Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels  💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : Princess Meerah 🎀💋 THE WRITER'S OF TAURIN ZUCIYA EXILED PRINCE HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) TAURIN ZUCIYA ( RETURN ) * Wannan gajeran labari ne , labarin soyayya tsakanin Fari da Baki , Soyayya tsakanin abun da ba za su taba kasancewa a waje guda ba , ga cin amana , na jinin ka ma ba zai kyale ka ba , wannan labarin da ga karkashin zuciya ta ya fito , duk wanda ya sauya min ko da kalma daya cikin abun da na rubuta ban yahe mishi ba , sannan duk wata kalma da na fada ba dai'dai ba ko na yi kuskure to ku yahe min , Duk kuma wanda ya fadi wata mumunar kalma a kai na , to shi da Allah * GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION 👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {PAGE 1 & 2 💦🔥 } ▪UNITED STATE OF AMERICA ( U.S.A ) ▪NEW YORK STATE ▪GREENWICH STREET Wata kyakyawar Budurwa ce ke tafe a saman titin waya a kunne Ta na sanye cikin Wando palazzo Black colour da Shirt Navy blue , ta yi Rowling wani veil navy blue a kan ta , ta na rataye da wata yar bag Black ita ma , hannun ta na dama ta rike da wani cup na coffee dayan kuma ta na rike da wayar ta a kunne Budurwa kyakyawar gaske ce , amma kallo daya za ka yi mata ka san ba jinin turawa ba ce , a shekaru za ta kai 22 years Skin din ta fara ce kal amma ba kamar na turawa ba , ta na da dara daren idanun ma su daukar hankali , farare kal kwayar cikin su kuma Black ce , Black din ya ciza sosai har wani kyali ya ke yi eyelashes din ta dogaye da su kuma baki kirin , ta na da dogon hanci kamar pencil , design din lips din ta gwanin burgewa , pink colour da su ga bala'in laushi , sun sha lips balm , ta saka wasu medical glasses a idanun ta Ta na da shape kamar na coca cola , hips da breast din ta cike su ke bam dai'dai shekarun ta , ta hadu iya haduwa kamar ita ta yi kan ta Masha Allah Wani cool murmushi ta saki cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa ta ce " Momy , ki bari har na samu hutu , in sha Allah ina nan zuwa , kin San ba yadda za a yi auren Yasmine ba na nan " ta fada da haoussa , hakan na nufin ita bahaoushiya ce ? Ta dan dauki lokaci kafin ta saki yar karamar dariya ta ce " Momy , aure fa lokaci ne , in sha Allah in na wa lokacin ya zo zan yi , amma gaskiya ban da ra'ayin aure a yanzu " ta kai karshen dai'dai ta sha wata kwana Kawai sai jin ta ta yi ta bugi mutun har sai da cup din hannun ta ya kubce mata ya fadi kassa cikin sa'a bai bata mata kaya ba Da sauri ta dago kai ta ja da baya Wasu samari ne tsaye a gaban ta , sam ba su yi kama da mutanan kirki ba Kare musu kallo da kyau ta yi kafin ta ce " momy ina kiran ki " da ga haka ta sauko da wayar ta , ta kashe kiran sannan ta ce da samarin nan " How can i help you ? " Wanda ta yi karo da shi ne ya mika ma ta hannu cikin tsawa ya ce " Give me your phone " " why ? " ta fada mishi cikin ko in kula Wata yar karamar dariya ya yi kafin ya fido gun a bayan shi ya saita kan ta , da sauri ya na fadin " give your phone , give your phone " Dayan saurayin ne ya katse shi da cewa " and her bag " Wata yar kara budurwar nan ta yi kafin ta mika mishi wayar ta da sauri hannun ta har kerma ya ke yi ta fido jakar ta , ta mika musu ta na fadin " please let me , ga su nan na ba ku " Su na karba su ka yi kwanar da ta fito da gudu Su na barin wajen ta daura hannayan ta saman kai nan take idanun ta su ka kawo ruwa ta na fadin " wayooo Allah na shiga uku na , ina zan sa kai na yau ni Esra , duk keys din apartments di na su na a ciki ya zan yi da raina ni " Sai sambatun ta ta ke yi ita kadai dan hanyar babu kowa saman ta Kamar da ga sama ta jiyo Muryar mutun a bayan ta ya na fadin " Miss wannan na ki ne ? " A dubu dari ta juyo ta na kare mishi kallo Saurayin ya hadu ba laifi gaskiya , a shekaru zai kai 33 years Fari kal da shi kamar ka taba jini ya fito , ya na da sexy eyes farare kal kamar madara , kwayar cikin su kuma light Green ce , da dan karamin bakin shi , lips din shi kuma duk pink color ne , gashin kansa Darck black curly ne amma bai tara suma sosai ba , ta zubo mishi gaban goshi kadan ta rufe idanun shi , ya na saka wani earring a kunnen shi na dama ga wani saje baki kirin konce a fuskar shi , ya na da tsayi ga kuma murdaden jiki sosai allamun ya na yawwan motsa jiki Ya na sanye cikin wando Crazy jeans blue color , sai yar singlet fara wadanan karfafun damtsen na shi duk a waje su ke , kafafun shi su na cikin wasu sneakers ma su mugun kyau farare , A hankali ta sauko da kallon ta kan abun hannun shi , ta na ganin bag din ta da phone din ta ta saki wani kyawatencen murmushi Da sauri ta kai hannu ta kwace su , ta na fadin " eh , nawa ne , na gode sosai , na dauka na rasa su kennan har abada " Hannayan shi ya saka cikin aljihun shi kafin ya ce " sai a bani ladan aiki na ko , ko 100$ ce za ta ishe ni " ya kai karshen ya na fudo hannun shi ya kai bayan keyar shi Kare mishi kallo ta yi da ga sama har kassa kafin ta ja wani dan siririn tsaki ta juya ta ci gaba da tafiyar ta , ta rataya bag din ta Ta na shirin mayar da phone din ta cikin bag din ta , ta ji an zabce mata ita A dubu dari ta dago kai ta na fadin " waye ne ? " , nan ta ga saurayin nan ne , ya na zabtar wayar ta ya yi gaba ya yi wata yar kwana da ke gaban su kadan Da sauri bi bayan shi ta na fadin " kai malam ban waya ta " dai'dai lokacin da ta yi kwanar ita ma Cak ta tsaya ba shiri , ashe ba kwana ba ce , irin dan kwangon nan ne da turawa ke yi dan ajiye trash bin Cen ta hango shi zaune saman wasu kwali , ya na rike da wayar ta ya na jujuya ta , hannu gudan kuma ya na rike da taba ya na busawa ( YANZU DA YIN KWANAR SHI HAR YA SAMU DAMAR KUNNA TABA ? 🤔🤔🤔 ) A hankali ta karaso gaban shi ta na sa hannu ta janyo veil din ta , ta toshe hancin ta dan wajen ya na mugun wari , ga kuma na tabar da ya kunna , amma shi sam bai damu ba ya saba da wannan warin Gaban shi ta karaso ta mika mishi hannun ta , ta na fadin " give my phone please , wlh na yi late a wajen aiki " Ba tare da ya dago kai ya kale ta ba ya ce " cewa na yi ki ba ni ladan aiki na amma ki ka ki , kin san idan na sayar da wayar nan za ta fi 100$ ? " Da sauri ta ce mishi " eh na sani , ka yi hakuri ban rike da kudi amma gobe zan kawo maka please ban waya ta " A hankali ya kai tabar shi baki ya ja kafin ya sauke ta ya busa hayakin a saitin ta Da sauri ta kauda kai gefe ta na dan lumshe idanun ta " What's your name ? " ya fada ya na meda tabar shi baki Dan tsaki ta ja kafin ta ce " don Allah ka ban waya ta " " who is Allah ? Ni ban san shi , dan haka in ki na son wayar ki , ki amsa min tambayoyi na " ya fada ya na kunna wayar ta ya kali screen din , hoton ta ne ke sama , ta na sanye cikin wata gown pink colour , zaune cikin wani garden ta saki murmushi gwanin burgewa Da sauri ta ce mishi " Esra Yahaya " A hankali ya gyada kan shi kafin ya ce " okay , my name is Kim , are you married ? " " no " ta fada a takaice " okay zan ba ki wayar ki , but promise me za ki kawo min Chocolate gobe , ko ba ki zo ba ni zan tarda ki gida " ya fada ya na mika mata wayar ta Maganar shi ba karamin mamaki ya ba ta ba , ba ta san lokacin da ta ce mishi " me kuma za ka yi da chocolate kai da ke shan taba , na dauka kudin sayan tabar ka ke so " Slowly ya sunkuyar da kan shi ya ce " Kudin sayan tabar ba za su yi min wuya ba , kawai chocolate din na ke so " Kare mishi kallo da kyau ta yi kafin ta kai hannu ta karbi wayar ta juya ta fara takawa za ta bar wajen Ya na jin ta fara takawa ya dago kai slowly ya na kallon yadda ta ke tafiya cike da nitsuwa Sai da ta kusa fita wajen ta jiyo Muryar shi ya na fadin " Ki daina biyowa hanyar nan , akwai gangster sosai a wannan lokacin , ba ki ga babu kowa saman hanyar ba " Dan karamin murmushi ta yi mishi kafin ta ce " na gode , gobe zan kawo maka chocolate din ka " da ga haka ta juya ta fice wajen Har ta bar wajen bai janye kallon shi ba , sai da ya dauki lokaci kafin , ya sa hannu cikin gashin shi duk ya cakuda , ya sa hannu cikin aljihu ya ciro kwalin tabar shi ya ciro guda ya kunna ya ci gaba da aikin shi Esra kuma ta na barin wajen ta fara tafiya da sauri sauri ba ta dauki 6 minutes ta iso bakin wani tanpasheshen building duk na zallar glass ▪ONE WORLD TRADE CENTER ya na da ga cikin jerin manyan building goma na cikin New York , ya na dauke da hawa dari da hudu , wannan ginin sai da ya dauki wajen shekara 7 a na yin shi , sannan an kashe mishi makudan kudade wanda za su kai 3,9 milliards na dollars Da sauri ta shiga cikin building din ta na duba watch din hannun ta Kawai sai jin ta ta yi ta bugi kirjin mutun , har sai da bag din ta , har takardun da mutuman ke rike da su ka zube Ba tare da ta dago kai ba ta ga wanene gaban ta ba ta duka da sauri ta dauki jakar ta , ta rataya sannan ta fara tatare takardun shi ta na fadin " yi hakuri don Allah , wlh sauri na ke tun Sir Kevin bai gan ni ba , na....... " kut maganar ta yanke sakamakon dago kan ta da ta yi ta ga wanene ke gaban ta Tsaye ya ke cak cike da kwarjini ya na sanye cikin Suit farare kal gwanin burgewa Cikeken bature ne fari kal da shi kamar ka taba jini na hito , ya na da dan tsayi amma ba sosai ba , da murdaden jiki , ya na da kananan idanu farare kal kwayar cikin su kuma black ce , ya na da dogon hanci , da jajayen lips shape din su kamar heart , bai wani tara gashin kai ba shi ba baki ba , shi ba brown ba , sumar shi a konce ta ke lufff gwanin burgewa , gayen ya hadu sosai amma fuskar nan ta shi a daure ta ke tamau kamar hadari Murya na kerma Esra ta shiga fadin " So.......sorry sir " ta kai karshen ta na mika mishi takardun shi da ta su ka fadi Hannun ya sa ya karbi takardun shi ya na tsare ta da wadanan kananan idanun shi Ya na karba ta yi sauri ta raba ta geffen shi ta wuce Ba ta yi wani taku biyu ya kira sunan ta cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa da izza , cak ta tsaya ta lumshe idanun ta na karanto duk wata adu'ar tsari da ta fado mata a zuciya A hankali ya daga kafa ya dawo gaban ta ya tsaya ya na ci gaba da kallon ta Sai da ya dauki wajen good ten minutes a haka kafin ya bude bakin shi a hankali ya ce " open your eyes " Dum ta ji gaban ta ya fadi , zuciyar ta ta shiga duka uku uku , a hankali ta fara bude idanun ta , sai cikin na shi , da sauri ta sunkuyar da kan ta , dan ba za ta iya jure kallon cikin idanun shi ba A hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce mata " me ya tseda ki , yanzu karo na hudu ki na zuwa a makare cikin satin nan , apartments din ki fa just behind ya ke , ba zai wuce ki dauki 15 minutes cikin kin jima kafin ki zo , amma kullum sai kin yi late " Wasu yawu ta hadiye kafin ta bude baki lips din ta har kerma su ke yi wajen cewa " I'm so sorry , wlh wasu........ " A hankali ya katse ta ta hanyar daga mata hannu ya daura da cewa " ki bi a hankali Miss Esra , in har ki na son aikin ki , dole ki kiyaye nan gaba ba zan iya daukar wannan late ba " " nagode Sir in sha Allah zan kiyaye " ta fada cikin girmamawa Sai da ya tsaya kallon ta da ga sama har kassa sannan ya raba ta geffen ta ya fice abun shi Ya na fitowa sai saman wata dankareriar mota baka kirin har wani kyali ta ke yi kamar mirror , kudin motar nan kadai ya isa mutun ya yi lafiyayen gida har ma ya ja jari Da sauri driver din shi ya bude mishi kofar baya , ya na shiga ya meda kofar ya rufe ya koma wajen shi da sauri ya tada motar su ka bar wajen da gudu Da kallo Esra ta raka shi sai da ya bar wajen sannan ta sauke nanauyar ajiyar zuciya har sai da ta dan lumshe idanun ta ta na dafe saitin zuciyar ta ta na fadin " Allah na gode maka " da ga haka ta daga kafa ta nufi lift kai tsaye hawa na 97 ta nufa dan ta na cikin manya manyan ma su aiki a wajen Sai da ta dauki wajen 2 minutes kafin lift din ya bude ta fito Wajen cike da ya ke da mutane sai zirga zirga su ke yi , kowane rike da file a hannun shi sai sauri su ke yi Da sauri ta nufi wani dan madaidaicin office na glass Ta na isa ta daura hannun ta saman finger print nan take door din ta bude kan ta Har ta daga kafa za ta shiga , ta jiyo Muryar wata yan mata a bayan ta ta na kiran sunan ta Slowly ta juya ta na ganin yarinyar ta saki wani cool murmushi sannan ta shiga cikin office din , ta na shiga ita ma yarinyar nan ta shigo Yarinyar cikakiyar baturiya ce a shekaru za ta kai 24 haka , ta na sanye cikin wata gown dai'dai guyiwa navy blue , ba laifi ta hadu Sai da Esra ta nufi desk din ta , ta zauna saman chair sannan ta ce " Hi ! " ajiye bag din ta ta yi saman desk sannan ta juyo ta kali baturiyar nan ta ce " Good morning Cherry " Gyada kan ta Cherry ta yi sannan ta ce " lafiya ki ka yi late haka , ko dai har yanzu ba su gyara Lift din building din ku ba , ya kamata ki sauya apartments gaskiya Esra " Dan karamin murmushi Esra ta yi ta na zama saman chair din ta , ta ce mata " Cherry in na sauya na tafi ina , kar ki manta ba ni daya ba na ke zaune ciki ba , Sun gyara lift din tun shekaran jiya , Wlh tsotsayi ne ya kai bin GREENWICH STREET a tunani zan fi sauri , kawai na hadu da wasu yan iska su ka kwace min Bag di ta da waya ta " " No , har yanzu a na yaayin wannan abun ? To ya a ka yi ki ka karbo su ? " Dan karamin tsaki Esra ta yi kafin ta ce " Wani dan iskan kamar su ya amso min su , shi ma da kyair ya ban wayar cewa ya yi sai na ba shi wani abu , ni kuma babu cash a jiki na " Yar karamar dariya Cherry ta yi sannan ta ce " Esra akwai ki da abun da dariya , wai wani dan iskan kamar su , inda dan iskan ne ba zai medo miki kayan ki ba sai dai ya yi gaba da su , kin san dama raba sata ga barawo........ " Ba ta karasa maganar ta ba wani bature ya turo kofar office din Esra ya shigo ya na sanye cikin Suit Bakake Ya na shigowa ya nufi wata yar sofa da ke fuskantar Desk din Esra Wani cool murmushi ya saki kafin ya ce " Miss Esra yau ma late , hope dai ba ki hadu da wannan mai fuskar shanu ba , dan fa yau a sama ya ke " Yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " ni ko na hadu da shi , har mu ka buge juna , ai shi dama kullum sama ya ke " Wannan karan a tare duka su ka yi dariya sannan baturen ban ya daura da cewa " Amma kin yi sa'a fa , yanzu haka abun da na ji ya sallami ma'aika ta har biyu ba su ji ba , ba su gani ba " Dan zaro idanu Cherry ta yi ta na komawa geffen shi ta zauna ta ce " please da gaske ka ke Arthur ? " Gyada mata kai ya yi ya na fadin " da gaske na ke , yanzu haka ma sun bar building din " " Toooo , lafiya ya sallame su haka kawai " Esra ta fada cike da tsoro cikin zuciyar ta Mikewa tsaye Arthur ya yi , ya dawo bakin kofar office din ya dan soko kai , ya leka ya ga ba kowa sannan ya koma ya rufe kofar , ya rage sautin Muryar shi ya ce " ni ma ban sani ba amma na ji an ce wai , ana fitar da kudi da ga cikin account din companyn , last relieve ma babu one Milliard , kuma ba yanzu ba a ka fara , in dai wannan satar ta ci gaba ina ga Dukan mu sai dai mu nemi wani wajen aikin daban " " Arthur , one milliard fa ka ce ? " Cherry ta fada a hankali ya gyada mata kai ya na fadin " Abun da ya fi Hakan ma , kin san fa PDG din companyn nan sam bai damu da abun da ke faruwa cikin ta ba , karewar zancen , big bro din shi ke kula da gidan nan , da sauran companyn shi " " Wait , ka na Nufin Sir Kevin ba shi ne mamallakin Companyn nan ba " Esra ta fada cike da rudu har da dan zaro idanu 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : Princess Meerah 🎀💋 THE WRITER'S OF TAURIN ZUCIYA EXILED PRINCE HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) TAURIN ZUCIYA ( RETURN ) GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION 👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM PAGE 3 & 4 💦🔥 Har hada baki Arthur da Cherry su ka yi su na ce mata " wai ke dama a tunanin ki shi ne mai wajen ? " a hankali ta gyada musu kai ta na fadin " Ni na zata shi ne mai wajen , saboda shi ke kula da komai tun lokacin da na fara aiki a wajen nan , kuma ban taba jin wani ya ce akwai wanda ke sama da sir Kevin " dan tabe baki Cherry ta yi kafin ta ce " tabb ki na cikin Duhu ko " Arthur ne ya katse ta da cewa " Wannan companyn da ki ke gani , ni da kai na ban taba ganin mai ita ba , Abu guda na sani , sir Kevin big brother din shi ne , Da farko Companyn ta mahaifinsu ce , amma ya kamu da ciwon zuciya a tunanin shi mutuwa zai shi ya sa ya mallakawa yaron shi na biyu duk wata company da ya mallaka , shi kuma ya ba wa Sir Kevin ragamar kula da su baki daya " " me ya sa ba zai kula da kayan shi ba , tunda mahaifin nasu bai mutu ba , ya meda mishi companyn shi in ba zai kula da su ba " " Ni ma haka na gani , yanzu ga shi bai ma san abun da ke faruwa cikin companyn shi ba " Cherry ta fada ta na komawa geffen Arthur ta zauna ta na zama ya ce mata " ba mamaki sir Kevin da kan shi ke satar kudin , ko ni na ji an ce mahaifin mu ya ba wa little brother di na duk abun da ya mallaka , ba zan hakura da sauki ba " hararrar wassa Esra ta yi mishi kafin ta ce " kai dai Arthur , a dinga fadin gaskia , Sir Kevin ta ya zai iya satar kudin dan uwan shi " mikewa tsaye Arthur ya yi ya na fadin " Humm a na ki tunanin ko , amma ai mu na tare da ke , za ki gani " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya fice Office din da kallo su ka raka shi har sai da ya fita sannan ita ma Cherry ta mike ta na fadin " ya ne yau za mu je shan coffee ne ? " " No gaskiya yau ba zan samu dama ba , may be tomorrow " Esra ta fada ta na dan marairaice fuska wani cool murmushi Cherry ta saki kafin ta gyada mata kai a hankali ta sa kafa ita ma ta fice office din , su ka bar Esra ita daya cikin office din su na fita ta fido laptop din ta da ga cikin bag din ta , ta fara aikin ta a haka ta ci gaba da aikin ta ita daya cikin nitsuwa har wajen karfe 6 na yamma sannan ta baro building din a hankali ta ke Tafiyar ta saman Titi , ta na taku cike da nitsuwa ta na kallon gaban ta kamar da ga sama kawai ta ji an kwace mata bag din ta ta baya dum ta ji gaban ta ya fadi , a razane ta juya ta na shirin ta saki kara ta na ganin shi ta rufe bakin ta , ta na dan lumshe idanun ta , ta sake bude su ko sannu bai ce mata ba ya bude bag din ta ya na leko ya ce " where is my chocolate ? " " ka ga malam ka ban jaka ta , ni ba wani chocolate da gare ni " ta fada ta na mika mishi hannun ta allamun ya bata jakar ta a hankali ya juya ya fara takawa ya na rike da bag din ta ta da sauri ta bi bayan shi ta sha gaban shi ta marairaice fuska ta ce " please ka ban jaka ta , mu tafi zan saya ma " tsaya wa ya yi ya na kallon ta na dan lokaci kafin ya ce " Mu tafi yanzu " " shikenan ban jaka ta , sai mu tafi " ba musu ya mika mata jakar ta , da sauri ta sa hannu ta karba ta na sauke ajiyar zuciya sannan ta ce " yanzu idan na saya maka chocolate din shikenan mun rabu ? " a hankali ya gyada mata kai allamun eh wani dogon nunfashi ta ja kafin ta ce " shikenan mu tafi " ta fada ta na fara takawa ta bi ta geffen shi ta wuce a hankali ya juya shi ma ya bi bayan ta a tare su ka yi tafiyar su ba wanda ke ce ma wani ufan har su ka iso cikin wani dan market ya na biye da bayan ta su na shiga ta nufi kai tsaye wajen Fridge , ta bude ta dauko Chocolate har biyar sannan ta rufe ta dawo ta nufi reception ta biya kudin su ka fito market din su na fitowa ta mika mishi chocolate Hudu ta rige gudar kallon chocolate din ya yi kafin ya ce " Dayar fa ? " hararrar shi ta yi ta na fadin " tawa ce , ka karba mana " a hankali ya girgiza mata kai ya na fadin " no , ni wacen na ke so " ya fada ya na nuna dayar da ke cikin hannun ta guda kallon shi ta yi baki sake cikin zuciyar ta ta ce " amma wlh ya raina min hankali " ba ta gama fadar haka ba kawai ta ji ya kwace mata chocolate din a razane ta dawo cikin hayacin ta na shirin yi mishi magana ta ga ya fara takawa ya yi gaba dan karamin tsaki ta ja kafin ta fara takawa ita ma a hankali har ta kamo shi har ya bude Chocolate din ya fara ci cikin konciyar hankali ya ke cin chocolate din nan , har wani lumshe idanu ya ke yi , da allamun ya na son chocolate sosai kawai sai ji ta yi ta tsargu da kallon shi , ba karamin burge ta ya yi ba har sai da ta saki wani cool murmushi ba ta sani ba ta na a haka kawai ta jiyo Muryar shi ya na fadin " daina kallo na haka kar ki cinye ni " da sauri ta kauda kan ta gefe ta na fadin " ni ba kai na ke kallo ba " " uhm uhm to me ki ke kallo ? " ya tambaye ta dai'dai ya kai chocolate din shi a baki " ni chocolate di na na ke kallo , wannan na ke so amma ka kwace min ita " ta fada ta na dan turo baki , ita wai ta ba kallo ba a hankali ya tsaya da ya tafiyar shi , cak ta tsaya ita ma kamar ya riko ta slowly ya juyo ya kale ta ya ce " shikenan karbi kayan ki " ya fada ya na mika mata ledar chocolate din dan ya cinye kallon ledar ta yi kafin ta saki wani dan karamin murmushi mai sauti ta ce " amma ka raina min hankali ko ? bayan ka cinye , rike ba na so " ta kai karshen ta na fara takawa da sauri ya ce mata " ji mana yan mata " cak ta tsaya da tafiyar ta , ta juyo a hankali ta na matse gera daga mata gera guda ya yi ya na fadin " please ko za ki kara min wata , ba ta ishe ni ba " ya kai karshen ya na dan marairaice muryar shi yanayin da ya yi mata maganar ba karamin tada mata gashin jikin ta ya yi ba , nan take ta ji zuciyar ta ta fara duka uku uku kawai ta tsare shi da ido , su ka yi ido hudu babu ko kiftawa a hankali ya daga mata gera allamun minene da sauri ta janye idanun ta , ta na girgiza mishi kai kafin ta mike mishi sauran chocolate din hannun ta wani cool murmushi ya saki kafin ya tako a hankali ya tsaya gaban ta , ya kai hannu ya karbi chocolate din ya na fadin " Thanks " da ga haka ya juya ya fara takawa tsaya wa ta yi ta na bin shi da kallo , sam bai yi kama da wadanan bata garin ba , da ga yanayin da ya ke maganar shi ma , cike ta ke da nitsuwa ga kaifin harshe duk yadda a ka yi wannan ba bata gari ba ne akwai dai wata a kassa sai da ta dan dauki lokaci ta na kallon shi kafin ta juya ita ma ta fara takawa ta nufi apartments din ta , ba ta dauki five minutes ta iso building din ya na da girma sosai , a killa zai kai hawa 40 , a kowane hawa kuma part 5 a dakwai , duk da Parlour guda , Bedrooms biyu , toilet guda sai kitchen kuma dukkan su design guda gare su kuma piece of furnitures din iri daya ne har colors din ta na shigowa building din kai tsaye lift ta nufa , ta shiga ta Haye Floor na 10 ko da ta fito lift din wani dogon corridor ne da ga dama zuwa hagu , mai dauke da doors har biyar kofar lift din kuma ta na fuskantar kofar wani daki , an rubuta ROOM 52 da manyan harufa mai launin White hannun damar ta ta yi ta nufi Door ta Biyu an Rubuta ROOM 51 a sama ita ma ta na isa ta kai hannu cikin bag din ta ta ciro key , ta saka kofar ta bude sannan ta zame key din ta tura kofar ta shiga ta na sallama , sai da ta shiga sannan ta juya ta rufe kofar sannan ta juya ta karaso cikin parlourn ba laifi wajen a gyare ya ke masha Allah , duk furnitures din white and green color ne , da wata yar karamar Tv plasma din ta parlourn gaskia ba shi da laifi ya na da dan girma komai na ciki White and green colors ne a geffen dama akwai wata yar karamar table allamun dining table ce mai chair biyu bayan ta kuma kitchen ce , har da fridge geffen Hagu kuma wani corridor ne na hango , akwai wasu door din bedroom biyu a ciki su na fuskantar juna sai guda a tsakiyar su wadda ina kyautata zaton toilet ce a hankali ta karaso cikin parlourn ta na sallama , sannan ta ajiye Bag din ta saman table din tsakiya ta nufi corridor ta shiga bedroom din da ke saman damar ta , ta