ta ba? Sai ta bashi tausayi yadda take magana ya fahimci ya yi hurting ɗin ta. "I'm sorry." "I'm sorry ina ta so na faɗa miki ne ki yi haƙuri please." Lamiɗo na birge ta ba shi da girman kai. Ko ya yi laifi ko bai yi ba zai ba da haƙuri domin a samu daidaito. "Bilkisu." Ya kira sunanta a kausashe. Ta kalle shi tana fahimtar duk maganar da zai faɗa da gaske ne. "Na gode sosai " Ya faɗa yana yi mata mirmishi sannan ya sumbaci kumatunta har yana saka harshen shi ya lashi hawayenta. Ta kankame shi jikinta na shaking kamar tana jin sanyi. "Thank you. Thank you for marrying me, for giving birth to our childreen and for your love and everthing. I love you." Ya faɗa yana sake ƙamƙameta itama tana ƙamkame da shi tana hawaye raɗaɗin dake cikin zuciyanta na raguwa "Kana sona? Ni fa Fulani ce ta yi maka tayi na.? Ita fa cewa ka yi kana son ta." Tana jikinsa take faɗin haka. Ya yi shuru kawai yana sauraranta. "Kana yi mata wasu abubuwan ko da ban yi niyar kishi ba sai na ji kishi. Sai nake tunanin kana fifita ta sama da ni saboda ka fi son ta." "Na ce ba gaskiya ba ne ko?." "Wallahi tallahi kinsan rantsuwa ko? Sai ta ɗago tana kallon shi ba ta taɓa jin ya yi rantsuwa haka ba. "In za ki yarda da ni, ban fi son wata akan wata ba." "Ban fi son Umma Salama a sama da son da na ke yi miki ba." Ta yi ƙuri tana kallon shi. Ya ɗan sauke numfashi kaɗan yana kallonta itama shi take kallo, sai ya ɗan kauda kai, saboda abin da yake faɗa sabanin abin da ke zuciyarsa ne amma saboda samun daidato da zaman lafiya gwara ya faɗi saɓanin gaskiya. ta sakalo hannayenta ta wuyansa  suna masu kallon juna. "Ke na fara aure ke kika fara mayar da ni uba me ya sa zan fifita wata macen sama dake? "Dukkan ku ina son ku i'm sorry ba ina nufin na ɓata miki rai ba. Ina son Umma Salma a yadda take, kema ina son ki a yadda kike. Bana son wannan canjin a tare dake. I love you do way you are. Itama haka nake son ta a yadda take." Ya lumshe idanuwana ya buɗe sun ɗan rusuna sannan muryansa ta ɗan shige ciki. "Ki daina damuwa da cewa ina son ta sama dake ba gaskiya ba ne. Sannan maganar ina ririta ta kuma kin san ba ta da lafiya ta rasa Baffa ta rasa jariri she is not fine, ina tare da ita domin kar ciwon damuwa ya kamata ga shi ta zo ta sake samun wani cikin, tana cikin hatsari tana da Bp komai kin san zai iya faruwa. Received at 08:43Reactions: ❤ 5, 👏 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Maganar zuwa Egypt kuma tun wancan haihuwan a can na tsara za ta haihu sai kuma ga kaddaran da ya faru ba nufina na ɓoye miki ba i'm sorry da ban faɗa miki akan lokaci ba." Ya yi shuru yana kallonta. Yana so ya ga yadda ta karɓi maganganunsa da alamu sun shigeta ta daina kuka fuskarta ta nuna tana fahimtarsa "Ba kuma a can zan zauna ba, muna zuwa aka gama komai zan dawo na bar su a can tare da Mami na san she'll be okay with her." "I'm sorry." Ya sake ba ta haƙuri sai ta lumshe idanuwana ta buɗe sannan ta kalle shi. "Do you love me? "Yes i do." "I love you so much." Ya faɗa cikin sanyin murya. Sai kawai ta sake ƙamƙame shi. "In dai kana sona za ka cigaba da sona, sannan in dai ba ka fi son Ummu Salma sama da ni ba i'm okay." Kanta yake shafawa zuwa bayanta alamun lallashi. "In ba ki shawara? Ya faɗa yana ɗago fuskarta sai ta gyaɗa masa kai "Ki daina bari zuciyarki na jin zafi akan wani abu. Aure fa umarnin Allah ne, tunda haka ne bai kama ta ki bari kina damuwa ba. Please ki cire komai a zuciyarki ki sani ina tare dake har abada." "I will." Ta faɗa tana share hawayenta da bayan hannunta. "Zuciyata ke zafi in na ganta a kusa da kai ban san yadda zan yi ba." "Ki yi hakuri." Hakuri ne kawai zai iya bata. Domin ba zai iya cire mata abin da ke zuciyanta ba. Za ta cigaba da ganinsa da Ummu Salma har abada. To gwara ta yi hakurin shine mafi alheri. A daran kuma ya sake tabbatar mata da cewa Ummu Salma ba ta fita a wajensa ba. Koma mene ne ya bar ma zuciyarsa wannan amma shi ɗin banza ne ya isa ya iya daidaita soyayyar mata biyu a zuciyarsa? Dole akwai wacce ya fi so, sannan ko wacce akwai dalilin da ya sa yake son ta amma domin a zauna lafiya sai ya nuna ma Bilkisu ita ce tauraruwa tunda ya fahimci ita a komai ta fi son ta shiga gaba sai ya nuna mata ita ɗin ce a gaba domin a zauna lafiya. Ya fahimci akan kishin Ummu Salama za ta iya kamuwa da wata cutar to a haka ma ya aka ƙare ballatana ta tabbatar da hasashenta na cewa ya fi son Ummu Salama ai ba zaman lafiya. Shima a bangaren sa ya yi tunanin zai dinga kiyayewa saboda gudun nuna bambamci ko kawo ɓaraka a rayuwar gidan shi da iyalansa, kuma daman fatan shi a koyaushe Ubangiji ya ba shi ikon ci gaba da yin adalci tsakanin Bilkisu da Ummu Salama. Kawai ta zauna a yadda take Bilkisunta ba Bilkisun yanzu mai ƙorafi da yawan fushi ba. Suka kwana cikin farinciki suka tashi cikin farinciki ya faɗa mata zuwan su Mami ta ce Allah ya kawo su lafiya ta fita da kanta ta ce Hidaya ta shiga bangaren Ummu Salma ta gyara Debora kuma ta ce ta shirya abinci. Har da asuba nan sai da Lamiɗo ya sake yi mata sabon lallashi da alƙawarin in Ummu Salma ta haihu za su tafi duk ƙasar da take so shi da ita tunda karshen shekara ya zo. Ta dinga murna tunda ta ji ya ce daga shi sai  ita yara ma a gida za su bar su kanta ya fashe tana jin kanta kamar sarauniya. Tana so ta koma yadda take a baya amma kishin ne ke murƙusaan zuciyanta Ta rasa yadda za ta yi, sai ta kira Umman Kano bayan sun gaisa take ce mata. "Umma wani addu'a mutum zai yi Allah ya rage masa zafin kishi a zuciya? Tunda dai har abada za ta cigaba da ganin Ummu Salma a kusa da mijinta. Gwara ta nemi hanyar da za ta samu sauƙi kar kishi ya yi ajalinta watarana. Umman Kano ta yi dariyansu na manya kafin ta ce." Ni kika gado a kishi Bilkisu, amma kuma ba ki gado yadda za ki yi yaƙi da shi ba. Na sha faɗa miki wannan kishin na ki illa zai yi miki watarana ba ki sani ba." "Umma ina son na samu sauƙi a zuciyata ya zan yi.? Ta faɗa kamar ta yi kuka, ta gaji tana son zuciyanta ta samu hutawa "Kishi halas ne Bilkisu ba ki yi laifin komai ba. Na fiki zafin kishi amma kika ga na zauna da kishiyoyi kuma na iya allona haƙuri ake yi kawai sannan ki dinga maimaita Hasbunallahi wa'imal wakel a cikin zuciyarki a duk lokacin da kika ganta. A sallolinki ki dinga faɗa ma Ubangiji ya sanya miki sassauci da salama ki dinga samun lokaci ki tashi cikin dare ki yi salla ko raka'a biyu ne ki roƙi Allah ya sanyaya miki zuciya ya ɗaga tauraruwarki a zuciyarki mijinki. Kar ki sake bari ya fahimci kina da kishi mai zafi. Received at 08:43Reactions: ❤ 8, 👍 1 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ki iya kissa da kisssinan da za ki fi kowa a wajen mijinki in kika yi haka a hankali a hankali komai zai dinga raguwa har ma watarana in kin gansu tare ba za ki ji komai ba." Umma ta daɗe tana ba ta shawarwari masu kyau, irin wanda Ya Hadiza take ba ta take ganin kamar su ba za su gane ba ne. Amma yanzu ta fahimci maganganunsu, tunda Ummu Salma ba za ta bar mata mijin ta ba, gwara ta koyi yadda za ta rayu tare da ita cikin salama ta gaji tana bujatar ta zauna da zuciyanta lafiya Ita yanzu kawai mijinta za ta kama a hannunta yadda Ummu Salma za ta fahimci da sauran ta a jira. Ƙarfe huɗu da wasu mintina Bilkisu da Lamiɗo suka je filin jirgi suka ɗauko Ummu Salma da Mami tare da Harira. An gyara gida ko'ina kal yana tashin ƙamshi karon farko da Mami ta taɓa taka gidan Lamiɗo a rayuwarta kenan. Bilkisu ta yi ƙokarin sakin jikinta da fuskarta saboda Mami kuma Mamin ta yaba mata sosai. A bangaren Ummu Salma ta sauka a tare da yaran gabaɗaya suka ci abinci a saman dinning gida ya yi daɗi ana ta hira. Saboda Mami sai Umma Salma ta ce Lamiɗo ya je wajen Bilkisu kawai ya kwana ita yanzu ma ta kanta take yi. Zuwa wayewan gari duk sun gama haɗa kayan tafiya. Kayan haihuwa kuma daman kaɗan suka ƙara siya wannan karon tunda akwai ma wancan da yake both boy and girl suka siya, jirgin dare za su bi Ummu Salma ta kira duka yayyenta sun yi sallama tare da yi mata fatan alheri. Baɗɗo ta ce tana nan ne amma gabaɗaya addu'anta na kan Ummu Salma in sha Allahu za ta haihu lafiya. Ammah kuma da suka yi sallama ta ce duk safiya ta dinga karanta ayatul kurusiyu tana tofawa a ruwa tana sha komai zai zo da sauki. Bilkisu da yaran gabaɗaya suka raka su har filin jirgi misalin tara na dare James ya tuƙa su. Harira na ta murna za a je kasar larabawa daman ta san da tafiyar tunda tun kafin su zo bikin Baɗɗo Lamiɗo ya sa aka yi mata international passport tunda karon farko kenan da za ta bar Nigeria itama Ummu Salma sabo ya sake yi mata, na ta na shekara biyar ne ya yi expire, Mami ne da shi suke da na shekaru goma-goma su ba su da matsala. Ummu Salma na sanye da a baya baƙa. takalmin kafarta mai saukin tudu ne amma dakyar ta tura shi saboda kumburin kafarta. Yaran ɗaya bayan ɗaya suka rumgumeta suna yi mata sallama wai suna jiran now baby tunda Papa ya ce Anty Umma tare da Baby za ta dawo. Har da su Sabuwa aka zo filin jirgi yin sallama, Anitha da Debora da aka bari gida kafin fitowarsu suna ta mata fatan dawowa lafiya tare da Baban Adila. Bilkisu ta ba ma Ummu Salma hannu suka yi masabaha. "Allah ya raba lafiya" "Amin na gode." Ummu Salma ta amsa tana mirmishi. "Ki yafe mini in na yi miki laifi. Ban sani ba ko Allah zai sake haɗa fuskokin mu" Ummu Salma ta faɗa idanuwanta sun cika da kwallan gani take yi kamar a wajen haihuwan nan za ta mutu duk a firgice take. Bilkisu ta kalleta ta yi mata laifi mai girma ta aure mata miji. Ƙananun laifukan kuma daman kowa ya yi ma ɗan'uwansa. "Bakomai nima ki yafe mini." "Allah ya yafe mana gabaɗaya." Bilkisu ta yi sallama da Mami ta amsa mata cikin yanayinta na koyaushe. Sannan suka rumgume da Lamiɗo lokacin Mami ta juya baya tana magana da Daddy a waya. Yaran ma ɗaya bayan ɗaya ya rumgume su suka yi sallama. A filin jirgin suka barsu suka koma gida. Jirgin na su sai ƙarfi sha ɗaya na dare ya ɗaga zuwa EGYPT babban birnin Cairo Ƙasar da Annabi Musa ya yi rayuwa wanda a wancan zamanin ake kiran ƙasar da ƙasar MISRA. *Janafty* Received at 08:43 11 people reacted with ❤ [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. *CAIRO, EGYPT.* EL NADA HOSPITAL. A safiyar ranar talata suka sauka a ƙasar Egypt babbar birninta Cairo. Tun kafin su sauka motar asibitin da wasu daga cikin nurses ɗin asibitin suka zo tarban su. Da yake yanzu zamani ya kawo mu komai ta waya ake yi, ta email Lamiɗo ya yi magana da asibitin tun bayan da ya yi bincike kan asibitin kuɗi mai kyau a ƙasar in da Ummu Salma za ta haihu da ikon Allah da kuma ƙwarewarsu. Ta Email ɗin ya tura musu duka bayanan Ummu Salma sannan suka ba shi lambar da zai dinga magana da su. hatta booking ɗin komai an gama jiran su kawai ake yi, shi ya tura musu sakon ticket ɗin su da lokacin da za su ta so da kintatan lokacin da za su sauka shi ne kafin su saukan ma suna filin jirgi suna jiran su. Tun a filin jirgin Lamiɗo ya tabbatar da Ummu Salma za ta samu kulawa na musamman. Sun taho da gadon marasa lafiya ga wheelchair bayan an ɗaura ta daga bakin jirgi zuwa motar asibitin su kuma suka bi su a motar haya har zuwa asibitin. Garin daman na larabawa ne asibitin ma yawaanci duk labarawan ne duk da akwai turawa asibitin ya haɗu haɗuwarsa ya wuce a zauna ana rubutawa Harira baki kawai take saki tana yi ma Allah kirari. Mami kuma daman ta saba zuwa ta san Egpyt sosai suna yawan zuwa da Daddy sannan lokacin da ta haifi Islam sai da ta yi kusan wattani biyu kafin ta koma Nigeria so Egypt ba baƙo ne ba ne a wajenta. Lamiɗo ma da bai taɓa zuwa ƙasar ba shi dai daga ƙasar Malaysia sai Saudia Arabia ya taɓa zuwa haka na musamman Malaysia saboda can ya kwashe shekaru sama da huɗu yana karatu, Saudiya kuma ya je sauke farali da Umra bai san sau adadi ba. Sauran ƙasashen kuma aiki ke kai shi daga ruwa sai ruwa ba yawo suke yi a cikin gari ba amma duk da haka ba za ka gan shi ka ce masa baƙo a ƙasar ba saboda iliminsa da wayewa. Ummu Salma ma wannan ne karon ta na farko. Ita daman Umra kawai ta taɓa zuwa sanadin Daddy da Mami tana da burin zuwa Saudia ta sauke farali tun a baya ballatana yanzu da take son ta je ta roƙa ma Baffa gafara da rahama a wajen Allah. Tabbas Hajji kiran Allah ne ba rashin kuɗi ba ne ya hana ta zuwa Allah ne bai kirata ba. Suna zuwa asibitin wasu takardu ne kawai Lamiɗo ya cike maganar payment daman tun a Nigeria ya tura musu kuɗaɗen da suka caje su a ƙiyasi dai Ummu Salma za ta iya yin wata ɗaya ƙarƙashin kulawarsu tunda EDD ɗinta tara ga watan November ne sun kuma sauka a asibitin 31 ga watan actober. A wani ƙayattacen ɗaki na musamman aka ware ma Ummu Salma ga girma ga shi abu abin da babu a cikin ɗakin nan kamar irin ta zo shaƙawata ba haihuwa ba. Babu abin da za ta nema ta rasa. Sannan kafin a shigar da ita sai da suka sanya mata kayan su na asibitin wani fari mai layi layin baƙi, riga da wando masu sakewa ba su kama ta ba, har da irin hulan su na asibitin da takalminsu ga blanket komai anan suka samu Kuma ba su buƙatar masu jinya su kwana su za su dinga kula da majinyaci sai dai daga safiya zuwa yamma. Har sun fara duba lafiyarta an yi ma gwaje gwaje domin a fahimci matakin da take har scan na cikin ta sun sake yi mata duk da an turo bayanan ta suna bukatar ganin komai da kansu sun yi tsarin cewa har abincinta su za su tsara da lokacin cin ta lokacin da za yi dinga barci saboda jininta ya yi sama akwai buƙatar ya sauka kafin haihuwar ta zo. Daga ganin wannan asibitin za ka san naira ce ta yi kuka naira mai suna naira miliyoyi da ba za su ƙirgi ba. Lamiɗo da Mami har da Harira suna asibitin sai gabda azahar suka tafi Hotel ɗin dake kusa da asibitin mai suna NADA HOTEL 3star hotel ne mai kyau hadaɗɗe mai hawa hawa ba iyaka. Lamiɗo ya yi musu booking ɗin ɗakuna nan za su zauna sai dai za su dinga zuwa lokacin da asibitin da tsara suna duba Ummu Salma shi yana gama abubuwan da zai yi yana so ya koma saboda ranar friday zai koma bakin aikin shi. Received at 18:55 Rabi'atu reacted with ❤ [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ko da suka baro sun ba ta abinci sun yi mata allura ta fara barci. Akwai wayarta a hannunta za ta dinga amfani da ita amma sun ce ba za su bari ana damunta da hayaniya ba a takaice dai tana under control ɗin su ne. Suma an kawo musu abinci mai rai da lafiya bayan sun yi wanka sun yi salla suka ci suka kwanta suna barcin da ba su samu damar yi a jirgi ba. Lamiɗo ya so ya kama ma Mami ɗakin ta ita kaɗai amma ta ce ba ta son zama ita kaɗai ya kama musu ita da Harira shi kuma umarninta saman muradinsa ne sai ya yi mata yadda take so. Mai martaba ya daɗe yana faɗa masa Mami ta fi kowa son shi ba ta dai nunawa ne sannan wani lokacin in suna hira da Ummu Salama in ya ce Mami ta fi son ta sai ta ce kara take yi maka. In ya ce Ammah ta fi son shi sai Ummu Salama ta ce kara take yi maka amma ba wacce za ta fi uwa son abin da ta haifa. Ya tabbatar da haka yanzu da suke samun kusanci ya ɗauka a baya duk wani abu da ya shafe sa ne ba ta so har da shi ma sai daga baya ya fahinci tabbas kara take yi ma Ammah da Baffa sai wata darajarta da ƙimarta suka ƙaru wajensa sannan kwanaki ya ji wani wa'azi malamin ya ce ko a bakin kura kake to wajibi ne ka yi ma mahaifiyarka biyayya sai ya zauna ya yi tunanin tun tasowar sa wani biyayya ya yi ma Mami a matsayinta na uwa a gare shi? Ya kasa tunawa shi ya sa yanzu ya gyara biyayya yake yi mata duk da ko a baya yana yi mata biyayya shaƙuwa ce dai a tsakanin su sannan ba sa shiga rayuwar juna amma dalilin Ummu Salma ya sa yanzu zai iya doguwar magana da Mami bai sani ba itama za ta zauna ta yi masa mganganu ba ta sani ba, a hankali dai tazaran rashin shaƙuwar dake tsakaninsu tana ta haɗewa ba tare da sani ba. Ba za su koma asibiti ba sai da yamma. Yanzu ɗin ma Mami ce ta baro ɗakin su zuwa na shi ta ce ta gaji da kwanciya. Shi kuma daman bai iya barcin ba yana dai kwance yana hutawa bayan ya gama waya da Bilkisu ya sanar da ita sun sauka tunda suna sauka ƙasar ya siya sabon layi ya fara amfani da shi. Mamin ce ma ta tuna masa ya kira su Ammah ya faɗa musu sun sauka sai ya kira har ya ba ma Mami suka yi magana tana faɗa mata asibitin suna da ƙwarewa da ikon Allah Ummu Salma wannan karon za ta haihu da kanta. Bayan sun gama waya da Ammah sun jima suna hira da Mami tana faɗa masa yadda yanayin asibitin da ya nema sun birge ta kuma daga gani za a samu abin da ake so. Tana faɗa masa itama asibitin da ta haifi Islam mai kyau ne sosai sun kula da ita sosai nan take ta shiga nuna masa hotunan a wayan ta, ga lokacin da suka yi hotuna da likitocin larabawa ga Islam tana jaririya gwanin sha'awa Mami ba ruwanta duk hiran da ta zo bakin ta faɗa masa take yi, har tana ce masa ta sha wahala an har kusa yi mata C.S Allah ya taimaka ta haihu da kanta. Shekaru sama da ashirin kafin ta haifi Islam dole ta ji jiki. Wani maganarta na ta ya yi ɗan mirmishi wani kuma ya jinjina kai. Shi dai ba hira yake yi mata ba domin bai iya ba ita ce ke hiranta yana amsa mata in buƙatar hakan ya ta so, to sanin halin shi itama ba ta damu ba. In hira ta yi mata daɗi har dafa kafaɗan shi take yi. Akwai wani suna da take kiran shi yana yi masa daɗi sosai. Muhammadu ta ke ce masa, ta kan jima ba ta kira shi da Lamiɗo ba. Ko ta ce Ɗan Ammah amma in ta kira shi Muhammadu sai zuciyarsa ta yi masa ɗumi. Lokacin salla la'asar ne ya yi, ya sa hiran ta su ta katse. Ta koma ɗaki shi kuma ya shirya ya fita masallaci akwai masallaci a cikin hotel ɗin tunda duk musulmai ne. Sai dare suka koma asibiti suka sake duba Ummu Salma ba su daɗe ba mintina talatin ne kawai suka ba su, suka ce za ta ci abinci ta kwanta. Tana ji tana gani suka tafi suka barta har kuka sai da ta yi. Kewa duk ya ishe ta ga kaßaici ita kaɗai ba wanda ta sani sai baƙin fuskokin Nurses da likitoci larabawa. Ga shi duk a tsorace take gani take yi kamar wannan karon ma haihuwa za ta zo da targaɗa kamar ta baya. Sannan ba ta so a sake yankata ta fi so ta haihu da kanta wannan karon yawan yin C.S ga mace na rage mata karfin jiki. Received at 18:55 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby lokacin ma ya san Yariman ya zo garin ko shi Mai martaba bai yi zencen da shi ba Fulani ce kawai ta sani kuma ba ta faɗa ma kowa ba. Sannan a daran ya sake haɗa musu wata ganawar ta sirri da malamai da masu iko a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba. Suma tattaunawar ta su ta ɗau tsawon awanni huɗu kafin Mai martaba ya sallame su. Washegari kuma Mai martaba ya karbi baƙuncin Baban Alkalin kotun musulunci na jihar Katsina Qadi, shima ɗin tattaunawa ce ta sirri, bayan tafiyar shi ya gana da Limamin jumma'a na masallacin cikin fada a daran kuma ya gana da sauran hakimai da dattawan fada. Daga lokacin Masarautar aka fara yaɗa jita jitan magana duk da ba wanda ya san asalin abin da Mai martaba yake son aiwatarwa amma maganganun nata ta shi tunda ba a taɓa ganin Mai martaba ya yi irin waɗanan ganawar cikin sirri haka ba, ba kuma wanda ya sani waɗanda suka sani ɗin kuma ba su da ikon cewa komai. Manyan majalisar zaɓen fada da suka yi ta shiga suna fita su ne su Waziri, Madaki, Galadima da Yarima Lamiɗo, sai Sallama musamman mai sharia da zuwansa fada wajen su uku. Kuma ga shi ba wani magana da ta fito daga fada daga yawun Mai martaba amma mganganu na ta tashi. Gimbiya Shahida ta so tambayan Mai martaba abin da ke faruwa ba ta samu fuska ba, ba ma ita ba duka sauran mata ya ce su jira lokaci kawai. Gimbiya Hadiza har ta kira Bilkisu ta faɗa mata wani abu zai faru Yarima ya zo Daura kuma Mai martaba na ta ganawar Sirri da Manyan wakilan fada. Ga shi daman Bilkisun ba ta samun shi a waya har ta shaƙa da kishin ya tafi can wajen Ummu Salma ya manta da ita ashe yana Daura, kuma bai faɗa mata zai zo Daura ba. "Ya Hadiza me ke faruwa ne? Bana samun wayar Lamiɗo wajen kwana uku kenan? "Ba za ki same shi ba, ba shi da lokaci ana ta tunanin ko sabon Sarauta Mai martaba zai yi masa" "Akwai Sarautan da ta fi Yarima ne? Gimbiya Hadiza ta ce" Ko Chiroma zai yi masa, kin san Sarautar Yarima ba dole sai wanda zai gaji Sarki ba ita kuma Sarautar Chiroma magajin Sarki ne kuma babban ɗan sarki ake ba ma wannan Sarautar na fi tunanin wataƙila tunda Mai martaba na son ya gaje shi bayan ba shi shi yasa ya yanke shawaran yi masa wannan sarautar yanzu." Bilkisu ta gamsu kamar yadda itama Gimbiya Hadiza take tunani. Ba ma su ba kowa tunanin da yake yi kenan. Ba wanda ya yi tunanin Mai martaba zai iya tsallake gurbabe masu girma har ya kai matakin da ya yanke a yanzu. * Ummu Salma ma daga nan Egypt hankalinta duk a tashe tunda Lamiɗo ya tafi bai kira ta ba, itama ta kira shi ba ta same shi ba. Hankalinta ya ɗan kwanta ne da ta kira Fulani ta ba ta tabbacin yana lafiya har a lokacin yana Daura wasu azurori ne masu girma suka sha masa kai, shi ya sa ta ɗan kwantar da hankalinta. Amma mamakinta kwana uku huɗu a ce Hamma bai kira ta ba, ko Daura ya je ba ya kwana bai neme ta ba in ma an kwana ba za a yini ba. Amma har kwana huɗu shuru babu wayarsa sannan abin da ya ba ta mamaki daɗewarsa a Daura ahalin ya ba ta tabbacin in ya daɗe ne ya yi kwana biyu. Ga shi Fulani ta ce wasu uzirori sun riƙe shi, da ta kasa gane wasu irin uzirori take magana, suma can Adamawa suna video call ko vioce call suke yi da su ko ta wayar Baɗɗo ko ta wayar Hamma Saddam suma ɗin sun ce ba su yi magana da Lamiɗon ba. Har Ammah ta ce tun saukarsu da suka yi magana ta kira wayarsa a kashe a bakin Mami ma take jin Mai martaba ne ya kira shi yana can Daura. Babu wanda ya yi tunanin a halin da Lamiɗo yake ciki ba ya ma tunanin su, tunanin tarin wasu nauyin alummar dake ƙoƙarin rataya a wuyansa yake yi. Waya ma ya manta da ita. Barci sai dai ɓarawo kawai ke iya fizgan shi. Yana cikin damuwar, kuma dole ne ya cika Umarnin Sarki ko yana ko ba ya so. Mami ce dake tare da Ummu Salma ke kwantar mata da hankali. Domin ba a so kuma ta shiga damuwa har jininta ya ɗaga. Hankalinta ya kwanta tunda yana can Daura ta tabbatar yana lafiya amma nemanta ne da bai yi ba zuciyarta ba daɗi. Received at 18:55 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ranar talata da suka cika sati ɗaya a kasar na Egypt, ya kama kwanan Lamiɗo biyar da tafiya kenan cikin dare 8 ga watan November misalin uku na dare Ummu Salma ta haihu, Alhamdulillah kawai za ta ce da godiya ga Allah. Kamar wasa tana cikin barci naguda ya tashe ta daman akwai wata na'ura ta emergency dake gefenta an faɗa mata in wani abu ya taso ta danna wannan na'uran zai yi ja, ya yi ƙara domin a san tana buƙatar taimako. Da ta ji ciwon baya ga maranta ya riƙe ta so ta miƙe ta kasa da wani ciwon maran ya tirniƙeta ba ta san lokacin da ta matsa abin nan ba ya yi ƙara cikin lokaci sai ga likitoci da Nurses sun cika ɗakin da take ana gwadata aka ce haihuwa ce ta zo gab. Ba ta taɓa tunanin za ta iya haihuwa da kanta cikin lokaci haka ba. Da fara naƙudarta da haihuwarta mintina talatin ne ta haifi ɗiyarta mace kyakyawa ƙatuwa da ita kamar Lamiɗo ya yi kaki, kuma cikin ikon Allah ko ƙaruwa ba ta yi ba. Cikin awa ɗaya nurses suka gyara ta, tare da Baby gabaɗaya ɗakin ya dawo fes kamar ba a haihu ba. An yi ma jinjirar wanka an saka maka kayan sanyi masu kyau daman kayan haihuwan da suka taho da shi suna cikin drowers ɗin cikin ɗakin. Nan da aka kawo ƙaramin gado na jariri aka saka ta a ciki sai wuntsila kafafu take yi irin na yara amma kafin nan sai da aka ba ma Ummu Salma jaririyar ta rumgume ta ji ɗuminta tana hawayen farinciki. Ta ba ma Nurses ɗin wayarta suka ɗauke su hotuna sannan suka yi ma jaririyar hotuna itama Ko kafin Asuba har ta koma barci, kamar ba ta haihu ba. Ummu Salma ta tabbatar wannan asibitin wajen kulawa da ba ta ki duk haihuwanta ta haihu anan ba, ga shi jininta bai hau ba sun ce 120 sannan su za su yi maka komai kamar kana ɗakin mahaifiyarka. Ga abinci mai rai da lafiya da zai ingata lafiyarka. Karfe shidda na safe ta tashi barci Nurses suka tashe ta, ta yi wanka ta gasa jikinta sosai suna faɗa mata kar ta yi amfani da ruwa mai zafi sosai saboda BP. ta ce musu to amma ba ta sauraresu ba, ba za ta biye musu ba gwara ta gasa jikinta. Da harshen turanci suke magana tana ji sai dai mayarwa ne take amsa musu da iya abin da ta iya kuma suna ganewa A karo na farko Ummu Salma ta ji ra'ayin son komawa makaranta domin maganar Hamma Kabiru gaskiya ne ilimi ginshiƙi ne na rayuwa akwai in da za ka je ka ga ana yi babu kai. In ta ga yadda Mami ke turanci sai ta ji ta burgeta har ta ji wataƙila ta sauya ra'ayi ta koma makaranta. Sun yi ma jinjirar wanka an sauya mata kaya ba su damu da nono ba har sun fara ba ta madara. Ita ma daman ruwan nonon bai zo ba har matsawa ta yi sai dai kaɗan kaɗan, Itama sun ba ta abin kari mai kyau ta karya sannan ta karɓi jinjirar ta rumgume tana yi ma Allah godiya. Bayan fitan Nurses ɗin ne ta samu damar kunna data, Lamiɗo ta so ta fara kira amma baya online sai kawai ta tura masa hoton jinjirar. Sannan kira Mami domin ta ga tana online. Video call ne Mami na ɗauka sai ganin Ummu Salma ta yi da jinjira a hanunta baki ta saki. "Me zan gani? Daughter kin haihu ne? "Mami na haihu, abin mamaki Mami na haihu." Ummu Salma ta faɗa tana washe baki idanuwanta sun cika da ƙwalla. Mami ta yi kabbara tana jera Hamdala Ummu Salma na ji Mami na ƙwalama Harira kira sai kuma ta katse wayar. Baɗɗo ta so ta kira sai ta ga ba ta online sai kawai ta tura mata hoton su da aka yi mata da jinjirar lokacin da ta haife ta. "Alhamdulillah ɗiyarki ta zo duniya jiya da daddare" Ta so ta tura a gidan Baffa da Ammah kunya ya sa ba ta tura ba. Kafin ta kashe datar sai da ta koma ta kira lambar Hamma shuru ba ta same shi ba tana farikciki amma ya ɗan samu nakasu, tunda ba Hamma a kusa da ita. Ta haihu amma bai sani ba ta kira shi kuma ba ta same shi ba. Hoton jinjirar ta tura ma Gimbiya Shahida sannan ba ta kashe datar ba ta koma ta kwanta ba kawai ta yi zaune tana ta kallon jaririyar tana ta barcinta hankalinta kwance. Mami da Harira suka baro hotel suka hau Taxi zuwa cikin asibiti. Suna cikin tafiya ne Mami ta shiga instagram saƙon da ta ci karo da shi yana yawo ne ya firgita ta. Received at 18:55 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby BBC HAUSA suka fara fitar da sanarwan sannan sauran gidan jaridu suka fitar tare da sauran mutane suna ta sawa. Hannunta na rawa ta fita ta shiga goggle ta yi searching Masarautar Daura sai ga labarin ya fito, ta zaro ido cikin mamaki. "Kai.." Ta faɗa da ƙarfi har Harira na tambayanta ko lafiya ta kasa cewa komai da ta shiga wasop ta ga Hajiya Falmata ta turo mata. Sannan Hamma Kabiru ma ya turo mata. "Mami is this true? "Na kira wayar Amini a kashe" Itama abin da ta gani kenan amma ba ta da tabbacin domin ba ta san komai ba tunda kuma ga shi ana yawo da shi gaskiyan kenan. Suna isa asibitin waya a hannunta ta shiga ɗakin da Ummu Salma take suka same ta ga jaririyar kwance gefenta ga kuma wayarta a hannunta. Suna shigowa ta ɗago tana kallon su. "Mami." Ta kira ta da ƙarfi. "Mami wai Hamma ya zama SARKI? Ummu Salma ta faɗa cikin ƙarajin da muryanta cikin ruɗewa Mami ta ƙarisa kusa da ita Harira kuma ta sandare a tsaye. "Mami da gaske ne? "Nima haka na gani." Mami ta amsa mata tana jin wani abu a ƙasan zuciyanta da ta rasa ko mene ne. Hannu ta miƙa ta ɗauki jinjirar ta rumgume kawai ta yi tsaye. Ummu Salma ta ce"Mami BBC suka sanar ga sauran gidan jaridu nan ma na fitar sanarwan Mami ga shi su Hamma Kabiru a group ma suna mganar" Take faɗa cikin ruɗewa sannan ta fara karanta abin da BBC HAUSA suka fitar da hoton Mai martaba. "SARKIN DAURA ALHAJI DR NASIRU MUHAMMAD SHITU, YA YI MURABUS DAGA KAN ƘARAGARSA A DARAN JIYA SANNAN YA ƊORA BABBAN ƊANSA MUHAMMAD NASIRU MUHAMMAD A MADADINSA." Duk in da ka shiga labarin dake yawo kenan bisa laka'ari da cewa ba a cika samun Sarki ya yi murabus ya gadar ma wani ɗansa Sarauta ba an fi dai samun Sarki ya rasu a fafata a zaɓen majilisar fada har a samu wanda zai gaje shi sama da shekari hamsin a tarihin Masarautar Daura haka bai taɓa faruwa ba shi ya sa ya zama sabon abu. Ummu Saalma sai hawayen farinciki daman shi ya sa aka ji Hamma Shuru shi kaɗai ya san halin da yake ciki. "Allah sarki Hamma ba ya son sha'anin mulki. Daman abin da muke so ba shi Allah ke bamu ba, sai wanda ba mu saka rai da samun sa ba." Sai hawaye shar sannan ta cigaba da faɗin. "Ko ya zai ji a yanzu? Shi kawai take tunani ga shi ba ta kusa da shi da ace tana kusa ma ba za ta samu ganin shi ba. Yanzu ba Yarima ba ne Sarkin Daura ne. "Allah ya ta shi riƙo. Allah ya tsare shi." Mami ta faɗa duk koƙarinta na kar ta yi hawaye sai da ta yi ta tuna maganar Baffa in tana cewa ta tsani abin da ya shafi Sarauta "Ki kika sani ko ɗanki ya zama Sarki watarana Fatima? Ko ba na raye hakan ta faru ki yi masa fatan alheri Ubangiji ya kaddara haka ki daina jayayya da kaddara " Ta fashe da kuka tana rumgume Jaririyar Hannunta. "Allah ya gafarta maka Baffa." "Kin zo duniyar a ranar da mahaifinki ya zama Sarki. Barka da zuwa SARAUNIYA DAURAMA." "ALLAH ga bawan ka nan Muhammadu ya zama shugaban wasu al'umma a yau, Allah ka ta ya shi riƙo ka jiɓanci lamuran shi, ka kiyayesa ka taya shi kar ka barshi shi kaɗai Ubangiji ka taya sa riƙo." Ummu Salma da Harira suna taya ta da amsawa da Amin a tare wayoyin su suka ɗau kara Video call ne ita Ummu Salma Baɗɗo ce ke kiranta ita kuma Mami Hamma Saddam. Jaririyar Mami ta miƙa ma Harira ita kuma ta ɗauki wayar sai ga Ammah da Hamma Saddam da Hamma Abdulrahim, har da su Hamma Abdulrraham daga gani daga salla asuba suka zarto gida kowanne da Jallabiya. "Fatima Lamiɗo ya zama Sarki." Ammah ta faɗa cikin wani karaɗi a muryanta. Mami ta ce haka ta gani Hamma Saddam ya yi jinjina. 