tura kofar ta shiga ta na sallama bedroom din ya na da dan girma saman damar ta wani Desk ne da chair kamar dan office , da wasu takardu a sama gaban shi kadan akwai wani dressing mirror , dauke da lotion perfume da sauran su a geffen hagu kuma Wani closet ne White color na kayan ta me door hudu a cen cikin dakin geffen hagu akwai bed din ta game da bango , shi ma white color har bedsheet din shi white color ce , da bedside drawer din ta , ta daura wata bedside lamp da alarm clock ta na shigowa ta warware veil din kan ta , ta yi baya da kan ta , ta girgiza shi a hankali nan take jelar gashin kan ta , ta zubo mata , ta na da gashi gaskia , smooth da shi brown color kamar na turawa ajiye veil din ta ta yi saman bed din ta , sannan ta nufi closet din kayan ta , ta bude na karshe underwear ne cike a wajen , da pant da bra har da wasu towel white , pink , green colors hannu ta kai ta dauki Towel Fari sannan ta juya ta fice dakin kofar toilet ta nufa ta bude ta shiga sannan ta turo kofar ta rufe After some minutes ta fito Daure da Towel a kirjin ta , kai tsaye bedroom din ta ta nufa ta shiga ta na shiga ta nufi closet din ta , ta bude door ta uku , ta fido Wasu kayan barcin ta wando da T-shirt pink color ta saka kayan ta , sannan ta dauki Hijabin ta pink color shi ma , ta dauki Daddumar ta ta nufi dan carpet din da ke gaban gadon ta ta shinfida sannan ta saka hijabin ta , ta tada sallar ta bayan ta Kamala ta tashi ta fida Hijabin ta , ta nufi Dressing mirror din ta , ta dauki lotion din ta ta fara shafawa , sannan ta feshe jikin ta da perfume sannan ta nufi kofar fita dakin ta fito parlour ta na fitowa ta nufi doguwar Sofa ta zauna sannan ta janyo table din tsakiya gaban ta , ta dauki Jakar ta , ta fara fido abun da ke ciki daya bayan daya ta na a haka wata kyakyawar budurwa ta bude kofar gidan ta shigo ta na Sallama Budurwar kyakyawa ce gaskia , a shekaru za ta kai 22 to 23 years , Skin din ta chocolate ce mai mugun kyau , da ga kan ta ka ga jinin Hausa fulani ta na sanye da Wando palazzo black color da t-shirt Orange , da wani Veil shi ma orange ta yi Rowling din shi a kai , ta na rataye da wata yar karamar bag a bayan ta , ta karaso cikin parlourn ta na kokarin cire bag din dago kai Esra ta yi ta na kallon ta , ta amsa mata sallamar ta sannan ta daura da cewa " Safna , yau kuma sai yanzu ki ka dawo " ajiye bag din ta Safna ta yi saman sofa geffen Esra sannan ta zauna ta na fadin " Kin dai gani wlh duk na gaji jiki na har ciwo ya ke min " yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta juya kan ta , ta ci gaba da fido abun da ke cikin Bag din ta mikewa tsaye Safna ta yi ta dauki bag din ta , ta na fadin " na shiga wanka " ta fada ta na fara takawa ta nufi corridor da to kawai Esra ta amsa mata ba tare da ta dago kai ba ta na tsaka da fido kayan bag din ta , ta fido wani dan karamin abu baki kamar USB stick haka dago USB din ta yi ta kawo ta saitin fuskar ta , ta na bin ta da kallo " wannan kuma da ga ina ? " ta fada dan ita a sanin ta ba ta da USB key sai da ta dan dauki lokaci ta na kallon USB din nan kafin ta janye ta da ga gaban face din ta , ta dauki bag din ta ta fara meda duk kayan da fido ban da wayar ta , da laptop sai da ta Kamala meda wa sannan ta dauko laptop din ta , ta daura saman cinyoyin ta , ta kunna ta , sannan ta saka USB key din a ciki ta fara latsawa ta dauki wajen good Five minutes a haka kafin ta mike tsaye a dubu dari ta na rike da laptop din ta , ta na zaro idanu ta ce " oh my God , ya Allah me na ke shirin gani haka " ni dai ban san me ta ke kallo ba , wasu rubutu ga su nan irin statistics haka , ita kadai ta san abun da ta ke gani slowly ta koma ta zauna ta rufe laptop din ta ta zame USB din ta meda cikin bag din ta , sannan ta dauke ta , ta koma bedroom din ta , ta ajiye saman table din office din ta , sannan ta juya ta fito dai'dai lokacin da Safna ta fito da ga cikin toilet ita ma ta na sanye da bathrobe white color ko sannu ba ta ce mata ta sa kai ta fito corridor din ta koma parlour Safna kuma ta shiga bedroom din ta jim kadan ta fito Sanye da kayan barcin ta ita ma amma nata navy blue ne kuma wandon ta iya cinya ne kawai ta na fitowa ta nufi parlour ita ma ta zauna geffen Esra ta ce mata " wai ba ki gyara komai ba yunwa na ke ji " dan karamin murmushi Esra ta yi kafin ta ce " kin gan ni nan , ko kitchen din ma ban shiga ba , bare na yi tunanin gyara wani abu , ni na zata za ki biyo mata da take away da ga Restaurant din ku " dan karamin tsaki Safna ta yi kafin ta kauda kan ta , ta ce " wane restaurant , yau bayan wuya ba abun da na sha , dan jaraba ni su ka bari serving yau , Wlh ba zan yarda ba , ni fa a matsayin Chef na nemi aiki cikin restaurant din , amma wai su ka ba ni receptionist" yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " To tashi mu koma Nigeria mana " dan zaro idanu Safna ta yi ta na fadin " wa ? ni ? ai ni da Nigeria sai dai Ziyara , Ziyarar ma , sai da babban dalili " 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITTEN BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION 👇👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM PAGE 5 & 6 💦🔥 Dariya sosai Esra ta yi , wai Ziyarar ma sai da babban dalili kenan sai in parents din ta sun mutu ko kuwa ? hararrar wassa Safna ta yi mata ta na fadin " matsala ta da ke kenan ba a iya hira da ke " tsagaita dariyar ta Esra ta yi kafin ta ce " Oya shikenan na daina " " ko ke fa , amma ba ki tambaye ni abun da ya faru restaurant ba yau " daga mata gera guda Esra ta yi ta na fadin " Oya fadi ina jin ki ! " gyara zaman ta Safna ta yi , ta juyo su na fuskantar juna ta ce " Shugaba ku na ONE WORLD TRADE CENTER , ya je sun yi wani meeting da wasu mutane a restaurant din mu , ni da kaina na yi serving din su , sai wajen karfe 4 na yamma su ka tashi " dan tabe baki Esra ta yi ta na fadin " no really , kenan Saurin da na ga ya na yi da safe cen za shi ? " daga kafadun ta Safna ta yi ta na cewa " na san ba , amma kin san abun da ya fi ba ni mamaki ? " girgiza mata kai Esra ta yi allamun a'a " wani hadaden saurayi ne na gani a tare da su , Esra ina fada miki , duk zaman da na yi a New York , ban taba gani Saurayi hadade irin shi " katse Esra ta yi ta na tsaki sannan ta ce " Shi ne abun mamakin ? " ta kai karshen ta na kauda kai cike da zumudi Safna ta ce mata " Ki tsaya ki saurare ni mana " juyo da kan ta Esra ta yi kafin ta ce " to shikenan ina jin ki " " yawwa ! ni fa ba haduwar saurayin nan na ke fada miki ba , idan ki ka gan shi ba zai wuce 30 years ba , amma duk mutanan da su ka halarci Meeting din da Boss su ke kiran shi , har shi kan shi shugaban ku , a sani na Kevin Brian shi ne Boss din ku , ko kuma akwai na sama da shi ? " " haka na ji su na cewa amma wlh ban sani , Fada min ya kamanin shi su ke ? " yar karamar dariya Safna ta yi kafin ta ce " Gaskia a jiki dai ya hadu ga tsayi ga fafadan kirji kamar mai dambe , sai dai ya na sanye da face mask ban samu na ga fuskar shi ba , idanun shi kadai na gani , ya na da dara daren sexy eyes , Sai dai kwayar cikin su ban sani ba in blue ce ko green dan da ga nesa na gan shi kuma ya sunkuyar da kan shi , amma dai between Blue or green ce gaskia , ni sai da na ji Muryar shi ma na kara tabbatar wa da shi ne boss din su , kar ki so ki ji Muryar shi kamar a na busa sarewa dan dadi , kuma cikin nitsuwa ya ke magana kamar an yi mishi dole , kai gayen nan duniya ne kawai wannan ina ga shi ne Mister US baki daya ma " Dariya sosai Esra ta yi har da lumshe idanun ta , ta na fadin " Ni dai na san akwai Miss US , amma ban taba jin Mister US ba sai yau " hararrar ta da kyau Safna ta yi kafin ta ce " ke wlh dan ba ki gan shi ba ne , amma Allah ya sa su dawo restaurant din sai na dauki pics din shi dan ki gani " tsagaita dariyar ta Esra ta yi ta na fadin " hum na ji dai malama , yanzu tashi gyara mana wani abu mu Ci yunwa na ke ji " hararrar wassa Safna ta yi mata kafin ta ce " kin yi sa'a ni ma ina jin yunwa ba dan haka ba sai dai ki sha ruwa " ta kai karshen dai'dai lokacin da ta shiga kitchen din yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta dauki wayar ta saman table ta na daukar wayar ba abun da ya fado mata a rai sai Kim , kawai sai ta saki wani cool murmushi cikin zuciyar ta ta ce " ko ba komai ya Hadu gaskiya " ta na tuno yadda ta gan shi ya na shan chocolate din shi cikin konciyar hankali , duk yadda a ka yi wannan akwai wani boyayen Al'amari a tare da shi ta yi nisa cikin duniyar tunanin ta , ta jiyo Muryar Safna ta na cewa " ke malama tun dazu a na kiran ki a waya ba ki jine ? " a dan razane ta dawo cikin hayacin ta dago wayar ta ta na kallon screen din wani cool murmushi ta saki kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na fadin " Amarsu ta ango , lfy a ka kira ni warhaka ? " wata yar karamar dariya na fara jiyowa kafin na jiyo Muryar wata macen da ga jin ta ta budurwa Ce ta na fadin " Za ki fara ko ? ni yanzu fada min yaushe za ki zo kin san fa jiya a ka kawo lefe amma ko kira na ba ki yi ba " a kai karshen cikin shagwaba yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " Sorry sister na , ya ki ke ya su momy duk da ma mun yi waya da ita da safe " " Fine ! kowa ya na nan lafya , yanzu fada min yaushe za ki zo ne ? " " kawai dan ki tambaye ni yaushe zan zo , auren da ko rana ba saka ba " Esra ta fada ta na mikewa tsaye ta fara takawa ta nufi corridor a daya bangaran kuma a ka ce mata " Hum wa ya fada miki , ai jiya a ka saka rana , Farko ga watan March " " wow ki ce nan da two months " ta fada dai'dai lokacin da ta ke shiga cikin dakin ta " eh , nan da kwana 52 bai kai two months ba " yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " to sannu malama har kin kirga ko kwana nawa ne " " eh mana dole na kirga kwana nawa su ka yi mana saura ni da Habibi kafin mu zama Mr & Mrs Raouf " ta kai karshen ta na yar karamar dariya dan karamin tsaki Esra ta yi kafin ta ce " ke ki ka san wani Habibi , kin ga sai an jima ni Sallat zan yi , sai da Safe " ta na gama fadar haka ta sauko wayar ta katse kiran ta nufi closet din ta , ta bude ta dauki wani Hijab White color ta saka , har kassa sannan ta dauki Sallayar ta shinfida , ta Haye ta tada sallar ta cikin konciyar hankali ___________________________________________ WASHE GARI ▪GREENWICH STREET a hankali ta ke tafiya saman titin , ta na sanye wando palazzo pink color da Shirt White color , ta yi Rowling veil din ta a kai shi ma White color , ta na rike da bag din ta , ta na tafe ta na juyawa kar a je yau ma akwai baratin nan da su ka tare ta a haka har ta karaso wannan kwangon da ta ga Kim ya shiga a jiya ta na shiga ta hango shi cen zaune saman wasu case , ya hada bayan shi da bango ya lumshe idanun shi , ya na sanye cikin wando Crazy jeans black color , da wata T-shirt white color gaskia wannan bai min kama da dan shaye² ba , dubi yadda ya ke a wanke tsab tsab Masha Allah akwai dai wata a kassa a hankali ta karaso gaban shi ta na Sallama duk da ta san abu me wuya ne a ce zai amsa mata ko motsi ma bai yi ba , amma ya san da ita dan tun lokacin da ta yo kwanar ya jiyo qamshin turaren ta Murya cen kassan makoshi ta ce mishi " Kim ? " ta fada ta na dan lekon Face din shi ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce mata " What are you doing here ? " ya fada cikin sanyin murya da sauri ta yi baya kadan , ta janyo veil din ta , ta toshe hancin ta " Kim , wine ka sha amma ko ? " ta fada dan ta jiyo warin ta cikin breath din shi gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba " Why ? " ta fada mishi cikin sanyin murya wani dan karamin murmushi Geffen fuska ya yi kafin ya ce mata " ke ni fa dan iska ne , shan wine karamin abu ne waje na , wai me ya kawo ki nan ma please let me " cikin Sigar