'Sannu Fulanin Daura an gaishe ki." Aka kwashe da dariya. Ammah na hawaye tana addua'n Allah ya ta ya Lamiɗo riko. Su Hamma Saddam na ta murna da ihu sannan ga murnan Auta ta sauka an haskota tana videa call da Baɗɗo wacce ke ta murna da tsalle. "Ranki ya daɗe da gaske dai kin zama Sarauniyar Daurama." "Kin iya haihuwa tarihi ba zai manta da wannan haihuwar taki ba Sis na." Ga murnan haihuwa ga ta Sarauta. Ummu Salma ta yi magana da su Ammah kowa sai da ya kira su video call har Hamma Kabiru ya ce bai samu Hamma Lamiɗo a waya ba. Received at 18:55 Bilkisu reacted with ❤ [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Mu ma nan ba mu same shi ba tun tafiyan shi. Yanzu ɗin ma ba lalle a same shi a yanzu ba mu jira ya neme mu." Haka Mami ta faɗa, dole kam a jira jin ta bakinsa. Yayyenta duk sun mata barka suna faɗin ta iya haihuwa. Kafin ka ce me gabaɗaya social media da dukkan wani platform sun saka labarin abin da ya faru a Daura. Sannan hotunan Lamiɗo sun fara yawo tare da cikakken tarihinsa wasu hotunan da naɗi a jikinsa irin wanda ake yi masa da salla ne sai wasu hotunan kuma yana cikin Uniform ɗinsa na tukin jirgin ruwa. "MUHAMMAD NASIRU MUHAMMAD LAMIƊO, SHI NE ƊA NA FARI GA MAI MARTABA SARKIN DAURA MAHAIFIYAR SA HAJIYA FATIMA BABA, BA YAR MASARAUTA BA CE SUN RABU TUN KAFIN TSOHON SARKI MAI MURABUS YA HAU KAN KARAGA. MUHAMMAD LAMIƊO MATASHI NE ƊAN KIMANIN SHEKARU ARBA'IN A DUNIYA YA YI KARATUNSA NA TUKIN JIRGIN RUWA A ƘASAR MALAYSIA YANZU HAKA MA'AIKACI NE A KAMFAMIN CHEVRON NIGERIA LIMITED A MATSAYIN ƊAYA DAGA CIKIN MARINE, MA'ANA CAPTAIN ƊIN SU MASU JIGILAN JIRAGENSU ZUWA ƘASASHEN WAJE YANA DA MATAR AURE GUDA BIYU DA YARA BIYU, MATARSA TA FARKO HAJIYA BILKISU USMAN BAYERO ƊIYAR SARKI KANO USMAN BAYERO." Rubutun dake ta yawo kenan tare da hotunan Lamiɗo nan da nan yan'uwa suka fara status na ta ya murna ga Lamiɗo da kuma na samun ƙaruwa. Gimbiya Shahida ta kira Ummu Salma a waya sun yi magana ta ce Fada ta cika saboda murabus ɗin mai Mai martaba a maganar da take yi ma tuni Lamiɗo na fada a matsayin Sarkin Daura. Ta ce su kan su ba su san hukunci da Mai martaba ya yanke ba kenan. Ana ta yawo da maganar ko wata Sarautar zai canza ma Yarima ashe Murabus zai yi suma tun jiya ba su gan shi ba murabus ɗin cikin dare aka yi shi a daran kuma aka naɗa Lamiɗo sai dai Kawai aka wayi gari da sanarwaan amma zuwa yamma Mai martaba zau gana da yan jaridu da gidajen talabijin zai yi bayani ga al'ummar Daura da sauran mutane. Ta kwantar ma da Umma Salma hankali da cewa ta kwantar da hankalinta ta samu lafiya ta kula da kanta da jaririyarta. Har zuwa nan da kura ta lafa yanzu dai Lamiɗo ba zai samu kan shi ba gaskiya. Kuma gaskiya ta faɗa tabbas sai nan da lokaci kaɗan maganar haihuwa ma bai sani ba domin ba a faɗa masa ba waya ce kuma ba ta tare da shi. Kamar yadda Ummu Salma ta ga abin daga sama haka Bilkisu ta ji, ita tana barci daga cikin ahalin gidansu aka samu wani yayanta ya kira ta ya faɗa mata tana hawa social media ta samu tabbaci jiki na rawa ta kira Gimbiya Hadiza ta ƙara samu tabbaci. Ta tabbatar mata da cewa da suma haka suka wayi gari amma kamar Fulani da duka yan'uwan Mai martaba mai murabus sun san da faruwar komai. Bilkisu ta daka tsalle ta dira saman gado ta fita falo daga ita sai rigar barci ta dinga kiran Sabuwa sai ga su a rikice sun ɗauka wani abu ne ya faru sai ga shi tana faɗa musu Yarima ya zama Sarki bayan ta rumgume Sabuwa. Su Debora da Anitha suka rumgume juna suna yi ma Bilkisu congratulations yara ma ihun murnanta ya tashe su ai sai ta shiga ɗaga su ɗayan bayan ɗaya tana juyi da su. Har da Hanan tana faɗa musu Papa is now a king of Daura duk da ba su wani gane ba suna ta murna. Bilkisu kai ya yi girma ta zama matar Sarki ta manta da batun wasu kishiya murna kawai take yi haka ta kira Umman kano tana murna ta ce suma sun samu labari. Ta ce sai ta yi ta ma Allah godiya tare da addu'an Allah ya taya mijinta riƙo. Sai bayan sun gama wayar ne ta lura da status ɗin Adda Safina da hoton jaririya ta fara cin karo. "Welcome to the world Princess. Kin iya zuwa duniya. Ranar da muke murna Babanki ya zama Sarkin Daura." Ko ba a fada ba wannan jaririyar ɗiyar Umma Salma ce ta haihu kenan? Ta san da Lamiɗo na cikin sukuni zai faɗa mata yanzu ko a duniya ta ji ta ce Allah y raya ba ta damu ba. Ita yanzu ba kishi ba ne a gabanta she is now Gimbiya Bilkisu Gimbiya Bilkisu matar Sarkin Daura. Ta zauna ta saka hoton Lamiɗo ta yi dogon rubutu na murna ta yi status dangi da abokan arzuƙa ana ta taya ta murna da barka da arziki. Received at 18:55 [6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ranar har busa ta yi connecting ta wayarta daga speaker ta fara juyi tana kaɗa kai ranar farinciki ce wayoyin ko da ta amsa na mutane ba ta san adadi ba har da su Sofia duk sun yi waya suna ta ya ta murna ko da hukuncin bai yi ma wasu daɗi ba hukuncin ya riga ya zartu ba yadda aka iya. Da yamma misalin shidda na yammaci aka fitar da maganar da Mai martaba mai Murabus ya yi da manema labarai aka watsa a duniya. "Ni Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu, a jiya 8 ga watan November wanda ya yi daidai da shekara ta dubu biyu da ashirin da biyar. Na yi murabus daga kan ƙaragar mulkin garin Daura na gadar ma babban ɗana Muhammad Lamiɗo ɗan Nasiru jikan Shitu, a kuma jiyan ya fara zama wakilin ku sarkin ku. Dalilina shi ne ina cikin jinya ina buƙatar hutawa domin inganta lafiyata. Bayan zama da masu ruwa da tsaki na fada majalisar zaɓe tare da malamai, Hakimai masu Sarauta alƙalai tare da limaman mu, sai kuma dattawan da hikaman mu a karshe suka aminta da tsarina bayan duba da cancantar wanda na kawo a matsayin wanda zai gaje ni. Alhamdululillah Allah na gode maka ina bayar da haƙuri duka al'ummata na Garin Daura da kewayenta. Da wanda ya ji daɗi da wanda bai ji daɗi ba, ku sani nima na ji daɗin tsawon shekarun da na kwashe ina mulki tare da ku, da wannan damar nake neman afuwarku na san a shugabancina ba zai yuyu na faranta ma kowa ba, ku yi mini afuwa in da na kuskure ina fatan Ubangiji ya tsare Masarautar Daura. Allah ya kare Jihar Katsina da Al'ummarta gabaɗaya. Ina mai yi muku albishir ɗin cewa za ku ji daɗin mulki Sarkin ku na Yanzu Muhammad Lamiɗo fiye da mulkina. Ubangiji ya taimake mu ya taimaki kasarmu Nigeria gabaɗaya ya ɗaga darajar Masarautun gargarjiya da addinin musulunci gabaɗaya.." Video ne ga Mai martaba zaune ya sha rawani, ana ta yawo da shi da fatan Allah ya ba sa lafiya wasu jama'ar Daura har da masu kuka domin sun san Tsohon Sarkin adali ne akwai masu cewa Saleem ne ya cancanta Hakimin Daura wasu kuma suna faɗin Yarima Lamiɗo ne ya fi cancanta kowa dai na faɗin ra'ayin shi. Sai da aka kwana biyu wannan murabus ɗin na Sarkin Daura ke trending a social media. Har kuma zuwa lokacin ba wanda ya ji daga wajen Sarki na yanzu wato Lamiɗo. Sai ranar ta uku ne cikin dare misalin uku da wani abu Lamiɗo ko na ce Mai martaba Sarkin Daura na yanzu ya kunna wayarsa ya kira Aminin shi a waya. Maganar haihuwar Ummu Salma sai jiya ya ji a bakin Fulani sarkaƙiyar da ya shiga ya sa ya manta da wata waya. Amma kuma duk damuwar da yake ciki bai manta da Ummu Salma dake can tsakanin rayuwa da mutuwa ba. Daga saukarsa a garin Daura zuwa yau ɗin nan rayuwarsa ta juya daga sama zuwa ƙasa nw. Juyin da bai taɓa tunani ba tun yana ganin wasa har sai ga shi ya tabbata amna yana gani kamar a mafarki ne, kamar in ya buɗe ido zai ga komai bai faru ba. Tun a daran da aka masa naɗin Sarautar Sarkin Daura bai sake cikakken barci ba. Ɓata dare yake yi cikin tunani da fargaba, ba zai iya ba ya faɗa ma Mai martaba amma bai saurare shi ba. Yanzu ɗin ma kafin ya kira Kabiru sai da ya tura ma kamfanin su takardaan ajiye aiki ya fi mintina talatin yana juya saƙon kafin ya tura musu ta email ɗin su. Shike nan yanzu ya yi sallama da mafarkinsa. Yana ji yana gani kaddara ta sake juya masa sabuwar rayuwa Da gaske ne shi ne Sarkin Daura an yi masa naɗi Mai martaba da iyalansa ma suna shirin barin fada ne zuwa wani gidansa dake cikin garin Daura shiryen shiryen gyara Masarautar ake yi tare da saka lokacin bikin naɗi yanzu shi ne ke zama a kan karagar mulki a fada, shi ake yi ma biyayya shi ne umarninsa ke saman na kowa. Allah mai iko da gagara misali. Shi ne ke shiga irin ta Sarki, alhalin Sarki na raye bai mutu ba. Ba zai iya magana da kowa ba a lokacin ba sai Aminin shi, yana kiran shi kuma har ta kusa katsewa ya ɗaga saboda shima gani yake yi kamar wasa. "Amini." "Kai ne? Sai kawai Lamiɗo ya yi gyaran murya Kabiru sai ya ji ya yi masa ƙwarjini duk da ba ganinsa yake yi ba. "Allah ya taimake ka Allah ya ƙara lafiya. Allah ya taya ka riƙo." "Amini." "Na'am Ranka ya daɗe." Received at 18:55 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Na zama Sarkin Daura amma kafin na zama haka ni ne dai Muhammad Lamiɗo aminin ka." Sai ya ɗan ja fasali kafin ya cigaba da faɗin. "So ka yi magana da ni kamar yadda muka saba." "To." Kabiru ya amsa domin yana ganin kamar a mafarki. Aminin shi ya zama sarki falo ya fita kar ya tayar da Safina dake barci. Duk da akwai yuyiwar faruwar haka amma komai ya faru a cikin lokacin da ba wanda ya yi tunanin faruwarsa. "Ummu Salama ta haihu, ka nemi visa da sauri don Allah ka je ka duba mini su, ka yi ma yarinya huɗuba." "In sha Allahu." "Da wani suna? "Ka tambayi Ummu Salama duk sunan da ta zaɓa ka yi mata huɗuba da shi." "In sha Allahu." Kabiru ya amsa masa kamar baƙin juna sai suka yi shuru. "Kana dai lafiya ko? Muryanka ta yi kama da wanda ya daɗe bai sami barci ba" "Lafiya lau." Kawai ya iya cewa duk abin da zai faɗa ba za a gane ba, bai kuma san me zai ce ba domin bai iya bayani ba. "In ka yi waya da Ammah ka ce ina gaisheta zan kirata in na samu sarari." Kabiru ya amsa da zai faɗa mata daga nan suka yi sallama. Sarauta gaskiya ce a muryan Lamiɗo har ta canza yana magana cikin natsuwa da ƙasaita duk da daman halin shi ne amma yau na dabam ne. Kafin ya kwanta ya fara neman visa ta online tunda yanzu komai a sauƙake ne ko wani kamfani suna da handel a social media xa ka iya samun su ko ta email. A daran Lamiɗo ya kunna data sakonni wasu na ture wasu bai buɗe na kowa ba sai na Ummu Salma ta turo masa hoton jaririyar ya buɗe ya gani. Sai da zuciyarsa ta yi haske daga wani shashe. Ya rasa me zai ce ma Ummu Salma ya so ya kira ta sai kuma ya kasa. "Thank you Ummu Salama. Thank you." Haka kawai ya iya rubuta mata. Sai saƙon Bilkisu na gayyar sticker da emojin murna da dogon magana da turanci na ta ya shi murna. "Bilkisu" "I will call you later." Abin da kawai ya ce mata kenan yana buƙatar natsuwa. Yana bukatar lokacin da zai karɓi wannan sabuwar rayuwar tashi tukunna kafin abubuwa su daidaita. *Janafty* Received at 18:55 Muhammad reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby MASARAUTAR DAURA. Har yau da kimanin kwana biyar kenan da tsohon Sarki Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu ya yi murabus daga ƙaragan mulki ya ɗora ɗan shi Muhammad Lamiɗo Al'ummar garinn Daura ba su daina cece-kuce ba. Wasu kuma suna ganin abin kamar a mafarki domin abu ne da ya faru ba tare da shiri ko barin wata alama ba. Wasu kuna suna tunanin rashin cancantar Lamiɗo wasu kuma tsohon Sarki suke so suna ganin a shekarunsa bai dace ya yi murabus ba, duk da ya faɗi dalilinsa ai suna ganin jinyar tunda ba ta kwantar da shi ba, bai kamata ya yi saurin yin murabus ba. Wasu kuma suna faɗin dama Hakiman Daura Saleem ya ɗaura a ganin su, shi ne ya fi kowa cancanta da wannan karagan tunda yawancin abubuwan fada da shi ake gudanarwa sannan ya sha wakiltan Mai martaba tsohon Sarki a wasu tarurruka masu muhimmanci an fi sanin shi tunda ana ganin shi saɓanin Lamiɗo da sai salla salla, amma in dai yana gari matasan garin Daura suna shaida zuwan shi saboda alherin shi. Sauran kuma ko maganarsu ba a yi. Yazeed da Sagir gani ake yi ana babbakan giwa wa zai tuna da zomo amma duk da haka a cikin mutane ba za a rasa masu kawo su a matsayin suma waɗanda suka cancanta ba ko'ina dai ceceku ce yaƙi karewa amma kuma ba abin da zai sauya wannan kaddara tun a ranar da Sarki ya yi murabus Al'umma Daura suka bar ƙarƙashinsa suka koma ƙarƙashin jagorancin Lamiɗo Sarki na yanzu. A cikin Masarauta ma kowa ka gani lamarin bai gama kama jikinsa ba. Nan ma mganganu suna ta tashi da cewa Sarki ya yi gaggawa ko na ce tsohon Sarki sannan ya yi shammata. Duk da duk wanda yake tare da Mai martaba tsohon Sarki kowa zai iya shaida Lamiɗo yake so ya gaje shi amma ba wanda ya taɓa tunanin da ran tsohon Sarki hakan zai faru masu hangen nesa ma gani suke yi Lamiɗo ba zai yi Sarauta ba, in Sarki ya rasu ba lalle ma ya fito neman karagar ba duba da ba ya son Sarauta ko da ma ya fito suna ganin majalisar zaɓe ba za ta zaɓe shi ba. Sai ga shi komai ya faru a cikin dare ɗaya aka wayi gari da fashewar boom ɗin da kowa bai taɓa tunani ba sai ƙalilan mutanen da suke da alhakin sanin komai kafin zartarwa. Kafin kowa da Fulani tsohon Sarki ya fara tattauna shawaransa da matsayarsa ta kuma ba shi goyon baya saboda itama a suffa da hallaya ba tun yanzu ba ta daɗe da ganin cancantar Lamiɗo a matsayin wanda zai gaji karagan mulkin Mai martaba. Kuma lokaci ya yi da zai dawo gida ya rumgumi rayuwarsa hannu biyu lokacin da ya ganawar sirri da sauran yan'uwansa mata ne wasu suka nuna ba su amince ba. Kamar Hajiya Kilishi a rashin nuna ba ta amince ba dalilinta shi ne ai ba jinya mai tsanani Mai martaba yake ciki ba, a ganinta bai kamata ya yi murabus ba. Haka ma Hajiya Zaliha ta ce, sauran kuma irin su Hajiya Binta suna nuna cewa bai cancanta Lamiɗo ya yi gadon karaga ba. Me ya sani game da harkan mulki? sannan mahaifiyarsa ba yar sarki ba ce me ya sa zai mulke su! Mai martaba shi ne mahaifin Lamiɗo kuma ya cika duka sharaɗan zamowa Sarki saboda haka yana neman yardansu zai yi murabus sannan zai kai maganar wajen wakilan zaɓen Sarki, sun daɗe suna tattaunawa kafin a samu daidaito, kawai dai sun amince ne domin ba su da ta cewa tunda ba su cikin masu zartawa wannan alhakin majalisar zaɓe ne. Ko da ya kira Lamiɗo ya taho Daura ya riga ya gama shirya komai. Ya san zai ce ba ya so shi ya sa ya ce umarni ne ba neman yarda ba, bai ma tsaya masa wani jawabi ba sai dai kawai ganin shi ya yi ya gayyato Kingmakers. Majalisar zaɓe tunda ya ga haka ya san an zo bus stop, sannan ya saurari duk abin da suka tattauna suma ɗin dai wasu sun amince da tsarin Mai martaba wasu kuma ba su amince ba amma dai ya tattauna da su sannan ya kawo musu hujjojinsa masu ƙarfi ya kuma ce su je su zauna su sake nazarin komai a tsanake amma kar ya ɗau lokaci, Lamiɗo kuma ba a ba shi wata dama ba a wannan gabar jiran umarni ne kawai na shi ko ya yi magana a wannan gabar lokaci ya ƙure masa. Received at 15:16 11 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ba duka ne waɗanda ke da alhakin zaɓen Sarki suka amince da tsarin tsohon Sarki ba amma tunda majority sun amince sun ga kuma cancantar Lamiɗo. Majalisar zaɓe da Mai martaba ya fara ganawa da su, a hukumance su ke da alhakin zabe ko tsige Sarki. Ko kuma rashin lafiya mai tsanani. Kuma majalisar zaɓe ta ƙunshi manyan Hakimai guda hudu zuwa biyar. Mai sarautar Madaki, Waziri,Galadima da Chiroma ko Yarima babban yaron Sarki da sallama mai kula da ƙofar fada. Aikin su daman taruwa ne a ɓoye domin nazarin lamarin. Suna yin shawarwari kan mutumin da ya dace bisa tsarin mulki na gadon Masarautar. Su ne kuma ke gabatar da dalilai ga majalisar Sarki ya yin sauke shi ko tsige shi. Babban Alƙali kuma shi ne shugaban sharia' yawaancin shawararsa kan halascin sauke sarki ko zaɓen shi a addini ne bisa shari'ar musulunci. Sai limamin Juma'a; wannan mutumin yana da mutumci a idanuwan talakawan gari, shawararsa kan zaɓen shugaba mai adalci yana da tasiri ga al'ummar garin gabaɗaya. Sai sauran Hakimai da Dattawan suma wajibi ne a ji ta bakin su domin samun amincin talakawa. Sannan akwai alhakin amincewar Gwamnati shi ya sa Mai martaba bayan duk ya gama samun amincewar Fada da sauran masu ruwa da tsaki a safiyar da murabus ɗinsa zai fito ya ɗauki Lamiɗo suka je har gidan Gwamnati suka gana da Gwamnan Jahar Katsina tattaunawa mai tsawo bai baro gidan Gwamnatin Katsina a daran ba sai da ya samu sahalewarsa sannan Gwamna da kan shi ya ce zai yi waya ya sanar da shugaban ƙasa. Shi ya sa a daran ba tare da sanin kowa ba wakilan fada da hakimai tare da dattawan fada da majalisar Sarki haɗe da limamin fada a gaban su a ka yi komai Mai martaba tsohon Sarki ya yi murabus nan take aka maye gurbin shi da Muhammad Lamiɗo shi ya sa a wayewar gari labarin ya fita bayan tsohon sarki ya sanar ma media team ɗin shi ya ba su izinin fitar da murabus ɗin ga duniya. Matan Mai martaba mai murabus ji suka yi kamar a mafarki. Kuma ba wacce ta ji daɗi, ba wacce za ta so tana matsayin matar Sarki ta tashi daga wannan muƙamin na ta. Ko da suke ganin Mai martaba ya fi son babban ɗan shi ya gaje shi ba su taɓa tunanin da ranshi haka zai faru ba sai ga shi ya faru kuma abin ya tabbata. Gimbiya Shahida da ake ganin za ta nuna rashin jin daɗin ta ma ba ta nuna ba, tunda an fi ganin cancantar Saleem a kan karagar Mai martaba, ba ta nuna damuwa ko a fuska ba, koma akwai ba ta bayyana ba shi kan shi Saleem ɗin bai nuna bore ba, shi kan shi ya faɗa Lamiɗo ya fi shi cancanta. Gimbiya Hadiza ce ita da take da yara mata amma ba ta ji daɗi ba, tana matsayin Gimbiya matar Sarki darajanta zai yi ƙasa amma ta yi murna saboda zamowar Bilkisu cikakkiyar Gimbiya a Masarautar Daura. A bangaren Gimbiya Maimunatu ta fi jin zafi ganin ga yaranta Yazeed da Sagir, da arziƙi a garin wasu ai gwara a garin ku a garin ma na ku ma a gidan ku a gidan na ku ma ya kasance kai ne ke da alhakin komai. Maganganu dai na ta tashi kowa na faɗin albarkacin bakin shi amma babu abin da zai dawo baya bakin alƙalami ya riga da ya bushe. Ƴa'ƴan Mai martaba ƙannen Lamiɗo suma duk haka suka ji batun wasu ma a kafafen sada zumunta suka fara sanin abin da ke faruwa wasu suna cewa an yi daidai wasu suna ganin Sarki ya yi son kai ko ya yi gaggawa. Amma duk da haka sun fito group suna ta fatan alheri irin su Sakeena sun neme wayar Lamiɗo ba su samu ba amma sun tura masa saƙonnin ta ya murna. Tunda tun ranar da tsohon Sarki ya yi murabus Sarki na yanzu Muhammad Lamiɗo ya fara gudanar da sha'anin mulki. Sarki ya haɗa shi da amintattun shi na fada irin su Waziri, Shamaki da madaki ya ce su zama idanuwan Lamiɗo tare da bashi shawarwari a mulkinsa tsohon Sarki ya yi ma Lamiɗo umarnin shima ya riƙe su domin za su taimaka masa, suma kuma ya ce su ji kamar shi ne domin inganta Masarautar Daura. Amma zai iya sauya wasu miƙaman na hakimai a matsayin shi na sabon Sarki yana da damar da zai yi sabon naɗe naɗe a tsarin mulkin shi. Received at 15:16 14 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sannan tuni tsohon Sarki ya ba da umarnin a fara gyaran gidan shi dake cikin garin Daura shima babban gida ne nan za su koma shi da iyalansa da mahaifiyarsa Fulanin Daura. Gidan Sarki na yanzu kuma shima za a yi masa gyara ciki da waje domin sabon Sarki ne yanzu da iyalansa za su zauna a cikin gidan komai da ya danganci Sarauta hadimai, dogarai masu kaki duka yanzu suna ƙarƙashin mulkin sabon Sarki Muhammad Lamiɗo ne a yanzu a Daura gabaɗaya maganarsa tana sama da ta kowa har ta Tsohon sarkin gabaɗaya. Lamiɗo gani yake yi abin kamar wasa wai shi ne zaune a fada a kan kujeran Sarki yana hakimce da rawani da Alkeybba ga hakimai suna zagaye da shi, kamar a mafarki haka yake ganin faruwar komai kamar irin ya kwanta barci ya tashi ya ga ba haka ba ne. Sai dai ba mafarki ba ne duk abin da ke faruwa gaskiya ne. A daran ranar kwana na biyar da zamowarsa Sarki sun yi ganawa mai tsawo da Mai martaba a bangaren shi. Bangaren da nan da lokaci kaɗan zai zama mallakin Lamiɗo a matsayin sa na sabon Sarki. Ya yi masa batutuwa masu ratsa jiki da zuciya da suka saka Lamiɗo miƙa wuya. Ya kuma karɓi kaddaransa da hannayensa biyu. Mai martaba tsohon Sarki ya miƙa duka yardansa da yaƙininsa a kan Lamiɗo kuma yana fata ba zai ba shi kunya ba. Ya nuna masa muhimnancin miƙa wuya ga sabuwar rayuwarsa da kuma tunasar da shi irin nauyin da yahau kan shi na al'ummar mutanen Daura da ma arewancin nigeria gabaɗaya Daga karshe Mai martaba mai murabus ya yi masa fatan alheri da fatan Ubangiji ya taya shi riƙo. Sannan daga ƙarshe ya ce yana tare da shi domin neman shawara ko wani abu da ya shige masa duhu na sha'anun mulki yana nan a gefen shi. Sannan sun yi magana kan haihuwan Ummu Salma, ya ce Gimbiya ta sanar da shi an samu ƙaruwa. Ya tambayi Lamiɗo wani tsari gare shi, yanzu dai ba shi da ikon barin Fada sai komai ya natsa tukunnah. Amma zai iya tura wakili can ƙasar da Ummu Salma ta haihu tunda shi ba zai samu zuwa ba. Nan Lamiɗo ya faɗa masa tsarin shi, ya tura Kabiru shi zai isa can ƙasar Egypt domin ya yi ma jaririyar huɗuba anan gida kuma zai kira Abdullahi za a siya raguna a can Adamawa a yanka. "Hakan ya yi sosai Allah ya raya ya yi mata albarka wani suna za ku sanya mata? Mai martaba mai murabus ya tambaya. Cikin ƙanƙantar da kai, Lamiɗo ya ce" Ba mu riga mun yanke shawaran sunan ba Ranka ya daɗe." "A'a yanzu ai kai ne ranka ya daɗe." Mai martaba ya faɗa yana ɗan mirmishi. Yana zaune a ƙasan cafet Lamiɗo na gefen shi. "Allah ya yi albarka. madallah sai ka yi magana da duka matanka ku tsara lokacin da za su baro can su dawo nan. Yanzu ne nan ne muhallinsu har zuwa lokacin da Ubangiji ya iyakance." Sannan ya cigaba da faɗin daga baya za a yi taron naɗi da za a yi masa za a yi gayya tare da gangami taron taya shi murnan zamowarsa Sarkin Daura. Ya daɗe a bangaren Mai martaba har wajen sha ɗayan dare sannan ya koma bangaren shi barcin ma yanzu rabi da rabi ne yana jin sa kamar ba shi ba. Kamfaninsu sun turo masa amsar saƙon shi na ajiye aiki sun nuna rashin jin daɗin barin shi aiki tare da su, suna kuma cewa matujar yana neman ƙarin albashi ne ya zo su tattauna za su iya ƙara masa amma suna jin daɗin aiki da shi. Duk yadda yake son aikin shi amma ya rasa shi ba shi da wani zaɓi ne. Rayuwarsa kamar ƙifawan ido komai na shi ya sauya a kwanaki shidda baya shi Captain ne na jirgin ruwa amma a yau kuma shi Sarki ne, sarkin Daura mai ƙaraga. Bai samu sararin kiran kowa ba, ba ya cikin natsuwarsa. Da Kabiru kaɗai ya yi magana da asuba ma sun sake magana daman ya ce ya matsa a samu visa da wuri tunda gobe ne bakwai da haihuwa to ya kira shi ya ce Visa ta samu jirgin shi zai ɗaga daran yau ta Abuja zai isa kasar Cairo a wayewar garin gobe. Da yake kuɗi ya saki a wajen Visa yanzu kuma kasar mu in dai da kuɗi abin da ma ba zai yuyu ba yuyu yake yi. Received at 15:16Reactions: ❤ 5, 👍 2 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Bai kira Abdullahi ba saƙo ya tura masa na cewa ya tura masa kuɗi a siya raguna a yi ma jaririyar Umma Salama Shaƙika na suna, duk da tarin saƙonnin da mutane ke ta tura masa na fatan alheri bai buɗe ko ɗaya ba, har su Hamma Jibo duk sun yi masa saƙo ko zai iya duba wannan sai daga baya in hankalin shi ya kwanta wannan sabuwar rayuwar ta bi jikinsa tukunna. A ranar ma ya gana da duka wakilan fada da hakimai manya da ƙanana sannan ya gana da shugaban dogarai da magajiyar Hadimai na bangaren mata, sannan ya nemi zai gana da sarakunan ƙauyakun dake zagaye da garin Daura da Katsina gabaɗaya. Jakadiya kuma daman tana nan a matsayin jakadiyar Sarki mai zamani a yanzu kuma abin sha'awa a gefen Lamiɗo ƙanin sa ne Saleem tare suke gudanar da komai hakan kuma ya yi ma Mai martaba daɗi, ko bakomai Saleem ma zai sake taimaka masa sosai. Sabanin Yazeed da yake can ƙasar da yake karatu cikin takaici yana son mulki sosai ko daga yadda yake jin ƙansa yaro ne matashi amma yana da izza da girman kai har ya fi Sageer da yake yayan shi son mulki da izza. Mai martaba ya shammace su sosai da a ce mutuwa ya yi za a yi zaɓe sun tabbata Lamiɗo ba zai taɓa kai labari ba. A daran kuma a bangaren Fulani ya ci abincin dare itama sun daɗe suna tattaunawa kamar dai Mai martaba mai murabus, itama sake nuna masa muhinmancin zamowar sa Sarki tare da tunasar da shi nauyin dake kansa ta yi. Kowa sai ya ce ya cancanta shi kuma yana ganin bai cancanta ba a shekarunsa na arba'in da haihuwa a duniya gani yake yi ya yi ƙanƙanta da hawa wannan ƙaragar sannan yana ganin ba zai iya ba amma Mai nartaba ya saka yaƙini akan shi da zai iya haka ma Fulani. Itama ta yi maganar sunan jaririya yadda ya faɗa ma Mai martaba haka ya faɗa mata. "Na yi magana da ita Ummu Salaman da rana, ta ce har yanzu ba ku yi magana ba" Lamiɗo ya jinjina mata kai. Saƙo nan kawai ya tura musu daga ita har Bilkisu ba ma su ba, bai yi magana da kowa ba bayan Kabiru da Abdullahi. Fulani ta ce ya kama ta ya neme ta su yi magana duk asan abubuwa sun zo ba yadda aka yi tsammani ba. Amma dai ya kira ta tunda haihuwa ta yi, ko yaya ne za ta ji daɗi. Ya amsa ma Fulani a ladabce da cewa zai kira in sha Allahu. Shi yasa yana komawa bangaren shi wajen sha ɗaya na dare ya yi wanka ya yi shirin kwanciya lokacin sha biyu na dare a Nigeria yana tunanin Ƙarfe ɗaya na dare a can Egypt tunda tsakaninsu da Nigeria awa ɗaya. Ya ga saƙon Aminin shi ma da cewa ya isa Abuja tun da yamma zai tsaya gidan Hamma Jibo, ƙarfe ɗaya na dare jirginsu zai ta shi. Ya ga saƙon amma bai ba shi amsa ba lokacin yana ganaawa da malaman fada ne. Datar shi daman a kunne ta ke a kodayaushe Ummu Salama ya duba tana online sai ya kira ta vioce call har sau biyu ba ta ɗauka ba, ya san cewa ta yi barci tunda can dare ya yi nisa sai kawai ya yi ma Bilkisu waya direct call. Kira ɗaya kamar wayar na hannunta ta ɗaga kiran shi. "Ranka ya daɗe" Ta faɗa cikin zumuɗi domin wayar na hannunta tana I.g tana kalle kalle. Ita fa ba ta san haka zamowar matar sarki ke da daraja ba sai da ta zamo, ta shaida zamowar yar Sarki da matar Yarima amma zamowa Gimbiya ne sai yanzu ta san yadda ake ji. Ashe ko a baya kishi ne ya rufe mata idanuwana take ganin gwara Lamiɗo kar ya zama Sarki da ya zama Sarki ya ƙaro auro, yanzu kuma wannan ba ya gabanta tunda dai ta zama Gimbiya tana tunanin ta sha gaban kowa. Har Umma Salaman ta manta da ita, duk da ta ga jaririyar su Hamma Saddam na ta sawa ba ta da lambarta ba ta yi mata barka ba amma ta kira Ammah sun yi magana. Tun yanzu har an fara kiran ta Gimbiya Bilkisu, kafin ta shiga Masarautar Daura ta fara zuba mulki da iko lokacin da ta ga kiran Lamiɗo ta ɗauka wasa ne domin tun saƙon da ya tura mata ta chart ba ta sake jin sa ba. Shi ya sa jikinta na rawa ta daga kiran a muryanta ma za ka fahimci tana cikin tsananin farinciki. Gyaran murya ya yi,amma bai yi magana ba. Shi fa mulki ba ƙarya ba ne yawo ma yake yi a cikin jini. Ko ba ya so yanzu shi Shugaba ne sannan wakilin Alumma, ba ya ma sanin lokacin da komai na shi ke sauyawa yanzu ko magana zai yi za ka fahimci natsuwa da kamewa a cikinta. Received at 15:16 10 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Ranka ya daɗe muna murna ni da yara mun yi kewar ka." Ta sake faɗa cikin bayyana farincikinta. "Congratulations Papa. Allah ya taya ka riƙo." "Amin" Karo na farko da ya yi magana sannan a kame ya ce ya gida yana fatan tana lafiya tare da yaran gabaɗaya.? Ta ce duk suna nan lafiya sai dai kewarsa. "Yaushe za ka zo? "Ku ne za ku taho." Ya faɗa a rabe kafin ya sanar da ita cewa in komai ya daidaita an gama gyara Masaurata za su tattaro su dawo nan gabaɗaya. Bilkisu ta washe baki kamar yana ganin ta, murna da farinciki sun cika ta. Tana tambayan shi wai dukkansu gabaɗaya har da su Debora ya ce in tana so ba shi da matsala. Farincikin Bilkisu ya kasa ɓoyuwa, tana faɗa masa Umman Kano ta ce ta kira shi ba ta same shi ba, ya ce bai ɗaga wayar kowa ba amma daga baya zai kira ta. Sun jima suna mgana yara daman ta ce sun yi barci amma ba su da magana sai na shi, ya ce yana gaishe su zai samu lokaci ya kira lokacin da suke gida sun yi maganar makarantarsu, yanzu sun kusa fara jarabawar second term ne, wataƙila ma ba lalle ko an fara jarabawan a gama da su ba da zaran lokaci ya yi za su bar Lagos gabaɗaya su koma Daura. Har suka yi sallama bai yi mata maganar Ummu Salma ba, itama ba ta yi masa ba daman kuma shi ba zai yi ba. Bai taɓa kawo mata maganar ta ba in dai ba ita ta kawo ba ko ta kawon ma yana kaucewa. Lokacin da suka gama waya da Bilkisu ɗaya saura na dare sai ya sake kiran Ummu Salama ta vioce call, har ya cire rai da zai same ta sai kuma kawai ya ji ta ɗaga kiran. "Hello." Ummu Salma ta faɗa cikin barci, barci take yi ba ta ma ko duba mai kiran ba. Cikin magagin barci ne wayar ta dame ta da kara ta zura hannu idanuwanta a rufe suke. Ta ce Hello amma ta ji shuru ba a yi magana ba ta ƙara cewa Hello nan ma shuru gyaran murya da ya yi ne ya sa ta fahimci wane ne. Da sauri ta watsaƙe ta miƙe zaune akan gadon da take, daga gefen gadon ta ta latsa wani abu sai fitilar ɗakin ta kawo gabaɗaya haske ya haskaka ɗakin ta cire wayar a kunne ta duba sai ta ga Hamma ne yake kiran ta. Daman tunda ta ga saƙon shi kewar sa ya ta so mata. Ko ba ta ganshi ba ta yi magana da shi ko ta ji sanyi. Ta mayar da wayar kunne a shagwaɓe ta ce. "Hamma." "Hamma ka manta dani." "Ka manta da ƙanwarka." Sai da ya yi mirmishi, gefe da gefen bakin shi suka motsa. Mirmishin da tun da ya zama Sarki bai yi irin shi ba. Shi a wajenta ba Sarki ba ne mijinta ne da kuma Hammanta. Kuka kawai ta saka masa tana masa shagwaɓa da rigiman ya manta da ita. "Shike nan haka ake yi tunda ka zama Sarki ka manta da ni" Ta gama faɗa har tana matse murya, kuma kukan da gaske take so ta yi. "I'm sorry." Ya furta a hankali. "Ba wani sorry, na haihu amma ba ka damu da ni ba ballatana jaririyar da muka haifa." "I'm sorry na damu mana" Ya furta a hankali yana mai lumshewa idanuwana ya san halinta da rigima daman. "Ummu Salama." Ya kira sunanta a kausashe. Bai jira ta amsa ba ya cigaba da faɗin. "Ba ki san na zama Sarkin Daura ba ne? Abubuwa sun zo ban shirya musu ba." "Ni ina ruwana da zamowarka Sarki, Ni Hamma na sani, da mijina ba ruwana da wata Sarauta." Ta gama faɗa har tana tura baki kamar yana ganinta. Ya yi mirmishi mai sauti. "Ummu Salama." "Mu yi video call? Ya tambaye ta cikin wani narke murya, yana kwance ne amma kuma kewar Ummu Salama duk ta gama mamaye shi daurewa kawai yake yi da abin na hausawa da ake cewa sahun giwa ya take na raƙumi. Bai jira cewarta ba ya katse vioce call nan take ya kira ta video call itama kamar tana jira ta ɗauka suna masu kallon juna. Ta yi kewarsa sosai kuma har kewar ya bayyana a idanuwanta. Ƙwallar da suka taru suka sauko mata ta saka hannu ta share, shi kuma yana kwance kansa kawai ya ɗan dago jikinsa ba riga amma ya rufe da blanket. Ummu Salma ce ta zuro kafafunta ƙasan gado ta saka tattausan silafas ɗin dake wajen. Yana kallonta yana jin zuciyarsa na tsukewa a waje ɗaya. Ta kara masa fari sannan ya ga ta kumbura. "Me ya same ki? Fuskarki ta kumbura." "Haihuwa ce." Ta amsa mishi tana shafa fuskarta. "Kina lafiya? "Ba wata matsala? "Ina Babyn mu? Ya tambayeta a jere amma a rarrabe. Received at 15:16Reactions: ❤ 14, 🥰 2 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Lafiya lau na haihuwa cikin kulawa baby tana lafiya bari ka ganta." Ta tashi ta isa in da ɗan gadon jariiyar in da take ciki tana barcinta ta haska mishi ita. Ya ƙura mata idanuwana yana kallonta cikin wani shauƙi. "She is so cute." "Kama da kai take yi " "A'a ke ce." "Ka duba da kyau Hamma." Tana cewa shi ne yana cewa ita ce, daga karshe ya sakar mata da cewa da shi take kama duk da shima ya ga haka. Ɗauko yarinyar ta yi ta koma gefen gado ta zauna tana riƙe da ita suna cigaba da magana. Nan yake faɗa mata Hamma Kabiru na hanya da kuma yankaar da za a yi gobe a can gida Adamawa. Daman sun yi vioce call da Baɗso ɗazu ita ta ba ma Ammah waya suka yi magana. Ta faɗa mata an siya raguna guda huɗu za a yanka sunan yarinyar suka yi magana ta ce ba su yi magana da Hamma ba tukunna, na zuwan Hamma Kabirun kuma kafin Mami su tafi masauki ta faɗa mata ya yi mata saƙo yana tafe. Cewa ya yi ta yi ta haska masa baby yana kallonta. Ta yi masa abin da yake so, ga shi tana da barcinta ba ta ma san ana yi ba. "Hamma." Ta faɗa tana karkato da wayar a fuskarta. "Ba ka faɗi sunan da za mu saka mata ba! Ko ka faɗa ma Hamma Kabiru ne? "Aa ban faɗa masa ba " "Shima na ce in ya zo ya tambaye ki." Ya amsa mata yana kafe ta da idanuwansa masu sanyata jin kamar tana jin sanyi. "Ni zan faɗi sunan Hamma? Ta faɗa tana mirmishin jin daɗi "Na ba ki zaɓi" "Da namiji ne mai sunan Baffa ne, amma tunda mace ce Allah ya ba mu na ba ki zaɓi" "FATIMA." "NA ZAƁA MATA FATIMA." Ta furta tana kallon shi. Sai ya jinjina kai ya gyara kwanciya yana faɗin. "Allah ya raya mana mai sunan Mami, Allah ya yi mata albarka." Ta amsa da Amin tana dariya. Shima mirmishin yake yi, Ummu Salma kamar tana shiga zuciyarsa yawanci tana cika muradinsa tun kafin ya furta tun lokacin da na'ura ta nuna mace Ummu Salama za ta haifa a zuciyarsa ya ce zai yi ma Mami takwara, tunda ya yi ma Ammah to ya ba ma Ummu Salma zaɓi ne yana tunanin ra'ayinsu zai zo ɗaya sai ga shi ba ta ba shi kunya ba. Sun yi shuru kawai suna kallon juna shi ne ya katse ta da cewa ba ta jin komai ba ta da wata matsala ta ce babu nan ta shiga ba shi labarin yadda ta haihu. "Hamma abin mamaki ko awa ɗaya ban yi ina naguda ba na haihu, kuma jinina normal na haihu lafiya" "Alhamdulillah." Ya faɗa yana cigaba da sauraran ta tana cigaba da ba shi labarin Mami ta matsu su koma gida saboda wai ta yi mata wankan jego na gargajiya, sannan ruwan nonon ta, bai zo da yawa ba ta ce in sun koma gida a nemi maganin gargaji yanzu Baby sai dai ana haɗa mata da madaran yara. Shi kuma ya ce za su dawo gida in dai likitoci sun tabbatar da ba matsala in Hamma Kabiru ya sauka zai yi masa waya kawai ya jira su taho tare. "Hamma wani suna za mu dinga yi ma Baby alkunya? "Ni kuma? Ta ya zan sani" "Mu kira ta Baana tunda muna da Beena? "Baana? Ya maimaita cikin sigar tambaya. "Mene ne ma'anarsa? Ta fara dariya tana faɗin ba ta sani ba. "Nima ban sani ba ko Beena Bilkisu ce ta saka mata." "Ki samu suna mai ma'ana kar ki je ki saka ma ƴata sunan mayu." Ya faɗa har yana yi mata gargaɗi da hannu ta fara dariya har sai da baby Fatima ta farka ta yi saurin danne bakinta. Cewa ya yi ta ba ta nono yana gani sai ta ajiye wayar ta saita a saman ɗan drower ɗin dake gefen gadon ta fara ba ta nono yana kallon su cike da sha'awa da kewa ba domin wannan sarautar ba da yana tare da su a halin yanzu. Ita kuma tana so ta tambaye shi Hanan tana jin kunya, ta san ko ta nan ko ba ta nan Hanan tana cikin ƙoshin lafiya. Kallon su kawai yake yi, Ummu Salama ce ke magana shi dai na shi kallo ne da ji, sai da ta gama ba ta nonon ta ƙoshi sannan ta je ta kwantar da ita aɗan gadon ta saboda ta koma barci. Sannan ta dawo ta ɗauki wayar suka cigaba da hira. "Hamma." "Matar Hamma" "Kana cikin damuwa ko? Na sani ba ka san sha'anin mulkin. Amma ina so ka sani haka Allah ya kaddaro mana ba mu da yadda za mu yi." Ta dakata tana kallon shi yana lumshe idanuwana yana buɗewa. "Gani nake yi kamar ba zan iya ba. Akwai wahala mulki Ummu Salama akwai wahala." Ya gama faɗa a muryansa za ka gane yana cikin kasala da sanyin jiki. Received at 15:16Reactions: ❤ 17, 🤗 2 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sannan ya ga Hamma Saddam online jin yana gida sai ya kira video call na gabaɗayan su a group na Ammah da Baffa, waɗanda ke kusa suka ɗaga kamar Hamma Saddam da Hamma Abdulrraham da Hamma Abdulrahim sai Hamma Abdullahi Hamma Mustapha ne bai ɗaga ba sai Lamiɗo, Ummu Salma ma ta kama a wayarta. Hamma Saddam ya je falon Ammah tana tare da Umma Balki da ta iso a daran jiya, shi kuma Hamma Abdulrahin yana tare da Baɗɗo ne. Kowa na ganin kowa nan ya ce ga shi ya iso har an yi ma yarinya huɗuba da Fatima. "Allahu akbar Allah ya raya mana Fatima." Ammah ta faɗa tana cigaba da addu'a. Umma Balki ma ta yi fatan alheri tunda har Ummu Salma tana kai. "Gimbiya Auta ya jikin na ki? Umma Balki ta faɗa ta saka kowa dariya sai yi ma Mami tsiya take yi wai ta yi takwara baki yaƙi rufuwa. "Ina shi Lamiɗon na ɗauka ni zai yi ma takwara sai ya yi ɗanwaken zagaye? Idona idon sa sai na ci ƙaniyarsa." "Umma Sarki ne fa, yanzu ko magana kika faɗa mara daɗi dogarai za su yi miki ladabi." Hamma Saddam ya amsa mata ana ta dariya bayan ta ce ƙaniyarsa. Tana faɗin suna murna ga Lamiɗo Allah ya ta ya shi riƙo. Sannan da cewa yaushe za su dawo? Mami ce ta amsa da cewa sun kusa dawowa ƙila ma su dawo tare da Hamma Kabiru gabaɗaya. Bayan an gama ganin juna da gaisawa aka haska ma Umma Balki da Ammah takawaran Mami suka ganta, sauran duk sun bar video ca ɗin tunda Hamma Abdullahi ya ce zai zo gidan yanzu da masu yanka mahauta kenan za a yanka ragunan a gyara. Ammah ta ce ta faɗa ma maƙota da sauran abokan arzuƙa za ta ɗan yi taron suna a yau ɗin Mami ta ce hakan ma ya yi. Daga karshe Baɗɗo kawai aka bari da Ummu Salma suna magana, Hamma Abdulrahim ya bar mata wayarsa. "Sisna, Allah ya raya mana takawaran Mami ko na ce Sarauniyar Daurama." "Amin" Ummu Salma ta amsa tana mirmishi. Tana yi ma Baɗɗo tsiyan ya amarci ta ce gamu cikin shi Ummu Salma ta ce Allah ya ba da sa'a. "Wani inkiya za mu dinga kiran takawaran Mami? "Banafsha na daɗe ina son sunan nan." "Miye ma'anarsa? Mai Martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ya ce kar na saka ma ɗiyarsa sunan mayu." Ta faɗa ƙasa ƙasa kar su Mami su ji Baɗɗo ta fara dariya. "Suna ne mai kyau da tarihi. Sunan larabawa ne, kuma yana nufin mace mai kamewa da natsuwa" "To shike nan, ki faɗa ma kowa sunan da za mu dinga kiran takwaran Mami Banafsha." Baɗɗo ta amsa da yanzu kuwa sun rabu bayan ta ce Umma Salma ta ɗauki hoton Banafsha ta tura mata, tana hannun Mami ne, likitocin ma ba sa bari ana ɗaukanta sosai sun fi son ta a kwance a ɗan gadon ta. Sai da Nurses suka shigo sannan Banafsha ta dawo gadon ta lokacin Ummu Salma ta ɗauke ta hoto an yi mata gayu da wasu fararen kayan sanyi. Nan take ta tura ma Baɗɗo itama a karo na farko ta yi status da hoton Fatima(Banafsha) "Alhamdulillah it's a Baby girl. Today, we named her Fatima, Fatima Muhammad Nasiru(Banafsha.)" Haka ta yi status, waɗanda suka gani suna ta Allah ya raya. Hamma Saddan ne yan gaba gaba tuni ya ɗauka shima ya yi status da shi. Sannan Iklima da su Kaltume duk sun gani sun yi mata barka tana da lambar Hajiya Falmata itama ta gani ta ce haihuwar na su ne tunda takwaran Mami ce daman ta yi mata barka da suka yi magana ta wayar Mami. Sai su Adda Suwaiba suna ta Allah ya raya tare da tambayan yaushe za su dawo ta ce an kusa. Ta tura ma Hamma Lamiɗo hoton, ya tafi sai dai kafin ya duba ne aiki a baya ma ana fama ballatana yanzu. Ba ta yi wani mamaki da Bilkisu ba ta yi mata barka ba, ba su da lambar juna amma ai haihuwa ta wuce wasa. Ranar ta kama bakwai da haihu itama ta sha kwalliyarta cikin leshi , kamar ba asibiti ba. Sai ga Bilkisu ta yi ma Mami voice call sun gaisa. Ta ce a ba ma Ummu Salma wayar, suka gaisa ta yi mata barka a status ɗin Adda Safina ta ga sunan jaririyar Fatima. Da yake ba su saba waya ba, kawai dai ta yi mata barka ne kawai sai ta haɗa ta da yara Sultan da su Beena har da Hanan suna ta cewa suna son ganin jariri. Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 👏 2 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sai Mami ta ce a kira video call, Mamin ta karɓi wayar ta kira yaran suka ga ƙanwarsu suna ta zillo a waya kamar za su faɗo ta cikin wayar lokacin sun yi shirin makaranta ne safiya ce a can Nigeria domin uniform ne ma a jikinsu. Har su Sabuwa sun leƙo sun gaishe da Ummu Salma da su Debora suna ta murna da suka ga yar jaririya fara sol da ita. A cikin masu yi ma Ummu Salma murna da status ɗin da ta saka har da Shamsiya da yake ta yi saving ɗin lambarta. Ta gani ta yi mata magana da tambayan ta haihu ne? ta amsa mata da eh, ta yi mata barka da murna har tana cewa za ta zo barka tana ina ne? "Ina Egpyt a can na haihu amma zan dawo Jimeta nan ba da daɗewa ba" Jiya sun yi magana da Hamma in suka dawo Jimeta za ta zauna kafin komai ya kamkama su koma Daura gabaɗaya. Shamsiya ta yi mata alƙawarin za ta zo, in ta dawo ta kira ta ta ce in sha Allahu. Tausayin Shamsiya take ji, duk da ta tsane ta a baya amma yanzu tausayi take ba ta, Habib ne har abada bai taɓa ba ta tausayi ba. Abin da ya aikata ne ya ga sakamakon sa. Hanan ɗin da ya so ya salwartar ita ce dai sanyin idaniyarsa. Ba shi da wani ƙwai a duniya Allah ne ya jarabce sa. Kuma ya ga ishara ga rai ga lafiya amma haihuwar ce Ubangiji ya hana shi domin nuna masa ishara kan niyarsa ta baya. An yi yanka raguna huɗu a can Adamawa Ammah ta yi taron suna an ci an sha, naman suna kuma an soye shi an yi rabo sai fatan Allah ya raya Fatima Banafsha. Sakeena daga England ta yi ma Ummu Salma barka haka ma Badia'tu daga Nigeria sai Gimbiya Shahida da suka sake yin magana Hajiya Kilishi da Hajiya Zaliha ba ma sau ɗaya ta yi magana da su ba Saleem dai ba su yi magana ba ya dai yi mata saƙon ta ya murna da Allah ya raya ta chart. Kwanan Hamma Kabiru uku da zuwa suma suka fara shirin tahowa gabaɗaya sun sake magana da Hamma sau ɗaya ya ce tunda likitocin sun ba da tabbacin ba wata matsala to ba amfanin zaman su taho kawai gida. Sai da suka kwana ashirin cif da saukan su a ƙasar Egpyt a daran ranar Jirgi ya kwashe su zuwa Nigeria. Ummu Salma da Banafsha sun sha hotuna da larabawan kasar Egypt kafin su baro kamar kar su dawo saboda yanayin kasar akwai daɗin zama. Ta Abuja suka sauka da safe a gidan Hamma Jibo suka fara yada zango Nan Mami ta fara gasa jikin Ummu Salma can fa ba sa bari ta yi amfani da ruwa mai zafi saboda BP ita kanta Banafsha da ruwa ɗumi kawai suke mata wanka wata rana ma goge jiki ne. Nan suka kwana Adda Nauwara ta dama mata kunun tsamiya ga ferfesun ganda da na kayan ciki, shi Hamma Kabiru a jiya ya bi jirgi zuwa Taraba. Ya ce za su dawo tare da Adda Safina da yara in sun koma gida. Su kuma sai a washegarin bayan sun kwana sun hatse suka bi jirgin Yamma zuwa Adamawa Yola. Hamma Saddam ya je da motar Hamma Lamiɗo ya ɗauko su zuwa gidan Ammah. Tuni an gyare ɗakin Umma Salma nan ta sauka daman ta ce ma mijinta anan wajen Ammah za ta zauna ya ce yadda take so haka za a yi. Gida ya cika da su Adda Suwaiba da su Ummi ikki ɗakin Umma Salma cike ana ta hira ana mayar da magana da labarin komawa Daura Adda Suwaiba na faɗin za su sha bikin naɗin Sarauta har tana cewa kowa ya tanadi kuɗi shigar manyan mata suma za su yi ana ta dariya. Ummu Salma ta tura ma Lamido sakon sun sauka. "Mun dawo gida Mai martaba na" "Welcome back home Sarauniya ta" Ta yi mamakin yadda ya samu sararin bata amsa shi da yake can yana fama da sha'anin mulki ga shi komai sabo zai gani tunda baƙo ne hakan a gare shi a matsayin shi na Sarki. Kowa sai mamakin kiban Ummu Salma yake yi ana cewa ƙasar waje ta karɓeta. Banafsha ma ta yi ɓul, kuma suna dawowa Ammah ta fara mata kunu gero da na shinkafa sai ga ruwan nono, Ummin ikki ke yi mata wankan jego, Mami ta koma Kaduna ita da Barira ta duba gida tunda ta daɗe bata nan. In Lamiɗo ya samu dama suna waya da Ummu Salma bayan kwana ɗaya haka watarana ma duk dare. Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 🔥 1, 🥰 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Yanzu a ƙarshen watan nan Mai martaba mai murabus za su yi ƙaura zuwa can gidan shi na cikin garin Daura an tsara za a yi shagalin naɗin sarautar Lamiɗo a farkon watan December su Hajiya kilishi sun haɗu sun tattauna da cewa za a haɗe shi da taron sunan Banafsha a Masarautar Daura gabaɗaya. Da suka zo barka ne suka faɗa ma Umma Salma. Hajiya kilishi, Hajiya Zaliha da Hajiya Binta sai Gimbiya Shahida da Gimbiya Amaratu da matar Waziri da Shamaki. Sun kawo akwati guda goma biyar na mai jego, biyar na Banafsha, sai kuɗi a takarda miliyan biyu daga Fulanin Daura. Sai kyautar mota sabuwa GLK daga Uban Lamiɗo kakan Banafsha tsohon Sarki mai murabus, Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu mota na can masarauta tana jiran su. Wani kaya sai amale, sun ce ranar tara ga watan December za a yi naɗin saboda haka Ummu Salma ta yi magana da Lamiɗo, su fara shirin komawa can Daura domin gabatar da shirye shirye, ga shi kuma za a haɗe shi da taron suna Sannan sun ce duk waɗanda za su je akwai jirgin da Mai martaba zai ba da, sannan za a turo lafiyayuun motoci daga Masarauta ta ɗau mutane tare da wasu kaya. Lokacin da suka zo Shamsiya na gidan tare da Habiba da Gwaggo sun zo barka tunda Shamsiyar da ta gaji jiran kiran Ummu Salma sai ta kira ta shi ne Ummu Salma ta sanar da ita ta dawo tana gida shi ne su ka zo zuwan su kenan ma sai ga baƙin Masarauta. Sai suka koma gefe suna ganin arziƙi, Habiba a fili take faɗin Allah ya rabamu da talauci. Domin talauci bai yi ba Annabi ma Salallahu alaihi wasallam ya nemi tsari da talauci. Sai da su Hajiya Kilishi suka tafi sannan aka ma tuna da su Shamsiya. Da gayya Baɗɗo ta ce in za samu zuwa suna gayyatarsu Daura naɗin Sarauta da taron suna tun kafin Shamsiya ta amsa Habiba ta ce za su je. Domin za ta je ta ga kuɗi da masu kuɗi. Shamsiya na faɗin sai sun tambayi Habib a zuciyar Habiba ta ce bai isa ya hana ta ba, duk da yanzu abubuwa sun ragu tunda yana koyarwa yana kuma aikin karfi kamar aikin gini sannan ga Shamsiya tunda ya aure ta ya samu wasu sauƙin abubuwa. Amma a rashin mutumcin Habiba ba wanda ya ragu ita sai Habib ya sake ta shi kuma ya ce da ita aka fara da ita kuma za a gama. Suna gidan har yamma sannan suka tafi. A daran Ummu Salma ta kira Mai martaba mai murabua daman da suka dawo sun yi magana sau ɗaya ya yi mata barka da samun kai lafiya. Godiya ta yi masa ya ce bakomai kin iya haihu tunda kika haifi Batula. Ya ce yana jiran amaryan sa ta zo ta gaishe shi. Ummu Salma ta amsa da in sha Allahu cikin ladabi mai yawa. Da suka yi waya da Lamiɗo ta faɗa masa zuwan su Hajiya kilishi duk da ya san da zuwan su amma bai gwalese labarin ba. Faɗa mata yake yi an gama gyaran Masarauta Bilkisu za ta fara yo gaba ita da yara daga Lagos daga baya ita Ummu Salama sai ta taho daga nan Adamawa ta ce babu matsala hakan ma ya yi. *Janafty* Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 🥰 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. BAYAN SATI ƊAYA. Ta ko'ina shirye-shirye ya fara gudana. Ga shi yau har biyar ga watan December saura kwana huɗu bikin naɗin sarautar Lamiɗo tare da taron sunan Banafsha. Tuni Mai martaba tsohon Sarki mai murabus da iyalansa sun bar cikin masarauta sun koma gidansa dake cikin garin Daura ɗan gaba kaɗan da masarautar, shi kenan fa haka rayuwa take ko mutuwa ne haka za a yi a gama suma ga shi kamar ba su zauna a cikin masarauta ba yau ga shi zamansu ya ƙare daman in yau kai ne gobe ba kai ba ne. Allah ya sa mu dace. Lamiɗo ya so Fulani ta zauna tare da shi a Masarauta ta ce ba za ta zauna ba duk in da Nasiru yake tana tare da shi. Tare da ita aka koma wancan gidan shima kato ne mai kyau na alfarma da zanen gidan Sarauta a jikinsa. Masarauta kuma tuni ana ta gyara an sauya tsarin duka bangarorin gabaɗaya komai sabo ake saka kama daga furnitures da komai da fenti sabon Sarki sabon gyara. Tuni tsarin katin gayyata har ya fara isa ga manyan kasa da za a gayyata. Masu Sarautu ma'aikatan Gwamnati, gwamnoni yan kasuwa yan majalisu da sauran su. Daura za ta cika ba matsaka tsinke baƙi ne za su sauka a garin daga kowani yanki na Nigeria. A can Daura ma an kacame da shiri domin kaf iyalan Marigayi tsohon Sarki Muhammad Shitu za su hallaci wannan naɗin kama daga waɗanda ke gida Nigeria da mazauna kasashen waje, kaf ƙannen Lamiɗo za su taho gida ayi biki wannan naɗin da su tare da bikin sunan Fatima(Banafsha). Ummu Salma ma anan Jimeta shiru kawai suke yi, suma daga bangarensu gayya guda ne ce za su tafi Daura. Kaf yayyenta maza da matayensu tare da yaransu za su je Daura wannan taron naɗin sannan akwai wasu daga Mubi irin su Baffa Umaru Umma Balki da Umma A'i ita Umma Salamatu tunda tana fama da ƙafa ya'yan ta mata ne guda biyu za su je, sannan har da Hafiz da matarsa Salima Ummu Salma ta gayyata tunda su suna ma cikin garin ne a can kawai za su haɗu. Ummin ikki har da Iklima da Kaltume Ammah na cewa ba za ta je ba kowa na ce ta je amma ta ki Ummu Salma ta faɗa ma Lamiɗo abin da Ammah ta ce ya ce za ta zo in sha Allahu zai yi magana da ita. Har kuma yau bai zo ya ga Ummu Salma ba, ballatana Banafsha sai dai a hoto ko kuma a video call ta gaji da yi masa ƙorafin bai zo ya gansu ba ta ƙyale shi. Bilkisu gobe za su baro Lagos su sauka a garin Daura Hidaya ta faaɗa ma Harira da suka yi waya. Su za su fara sauka ita Ummu Salma tana tunanin sai ranar alhamis, wasu kuma dole a mota za su je saboda tafiya da wasu kayan. Mami daga can Kaduna za ta dira a ranar Jumma'a tunda taron naɗin ranar asabar ne. Tare da Islam da Faruk da Hajiya Falmata za su je Daddy yana Abuja amma a ranar asabar ɗin zai isa can Daura. Shiri kawai kowa yake yi saboda za a je a baza kafacity Ummu Salma ta ba da ɗinkuna sama da kala talatin ta ɗiba cikin kayan da aka kawo mata daga Daura sannan ta sake ɗinka na cikin lefenta domin har lokacin ba su ƙare ba. Ga Lamiɗo ya tura mata 5M bayan ATM ɗin shi dake hannunta kuma akwai kuɗi a ciki duk ta haɗa ta yi siyayya ta yi duk abin da za ta yi in ma bai isa ba ta faɗa masa. Ɗinkunan daman Kaduna ta aika da shi telan Mami na zaria ya iya ɗinki shi zai ɗinka mata, nan Jimeta ma ta bayar da wasu tare da na Harira sannan an yi ma Beena da Hanan wata atamfa gold mai kyau iri ɗaya. Ba anko za a yi ba amma an ce kowa ya ɗinka leshi na fita kunya kowa ya siya kalan na shi daidai ruwa daidai kurji. Duk da akwai leshina masu tsada a ɗinkunan Ummu Salma sai Mami ta saka siyan wani na miliyan uku da rabi wanda za ta saka ranar naɗin a can Kaduna Mami ta siya ta ba da ɗinki bayan an tura ma Ummu Salma ta zaɓi kala sannan ta sake siyan gold na miliyan huɗu ta haɗa da kuɗin da Fulani ta ba ta, ta siya domin Mami ta ce ɗiyarta ta kai kuma itama ta isa ta yi shigar ke ce reni da alfarma Ammah ce ke cewa su rage kashe kuɗin nan sun yi yawa Mami ta ce kuɗi tunda akwai su za su yi ta kashewa kamar ba su san zafin su ba. Received at 15:21Reactions: ❤ 14, 👏 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ita kanta Ammah miliyan uku Lamiɗo ya tura ya ce a yi mata siyayya kuma ya ce sai ta je Daura. Ba tare da ta sanin ta ba Adda Suwaiba ta siya mata rantattsun kaya masu tsada aka ba da ɗinki kowa fa zai je ai ba zai yuyu a barta ita kaɗai a gida ba. Bangaren gyaran jiki kuma har skin care Ummu Salma ta je an yi mata sannan ga jego sai ta yi wani kyau da haske ga shi ta ɗan yi kiba kamar ba ita ba. Sannan har ƙunshi da gyaran kai anan Jimeta za ta yi kafin su tafi maganar kayan gyara majalisar ɗinki duniya ma wannan karon ba ta jira Mami ba da kanta ta yi ma Surayya Dee 080322773332 Bojuwa waya ta haɗo mata package ɗin mai jego har an aiko mata da shi ta fara sha tunda jinin haihuwar ya tsaya ta yi tsarki har ta fara salla. Banafsha ma acan Kaduna Mami ta yi mata siyayyan kayan alfarma da za ta ci taron suna da shi, domin itama ranar ai ranar ta ce. Tunda December ta shiga kowa shiri yake yi in aka taru a falon Ammah ba a da magana sai na taron naɗin da za a yi ma Lamiɗo a Daura abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Irin manyan baƙin da aka gayyata ma kawai abin birgewa ne. Abin da ya danganci wannan daga can Masauratar Daura ake gudanar da duka shirin, su nan sai dai ƙarishe kawai amma can suke da shiri sosai. Lamiɗo yanzu ya zama babban mutum nauyi ya hau kan shi ba a cika samunsa ma a waya ba. Ko Ummu Salma sai can dare suke magana yanzu ma da abin ya taso na taron naɗin nan sun kwana biyu ba su yi magana ba. A chart ma ta yi masa sako bai buɗe saƙon ta ba, rigima take yi masa da cewa in har ya bari ta zo Daura to sai ya biya kuɗin siyan baki zai gansu ita da Banafsha da ta yi fushi da shi, a tunanin Ummun Salma ko ma ya ya ne ai sai ya samu ko bai kwana ba ya zo ya gansu ya koma ita ba ruwanta da wani Sarki mijinta kawai take ji amma ya yi mata nisa tana tunanin ko can suka koma ba za ta samu ganinsa sosai kamar yadda take samun ganin shi a Lagos in yana gari ba. Yanzu abubuwa da dama sun canza, in kiɗa ya canza dole rawa ma ya canza. * Da daddare ne duk suna falon Ammah suna ta hira, hiran daman ba ya wuce hiran taron naɗin Sarautar da zai gudana a garin Daura. Ammah ke zaune a ƙasan cafet tana rike da Banafsha da ta fara rigima ta karɓeta sai Hamma Saddam da Abdulrrahaman sai Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrahim, suna zazzaune saman kujerun falon Ammah, Ummu Salma da Baɗɗo ma duk suna falon ana hira ana faɗin irin kafaciy ɗin da mutanen Jimeta za su baza a garin Daura. Harira na ciki ta kwanta. "Ina faɗa muku, irin shigar da zan yi zan fito asalin ƙanin Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo." Hamma Saddam ya faɗa, har yana miƙewa yana gwada irin tafiyar da zai yi ranar ana ta masa dariya Ammah na faɗin ya yi addu'an Allah ya sa yana raye da rai da lafiya. "Ammah ina raye da ikon Allah, da lafiyata in sha Allahu." Ya amsa mata da sauri, kamar yana jira nan ma dariya aka sake saka masa. "Ai in dai ba mutuwa Saddam ya yi ba, to ko yana gargada sai ya je Daura." Hamma Abdullahi ya faɗa, Hamma Abdulrahim ya amsa da cewa ko yana tashi daƙyar ne sai ya je saboda yadda ya ci buri sosai. Ya ce wallahi in bai samu zuwa Daura ba akwai matsala irin yadda yake saka katinan gayyata naɗin nan a duka paltform ɗin shi na Social media kowa kawai jira yake yi ya hango shi a kusa da Sarkin Daura a ranar. "Ni fa ba wanda bai san Hamma Lamiɗo yayana ba ne, in ban je ba akwai matsala." "Za ka je in sha Allahu." In ji Hamma Abdulrahaman ganin Hamma Saddam ɗin ya fara karaya yana cewa su yi shiru don Allah baya son ma maganar suna ta yi masa dariya har da Baɗɗo. Ummu Salma ce kafarta ba safa Ammah ta fara mata faɗa. "Sanyi ake miki gudu ya kama jikin ki, tashi ki je ki saka safa sannan ki saka hijabi ki rufe jikin ki." Tura baki take yi, ta gaji da wannan jegon zafi take ji ga shi Ammah ta hana ta amfani da fanka yanzu in ma a falo ne in dai tana zaune sai ta ce a kashe fanka ba ta da damar zama a ƙasan cafet sai Ammah ta yi magana in ta zauna ba safa ma haka sannan ba ta barinta saka wasu kaya haka, sai masu nauyi da za su rufe mata jiki ruf ta ji ɗumi, ga kunun da take dama mata duk safiya da maraice abinci ne Received at 15:21Reactions: ❤ 15, 🥰 2, 👎 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby mai rai da lafiya Ammh ke matsa mata sai ta ci, ga shi wanka safe da rana ba da ganye ba ne, amma dai da towel ne, tunda Umma Balki ta koma sai ta koma tana yi da kanta Ammah dai ta ce in ta gasa jikinta ita ta sani in ma ba ta gasa ba, ita ce za ta ɗanye ce ita dai ba ruwanta. Dole Umma Salma ta dake tana kula da kanta kuma ta ga amfanin haka ɗaki ta koma ta saka safa doguwa domin Ammah ba ta barinta ta saka gajerun da take da su na gayu sai ta ce wai ba safa ba ne ta siya wasu dogaye masu kaurin tsiya ga su har gwiwar kafa in ba ta saka ba Ammah ta dinga masifa tana faɗin da ta bi uwarta can Kaduna ita ba za ta iya da wannan abin nata ba. Hijabin ta saka har ƙasa ta rufe jikinta ta koma falo, aka cigaba da hira ana ta maganar Baffa ya kusa shekara a kasa Allahu akbar. "Ranar mun kai wani maƙocin mu da ya rasu a can, na kasa gane kabarin Baffa alaman da muka sanya ya bace Ammah an zuba da yawa a cikin shekaran nan wallahi su Baffa suna can ciki ba ma zan iya gane wajen ba." Hamma Abdullahi ya gama faɗa yana jinjina kai. "Allahu Akbar. Allah ya gafarta maka Baffa Ubangiji ya sa kana cikin rahamar Ubangiji." Ammah ta faɗa tana jin hawaye na cika kwarmin idanuwanta Banafsha na cikin jikinta ta rufeta ruf ta sake rumgumeta. Da a ce yau Baffa na raye ya zai ji in har ya ga jinin Ummu Salama da Lamiɗo ga shi yau Lamuɗo ya zama Sarki ga shi Baffa ba ya raye shi daman ya daɗe yana faɗin yana ji a jikinsa watarana Lamiɗo zai iya Shugabantar al'ummar Daura. Kowa jikinsa ya yi sanyi da tuna Baffa. Ummu Salma sai da ta share hawaye. Ta jima tana tunanin yadda radaɗin rasa mahaifi yake, sai da ta rasa nata ta san irin zafi da raɗaɗin da ake ji, ta kasa mantawa da Baffa rana ba za ta fito har ta faɗi ba ta tuna da shi ba, Allah ya gafarta masa amma mikin nan na rashin Baffa mai girma ne a zukatansu ba zai gushe ba har abada. Suka taru suka yi ma Baffa addu'a sannan suka cigaba da hiran tafiya Daura. Hamma Abdullahi na faɗin jirgin da za a ba da ma ai ba zai ɗauki duka mutanen ba. "Ai wasu dole su bi mota. Ɗazu ma mun yi charting da Gimbiya Shahida ta ce mota za ta zo ranar alhamis ranar da za mu tafi kenan da yamma ta kwashi wasu da kaya a safiyar Jumma'a kenan za su isa Daura a daran ranar." Ummu Salma ta faɗa tana cigaba da faɗin Mami ta tsara waɗanda za su rakata. Tunda Hamma Jibo daga can Abuja za su wuce Daura haka ma Hamma Kabiru ya ce ba za su biyo ta nan ba shima ranar alhamis za su isa Hamma Mustapha ne kawai za su biyo ta nan sannan su tafi tare da su Ummu Salama. "Mami ta ce ni da Ammah da Ummin ikki da Ummu Balki da su Umma A'i, da su Baffa Umaru sai Baɗɗo da ku gabaɗaya ni ban ma san waɗanda za su bi motar ba" "To ku matan ku bi jirgin ku, mu kuma mazan sai mu tsaya mu tafi a mota za a tafi da wasu kaya ne? Hamma Abdullahi ya tambaya yana kallon Ummu Salama. "E akwai kayana a can gida da wasu anan da zan tafi da su gaskiya." "To ba matsala sai mu yi hakan ko? Ya faɗa yana kallon Hamma Abdulrrahan da ya jinjina kai ya ce hakan ya yi. Saddam ya tura baki ya ce jirgi zai bi, ba zai iya tafiyan mota ba. Hamma Abdulrahim ya ce suma ai ba wai kuɗin jirgin ne ya gagaresu ba, gwara su yi tafiyar mota ko za su ga gari. Ammah ta amsa da cewa tafiya kuma mabuɗin ilimi ba. Saddam tunda ya ce ba ya son tafiyar mota aka ce sai su tafi tare da su Ummu Salama amma har su Baffa Umaru Hamma Abdullahi ya ce tafiyar mota za su yi gabaɗaya su mazan a daran Jumma'a za su isa a yi taron naɗi ranar asabar, lahadi litini su dawo gida ba shikenan ba. "Shike nan, kuwa amma ni ina gida ba zan je ba" Gabaɗayansu suka kalli Ammah, sun ɗauka ta daina maganar cewa ba za ta je ba "Ammah za ki je mana, Hamma Lamiɗo ba zai ji daɗi in ba ki je ba." In ji Hamma Abdullahi, Hamma Saddam na ta faɗin Ammah sai fa kin je tana faɗin to ubana. "Ammah Hamma ya ce da ke za a zo fa." Ummu Salma ta faɗa tana kallon ta. "To in ma ba ta je ba gida fa ba kowa." In ji Baɗɗo. "Za ta je ma in sha Allahu." Hamma Abdulrraham ya faɗa yana danna wayarsa. Received at 15:21Reactions: ❤ 14, 👏 2 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Me zan je na yi? Fatan alheri ne, na yi ma Lamiɗo a waya duk waɗanda ya kamata za su tafi ni ba sai na je ba." Ammah ta gama ta faɗa tana jadaddawa amma ba ta rantse ba. "Kowa fa zuwan shi na dabam, Ammah ke ce uwar Sarki ce kin ga ko zuwa Daura Dole " In ji Hamma Saddam yana dariya. "Mami fa a matsayin uwar Auta za ta je gwara ki je, ke ma ki yi capacity a matsayinki na wacce Sarki ya fi darajawa a duniya " "Gaskiya Ammah sai kin je, haba ya ma za a yi ba ki je ba ai sai Hamma ya ce duk mu ba mu da amfani in har bai gan ki ba." Hamma Saddam ya faɗa yana girgiza kai, har yana haɗa hannayensa yana riƙon Ammah ta je kar ta ce ba za ta je ba. "Kai ba zan je ba, kar ka dame ni." Ammah ta gwale shi, Baɗɗo ta saka baki Ammah ta ce ba za ta je ba ta ñaɗa Ummin ikki ga su Umma Balki ba sai ta je ba. Kowa ya yi shuru ganin ta dake, Ummu Salma ta ce a zuciyanta Allah ya jiƙan Baffa da yana raye shi zai tankwasa Ammah sai ta je amma tunda ba shi Lamiɗo na raye shi ne kawai in ya yi magana da ita za ta amince. "Ammah Hamma ya ce tare dake zamu taho " "Shima zan faɗa masa dalilina." Ammah ta faɗa alamun da gaske take yi, sai kowa ya yi shuru domin anan dai ba wanda zai tursasata ta amince, Ummu Salma ta kira wayar Lamiɗo ta shiga amma bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙon text massages da cewa Ammah ta tubure ta ce ba za ta zo ba, ya kira waya ya yi magana da ita. Daga baya ma sai aka bar maganar. Falon ya zama kowa da abokin hiran shi, ita Ummu Salma da Baɗɗo suke hira tana nuna mata irin ɗinkin da Mami ta turo mata ta ce a I.g ta gani ko a yi mata a leshinta ne Baɗɗo ta ce ɗinkin ya fita gaskiya a yi mata irin shi, itama ta ce shigen shi ta ba da a yi mata a wani ɗaya daga cikin leshinta na lefe suna ta kuskus ɗin su Hamma Saddam da Hamma Abdulrahima ma sun haɗa kai suna kallon wani abu a wayar Saddam ɗinm Hamma Abdullahi ne da Hamma Abdulrrahaman suma suke hiran su, Ammah ta yi shuru kawai tana tunanin Allah ya taimaketa ma ba ta da hawan jini amma da a halin da ta shiga na damuwar rashin Baffa da tana da shi da yanzu ta faɗi, Allah kuma ya taimaka daman ita ɗin Jaruma ce. Sun daɗe suna hira sai goma da rabi suka watse a bangaren Ammah. Su Hamma Abdullahi suka yi sallama suka tafi gidajen su Baɗɗo ta wuce bangarenta ita da mijinta haka ma Hamma Saddam Ummu Salma ta karɓi Banafsha ta shiga ciki itama Ammah ciki ta shiga ta yi shirin kwanciya. Sai da asuba Ummu Salma ta ga saƙon Hamma Lamiɗo. "Ammah za ta je Daura in sha Allahu." Kuma ta duba ba ta ga kiran shi ba, ita kaɗai ta yi ta tura baki tana kunƙuni ta yi kewarsa, kewarsa na murƙukusan mata zuciya da gangan jiki haƙuri kawai take yi sama da kwana ashirin ba ta gan shi ba Banafsha ba ta ji ɗumin babanta ba tunda ta zo duniya. Da gari ya waye ranar laraba kenan bayan ta yi wanka Ammah ta yi ma Banafsha wanka suka shirya. Breakfast Baɗɗo ta ba su ita ke girki tana ba ma Ammah yanzu Harira ce ke taya ta aikace aikace gida kamar shara ko wanke wanke. Tare da Baɗɗon suka fita zuwa wajen Saloon Ummu Salma ta yi driving ɗin su a motar Lamiɗo. Zuwa wani ƙaton shagon saloon suka je mai kyau booking Ummu Salma ta yi musu har da gyaran kafa za a yi musu Harira dai wanke mata gashin ta aka yi ta ce kitso za ta yi, ita ce ke renon Banafsha. Suna can shagon har bayan azahar an gama musu gabaɗaya suna ma shirin tahowa ne ma sai ga wayar Lamiɗo. Ta yi mamakin kiran shi da rana tsaka haka. Yanzu ba H. lamiɗo ba ne tuni ta goge ta mayar da shi Hamma na. Yanzu ma jikinta na rawa ta ɗaga kiran na shi cikin zumuɗi. "Hamma na." "Ranki ya daɗe." Ya faɗa cikin kasaitar shi wanda da yanzu kamar ma ya fi na da. Sai ta ji kunya, ita fa mantawa take yi da yanzu Hamma Sarki ne sai ta dinga ganin kamar komai bai sauyawa ba. "Ayi mini afuwa ranka ya daɗe" Ta faɗa tana mirmishi gefe ta koma tunda Baɗɗo ta ga tana dariya a fili ta furta mai Daura ne. "Kina ina? Received at 15:21Reactions: ❤ 14, 🥰 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Abin da ya faɗa kenan ta amsa masa da cewa suna shagon Saloon ita da Baɗɗo sai ya tambaya za su koma gida wuri ne? ta ce sun gama ma, ga su nan a hanya daga haka ya kashe wayar ta ɗauka ma za su yi magana ne jin ba ta gida shi ya sa ya kashe. Nan ta ce su tashi su tafi ATM ta ba da aka cire kuɗin masu yawa tunda speacial booking suka yi sannan mai tsada ne Saloon ɗin da aka yi musu. Sun taho ma suna hanya Ammah ta kira wayar Baɗɗo tana ta faɗan sun je sun zauna ta kira wayar Ummu Salma ba ta samu ba ahalin ta