rarrashi ta ce mishi " please ka daina , wlh za ta iya maka illa ba kadan ba " irin wannan murmushin Takaici ya yi kafin ya ce " please ki daina nuna kin damu da ni , ba ki san ni ba , ba ki san ko wanene ni ba , ki na ganin wajen da na ke zaune , kullum cikin tsangwamar mutane na ke , su na zagi na , Kalle ki , ki kale ni rayuwar mu ba daya ba ce , dan haka ki daina kula ni please ba na bukatar kindness din ki , ki tafi ki kyale ni " " tabass ban san ka ba , ba ka san ni ba , amma ai ka taimake ni duk da ba ka san ni ba , ka ga ko dan hakan zan iya nuna damuwa gare ka , ni gaskiya ce na fada maka , shan wine babu kyau , ta na iya janyo maka cancer , sannan cikin adinin mu , shan wine Haramun ne " ta fada dan ita sam ta manta da shi ba musulmi ba ne murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " Ke ki ka san wani addini , Ni ba ni da wani Aboki duniyar nan kamar Wine , duk lokacin da na sha ta na kan ji damuwa ta ta fi , na kan ji na daina kewar ta , please and please let me ki na damu na " tsaya wa ta yi ta na kallon shi ba tare da ta ce komai ba tabass akwai wani boyayen al'amari tare da shi , amma minene wannan abun ? ita ta ma rasa dalilin ya sa ta damu da shi lokaci guda haka , musaman dan ta gan shi yau ta fito tun karfe 7 ga shi kuma ya ce ta kyale shi , ko bude idanu bai yi ba bare ya kale ta a haka dai jiki a mace ta juya ta fara takawa ta bar wajen ya na jin ta fara takawa ya bude idanun Slowly sun yi jazir ko , lalle ya na cikin maye wani dishi dishi ma ya ke gani , amma a haka ya raka ta da kallo har sai da ta bar wajen , sannan ya meda idanun shi ya lumshe a hankali ta ke Tafiyar ta duk ta yi nisa duniyar tunanin ta ba ta fi ten minutes ba ta iso hall din ONE WORLD TRADE CENTER sai a lokacin ta dawo cikin hayacin ta , ta na shirin shiga ko ta ga Kevin ya fito da ga cikin building din , ya na sanye da Suit sky blue ma su mugun kyau , ya na sanye da bakaken glass a idanun shi , ya na takawa cike da kwarjini a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ci gaba da takawar ta kai a sunkuye yau duk jikin ta a mace ya ke har ta kai bakin kofar ta jiyo Muryar Kevin ya na kiran ta dum ta ji Gaban ta ya fadi har sai da ta karanto kalmar shahada a haka ta juya ta nufe shi ya na tsaye bakin motar shi , driver ya bude mishi kofar kai a sunkuye ta ce mishi " Good morning Sir " a hankali ya sa hannu ya sauke glass din shi ya zuba mata idanu babu ko kiftawa nan take ta ji duk ta tsargu , slowly ta dago da kan ta , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi da sauri ta meda kan ta ta sunkuyar ta na sunkuyar da shi , shi kuma ya meda glass din shi ya ce mata " lafiya yau ki ka zo da wuri ? " ba tare da ta dago kai ba ta ce " nothing Sir " gyada kan shi ya yi a hankali kafin ya ce " no wonder , Hope za a ci gaba da zuwa a cikin lokaci " ya na gama fadar haka ya juya ya shiga cikin motar shi ya na shiga ita ma ta juya ta nufi building din ta shiga dai'dai lokacin da motar su ta bar wajen da mugun gudu kai tsaye lift ta shiga ta nufi floor na 97 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : Meerah 🎀💋 THE WRITER'S OF TAURIN ZUCIYA EXILED PRINCE HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) TAURIN ZUCIYA ( RETURN ) GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION 👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM P A G E 7 & 8 💦 🔥 kofar Lift na budewa ta daga kafa ta fara takawa ta nufi office din ta , ta na isa ta kai hannu saman finger print , nan take kofar ta yi wata yar kara ta bude kan ta , a hankali Esra ta shiga ta na sallama cen kassan makoshi , office din ta ta nufa , ta ajiye bah din ta a saman desk din , sannan ta zagaya ta zauna saman chair din ta ta na zama ko Cherry ta turo kofar ta shigo office din da murmushi a fuskar ta ta ce " Hi Esra , How are you ? " murmushi kadan ita ma Esra ta yi mata kafin ta ce " Fine Cherry " karasowa cikin office din Cherry ta yi ta nufi daya da ga cikin chair din da ke gaban desk din ta janyo ta zauna ta na kallon Esra ta ce " ya a ka yi ki ka riga ni zuwa yau ? " murmushi mai dan sauti Esra ta yi kafin ta ce " ai dama kullum sai na riga ki zuwa " wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na shirin magana Arthur ya shigo office din ya na fadin " wai da gaske Esra ce a karfe 8 dai'dai ? " hararrar wassa Esra ta yi mishi ta na fadin " wai kowa cikin companyn nan ido ya saka min " karasowa ya yi cikin office din ya ja chair din da ke geffen ta Cherry ya zauna ya na fadin " Ni ban sani ba , amma ni da Cherry dai mun sa miki ido " ya na gama fadar haka Cherry ta mika mishi hannu ta na fadin " ka gani ai , karfe 8 saura mintina biyu , ban kudi na " cikin rudu Esra ta ce mata " Wane kudi kuma ? " " oh bet mu ka yi , na ce mata yau ma sai kin late , ita kuma ta ce ba za ki yi ba " Fadin Arthur ya na fidda 100 Dollar ya ajiye saman hannun Cherry wani dan karamin murmushi Esra ta yi ta na kallon su ta ce " yanzu tsakani da Allah bet ku ke yi a kai na ? " " may be ba mu kadai ba ne , ko kuwa Arthur ? " Cherry ta fada ta na dawo da kallon ta kan Arthur wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " shikenan yanzu Esra minene ki ke son gwada mana , yi sauri kar Sir Kevin ya dawo ya tardo mu nan " gyada mishi kai ta yi kafin ta kai hannu ta janyo jakar ta , ta bude ta ciro laptop din ta , da wannan USB key din , bude laptop din ta ta yi , ta kunna ta , sannan ta saka wannan USB key din ta shiga latsawa na dan lokaci kafin ta juyawa su Arthur laptop din a hankali Arthur ya kai hannu ya janyo laptop din gaban su shi da Cherry su na kallon screen din can kuma sai Cherry ta daura hannun saman bakin ta , ta na zaro idanu ta ce " Oh My God , Esra ina ki ka samo wannan abun ? " " yadda ku ka gan ta haka na gan ta ni ma , abun ya yi matukar ban mamaki " Fadin Esra ta na gama rufe bakin ta Arthur ya ce " Esra , ba fa karamin abu ba ne a nan " ya fada ya na latsa laptop din wata ajiyar zuciya Esra ta fada kafin ta ce " ni kai na na yi mamakin ina na gamo da wannan abun wlh " katse ta Cherry ta yi da cewa " Duk wasu kudi da a ke fitarwa da ga account din company , duk relieve din shekarar nan su na a ciki , Idan har da gaske ne hakan na nufi abun da a ka sata cikin companyn nan sun kai wajan one Hundred Milliards of American dollars kuma duk da sunnan Sir Kevin " ta kai karshen ta na dawo da kallon ta kan Arthur " kenan Sir Kevin shi ke satar kudin companyn nan ? " Arthur ta fada ya na dago kai ya kali Esra kada mishi kafadu ta yi allamun ita ma ba ta sani ba da sauri Cherry ta ce " Tabass shi ne , a na satar irin wadanan makudan kudaden kuma ya yi shiru bai sa an fara investigation a kai ba , ku ma kun san da wata a kassa " gyada mata kai Arthur ya yi ya na cewa " ni ma abun nan ya tsaya min , ya san satar da a ke yi kuma bai sa an fara investigation a gano waye ke satar ba , shi ya ke aikata satar shi , shi ya sa ya ja baki ya yi shiru , sai dai ya yi ta sallamar ma'aikatan da ba su ji ba , ba su gani ba " ya kai karshen ya na dan tsaki " yanzu Esra ya ki ke so mu yi , dan gaskiya ba zan iya yin shiru ba , Idan ya ci gaba mu ma za mu rasa hanyar cin abincin mu , duk gidan mu fa da aikin ga nawa su ka dogara , idan ya kore ni akwai matsala fa ! " fadin Cherry cikin nuna damuwa Dan jinkirtawa Esra ta yi kafin ta ce " ni ma abun da ya sa na kawo muku ky gani kenan , saboda abun da ha ke ba dai'dai ba ne , Arthur ka ce ai companyn ba tashi ba ce ? " ta fada ta na kallon Arthur gyada mata kai ya yi kafin ya ce " eh ba tashi ba , ta little brother din shi ce " " Fine , shi ya kamata mu kai wa wannan abun ya gani " cikin nitsuwa Arthur ya katse ta da cewa " ki bar ma wannan tunanin , it's not sure ya yarda da mu , kuma wannan ba zai isa ba , dole mu samo File din in har ta cikin laptop ne zai iya cewa karya mu ke yi wa dan uwan shi " cikin rudu Cherry ta ce " wai wanene mai companyn nan , ni fa shekara uku yanzu ina aiki a ciki , ba dan jiya ka ce min ba sir Kevin ne ba PDG da ba zan taba sani ba " wata yar karamar ajiyar zuciya Arthur ya sauke , Kafin ya jingina bayan shi a jikin chair din ya ce " Ayden Brian , shi ne PDG din wannan company , asalin wannan companyn ta mahaifiyar su ce , ya na da shekara 20 ta rasu , duk wani abu da ta mallaka ta saka shi a sunnan Ayden Brian har da companyn nan , a lokacin ya na cikin kuruciyar shi ne ya sa mahaifin su yanke shawarar ba wa Kevin companyn dan ya kula da su , dan Ayden ya samu damar kamala karatun shi , bayan ya Kamala karatun shi ne ya shiga harkar restoration , yanzu haka maganar da na ke miki ya na da restaurant a ko ina cikin New York , Washington , New jersey da canada , ya fi meda hankali a kan Restoration din , da a ce ya meda hankali a kan Companyn nan , da zai gano irin satar da dan uwan shi ke yi mishi , ni dai ko so guda ban taba ganin shi cikin companyn da sunnan ya zo aiki , shi ya sa kowa ke ganin cewa Kevin shi ne PDG " ya kai karshen ya na jan nunfashi " kenan Restaurant din , da Safna ke aiki a ciki nashi ne ? " Esra ta tambayi kan ta cikin zuciyar ta ta na a haka kawai ta ji Muryar Cherry ta na fadin " Yanzu ya za mu yi mu samu file din , ya kuma za mu yi mu samo Ayden Brian yadda za mu gwada mishi tun kafin lokaci ya kure mana " " File din na san ba zai wuce cikin Office din Kevin ba , maganar Ayden kuma gaskiya abu me wuya ne samo shi " Arthur ya fada ya na gama rufe bakin shi ya jiyo Muryar Esra ta na cewa " ni zan Samo muku Ayden , ku yi kokarin samo mana File din nan t ........ " ba ta kai karshen maganar ta ba Arthur ta katse ta da cewa " ke malama shiga office din Sir Kevin ba karamin abu ba ne , A floor na 101 ya ke , kuma Security system din shi ya fi na kowane office , musaman scanner din na kwayar idon shi ce ba na hannun ba , sannan akwai wani password wanda Kevin ne kadai ya san shi , Idan ka yi kokarin saka password din da ba shi ba har sai uku , nan take machine din will send an electric shock before you even move, you will be electrocuted to death, on top of that, when Kevin closes his office with his magnetic card, there is a laser beam system which is triggered, the only way to deactivate it is with this magnetic card , so forget even the idea it's dead " " kun gani ko , dan ba shi da gaskiya ne ya sa wannan uban security , da a ce ya na da gaskiya password din ma kadai zai isa " Cherry ta fada cike da bacin rai a hankali Esra ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " yanzu babu wata hanya da za a shiga office din nashi ? " da sauri Cherry ta ce " System of climatisation " cikin rudu Arthur da Esra su ka maimaita abun da ta ce da sauri Cherry ta mike ta nufi bayan desk din Esra , ta na nuna mata wani air conditionner ta ce musu " duk yadda a ka yi akwai ac a office din shi , why ba za mu yi anfani da hakan ba wajen shiga office din nashi ? " " ki na da hankali kuwa ? dubi girman building din nan , kafin ma mu samo na office din shi zafi ya kashe mu , ko kuma mu bace " Fadin Arthur cikin nitsuwa Esra ta ce musu " ku na ji ko , ku bari idan mun sauka mu tafi apartments di na , ko kuma mu tafi shan coffee a cen mu yi maganar mu cikin konciyar hankali " a hankali Cherry ta dawo wajen Chair din ta ta zauna ta na fadin " okay hakan ma zai fi , kun san akwai camera cikin office may be maganar nan da mu ka yi ma sun jiyo mu " a tare Arthur da Esra su ke hada baki su na cewa " da gaske ki ke ? " su ka fada su na zaro idanu da ga gani sun tsorata wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na fadin " na so kun ga kawunan ku , wai da gaske ki ke ? , matsorata kawai " ta kai karshen ta na sakin wata dariyar a tare Arthur da Esra su ka ja tsaki su na cewa " Allah ya shirya ki wlh " cikin dariyar ta ta , ta ke fadin " da gaske na ke akwai