san ana jiran ta. Da Baɗɗo ta faɗa mata abin da Ammah ta ce sai da ta yi mamaki. "Ana jirana? Waye ke jirana? Ta tambaya cikin mamaki, lokaci ɗaya tana mayar da hankalinta wajen tuƙi. "Ban sani ba haka dai ta ce." "Ko baƙi kika yi? "To ƙila masu zuwa barka ne mu ƙarisa gidan" Suna zuwa gidan a waje Ummu Salma ta yi parking ɗin motar in wani cikin su Hamma Saddam sun dawo sai su shigo da ita. Suna shiga haraba suka ga wasu manyan jifa jifai baƙaƙen motoci guda biyu, ga dogari guda ɗaya da ɗan sanda sai wani mai suit. Mamaki ya kama su, Ummu Salma na ganin kayan jikin dogarin Daura ta faɗo mata arai sai ta kalli Baɗɗo tana faɗa mata baƙi ne daga Masarauta Suka rankwafa suna gaishe da Ummu Salma ta amsa sannan suka shiga cikin gida. Takalmin maza suka gani a ƙofar ɗakin Ammah takalmin mai kyau ne irin na masu Sarauta Ummu Salma ta kalli takalmi sannan ta juya tana kallon Baɗɗo. "Hamma ne" Ta faɗa da sauri kafin ta yi saurin faɗawa falon Mami har mayafin ta na yin ƙasa, Zuciyanta na bugawa, wanda take tunanin ganin shi ne ta gani, yana zaune a saman kujera cikin alkeybba da rawani ga wata sanda a hannun shi irin ta masu mulki, rawanin shi fari ne har bakinsa da hancinsa ba a gani idanuwansa ne kawai a waje. Ammah na gefen shi itama a saman kujera ta sadda kai ƙasa kwarjininsa da ƙamshin turaren sun cika falon gabaɗaya. Cak ta tsaya ta kasa gaba ballatana baya. Ba ta taɓa tunanin za ta ganshi a wannan lokacin ba. Baɗɗo da Harira suka shigo ai ganin shi ya sa Harira ta yi ƙasa tana gaisuwa. Baɗɗo ma ta rankwafa Sarki ne fa ba abun wasa ba ne. Allah ya sa Banafsha na bayan Harira a goye "Kika tsaya ma mutane a kai kuma." Ammah ta faɗa tana hararan Ummu Salma ganin ta tsaya kawai ta kafe Lamiɗo da idanuwana shima kallonta yake yi ta cikin rawaninsa yana jin zuciyarsa na yin ɗumi. Daman ya ce ba zai faɗa mata ba, bai yi tunanin zuwan na shi zai tabbata ba ne. Sai ga shi kuma ya tabbata irin yadda kewar Ummu Salma ya yi masa rugu rugu in zai furta ma ba za a amince ba. "Ki ƙariso ki gaishe shi, sun fi awa da zuwa kina can kun fita tun safe ba ku dawo ba." Ammah ta sake faɗa tana sake hararan Ummu Salama. Da ta kasa ma tafiya kafafunta na rawa itama ƙwarjini Hamma ya yi mata sosai sai ta ke jin sa kamar baƙo a gare ta. Da ƙyar ta samu ƙarisawa gaban shi, sai kawai ta ji ƙafafunta sun rinjayeta ta zube a gaban shi. "Hamma" Sai kuma da ta faɗa ta tuna da sauri ta rufe bakinta tana kallon Ammah dake hararanta. "Ranka ya daɗe." "Sannu da zuwa." Ta faɗa a rarrabe sai kuma ta sadda kanta ƙasa tana wasa da gefen mayafinta. Yana kallonta yana jin wani iri a jikinsa Ummu Salma ta canza ya ji daɗin ganinta ta yi kiba. "Mun same ku lafiya? Ya faɗa a ginshiƙe muryansa a kausashe kamaar yadda ya saba amma wannan karon a ƙasaice. Ta amsa da lafiya lau tana satar kallon shi. Ammah ta mike ta isa ga Harira ta karɓo Banafsha. Ta kai ma Lamiɗo har in da yake zaune ya karɓeta yana yi ma Ammah sannu tana ba shi ta bar bangaren daman Baɗɗo da Harira sun fice, suna bangaren Baɗɗo ita kuma Ammah sai ta shiga kitchen ɗin tsakar gida kamar za ta yi wani abu nan ko ba abin da za ta yi, ta ba su damar ganawa ne. Bayan fitan Ammah Lamiɗo ya ajiye sandar hannunsa a gefe ya riƙe Banafsha dakyau a cikin jikinsa yana kallonta barci take yi amma kamar ta sani sai da ta farka tana ta cilla kafafu irin na jarirai ya saka ɗan yatsan shi na hannun dama a cikin na ta yatsan na hannun dama yana kallonta da wani irin soyayya ta ɗa da mahaifi. Ummu Salma na zaune tana satar kallon shi tana mirmishi farinciki ya cika ta. Received at 15:21Reactions: ❤ 12, 👏 2 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Hamma ka daɗe da zuwa ne? "Shi ne ba ka faɗa mini ba? Ta gama fada har tana zumbura masa baki ya kalleta sau ɗaya ya kawar dakai in tana masa wannan shagwaɓar da za ta saka ya kasa riƙe kansa. "Tafiyar ce sai yau ta tabbata." "Na fara sauka a fadar sarkin Adamawa ne, ba daɗewa zan yi ba yanzu za mu tafi amma zamu biya gidan Gwamna kafin mu tafi." Ya gama faɗa yana sake wasa da hannun Banafsha dake hannunsa. "Na zo ganin ku ne." "Ke da takwaran Mami." Ya furta cikin wani irin amo, amon da ya shiga jinin jikinta ya sakar mata wani kasala. "Na gan ku." "Na ji daɗi." Ya gama faɗa ya ɗan kallon Ummu Salama. Itama shi take kallo cikin wani yanayi. "Come here." Ya furta yana cigaba da kallonta, sannan lokaci ɗaya yana nuna mata gefen shi, kamar daman tana jiran ya furta ta tashi da sauri ta ƙarisa gare shi ta zauna a gefen shi, tana zama ta rinjayi jikinta zuwa gefen kafaɗan shi lokaci ɗaya tana kwantar da kanta a kafaɗar na shi a saman alkeybban jikinsa da rawaninsa. "Na yi kewar ka." Ta gama faɗa tana turo hannunta ta sagalen hannayen shi ta riƙe shi, ga shi gidan ba kowa su Hamma Saddam duk suna wajen aiki. Kallonta ya yi ta cikin rawaninsa. "I miss you too.' A kalaman shi, ta ji gaskiyan abin da ya faɗa. Ta yi masa mirmishi, ta kalli Banafsha, dake hannunsa itama sai ta miƙa yatsunta suka sarke yatsun yarinyar a tare sau uku. "Ka ga takawaran Mami ko? Ta furta tana kallon shi, ya ɗan gyara zaman shi kaɗan. Ya saka hannu ya kama hannun Ummu Salma, sannan suka kama hannun Banafsha a tare suka jimƙe. "Na ganta. Kin iya haihuwa. Allah ya raya mana ita. Ubangiji ya yi mata albarka ita da sauran yan'uwanta gabaɗaya." Ta amsa da Amin Amin. Ummu Salma ta ga hannuwansu ya yi kyau sai ta kalle shi. "Hamma ina wayarka? Kafin ma ya yi magana ta ji tudun waya a jikin rigar saƙin dake jikinsa nan ta zura hannu a cikin akeybban ta zura can ta ciki ta ɗauko wayar. Ta ga akwai password kafin ta tambaya ya faɗa mata shekaran haihuwansa ne. Ta buɗe wayar ta ɗauki hannayensu hotuna, sannan ta yi musu selfie. Ta haɗe kanta tare da na Lamiɗo shi yana cikin rawani ta ɗauke su a tare. Sannan ta tashi tsaye ta ɗauke shi yana rike da Banafsha sai da ya gaji ya ce mata ta zo ta zauna sun kusa tafiya sannan ta haƙura da hotunan ta dawo ta zauna "Me kika za a dinga kiran ta? "Banafsha." Ya kalleta amma bai yi magana ba ta fara masa bayanin sunan mai kyau ne duk da ta faɗa masa ta chart wataƙila ma hankalin shi bai kai can ba. Tunda yanzu abubuwa sun ƙaru. "Banafsha." Ya maimaita sunan sai da gefe da gefen bakin shi ya motsa. "Nice name." "Sunan ya yi daɗi Baɗɗo ce ta zaɓa mata." Ya jita amma bai yi magana ba "Ba yau su Anty Bilkisu za su je Daura ba? "Su na can ma" Ta kalle shi cikin mamaki. Ta san dai a yau ɗin za su isa amma ta yi mamakin ashe sun isa da wuri. "Jirgin safe suka biyo." Ya sake amsa mata tambayarta tun kafin ma ta yi tambayar. "Allah sarki muma gobe muna tafe." Ya tambayeta tsarin tafiyar ta fara masa bayani. "Akwai jirgin da za ku bi da ƙarfe goma na safe, mutane ashirin kawai sauran akwai mota." Ta amsa mishi da cewa su Hamma Abdullahi sun ce a mota za su isa Daura ranar Jumma'a. "Me ya sa? "Sun ce suna son ganin gari." Ya ɗan jinjina kai. "Ba wata matsala? "Babu komai Hamma." "Are you sure? Ya sake tambayata sai ta amsa masa da cewa komai suna da shi sun siya. "Allah ya saka da alheri." Ya amsa da Amin a saman labɓan sa. "Ammah fa ta ce ba za ta je ba " "Na yi magana da ita. Za ku taho tare in sha Allahu " "Ta amince? Ta tambaya tana ɗan ware idanuwana. Ya lumshe idanuwana ya buɗe. "Uwata ce fa, za ta je ta sanya mini albarka." "Haka ne ɗan Ammah" Ta faɗa tana dariya hakoranta sun bayyana a waje ya shagala da kallonta. Itama shi take kallo zukatansu na fizgansu akan junan su. Ummu Salma ta bi shawaran zuciyarta ta barta ta rinjayi gangar jikinta sai ga shi ta na sumbatar gefen fuskar Lamiɗo, ya juyo ya kalleta ta sumbaci bakinsa ta cikin rawani. Ya kanƙance idanuwana yana kallonta. "Kar ki taƙale ni." "Ba anan ba." Received at 15:21Reactions: ❤ 12, 😁 2 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ya furta a rarrabe, ba ta ƙyale shi ba sai ji kawai ya yi ta tallabo kan shi ta zare rawanin ta yi kasa da shi, yana mata gargaɗi da idanuwansa ta yi kamar ba ta gani ba ta fara sumbatar bakin shi, shima kamar yana jira ya tarbi harshenta ya kuma saka hannu ya riƙe kugunta da hannu ɗaya, dayan hannun kuma ya riƙe Banafsha kar ta faɗi. Sai ga Mai Daura da Sarauniyar Daurama suna masu sumbatr juna cikin shauƙi da soyayya a falon Ammah, na sama da mintina biyar sannan Ummu Salma ta saurara ta lafe a ƙirjinsa tana mayar da numfashi. shima numfashin yake mayarwa a jere amma shi a saukaƙe yana so ya daidaita yanayinsa. "Kin cire ma Sarki rawani ko? Ya faɗa yana jin zuciyarsa na matsewa waje ɗaya. Yar dariya ta yi amma ba ta yi magana ba. "A gaban ɗiyata kike sumbata na Ummu Salama? "Muke sumbatar juna dai? "Kuma a falon Ammah na." "Ni ba ruwana, har da kai." "Sai da na ce kar ki yi. I warned you kafin ki fara." "Da na fara ai ba ka ture ni ba." "Kenan kana so? Ta faɗa tana kallon fuskar shi. "Ina so." "Sosaii.. ." Ya ja sosai ɗin yana jin wani iri, yana buƙatarta amma kuma ba lokacin hakan ba ne yanzu. "Ai Anty Bilkisu na nan yau." Ta faɗa tana ƙoƙarin danne yanayinta. Sai ya yi kamar bai ji ba ya kawar da maganar da cewa ta gyara masa rawaninsa ta saka hannu ta ja sama ta rufe bakin da hancin. "Ya yi? Kar Sarki ya ji kunya fa." "Ba wani kunya ya yi kyau, har ya fi ma wanda ka zo da shi." Ta gama faɗa tana danne dariyanta da gaske ya yi sakwa sakwa, tunda ya ga tana dariyan ya san bai yi kyau ba kawai ɗan girgiza kai ya yi bai yi magana ba. Tambayan shi take yi za a tafin mishi da wasu kaya daga nan ya ce no Need. Ita kam ta ce za ta tafi da wasu ya ce ta je da duk abin da take so. "Ranka ya daɗe ina so Asabe ta dawo bangarena in mun koma." "As you wish princess." Ta sumbaci ƙuncinsa tana sake yi masa godiya. "Mami sai jibi za ta taho daga Kaduna." "Mun yi magana da ita." "Mami ba ruwanta, ba irin Ammah ba ce. Na ce ga shi dai yau sila Mami za ta je Daura." "Saboda ke ce." Ya amsa mata kai tsaye. "Ba saboda ni ba ne." "A'a saboda ni da kai ne." "Ummu Salama." Ya kira sunanta ta amsa tana kallon shi. "Mami ce surukata. Ammah is my mother that's the truth" Ummu Salma ta fara dariya tana faɗin haka ka raba mana abin ya yi shuru ya ƙyale ta. kuma gaskiya ya faɗa Ita Mami a suriki ta ɗauke shi ba ɗa ba, Ammah ce uwarsa ba ta taɓa masa kallon suruki ba. Biyu har ta gota ya ce za su wuce a gidan Gwamnati za su ci abinci su yi salla daga can za su wuce. "Daga can Fadar Sarkin Adamawan aka tura aka ɗauke ku? Ya amsa mata da gyaɗa kan shi, miƙa mata Banafsha ya yi, sannan ya miƙe yana gyara alkeybban jikinsa Ummu Salma ta taya shi sannan ta ɗauko masa sandar shi ta miƙa masa. "Allah ya kara maka lafiya Hamma na " "Amin Sarauniya ta." Ya faɗa yana mai kallonta. Sai ya ware mata hannu suka shige jikinsa ita da Banafsha da hannu ɗaya ya ɗan yi tapping ɗin bayanta sannan ya duka ya sumbaci Banafsha. "Sai kun taho " "Sai mun zo ranka ya daɗe." Ta amsa masa suna mai sakin juna. Ya yi gaba tabi bayan shi yana fita ya zura takalmin shi, lokacin da suka iso dogarin da suka zo tare da jami'ai sun babbake za su shigo har cikin gida ya hana su nan ɗin gidan su ne, ba ya buƙatar nuna shi sarki ne, tafiyar daman cikin sirri ya yi ta, shi ya sa bai taho da tawaga ba. Mai martaba mai murabus ya ce ya je tare da Jakadiya ya ce ba sai ta je ba. Saleem ya bari da fada kafin ya dawo. Ummu Salma za ta yi fushi da shi, in bai zo ba kuma ko ya yi bayani ba za ta gane ba. Sai kuma ga daman zai kai gaisuwa wajen Gwamna da fadar Adamawa yanzu alaƙa ta ƙullu tunda ya zama Sarki ya zama dole ya fara sanin mutane sosai. Ammah na kitchen ɗin tsakar gida tun kafin Ummu Salma ta kira ta sai ga shi ta fito daman da hijabi a jikinta. Lamiɗo ya ce za su tafi yanzu. "Allah ya tsare Allah ya kai ku lafiya." "Amin Ammah sai kun zo." Received at 15:21Reactions: ❤ 15, 🥰 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta amsa da in sha Allahu Ya yi gaba yana tafiya cikin ƙasaita Ummu Salma na bin bayan shi amma sai ta lulluɓe mayafinta a saman kanta tana rike da Banafsha suka fita haraba dogari na ganin su ya taso ya tare su da Baban rigan shi. "Hattara dai, takawarka lafiya bajimi na al'ummar Daura. Barka da fitowar dogon sarki barka da fitowa farin Sarki ɗan Nasiru jikan Shitu Allah ya kara maka lafiya da tsawon kwana." Haka ya kare su suna tafiya har wajen mota da tuni masu kaki suka buɗe masa jeep ɗin guda ɗaya. "Hamma ba ka ga Saloon ɗin da na yi ba." A lokacin Ummu Salma ke masa raɗa ya kalleta ya ɗan murmusa amma saboda yana cikin rawani ba ta gani ba "In kin zo sai na gani " Ya amsa a hankali wanda ita kaɗai za ta ji. Ya kalleta ya ɗan rausayar dakai. Sannan ya shiga mota. Sai lokacin dogarin nan ya saki rigar sa. Ta yi baya tana ɗaga masa hannu dogarin ya shiga gaban motar Lamiɗo da direba a ciki mai suit ya buɗe get suka fita shi ɗayan jeep ɗin daman ta masu kaki ce sai da suka fita ya dawo ya rufe get ɗin sannan ta koma cikin gida tana mai farinciki. Wannan zuwan da ya yi ya gama wanke mata zuciya. Ko da bai zo ba, ba za ta yi fushi ba amma zuwan sa ya sa ta samu tabbacin Ummu Salama na da capacity. Lokacin da suka bar gidan Gwamna ya kira ta ya ce suna filin jirgi bayan la'asar lokacin ma Balkisu mai ƙunshi ta zo gida za ta yi musu tunda da safiyar gobe za su wuce Daura. Masu kunshi har biyu suka kira bayan Balki tunda su Adda Suwaiba sun taho gidan za a yi musu ga Maijidda za ta yi kitso har da Ammah za ta yi kitso ƙunshi ta ce ba ta so lallaɓe za ta yi su Adda Suwaiba na yi mata magiya. Kowa ya ji Hamma Lamiɗo ya zo sai ya yi ta mamaki haka ma su Hamma Saddan sun ciji yatsa da ba sa nan. "To ya kika gan shi? Hamma Saddam ya tambayam "Ya zama babban mutun ya kara ƙwarjini da Haiba." Ta ba shi amsa tana mirmishi. "Ya yi kyau a cikin rawaninsa." Ta faɗa tana wani lumshe idanuwana sai da Baɗɗo ta kai mata duka a baya. "Muguwa Sarauniyar garin Dauran kike duka.? "Gwara ta dake ki, kina neman suma saboda Lamiɗo" Adda Suwaiba ta faɗa ana ta dariya. Hamma Saddam na faɗin shifa ya gama shirinsa gobe sai tafiya ana ta dariya. Shi ya ɗauki Harira a mota ta je can gida ta kwaso ma Ummu Salma kayanta na masu amfani akwati biyu ta kawo mata, domin ta ce ba za ta bar kayan rikita maigida a Jimeta ba da shirinta za ta je Daura. "Sarki ne ba Yarima ba kuma haramu ne ki rikita Sarki." Baɗɗo ta faɗa tana dariya. "Ni ba Sarki na sani ba mijina na sani. Kuma in Sarki ne a fada ni a cikin bangarena ni ce Sarkin." "Capasicitated Autar Ammah" Adda Ummu Sulaim ta faɗa tana dariya har suna tafawa da Ummu Salma. A tsakar gida aka baza tabarmu ana ƙunshi Maijidda na ɗaki tana yi ma Ammah nata. Ƙunshi nan har dare ba a gama ba. Su Maijidda sai sha ɗaya na dare suka bar gidan sun sha kuɗi har Ammah an yi ma jan ƙunshi, Ummu Salma ja da baƙi aka yi mata ta yi kyau har ta gaji da kyau. Washegari da sassafe su Umma Balki da Umma A'i tare da ƴa'yan Umma Salamatu Adda Hauwa da Adda Khadija suka iso. Baffa Umaru sai da yamma za su taho tunda tafiyarsu sai safiyar Jumma'a. Jirgin ƙarfe goma ne kafin goman kowa ya hallara. Mutane ashirin ne daman za su bi jirgin. Tuni Ummu Salma ta tura ma Gimbiya sunayen masu tafiya a jirgi. Ammah, Ummu Salama, ga mutanen mubi mutum huɗu, ga Baɗdo su bakwai. Ga Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim, ga Ummin ikki ga iklima ga Kaltume ga Harira su goma sha huɗu, ga Adda Aisha suma da safen suka iso sai Hamma Saddam sai sai yaran Hamma Mustpha, Babban mai sunan Mami sai kuma Zainab. Su Adda Suwaiba a gidan iyayensu suka bar yaran su. Hamma Abdulrahim da su Hamma Abdullahi ne suka kwashe su zuwa filin jirgi. Kafin su tashi sai ga Shamsiya ta kira wayar Ummu Salma bayan sun gaisa ta ce Habib ya ba su izinin tahowa Daura. Ummu Salma ta ce su yanzu ma suna filin jirgi za su tafi akwai mota bari ta yi magana ta ji yadda ake ciki za ta kira ta. Baɗɗo ta ja gefe ta sanar da ita wayar su da Shamsiya. Received at 15:21Reactions: ❤ 10, 👍 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Ai ni da gayya na ce su zo, akwai mota na ji ba Umma Balki tana faɗin akwai matar Baffa Umaru da wasu matan ba, ki faɗa mata da sassafe ta je gida akwai motar da za ta ɗauko su, gwara ta zo ta fuskanci ke Sakin da Habib ya yi miki kamar gobarar Ummu Salma ce a garin Jimeta." Suka kwashe da dariya a tare har suna tafawa. "Ta ce wai har da ƙarin zuwansu ta ga Hanan" "Har uwar Hanan da uban Hanan duk za su gani." Baɗɗo ba ta da mutumci sai zaginsu take yi Ummu Salma na faɗin akwai tausayi ga talauci ga rashin haihuwa. "Ai bai kamata ma su haihu ba, sun wulakanta rai tun yana ciki fa." Haka nan Ummu Salma ta kira Shamsiya ta faɗa mata. Sun rabu akan za ta yi ma Hamma Abdulrahim magana amma su tabbatar da safe sun je gida tunda tafiyar mota ce, kayan da suka bari ma acan duk Hamma Abdulrahim ɗin ne zai tattara in ta su Hamma Abdurrahaman ne ƙila sai sun iso sannan za su tuna da wasu kaya ma. Sabbin ɗinkunanta kuma Mami ce za ta taho mata da su a gobe ba su ɗau kaya ba akwati ɗaya ne da jaka, kowa ka gani karamar jaka ce tunda ba daɗewa ba ne. Bayan tantancewa, suka hau jirgi sai katsina misalin sha biyu saura suka sauka Katsina Tawagan da za ta ɗaukesu tuni suna jiran su a filin jirgi. motoci sama da goma har da masu kakin masarauta ga dogarai da hadimai mata an taho da jakadiya a cikin masu tarban su. Sun isa Daura da azahar ne lalle Masarauta ta sha gyara ko'ina na ƙyalli an sauya ma tsarin Masarautar gabaɗaya. An haɗe shashen Mai martaba da bangaren Yarima rabi, rabin kuma aka shigar da shi a wani bangare na dabam. Bangaren Gimbiya Shahida nan ne bangaren da Bilkisu ta sauka. An sake faɗaɗa shi kamar ba bangaren ba. Sannan bangaren Gimbiya Hadiza an haɗe shi da na Gimbiya Maimunatu, an ɗiba an faɗaɗa bangaren. Na Gimbiya Amratu ma an sake faɗaɗa shi an kuma sake fitar da wani bangare na dabam ga shashem Fuani ma an gyara shi, ga na hadimai da bangaren madafi komai dai ya samu kyakyawan sauyi. Tawagan mutanen Jimeta kaf a bangaren Ummu Salma suka sauka zai ishe su. Daga Umarnin Sarki Hadima Tani ta jagoranci Ammah da su Ummin ikki zuwa masauƙin baki a cikin masarautar. Adda Safina a bangaren Bilkisu ta sauka su tun safe suka iso, tana jin yan Jimeta sun zo ta baro can tunda shima can ya cika da dangin Bilkisu ya'yan sarakuna ana ta baza capacity. Bangaren Fulani akwai baƙi nan ne su Hajiya Kilishi da iyalansu suke sauka, suna ta shirye shirye. Ƙannen Lamiɗo kuma duk sun iso suna can gidan Sarki mai murabus. An kawo masu abincika kala kala da ababen sha, komai ga shi nan ne kawai. Komai sabo ne a bangaren nan Baɗɗo na faɗin sabon Sarki sabon Masarauta. Yaran su Hajiya Kilishi sun shigo bangaren Ummu Salma sun yi musu maraba tare da ganin Banafsha. Ba su kuma ga Maimartaba Lamiɗo ba sai dare ya je can bangaren da aka sauki su Ammah ya gaishe su, suna tare da su Hamma Kabiru da Saleem su Yazid ba su zo ƙasar ba suna jin haushi. A daran Mai martaba ya ba da umarnin son ganin Ummu Salama da Banafsha a bangaren shi, lokacin da ta je bangaren sai da ta saki baki. Bangaren ya haɗu a cikin bedroom ɗin Mai martaba gadon sa mai rumfa ne da wasu labulaye na alfarma. Ta zo kenan Banafsha kawai ya ɗauka sai ga Bilkisu kuma taki fita Ummu Salma na son rumgumar mijinta ba hali. Sun gaisa da Bilkisu sama sama kamar yadda suka saba. Kowa ya kalli ɗan'uwansa ya kauda kai, Bilkisu ta ga Ummu Salma ta yi mata wani kyau, itama Ummu Salman kyan Bilkisun ta gani ga shi kowacce ta sha ƙunshi ta yi fes. Lamiɗo ne ya miƙa ma Balkisu Banafsha ta ɗauketa daman lokacin da suka iso ba ta shigo ba yaran ne suna isowa suka yo bangaren tun ɗazu saboda Banafsha. Ta ɗauketa ta yi Allah ya raya ba wani kasarsashi. Ummu Salma ta karɓi ɗiyarta, ta koma bangarenta tana jin haushi da kishi amma ba ta bari ya yi tasiri ba. Bilkisu kuma har ta ji haushi ganin Ummu Salma a bangaren Mai martaba sai yanzu ta dawo cikin hayyacinta har abada fa ba za ta so kishiya ba. Received at 15:21 7 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Washegari da safe bayan sun yi wanka sun karya. Mai Martaba ya ba da mota aka ɗauki su Ammah da Ummu Salma zuwa gidan tsohon Sarki suka gaishe da Mai martaba da Fulani tare kai masa Banafsha. Ya ɗauketa ya yi mata addu'a daga karshe ya ce Allah ya yi ma Batula albarka aka amsa da Amin. Ba su daɗe ba suka dawo su Hamma Abdullahi tun shidda na safe suka kamo hanya motar daman tun a daran jiya ta isa Jimeta, irin doguwar motar nan ne ta masarauta lafiyayya. Tare da su Shamsiya da matar Baffa Umaru da wasu cikin yaransu mata. Mami kuma sai da yamma suka iso Daura, mota ta je filin jirgi a katsina ta ɗauko su. Sai ga Hajiya Fatima Baba ta sake saka kafafunta a garin Daura. Garin da ta ji ya fita ranta ta tsane shi sama da shekaru talatin da biyar ba ta taɓa tunanin za ta dawo ba. Ta fita cikinsa cikin ƙunci da kuka ɗauke da Lamiɗo cikin jinin haihuwa yau ga shi ta dawo a matsayin uwar Sarki kuma surukar Sarki. Ubangiji mai yin yadda ya so a lokacin da ya so. Mami ta zo da ɗinkunan da aka yi ma Umma Salma rantatsu masu kyau, Sun iso ba daɗewa sai ga Hajiya Zeenatu da Hajiya Zannura sai Hajiya Binta tare da zugan yaran su manyan mata sun shigo bangaren Ummu Salma ganin Banafsha suka haɗe, ba sai an faɗa maka ba kana ganinta ka ga fuskar Lamiɗo. Balle ma Hajiya Binta ta faɗa musu tunda har da ita aka je Kaduna aka taho da Ummu Salama. Mami ba ruwanta sun gaisa sama sama sai juyi take yi cikin wani leshi wuyanta da hannayenta gwalagwalai ne kowa ya ganta ya san ta wuce tsara ga Islam da ta zama budurwa yanzu tana ma SS2 ne, har Faruk ya girma. Ammah suna can bangaren da aka sauke su da Mami ta je sai da ta yi magana. "Son kai, wato masauƙin uwar Sarki ma na dabam ne." Ammah ta ce ya son ranta su Umma Balki na ta yi musu dariya. Mami na faɗin ta ji ba komai da ka haifi Sarki ai gwara ka haifi matar Sarki Ammah ta amsa ta da cewa gwara ka haifi Sarkin. Suka bar su Ummin ikki da yi musu dariya. Gaskiya Mami ta faɗa domin masauƙin da aka sauki su Ammah ya haɗu, Hamma Jibo ma a ranar ya iso tare da Adda Nauwara. Adamawa da Jimeta sun haɗu a waje daya sai son barka. A kuma daran su Hamma Abdullahi suka sauka bayan mangriba. Suma a wani kayatattacen masauƙi aka sauke su gabaɗaya mazan, matan kuma aka kai su can wani masauƙin su Shamsiya Ummu Salma ta ce aka wo su bangarenta. Komai suke buƙata ga Hadimai nan motsi kaɗan za ka yi za a yi maka abin da kake so. Asabe tuni ta tare a bangaren uwar ɗakinta sun haɗe da su Harira. Washegari safiyar asabar aka tashi da shagalin bikin naɗi tare da shagalin sunan Fatima Banafsha. Ranar Ummu Salma na da kwana talatin da ɗaya da haihuwa A fada aka yi taron naɗin gwamnoni sun zo, sarakuna da yan majalisu yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati malamai da dattijan gari duk sun zo Hafiz ya zo tare da Salima sannan ya yi magana da wasu daga cikin yan'uwan su suma sun taho. Fadar Daura ko na ce Masarautar Daura ta cika da mutane ta dumbatsa ga masu kaɗe kaɗe da masu buga tambura. Masu busa da maroƙa a cikin waɗanda suka zo har da mawaƙan mu na arewa. Fada ta cika da busa sarewa da kaɗe kaɗe na tashi a status ɗin Hamma Saddam Ummu Salma ta fara ganin farin Sarki mai farar zuciya Ya sha rawaninsa fari alkeybbansa ma fara ce mai zanen baƙi haka yana zaune a fada a saman kujeran ƙaragar mulki ga manyan ƙasa ne zagaye da shi wasu a saman kujeru ga walikan fada kuma suna zazzaune a ƙasa.Har da tsohon Sarki mai murabus a wajen shima yana zaune akan kujera cikin kayan Sarauta. Suma a cikin gida kowa ya yi wanka ya yi shigar alfarma, Fulani da kaf matan Maimartaba da ƙannen Lamiɗo suna gidan su Hajiya Sakeena mutanen England duk sun zo ƙasar saboda taron naɗi nan. Kowa ka gani da ɗanƙareran leshi da gwalai gwalai a wuya da hannaye. Ummu Salma ma leshin ta saka mai kalan ja ya yi mata kyau ɗinkin bubu ne, wuya da hannaye gwala gwalai na ƙyalli, sannan Banafsha ma ta sha kayan alfarma. Received at 15:21 7 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ba su fita Fada ba sai gobe za a je a yi ma Sarki gaisuwa ta musamman amma a cikin gida an sha shagali a fada kuma acan an yi jawabai daga manyan mutane da wakilan fada har Sarki mai murabus ya yi jawabi haka ma sabon Sarki. Ga shi nan su Hamma Saddam suna ta ɗorawa a status ɗin su. A cikin gida kuma an yi busa manyan mata suna ta rangaji cikin kasaita da izza, an ci an sha abincika ba nau'in da babu ga shi an yi sevinors abin rabo an yi jakunkuna da hoton Mai martaba Lamiɗo, ga littafi mai biro, ga jakunkuna an yi mug da cokali an nannaɗe a kwali, an raba atamfofi iri ɗaya sak ga turarukan wuta, ga azkar ƙananu da aka rarraba ga key holder abin rabawar ne ba adadi ga su nan. Ummu Salma ta shiga ta fita, kuɗi ko wata ƙwarya ce sai da aka cika mata shi da kudaɗe, ga gefen gadonta ya cike da kaya wasu ma akwatina ne guda suke kawowa kuɗi kuma daga masu saka milliyan sai masu dubu ɗari biyar. Arziki na in da yake, Shamsiya ta ga duniya a Daura suna gefe amma babu abin da suka nema suja rasa suma. Habiba kam ta ruɗe faɗi kawai take yi Allah ya azurta su, sun ga Hanan sun saka leshi iri ɗaya da Beena yara ne amma gwal ne a wuyansu da hannayensu. Hanan ma kaɗai abin a tsaya a kalleta ne. Ba ma Ummu Salma ba Shamsiya sai hawaye a ɓoye, Ubangiji ya yi ma Ummu Salma kyakyawan sakayya. Bilkisu ma ta yi shirgar alfarma itama leshin ne mai tsada daman ga ta yar gayu sai kuma ya haɗe da yau Gimbiya take shiga kawai take yi tana fita. Dangin ta sun shigo bangaren Ummu Salma sun ga Banafsha itama ta zo ta rako Umman kano yau suka zo kuma a ranar suka koma. Kowa ta kalli yaruwanta ta kawar da kai. Cikin su ba wacce za ta ce ba ta ji kishin yaru'wanta ba. Umman Kano dubu ɗari biyar ta ba ma Ummu Salma, kuɗi akwai su ba ma ajin zafin fitar da su Ammah suna bangaren su tare da su Ummin ikki suma can Hadimai na kula da su. Washegari kuma baki suka kai gaisuwa fada ga Sabon Sarki yau ɗin ma farin rawani ya saka yana zaune akan ƙaraga dukkansu har da Bilkisu da yara suka fara zuwa suka kai gaisuwa, fadar ta cika da mata da maza sai ga Mami a fada tare da Ammah Lamiɗo na zaune kan ƙaraga Sarkin dogarai na faɗin Sarki ya amsa Sarki ya gaishe ku. Ga su Hamma Jibo a gefe a zazzaune abu kamar a mafarki kuma a zahiri ne. Lamiɗo na zaune ya hakimce ko iya ɗaga idanuwana baya yi saboda Sarauta da ƙasaita. Ubangiji ne in ya ce kum ya fakum ba wanda ya isa. An yi hawan dawakai. Sarki ma ya hau farin dokinsa ya zagaya cikin gari ya dawo tare da tawagansa sannan Bilkisu Gimbiya ta sauke shi a saman doki. An yi ma Bilkisu naɗin Gimbiya bayan an saka mata alkeybba ita kuma Ummu Salma aka saka mata alkeybban a matsayin Sarauniyar Daurama. Da yamma kuma Mami ta ce a kaita gidan Sarki Mai murabus ta duba shi, aka ba da mota aka kaita ita da su Islam da Hajiya Falmata tunda gobe baƙi za su yi halin su. Yau ga Mai martaba tsohon Sarki Nasiru ga Fatima Batula sun haɗu a garin Daura ba a matsayin mata da miji ba, sai a matsayin Baba da Mama, iyayen Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo su Gimbiya Maimunatu sai kallo domin dai yanzu sun san kishin Fatima ma ba shi da amfani tana da mijinta. Fulani ta yi mata karɓa na karramawa sosai domin ita tun bayan abin da ya faru komai ya wuce a matsayin y'a ta ɗauki Mami. Da za su tafi Tsohon Sarki ya yi ma Faruk da Islam kyautar kuɗaɗe Fulani ma haka ta yi musu kyauta haka Hajiya Falmata ma ta samu farar takarda cike da sabbin kuɗaɗe. Ranar litini baƙi suka fara watsewa. Mami ta riga kowa tafiya Daddy ma da ya zo a ranar asabar ya koma. Tawagan mutanen Adamawa duka jirgi Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ya ɗau nauyin su har da su Shamsiya da kowa da kowa. Kowanne da abin arziki bayan abin rabo ga kuɗaɗen da Masarauta ta raka su da shi. Ammah kuma tsohon Sarki ya sake biya mata kujeran Makka za ta sake komawa ta sauke farali. Su Hamma Jibo duk sai da suka je suka kai gaisuwa kafin su tafi. Received at 15:23 13 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Aka bar Ummu Salma da Banafsha da tarin dukiyar da suka tara. Tun da suka tafi Hadimai suke gyaran ko wani bangare. Ba su kaɗai ba har sauran dangin su na Daura suma sun koma da sha tara na arziƙi sai a lokacin suka ga Mami wasu ma ba su santa ba sai dai labarinta. Waɗanda suka santa ɗin iyayensu ne sun kuma rasu sai yara da jikoki an yi zumunci kuma sun ji daɗi kwarai. Sun tafi sun bar Daura da Sarkin su Muhammad Lamiɗo da matanshi tare ya'yan shi a cikin Masarautar Daura in da za su fuskanci Sabuwar rayuwa. *Janafty* Received at 15:23 12 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby *FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.* 08032773332 09069067488. Alhamdulillah baƙin da suka zo Daura duk sun koma gidajensu cikin ƙoshin lafiya da aminci kowa na ta son barka tunda sun koma gidajensu da sha tara na arziƙi sai dai fatan Allah ya ta ya Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo riƙo Ubangiji ya ba shi sa'a ya kuma tsare shi. A satin kaf duka platform na social media da manyan bloggers ɗin arewa hotunan Lamiɗo ne kawai ke yawo cikin shigar Sarauta ya yi kyau har ya gaji da kyau saboda shi ɗin mai kyau ne, yan comments section na ta faɗin albarkacin bakin su mafi yawancin su dai suna yabon kyau da zati ne irin na sabon Sarkin Daura wasu kuma suna masa laƙabi da matashin Sarki, suna ganin cancantarsa wasu kuma suna ganin kamar shekarunsa sun yi ƙanƙanta kowa dai na faɗin albarkacin bakinsa ba tunda ba wanda aka hana faɗin ra'ayinsa. Ummu Salma ta kira duka danginta da suka zo ta yi musu bangajiya da godiya. Ita kaɗai a bangarenta daga ita sai Harira sai Asabe da Banafsha Hanan na can bangaren Bilkisu ita da su Sultan da Beena amma kusan a bangaren Ummu Salma suke yini saboda Banafsha. Daman ita Ummu Salma ba ta ce za ta karɓi Hanan ta dawo bangarenta ba. Ta san Lamiɗo ba ya son a raba ko makwamcin Beena da Hanan  ne kuma tunda Bilkisun ba ta nuna komai ba ta cigaba da zama a can ba za ta taɓa mgana ba, a baya ma ta zauna tare da ita kuma ba abin da ya same ta ballanta ma yanzu da suke ƙarƙashin rufi ɗaya na gida ɗaya. Tuni Mai martaba Lamiɗo ya miƙa a mulkinsa ya yi sabon naɗe naɗen hakimai ya sauya wasu sarakunan ƙauyaku sannan ya sauya masu sarautunsu. Sannan an ƙaro hadimai da dogarai tare da dirobobin masarauta. Ummu Salma an ba ta hadiman bangarenta sai ta naɗa Harira a matsayin shugabansu ita da Asabe. Bilkisu kuma daman Debora da Anitha sun taho bayan taron naɗi ta tabbata dai ba za ta barsu ba suma kuma ba za su barta ba, sun shigo har bangaren Ummu Salma sun gaisheta sun kuma ga Banafsha Debora ke faɗa ma Ummu Salma James da Baban Adila na can Lagos za su kula da gidaje da motocin dake can. Ummu Salma ta san daman ba za su tafi ba, yadda suke jin daɗin aiki a ƙarƙashin Hamma Lamiɗo ta san ko da suma sun amince zai ce ne su taho Masarauta su cigaba da aiki can ɗin ma da za su zauna ba duk wata suna da albashi sauran buƙatunsu ma ba zai taɓa gajiyawa ba. Kamar maigadinsu na Jimeta ne, shima aikin shi kawai ya kwana ya kula da gida amma tarin alherin da yake samu ta hannun Lamiɗo ko wani ma'aikacin gwammati sai haka. Tuni Masarautar ta ragu, baƙi duk sun koma gidajensu har da na ƙasashen waje da suka taho. Yau sati ɗaya da yin taron naɗin nan, kimanin kwana talatin da takwas da haihuwan Ummu Salma saura kwana biyu su yi arba'in ta dage da kula da jikinta kamar yadda Mami ta faɗa mata in dai suka yi waya sannan ta dage da shan magungunar wajen Surayya Halin yau, domin ta kame ta yi tsam yadda Mai martaba zai manta cewa ta haifi Banafsha. Ita tun da aka yi taron naɗin  ba ta je bangaren Mai martaba ta kwana ba, ta kan je da safe kafin ya fita fada ta gaishe shi ta kai masa Banafsha wani lokacin kuma sai da daddare in ya shigo ta aiko jakadiya ta yi mata iso, in kuma ta je ba ta wani daɗewa take dawowa bangarenta duk da ta yi kewarsa amma tuna tana jego ya sa ba ta yi tunanin kwana a wajensa ba. Ta ɗauka Bilkisu na zuwa wajensa ganin bai taɓa mata magana ba, a tunanin ta ya san in mace ta na jego in tana da abokiyar zama ta kan ɗan ɗaga kafa da zuwa turaka amma ba addini ba ne al'ada ne kawai. Shi kuma ya na ganin ba ta kwana a wajen sa in Bilkisu ta yi kwana biyu, ba ta sake zuwa sai bayan kwana biyu a tunaninta yana tare da Ummu Salma ne, shi kuma ba ta zuwa ko ma ta zo sai ya ga ta tafi ba ya son dogon magana ko tambayoyi shi ya sa bai tambaya ba. Sannan ga sha'anin mulkin da ya yi masa tsaye a rayuwarsa. Duk yadda ba ya son mulki sai da ya zo ya sarƙe shi a lokacin da bai yi tunani ba. Received at 19:42 12 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Duk yadda ya kai ga hasashen wahalan mulki ashe wasa yake yi sai da ya gan shi ya ciki ya tabbatar da wahalansa ya fi hasashensa yawa. Tunda Mai martaba tsohon Sarki ya yi murabus bai kwanta tun daga dare har wayewar gari yana barci ba, bai samu kebewa da iyalansa tun daga safe zuwa yamma ba. Bayan an yi taron naɗi kuma ba shi ma da lokacin kansa yana ta ganawa da sarakunan ƙauyaku da malamai da dattawan gari sannan jiya ya fita sun je wani ƙauye nan kusa da aka samu barkewan cutar amai da gudawa a dare ɗaya yara goma sha suka rasu, yau ɗin ma sai da yamma ya dawo fada ya biya wajen Mai martaba tsohon Sarki domin ba ya gudanar da komai sai da shawaransa kuma yana ganin amfanin haka. Sai dare ya baro fada sun ci abincin dare tare da wakilan fada da Saleem da tare suke yini a fada, Mai martaba Lamiɗo ya yi masa masauƙi a cikin Masarauta wani lokacin ya kwana anan wani lokacin kuma ya koma gida, ya gama karatunsa yanzu aiki kawai ya ke jira, daman ya yi degree ɗin sa da farko ya dawo gida ya yi service sai ya koma domin ya haɗo masters ɗin shi yanzu kuma ya gama shi ya sa ya dawo gida. Goma da wasu mintina ya iso bangaren shi. Ya yi wanka ya saka sauƙaƙun kaya duk yadda ba ya shiri da zafi yanzu ya fara. Tunda yini yake cikin manya kaya da rawani. Ya ƙoshi tunda sun ci abinci amma sai ya ji yana marmarin shan ruwan zafi a daran nan kafin ya kwanta kuma ma a ce Ummu Salma ce za ta dafa masa, ya samu saƙon ta, ta hannun jakadiya kuma itama ta yi masa test messages ta faɗa masa tana son a kawo mata kayan abinci a store ɗin bangarenta da cefane za ta dinga girki da kanta. Ya ba da umarnin a yi mata yadda take so yana marmarin girkinta bakin shi na buƙatar ɗanɗanon abincinta da ya daɗe bai ci ba, sannan kuma ya yi kewarta, hirarta kawai yake so ya ji kafin ya kwanta ya rasa me yasa take gudun sa? Kwana biyu Bilkisu ke ɗebe masa kewar dare, to kuma kowa da abin da ya iya, ita ba ta iya hira ba shi kuma yana so a yi masa hira ya saurara ko da ba zai yi magana ba. Ba faɗa masa ta yi ba ya fahimci ta ɗauka Ummu Salma na zuwa ne shi ya sa in ta kwana biyu sai ta ɗauke kafa sai bayan wani kwana biyun bai taɓa faɗa mata ai Ummu Salma ba ta zuwa ba, bai cika magana ba sannan ba ko wani ƙaramin abu ke saka shi magana ba. Wayarsa ya ɗauka ya kira Ummu Salma a jiya Bilkisu a wajensa ta kwana yana sane yau ba za ta zo ba. Ita kuma Ummu Salma a waya suka gaisa yau jiya ne kaɗai suka haɗu da safe da ta zo gaishe shi ita da Banafsha. Wayar har ta katse ba ta ɗauka ba, sai ya ƙyale ta a tunanin shi ta yi barci kamar ko ya sani ta yi barci domin da wuri suke kwanciya yanzu. Cikin barcin ta ji kiran wayar ta dake gefenta ko da ta farka wayar ta katse tana dubawa ta ga Hamma na sai ta watsake ta bi bayan kiran na shi. Lokacin Bilkisu ya ke so ya kira ta kawo masa coffea mai zafi, yana so ya sha kafin ya kwanta. Wayar ta shiga ta ɗauka ta fara gaishe shi kenan kiran Ummu Salma ya shigo a waiting call yana dubawa ya ga ita ce sai ya fasa faɗin abin da yaso ya faɗa. "Kuna lafiya? How are my childreen? Ta amsa masa da suna lafiya, ɗazu ma suna tare da Sultan wani lokacin yana zama tare da shi a fada, ko kuma in zai je can wajen Mai martaba tare suke tafiya. Beena ce da Hanan jiya da Safe sun taho bangaren shi, su ne yake yini bai gan su ba. Ya sauya maganarsa da cewa ya kira ya ji lafiyarta ne da ta yara ta ji daɗi. Daman tana zaune da waya ne amma tana tunanin shi yana can tare da Ummu Salma duk da abin ya fara mata sauƙi zafin kishin yana raguwa tunda Umman Kano ta ce ta dage da addu'a yanzu da za ta ga Ummu Salma ta ji zuciyarta ta fara zafi yanzu za ta fara kiran sunan Allah, sannan tana yawan addu'an Ubangiji ya rage mata zafin kishi tunda dai ta fahimci Ummu Salma ba za ta bar mata Lamiɗo ba gwara ta koyi yadda za ta rayu da ita a matsayin kishiyarta sai dai har abada ba za ta so ta ba. Received at 19:42 6 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ya zura mata idanuwana yana kallonta. Sai ta sadda kanta ƙasa. "Hamma kar Anty  Bilkisu ta zo ta ganni ba daɗi." Ya yi mata wani kallon ƙasa ƙasa sannan ya ɗauke kansa kamar bai ji abin da ta ce ba. "Ya aikin? Ka gaji ko? Nan ma bai amsa mata ba. "Na yi kewar ka Hamma " Ta faɗa cikin shagwaɓa, kuma da gaske ya ji kewar shi a muryanta da ya kalleta sai ya ga idanuwanta har sun fara tara kwalla yana kallon fuskarta yana mai nacin kallonta kamar ya daɗe bai ganta ba yana jin zuciyarsa na warwarewa a kanta. "Da gaske na yi kewar ka." Ta sake faɗa tana lamgwaɓe masa kamar wata karamar yarinya. "Yanzu bana ganin ka sosai, ka zama na mutane ba na Ummu Salma ita kaɗai ba." Ta gama fada tana masa fari, sai da ta kusa saka shi dariya ya yi maza ya kame Hattara dai Sarki ne fa. Mug ɗin hannun shi ya ajiye a saman teburin dake gaban shi na tangaran. Ta janyo jikinta zuwa wajen kafafunsa ta kama da duka hannuwanta ta rumgume a ƙirjinta "Yaushe rabon da mu yi hira! Hammaaaaa" Ta ja sautin sunan sai da ya ji a zuciyarsa jikinsa ya ɗau ɗumi ta saka kanta a tsakanin kafafunsa kamar wata yarinya. "Har na fara rama saboda rashin ka." Ta gama faɗa tana sake tusa kanta a tsakanin kafafunsa nenan ta birkita shi take yi, ya yi saurin matse kafafunsa ya saka hannu ya jawo kanta sai kawai ta ɗora kan a saman kafafunshi tana sauke masa ajiyar zuciya. "Hamma." Ya ƙi magana ta sake kiran shi. "Hamma na." Nan ma ya yi mata shuru kawai. Ta ɗago tana kallon shi ya  ɗauke kansa sama yana wani ginshiƙa. "Hammaaaaaaaaaa." Ta ja sautin sosai sai da ya kalleta bai shirya ba. Sai kawai ta tashi ta haye saman cinyarsa ta yi ɗare dare "Hamma." Ta sake kiran shi tana tallabo fuskar shi, suna kallon juna cikin idanuwansa. "Hamma" "Ummu Salama." Ya kira sunanta cikin ƙosawa. "Ni dai ka amsa." "Me? "Hamma na." Sai da ya ɗan juya bakin shi yana so ya yi dariya cikin zuciyarsa ya na jin salama. "Na'am" "Shike nan? Ya faɗa yana kafe ta da idanuwana, sai ta yi masa mirmishi ta sumbaci bakin shi. "Ba ka yi kewata ba ne? "A'a." Ya bata amsa kai tsaye ta kalle shi ta yi masa narai narai kamar za ta yi kuka. "Ni ko? "Ba komai to." Ta gama faɗa tana ƙokarin sauka daga kafafunsa ya sanya hannu ya jawo ta, ta faɗo saman ƙirjinsa ya rumgumeta da tattausan hannayensa zuwa faffaɗan kirjinsa a tare suka sauke numfashi, kowa na jin zuciyarsa na ɗaukan ɗumi na rashin ɗan uwansa sun jima a haka suna jin bugun zuciyoyin junan su. "Hamma." "Uhm." "Ina son ka." Sai ya yi shuru kafin ya ɗan gyara kafafunsa. "Kin daina sona yanzu? Da sauri ta kalle shi "In ji waye? "In ji ni." Ya amsa mata kai tsaye. "Tunda na zama Sarki. Kin fara guduna." Ya faɗa yana kafeta da idanuwana ta zaro idanuwana tana kallon shi. "Yes" Ya faɗa yana kara haɗe rai, har yana wani ɗauke kansa "Yaushe ne na guje ka? "Ba ga shi nan ba kin taɓa zuwa kin kwana a waje na tunda kika zo? Ya tambayeta yana kafe ta da idanuwansa masu sanyata kasala da mutuwar jiki. "Au wai daman shi ne kake magana." Ta faɗa tana rufe baki, ya balla mata harara amma bai yi mgana ba ta kwashe masa da dariya sai ya yi fuska bai sake kallonta ba. Ta rumgume shi tana faɗin" Hamma ma ina sonka abadan abadan har ƙarshen numfashina." "Sweet mouth." Ya faɗa yana ƙokarin cire ta daga jikinsa. "Zo ki tafi,." Ya faɗa a hankali ta maƙake masa yana so ya ɗago ta tana ƙara ƙamƙamesa. Sai ya ƙyaleta sai don kanta ta sake shi tana shafa sajen shi. "Ranka ya daɗe." Ya ƙura mata idanuwana zaman ta a saman jikinsa har wani kasala ya sakar masa. Ta kama hannuwansa ta damƙe a cikin na ta. "Hamma." "Saura kwana biyu na yi arba'in." Bai tambaya ba amma yanayin kallon da yake yi mata na neman ƙarin bayani ne. "Kasan in mace ta haihu a al'ada sai a ce sai ta yi arba'in sai ta koma ma miji, balle ni tunda ga Anty Balki shi ya sa ka ga ba na zuwa amma ba gudunka nake yi ba." "To mene ne? Ya tambaya yana kallonta. "Ba ka gane ba? Ta tambaye shi tana kallon shi. "Ai ba umarnin Allah ba ne" Ya ba ta amsa kai tsaye. "Ke da al'ada kuke rayuwar aure ba addini ba? Received at 19:42 12 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Wa ya ce sai an yi kwana arba'in? "Haka fa ake yi, ko su Ammah da Mami duk haka suka yi." Ta ba shi amsa tana masa shagwaɓa. "Ba dai Ammah na ba, da na zama ɗan gata da ace zan samu rabin abin da Ammah take yi ma Baffa." Kai tsaye ya yi maganarsa ta saki baki tana kallon shi. "Ammah is a good wife. Ba ta taɓa barin kusa da Baffa ba. Da a ce Ammah ce ta riga Baffa rasuwa da har abada ba zai samu kamarta ba." "Hamma." Ta kira sunan shi. "Ba wani Hamma, ba haka Ammah ke yi ba sai dai in Mamin ki." Ya gama faɗa yana wani daƙuna fuska, dariya ta so kamata ganin ba wasa ya sa ta danne dariyanta. "To na ga ina jinin haihuwa ne fa ga kuma ga Banafsha" "To me zan miki? Ummu Salma kawai na ganki a kusa da ni a feel safe " Yadda ya yi maganar daga ƙarƙashin zuciyarsa ne sai da jikinta ya yi sanyi. "Sorry." "Ka yi haƙuri." "Kuma ba ki faɗa mini ba, kawai ba kya zuwa wajena." "Kin kyauta? "Ban kyauta ba." Ta yi saurin amsa mishi tana wani lamgwabe kanta. "Ban kyauta ba, ba zan ƙara ba." Ya yi mata shuru, yana kokarin cewa ta ɗaga shi, ta zo ta tafi dare ya yi. "Anan zan kwana." "A'a ni bana so." Ya amsa mata ba wasa a maganarsa. Ya miƙe tsaye tare da ita, ya juya ya ɗauko mata Banafsha, ya miƙa mata ta karɓa tana kallon shi. "Hamma." "Na ce fa ka yi haƙuri." "Na haƙura" "Ki bari sai kin yi arba'in." Ya sake jadadda mata, kuma tunda ya furta ba zai sauya magana ba, sai kawai ta juya ta wuce ya bi bayanta har bakin bangaren shi sannan ya ba ma dogarawan dake gadin bangaren shi umarnin su yi mata rakiyar har sai ta shiga bangarenta suka amsa masa da girmamawa. Sai da ta shiga bangarenta sannan suka koma, ta damu da fushin Hamman nata, da ta koma kafin ta kwanta sai da ta tura masa saƙon ban hakuri bai ba ta amsa ba a chart ma ta ga yana online ta yi masa saƙo bai buɗe ba sai ta ƙyale shi. Kuskurenta ɗaya da ba ta faɗa masa ba, ita ina ta san bai sani ba amma abin da ya ba ta mamaki Bilkisu ba ta zuwa ne? Ta so ta tambaye shi, sanin ba zai amsa mata ba shi yasa ba ta tambaya ba, sanin halin shi ba ya tattauna duk abin da ya shafi Bilkisu da ita, itama ba ta damu da ta sani ba, gwara haka kowa ya tsaya iya matsayinsa. Washegari da wuri suka yi wanka tare da su Banafsha suka je masa gaisuwan safe kafin ma ya fita Fada yaran suna nan sai sabuwar shekara za a sanya su a makaranta. Ko a fuska bai nuna mata yana fushi da ita ba. Itama ba ta nuna masa komai ba ta so dai su keɓe amma yaran ne suka hana, kuma zai fita Fada ba su samu lokacin keɓewar ba. Sai ta bar shi a tunda gobe za ta yi arba'in jibi sai ta shirya masa tarba yadda za ta wanke kanta. Duk da ya ce ba komai ta san yana fushi da ita fushin nan na shi mai shiga jiki yana illata mutum bai sani ba. Ranar da ta yi arba'in da kanta ta jagoranci girke girken da aka yi, tana so za ta je gaishe da Mai martaba da Fulani shi yasa ta yi abinci daman ta ce ita za ta dinga yi ma Mai martaba girki duk ranar girkinta da kanta a kitchen ɗin bangarenta. Saƙo ta tura ma Mai martaba na fitan da za ta yi ya amsa mata da Allah ya tsare. Su Beena ma suka ce za su je ta ce su je a shirya su, ita da Harira ne da Asabe sai wata Hadima Habi, motoci biyu suka yi amfani da su akwai sau dogarai guda biyu sai masu kaki guda biyu, duk da ba nisa za su yi ba umarnin Sarki ne su yi mata rakiya. Abinci kala uku ta yi, tuwon shinkafa miyar agushi da naman ganda sai farar shinkafa da miyar kaza, sai dambun couscous, na zogale mai hanta sai lemun kankana da ayaba, sai zoɓo mai sanyi booth sai da ya cika da manyan kololin alfarma. Sai dai suka gansu kwatsam tunda Ummu Salma ba ta sanar suna tafe ba. Mai martaba mai murabus ya ji daɗin ganin su, sai Ummu Salma ta ga ya yi kiɓa ya samu hutu sosai sai dai farin gashi duk ya mamaye masa fuska. Ya ce ya ji daɗin ganinta ga shi ta zo da yaran gabaɗaya ta kawo masa Batula da ta yi kiba tana da wuntsila kafafunta ta samu ruwan nono sannan ga madaran yara. Fulani ma ta yi ta saka albarka, a gidan suka yini har yamma. Received at 19:42Reactions: ❤ 13, 👍 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Gimbiya Shahida da Gimbiya Amaratu ne daman iyayen ɗakin Ummu Salma Gimbiya Hadiza da Maimanatu sama sama ne, Hafsat ta koma makaranta Amir ne kawai da Amira a gidan. Da za su tafi haka Mai martaba ya ba ta farar takarda cike da kuɗi ita da Banafsha tare da yaran gabaɗaya haka ma Fulani Ummu Salma ta rasa ma ina za ta kai kuɗaɗe kamar ma sun yi mata yawa ga uban na sunan da ta samu ba ta ko kirga ba kuɗi ne ba kaɗan ba suna cikin kwandon da aka tara su a cikin bedroom ɗinta ba ta bi ta kansu ba ma. In ta zauna tana duba rayuwarta tun daga farko har matakin yau sai ta yi hawaye. Ba ta taɓa tunanin rayuwa za ta juya mata haka ba. Yau ita ce a matsayin matar sarkin a gidan Sarauta na Daura a matsayin Sarauniyar Daurama. Yau ita ce a matsayin matar Hamma kuma wai sun haihu tare sai ta yi ta mamaki, tana jinjina ma ikon Allah, ta juya ta ga irin daula da ni'imar da take ciki sai ta yi hamdala. Ta tuna da Baffa ta yi hawaye tana nema masa gafara Baffa ya sha faɗa mata ta kwantar da hankalinta Lamiɗo zai zame mata mjjin marainiya ga shi kuma ya zama amma Baffa ba shi da rai ballatana ya ga wannan daular da kuma cigaban rayuwar da ya same ta, har abada ba za ta manta da rashin Baffa ba. A baya tana ganin kamar in tunda ta rasa Habib ta rasa komai tana ganin ba za ta samu madadinsa ba. Haka ma Shamsiya ta taɓa faɗa mata a wancan lokacin ta tabbata yanzu da ta zo ta ga yadda rayuwarta ta koma za ta karyata kanta da kanta. Ƙwata ƙwata ta ma manta ba ta kira ta yi musu bangajiya ba, a daran suka sake mgana da Baɗdo tana faɗa mata ta rasa ina za ta zuba kuɗaɗen nan da ta samu. "Ki kai su a ɗura su a cikin banki ya fi sirri." "To wa zai kai min! Kin san dai nan ba Jimeta ba ne, Hamma ba zai bar ni na je banki ba " "Kuma haka ne, to ki yi mgana da shi dai ki ji." Sai ta ce za ta faɗa masa, kuɗin akwai abubuwan da za ta yi da su za su yi mata amfani sosai. Hamma Lamiɗo kuma sai washegari take so ta tarbe shi za ta yi masa mganar abin da ta yanke domin ta ji shawaransa. Sai washegari ta kira Shamsiya a waya ta ba ta haƙuri tare da yi musu bangajiya da fatan sun koma gida lafiya "Lafiya lau ranki ya daɗe, na so kiran ki sai kuma na ce ba lalle ki ɗauka ba kuna ta fama da jama'a" Wani girma take ba ma Ummu Salma rayuwa kenan, Shamsiya ce ke godiya da irin tarban arzikin da aka yi musu da abubuwan alherin da suka samo a Daura Ummu Salma ta ce bakomai ba su jima suna yawa ba suka yi sallama ta tambayi Hanan Ummu Salma ta ce ba ta nan tana bangaren Bilkisu. Lokacin da Ummu Salma kira Shamsiya suna tsakar gida ne tare da Gwaggo da ƙannen Habib maza da matan masu aure kuma hiran Daura take yi musu, tunda ta dawo kullum sai ta ba su labarin abin da ya faru a can, suna ta cewa lalle masu mulki da masu arziki sun huta duk sun zo da jakar da aka raba da calander da duka abubuwan da aka raba duk wanda ya ga hoton Lamiɗo sai ya sarara ya ce rabo ne kawai ya haɗa auren Habib da Ummu Salma tun farko amma ba tsaran juna ba ne. Shi kan shi Habib ɗin duk Shamsiya ta faɗa masa duk abin da ya wakana a can Daura yana ji nadama na sake kama shi, ya yi sakaci ya yi wasa da damar shi, ga shi Ummu Salma ta yi masa nisa, shi dai ya rasa komai na shi, sai godiyar Ubangiji kawai Habiba ma haka ta je gidan su tana ta ba da labarin abin da ya faru a Daura ga abubuwan da suka dawo da shi, har jin daɗi take yi tana ba da labari, tana faɗin wata miyar sai a maƙota. Tana faɗin Habib ba shi da kuɗin da zai iya siyan takalmin da Hanan take sawa ba ma sutura da sauran bukatu ba, sai dai kawai ya yi hakuri a dinga ba shi aron ta amma Hanan ma ta fi ƙarfin shi ballatana Ummu Salama. Ga shi tana ta faɗin a jirgi suka dawo ita dai Habiba ta gama ganin duniya, faɗi take yi Habib ya cuceta da bai sake ta ba, ta tsani zama da shi, ba shi da komai sai haƙuri da rayuwa. Amma ta ga alamun ba zai sake ba kamar yadda ya faɗa ba yana so a sha wahala da ita, ta roki Baba Usman ya shiga mganar ya ce ba zai shiga ba sai dai ta yi haƙuri kawai dole ta haƙura amma tsakaninta da Habib ba rangwame ba tausasawa. * Received at 19:42 11 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ranar da Ummu Salma za ta tarbi Lamiɗon da wuri ta yi aikace aikacenta tare da su Harira da sauran Hadimai masu kama mata girke girke ta yi masu rai da lafiya da yamma ta tura masa saƙon yau za ta kwana a bangaren shi bai ba ta amsa ba. Abincin da ta yi duka a bangaren Mai marbaba aka je aka jera ba ta ci ba ta saka a zuciyarta tare da shi za su ci abincin dare yau. Kwalliya ta yi mai ƙayatarwa cikin wata atamfa ta san ya na son ya ga ta saka atamfa ya na yawan kallonta. Ba ta yi ƙunshi ba saboda wanda ta yi bai fita ba gashinta kuma ta gyara shi ta saka masa mai yana ta ƙyalli. Da wuri ta tafi bangaren tare da Banafsha ta ɗaukan musu duk abin da za su buƙata kafin gobe da safe. Bangaren Mai martaba ƙal yake a gyare yana tashin ƙamshi ga kalolin abinci na garari an jera a saman dinning ta dafa masa ruwan tee mai kayan ƙamshi irin wanda yake so, anan ta yi sallar isha'i daman da alwalanta daman haka take so in ya shigo daga Fada kawai ya fara tozali da ita. Ta sha zama wajen karfe tara da rabi na dare wayar ta ce ta ɗebe mata kewa ta shiga youtube ta cigaba da sauraran labarin Turken gida na Janafty a tashar tsakar gida, ta gama ɗingishin kwaɗo, yanzu tunda kallo ya fita kanta ta koma jin Audio kuma yanzu ya zame mata jiki tana aikinta tana saurarawa, ko tana zaune yanzu ma Turken gidan tana gama ji za ta saurari buzu na Marubuciya Ayushercool. Yanzu ma tana zaune a saman resting chair na bedroom ɗin Lamiɗo, Banafsha na gefenta tana da wassaninsu na yara, itama ta sha gayunta tana ta ƙamshin turare, ita kanta Ummu Salma wani irin ƙamshi ne ke tashi daga jikunta, turarakan Maryam suna da matukar kyau da kama jiki, in ta yi amfani da shi, Lamido na yabawa ballatana shi da ba ya son ƙamshi mai karfi duk sun cika ɗakin da ƙamshin su. +234 812 195 7799 Hankalinta na can wajen jin diraman Sadiya da Yallaɓai, in da ya ce ta tafi gida saboda Gimbiya tana saurara tana kumduma ma Yallaɓai a shar a cikin zuciyarta tana kuma jin zafin lamarin sosai sai ga Bilkisu ta shigo itama ta ci gayunta masha Allah Ganin Ummu Salma ya sa ta yi turus tana kallonta, itama ta ɗan ji wani iri da ta ganta amma ba ta nuna ba sai ta wayance ta gaishe ta Bilkisu ta amsa daƙyar fuskarta ba fara'a Ta juya za ta bar bedroom ɗin sai Ummu Salma ta miƙe bayan ta tsayar da karatun gwara ta yi mata bayani kar ta ce ta yi mata rashin adalci. "Anty Bilkisu." Ta kira sunanta sai ta juyo tana kallonta. Ummu Salma ta tako har gabanta ta tsaya. "In ba damuwa ina son magana dake." Sai ta ɗan juya idanuwanta kafin ta ce" Uhm ina jin ki." Sai ta ɗan yi shuru kafin ta ce" Ki yi haƙuri ban faɗa miki ba, na ɗauka kin sani tunda na dawo ban kwana a bangaren nan ba, tunda na haihu ban yi arba'in ba sai jiya ne muka yi kwana arba'in" Bilkiisu ta kalleta tana nazarin maganarta. "Yau ne zan kwana da gobe, jibi kuma sai ki karɓa. Ko kuma na koma mu dawo daga farko tunda ke ce babba, ni jibin sai na karɓa. Ta faɗa tana kallon Bilkisu, da ta yi shuru ba ta yi magana ba. "No. Alright." Ta amsa mata sannan ta juya za ta bar ɗakin sai ga Lamiɗo ya shigo, tun daga falo ya cire alkebban jikinsa da rawaninsa. Ganinsu tsaye suna kallon shi sai ya ba shi mamaki amma bai bayyana haka a saman fuskar shi ba. Bilkisu ta fara masa barka da shigowa ranka ya daɗe. Ummu Salma ta ce sannu Hamma, ita manta ma take yi da wani ranka ya daɗe ya amsa ba tare da ya kalle su ba, sai da ya zauna a saman kujera yana ajiye kayan hannun shi sannan ya kalle su amma bai yi magana ba. Bilkisu ta yi musu sallama ta fice Ummu Salma ta bi ta da kallo, ta faɗa mata gaskiya ne kar ta ɗauka tana shiga hakkinta ne. Shi dai bai tambaya ba, kuma Ummu Salma ba ta faɗa masa ba, ta taya shi rage kayan jikinsa ya shiga wanka ita kuma ta hau ninke kayan tana kai su ma'adanan su. Bilkisu kuma ba ta yi mamaki ba sanin halin Lamiɗo, baya ƙarin bayani duk abinda kika gani kawai ki yi shuru, ta yarda da Ummu Salma domin ta sha zuwa bangaren da daddare ranar da ba ita ba ce sai ta ganshi shi kaɗai bai taba faɗa mata ba. Ba ma zai faɗa ba wataƙila ma tunanin hakan bai kawo masa ba. Received at 19:42 8 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta ji kishin barin Ummu Salma da mijinta har ta kai bangarenta zuciyarta na zafi sai da ta dinga addu'a tana neman tsarin sheɗam sannan ta samu sauƙi. A can bangaren Mai martaba kuma bayan ya fito wanka tuni Ummu Salma ta ɗauko masa saukaƙkun kaya ya saka, ta ce masa ga abinci daman daga baya ta tura masa saƙon za ta yi abinci. Cewa ya yi ta kwaso abincin zuwa ciki ya gaji ba zai iya fita ba. Ta bi umarninsa anan suka ci abincin kuma ya ci sosai, ya sha ruwan zafin da ta dafa masa ita ma ruwan zafin kawai ta sha, Banafsha ke hannunta tana shayar da ita bayan ta gama ta ba shi ita ya riƙe ita kuma ta kwashe komai ta mayar saman dinning ta gyara wajen sannan ta zo ta yi shirin kwanciya ta sauya kayan jikinta zuwa na barci haka ma Banafsha ta rage mata kaya masu nauyi daga jikinta zuwa masu sauƙi. Suka saka ɗiyarsu a tsakiya suna kallonta Lamiɗo na rike da Hananun Banafsha, sai Ummu Salma ta riƙe hannun shi tana kallon shi, ya kalleta amma bai yi magana ba "Hamma " "Uhm" "Na yi arba'in." "Congratulations" Ya faɗa yana kallonta sai ta yi masa mirmishi, ya yi shuru yana wasa da hannun Banafsha, sai Ummu Salma ta tashi ta janye Banafsha gefe yana kallonta bai yi magana ba. Ta tsallako ta zo ta shige jikinsa tana sauke numfashi, ya ƙi riketa ta fara shafa fuskarsa tana kiran sunan shi. "Uhm" "Na ce na yi arba'in.". Ta gama faɗa cikin shagwaɓa, kamar za ta yi kuka. "Me zan miki? Ya ƙura masa ido tana kallon shi. "Hamma." Ta kira sunan shi tana dukan ƙirjinsa, haushi ta ji wai me zai yi mata sai kawai ta juya masa baya tana jin hawaye na taruwa a kwarmin idanuwanta. Ya fa san abin da take magana amma yana yi mata wulakanci, ta ɗauka ba zai lallasheta ba ganin an fi mintina biyar bai riƙeta ba sai can ta ji shi a bayanta ya ɗora kansa a saman kanta yana rumgumeta. "Sarauniya ta." Ya faɗa a hankali yana shafa bayanta zuwa maranta, ta rike hannun shi amma ba ta yi magana ba "Na yi kewar ki." Ya faɗa yana yi mata raɗa. "Ki taƙale ni, ina ina soo.." Ya faɗa kamar wani yaro yadda ya yi maganar ne sai da ta ji motsi a cikinta duk yadda ta so ta ja aji ta kasa dole ta juyo da sauri ta kama kanshi, ya riƙe ta gam suka fara sumbatar juna kamar suna jira, da zafi zafi suna saman gado mai rumfa, da wasu labulaye masu kyau da yarari da suka rufe gadon gabaɗaya Banafsha na gefe iyayenta na gefe suna shan shagalinsu. Ummu Salma ta kusa saka Mai martaba Sarkin Daura ihun sarari, duk kamewarsa sai da ya yi mata sambatu, wani irin salo ta dinga yi masa na salon da za ta rikita shi ita ta jagoranci komai shi dai kawai ɗan rakiya ne. Bayan sun gama tsarkake jikinsu suna ƙamƙame da juna, yana yi ma Ummu Salma raɗa a kunne tana masa dariya. Ta fara masa cakulkuli ya daure ya zille amma sai da ta saka shi dariya. "Hattara dai Sarki ne ni." Yake faɗa yana kallonta. "A waje kake Sarki, a gaba na kai ba Sarki ba ne." "I see." Ya faɗa yana jan hancinta. "Thank you," Ya faɗa yana sumbatar goshinta, ya rasa me zai ce mata! Amma ta saka shi farincikin da tunda ya zama Sarki bai yi irin shi ba. Hira suke yi a hankali, Ummu Salma ta juya kanta na saman hannun Lamiɗo yana ta bayanta ɗayan hannunsa ya zagaye cikinta zuwa Banafsha dake gefensu, kamar ba dare ba suna ta hira ƙasa ƙasa Umma Salma na ba shi labarin kudaɗen da ta samu masu yawa. "Hamma ina so na cigaba da tafiyar da girke girkena a social media sannan ina so a ƙarƙashin haka na buɗe wata gidauniya domin taimaka ma marasa karfi." Ya ce mata idea ne mai kyau, sannan ta cigaba da faɗa masa filayenta na Jimeta tana so ta ba da su a sadakatul jariya ga Baffa, tana so ta ba da su a gina islamiya da masallaci Sai Lamiɗo ya tambayeta mene shawaranta ta ce babban filin za ta ba da shi kyauta a gina makarantar islamiya, ƙaramin kuma tana so ta gina masallaci da kanta domin Baffa. Nan ya ba ta goyon baya ya ce abin da za ta yi tunani ne mai kyau sosai. "Za ki samu duka support ɗina. A matsayin Miji da Yaya in sha Allahu, duk abin da kike bukata ki zo kai tsaye ina tare dake har abada." Received at 19:42Reactions: ❤ 11, 👍 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta sake shigewa jikinsa tana yi masa godiya. Maganar girke girkenta kuma ya ce gidan abinci take so a buɗe mata? komai take so zai yi mata saboda ya yi supporting ɗinta sai ta ce tukunna dai ba ta da sha'awar gidan abinci ta fi bukatar buɗe wani training center domin koyar da matasan mata girke girken zamani da na gargajiya da kuma koyar da su yadda za su iya sarrafa fulawa domin samun sana'ar dogaro da kai. Ya ce hakan ma tunani ne mai kyau yanzu dai sun yi shawara za ta cigaba da ɗora video na girke girkenta sannan daga baya komai sai ya biyo baya. Sai wajen biyu na dare suka yi barci da asuba kuma ta yi masa zencen gobe Baffa zai cika shekara ɗaya da rasuwa za ta yi girki mai yawa za a yi sadaka ya ce babu matsala. Za a yanka Sa saboda a samu nama, abubuwan buƙata kuma ya ce ta rubuta ta ba ma Jakadiya ta amsa masa da to da safen ma sai da ta ƙara taƙalan shi, sannan suka yi wanka ya fita Fada ita kuma ta tattara ita da Banafsha suka koma bangaren su. A bangarenta ta shirya yin girkin. an kawo cefane ma su yawa sai da ta ce su Harira su rage su kai babban Kitchen sannan an yanka sa an shigo da naman ta tara hadimai suka gyara aka tafasa. Jalof ɗin shinkafa za ta yi mai kayan lambu da nama, a daran har naman ta saka aka soya, sun yi waya da Ammah suma acan za su yi abincin Sadaka. Buhu uku za su dafa na shinkafa da miya Lamiɗo ya tura musu kuɗi masu yawa, sauran kuma su Hamma Abdullahi Gabaɗaya suka haɗa, suma sun siya rago an yanka abincin da yawa ne za a kai masallatai da makarantun allo, har da su Adda Suwaiba duk za su zo su taimaka ayi girkin. Mami da suka yi waya da Ummu Salma ma tun kafin ta faɗa mata za ta yi, Mami ta faɗa mata itama za ta yi abincin Sadaka saboda gobe Baffa ke da shekara ɗaya da rasuwa. Ashe kowa na lissafe Daran ranar ya yi ma Ummu Salma tsawo har mafarkin Baffa ta yi, ya zo ya ga Banafsha suna ta hira ya ce ta gaishe masa da Lamiɗo har tana cewa Baffa Hamma Lamiɗo ya zama sarki, ya ce na sani Auta ina yi masa fatan alheri ya horeta da ta zama mace ta gari. "Ki yi duk abin da zaki yi ki zama mace ta gari a wajen mijin ki. Ki zama mai ilimin da za ki taimaki mulkin mijin ki ta bangaren alheri Auta " Da Baffa zai tafi ta dinga kuka ashe a sarari take yi, sai da ta ji Hamma na kiran sunanta sannan ta farka ta ganta a jikinsa sai ta ga tana hawaye ashe da gaske kuka take shi ne take faɗa masa mafarkin Baffa ta yi ga abin da ya ce mata sai ya rumgumeta yana lallashinta. "Baffa na cikin rahamar Ubangiji in sha Allahu." Haka yake faɗa yana shafa bayanta alamun lallashi, ranar duk sukuku ta yini kamar ba ta da lafiya abincin Sadakar ma ya ce in ba za ta iya ba Hadimai su yi ta ce za ta iya. Rashin Baffa ne ya taso mata, wato duk wanda ya rasa mahaifi ya yi rashin bango, ballatana ita mai uba ma irin Baffa. Haka ta zage suka yi wannan abinci takeway ɗari biyar suka yi, ga nama ga ruwa da lemu an raba wasu a cikin masarauta ga hadimai da kuma dogarai, sai kuma wasu dirobobin Masarauta suka fita da shi za su je cikin gari a raba ma mabuƙata. Lamido kuma a safiyar ranar ya yi sadakar kuɗi, ya gana kuma da matasan garin Daura ya ji ta bakin su, masu karatu da ba su samu aiki ba, ya ce su tattaro tarkadunsu suma yanzu sun shiga gwamnati sannan na ɗa shugaban media team ɗin shi, su za su dinga zaƙulo masa abubuwan dake faruwa a yankin da yake mulka. A masallaci ma da asuba sai da Mai martaba ya sanar da liman a yi addu'a ga mahaifinsa da ya rasu tare da sauran musulmai, da asuba an yi haka ma da mangariba ma Ummu Salma na bangarenta ta ji ana yi ma Baffa addu'a itama tana saman darduma ne ta idar da salla. Ta girgiza kai tana hawaye a sarari ta ce Allah ya gafarta maka Baffa mganganun da ya faɗa mata suna mata yawo ya ce ta yi komai domin ta taimaka ma mijinta ta fuskar alheri ta shiga tunanin me za ta yi da za ta taimakama Hamma a wannan jagorancin na shi, sai ta ga buɗe gidauniyar da ta yi magana shi ne farko a ƙarƙashin gidauniyar za a tallafa ma mutane da dama daga wannan Masarautar Received at 19:42Reactions: ❤ 15, 😁 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby A ranar ta kira Hamma Abdulrahaman ta yi magana da shi, shi ne lauya kuma shi ne ya siya mata filayen nan kuma takardun suna hannun shi, shi ta ba ma ajiya daga baya. Sun daɗe suna mgana ta faɗa masa niyyarta ya ji daɗi sosai ya ce su yayyenta ma ba su kawo wannan tunanin ba su tunaninsu su gina bohol ne saboda sauƙaka ma mutane wahalan ruwa da kuma gina rijiyoyi tabbas ya yaba da tunaninta ya ce zai bincika wannan babban filin za a damƙa shi a wata kungiyar domin samar da makarantar islamiya, ƙaramin filin kuma tunda magana ce ta gina masallaci shima zai bincika duk yadda ake ciki zai neme ta, ga shi dai ƙarama ce a cikin su amma ta yi tunani irin na manya. Shi da kan shi ya je group ɗin su