cameras , sai dai ban sani ba in akwai cikin office din mu ba " mikewa tsaye Arthur ya yi ya na fadin " ni na tafi Abu na tun da haka ne " wata yar karamar dariya Esra ta yi ta na fadin " kenan da gaske ta ba ka tsoro ? " " kin san an ce hanyar lafiya a bi ta da shekara , gwara na tafi kamar yadda na shigo , sai mun hadu an jima " ya na gama fadar haka ya kafa ya fice ya na fita Cherry ta kalli Esra ta ce " yau ba ki hadu da dan iskan ki ba ? " ta kai karshen ta na daga mata gera tsuke fuska Esra ta yi ta na fadin " kin ga malama tashi fice min da ga nan " wata yar karamar dariya Cherry ta yi ta na kokarin tashi ta ce " da ga tambaya ? , ni ma na tafi tun da haka ne ". " ai dama ban kira ki ba " Esra ta fada ta na kai kallon ta kan laptop din ta " okay , see you later " Cherry ta fada ta na sa kafa ta fice office din 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : Meerah 🎀💋 THE WRITER'S OF TAURIN ZUCIYA EXILED PRINCE HASKE BIYU ( YAR JARIDA ) TAURIN ZUCIYA ( RETURN ) GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION 👇👇👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 9 & 10 💦 🔥} a haka Esra ta ci gaba da aikin ta ita kadai cikin Office din , sai da ta share wajen good one hour a haka kafin ta ja wani dan karamin tsaki ta kai hannu cikin bag din ta ta fido wayar ta , ta saka karatun kur'ani ta aiki ta na saurare _________________________________ ▪BROOKLYN wata kyawatencen balcony ne Fari kal , ya sha tiles farare kal ma su mugun kyau da haske ga wata katuwar Swimming pool , ruwan cikin ta sky blue ne saboda tiles din da ke cikin pool din blue ne sai ruwan su ka dauki launin tiles din pool din zagaye ta ke da wasu umbrella irin na bakin beach haka kassan kowace akwai wasu chair guda biyu dogaye kamar na icce , da ga tsakiya su akwai wata yar karamar table ta glass saman kowace akwai Towel farare guda biyu ajiye bayan wadanan chair din dan nesa kadan akwai wani kyawatencen parlour wall din da ke fuskantar pool din duk da glass ne an rufe shi da wasu curtain farare kal parlourn ya kawatu da duk kayan more rayuwa , ilahirin abun da ke cikin parlourn Milk color amma bari mu koma cikin labarin mu dan tukunna ba mu isa parlourn ba duk balconyn zagaye ya ke da glass ka na iya ganin duk yanayin garin wani kyakyawan Saurayi ne zaune saman daya da ga chair din bakin pool saurayin kyakyawa ne , a shekaru zai kai 32-34 years , fari ne kal cikaken bature gaba da baya , ya na da wani kontancen gashi color din shi baki kirin ne amma harshen su duk blue ne , ya konta min a baya gwanin burgewa sai wasu da su ka zubo mishi gaban goshi ya na da kananan idanu farare kal kwayar cikin su kuma Ash ce , ya na da dogon hanci da dan karamin baki lips din shi kuma pink color ne ya na da wani piercing a kunnen shi da na dama ya zaune saman chair din ya mike kafafun shi da ga shi sai short , a hannun shi na dama akwai wani Tattoo kamar flowers haka ya na rike da wani magazine ya na karantawa cikin konciyar hankali ya na a haka wani server ya shigo wajen ya na sanye da wasu Suit bakake hannun shi rike da tray dauke da glass biyu ya juice da wani dan plate na fruits kai tsaye wajen wannan saurayin ya nufa ya kai hannu ya dauki glasses din nan ya ajiye saman table din geffen shi da plate din fruits din sannan ya mike ya koma dayan geffen saurayin ya ce " sir , ku na bukatar wani abu ? " a hankali Saurayin nan ya girgiza mishi kai ya na murmushi ya ce "No , za ka iya tafiya na gode " gyada mishi kai kawai server din nan ya yi kafin ya juya ya bar wajen wani dan karamin tsaki saurayin nan ya yi kafin ya ce " wai kai malam ba za ka fito ba , ka yi wajen two minutes a ciki fa " ya fada da turanci ya na gama fadar haka wani saurayin ya fito da ga cikin pool din ya juyawa saurayin da ke zaune baya , Babu riga a jikin shi , gashin kan shi kawai a ke iya gani ya zubo mishi har baya keya ya konta mishi luf amma light green ne , amma da ga gani ba karamin namiji ba ne dan damtsen shi a murde ya ke kamar dan dambe , a hankali na jiyo Muryar shi ya na fadin " lafiya ka fiddo ni ? " cike da nitsuwa ga murya ta shi a sanyaye kamar an busa sarewa " Ayden wai yaushe za ka daina harkar restaurant ka kama companyn ka , ka fi kowa sanin satar da Kevin ke yi maka amma ka yi shiru " ko sannu Ayden bai ce mishi ba ya koma cikin ruwan wani dogon nunfashi saurayin nan ya ja ya na cewa " oh ni Adrian , ba da kai na ke magana ba ? " Ayden ya na jin shi amma ya share ya ci gaba da yawon shi cikin ruwan wani dan karamin tsaki Adrian ya ja ya na fadin " shikenan amma kar ka ce ban fada maka ba " ya na gama fadar haka ya kai hannu ya dauki glass din juice ya kai baki ya surba Kafin ya mayar ya ajiye sai da ya yi wajen two minutes a haka kafin ya sake fitowa da ga cikin ruwan , yanzu ma ya juyawa Adrian baya a hankali ya kai hannu ya yi baya da gashin kan shi da ya jike cikin nitsuwa ya ce " Guy , don't worry , na kusa gamawa da Maganar Kevin , kawai ina son na gama da Business din restaurant din nan ne , da kai na zan koma Companyn , yanzu ka yi kawai abun da na saka ka " sai da Adrian ya dan jinkirta kafin ya ce " na shirya ground plan din companyn , sign din ka kawai na ke jira " " okay " ya fada a takaice kafin ya yi kassa ya koma cikin ruwan wani dan karamin murmushi Adrian ya saki kafin ya ci gaba da karatun shi ▪ESRA 💕 Zaune ta ke cikin parlourn su , ta na sanye da wani dan karamin wando dai'dai cinya , da wata t-shirt white color mai kyau ta mike kafafunta saman sofar , ta daura laptop a sama ta na latsawa cikin konciyar hankali ta na a haka Safna ta turo kofar part din ta shigo ta na sallama , ta na sanye da uniform din restaurant din su amsa mata sallamar ta Esra ta yi ta na fadin " sai yanzu ki ka dawo ? " da murmushi a face din ta Safna ta karaso cikin parlourn ta ajiye bag din ta saman table sannan ta zauna ta na fadin " kin dai gani " " okay , je ki yi wanka , na shirya mana diner " Esra ta fada ba tare da ta kalle ta ba wata yar karamar dariya Safna ta yi har da tapi ta na fadin " iyeeeee , wai Esra da gaske kin shirya mana diner ? lafiya ? ko dai tsintuwa ki ka yi ? " wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " ba abun da na yi kawai dai na dawo ne ina jin yunwa shi ya sa na shirya mana " " okay bari na je na yi wanka " ta fada ta na kokarin tashi da sauri Esra ta tsayar da ita ta na fadin " please , zauna ina son na yi miki wata tambaya " ba musu Safna ta koma ta zauna ta na fadin " wace tambaya kuma ? " a hankali Esra ta rufe laptop din ta sannan ta sauko da kafafun ta kassa ta zauna bakin sofar ta na fadin " dama a kan restaurant din ku ne , na ce kin taba ganin mamallakin wajen ? " a hankali Safna ta girgiza mata kai ta na fadin " no gaskiya ban taba ganin shi ba , but ba restaurant guda ba ne , restaurant din shi su na da yawa gaskiya , wanda na ke aiki ciki karami ne ma sosai , na so ki ga restaurant din shi na Washington , sai ki rantse da glass a ka yi shi , musaman sai manyan ministers da yan kasuwa ke shiga restaurant din , shi ma sai sun yi booking one week before , ba karamin mutum ne ba wlh " cikin nitsuwa Esra ta ce mata " but , ko so guda bai taba zuwa restaurant din ya duba ba ? " girgiza mata kai Safna ta yi ta na fadin " no gaskiya , ko so guda ban taba ganin shi ba , ni ko sunan shi ma ban sani ba wlh , kawai dai in mu na meeting ne manager din mu na maganar shi amma bai taba fadin sunan shi ba " " okay , na gode " Esra ta fada kafin ta bude laptop din ta ta ci gaba da aikin ta ita dai Safna ta tsaya ta kurawa waje guda ido kamar mai tunanin wani abu cen sai ta ce wa Esra " Esra , kin san wani abu ? akwai wani mutum da ke yawan zuwa restaurant din duk Monday , kullum shi ne first client din mu , kuma kullum in ya zo coffee ne kadai ya ke sha ya yi tafiyar shi " a Hankali Esra ta dago kai ta kalle ta ta ce " ki na iya gane shi idan kin gan shi ? may be shi ne mai restaurant din ba ki taba sani ba " " Eh zan iya gane shi , sosai ma , kin ga ko wlh kullum in ya zo da laptop a hannun shi ya na typing , sai wajen karfe 9 sannan ya ke barin restaurant din , watarana su biyu ma su ke zuwa , amma gudan ban taba ganin face din shi ba gaskiya " " okay , yanzu je ki yi wanka mun yi maganar da ga baya " da to kawai Safna ta amsa mata kafin ta tashi ta dauki bag din ta , ta nufi corridor ta shiga bedroom din ta , ta bar Esra nan zaune ita kadai ta na aikin ta ____________________________________ ▪LAGOS ( NIGERIA ) wani kyakyawan matashi ne zaune saman chair , tsakiyar wani kyawatencen garden matashin kyakyawa ne ba laifi , a shekaru ba zai wuce 36 years ba , skin din shi chocolate ce , da ga gan shi ka ga cikaken bahaushe gaba da baya ya na sanye da wasu suit khaki , ma su mugun kyau sun zauna mishi a jiki ya na rike da wayar shi ya na latsawa ya na sakin murmushi ya na a haka wani kyakyawan dattijo ya iso wajen ya na sallama , ya na sanye da wata jallabiya white color mai dogayen hannu , fuskar shi babu yabo babu fallasa , a shekaru zai kai 60 haka , amma da ga ganin yanayin jikin shi ya na samun hutu dan har ya fi saurayin da ke zaune haske , ga shi kuma bai tare kyasumba ba sai ka yi tunanin kamar dan shekara 40 ne a hankali matashin nan ya dago kai ya na amsa mishi sallamar shi kafin ya mike tsaye ya na mika mishi hannu ya na fadin " Barka da fitowa uncle " wani dan karamin murmushi mutumin nan ya yi , ya na mika mishi hannu su ka yi musbaha sannan ya zauna saman dayan chair da ke geffen ta matashin nan sai da ya zauna sannan ya ce " Irfan , sai yau ka tuno da ni ko ? " komawa Irfan ya yi ya zauna ya na dan sunkuyar da kai ya ce " a'a wlh uncle , kun san yanayin aiki ne , ko wannan zuwan na tsaye ne komawa zan yi dan gobe zan koma London " " Masha Allah , Allah ya taimaka , Allah ya kara daukaka " " Ameen ya rabbi , na gode uncle " Irfan ya fada cike da girmamawa wani kyawatencen murmushi mutumin nan ya saki kafin ya ce " ya ka baro mahaifin naka , da momyn ka da sauran yan uwan ka ? da fatan ka baro su lafiya ? " " Alhamdoulilah uncle , su na nan lafya , sun ma ce na gaishe ku idan na zo " gyada kan shi mutumin nan ya yi a hankali ya na fadin " Masha Allah , ba zan tsayar da kai ba , dama ni na yi wa mahaifinka magana ya turo ka , mu yi magana , ina fatan za ka saurare ni da kunnen basira " cikin girmamawa Irfan ya ce " uncle ba sai kun yi min maganar ba , na riga da na san komai dan Daddy ya fada min , kuma ina goyen bayan ku dari bisa dari , in sha Allah ba za mu ba ku kunya ba , zai kara dankon zumuntar da ke tsakanin familyn mu , ni dai ta bangare na ba ni da matsala , kawai fata na Allah ya tabbatar mana da al'heri " Hamdala mutumin nan ya yi ya na fadin " Alhamdoulilah , Alhamdoulilah , ka san ni da mahaifin ka tare mu ka taso , tun muna yara , a tare mu ka yi wassan kassa , a tare mu ka yi karatu , aiki ne kawai ya raba mu , tun muna matasa mu ka yanke wannan shawarar , ina fatan hakan zai zama karin dorewar abotar mu , mu zama family guda ta hanyar ku " wata yar karamar dariya Irfan ya yi kafin ya ce " uncle , ai mu dama family guda ne , kar ka manta a nan na taso , ina tune lokacin da na ke wassa saman cinyoyin ku , in sha Allah za mu cika muku burin ku , albarkar ku kawai mu ke nema da addu'ar ku " " Albarka kullum cikin saka muku ita mu ke yarona " " na gode Uncle , i'm sorry amma tafiya zan yi , akwai inda a ke jira na " wani kyawatencen murmushi Mutumin nan ya saki kafin ya ce " no , kar ka damu , amma ka yi hakuri tukunna ba ta dawo ba , amma zan turawa Daddyn number din ta ya ba ka ko da gaisuwa ce kafin lokacin ya zo " " kar ku damu uncle , na gode sosai " ya kai karshen ya na mikewa tsaye a hankali shi ma mutumin nan ya mike tsaye su ka yi musbaha , da ga nan su ka yi sallama Irfan ya bar wajen , shi kuma ya