ya faɗi ƙudirinta yayyyenta suna ta saka mata albarka da fatan Allah ya jikan Baffa da rahama Ammah da ta ji sai ta yi kuka Mami ma ta ce itama za ta gina bohol anan cikin garin Kaduna, kowa dai ya ce zai yi wani abu domin Sadakatul jariya ga Baffa Allah ya yi masa rahama. Ummu Salma ta yi shawara da Baɗɗo da Mami kan mganar ƙudirinta na buɗe gidauniya amma ƙarƙashin tsarin girke girkenta da za ta dawo da shi dukkansu sun ba ta goyon baya, ta ce za ta sauya suna daga oum Hanan Delecious, zuwa SARAUNIYA DAURAMA'S KITCHEN. Mami ta ce sunan ya yi sosai, ta ce a ƙarƙashin sunan sai ta buɗe Sarauniyar Daurama Foundation, domin tallafama mata da jari da kuma duba marasa ƙarfi da masu neman tallafi na rashin lafiya. Bayan ta yi mgana da su ta sake magana da Mai martaba ya ce ga kafaɗarsa ga bayansa shi zai yi supporting ɗinta har ta kai ga nasara. Komai take buƙata kawai ta yi masa mgana, wato shi fa a rayuwa in ka samu miji mai girmama duka ra'ayinka ka gama yin dace, sannam mu mata muna ɗan taɓa kuskure, sai mace ta dinga yi abu gaban kanta ba neman shawaran wanda kike zaune domin shi, ki sani shi ne fa mijinki kuma shugabanki sannan yana gaba dake a halitta da tunani gabaɗaya. Komai lalacewarsa namiji ne ba faɗuwa za ki yi in kika nuna masa yana da muhimmanci ba, ko da ba zai ba ki komai ba in ya yi miki addu'a da fatan alheri ko shawara ya baki ai gama miki komai, mu daina ganin cewa shawara da miji ba wani abu ba ne, girmamawa ce da ganin ƙima Ubangiji Allah ya sa mu dace Amin. Yanzu matakin farko shi ne ta dawo da handels ɗinta na social media shekara ɗaya kenan har da wattani ba ta ɗaura komai ba, ba ta ma tsayawa dubawa tun daga rasuwar Baffa da rashin jaririnta sai kuma ta zo ta samu cikin Banafsha abubuwa suka ƙaru amma yanzu tunda ta samu natsuwa za ta dawo gadan gadan. Da canza sunan handels ɗinta ta fara, ta koma Sarauniyar Daurama's Kichen, daman ta fi ɗora video ɗinta a youtube ne da Tiktok. Youtube ɗin ma ya yi kasa saboda ta daɗe ba ta ɗora komai tiktok ma ta kai followers dubu hamsin a shekaran ɗaya sama da mutane dubu goma ne suka yi followiing ɗinta saboda ana kallon girke girkenta ana sharing kuma. Tuni ta dawo bakin aiki, daman ita ke girkinta a bangarenta ta naɗa ta yi posting ana ta mata welcome back domin mutane na gane bayananta suna kuma gwadawa su ji daɗin girkin da ta ɗora musu a shafinta. Sunan da ta canza ma ya jawo hankalin mutane sannan ga sabon kitchen dalilin haka ta ƙara tara mata mabiya sosai, ana yi mata Dm ana tambayanta da gaske ita ɗin sarauniyar Daurama ce? ba ta amsawa, domin ba yanzu za ta bayyana wace ce ita ba. An shiga sabuwar shekara da burika ita dai burin Ummu Salma duk abin da ta yi kuɗiri ya tabbata kafin shekaran ta ƙare. An saka su Hanan wata makarantar kuɗi mai kyau a Daura sannan aka sanya su a islamiya yamma, rana ku biyar alhamis da Jumma'a suna gida weekend kuma an ɗauko musu wani malami yana koyar da su Haddar AlQur'ani a cikin Masarauta, Ummu Salma ta ba da shawara ta ce hakan zai taimaka musu, duk da itama tana koya musu musamman azkar, hadisi, kuma yaran suna da ƙokari balle ma makarantarsu ta can Lagos mai kyau ne sun samu matashiya mai kyau. Received at 19:42 11 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Bilkisu ma ta fara aiki a General Hospital Daura. a garin Daura. Ta nuna ma Lamiɗo tana son ta cigaba da aikinta shi kuma ya ba ta goyon baya duk da a al'adun sarautu na gargajiya matan sarakuna ba sa aikin gwammati, amma ba addini ba ne ya hana sannan ba doka ba ce, shi kuma Lamiɗo mutum ne mai girmama ra'ayin kowa da ba ma duka matansa dukkan dama, Bilkisu likita ce ba za a tauyeta ba sannan yanzu ma sarautun sun koma na zamani ana samun matan sarakuna da ayyukan gwamnati kamar koyarwa, aikin asibiti da NGO wasu kuma suna yin kasuwancin su. Shi yasa ta da bukaci cigaba da aikinta ya yi supporting ɗin ta. Yanzu direban masarauta ne ke tuka ta tare da Sabuwa in za ta je asibiti, sai su yi sati ba su haɗu da Ummu Salma ba kowa na bangaren shi yana harkan gaban shi, ita Ummu Saalma ta duƙufa kan abin da ta saka ma gaba, so take nan da tsakiyar shekara ta yi online class na mutane ɗari bayan an gama na sati biyar sai ta tallafa musu da kudaɗe, haka ta saka a diary ɗinta domin yanzu duk wasu abubuwan da take son cimmawa tana rubutawa. Yanzu maganar ginin masallacin ne a gabanta babban filin ma tuni an bayar da shi a gina makarantar islamiya sadakatul jariya takardun filin ma ya tashi daga nata ya koma ƙarkashin kungiyar da za su gina makarantar. Yanzu filin da za a gina masallacin ne aka nemo amintattu aka ɗora su a wajen aikin ta tura kudaɗe sama da miliyan goma da za a fara aikin da shi, kuma kuɗin ta ba su kare ba ga Mai martaba ya ce in ana buƙatar wani abu ta yi masa magana tana so ta yi komai da kanta ne sai ta kai ƙarshe in tana bukatar tallafi sai ta yi masa mgana. Cikin lokaci aka fara ginin wannan masallacin daman gini in dai da kuɗi ba a ɓata lokaci. Duka duka wattani uku aka ɗauka kafin a kamallah gina masallacin nan. Ga masallacin mai kyau ne kamar a saudiya Mai martaba ya saka kuɗin shi shima sama da miliyan biyar, ga shi an yi bohol a masallacin bayan an gama aka damƙa ma limanin masallacin da Baffa ke salla shi ya je ya samu malaman anguwan da limaman masallaci suka zauna da shi ya yi musu bayani suka yi ta saka albarka. An yi taron Buɗe masallacin bayan ƙaramar salla ne Ummu Salma da Mai martaba Sarkin Daura sun zo, amma ba su kwana ba a ranar suka koma, Mai martaba mai murabus yana can London wajen wattani biyu kenan yana hutawa sannan yana ganin likita, tare da Gimbiya Shahida suka tafi amma ta dawo Gimbiya Hadiza ta koma wajensa. Fulani ce da su Gimbiya Amratu ke gida, itama Fulani wannan shekaran za ta koma Saudiya Ammah ma ana ta shirin tafiya. Tare za su tafi da Fulani da Gimbiya Maimunatu. Baɗɗo ta samu ciki har ya fito. Tana gida tare da Ammah, da yake kasuwancinta na online ne tana gida tana cigaba da kasuwancinta. Da babbar salla ba su zo salla ba tunda Ammah bata nan sai da ta dawo suka taho gabaɗaya har da Mai martaba da yaran suka yi mata sannu da zuwa Banafsha, ta yi wayau har ta fara zama tunda yanzu tana wattani na biyar cikin na shidda ne da haihuwa, Mai martaba kwana ɗaya ya yi ya koma sune sai da suka yi sati Bilkisu kuma daga nan Kano ta wuce tare da su Sultan Hanan kuma an kaita gidan babanta. Shamsiya ta faɗa ma Ummu Salma ta samu ciki wata biyu da kwanaki ta yi ɓarin shi, har tausayi take ba ma Ummu Salma, ga wahalan rayuwa tana tunanin in dai ta buɗe foundation ɗin ta, Shamsiya za ta shiga cikin waɗanda za ta fara tallafamawa, sannan ta roƙeta yan ajinsu na makaranta suna ta tambayan lambarta tana neman izinin ta tura musu? Ummu Salma kuma ta ce ta ba su ba komai ikon Allah kenan yanzu tunda ta zama matar Sarki kowa neman ta yake yi an mayar da ita group na makaranta girmamata suke yi ranki ya daɗe sama da ƙasa ba mai kiran sunanta ko kuma su ce Sarauniyar Daurama. Ita dai sama sama, duk wanda ya kira ta za su gaisa amma tun daga kan Shamsiya ta daina aminci da yarda da ko wata ƙawa. Received at 19:42 8 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Tana da Baɗɗo ba ta neman kowa a halin yanzu, amma in abu ya faru na buƙatar taimako tana taimakawa iya ƙarfinta ko kwanaki wata class mate ɗinsu ta samu hatsari za a yi mata aiki a kugu ana neman dubu ɗari takwas, mijin ba shi da karfi ana neman taimako ta yi ma Mai martaba mgana ya ba ta kuɗi ta tura musu dubu 1M mazan su da matansu haka suke yi mata godiya. Sannan sun ce suna so su shirya haɗuwa na mates ɗin su, ta ce su shirya ba sai sun jira ta ba, ƙarshen shekara aka ce ta ce lokacin suna Abuja bikin Saleem amma daga can za ta zo Adamawa. Saleem zai auri ƴar sarkin zazzau ne kuma a garin Abuja za a yi duka bikin angon ma a can za su zauna tunda anan yake aiki. Sagir ne ma ya dawo garin amma ya koma ya ce sai ya haɗo Phd ɗinsa Yazeed kuma yana masters ne. Mai martaba mai murabus kuma ya samu lafiya da kwanciyar hankali ya dawo yana gida yana hutawa. Ummu Salma su ta riƙe a matsayin iyayen ɗakinta duk sati tana hanyar zuwa, da abinci domin Mai martaba mai murabus har jiran girkinta yake yi Lamiɗo ya faɗa masa abin da take so kenan harkan girke girke Mai martaba ya ce za a buɗe mata har gidan abincin in dai tana so tana ta godiya. Burinta ya kusa cika ta kai in da take so ta shahara, ta samu ƙwarewa daga mabambamta makarantu na online sun fi biyar sannan ta zo ta yi online class na mutane ɗari sannan bayan an gama ta raba musu dubu hamsin hamsin ta ce su je su ja jari ko wacce ta je ta kafa abin da ta iya. Wannan dalilin ya sa ta yi suna sosai kaf arewa a cikin masu girke girke za ka ji ana zencen Sarauniyar Dauramas Kitchen, cikin ƙanƙanin lokacin sunanta da komai na ta ya tafi viral tuni mutane sun fara yarda matar Sarkin Daura ce wasu har sun lalubo hotunanta ana yawo da shi, yanzu social medi ba tsaro in suka taso ka gaba sai Allah. In da ta gode ma Allah ba ta samu ciki ba ga shi har Banafsha na shirin shekara har ta fara tafiya ba in da ba ta zuwa. Shi yasa sai komai ya zo mata da sauki Baɗɗo ce kamar P.A ɗinta Mami kuma mai ba ta shawarwari ita da Hamma Saddam kuma tana jin daɗin haka sosai. Har sun fara maganar foundation da Hamma Abdulrahaman ya ce zai haɗa ta da wata Barrister Salamatu Doma, a nan Abuja take tana aiki da suprime court Abuja, itama suna da wata foundation da take jagoranta za ta taimaka mata sosai. Yanzu sun ajiye mganar in suka je Abuja bikin Saleem za ta je har gida ta samu Barrister Salamatu Doman su yi magana. A karshen watan november Baɗɗo ta haifi ɗa Namiji ya ci sunan Baffa, suna kiran shi Junior. Ummu Salma ta zo suna, Bilkisu lokacin ba ta nan ta je Canada hallatar wani Seminar na su na likitoci. Da za ta koma da Islam ta koma ta gama jarabawar fita babban sakandiri kafin sabuwar shekara za ta fara jami'ar a Kasu dake Kaduna in da Mami ke aiki. Tana komawa Daura ta fara zazzabin dare sai amai ana duba ta sai ga ciki har ya yi wattani uku ma ba ta san da shi ba. Duk da tana jin canje-canje a jikinta. Ta ji daɗi amma ba ta ji ba saboda cikin zai yi mata cikas da shagalin biki, sannan ga shi Mai martaba ya yi mata alƙawarin zuwa Saudiya, yanzu kuma ciki na ɓulla ya ce sai ta haihu yaro ya yi ƙwari, sai da ta yi kuka ta so ta je Saudiya ta yi ta ibadu tana roƙa ma Baffa gafara a harami. Allah ya sa ma cikin bai ba ta wahala kamar na Banafsha ba. Shi ya sa har ta samu daman shiga ciki ana ta shirin biki da ita. Gimbiya Shahida da ya'yanta suna girmamata shi yasa itama ba ta sanya a duk abin da ya shafe su. Islam sun haɗe da Amira da su Hafsat, da yaran Sakeena, Amiran ma wannan shekaran za ta yi candy Hajiya Zaliha suke da biki a zaria ƙanwar mijinta ne Saleem zai aura. Tun a satin biki suka tafi Abuja, akwai gidan Mai martaba acan suka sauka ana ta shirin biki. Ango kuma yana Daura sai sun ɗaura aure a zaria za a taho da Amarya Abuja a yi dinner. Saddam na cikin abokan ango shi da Hamma Abdulrahim sun saje da yaran manya nan ma tare da Adda Nauwara ake yin komai tunda suna gari. Received at 19:42Reactions: ❤ 7, 👎 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Kowa ya ga Ummu Salma ko ba ta faɗa ba sai a ce tana da ciki, ta yi kiba kamar ba ita ba. Gimbiya Shahida na Daura nan za ta yi taron ta sai ranar Dinner za ta taho. Ammah da Ummin ikki Daura suka fara sauka. Daga can ne ranar ɗaurin aure suka taho Abuja a jirgi suna isowa ba daɗewa ango da tawagarsa tare da amarya da danginta suka sauka. An sauketa a ƙayattacen gidanta mai kama da aljannar duniya A daran aka yi wata lafiyayyiyar Dinner a ɗaya daga cikin manyan hall na garin Abuja, an barar da dukiya kamar ba san zafinta ba an ƙure adaka ankon leshi ne amma kowa ya saka kalan na shi Ummu Salma ta yi makeup, duk da ba ta ji daɗi ba Baɗɗo ba ta zo ba saboda jego, Hamma Abdulrahim ƙiri kiri ya ce ba za ta zo ba ga shi ta saka rai. Bilkisu ma ta zo, yaran ma duk tare da su suka zo suma sun kure adaka, Hanan da Beena sun girma in ka gansu kamar wasu yan biyu, yanzu Mahma suke kiran Ummu Salma tunda suka ji Hanan na faɗa Bilkisu kuma Momi, Lamiɗo kuma Papa, Sultan an girma shekaransa sha biyu yanzu amma yana da girman jiki da tsawo kamar ɗan shekara sha biyar. Mawaƙa sun zo sun baje kolinsu sun kwashi kuɗi. Anan ne Ummu Salma ta haɗu da Hajiya Hauwa Inuwa Aminu(Anty Hairi) daga haɗuwarsu suka gaisawa shikenan suka yi ta hira da Ummu Salma, Anty Hairi sune tawagan amarya daga masarautar Zazzau, sai ga shi har suna sharing contanct. Anty Hairi akwai kirki sosai mace ce mai karamci Allah ya kara wadata ya kuma raya mata zuru'a Amin. Ummu Salma ta tura ma Lamiɗo hoton ta ita da yaran da ta ɗauke su, sai dare ya duba ya tura mata emojin harara. Cewa ya yi sun tafi sun bar shi, ta ce ya zo shima ya ce in ya tafi wa zai bar ma Daura, ta yi ta masa dariya. Amma ya ce ta yi kyau sosai ya yi kewarta. Ummu Salma ma har videon Bilkisu ta ɗauka a wajen ta tura masa, ita ba ta da wannan Ummu Salma ce komai da ruwan ka, kuma a hakan Lamiɗo ke son kayansa ba Bilkisu kaɗai ba har video ta dinga masa tana tura masa wai kar ya ji kewa shi bai zo ba, gwara ya ji kamar yana wajen shi dai ta saka shi mirmishi kamar wani yaro ƙarami. Shi dai na shi karɓo aure ne kuma sun je Zaria sun karɓo aure sun dawo Daura. A garin Abuja suka ci bikinsu suka suɗe, daman ita Ummu Salma Jimeta za su wuce tare da su Ammah, amma kafin tafiyarsu sai da ta je ta gana da Barrister Salamatu Doma. Hamma Abdulrrahaman ya tura mata lambarta ta kira ta, adireshinta ta tura mata direba ya kaita sai da suka haɗu a a fili sannan ta ga kirkinta da Hamma Abdulrrahaman ke faɗa, sum yi batutuwa sosai ta ba ta shawarwarin yadda za ta tafiyar da ƙudirinta, kuma ta ji daɗin magana da ita sun rabu da cewa za su dinga tattaunawa ta waya in sha Allahu. Sun bar Abuja 28 ga wata ne, tunda bikin 25 ne aka yi, ta je Jimeta saboda talatin ga wata za su yi class reunion ɗin su kuma yadda suke kiran ta ana buƙatarta a wajen da ta faɗa ma Mai martaba ya ce ta je ba matsala dalilin wucewarta Adamawa kenan amma Bilkisu Daura ta koma, ita kuma Ummu Salma ta taho da yaran Adamawa tare da Harira yar amanarta da duk in da za ta je tana tare da ita Islam na Abuja tare da su Hafsat Daura za su koma ta ce ba za ta je Jimeta ba. Baɗɗo ta sha takaicin rashin zuwa bikin nan haushin ma ya ragu tunda shi Hamma Abdulrahim bai je Abuja ba daga Zaria gida ya dawo saboda Baɗɗo tunda Ammah bata nan. Ranar reunion ɗin su shigar alfarma Umma Salma ta yi na super wax sai ta naɗa lafaya jakarta da takalminta ma abin kallo ne kama daga kyawawan ya'yanta Hanan da Banafsha ga su Sultan, Harira ce ke rike jaka da Banafsha ga matashin cikinta ya fara fitowa da ya ƙara mata kyau da ƙwarjini. A toyota ɗin Lamiɗo ta tuka su, zuwa makarantar a can aka shirya taron a babban hall ɗin makarantarsu ta Ahmadu ribaɗu Collage Kowa a wajen nan Ummu Salma kawai yake kallo da ya'yanta da motar da ta tuƙo, Shamsiya ko duk ta bushe gaisawa kawai suka yi da Ummu Salma, ta ɗauki Hanan tana yi ma Banafsha wasa, wasu sun samu labarin matsalan da aka samu tsakanin Ummu Salma da Shamsiya tunda abin duniya ba ya ɓoyuwa, ana ta kuskus ganin Shamsiyar gefe ko Harira Hadimar Ummu Salma ta fita kyan gani. Received at 19:42Reactions: ❤ 11, 👍 1, 👏 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ummu Salma ta haɗu da Madeena Jaafar lokacin lokacin suna makaranta sun yi mutumci sosai ta yi aure da yaranta uku tana koyarwa. An ci an sha an yi hotuna tunda sun haɗa kuɗi Ummu Salma 2M ta ba su, su Hanan sun sha ɗauka kamar yaran turawa. An yi jawabai sosai tare da cewa za a kafa asusu domin tallafawa in wani abu ya taso na biki ko suna ko ciwo a cikin su, an naɗa shugabanin rikon kwarya sai ga shi sun ba ma Ummu Salma matamakiyar shugaba, ta ce ba za ta karɓa ba suka ce sai dai in ba ta so ne shi yasa ta yi shuru. Yanzu duniya in kana da shi kai Sarki ne ta karɓi mic ta yi jawabai anan ta yi maganar za ta buɗe foundation domin tallafawa ma mata da ƙananun yara ana ta mata fatan alheri sun gayyaci wasu malamansu wasu ma duk sun rasu, a jin na su ma an rasa wasu, an fara saka kuɗi a asusun nan take ta saka kuɗaɗe masu kauri hall ya ɗau ihu ana faɗin Allah ya taimaki Sarauniyar Daurama. Shamsiya na gefe tana hawaye tana mai nadamar biye ma zuciya da sheɗan ba domin soyayyar Habib da ta zama kaddaranta ba, da yanzu ita ce a gefen Ummu Salma tana shawara da ita, amma ga Ummu Salma can a sama an zagayeta ta yi mata nisa, ita ko tana gefe in da take ma in ta ce za ta je ita ce za ta muzanta. An yi taro lafiya an ta shi lafiya Ummu Salma ba daliɓai ba har malamai sun karɓi lambarta suna mata magana cikin girmamawa, balle mates ɗin su, an karɓi lambarta kamar ba gobe kowa ya na so ya shige mata. Da za tafi ne ta nemi shamsiya ta ba ta dubu Hamsin tana da canji a cikin jakarta ta tausaya mata ne amma ba domin Habib ta yi ba. Shamsiya har tana hawaye. "Na gode sosai Ummu Salama." Kamar ta san suna cikin wani hali, ga kuɗin hayar in da Habiba take, ita ma ba ta lafiya tunda ta yi ɓarin nan lokaci bayan lokaci tana fama da zubar jini tana bukatar zuwa asibiti. Ga rashin abinci, komai dai ya kwaɓe albashinsu ita da Habib ba shi da yawa ba zai iya rike su ba sai ga tallafin Ummu Salma, kuma ta yi mata alkawarin za ta tallafa mata da zaran gidauniyarta ta fara aiki. Haka Ummu Salma ta shiga mota ita da ya'yanta ta bar makarantar ana ta ɗaga mata hannu. Kowa sha'awa take ba shi, rayuwa kenan wasu a cikin sun yi karatun amma babu aiki yi wasu kuma an yi aure an haɗu da gwagwarmayan gidan miji ga ƴaya a lokacin duk wanda ya ji Ummu Salma ba ta cigaba da karatu ba sai ya ce ita ko me ya sa. ? Suna ganin kamar rashin ilmin da ba ta yi ba zai katangeta da samun alheri cikin su har da Shamsiya domin a baya tana ganin boko shi ne matakin arziki. A wajen suna ta cewa suna bibiyar girke girkenta ba su san ita ba ce sai yau da ta faɗa Shamsiya ta ce itama tana bibiyan Ummu Salma amma ba ta taɓa sanin ita ba ce duk da ranar da fara jin muryan sai da ta ji kamar ta san me muryan. Yau ga shi Ummu Salma da iya sakandirin tana auren ɗan Sarki ta samu dukkan cigaban rayuwa. Su kuma ga kwalin degree ɗin amma suna cikin kalubalen rayuwa Rayuwar nan ka bi ta a sannu kawai abin da kake tunanin ba zai yuyu ba shi yake faruwa. Ilimi na da amfani amma kar ka dogara da shi, mu tashi mu nema mu dogara da kanmu, in karatun ya yi mana amfani muna da plan B ba za mu zauna jiran Gwamnati ba, yanzu Nigeria ta yi yawa ba zai yuyu kowa ya samu yadda yake so ba. A yi ilimi amma a nemi abin da za a dogara kar a sakankance da boko ce ƙarshen tsira. *Janafty* Received at 19:42 15 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ummu Salma ta so su koma Daura first week of January ne saboda yara za su koma makaranta, har sun fara shiri sai kuma Adda Suwaiba ta haihu, Ummu Salma ta san tana da ciki amma ba ta taɓa tunanin cikin ya isa haihuwa ba tunda ba ta da girman ciki sai ko ga shi ta haihu da ta faɗa ma Mai martaba Lamiɗo ta nuna masa tana so ta zauna sai an yi suna ya ce ta yi yadda take so ba zai hana ta ba. Dalilin tsaikon tafiyarta kenan amma ita Bilkisu ta koma Daura bayan an shiga sabuwar shekara. Islam na can tunda tare da su Hafsart suka koma Daura daga Abuja tana gidan Sarki mai murabus, tare da su Amira da Hafsat tunda Ummu Salma ba ta dawo ba. Da suka yi magana ta waya Ummu Salma ta ce me ya sa ba ta zauna a masarauta ba tunda Bilkisu ta dawo "Ya Umma ni fa ban wani saba da Anty Bilkisu ba gwara na zauna anan ga su Amira da Hafsat." Haka ta faɗa, kuma gaskiya ta faɗa Bilkisu ba ta sakin jiki da kowa, matar nan rayuwarta ma na dabam ne, ba irin na sauran mutane ba ne shi yasa ba ta damun Ummu Salma domin ta fahimci har danginta ba da kowa take shiri ba sai wanda Allah ya haɗa jininsu, ballatana ita kishiya da zuwan ka zo na zo ne. Suna haɗa sati ba su haɗu da juna ba, ba ta shigowa bangarenta itama Ummu Salma ba ta shiga, amma yaran suna zuwa wajenta haka ma Banafsha, su Debora dai suna shigowa barin ma Hidaya, Sabuwa ce sai jifa jifa. Sun fi haɗuwa wani lokacin a bangaren Mai martaba ko kuma in ta je can gidan Sarki gaishe shi ta ganta, tana gaisheta duk in da ta ganta ta amsa a tsume, amma bayan gaisuwa wata mgana mai tsawo bai ta taɓa shiga tsakaninsu ba, miji ɗaya dai suke aure amma rayuwar kowa tsarin shi yake yi, shi kuma Hamma Lamiɗo bai damu ba, ba shi da yawan saka ido, kuma ya san haka suke tsarin su ya yi masa daidai muddin ba a zaman gaba kuma ba a faɗa. Da niyyar zama ta yi sunan Adda Suwaiba ta tsaya amma kuma kana naka Allah ya gama na shi, mura ta yi mata mugun kamu da ta saka mata zazzaɓi mai zafi, kuma wannan cikin ma ba ta sha ruwan sanyi ba, ba ta yi laulayi mai zafi ba, amai ma sau uku ta taɓa yi ta dai san tana cin abinci sosai shi yasa ta fara kiba da naman wuya. Ta yi tunanin sanyin December ne ya kamata a garin Adamawa. Har Banafsha ma sai da ta kwanta zazzaɓin nan sai da suka je suka ga likita aka ba su magunguna. Sunan da ba ta samu ba kenan tana gida a kwance, muryanta har ta dishe ta yi ƙatuwa saboda mura, in suka yi waya da Mai martaba sai ya ce muryansu iri ɗaya yanzu ba maraba ta yi ta masa shagwaɓa tana masa kuka shi kuma yana jin daɗin tsokanarta. Mami ta zo suna an yi suna lafiya mace ta haifa yarinya ta ci sunan mahaifiyar Adda Suwaiba Zainab, bayan sunan ne Ummu Salma ta yi ma su Mami bayanin haɗuwarta da Barrister Salamatu da shawarwarin da ta ba ta, da cewa sai ta koma Daura in sun sake yin magana da Hamma sai su ga ta yadda za su fara kudirinta kafin shekaran nan ta kare Foundation ɗin da za ta kafa ta yi ƙarfin da za ta fara aiki ba ɓata lokaci. Sun yi na'am da shawaranta, Mami ta ji Ummu Salma ta gama birgeta duk abin da za ta yi za ta ce sai ta yi shawara da mijinta. Kenan hakan ya nuna tana girmama Lamiɗo ba ta iya aiwatar da komai sai ta faɗa masa ya amince sannan, tana alfahari da hakan, ko ita ba ta yin wani abu ba tare da sanin Daddy ba abu daya ta taba aiwatarwa bai sani ba haɗin auren Ummu Salma da Lamiɗo, wannan kuma ba ta son kowa ya sani ne shi yasa ba ta faɗa masa ba amma tana da tabbacin in da ta faɗa masa zai ba ta goyon baya tunda a komai na ta yana supporting ɗin ta, in ka samu miji mai goya maka baya a duk abin da ka saka ma gaba, to ka gode ma Allah domin watarana za ka cimma in da ba ka yi tsammani ba. Kwana biyu Mami ta yi ta ce za ta koma ba ta zo da Faruk ba yana gida tare da Daddy, sai ta ce a ba ta Banafsha ta tafi da ita ta yaye ta a can tunda nan in ta ga Ummu Salma tana rigiman nono, Ammah ta ce a barta ta yi wata goma sha biyar sai a yayeta, Mami ta ce aa gwara a yayeta yanzu tunda shekararta ɗaya har da wata biyu, kuma lafiyanta lau ba abin da ba ta ci, babu matsala in an yayeta a yanzu. Received at 08:04Reactions: ❤ 14, 👍 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ummu Salma ta ce bari ta kira Hamma Lamiɗo ta faɗa masa, ta kira shi bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙo amma har dare bai kira ba sannan bai ba da amsa ba. Da ta hau whatsApp ta yi masa mgana ta ga ya duba saƙon ta amma bai ce komai ba sai ta yi masa uziri. Amma har dare shuru kuma washegari Mami za ta koma Kaduna. Tana ɗakin ta na cikin bangaren Ammah Mami ta shigo tana tambayanta yadda suka yi da Lamiɗon. "Mami bai kira ni ba, na yi masa saƙo nan ma shuru." "To ni bari na kira shi na faɗa masa." Mamin ta faɗa tana barin ɗakin, Ummu Salma barci ta yi domin cikin nan cutar barci ya saka mata, ta yi da rana ta yi da safe daran ma ana mangariba za ta fara jin barci sai ta yi da gaske take zama sai ta yi sallar isha'i, ko gajiya da barcin ma ba ta yi amma ta farka sau nawa cikin dare in yunwa ta ƙwaƙuleta. Yanzu ma sallar ta idar ta ci abinci ta bi lafiyan gado su Hanan suna can bangaren Baɗɗo can suke yi mata hiran, sun yi ma waya da Shamsiya da safe tana tunanin gobe za ta roƙi Hamma Saddam ya kai Hanan gidan babanta ta yi kwana biyu kafin su koma, ba saboda Habib ba ne saboda Shamsiya ce da take son Hanan tana yi mata so kamar ɗiyar cikinta watakila don ba ta samu haihuwa ba ne. Ba ta san ko Mami sun yi wayar da Hamma Lamiɗo ba, sai da safe ta ga tana shiri ta ce a haɗa mata kayan Banafsha tare za su tafi, sai ta tambayi Mami ko sun yi waya da Lamiɗo sai ta amsa mata da sun yi magana. Ba ta kawo tunanin wani abu ba, domin a mganarta ba ta yi tunanin ta yi laifi ba. A ranar Mami ta koma Kaduna tare da Banafsha, ita murna take yi ba ta yi tunanin in ta tafi ba yanzu za ta dawo ba sannan Ummu Salma ba ta fito ba yaran ma aka hana su, domin kar ta gansu ta yi rigima. Bayan sun tafi itama Hanan Hamma Saddam ya kai ta gidan su Habib tare da su Sultan suka je tunda a mota ne, Hanan ta ce ita kwana ɗaya za ta yi gobe a zo a ɗauketa Hamma Saddam ya dawo yana faɗa ma su Ammah. "Yarinya ta gaji da zuwa wannan gidan ta ce Uncle ni gobe ka zo ka ɗauke ni " Ya gama faɗa yana ta dariya Ammah ma sai da ta yi mirmishi. "Saboda su Sultan ne, ba ta son barin su ne." Ammah ta faɗa Amma sai Hamma Saddam ya hau cewa ba saboda haka ba ne, wannan gidan ai suna fama da rayuwa shi bai ma ga amfanin kai Hanan wajen su ba, uban fa ya ce ba ya son cikin me ya sa yanzu kuma zai karɓa. "Ai ba a canza ma tuwo suna Saddam, Habib shi ne uban Hannatu, kuma in ta je ba laifi ba ne ai ba wajen su take zaune ba, kuma ban da abin ka ma suna komawa kafin su dawo an ɗauki lokaci." Suna cikin maganar ne Ummu Salma ta fito ta tashi daga barcin tana jin yunwa ta zauna a gefen Hamma Saddam tana tambayan Harira. "Suna can bangaren Aisha." Wayarta ta koma ɗaki ta dauko ta kira Baɗɗo tana tambayanta abin da ta dafa, ta ce tuwo ne miyar zogale. "Bana jin ci, ki ce kawai Harira ta zo ta dafa mini wani abu." Baɗɗo ke faɗin me take so sai ta dafa mata anan sai ta ce ta bari kawai Hariran ta yi bayan sun gama waya Ammah ke faɗin ga tuwon ma nan da Baɗɗo ta kawo da yawa ta ɗiba ta ci mana. "Ammah ni ba tuwo nake so ba." Ammah ta kalleta amma ba ta yi magana ba. "Girman ki ne Sarauniyar Daurama, ko talo talo kika ce za ki ci sai a nemo miki." Ya gama faɗa yana dariya Ummu Salma ta daki kafaɗan shi tana hararan shi, Ammah na zaune kanzil ba ta sake cewa ba sai da Saddam ke ba da labarin sun yi waya da Hamma Lamiɗo akan aikinsa ya ce ya jira shi soon, lokacin da ya tura masa VC ɗin sa ya ce ya tura Mai martaba mai murabus a wancan lokacin sai jikinsa ya tashi shi yasa aka samu tsaiko amma yanzu za a neme shi in sha Allahu. "Allah ya amsa Amin." Ammah ta faɗa Ummu Salma da Saddam suka sake amsawa da Amin a tare. Harira ce ta shigo ɗauke da Junior ta miƙa ma Ammah shi ta yi saurin karɓan shi, tana masa wasa tana kiran shi da maigida na, Saddam na gefe ya ce Ammah yanzu kamar Junior ne ya kwace son da kike yi ma Baffa mu ai ba ma kya maganar mu." Received at 08:04 12 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta harare shi ba ta yi magana ba ya koma yana dariya. Ummu Salma na taya shi, kuma gaskiya ya faɗa Ammah yadda take son Junior kuma nunawa take kowa na gani ba kunya ba kamar sauran jikokinta da take nuna musu halin ko in kula, amma wannan har goya shi take yi ya yini a wajenta in ba nono zai sha ba, da yake ma ba shi da rigima sosai. Suna ta gulmanta ƙasa ƙasa ba ta ma san suna yi ba tana ta yi masa wasa, yana bangala dariyansu na yara, Harira kuma ta tafi kitchen Ummu Salma ta ce ta dafa mata indomie ta saka kayan miya amma kar ya yi yaji. Mintina kaɗan ta gama ta kawo mata ba ta ci ita kaɗai ba Beena ta zo ta zauna ta ce za ta ci Sultan kuma ba shi da wannan yana da kamewa kamar baban shi. Beena ce kamar ba ɗiyar Lamiɗo da Bilkisu ba, kamar ɗiyar Ummu Salma shegen surutu da ƙiriniya irin ta irin Hanan shi yasa ta so ta zo ɗaya yanzu ɗin ma tambaya take yi yaushe Hanan za ta dawo Ummu Salma ta ce gobe. "Mahma ni dai zan je wajen Hanan." Beena ta faɗa tana kallon Ummu Salma. "Aa ki bari za ta dawo." "No ni ina so na je za mu yi wasa." "Ke wannan gidan ai ba za su iya ɗaukan nauyinku ke da Hanan ba, madaran da kuke shan tea da ita ma ba za su iya siya ba." Hamma Saddam ya faɗa yana dariya Ammah ta yi masa dakuwa tana ba zai daina ba ko? "Na daina Amnah in sha Allahu " "Ba ka dariyan kaddaran wani domin kai ma ba ka san mai gobe za ta haifar ba." "Haka ne, amma mu dai ba mu cuci kowa ba Ammah, in sha Allahu rayuwarmu za ta cigaba da kyau har ƙarshe." Ta amsa da Allah ya sa, rigimar Beena na sai ta je wajen Hanan Saddam ne ya ɗauke ta suka fita ta girma shekaran ta Bakwai da wattani Hanan ce biyar Sultan kuma yana cikin shekarunsa na goma sha ne shekara mai zai gama primary, Hanan na primary 1 Beena kuma 3. Da yake yaran yan hutu ne suna cikin daula girman jikinsu ya ɗara shekarunsu ga wayau da iya mgana turanci da labarci kan ya zauna a bakinsu sosai a dangi ma yaran abin sha'awa ne kowa kallon su yake yi, mate ɗin ta ma da suka haɗu wajen renioun ma ta ga suna saka su a status har tambayanta suke yi wai yara nan nata wata makaranta suka yi ne? Ta ce a can Lagos ne, mamakin ƙoƙarin yaran suke gani. Kowa yanzu neman ta yake yi a rana ba ta san adadin wayar da take amsawa ba, sai dai ta ji ana cewa wane ne kaza na makarantarku ana roƙonta don Allah ta yi saving lamba matan kuma suna ta kamun kafa suna kawo matsalolinsu da cewa in ta fara taimako ta saka sunan su ta ce ba matsala za a yi komai cikin tsari za kuma a ba da tallafin ga waɗanda suka cancanta ne. Hanan washegari ƙanin Habib ya dawo da ita, sai bayan tafiyan shi ne Shamsiya ta kira ta tana magana dakyar ta ce ba ta da lafiya shi ya sa ba ta zo ba. Ga Hanan nan sun gode sosai. Ummu Salma ta ce ba komai, ta ga an dawo da ita da tsaraban bickit da su minti tana can falo tare da yan'uwanta. Ta yi mata sannu da jiki, Shamsiyar na tambayar yaushe za su koma!? Ta ce ba ta saka rana ba amma a cikin satin da zai shiga saboda makarantar yara. "Allah ya maida ke lafiya." Ummu Salma ta amsa mata da Amin suka yi shuru na wani lokaci. "Ummu Salma." Ta kira sunanta ta amsa tana sauraranta. "Don Allah ki yi haƙuri." "Ba komai ai na faɗa miki ya wuce." "Habib..' Ta yi shuru ta kasa faɗin maganar da take son faɗa. Ita ko Ummu Salma tuni ta haɗe fuska kamar Shamsiya na ganinta. Ita fa tsanar da ta yi ma Habib ko sunan shi ta ji an kira sai ranta ya ɓaci. "Ki yafe masa, don Allah." "Na ce na yafe ba wani abu." Ta faɗa cikin kosawa tana son katse wayar ne ta gaji da jin mgana ɗaya. "To in haka ne ga shi ku gaisa." Ummu Salma ta yi kasaƙe, tana jin Habib ya amshi wayar ya yi sallama da muryansa, wacce ba za ta bace mata ba muryan da a baya ta kasance lu'u lu'u a gare ta amma a yanzu ba muryan da tsana sama da muryansa. Ta ji ya yi sallama ya ƙara yi ta yi shuru ta kasa amsawa daga ƙarshe ma sai ta kashe wayarta. Tana gani Shamsiyar na sake kiran ta ba ta ɗauka ba. Received at 08:04 12 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ba ta fatan wata mu'amala ta sake haɗa ta da Habib har abada Shamsiya ma kawai saboda Hanan ne sannan tausayinta take ji amma ko ita ba ta son ta shigo jikinta har abada ƙawancen dake tsakaninsu ya ƙare tun a shekarun baya. Sako ta tura ma Shamsiyar domin ba ta so nan gaba ta sake yi mata wannan gangancin. "In kina so na cigaba da amsa wayarki ki nisanta ni da mijin ki, ba ni da wata alaƙa da shi, laifi ne ya roke ni tuntuni na ce na yafe ba bukatar wani abu kuma. Don Allah mu girmama junan mu ko saboda Hanan." "In sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba. Ki yi haƙuri." Shamsiya ta turo mata reply ta karanta ba ta bi ta kanta ba. Habib yana cikin wani shudaɗɗen babi ne na rayuwarta ya shuɗe har abada yanzu Lamiɗo ne a rayuwarta saboda haka ba ta buƙatar tuna rayuwarta ta baya Hanan ce tana zuwa wajen su amma har abadan ba za ta ba shi ɗiyarta ba kamar yadda ya ce ya bar mata, to haka ne Hanan ɗiyarta ce har gaban abada sai dai ya dinga samunta a matsayin aro. Habib daman ya san Ummu Salma ba za ta yi magana da shi ba Shamsiya ce ta matsa masa saƙon ma na Ummu Salman suna tare ya shigo shi yasa ya gani. "Ka yi haƙuri." Shamsiya ta faɗa tana kallon shi, ya girgiza kai kawai yana ɗan mirmishi. "Ba komai ni daman ban matsa ba, mai muhimmamcin yafiyar ne kuma tunda ta yafe shike nan." Bai sake magana ba ya tashi ya fita ta bi shi da kallon tausayi tana hawaye. Ko bai fada ba ta san yana son Ummu Salma har yanzu, sun sha suna mu'amalan aure ta ji yana kiran sunan Ummu Salma ba ta taɓa nuna masa ba, ita kaɗai take shan kukanta, koma mai ya faru ita ce sila, ita ce ta yi shuru amma Habiba ƙara ta kawo shi gidan su wai yana tare da ita amma yana tunanin matar auren da har ya mutu ba zai sake samun zama da ita ba, ta tona masa sirrin shi a idanuwan kowa har sakinta ya so yi Shamsiya ce ta hana shi ta danne shi. Habiba kaɗai aka bar Habib da jarabawarta mai zafi ce a gare shi, bayan wasu matsalolin rayuwa musamman talauci da halin babun da suke ciki, aikin koyarwa ne sai karshen wata karshen watan ma kafin nan duk an ci ba shi ga albashin babu yawa. Godiyarsa Allah Shamsiya tana taimaka masa shi yasa in ya kalleta sai ya gode ma Allah da ya sa itama bai rasa ta ba da yanzu rayuwarsa na cikin uku, yana karɓan sakamakon abin da ya aikata daki daki, ga takardun amma aiki ya gagara har ya gaji da tura CV Alhaji Sherif ma duk ya karɓa ya tuttura amma ba a dace ba a hakan ma godiya yake yi ma Allah da ya barsa da lafiyarsa. Lafiya jari ce in da ya rasa lafiya da komai ya kwaɓe masa. Shi ya yakice Ummu Salma a cikin rayuwarsa yana tunanin ita ce za ta shiga garari sai ga shi, ita ce ke cikin ni'ima shi kuma rayuwarsa na cikin garari, soyayyarta dake zuciyarsa ma kaɗai ishara ce ga masu hallayar irin na shi. * Ummu Salma da yara sun koma Daura bayan watan January ya raba tsakiya. Ko da ta koma ba ta samu Islam ba ta koma Kaduna za ta fara registration ɗin fara jami'ar Kaduna. Ranar da suka dawo ko bangaren Mai martaba ba ta je ba, tana idar da sallar isha'i barci ya rinjayeta. Washegari sai ta je can bangaren tun mangariba saboda cutar barcin dake damunta yanzu ko ita ba ta iya yi ma kanta wani abu, girkin ma Harira ce ta kama mata suka yi. Ko da ya shigo bangaren daga Fada har ta kwanta ta fara barci amma barcin bai yi nisa ba, ta kunna littafin Rufaffen Duma na marubuciya Ummulkhairi Sani Panisau a tashar tsakar gida tana sauraro, ta fara ji amma barci ya tafi da ita, wato kana girma rayuwarka na canzawa yanzu ko da kuɗi aka ce ta tsaya ta yi kallo ba za ta yi ba, karatun ma sai dai ta ji Audio. Ta san dai sun yi magana da Hamma amma ba za ta tuna me ta ce masa ba barci ya fizgeta sai da ya dawo daga masallaci ne sallar asuba tana zaune saman darduma tana azkar lokacin da ya shigo, ya cire babban rigan shi da wani farin harami sannan ya hau saman gado ya ɗau wayarsa yana dubawa. Received at 08:04 14 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta shafa addu'arta a duka jikinta sannan ta miƙe ta yaye hijabin jikinta, rigar jikinta fara ce mai santsi ta ɗora zani a saman rigan da za ta yi salla duka ta cire ta watsa su saman kujeran dake bedroom din sai jin ta kawai ya yi a saman jikinsa. "Good morning my king." Ya kalleta amma kuma bai bar kallon wayarsa ba. "Kin tashi lafiya? "Sarauniyar barci." Ya gama faɗa yana ɗan jan karan hancinta. Mirmishi ta yi kafin ta ce" Babynmu ne ke saka ni yawan barci da kasala." Ta gama faɗa tana jan hannunsa zuwa ƙasan maran ta dole ya ajiye wayar ya tallabeta, shafa cikin yake yi ita kuma tana shafa hannunsa, cikin na ta har ya ɗan turo. "Shi ne ya sa shekaranjiya aka ƙyale ni ko? "Ban ma san na yi barci ba." Ta gama faɗa tana yar dariya, ta cigaba da ba shi labarin barcin da ta dinga yi a Jimeta har Ammah na faɗin kamar wata kasa. "Ba fa na gajiya ko yini zan yi na kwana ina barci fa." "I see." "Jiya ina mgana shuru, kina ta dai kiran sunana na gaji da amawa na ƙyale ki." Ta ƙyalƙyace da dariya tana shafa ƙirjinsa. "Ni dai na san na ji muryanka amma ban san abin da ya faru ba." "Kina magagin barci." "Ga waya a kunne sai da na kashe" Ya ba ta amsa yana shafa gashin kanta zuwa wuyanta ƙamƙame shi ta yi "I miss you." Ya yi shuru bai yi magana ba amma ya ɗora kan shi a saman kanta, ita kuma tana kwance a saman jikinsa ya yin da shi yake kwance a saman gado. "Ka ji." "Na ce na yi kewar ka? Ko ba ka yi kewata ba ne? "Na yi" Ya faɗa muryansa a dishe kamar mai jin barci ta ɗago tana kallon shi akwai haske a ɗakin suna masu kallon juna cikin idanuwansu. "Ba ka yi ba." "Who tell you! I miss you sosaai." Ya faɗa yana sumbatar bakinta, ta yi masa mirmishi da fari, kafin ta koma ta kwanta a saman ƙirjinsa. "Ina son Hamma na " "I know." "Nima kin san ina son ki ko? Ta gyaɗa masa kai, sai ya gyara mata kwanciya a saman jikinsa. Yana faɗin su yi barci, ta ce to wayarta dake gefe ta zura hannu ta jawo ta shafa haske ya kawo hoton hannunsu ne tare da Banafsha wanda suka ɗauka a Jimeta tun tana jaririya shi ne a fuskar a wayar in ta buɗe wayar hoton su ne ita da Hamma Lamiɗo ranar graduation ɗin su na catering school ɗin da ta yi a Lagos tana son hoton nan sosai. Shi ya lumshe idanuwa kamar mai barci ita kuma tana duba wayarta, saƙonnni take dubawa sai ta ga Mami ta turo mata hoto tana shiga ta ga hoton Banafsha ne sun je park tare da Mami da Faruk, sai ta ɗago tana kallon shi lokaci ɗaya tana kara masawayar. "Banafsha an zama yan kaduna." Ya yi shuru bai yi mgana ba ya buɗe idanuwansa ya kalla ya koma sake ya lumshe idanuwansa "Hamma " "Uhm" "Ko za mu bar ma Mami Banafsha ne? Ya yi shuru kamar bai ji abin da ta ce ba. "Ba ka ce komai ba? Sai da ya ɗan muskuta sannan ya ce" Me kike so na ce? A' a in kina son ki ba ta ita go ahead daman ke ma a wajenta na gan ki." Kai tsaye ya yi maganarsa amma sai da ta yi dariya "Aa a ɗakin Ammah ka fara gani na dai." "Ina zuwa Kaduna saboda ina son Mami sosai." "To masu Mami ni ma dai ina da tawa Ammah." Ta fara dariya tana faɗin ita ba ta ce ba shi da shi ba "Kafin ki ce ne na faɗa miki." Ta mike zaune daga kan jikinsa. Ta zauna a gefen shi ta yi kwanciyar ruf da ciki da sauri ya ce" Na hana ki ko? Ba ki ga kina da lalura ba ne? Sai ta yi saurin mirginawa suna fuskantar juna. "Na bari." "Better." Ya gama faɗa idanuwansa na sake lumshewa. "Ya aiki? Akwai wahala ko Mulki? Ta gama faɗa tana shafa sajen fuskarsa. "Na fara sabawa, shekara ɗaya kenan ina matsayin Sarkin Daura." "Haka ne Allah ya kara tsare mana kai ranka ya daɗe." Ya amsa da Amin a fatar bakinsa ta fara masa tambayiyo daman aikinta kenan yana amsa mata, yau ma masarautar katsina zai je, akwai taron sarakuna na yankin katsina da zamfara da za a yi. Ya gaji ya ce mata su kwanta ta kara shigewa jikinsa har ya fara barci ta tashe shi da kiran sunan shi. "Hamma." "Ummu Salama." Ya kirata cikin ƙosawa, ya gaji yana so ya kwanta ba ya son hiran nan a yanzu. "Na ce miki mu kwanta ko? Bana son magana." Ya faɗa idanuwansa a lumshe muryansa ta yi laushi alamun da gaske barcin ya ke ji. Received at 08:04 14 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Hamma na tuna wani abu, saƙon da na yi maka na tafiyar Banafsha kaduna me ya sa ba ka amsa ni ba? Ta gama faɗa tana kallon shi, yana jin ta ya yi kamar bai ji ba har tana buɗe masa idanuwana da hannunta. "Ka faɗa mini sai mu yi barcin." Ya takura sosai ba ya son magana a lokacin kuma tana sane ta takura masa. "Ummu Salama." Ya kira sunanta a kausashe sannan ya buɗe idanuwana yana kallonta. "Kina so na yi miki faɗa ne? "Dililin da ka share saƙo na za ka yi mini bayani." Ta faɗa cikin shagwaba har tana murza idanuwana. "Faɗa zan yi miki, shi ne dalilin." Ta ware idanuwana a kan shi cikin mamaki. "Me ya sa kika ce ma Mami sai kin tambaye ni? "Ni zan ce a'a ne? "Kina so ki haɗa ni da mamarki ta yi mini faɗa ne? A jere ya yi maganar sai ta rasa ma abin da za ta ce masa. "Kin sa Mami tana mini faɗa wai na zo na karɓe Hanan wannan ma me nake nufi? Ummu Salma ta fara dariya tana danne bakinta. "Ba abin dariya ba ne." Ya faɗa ba wasa a fuskarsa sai da gimtse dariyarta "Ni na isa na ce kar Mami ta tafi da Banafsha ne? Ko ke ta ce za ta tafi dake ba zan ce aa ba." "Na faɗa maka ne saboda ya kama ta ka sani." "No, ba ki kyauta ba. Ba haka za ki yi ba." Sai ya ɗan miƙe zaune kaɗan yana kallonta. "Ba cewa za ki yi Mami na son tafiya da Banafsha ba neman izinina za ki yi ba. " "Cewa za ki yi Hamma Mami za ta tafi da Banafsha, a matsayin kin faɗa mini na sani ba neman amincewata ba." Ta ƙura masa idanuwana tana kallon shi wani son shi na kara shiga zuciyarta da gangan jikinta. "Mami ta ɗauka amincewata kika nema sai ba ta ji daɗi ba. Nima ban ji daɗi ba." "Sorry ni ce ban saka mganar dakyau ba." "Is Okay, shi ya sa kika ji ban miki mganar ba. Daman na ce zan miki gyara saboda next time." "To ba za a ƙara ba." "Da ni da ke da ya'yanmu duka Mami na da iko akanmu, ita ce za ta ba mu umarni ba mu ne za mu ba ta umarnin ba." "Haka ne ba za a ƙara ba" "Aa ni kawai na miki gyara ne, saboda ni ta ga laifina ba ke ba, ke ai tana son ki. Ba za ta ce ba ki kyauta ba." "Kai ma haka Ammah ke yi, ba ka laifi." "She's my Mother." Ya faɗa cikin alfahari, har yana wani mirmishi. Ta koma ta kwanta a saman kirjinsa shi kuma ya rumgumeta. Tana so ta yi magana ya yi saurin hana ta. "Ummu Salama." "Bana son mgana, in ba za ki yi barci ba you can go back." Ya furta a hankali tana jin abin da ya ce ta yi saurin kama bakinta tunda ta ji ya fara maganar ta koma bangarenta ta san ta dame shi, da har so ta yi ta ɗauko masa maganar haɗuwarta da Barrister Salamatu Doma amma dole ta yi shuru. Kamar yadda ya ce ranar Masarautar Katsina ya tafi sai yamma ya dawo, kuma ranar ba a wajensa ta kwana ba Bilkisu ce, sai da kwana ya zagayo kanta sannan suka yi maganar ya ce ba matsala ta fara shi dai ya ce duk abin da take buƙata yana nan yana jiran ta. Ta kira Barrister Salamatu sun yi mgana abu na farko sunan Foundation sai kuma register da Corporate Affairs Commission CAC. A katsina ta je ta yi register ɗin CAC Mai martaba ya haɗa ta da dogarai da masu kakin masarauta ita kuma sai ta tafi tare da Harira da Asabe ta shigar da sunan ta a ƙarkashin Foundation ɗin. Ummu Salma Muhammad Lamiɗo ta yi amfani da shi, daman ko asibiti da wannan sunan take amfani. Bayan an yi register kungiya ta kafu da kanta ta je ta faɗa ma toshon Sarki ya saka albarka nan take ya ce ya ba da gudummuwar miliyan goma, Fulani ta saka miliyan biyar, Gimbiya Shahida miliyan uku Gimbiya Amratu miliyan biyu, daɗi ya kama Ummu Salma nan da ta fara ƙokarin buɗe ma gidauniyarta asusun banki, guda uku ta buɗe first bank, Gt bank da Zenith bank, da kuma sunan gidauniya Sarauniya Daurama's Foundation, tuni har kuɗaɗen da aka ba su gudummuwa sun samu matsugunni a cikin ɗaya daga cikin bankunan gidanuniya. Ta saka lambarta da lambar Mami tare da Baɗɗo a duka bankunan da ta buɗe ma gidauniyar. Received at 08:04 13 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Mai martaba Lamiɗo ya ba da na shi gudummuwar shi ya ce tunda akwai tsarin za a raba kayan abinci na tallafi da azumi shi zai ji da komai, sannan ta ɗau masu mataimaka mata ga Baɗɗo daga can Jimeta kamar P.A ɗin ta sannan anan Daura akwai Salima matar Hafiz sai kuma wata Mardiya wazirin Daura kakanta ne, tana aure a gidan wani attajiri a katsina. Gimbiya Amratu ta haɗa su da Ummu Salma, tunda ita ma Hajiya Mardiyan a can katsina tana harkan gidauniya na ba da tallafi ga mata da ƙananun yara sannan a gefe ɗaya ga Mami ta ce ba za a barta a baya ba. Aikin alheri ne da ita za a yi komai cikin wattani biyu gidauniyar Sauraniyar Daurama Foudation ta zauna da kafafunta har sun buɗe karamin ofishi anan garin Daura Ummu Salma ce shugabar ta fara zama busy tunda suna ta tsare tsaren yadda za su fara fidda tallafinsu na farko na watan azumi dake gabatowa. Kowa ya ji ƙudirin Ummu Salma sai ya saka albarka ya yi son barka Yayyenta suna ta yabawa da basiranta da ƙokarinta Hamma Kabiru ko da suka yi waya sai da ya ce da a ce ta yi karatu mai zurfi da komai zai zo mata da sauƙi sai dai kawai ta yi dariya ba ta ce komai ba shi dai ba zai daina yi mata maganar komawa makaranta ba. Bilkisu ma sai da ta ji labari a bakin Sofia, suma a group ɗin su na iyalan Mai martaba Saleem ya faɗa Lamiɗo bai faɗa mata ba kuma da ta ji labari ba ta yi tambaya ba. Itama shiryen shiryen tafiya Canada take yi akwai wani course da za ta yi na shekara ɗaya amma ba yanzu take son tafiya ba sai karshen shekara kuma da suka haɗu da Ummu Salman a bangaren Lamiɗo ba ta nuna mata ta ji labari ba, ballatana ta yi mata fatan alheri, haushi take ji ganin Ummu Salma da wani cikin ita kuma shuru duk ta cire abin da ta saka na tsayar da haihuwar tunanin ta me ya sa za ta zo ta fita har yawan haihuwa? Ita ko Umma Salma abubuwan dake gabanta ma sun isheta ga tafiyar da handels ɗinta na girke girke tuni Youtube har sun fara biyanta saboda ta gama tara musu abin da suke so amma ita ba wannan ne a gabanta ba, ta kai in da ta ke muradi da kuma fata. Kuɗi ba matsalanta ba ne, suna da kuɗi ita cimma nasara da fata ne kawai a gabanta. An tsara yadda za a fara tallafin azumi, Mai martaba ya saka an kawo kayan abinci shinkafa na ƙananun buhu guda ɗari biyar ga taliya ga macaroni, ga manja da mangyaɗa ga rafar dubu goma na cefane, kuma a jikin duka kayan akwai sunan Sarauniyar Daurama's Foundation, an raba kayan gida uku ne, ɗaya anan Daura ɗaya katsina Hajiya Mardiya za ta raba ɗayan kuma aka aika da shi Adamawa wajen Baɗɗo a kuma rana ɗaya suka yi rabon bayan sun tattara sunaye, tunda an ta yawo da abin a kafafen sada zumunta bayan tantancewa aka cire adadin mutanen da za su samu tallafi. Ana azimu saura kwana biyar aka raba kayan tallafin Ummu Salma da kanta a gaban ofoshin su dake gaba da Masarauta kaɗan aka yi rabon mutane dafi dafi kamar salla, ga kayan abinci sannan ga kuɗin cefane duk da mata sun fi yawa amma kuma har da maza, an ɗau hotuna ana ta yawo da shi a kafafen sada zumunta da cewa matar Sarkin Daura Ummu Salma Muhammad Lamiɗo Sarauniyar Daurama ta yi rabon kayan abinci tallafi ga marasa karfi ƙarkashin gidauniyarta na Sarauniyar Daurama Foundation a garuruwan Daura, Katsina da jiharta ta haihuwa Adamawa Yola. Can ma Jimeta hakan ce ta faru a ƙofar gidan Baffa Baɗɗo ta tara na ta jama'ar tare da taimakon su Adda Suwaiba. A cikin waɗanda suka karɓi tallafin har da Shamsiya domin Ummu Salma ta ce a saka sunanta Mutanen anguwa suna ta godiya, domin kowa ya ji tallafin daga Sarauniyar Daurama ne sai ya cika da farinciki, ana ta yabon kirkin Baffa da cewa Ummu Salma ta samu kyakyawan tarbiya daga gare shi ne. Haka ma Katsina ya gudana da jagorancin Hajiya Mardiya Kaduna kuma Mami ita ce kamar ma'aji mai kula da kudaɗen gidauniya, komai ya tafi kamar yadda aka tsara, aka fara azumin ramadana cikin farinciki a lokacin kuma suka fara shirin tallafin kayan salla, shi ga mata ne da ƙananun yara sannan Ummu Salma ta yi Ramadan kitchen by Sarauniyar Dauramas Kitchen, har zuwa karshen azumi ta kuma yi giveaway ɗin dubi hamsin hamsin ga zakarun da suka fi ƙwarewa Received at 08:04 14 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby wannan abin ya sake jawo mata mabiya sosai kamar yadda suka tsara kafin sallar ma suka raba tallafin atamfofi da yadikan maza na yara, a garuruwa uku nan gaba Ummu Salma na fata tallafin gidanuniyarta ya zaga arewa gabaɗaya. Ga shi yaɗarwar da ake yi a social media ya sa gidauniyar ta yi suna sosai tunda Hajiya Mardiya na tafiyar musu da gidauniyar a zamanance, sannan Barrister Salamatu Doma na iya bakin ƙokarinta da shawara ko gyara, suna ta samun tallafin manyan kuɗaɗe daga manyan mutane da masu Gwamnati, kuma sai abin ya zo da ita matar Sarki ce har gidan Gwamnatin Katsina an kira Umma Salma ta je, ya ba da tallafin naira miliyan ashirin haka ma mai martaba Sarkin katsina ya ba da miliyan goma. Foundation ɗin kuma da yake na masu kuɗi da mulki ce sai ta fara da ƙarfinta ita kanta Ummu Salma mamaki take yi, amma dai tana yawan cewa bayan wannan nasaran nata akwai wani gwarzo, jarumi wato mijinta Mai martaba Sarkin Daura da bai amince ba da duk ba ta yi wannan ba, ga ciki a jikinta har ya turo Allah ya sa ba ta laulayi shi yasa ta samu damar aiwatar da ayyukanta shi kuma bai hana ta ba, sannan ta samu goyon bayan surukanta da mutanen dake zagaye da ita. Ranar ana gobe salla ma shanaye biyar suka yanka a Daura aka raba ma magidanta da dubu ashirin ashirin na cefane a katsina ma an yi haka sai Jimeta, Baɗɗo ma yanzu ba ta samun lokacin kanta mata suna fita wasu na shiga a gidan Ammah, sauƙin ta ma Ammah na nan ita ke ɗawainiya da Junior, sannan ga Hamma Saddam na gida yana taimaka mata da rubuce rubuce, a bangaren Hamma Abdulrahim ma shima yana ba da na shi gudummuwar, haka ma su Adda Suwaiba suma suna ƙokarin ta ya ta tantance matan da za a raba ma tallafi. Mami ma acan Kaduna ta yanka Sa itama ta raba shima Daddy ya jefa na shi gudummuwar ya ce ba za a bar shi a baya ba. bayan na salla sai kuma suka fara tsarin raba ma mata ɗari uku tallafin jarin da za su kama sana'a domin dogaro da kansu, suna da kuɗi sosai a ƙasa ko Hajiya Zaliha miliyan goma ta saka ita da Hajiya Kilishi, har da Hajiya Binta da Hajiya Zannura tare da yaransu duk sun ba da ta su gummuwar, tuni garin Daura da kewaye ya ɗauka kowa Sarauniyar Daurama hatta sauran danginsu dake ƙauye Ummu Salma ba ta manta da su ba tallafin na zuwa musu, sannan kuma hadiman masarauta ma da sauran dogarai da ma'aikata suna cikin alheri domin Sarauniya Daurama alheri ce, da salla haka ta yi ma Mai martaba mgana suma suka samu tallafi su da yan'uwansu gabaɗaya. Gimbiya Hadiza da yaranta na ta yi ma Bilkisu zugin tana zaune amma Ummu Salma na neman ta ƙwace komai, sunan ta kawai ake ji kamar ita kaɗai ce matar Sarki sannan ganin manyan mata na zuwa ganinta sai suke ganin Bilkisu ta yi sake, ita kuma ta saduda ne yau dai duk adawarta da nuna cewa Ummu Salma ba ta isa ba, sai ga shi a yau ta isa da ita ake damawa ita kuma ba ta son ta yi kwaikwayo ita likita ce ba ta da wannan lokacin shi yasa take son ta faɗaɗa bangarenta domin gobenta, duk abin da suke faɗi tana jin haushi amma kuma ba ta da yarda za ta yi, ba ta gasa amma ko su Fulani yanzu Ummu Salma ce gwana a wajen su, mutanen Daura kuma da kewayenta da sauran matan manya duk Ummu Salma suka sani a yanzu ba ita ba. Ita a ganinta haka ne amma kuma su a wajen su duk ɗaya suka ɗauke su. Ummu Salma ko da zuciya ɗaya ta fara wannan gidauniyar da kuma saka ran duk abin da take yi na lada ya kai kabarin Baffa ya samu salama, rana ba ta fitowa ta faɗi ba ta tuna da shi ba, albarkar da take samu na jama'a kuma addu'ar iyaye ce kawai dalilin wannan gidauniyar har waya ta yi da matar mataimakin shugaban kasa matan gwamnoni da matan Sarakai kaɗan ne yanzu ba ta waya da su, suna kawo mata ziyara saboda suna ganin kamar ta zo da wanii abu sabo da ba su sani ba. Ita ɗin da ake ganin ba kowa ba ne, ita yanzu wata ce. Tunda aka yi sallar azumi babbar salla ta karato Mai martaba Lamiɗo da Bilkisu za su tafi Saudiya da tare da Ummu Salma ne to ciki ya hana ta zuwa. Mami ma za su tafi tare da Daddy da Islam, Faruk kuma wajen Ammah za a kawo shi Barira kuma za ta je gida, itama ta kusa komawa can gabaɗaya za a yi mata aure. Received at 08:04 9 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Sai a lokacin Mami ta dawo da Banafsha da ta yi wayau, sai ƙirniya kamar Hanan Lamiɗo har yana faɗin ko haka goyon Mami yake? Ummu Salma surutu Hanan surutu da ƙirniya ga Banafsha ma, Ummu Salma ta yi ta dariya da wuri suka tafi tunda Lamiɗo ne amirul hajji na jihar katsina a shekaran Bilkisu kuma na cikin liktocin da za su tafi daga Jahar ta katsina. Ummu Salma aka bari a gida tare da yara Masarauta kuma an barta hannun Waziri kafin Mai martaba ya dawo. Da Babban sallar ma Foundation ɗin Sarauniya Daurama sun raba shinkafa da atamfofi sun raba ragunan layya ga mazan da ba su da karfi sun raba kayan salla ga mata da yara. Kamar yadda tsarin ya gudana, Ummu Salma so ta ke yi sai Foundation ɗinta ya yi karfi sannan sai ta fara tunanin samar da wani reshe domin buɗe wajen da za ta dinga koyar da mata da y'an mata girke girken zamani da na gargajiya tare da iya sarrafa fulawa domin samun abin dogara da kai, ta tara mabiya a shafinta na tiktok mabiyanta sama da miliyan buyu, youtube kuma ta kai subcriver dubu dari da Hamsin, kuɗin da suke biyanta duk a gidauniyarta take sakawa tana fata nan gaba kamar yadda suka buɗe ofishi a garin Daura su samar a katsina da Jimeta tare da Kaduna kafin sauran jihohin. Lokacin da su Mai martaba suka dawo cikinta na wattani takwas ne, duk da ya tsufa ba ya damunta sai dai ta fara fuskantar jiri da kumburin kafa daman kuma a General hospital Daura take awo asibitin da Bilkisu ke aiki sun faɗa mata stress ya saka jininta yana sama sosai sai ta fara jin tsoro, da ta faɗa ma Lamiɗo nan take ya ce zai nemi Visa ta koma Egpyt ta haihu kamar haihuwan Banafsha ba shawara ba ne umarni ne, haka kuma aka yi ya shirya musu tafiya kamar dai baya sai dai wannan karon tare da Ummin ikki ne Mami ba ta nan lokacin za a yi bikin Barira kuma ba zai yuyu ba ta nan ba ta Lagos suka ta shi amma sai da suka kwana uku a gidan su dake Lagos su James nan na ta kula da shi Bilkisu dai na yawan zuwa ita, tunda suna yawan zuwa Lagos hallatar Seminar na su na likitoci, motocin su na nan da shi suka zaga gari da suka zo da yake a can Daura Ummu Salma na amfani da GLK ɗinta da Mai martaba ya ba da ta da haihuwan Banafsha ne sannan akwai motocin Masarauta sai wanda ka ga dama za ka shiga direba da masu kakin masarauta su tuƙa ka bayan haka a ƙarshen wancan shekaran ma Lamiɗo ya siya musu sabbin motoci jifa jifai ita da Bilkisu. A watan july farko Ummu Salma ta sake haihuwar ɗan ta namiji kato mai kama da Mai martaba Lamiɗo ma a wannan karo daman tun a scan aka ce namiji za ta haifa, ba kuma jira Mai martaba ya dira a ƙasar ya yi ma yaro huɗuba da Hadi, daman a tare ya nema musu visa sune dai suka fara yin gaba daga baya shi ya biyo su, ba su daɗe ba wannan karon tunda lafiya lau ta haihu ba wata matsala kwanansu goma suka dawo Nigeria, sun sauka ta Abuja amma wannan karon a ɗaya daga cikin gidajen Mai martaba suka sauka suka kwana ɗaya washegari suka juya Daura bayan Adda Nauwara da Hamma Jibo sun je sun gan su. Tuni social media ta ɗauka Sarauniyar Daurama ta haifi ɗa namiji, waya ko har sai da ta gaji da amawa. Da suka dawo baƙi manya manya suna ta zuwa, musamman amaryan Gwamnar Katsina da suka zama ƙawaye da Ummu Salma, ga Hajiya Mardiya matan sarakuna waɗanda ma ba sa aminta suna girmama ta itama haka sannan kama daga mates ɗin ta wasu ma ba ta iya gane su ba, a can Adamawa ma yan anguwa wasu ma ba ta san su ba suna kiran ta a waya don dai ta zama wani abu shi shi ya sa kowa ke son raɓarta rayuwa kenan. Rayuwa ta saka yau ita abar girmamawa ce ga kowa, kowa na son ya raɓe ta saboda ta zama wani abu. Shamsiya ko kamar ta yi mata sujjuda, rayuwarsu akwai tausayi har ciki ta sake samu bai zauna ba. Shi yasa itama Ummu Salma ta yi magana suka ɗauki Shamsiya ta a cikin agent ɗinsu, tana kawo musu sunayen mabuƙata su tantance sannan duk tallafin da za a ba da ana bayarwa da ita, ita kanta Baɗɗo da ke adawa yanzu ta daina daman ta ce burinta kenan Ummu Salma ta samu arziƙin da watarana daga Shamsiyar har Habib a ƙarkashinta za su samu sai ga shi ya faru tun a duniya suna ganin ƙarshen su. Received at 08:04 14 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby A Masarautar Daura wannan karon aka sake yin taron sunan Hadi wanda Ummu Salma ta ce za su dinga kiran shi Sadauki, tabbas mai sunan Baffa ya cancanci ya zama Sadauki finally dai ta samu mai sunan Baffa shi ya sa aka ce wani hanin ga Allah baiwa ne sannan wani jinkirin alheri ne. Taron sunan da ya haɗa manyan mata masu ji da kansu, ma su ji da mulki da kuɗi bayan Baɗɗo yanzu Ummu Salma na da wasu mutane da suke da muhimmanci amma ba wanda zai kama kamar Baɗɗo a wajenta. Akwai Badi'a ga Sakeena mutanen England ga Amaryan Gwamnar Katsina duk da ta girme mata sannan ga Hajiya Mardiya ga kuma Hajiya Hauwa(Anty Hairi) sai kuma Dr. Fadila Kabir, Anty Fadila suna da alaƙa da Masarautar Bunza shi yasa Ummu Salma ta san ta, ga Barrister Salamatu Doma, ga Hajiya Aisha Ahmad iya, ta santa sanadiyar Foundation, mace ce mai son kyautatawa da taimakon marasa karfi ga kuma Hajiya Zainab Inuwa(Antysis) itama sanadiyar Gidauniya ta san ta ana ɗaukan nauyi tana kai ruwan sadaka asibitoci da makarantu, itama mace ce mai kirki da karamci. gidauniyar Sarauniyar Daurama ma na shirin tallafa mata domin aikin alherin da take yi ya zagaya garin Funtu'a gabaɗaya. Kamar sunan Banafsha wannan sunan ma haka Ummu Salma ta sake tara dukiya kamar ba son zafin ta ba wannan karon Ummu Balki da Ummin ikki sai da ta yi sati uku da haihuwa suka koma Mubi Mami ta zo taron suna ba ta kwana ba ta koma gidan ba kowa tunda Barira ta yi aure ba ta samu wata mai aikin ba sannan ga makaranta, Allah ya sa ma Islam na kusa to itama karatu ya saka ta gaba ko sunan Sadauki ba ta samu zuwa ba. Bilkisu ta shigo ta yi barka ta dauki Sadauki ta gani, daga nan ba ta ƙara shigowa ba amma ta aiko da kayan jarirai masu kyau ta ce a ba ma Sadauki Ummu Salma ta ji daɗi a zuciyarta ta ce Bilkisu ta fara canzawa, sannan har shi kan shi Mai martaba da ta faɗa masa ko da bai yi magana ba amma gefe da gefen bakinsa ya motsa alamun ya ji daɗi. Rayuwa ta cigaba da gangarawa gefe ɗaya Ummu Salma na renon Sadauki da taimakon su Harira sannan tana gudanar da Foundation ɗin su ƙarshen shekara na yi Bilkisu ta tafi Canada shekara ɗaya za ta yi sannan ta dawo yara kuma suna tare da Umma Salma ga Hadimai su Anitha ma duk suna nan amma sukan je garuruwansu hutu lokaci bayan lokaci. Zuwa lokacin gidauniyar Ummu Salma ta kafu sosai sannan kuma yanzu ƙokarinta samar da wajen da za ta buɗe kamar makarantar koyon girki sun fara magana ma da Mai martaba ya ce za a gina mata tunda tana ra'ayi. A lokacin shekaran Baffa uku da rasuwa shi kuma Lamiɗo yana da shekaru biyu a saman Ƙaraga. Abubuwa sun canza domin ko can jimeta ma an ƙara gyara gida ya zama wani mansion. Hamma Saddam ya samu aiki da kamfanin leadership dake Abuja kiran sa kawai aka yi yaje aka yi masa gwaji kuma ya haye. Baɗɗo ma wani cikin ne da ita amma hakan bai hana ta aikin alheri ba. Shekaran ɗaya Bilkisu ta yi a Canada ta dawo Mai martaba ya kai mata ziyara har sau biyu tana dawowa sai ga ta da ciki har ya fito ma. A shekaran Ummu Salma ta je Saudiya ta sauke farali ita da Mai martaba Lamiɗo suka je Bilkisu tana gida tare da yara, yanzu bayan dawowarta tana duba majinyata a clinic ɗin Masarauta bayan ta dawo daga Canada kuma sai ta koma aiki da Federal goverment. Bilkisu ta haihu ta ƙara samun namiji Lamiɗo ya ba ta zaɓi ta zaɓa masa suna Aliyu. Burin Ummu Salma ya cika ta je ka'aba ta yi ma Baffanta addu'a ta yi ma mijinta da yaransu ba wanda ba ta yi ma addu'a ba. Foudation ɗinta na ta cigaba sun samu nasaran buɗe ofishi a Jimeta tunda nan ne mafarin komai, sukan je Jimeta da Babban salla in suka je ana kai Hanan gidan mahaifinta ta kwana biyu. Mai martaba Lamiɗo ya cika alƙawari an siya fili a cikin garin Daura an kira magina da mazana sun zana, magina sun fara ginin center ɗin da Ummu Salma za ta buɗe na koyon girki, sannan duk shekara yanzu suke ba da tallafin jari ga mata, kuma alhamdullah matan da suka samu tallafin sun samu abin dogaro Shamsiya yanzu sabulun wanke wanke take siyarwa da turaren ƙamshi na ɗaki har da na tiolet a jarin da aka ba tana kuma ganin cigaba har Habiba ta kawo an ba ta jari da wasu Received at 08:04 9 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby ƙannen Habib ko bakomai su ci albarkacin Hanan. Sai da suka samu ofishin Jimeta sannan suka samu na Katsina Hajiya Mardiya na kula da shi Lamiɗo na da shekara huɗu a kan ƙaraga Fulanin Daura ta rasu mai Martaba mai murabus da ake ganin kamar shi ne ba shi da lafiya to ta riga shi tafiya mutuwar da ta girgiza ahalin Muhammad Shitu tsohon sarki gabaɗaya an yi rashi a masarautar Daura, bayan rasuwarta Lamiɗo ya so Ammah ta dawo Masarauta da zama ta ce tana nan a Jimeta. Tunda kuma Lamiɗo ya yi magana ta ce a'a ba wanda zai iya tanƙwarata. Tuni an saka Banafsha a makaranta da itama bakinta ya buɗe, wannan karon sai da ta yaye Sadauki sannan Ummu Salma ta ƙara samu cikin. Kuma a lokacin ma ta gama yanke shawaran za ta koma makaranta ta haɗa degre ɗinta akan abin da take so wato girke-girke tunda yanzu tana mu'amala da mutane sosai. Tana faɗa ma Mai martaba, shi kuma ya ba ta goyon baya ta siya Jamb ta yi a garin katsina, kowa ya ji za ta koma makaranta sai ya yi mamaki Hamma Kabiru ya fi kowa jin daɗin haka ya ce lokaci bai ƙure mata ba. Ta samu nasaran cin Jamb, ta yi kuma post UME ta samu nasaran samun course ɗin da ta ke so. Bechelor of Arts BA in culinary Arts 4years program ne a Alƙalam University Katsina. Mai martaba Lamiɗo ya siya mata ƙaton gida ta koma can da zama, amma tana zuwa weekend duk sati ko shi in ya samu sarari ya leƙata tana tare da Harira da Asabe sai kuma direba guda ɗaya sai kuma escort mace tana aiki da DSS, sai maigadin dake kula da gidan suna zaune tare da ita yara kuma suna Daura Sadauki ne kawai tare da ita sai cikin jikinta. Da ta fara karatun ta ji kamar ta bari saboda wahala amma da ta yi kamar ta juya sai kafaɗan Lamiɗo ya tare ta sai ta sake miƙewa ta jajirce, tana kuma karatunta tana cigaba da gudanar da gidauniyarta tare da tsare tsaren buɗe SARAUNIYA DAURAMA CATERING CENTER DAURA. Tana so a yi gagarumin biki za ta gayyaci duka manyan Food bloggers na arewa wajen taron buɗewa sannan ɗaliban farko kyauta za su samu karatu, sannan za a ɗauki ƙwararrun malaman da za su dinga koyarwa itama tana so ta zama malama burinta ta gama karatu ta kara CHEF a gaban sunan ta. Wato CHEF UMMU SALMA MUHAMMAD