koma ya zauna ya fiddo wayar shi ya fara latsawa ya yi wajen ten minutes a haka kafin wata kyakyawar mace ta shigo garden din rike da wani tray dauke da wasu glass biyu na juice matar kyakyawar gaske ce , a shekaru za ta kai 45 to 50 years , kallo daya za ka yi mata ka san mahaifiyar Esra ce dan su na kama sosai , kawai Esra za ta gwada mata haske , amma da ga ganin yanayin jikinta ka san ta na samun huta , da kuma kula ta na sanye da wata Abaya red color mai kyau , da wani Hijab fari da kadan ya wuce kirji , fuskar ta dauke da wani cool murmushi , ta na tafiya cike da nitsuwa a haka har ta karaso wajen dattijon nan ta zauna saman chair din da Irfan ya tashi ta ajiye tray din a kassa dan babu table a wajen cikin sanyin murya ta ce wa dattijon nan " Engineer , har Irfan ya tafi ne ? ni da na kawo muku juice " [16/02 à 09:38] 🪷🩷: __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 11 & 12 🕊❤} wata yar karamar dariya Engineer ya yi kafin ya ce " No , ya ce wai ya na da aiki , may be next week ya dawo dan gobe zai koma London " gyada mishi kai ta yi a hankali kafin ta kai hannu ta dauki glass din juice ta mika mishi hannu ya kai ya karba ya na yi mata godiya ba ta ce mishi komai ta kai hannu ta dauki gudan ta fara sha cikin nitsuwa cen sai ta ce mishi " ka na ganin wannan shawarar da ka yanke me bulle wa ce ? " cikin rudu ya ce mata " kamar ya me bullewa ? ban gane ba " " ka fi kowa sanin halin yarinyar ka , idan ka ce za ka matsa mata da maganar ba za ta taba amincewa ba , ni ma ina son ta yi aure but ya kamata mu ba ta damar zabar wanda ta ke so ba mu cilas ta mata ba , a cikin 21st century mu ke , an daina wannan hadin auren da a ke " " ni dama na san ba za ki taba amincewa da wannan maganar ba Aysha , amma in ba haka ba ba za ta taba yarda ta yi aure ba , ki na gani US ta gudu dan kawai kar mu yi mata maganar , amma ina jiran ta dawo auren Yasmina , ba zan bari ta koma ba " wani dogon nunfashi Aysha ta ja kafin ta ce " ka yi dai tunani mai kyau , ba dan ka na son abotar ku da Wadi ta daukaka za ka hukuntar da yarinyar mu , kuma ba na tunanin za ta amince da auren nan , ni dai zan so ka zauna ka kara tunani , rayuwar ta ce baki daya ka ke shirin yin wassa da ita " shiru Engineer ya yi bai ce mata komai ba ya na ci gaba da latsa wayar shi , shi dai a wannan maganar ba gudu ba ja da baya duk abun da a ka yi sai ya yi auren Esra da Irfan dan shi ne babban burin shi a rayu ________________________________________ ▪US ( NEW YORK CITY ) ▪GREENWICH STREET a hankali ta ke tafiya cike da san'da kamar barauniya , ta na sanye da wata gown white color mai mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta Purple a kai , ta na rataye da bag din ta kamar kullum tafiya ta ke ta na waiwaye kar a je akwai gangs din da su ka fito a wannan lokacin cikin sa'a ko ba ta hadu da kowa ba har ta karaso wajen wannan kangon da Kim ke rama ta na shigowa ko ta hango shi cen zaune saman wasu box , ya na sanye da wani short white color da shirt Red color babu takalmi a kafafun shi , ya na rike da taba ya na sha cikin konciyar hankali a hankali ta karaso wajen ta na yi mishi sallama duk da ta san ba zai iya amsa mata ba ko sannu bai ce mata ba ya ci gaba da shan tabar shi a sanyaye ta ce mishi " Hi , Good morning " " Hi ! " ya fada a takaice ya na kai tabar a baki ya kara sha wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " Kim , tun da safe ka na shan taba ? ka yi breakfast ko ? " a hankali ta saki tabar ya sa kafa ya murje ta , ko zafin wutar bai ji ba , Esra kuwa har wani dan lumshe idanu ta yi ji ta yi kamar ita ta taka wutar shi kuwa ko ajikin shi kamar ba wuta ba ce ya taka a sanyaye ya ce mata " wai me ki ke yi a nan ? a sani na chocolate ne ya hada mu , kuma kin ba ni shikenan , why za ki takura min ? " wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " ni kai na ban san abun da ya sa na takura maka haka ba " " to ki rabu da ni mana " ya fada ya na kai hannu cikin aljihun shi ya fiddo wata sabuwar tabar da sauri ta kai hannu ta buge tabar ta na fadin " Please , stop , ka san irin illar da abun nan za ta yi maka ba , tun safe ka na sha " " breakfast ne na ke " ya fada ya na sake kai hannu ya fiddo sabuwar tabar yanzu ma hannu ta kai ta buge ta na fadin " mu je na saya maka breakfast to " " da kuma tabar da ki ka buge min " ya fada ya na kai bayan trush ya fiddo wasu sneakers purple ma su kyau , ya saka a kafafun shi kafin ya mike tsaye wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " na yarda , amma bisa sharadi guda " daga mata gera guda ya yi ya na fadin " wane sharedi kuma ? " " can i be your friend ? " ta qarashe maganar ta na mika mishi hannu kallon hannun nata ya yi na dan lokaci kafin ya girgiza mata kai a hankali ya ce " kin taba ganin duhu da Haske sun hadu a waje guda ? ni kamar duhu na ke , ke kuma haske , ba za mu taba kasancewa a tare ba , haka tsarin rayuwa ya ke " " to ka ba ni dama , na mamaye duhun rayuwar ka da haskena , ka ba ni dama na sauya wannan tsarin , kai ma ka na da izinin samun abokin da zai taya ka kuka , wanda zai taya ka dariya , wanda zai sauya maka rayuwa , ka ba ni damar kasancewa wannan abokin " sai da ya kare mata kallo da kyau kafin ya ce mata " shikenan , na yarda mu zama abokai just for two weeks , cikin satin nan biyu in har ki ka yi nassarar sauya min rayuwa , abotar mu za ta kasance ta har abada " wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ce " Eh , na yarda just two weeks , zan sa ka daina shan wine da taba , zan gwada maka colors din rayuwa , idan ban yi nassara ba zan kyale ka har abada " " All right ! " ya fada ya na riko hannunta su ka yi musbaha wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " shikenan , my new friend , mu je na saya maka breakfast , ina da sauran lokaci kafin karfe 8 ta yi ni ma zan samu na yi breakfast " bai ce mata komai ba ya janye hannun shi ya fara takawa zai bar wajen da sauri ta bi bayan shi ta na sakin murmushi su ka bar wajen , sai tafiyar shi ya ke cike da nitsuwa , ya na kallon gaban shi ita dai Esra sai satar kallon shi ta ke ta wutsiyar ido a haka har su ka karaso restaurant din da Safna ke aiki , cike da mamaki ta shiga restaurant din ta na tunanin yadda a ka yi ya san wajen nan amma ba ta ce mishi komai ba , su ka shiga restaurant din , su ka zauna saman chair sai da su ka zauna sannan Esra ta fara bin wajen da kallo , ta ga su kadai ne babu kowa a wajen , sai servers din da ke kula da wajen a ta mike ta na fadin " bara na yi mana order " gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta fara takawa ta nufi reception ta na barin wajen ko Adrian ya shigo restaurant din , ya na sanye da wasu suit bakake , hannayanshi rike da wasu paper da laptop , ya na taku cike da nitsuwa tun da ya shigo Kim ya tsare shi da ido babu ko kiftawa , har ya nufi VIP space ya zauna , ya bude takardun shi ya fara aikin shi a hankali ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ya kauda kan shi , dai'dai lokacin da Esra ta dawo wajen ta zauna saman chair din ta , ta na fadin " hope ka na shan coffee ? " " Coffeeeeee ? , na yi miki kama da me shan coffee ? may be ice tea zan iya sha , amma ban da coffee gaskiya " ya kai karshen ya na kauda kai wata yar karamar dariya ta yi , ta na shirin magana idanun ta su ka sauka saman Adrian da ke zaune bayan Kim , a VIP space nan take yanayin face din ta ya sauya , ta karewa Adrian kallo da kyau , nan take kalaman Safna su ka dawo mata a kai na wani da ke zuwa ko wace safiyar monday restaurant din amma ya a ka yi , yau Friday ba monday ba da sauri ta kai hannu cikin bag din ta ta fiddo wayar ta ta saita Kim akwai ta danna ta yi mishi pic , ga shi ko shi ma ita ya ke kallo pic din sai ya yi kyau gwanin burgewa wani dan karamin tsaki ta yi ta na fadin " Kim , yi gefe guda please " ba musu ya yi gefe kafin ya juya ya ga abun da ta ke son gani a hankali ya juyo ya na kallon ta ya ga Ta na yi wa Adrian Pic cikin rudu ya ce mata " celebrity ne ? why ki ke yi mishi pic ? " ba ta ce mishi komai ba ta sauko wayar ta , ta meda cikin bag din ta , dai'dai lokacin da Server ya iso wajen rike da tray din order da Esra ta yi , ya shirya musu abincin saman table din su sannan ya juya ya bar wajen ya na barin Wajen Kim ya kai hannu ya dauki Fork ya fara cin toast din da a ka shirya da Eggs , ita dai Mug din coffeen kawai ta dauka ta fara sha ta na kallon shi ya na cin abincin cike da nitsuwa , ga shi ko yadda ya ke aiki fork din sai ka rantse da Allah shi ne jikan Sarauniyar UK Elizabeth amma ita duk da idanun ta na saman shi , hankalin ta na kan Adrian , shi ko bai ma san abun da ke faruwa ba , sai aikin shi ya ke cikin konciyar hankali a haka har Kim ya kammala breakfast din , ya sha ruwa ya na yi mata magana amma ba ta ji shi ba a hankali ya kai hannu ya kyasta mata yatsu saitin face din ta a razane ta dawo cikin hayacinta ta kalle shi ta na fadin " What ? me ya faru ? " " za ki yi late wajen aikin ki " ya fada dan ya na son ya dan tsoratar da ita a razane ko ga dauki bag din ta ta mike ta na fadin " wayyooo ni Esra na shiga uku wajen Sir Kevin , na tafi " " wait , bari na raka ki " ya fada ya na mikewa tsaye ina ko sauraron shi ba ta yi ba ta nufi kofar fita , Kim kuma , a hankali ya juya ya kalli Adrian kafin ya juya ya bi bayan Esra su ka bar wajen su na barin wajen ko Safna ta shigo sanye da uniform din ta bangaran Esra kuwa , tafiya ta ke da sauri da sauri , Kim na biye da bayanta ya na kiran sunanta amma ba ta tsaya sai da ta karaso one world trade center sannan ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ta tsaya a hankali ta juyo ta kalli Kim da ke tsaye bayan ta ta ce mishi " na tafi sai mun hadu an jima " gyada mata kai kawai ya yi kafin ta juya ta shiga hall din ta na shiga ko Motar Kevin ta yi parking bakin hall din ya fito sanye da wasu suit purple ma su mugun kyau , ya na sanye da glass a idanun shi kamar an kira sunan shi kawai ya juya ya kalli saitin da Kim ke tsaye nan take su ka yi ido hudu , Kim na ganin hakan ya juya cikin nitsuwa ya bar wajen da kallo Kevin ya raka shi har sai da ya kurewa ganin shi sannan ya juya ya shiga Building din ▪ADRIAN sai da ya yi wajen good 30 minutes bayan fitar su Esra kafin ya jiyo Muryar Ayden ya na fadin " har yanzu ba ka gama ba mu tafi ? " wani dan karamin murmushi Adrian ya saki kafin ya dago kai ya kalli Ayden ya na tsaye gaban table din , ya na sanye da wasu Tracksuit white color ma su mugun kyau , rigar na da hula ya saka wasu sneakers green kalar gashin kan shi , amma ba ka iya ganin face din shi dan ya saka Face mask , da wasu glass kamar medical glass , amma su na dan duhu kadan ba ka iya ganin idanun shi " tun dazu kai na ke jira , ya ? a kawo maka coffee ? " Adrian ya fada girgiza mishi kai Ayden ya yi a hankali ya na fadin " No , idan ka gama tashi mu tafi kawai " " okay mu tafi " ya fada ya na tattare papers dinshi , waje guda sannan ya mikawa Ayden laptop din shi ba musu Ayden ya karbi laptop din , su ka fara takawa a tare su ka bar wajen har su karaso wajen Table din da su Esra su ka zauna kawai sai ya ji ya taka wata paper cak ya tsaya ya na kallon paper din kassan kafar shi a hankali ya sunkuya ya dauki paper din ya na kallon ta kafin ya kalli table din da su Esra su ka zauna , har yanzu ba a gyara table din kawai sai ya yi tunanin ko na wanda ya zauna a wajen ne da sauri ya taro Ayden da ya nufi kofar fita ya na fadin " Ayden wait two minutes please " a hankali Ayden ya juya , ya gyada mishi kai allamun okay wani dan karamin murmushi Adrian ya yi kafin ya nufi reception ya na fadin " excuse me , wanda su ka zauna a cen sun manta wannan , da allamun kuma ya na da mahimanci " wani cool murmushi Safna ta sakin mishi kafin ta ce " okay , na gode , za mu yi kiran su mu mayar musu " " okay " Adrian ta fada , ya na shirin dago paper din na hannun shi su ka kubce da sauri ya sunkuyo ya dauki takardun shi kafin ya mikawa Safna paper din da ya tsinta kafin ya juya ya bi bayan Ayden su ka bar wajen kallon paper din da kyau Safna ta yi , cen kassa a geffen dama ta ga an rubuta ONE WORLD TRADE CENTER , allamun da ga companyn su Esra paper din ha fito a hankali ta juya ta kalli dayar receptionist , cikin sanyin murya ta ce mata " Please duba min cikin register First client din mu na yau , minene sunan shi " ba musu ta duba register din gaban ta kafin ta ce " Esra yahaya , around 7h20 su ka shigo wajen nan " " okay , na gode " Safna ta fada ta na murmushi kafin ta ninke paper din ta saka cikin bag din ta bangaran Adrian kuwa ya na fitowa ya tardo Ayden zaune cikin wata dankareriar mota fara kal ta ji da gani , irin motar da sai wane jikan wane ke iya shigar ta ba banza bare ba , dan tayoyin ta ma sun isa daukar ido kai tsaye wajen driver ya nufa ya shiga dan ya San halin abokin nashi , ba ya son tukin mota , idan kuma ya ce zai yi tukin to tabbas mutuwa zai tunkara dan ba karamin gudu ya ke ba kamar zai tashi sama tada motar Adrian ya yi ya na fadin " ina za mu je ? " cikin nitsuwa Ayden ya ce mishi " One world trade center , ina son na yi wa kevin magana a kan tafiyar da za mu yi Washington dan ganin sabon building din da mu ke shirin budewa a cen , ina son mu ware Space din restaurant , at least ina son mu yi two type na restaurant a ciki " wani dan karamin murmushin geffen fuska Adrian ya yi kafin ya ce " wai me ya sa harkar abinci ke burge ka ? ka na fa cikin Top ten din billionaire din United State of America baki daya " " na sani , kawai restaurant din ne ke burge ni , yau Friday , ina fatan ka sa a shirya abincin da a ke aikawa gidan marayu ? " " yeah , ban manta ba , ai ko wace Friday abu na farko da ka ke fara tambaya shi ne Adrian ka sa a shirya abincin da za a kai gidan Marayu ? Adrian ka sa an shirya kayan da za a kai gidan marayu ? Adrian ka tura kudin da na ce ka tura gidan marayu ? wadanan tambayoyin kamar a bakin ka a ka yi su , but ina jin dadin hakan gaskiya , kar ka damu na yi duk wani abun da ka ce " " okay " Ayden ya fada a takaice da ga haka ba wanda ya sake ce ma wani ufan har su ka karaso wajen wani traffic light a hankali Adrian ya yi parking din motar , ya na jiran a ba su izinin wucewa a hankali ya juyo ya kalli Ayden , ya ga ya lumshe idanunshi ya tafi duniyar tunanin shi wani cool murmushi Adrian ya saki kafin ya juya ya ce " me ka ke ji in ka na tare da ita ? " kai tsaye Ayden ya ce mishi " peace " a takaice da allamun ba ya cikin hayacin shi murmushi mai dan sauti Adrian ya yi kafin ya ce " ka yi a hankali , kar plan din ka ya juye maka " shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba , da allamun ya lula duniyar tunanin shi bai ma san abun da ya ke ba a haka har traffic light din ya nuna green , Adrian ya ja motar su ka bar wajen [17/02 à 14:02] 🪷🩷: 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 13 & 14 🕊❤} a haka har su ka karaso one world trade center , sai da Adrian ya yi parking din motar a parking space sannan ya tabo Ayden cikin sanyin murya ya ce mishi " ta hanyar sirri yanzu ma za ka shiga ko kuwa ? " slowly Ayden ya ware idanunshi , ya sa hannu ya bude kofar motar ya na fadin " no , mu je kawai , two minutes sun isa " ya kai karshen ya na sauka ya nufi hanyar shiga building din cikin nitsuwa Adrian ya kashe motar ya sauko ya bi bayan Ayden ______________________________________ ▪ESRA 👑 da sauri² ta ke tafiya ko kallon gaban ta ba ta yi , idanun ta cike da ruwa , fuskar ta a marairaice kamar za ta yi kuka , kamar za ta yi kuka ta ke fadin " shikenan ta kare min , in ban samo takardar nan ba wlh mutuwa zan yi " ta na gama fadar haka kawai ta ji ta bugi kirjin mutun da karfi , fuuuuu ta yi baya za ta fadi ta na sakin wata yar karamar kara ta datse idanunta da karfi cikin zafin nama Ayden ya kai hannu ya damko kugun ta ya taro ta ba ta kai kassa ba da sauri ta kai hannu ta riko damtsen shi da kyau ta cak ya tsaya ya na kallon face din ta , ta wani lumshe idanunta ta na cije lips din ta na kassa gwanin burgewa lokaci guda ta tafi da imanin sa , dan ba karamar fadawa ya yi ba su na a haka Adrian ya karaso wajen , ya na ganin yanayin da abokin shi ke ciki ya ida isowa da sauri ya na fadin " Ayden , are you okay ? " a dubu dari Esra ta ware idanunta jin an ce Ayden , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi duk da ya na sanye da glass ba ta iya ganin su lokaci guda idanun su su ka sarkafe cikin na juna , shi kuwa Adrian sai pic ya ke musu dan ba karamin kyau su ka yi ba kamar irin masoyan nan na cikin film haka ma duk wanda ke cikin hall din cak ya tsaya ya na kallon su dai ba su ma san abun da ke faruwa a zagaye da su ba wata boyayyar Ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya mike a hankali ya gyara tsayuwar shi ya tallabo ta ta mike tsaye su na mikewa tsaye ko Kebin ya iso wajen ya na fadin " Ayden , me ya faru ? " ya kai karshen ya na tsayawa geffen Ayden ya na ganin Esra ya saki wani dan karamin tsaki ya na fadin " Miss Esra , you again ? what are you doing here ? " lokaci guda Kuka ya kubce mata , ta bude baki har wata yar kerma ta ke ta na shirin magana Ayden ya daga mata hannu allamun ta yi shiru ba musu ta yi shiru ta na sunkuyar da kai hawaye na zubo mata bibiyu cikin sanyin murya Kevin ya ce " Ayden , Adrian , ku tafi office di na ina zuwa , Miss Esra , koma office din ki " tun bai rufe bakin shi ba Esra ta raba ta geffen Ayden ta bar wajen da gudu ta na kuka sai da ta bar wajen sannan Ayden ya juyo ya kalli Kevin ya ce " me ya faru ne ? " wank dan karamin tsaki Kevin ya yi ya na fadin " nothing , kawai ba ta meda hankali kan aikin ta , shi ne na yi mata magana , mu tafi " " no , in mun je gida mun yin maganar , akwai inda zan je yanzu , Adrian mu tafi " ya kai karshen ya na fara takawa ya fice wajen Adrian na biye da bayan shi shi ma Kevin bayan su ya bi ya bar wajen dama fito ya ke son yi bangaran su Ayden kuwa , ya na isa wajen motar su ya shiga wajen driver , tun kafin Adrian ya iso ya tada motar da sauri Adrian ya nufe shi ya na fadin " Ayden please sauko zan yi driving , ban shirya mutuwa ba please " " za ka shiga ko na tafi ? " ya fada cikin wani yanayi kamar ran shi a bace ya ke da sauri Adrian ya zagayo geffen me zaman banza ya shiga ya zauna ya na zama Ayden ya tada motar ya bar wajen a 360 kamar zai tashi sama , ga shi kuma ya danne horn , ya ki saki da sauri motoci ke rabewa gefe su na ba su waje har police din da ke kula da traffic su ka yi kokarin tsayar da shi amma ya ki tsayawa sai da ya yi ten minutes ya na irin wannan tukin kafin ya ja wani mugun burki sai da kan shi ya bugi steering motar , shi ma Adrian kan shi ya bugu a gaban motar slowly su ka dago kawunan su a tare , sannan Adrian ya ce " you're mad ? kashe ni ka ke son yi ko kuwa ? " a sanyaye Ayden ya ce mishi " i'm sorry , idanu na ne su ka rufe " wani dan karamin tsaki Adrian ya ja kafin ya ce " sauko na mayar da mu gida , ni yunwa ma na ke ji " cikin nitsuwa Ayden ya ce mishi " mu fara biyawa gidan marayu , kuma gidan ka za mu tafi ba zan koma ya yanzu ba " " okay , yadda ka ke so haka za a yi " Adrian ya fada ya na bude kofar geffen shi ya sauko Ayden kuma maimakon ya sauko kawai sai ya matsa ya koma wajen mai zaman banza dan ba ya da ra'ayin saukowa ya shiga yin wani zagaye shi dai Adrian ba abun da ya ce ya shiga wajen driver ya tada motar ya reversing din ta , ya kama hanyar gidan marayu cikin abun da bai fi five minutes ba su ka iso kar ku so ku ga yadda yaran ke farin ciki ganin Ayden da Adrian , sun samu kyakyawan tarba , ga yaran turawa ko da mugun shiga rai ji na yi kamar na sace guda na gudu haka zalika Ayden ya ji wani mugun sanyi a ranshi ganin yaran nan , duk ya na sanye da face mask amma sai da ya yaran nan su ka gane shi , kenan sun san me kula da su Ayden kuma bai yi mamakin yadda a ka yi yaran su ka gane shi ba , sai da ya yi musu wassa kamar wani familyn su sannan ya yi musu albishir zai mayar da su makaranta baki daya kuma shi zai dauki nauyin karatun su ba yaran ba har mai kula da gidan marayu sai da ta yi farin ciki kamar ta yi kuka , ta na yi wa Ayden godiya duk da ba ta san ko wanene ba , ita dai kawai ta san kowace Friday ya na kawowa yaran abincin da kaya wani lokaci har kudi ya ke turawa a kai su shopping , amma ba ta taba sanin wanene Ayden ba sai da su ka yi wajen one hour a gidan marayu kafin su baro shi , su ka nufi gidan Adrian na san kuma ku na son ki san dalilin shi na kula da yaran nan kamar yan uwan shi , nan gaba kadan za ku sani amma ba yanzu wajen ba ku dai ku ci gaba da bibiyar labarin dan yanzu a ka fara kamar kullum ku na tare da alkalamin MEERAH ✌💕🕊 [18/02 à 11:55] 🪷🩷: 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 15 & 16 🕊❤} ______________________________________ ▪ESRA 💫 ido a rufe ta turo kofar office din ta ta shigo ta na kuka , hawaye na zubo mata bibiyu , kai tsaye chair din ta ta nufa ta zauna , ta kontar da kanta saman desk din ta na kukan ta a hankali ta fara rage sautin kukanta , lokaci guda abun da ya faru ya dawo mata a kai a dubu dari ta dago kan ta ta na zaro idanu , ta bude baki a hankali ta furta sunan Ayden , sannan ta ce " wannan shi ne Ayden Brian ? " da sauri ta mike tsaye za ta bar wajen kawai sai ta tsaya cak ta koma ta zauna ta ja wani dan siririn tsaki kafin ta ci gaba da aikin ta ______________________________________ ▪AFTER SOME HOURS misalin karfe 6 ta sauka da ga aikin ta , kai tsaye hanyar gida ta nufa , ta na tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki ta na tsaka da tafiyar ta kawai ta jiyo Muryar Kim a bayan ta ya na fadin " Miss Chocolate ! Miss Chocolate ! " ya fada da dan karfi da allamun ita ya ke kira cak ta tsaya da tafiyar ta har wani dan sanyi ta ji cikin zuciyarta lokaci guda a hankali ta juya , nan ta gan shi ya na tafiya ya tunkaro ta , bai sauya kayan jikin shi ba haka ta tsaya ta kura mishi ido har ya karaso gabanta ya tsaya ya na fadin " Miss Chocolate , tun dazu na ke ta kiran ki amma kin share ni " ba ta ce mishi komai ba ta sunkuyar da kai ta juya ta fara takawa a hankali a hankali ya fara takawa ya karaso geffen ta su ka jera , ya dan sunkuyar da kai ya na lekon face din ta cikin sanyin murya ya ce mata " Miss Chocolate , lafiya na ga face din ki ta kunbura haka , ko kuka ki ka yi ? " kamar dama jira ta ke a yi mata tambayar kawai ta dago kai ta ce mishi " Eh , kuka na yi , ni wlh gidan uwata ma zan koma , na gaji da wannan aikin , Wancen mara imanin mai fuskar shanun ya takurawa rayuwa ta , komai na yi wajen shi ba dai'dai ba ne " shi dai ya tsaya ya na kallon yadda ta ke magana cike da bacin rai idanunta cike da ruwa sai da ta gama maganar ta sannan ya ce mata " calm down , me ya faru ne a wajen aikin naki ? " " wani file ne da za mu tatauna a kai yau na manta dayar paper a gida , shi ne kawai ya rufe ni da fada gaban sauran ma'aikatan , sai da na ce ya bari na koma gida na dauko ta amma ya ki sauraro na " cikin ko in kula ya ce mata " ni wlh na dauka wani abu a ka yi , wai saboda paper ki ke kuka , paper din da na ke kunna taba da ita , mu je na saya miki wata " wata yar karamar dariya Esra ta yi ta na fadin " rike abun ka ba na so " ta kai karshen ta na kara saurin tafiyar ta ta yi gaba ya na ganin haka ya sa hannayan shi cikin aljihu , ya rage tashi tafiyar ya na kallon ta sai da ta yi mishi nisa sosai sannan ta juyo ta gan shi cen baya ya na tafiya jiki a mace cak ta tsaya ta na kallon shi har karaso wajen ta ya tsaya su na fuskantar juna a sanyaye ta ce mishi " lafiya ka ke