LAMIƊO.. burinta guda ɗaya ya cika sai godiya yanzu ɗayan ne take fatan ya cika kamar yadda ta ɗaura niyya. *Janafty* Received at 08:04 7 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby RUFEWA. BAYAN SHEKARA HUƊU. Ƙarfe shidda na yammacin ranar laraba suka iso Daura. Direba ke jan ta a sabuwar motar ta corolla ta kamfanin Toyota shi dai Allah ya ƙara masa lafiya Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ya fi son kamfanin toyota in dai a bangaren motoci ne duka motocinsa kamfanin ne har waɗanda yake siya musu suma kamfanin Toyota ne. Tare da Harira suke tafe sai Rukayya(Fulani) sai matashin cikin jikinta ɗan wattani biyar, sai dogari guda ɗaya da escort ɗin ta Fadila. Harira ke riƙe da Fulani da jakar tarkacen kayanta dake ciki, ƙaramar jakar Ummu Salma tana hannunta ta hana Harira ɗauka kar kayan su yi mata yawa, tunda itama ba ita kaɗai ba ne akwai ƙaramin ciki a jikinta. Harira yanzu matar aure ce, direban masarautar da Mai martaba ya ba ta suka koma katsina shi ya aureta a shekaran da ta gabata suna zaune a katsina tare da ita, Harira yar amana ce a wajenta ba ta fatan su rabu har abada shi yasa ta fi kowa jin daɗin auren Harira a kusa da ita. Sannan ita karan kanta ta ba ta ma jari ta fara kasuwanci domin dogaro da kanta. Sanye take da atamfa mai blue sai abaya kalan blue da mayafi takalmin kafarta mai sauƙin tudu ne, Ummu Salma Sarauniyar Daurama ta yi wani irin kyau da jikin murjewa tana tafiya ɗaya bayan ɗaya Fadila da Harira na take mata baya, dogarai da Hadimai na zubewa wajen kwasan gaisuwa. A bangaren Bilkisu suka fara yada zango lokacin tana Katsina Mai martaba ya faɗa mata Bilkisu ba ta da lafiya har an yi addmmiting ɗinta a asibiti, ita da Aliyu ta ɗauka ma ko laulayi ne tunda tun bayan da ta haifi Aliyu ba ta ƙara haihuwa ba, ita ko ta yi Rukayya wacce ta ci sunan Fulani sai kuma ga ta ɗauke da wani cikin, to yaushe ma Bilkisu ta zauna a gida ta yi wata biyu? A cikin shuɗewar shekaru huɗu ta tafi karin karatu ƙasashe sama da uku bayan canada yanzu haka tana koyarwa a Deparment of health Sciences A ABU Zaria shima ɗin a wata sau uku take zuwa kuma bayan aikin ta na asibitin Federal medical center Daura, ba irin shawaran da ba a bata na cewa ta buɗe clinic ba amma ta ce ba ta so, ita ba ta son ta yi abu ace ta ga wani na yi ne har yanzu ta na nan matsayinta sai dai a kwaikwaya a wajenta. Sannan tana son yin abin da wani bai taɓa yi ba, shi yasa take aiki a matsayinta na ƴar Sarki kuma matar Sarki. A ɗakin su kaf ita kaɗai ce take aiki kuma hakan abin alfaharinta ne ba domin kuɗi ko mulki ba sai domin ra'ayinta ne hakan. Yara duk suna nan suna ganin Umma Salma suka rufe ta da oyoyo Mahma suna rige rigen ɗaukan Fulani. Sultan ne kaɗai ba shi a falon yana cikin ɗakinsa Sultan an girma an zama samari shekarunsa sha biyar yanzu haka yana jss3 ne a makaranta. Hanan shekarunta goma kenan Beena kuma sha biyu, Hanan na primay 5 ita kuma Beena na Jss1. Banafsha shekarunta takwas daidai da adadin shekarun zamowar Lamiɗo Sarkin Daura. Sadauki shi ne shidda da wani abu sai Aliyu sai Fulani dukkansu suna makaranta Fulani ce kawai ba a saka ba sai ta shekara uku. Bilkisu na ciki sai da Sabuwa ta shiga ta yi mata mgana, Sabuwa da Hidaya na nan yan amana, Anitha ce dai ta koma garinsu ta yi aure Debora ma da kanta ta bukaci tafiya aka yi mata kyakyawan sallama. Lokacin da Bilkisu ta fito surutun yaran ya karaɗe falon kowa na faɗa ma Ummu Salma labarin abin da ya faru da ba ta nan, wani abun birgewa yaran su a tare suka taso cikin shaƙuwa, in Bilkisu ba ta nan yaran na wajen Ummu Salma in kuma dukkansu ba sa nan suna wajen Gimbiya Shahida a gidan Mai martaba tsohon Sarki burin Lamiɗo ya cika ya haɗa kan iyalansa a waje ɗaya. Sun gaisa da Ummu Salma kamar yadda suka saba ta yi mata ya jiki ta amsa suna nan a yadda suke mu'amalansu amma an ɗan samu canji kaɗan tunda yanzu suna da lambar juna in wani abu ya faru ɗaya na shiga wajen ɗaya. "Aliyu ma ya sha ciwo Ali sannu." Ummu Salma ta faɗa tana shafa kan yaron da ya kwanto da kansa a saman cinyarta. "Zazzaɓii ne kawai." Bilkisu ta ba ta amsa a yanayin maganarta. Ummu Salma ta gane cewa ƙasaita da jin kai a jinin Bilkisu ne ba za ta iya bari ba "Allah ya ƙara sauki ke kuma Alkah ya raba ku lafiya." Received at 08:05 9 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ta faɗa tana dariya Bilkisu ta kalleta ba ta ce komai ba ta kauda kanta. Sai ta ɗan yi mirmishi daidai lokacin da Ummu Salma ta mike matashin cikinta ya bayyana ta bita da kallo. Rayuwa kenan yau ga shi Ummu Salma ya'yanta uku tare da Lamiɗo har ga cikin na huɗu, a baya ji take yi in wata macen ta raɓu da Lamido har suka haihuwa za ta iya kashe kanta da taimakon Allah da taimakon Addu'a Allah ya saukaka mata kishi, shi yasa ta mayar da kanta Busy saboda kauce ma shiga tunani da ruɗani, itama da ta yi ta fama da ciwon jiki ta ɗauka ciki ma ta samu har Lamiɗo ma fatan da ya dinga yi kenan ashe ba ciki ba ne. "Ke dai Allah ya sauke lafiya. Amma ni ba ni da komai." Bilkisu ta faɗa itama bayan ta miƙe tsaye. "Kai wai ba cikin ba ne? Ummu Salma ta tambaya tana riƙe baki. "Na ce ma Hamma ko dai mun samu ƙaruwa ne ya ce e" "Haka zai ce kin san shi ba ya son tambaya." Bilkisu ta faɗa tana mirmishi, ta daɗe tana fafin Lamiɗo na musamman ne sai a yanzu ta fahimci ya fi na musamman. Ba za ki taɓa jin mganarki a bakin kowa ba yana da kamewa da rike sirrin kowa ya san iya zama da matansa sosai. "Ban ji daɗi ba gaskiya." "Haka Allah ya so." "Haka ne Allah ya kawo mai amfani " Bilkisu ta amsa da Amin a saman leɓenta. Tana kallon Ummu Salma, yanzu ko tana so ko ba ta so ta karɓi Ummu Salma a matsayin kishiyarta domin ta fahimci gaskiya tuntuni. Tana kallonta tana mamakin yadda take da ƙoƙari ga haihuwa ga karatu ga sauran ayyukanta. Tana ganin ƙoƙarinta sannan tana jinjina mata ga shi kusan a wata sau biyu ko uku tana hanyar dawowa Daura. Sallama ta yi ma Bilkisu yaran suka tashi za su bita Bilkisu ta ce su je can bangaren Ummu Salma dama ta gaji da hayaniyar su. Suka ɗumguma zuwa bangaren Ummu Salma, duk da ta so su zauna a bangaren Bilkisun saboda akwai ayyukan da za ta yi. Amma ba ta da yadda za ta yi tunda sun maƙale mata, tunda suka koma bangarenta suka tasa ta suna kirga sunayen in da za su je hutu aƙarshen shekara. Hanan da Beena suka ce Adamawa da Lagos, Banafsha ta ce Kaduna gidan Mami, Sadauki ya ce Abuja Ali ma ya ce Abuja Ummu Salma ta ce duk za su je duk in da suke so, daman ita ce ke tafiya da su hutun, ko wancan shekaran sun je Lagos tunda gidajensu na can su James na kula da su. Sun je har Jimeta ba za su manta mafari ba daga can suka sauka a Kano wajen Bilkisu suka kwana ɗaya suka dawo tare Masarauta, ita ce daman mai biye ma yaran Bilkisu ba ta da wannan lokacin, Mai martaba kuma sha'anin mulki ba ya barin shi ma, amma wannan shekaran tana so su je hutun gabaɗaya har da shi da Bilkisu. Kiran mangariba ya sa hayaniyar yaran ya ƙare, Sultan ya shigo ya ce Sadauki da Ali su zo su tafi masallaci sun san in ba su je ba Papa zai yi faɗa. Matan kuma suka yi a gida. Ummu Salma na idar da salla ta faɗa kitchen yau 8 ga watan September yau Hamma Lamiɗo ke cika shekaru arba'in da takwas a duniya ita kuma tana da talatin da takwas a jibi kenan. Dalilin dawowanta kenan daman sai kuma za ta je Center ɗinta watan da ya fita ba ta samu sarari ba, sau abu na uku kuma ta duba Mai martaba ya dawo daga London ganin likita, Mai martaba tsohon Sarki yana nan da ran shi cikin ƙoshin lafiya sai dai jikin girma da tsufa. Burukan Umma Salma sun gama cika a duniya. Gidauniyarta ta shahara a cikin shekaru shidda a arewa wajen tallafama mutane, suna da afisoshi yanzu a garin Kaduna da Abuja bayan na Daura da Katsina ga na Jimeta. Sannan shekaru biyu da suka gabata ta samu nasaran buɗe Cooking center ɗinta, gini ne mai girma akwai ajujuwa ga ɗakunan girki ba abin da babu, an ɗauki malamai ƙwararru da suka cancanta suka samu ƙwarewa a bangaren da za a yi taron buɗe wajen Ummu Salma da taimakon mijinta Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ta gayyaci manyan mutane, sannan ta gayyaci manyan masu girke girken online na arewa sannan a ɗaliban farkon da aka fara da su training ne na wattani uku kyauta sannan an ba su certificate da jarin dubu hamsin daga Gidauniyar Sarauniyar Daurama. Received at 08:05Reactions: ❤ 10, 👏 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Ana yin tranning na wata uku, wata ɗaya, sati uku, har na wattani shidda wajen ya samu karɓuwa sosai kuma kamar tallafawa ne ga mata da garin Daura gabaɗaya. SARAUNIYAR DAURAMA COOKING CENTER ya samu shaidar Rigister NAFDAC National Agency for Food  and Drug Administration and control in Nigeria. Ummu Salma na can katsina tana karatu amma in ta samu sarari ta zo Daura tana zuwa itama ta koyar duk da ta ce itama har yanzu tana koyo ne.Ɗayan burinta ne ke gabda cika, yanzu haka tana shekaran ƙarshe a Jami'a a ƙarshen watan gobe za su fara final exams ɗin su, Finally bayan duka wahalhalu da rashin barci yau burinta zai cika za ta haɗa Degree a bangarenta da take so wato girke girke, da gaske ne karatu yana da wahala amma in ka saka yaƙini da jajircewa Allah zai tallafa maka. In ta tuna gudummuwar da Lamiɗo ya ba ma rayuwarta sai ta ji tana hawaye anan duniya babu abin da ba za ta iya yi masa ba ciki har da rayuwarta ga fansar na shi rayuwar. Ya nuna ma duniya shi Miji ne, uba, Yaya kuma shugaba. Ya ba ta kafaɗarshi ta jingina ya juya mata baya ta kishingiɗa ya zama ginshiƙi na rayuwarta. Mami ce sanadi shi yasa har gobe ba kamarta a wajenta. Yanzu haka Mami aikinta na koyarwa ta ajiye tana zaune a gida tana hutawa tunda shekaru sun ja, sai dai kawai ɗan harkokin Foundation ɗin da take gudanarwa anan Kaduna. Islam ta gama degree ɗinta ta ɗora master ɗin ta tana Kano BUK. Faruk kuma yana jami'ar madina can ya fara karatun shi, mahaddaci ya ke son zama. In ta yi salla biyar a rana kamar yadda take saka Baffa a cikin addu'o'inta haka take saka Mami, ita ce tsanin da rayuwarta take kan wannan bingiren har kuma gobe ita ce ɗiyar ta Lamiɗo har abada ɗan Ammah ne. Tunda ta ce ta ba shi tun yana ƙarami har abada ta yi kyautarsa ba ta taɓa nuna duniya ɗanta ba ne. Har Kaduna suna zuwa da yara su yi mata hutu Ammah na Jimeta, tunda ta ƙi yarda ta dawo Daura ta zauna. Shekara ɗaya da rabi kenan Hamma Saddam ya yi aure, ya auro buzuwa daga adagex gashinta har gadon baya amma irin baƙaƙen buzayen nan ne masu kyau suna zaune a garin Abuja, amma ya gyara bangaren su na gida Jimeta nan suke sauka in sun je gida, Ammah girma ya zo amma tana cikin jin daɗi Baɗɗo haihuwanta uku duka maza su Adda Suwaiba ma duk suna zaune lafiya Hamma Abdullahi ne ya gaji Baffa tunda daman tare suke kasuwanci ya cigaba da gudanar da kasuwancin su har kuma gobe komai Mai martaba Lamiɗo zai yi ta hannun Hamma Abdullahi ne akwai amana a tsakaninsu. Sannan duk da yanzu Lamiɗo Sarki ne Amincin dake tsakaninsa da Hamma Kabiru bai rusuna ba. Shi ne amininsa da zai iya tattauna komai na shi da shi. Hamma Kabiru da iyalansa suna zuwa Daura su yi musu hutu duk lokacin da suka samu sarari suma suna zuwa tunda har naɗin sarauta Lamido ya yi masa maji daɗin mutanen Daura. Rayuwa ta yi kyau sai dai godiya Allah Baffa shekarar sa tara kenan da rasuwa amma har a wannan lokacin mutuwarsa na yawan fami ga iyalansa Baffa Salihu ma ya rasu shekaru biyu kenan yanzu Baffa Umaru ne kaɗai ya rage su Umma Balki duk suna nan suna cikin godiya da aminci. Ummi ikki da Ammah amintarsu tun na yarinta babu abin da ya canza sun manyata amma kuma amintarsu bai yi rauni ba. Rayuwa juyi juyi na gaba ya koma baya, an yi wayi gari yanzu Ammah ba ta wannan rawan jikin ga Bilkisu. Ita dai Ummu Salma ta ga canji sosai ta yi mamakin me Bilkisu ta yi ma Ammah! Duk da ko a fuska ba ta nuna wani abu amma ta rage zaƙewa kan lamarinta ko rawan jikin in suka zo Jimeta, tana so ta yi ma Ammah magana sai ta sha'afa sai da Baɗɗo ta faɗa mata abin da ya faru ta san ba banza ba canjin Ammah, ashe tun tana da cikin Banafsha, lokacin da matar mai martaba sarkin kano ta rasu, Ammah ta kira Bilkisu a waya ta yi mata gaisuwa bayan sun gama mgana ita Ammah ba ta kashe wayar a can bangaren ba, haka itama Bilkisu ta ɗauka Ammah ta kashe ne, ana ta mganar Ummu Salama da su Gimbiya Hadiza, Bilkisu ta buɗe baki ta ce ta tsani Ummu Salma da iyayenta da mganganun da take yi na raina su Ammah, ba ta san Ammah ta gama ji ba tas sannan ta kashe wayarta, Ammah ashe ta sha kuka jikinta ya yi sanyi, ta kasa faɗa ma kowa Received at 08:05 13 people reacted with ❤ [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby kar a yi mata dariya. Da Ummi ikki kawai ta tattauna mganar ita kuma ta ce ishara ce, gwara ta riƙe ƴaƴanta Ummu Salama dai ɗiyarta ne, haka ma Lamiɗo, Bilkisu kuma ta bar ta da halinta ga ta ga duniyar nan, Ummu Salama kuma da Lamiɗo kuma smutu ka raba. Shike nan Ammah ta kama kanta, yanzu kawaicin duk da take yi ma Auta ta rage sosai da Baɗɗo ke ba ta labari ga dariya ga takaici wato rayuwar nan darasi ne mai zaman kanta abin da ya sa ka dariya watarana kuka zai sanya ka, ta wani bangaren ta ji daɗi da Ammah ta fahimci halin Bilkisun an ce Bilkisun har Ammah ta kira a waya tana tambayan ko ta yi mata wani abu ne ta ga ta canza mata Ammah ta ce ba komai. Amma tabbas Bilkisu ta sha jinin jikinta, ganin Ammah da ke ta kanta ma yanzu ta daina dole ta yarda makaman yaƙin ta. Shamsiya ta samu canjin rayuwa ta sillar Ummu Salma, har yanzu tana aiki da su a Foundation ɗin su sannan Habib ya samu aiki a wani kamfani sarrafa takalamin fata anan garin Jimeta sun samu canjin Rayuwa. Suna nan tare da Habiba wacce ta haihu ɗiya mace har takwara aka yi ma Ummu Salma yanzu ta daina adawa itama, tunda ga shi sanadiyar Umma Salma ta samu jari tana kasuwancin online, sannan Habib ya samu rufin asiri ta yarda ta haihu da shi Shamsiya dai har an juya mata mahaifa domin ta yi rauni ta gaji da ɗaukan ciki tana ɓarin shi, Hanan tana zuwa musu hutu in dai ta je Jimeta. Ta riga ta san cewa Papa ba babanta ba ne, ta tambayi Ammah ta faɗa mata gaskiya sannan ta tambayi Lamiɗo ya amsa mata da cewa shi ne babanta amma mahaifinta Habib ne wanda take ce ma Abba. Duk da ta ji ba daɗi amma ta gode ma Allah, tunda tana da baba guda biyu. Riƙon ta da duka rayuwarta na Hannun Lamiɗo da Ummu Salma ne, amma in ta je Habib da danginsa na iya ƙokarin su wajen kyautata mata duk da sun san ba za su iya yi kwatanta mata gatan da Hanan take da shi ba. Sai dai su yi abin da za su yi Hanan ko kayan jikinta kaɗai ka kalla kasan yarinyar yar gata ballatana fatar jikinta, ga turanci ga labarci ga tarin ilimi, Habib ya saduda ya fahimci rayuwa ya gane kuskuren shi  ya fahimci cewa Ummu Salma na sama shi kuma yana ƙasanta. Har yau har gobe tana ɗora girke girke a shafukanta na yanar gizo, ta samu jama'a ta samu duniya sai godiya sannan har Pandora award ta karɓa a wancan shekarar a matsayinta na jajircacciyar mace mai tallafama gajiyayyayu da marasa ƙarfi sun je tare da Mai martaba Lamiɗo da yara suka karɓo award din tare, da aka bata shi ta ba mawa domin ta ce duk abin da ta kai a yau kafaɗarshi ce ta cinciɗata. Haka ta faɗa a wajen bayan yan jaridun sun tambaye ta ya take ganin nasaranta ko matakin da ta kai a yau? Hotunansu suka dinga trending a kafafen yaɗa zumunta ana faɗin sun bala'in dacewa ga shi suna kama da juna aka fara yawo da faɗin yan'uwan juna ne shi ya sa suke kama da juna, ga yaran su gwanin sha'awa kamar ya'yan turawa A garuruwa da dama sun ba da an yi rijiyoyi da bohol sadakatul jariya ga Baffa ta yi sannan suma yayyenta duk sun yi. Sau uku ta je Saudiya Umra kuma ba ta san adadi ba. Fulani ma a England ta haifeta wannan haihuwan ta ce a Saudiya za ta haihu. Bilkisu ma haihuwan Ali a Abuja ta haihu. Kasashen ƙetaren da ba ta je ba kaɗan ne sai ga ta har ƙasar Jordan ta kai ma Jamila Umar takwaran Janafty ziyara sanadin marubuciyar nan ta online ta san ta. Namesake tana da mutumci da girmama baƙonta Allah ya ƙara ma rayuwa albarka. Rayuwa ta cika da tarin ni'ima sai godiya. Lamiɗo na gudanar da mulkinsa cikin tsanaki, talakawa da mutanen gari suna son shi Yazeed da Sagir duk sun dawo gida sun yadda makaman yaƙin su, sun zo sun haɗa kai domin cigaban Masarautarsu. Sun yi aure sannan Lamido ya yi musu sabon naɗe naɗe, gabaɗaya manyan hakiman yan gidansu ya ba mawa, tunda kwanaki rigima ya ta so yaran ƙannen marigayi tsohon Sarki Muhammad Shitu kakansu Lamiɗo, sun ta so suma sai Sarauta ta dawo gidan su. Tuni su Lamiɗo suka haɗe kai suna fatan har nan da shekaru tamanin sune za su cigaba da mulkan kasar Daura. Burin Mai martaba kenan yau kuma burin shi ya cika. Received at 08:05Reactions: ❤ 4, 👏 1 [6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Amir ne kawai ke Delhi yana can yana karatun likita, Amira ma tana Base Abuja, Hafsart ce ta yi aure tana auren yaron Sarkin Adamawa. Sarakuna sun sha kawo ma Mai martaba Lamiɗo tayin auren ƴa'yan su amma ya ce baya buƙata shi mijin mata biyu ne a duniya Bilkisu da Ummu Salma, sun ishe shi rayuwar duniya har abada. Har bangaren Sarki mai murabus an sha zuwa shi kuma sai ya ce ai Lamiɗo Sarki ne ba wanda zai yi masa dole in yana ra'ayi zai yi in kuma ba ya ra'ayi babu matsawa, har a cikin ƴaƴan dangi ma ana ta kawo masa ya ce ba ya buƙata ba zai iya kara ma kansa wata hayaniyar ba, kuma daman ba shi da ra'ayin haka sannan har gobe kawo masa ake yi ba su haƙura ba. * Sai bayan isha'i ta gama girkin, ta so har cake ta yi to ba lokaci ne. Duk shekara tana haɗa masa walima daman wannan shekaran ma dalilin dawowarta daga makaranta kenan. Girki ta yi masa kala uku, tuwon shinkafa da miyar agushi, ferfesun kayan ciki pepe chikcken sai ferfesun dankalin turawa mai hanta, ta yi zoɓo da kunun aya sai lemun kankana da fruit salat, a ko wani shekara in za su yi irin wannan walimar can gidan shi na cikin gari suke zuwa gidan da Mai martaba ya mallaka masa gidan da Mami da tsohon Sarki suka yi rayuwa gidan da aka haifi Lamiɗo. Bayan ta gama girkin, ta bar ma Harira ta haɗa mata su a cikin kwanduna ta tura ma King ɗinta saƙon dawowarta tun ɗazu so take sai ta isa can gidan sai ta kira shi tunda yana fada. Yaran suna bangarenta bayan sun ci abinci suka koma suna kallo a falo, ta shiga ɗaki ta yi wanka bayan ta idar da salla ta zauna ta tsantsara kwalliya, wani leshi ta saka mai kyau da tsada, daman ta yi ƙunshinta ja tun daga katsina ta yi saloon an yi mata gyaran gashi. Ga shi tana tashin ƙashim turarre daman ba ta wasa da kayan gyaran Surayya akai akai tana siyan kayanta yanzu haka ma suna can a fridge a katsina ta siya ta fara amfani da shi. Alkeybba ta ɗora a saman kwalliyarta bayan ta ba da umarin duk an saka abincin a mota. Yaran ta bar su tare da Harira da su Asabe ba su san ma fitan ta ba ta ƙofar baya ta fita daga bangarenta. Mijin Harira ne amintattacen direbanta shi ya tuƙa ta zuwa gidan akwai hadimai dake kula da gidan tana zuwa suna ta faɗuwa suna gaisheta ta amsa suka kwashi kayan zuwa cikin gida. Gidan ba shi da girma sai fili cike da shukokoki akwai gidan gona, in da ake kiwon tsintsaye kifi da kaji. Akwai iska a gidan saboda lambu, dole ne ma kowa ya so rayuwa a wannan gidan Gidan yana gyare ko'ina yana tashin ƙamshi, tunda Hadimai na gyarawa. Sai da ta natsu sannan ta tura ma Mai martaba sakon in da zai same ta a cikin ɗin bedroom akwai gado mai rumfa, lulluɓe da labulayen alfarma komai na ɗakin kalan shi fari ne. Ta shimfiɗa darduma katuwa ta jera duka abincin sannan ta kame a saman kujera ta dora kafa ɗaya kan daya ta riga ta gama gwajin ta yau rawa za ta yi ma Lamiɗo sosai sun saba in dai suna cikin nishaɗi zai ce ta yi masa rawa, anan Daura ko in ya je dubata a katsina ta na yi masa kuma yana jin daɗi. Shin kina yi ma mijin ki rawa ko kema kin bar shi yana kallon matan tiktok ne? Ba su fiki iyawa ba, kema ki gwada domin nuna masa babu abin da matar aure ba za ta iya yi domin mijinta ba Ga dai Sarkin Daura shima a fada yake Sarki amma a cikin gida shi ba Sarki ba ne sai yadda aka yi da shi, zama yake shima ana juya masa yana jin daɗi. Karfe tara da mintina kaɗan ta ji diran mota ta san shi ne, shima amintattacen Direban shi ne ya kawo shi, kuma sun tafi anan za su kwana sai da asuba za su koma Masarauta. Saboda Mai martaba in bai je sallar asuba ba za a yi mgana. Ya shigo tana zaune tana kaɗa kafa, tana sanye da alkeybbanta ba ta cire ba, bakinta na shekin jan bakin da ta sanya. Lamiɗo na tsaye yana kallonta cikin naɗin rawanin shi da alkeybba shima a jikinsa daga fada yake sun yi tattauna da hakimai ne kan wani fili dake cikin gari ya ga saƙon Ummu Salma shi ya sa ko cikin gida bai shiga ba, a irin wannan rana tana zame musu rana mafi muhimmanci a duk shekara a rayuwarsu. Received at 08:05Reactions: ❤ 11, 👏 1 [6/26, 10:34 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Yana kallonta da mirmishi, zuciyarsa na buɗewa a kanta. Kamar yau ne kamar yau ne Mami ta ba shi umarnin auren ta, yana kallon ta yana kallonta a wancan shekarun na baya. Da a ce ya ƙi karɓan auren Ummu Salma da ya kasance cikin Fargar jaji har abada na rayuwarsa. Ya buɗe mata hannuwansa ta taso cikin mirmishi ta faɗa jikinsa ya rufe ta da alkeybban jikinsa da hannayensa. "Happy Birthday my King." "Happy birthday Sarauniyata in advance." Ya faɗa cikin kaushin muryansa amma tana fita cikin amonta na cikakkun maza masu kwarjini da haiba. Ta ƙamkame shi tana faɗin Allah ya raya mini kai ya yi maka albarka. "Amin Sarauniyata, Ke ma Allah ya raya mini ke." Ya gama faɗa yana shinshina saman kanta da yake jin ƙamshin gashinta yana wani lumshe idanuwana sun daɗe a haka kafin su saki juna. A tsaye nan ya shanye jan bakin nan tas har yana masa shaida a baki. "Ka shafi jan baki." Ta faɗa tana shafa bakinsa lokaci ɗaya tana dariya. Sai ya tura mata bakin yana faɗin" Shanye mini." Ba gardama ta mayar da bakinta ta goge masa da harshenta nan ma kugunta ya riƙe suna sake sumbatar juna. Dakyar suka yakice juna, ta riƙo shi zuwa gefen gado sannan ta taya shi ya sauke kayan jikinsa suna da da kaya a gidan amma ta taho musu da wasu kayan itama kwabewa ta yi suka shiga wankan tare yana goga mata sabulu tana goga masa haka suka yi wankan bayan sun fito, suka shirya kansu a tare. Shi saukaƙun kaya ya saka riga da wando, ita kuma Ummu Salma ta saka wata arniyar rigar barci ja, mai yar ciki da ta waje. Ba ta saki ta wajen ba ta ɗaure igiyar ta cikinta. Suka zauna suka ciyar da junan su, tana kan cinyarsa hannayensa na dafe da cikinta yana shafawa. Suna hira cikin shauƙi da soyayya in suna tare mantawa suke yi da komai na duniya sai kan su kawai. Sai ta sha zoɓo daga bakinta sai ta haɗe bakin su tana shayar da shi. Bayan sun gama cin abinci ba su kwanta ba, Ummu Salma ta kwashe kayan ta kai kitchen sannan ta dawo, har Mai martaba ya kishingiɗa a saman kujeran dake bedroom ɗin yana hutawa. Tana dawowa ta kashe wutar ɗakin ta kunna dumlight. Ta ɗau wayarta ta kunna waƙar burin zuciya na Hamisu Breaker. Sai ta cire rigar barcin ta sama ta bar ta ciki, iyakarta rabin cinyarta, shara shara ce ba abin da ba a gani a jikinta ga cikin ta nan da ya fito Kirjinta suna tashi suna sauka daga rigar barcin jikinta. Daga nesa ta fara masa taku cikin yanga tana nuna sa tana bin baitin waƙar "Burin zuciya haɗa da idaniya. " "Su samu ganin ka  ya mai saka ni dariya. Muradin duniya." "Son ka har ya yi luɓiya. Ka san duka zuciyata na bar maka naka ne." Ta fara masa rawa cikin birgewa tana jijjiga jikinta cikin ƙwarewa da wani salon jan hankalin shi zuwa gare ta. Yana kishigiɗe ne dole ya mike yana mai kafe ta da idanuwana. Ta tako ta zo gaban shi ta miƙa masa Hannu ya kama ta mikar da shi tsaye daidai baitin. "Kai na ke so." "Ka ga dafin so." "Tunda ka kalla me kake jira." "So nake yi ka zamo miji, a garan ka yi agaji" "Ka ga ba wani jan aji ka sani na san in dai akan son ka ban ji ban gani.." Tana yi tana riƙe hannunsa tana juyi shi kuma sai ya riƙe kugunta kamar suna rawan india, yana juyi da ita a ɗakin yana mai kallon fuskarta cikin shauƙinta. Ba zai iya jurewa ba, shi ya sa ya haɗe kugunsu waje ɗaya ya fara sumbatarta hannayensa na kara kaina a sassan jikinta. Itama tuni ta tallabe shi, wakar na tashi har ta kare wata ta shiga ba su sani ba. Su daga nan kan gado suka koma suna ba ma junan su natsuwa. Ummu Salma ta ja ragamar komai, ta kusa saka Sarki ihu, da sambatu ta tafiyar da shi cikin shauƙi da muradi irin shaukin da ke nenan zautar da mutum bai sani ba. Bayan sun yi wanka sun tsarkake jikinsu sannan Ummu Salma ta kashe wayarta suna can suna ba ma juna natsuwa a gefe ɗaya waƙoƙi masu sanya soyayya da natsuwa na shiga in wannan ta ƙare wannan ta ɗauka. Suna kwance a saman gado suma rumgume da juna babu kaya a jikinsu. Shafa ƙirjinsa take yi tana jin daɗi na ratsa zuciyarta da gangan jikinta. "Hamma." "Uhm" Iska ke kaɗawa ta waje har cikin ɗakin tunda window ɗin ɗakin na wajen gadon ne. Received at 08:05 12 people reacted with ❤ [6/26, 10:34 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby "Me ya sa ba ka taɓa canza mini suna ba? Ummu Salama sai wani lokaci ka kake kira na Sarauniya." Ya yi shuru kawai yana jin ta, bai yi magana ba. "Ka na ji? Ta faɗa tana ɗagowa , idanuwansa suna lumshe ne amma tasan ba barci yake ji ba. "Ummu Salama." Ya kirata sai ta amsa tana dariya. "Ba ki son sunan ne? "A'a ko a wayarka fa haka ka saka mini sai da na goge na saka maka My princess." "Ba ka gani ba? "Na gani." Ya amsa mata a sanyaye muryansa ta dishe. "Shi ne ba ka yi magana ba ko kasan ni na canza daman? "Na sani mana." "Ya aka yi ka sani? Ta faɗa tana ma jikinsa rumfa da jikinta. Cikinta da kirjinta suna sauka a saman jikinsa sai ya ɗan matsa ya mayar da ita gefe, ta yi filo da hannunsa na hagu, ya juya suna masu kallon juna ta ɗan hasken dumgliht ɗin dake ɗakin. "Na san ke ce." "Ba ka yi tunanin ko wa ba sai ni? Mirmishi ya yi mai sauti. "Na san halin duka mata na, na san abin da za ki yi na san wanda Bilkisu za ta yi ina gani na san ke ce." Ta fara dariya shi kuma yana kallonta. "Sunan ya yi maka? "Suna ba shi ne mai muhimmanci ba." Ya kama hannunta guda daya ya dafa a saitin zuciyarsa. "Abin da ke cikin zuciya shi ne mai muhimmanci, wani abin ba buƙatar baki ya bayyana shi ki bar zuciya kawai ta yi aikinta." "Na fi son na kira ki da sunan ki na fi jin shauƙin sunan a zuciyata." "Suna ba shi da tasiri, matukar zuciya ba ta ba da muhimmanci ba.' "Anan wajen kike da muhimmanci anan wajen ke ta musamman ce kina gani a aikace ba kya buƙatar wani suna domin tabbatarwa." Ta yi shuru suna kallon juna tana jin bugun zuciyarsa. "Zuciyata tana bugawa duk lokacin da tuna da ke, tana ɗaukan ɗumi da sukuni in tana tare dake." Da sauri ta sumbaci bakin shi tana masa mirmishi. "Ba bukatar bayyanawa Hamma." Ya lumshe idanuwana ya buɗe a kanta. "Ina son ka Hamma, ina son ka mijina duniyata." Ya sake lumshe idanuwana ya kuma buɗe a kana. "Ka rike mini hannu lokacin da na ke da rauni, ka nuna mini so lokacin da nake ganin ba zan samu wata dama, ka ba ni bayanka na hau lokacin da nake neman matallafi, ka ba ni kafaɗan ka na jingina lokacin da na gaji, ka ba ni jikinka na raɓu da shi lokacin da nake neman nasara." Ta gama faɗa hawayen da suka cika ƙwarmin idanuwanta suka samu daman zubowa, ya saka tattausan hannayensa yana share mata hawaye. "Hamma." "Allah ya jiƙan Baffa, daman ya ce zan yi alfahari da kai watarana." "Thank you for loving and caring for me. Na gode Ubangiji ya bar mu tare." Ta fashe masa da kuka, ya jawo ta jikinsa yana lallashinta. "Wannan gidan, ba gidan kuka ba ne, nan ne Mami ta yi rayuwarta ta reni cikina kuma ta haife ni." "Ummu Salama." "Kina cikin tarihin mahaɗin rayuwata. Kin canza ni, kin karramani kin nuna mini wata duniyar da ban sani ba.." "Ummu Salama." "I love you." "Sosaiii..." Ta ƙamkame shi, tana kukan farinciki. Ya yi mata raɗa a kunnenta. "Ki taƙale ni, ina sooo..." "Allah ina so." Ya gama faɗa yana yi mata rumfa ta gefe saboda cikin jikinta, sumbatar juna suke yi cikin muradi mai girma. "Daɗi." "Me? "Ummu Salama" "Kina da daɗi." Ta yi dariya tana shafa fuskarsa, tana kuma share masa gumin da ya tara a goshinsa kamar babu A.C "Kamar.." "Mazan... ƙwaila." Ya faɗ a rarrabe, rufe masa baki ta yi da bakin ta ya fara sambatu cikin fitan hayyaci bai ma san yana yi ba. Ta ƙamkame shi, tana shafa bayan shi zuwa kugun shi,. "Ummu Salama." "Ummu Salama.." "Ummu Salamaaaa." Sau uku ya kira sunanta tana amsawa. "Ina son ki..." Muryansa ta fita cikin wani amo, amon da ya sa Ummu Salma ta ji kamar kayan cikinta na motsi, jikinta na yin wani yam, kamar tana yawo a sararrin samaniya. A duniya nan ta tabbata ba wata macen da take matsayinta a yanzu dai, ta gama samun komai a duniya a lahiran ma tana fatan Lamiɗo ya zamo mijinta a Aljanna in sha Allahu. Nima ina son ku masu karatu "Alhamdulillah." Nan na kawo ƙarshen labarin littafin FARGAR JAJI, godiya ga Allah salati da rahama su tabbata ga shugaban halitta Annabi Muhammad Salallahu Alaihi wasallam tare da shi da iyalansa da sahabansa gabaɗaya. Received at 08:05Reactions: ❤ 12, 👏 1 [6/26, 10:34 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby Na fara ɗora alƙalamina akan wannan labarin a ranar wata asabar 05 ga watan June 2025 shekaran da ta gabata. Sannan na fara posting ɗin shi a 17 ga watan April 2026, na kuma ƙarƙare shi a ranar Jumma'a 12 ga watan june. Da rubutun da editing da posting gabaɗaya ya ɗauke ni shekara kenan. Alhamdulillah bayan duk walwalu da faɗuwa ga shi Fargar Jaji ya zo muku cike da yakini da fata, kuma na ji daɗi da fatana bai yanke ba, na gode sosai da yadda da kuka karɓi wahalata na shekara ɗaya. Allah ya saka da alheri Ubangiji ya haɗamu a Aljanna gabaɗaya Amin. Ina miƙa godiyata zuwa gare ku tsanin da na taka har na isa garin Jimeta Suwaiba Gulma, tare dake My Sweatheart Maneesha ina matuƙar godiya da gudummuwarku, da bakin ku na yi rubutu a garin Adamawan Yola kamar na taɓa zuwa da kaina. Na gode sosai Allah ya saka da alheri. Fatan alheri ga Yayana MLS JAMILU UMAR Federal medical center Taraba, ya yi ƙokarin ba ni dukkan wasu bayannan da na buƙata a wannan labarin Allah ya biya ka da alherinsa Amin. Fatan alheri a gare ku my TelegramFamily, da kwarin gwiwarku na kamallah wannan labarin, na gode da jimarin bibiyana nagode da ƙauna, a yi haƙuri ɗan adam tara yake bai kai goma ba wataƙila na kuskure ta wani fanni, ina fatan za ku yi mini afuwa. Na gode sosai Allah ya saka muku da alheri Allah ya haɗamu a aljannah Amin. *Janafty* 26/12/2025. ... *12/June/2026.* Received at 08:05Reactions: ❤ 23, 👍 4, 👏 1 Downloaded from NovelsHQ.com This Novel is downloaded from https://NovelsHQ.com to download more hausa novels visits our site at www.Novels.Com For feedback and support Facebook : https://facebook.com/NovelsHQ.com Twitter : https://twitter.com/NovelsHQ.com Telegram : https://t.me/NovelsHQ.com