tafiya a haka ? " slowly ya bude baki ya ce mata " ba ki saya min sigarin da na ce miki ba " ta na jin hakan kawai sai ta yi tunanin ko dan ya na son ya sha sigari ne ya ke wannan tafiyar sanyin tsuke fuska ta yi ta na fadin " ba zan saya ba , wuce mu tafi " ta fada ta na juyawa ta ci gaba da takawa tsayawa ya yi ya na kallon ta ta na tafiya , da ga ganin yanayin tafiyar ta ka san cikin fushi ta ke slowly ya juya ya yi hanyar shi ya yi wata kwanar Esra kuwa ba ta ma sani ba sai tafiyar ta ta ke , sai da ta fara hango building din su sannan ta tsaya ta juyo ta na fadin " ni zan sh...... " kassa kai karshen maganar ta yi saboda ganin bayan nata da ta yi fayam babu kowa a hankali ta kalli hagu , ta kalli dama ta ga babu Kim babu mai kama da shi " yanzu yaron nan dan na ki sayar mishi sigari shi ne ya gudu ? za mu hadu gobe ai " ta na gama fadar haka ta juya ta shiga building din kai tsaye Part din su ta nufa ko da ta shiga ta ajiye bag din ta saman table , ta wuce bedroom din ta , ta cire kayan jikinta , ta saka bathrobe sannan ta fito ta shiga toilet wanka ta yi sannan ta dauro da Alwalla kafin ta fito , ta shirya cikin wata gown mata nauyi irin ta zama gida haka ta saka hijab din ta , ta shinfida sallayar ta ta tada sallat ko da ta kammala ba ta tashi ba sai da ta zauna ta yi karatun kur'ani , har lokacin sallar isha ya zagayo , ta tashi ta gabatar da ita bayan ta kammala ta cire hijabin ta ajiye saman bed din ta sannan ta fito ta dawo parlour ta zauna saman sofa , ta kai hannu ta dauki bag din ta ta fiddo wasu takardu da laptop din ta dai² lokacin da Safna ta shigo gidan ta na sallama a sanyaye Esra ta amsa mata sallamar ta , ta na kokarin bude laptop din ta cikin nitsuwa Safna ta karaso cikin parlourn ta , ta zauna saman sofa ta na murmushi ta ce " ya ? Allah ya sa yau ma kin shirya mana Diner ? " " hmmm , ba abun da na shirya , ni bar ni da kayan takaici ma " Esra ta fada ta na latsa laptop din ta " takaici kuma , me ya faru ne ? " Safna ta fada ta na ajiye bag din ta saman table ba tare da ta dago kai ba Esra ta ce mata " yau akwai wani meeting da Sir Kevin ya shirya mana , wlh akasi a ka samu na yarda daya da ga cikin paper din file di na , mara mutuncin nan kawai ya same ni ya rufe ni da fada wai ba na aiki na yadda ya dace , sa'a ta guda ina da copy din file din a laptop di na , shi ne zan kammala yanzu na tura mishi ta Email " murmushi mai dan sauti Safna ta yi kafin ta kai hannu ta dauki bag din ta , ta bude ta fiddo paper din nan da Adrian ya ba ta ta mikawa Esra ta na fadin " sa'ar ki guda ki na da friend's din da ke aiki cikin restaurant din da ki ka je cin abinci har ki ka yarda paper din ki " slowly Esra ta dago kai ta kalli paper din , hakan na nufin a restaurant din da su ka ci abinci ta baro paper din ? ya a ka yi ta fito bayan ita ta san ba ta fiddo paper din ba ? ko dai wani ya fiddo ta ba ta sani ba ? wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta kai hannu ta karbi paper din ta na fadin " shi ya sa na ke mutuwar son ki , ki na ji tashi ki je ki shirya yau a restaurant za mu yi diner kuma ni zan biya " dan zaro idanu Safna ta yi ta na fadin " la , da gaske ? duk wannan farin ciki saboda paper ? wannan paper ? " " hmmm , Safna ba za ki gane ba wlh , ba ki san pression din da Sir Kevin ke daura min ba , kamar ni kadai ce ke aiki a wajen " ta kai karshen ta na tattare takardun ta , ta meda cikin bag din ta da laptop din ta ita kuwa Safna ta tashi ta shiga corridor ta wuce bedroom din ta da ga nan ta shiga toilet ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wata gown red color mai kyau , ta yi Rowling veil din ta white color a kai ta na fitowa parlour ta tardo Esra zaune saman sofa ta na sanye da kaya tak tak irin nata wata yar karamar dariya Safna ta yi ta na karasowa cikin parlourn ta na fadin " hmm , my twins ya a ka yi wannan hadin haka ? " " ke dai zan tambaya " Esra ta fada ta na mikewa tsaye ta dauki yar karamar bag din ta murmushi kawai Safna ta yi mata ba tare da ta ce komai ba su ka nufi kofar fita su ka fice a tare su ka rufe part din nasu ______________________________________ ▪KIM 🕊❤ a hankali ya ke tafiya saman wani kyakyawan titi , ya na rike da wani gwongwanin kamar na maltina amma ba maltina ba ce kayan nan dai na safe su ne a jikin shi , amma gashin kan shi a tirje ya ke , ya zubo mishi har gaban goshi ya rufe mishi idanu , ya sunkuyar da kai ya tafiya jiki a mace a haka har ya karaso wani kyawatencen garden cike da ciyayi , babu kowa a ciki sai tsintsaye a hankali ya nufi wata fountain fara kal , ya tsaya gaban ta ya na kallon kan shi ta cikin ruwan a hankali ya sa hannu ya janye gashin da ke gaban goshin shi , nan na ga idanun shi sun yi jazir , sun kunbura da allamun kuka ya yi wani cool murmushi ya sakin wa kan shi kafin ya bude baki a hankali ya ce " shikenan , haka rayuwar ka za ta kare ? , ka ta so a maraye cikin gidan marayu babu uwa ba babu uba , kuma ka mutu a haka ? ko friend babu sai wine da taba ? why Kim ? why za ka lalata rayuwar ka haka ? , na san da ki na nan haka za ki ce min , but now i'm alone , you're not here with me " ya na gama fadar haka ya saki kuka a hankali ya na fadin " why ? why za ki tafi ki bar ni bayan kin san ke kadai gare ni a duniyar nan , ya ki ke so na yi yanzu ? " ya na gama fadar ya zube saman guyiwowinshi ya na kuka kamar wani karamin yaro a hankali ya dago drink din shi ya kai a baki ya sha kadan ka fin ya sauko ya na kallon kan shi cikin ruwan foutain din ya bude baki a hankali ya fara rera waka ya na fadin " SUNDAY MORNINGS WERE YOUR FAVORITE I USED TO MEET YOU DOWN ONE WOODS CREEK ROAD YOU DID YOUR HAIR UP , LIKE YOU WERE FAMOUS EVEN THOUGH IT'S ONLY CHURCH WHERE WE WERE GOING , OHHHHH NOW SUNDAY MORNINGS I JUST SLEEP IN IT'S LIKE I'VE BURIED MY FAITH WITH YOU I'M SCREAMING AT A GOD I DON'T KNOW IF I BELIEVE IN CAUSE I DON'T KNOW WHAT ELSE I CAN DO , YEAHHHHHH AND I'M STEEL HOLDING ON TO EVERYTHING THAT'S DEAD AND GONE NO I DON'T WANNA SAY GOODBYE CAUSE THIS ONE MEANS FOREVER NOW YOU'RE IN THE STARS AND SIX-FEET'S NEVER FELT SO FAR AND HERE I AM ALONE BETWEEN THE HEAVENS AND THE EMBERS OHH IT HURTS SO HARD FOR A MILLION DIFFERENT REASONS YOU TOOK THE BEST OF MY HEART , AND LEFT THE REST IN PIECES " sai da kammala sannan ya kai hannu a hankali ya fara goge hawayen da su ka zubo mishi , ya dago drink din shi ya kai baki ya daga kai sama ya shanye ta lokaci guda kafin ya sauko ya tilla gongwanin cen gefe murya a disashe ya ce " I really missed you " ya na gama fadar haka ya lumshe idanunshi a hankali ya ida sulalewa a wajen ya konta , ya kankame kan shi waje guda ya na ci gaba da kukan shi kassa ( 🤧🤧 WLH HAR YA BAN TAUSAYI ) [19/02 à 10:53] 🪷🩷: *PAID BOOK* 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {F R E E P A G E 17 & 18 🕊❤} ________________________________________ ▪ESRA 💫❤ a hankali su ke tafiya ita da Safna saman titi , su na tafe su na dariya da allamun sun ji dadin fitar da su ka yi sai da su ka karaso wajen wani traffic light sannan Esra ta tsaya ta na fadin " tsaya mu tsayar da taxi ya meda mu ni gaskiya na gaji " a hankali Safna ta dawo ta riko hannun ta ta na fadin " please mu tafi , mun ma kusa isowa " marairaice fuska Esra ta yi kafin ta bi bayan ta su bar wajen ta na fadin " Uhm , Uhm ni kawai ki na son ki gajiyar da ni , to wlh in mu ka koma sai kai yi min tausa " wata yar karamar dariya Safna ta yi kafin ta zagayo da hannun ta a wuyan Esra ta na fadin " duk abun da ki ke so , yanzu dai mu tafi , Sarauniyar kyau ba " ta kai karshen ta na bushewa da dariya wani dan karamin tsaki Esra ta yi ta na fadin " ni wlh ba dan kin tare ni ba da na koma na yi mishi rashin mutuncin da ya dace shege dan iska kawai " sake bushewa da dariya Safna ta yi ta na fadin " haba Sarauniyar kyau , ke da fan din ki , ai ya ga abun d aya burge shi ne , amma bai san Esra ta fi karfin shi ba , sai dan sarki jikan sarki , ko ba haka ba Sarauniya " ta kai karshen cike da zolaya wani dan karamin tsaki Esra ta yi ta na kauda kai gefe Dum ta ji zuciyarta ta buga da mugun karfi , cak ta tsaya waje guda ta kura mishi ido a rude ita ma Safna ta tsaya ta na fadin " lafiya ki ka tsaya ? " hannu Esra ta kai ta janye hannun Safna da ke saman wuyan ta ta fara takawa da sauri ta tsallaka titi ta shiga garden din kai tsaye Kim ta nufa ta na kiran sunan shi ta na isa ta zube saman guyiwowinta ta talabo kan shi ta na fadin " Kim , wake up , me ka ke yi a nan ? " shiru ko motsi bai yi ba ta na a haka ta jiyo Muryar Safna ta na fadin " Esra , wanene wannan ? kin san shi ne ? " " Eh na san shi , please kama min mu tayar da shi " ta fada ta na sakin shi ta mike tsaye da sauri Safna ta ce mata " mu kai shi ina ? ki na da lafiya kuwa ? kin ga kyale shi , wuce mu tafi , in ya tashi zai bar wajen " cikin sanyin murya Esra ta ce mata " haba Safna , ina imanin ki ya yi ? dubi fa halin da ya ke ciki , ki na tunanin a banza zai zo wajen nan ya konta ? da ga gani ya na bukatar taimako , a matsayin ki na musulma ko dan halayan addinin mu ya kamata mu taimaka mishi , in mu ka bar shi a nan wani abu ya zo ya same shi kin san mu ma Allah ba zai kyale mu ba , saboda mu na ganin shi amma mu ka kyale shi har wani abu ya same shi ba mu taimaka mishi ba " wata nanauyar ajiyar zuciya Safna ta sauke kafin ta karewa Kim kallo da kyau , sam bai yi mata kama da yan shaye shaye ba , kawai sai ta yi tunanin abun da Esra ta fada gaskiya ne , ya na bukatar taimako dan ba ya cikin hayacin shi " shikenan , yanzu ina za mu kai shi ? ko kin san gidan su ? " Safna ta fada ta na karasowa dayan geffen Kim a tare su ka hada karfi su ka mikar da shi tsaye , gaskiya Kim ya ji nauyi , da kyair su ka mikar da shi , a haka su ka dinga jan shi har su ka baro garden din da shi sai da su ka fito sannan Esra ta ce wa Safna " no , ban san gidan su ba , but mu kai shi part din mu , da safe on ya ji sauki sai ya fada mana ina ne gidan su sai mu meda shi " " Esra , kar ki janyo mana matsala , a ka je dan yankar kai ne ? " " da ya fara cire naki kan " Esra ta fada cikin ko in kula wani dan karamin tsaki Safna ta yi ba tare da ta ce komai ba , su ka ci gaba da jan Kim har su ka iso building din su kai tsaye lift su ka shiga su ka nufi part su su na shiga su ka kontar da Kim saman doguwar sofa su na nishi kamar wanda su ka kwana su na gudu a hankali Esra ta zagayo ta cire mishi sneakers din shi ta ajiye a kassa geffen sofar , ita dai Safna tun lokacin da su ka kontar da shi ta juya ta nufi bedroom din ta a hankali ta zauna bakin sofar , ta dago hannu ta janye mishi gashin shi da ya zubo mishi saman forehead , ta na kallon face din shi da kyau nan ta lura da yadda idanun shi su ka kunbura kamar wanda ya yi kuka wani cool murmushi ta saki kafin ta tashi a hankali ta nufi corridor ta shiga bedroom din ta ta na barin wajen Kim ya bude idanun shi slowly , ya juyo da kan shi ya kalli saitin corridor din kafin ya meda shi ya lumshe su , ashe dama ya na cikin hayacin shi , kawai ya yi shiru ne ya ga in za ta kyale shi ko kuwa za ta taimaka mishi in har da gaske ta na son zama friend din shi sai ko ya ga ta taimaka mishi , ta kawo shi har cikin gidan su ______________________________________ ▪WASHE GARI ⛅💫⛅💫 A hankali ya ware idanunshi ya na kallon ceiling ba tare da ya motsa ba kamar da ga sama ya jiyo Muryar Esra ta na fadin " sai yanzu ka tashi ? " wani dan lumshe idanu ya yi ya na bude su a hankali , kafin ya sauko da kafafun shi kassa ya mike zaune bakin sofar da sauri ya kai hannu ya dafe kan shi , ya datse idanun shi da karfi da allamun kan shi ke yi mishi ciwo cike da kula Esra ta ce mishi " lafiya ? me ya faru ? " ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " a ina na ke ? me na ke yi a nan ? " wani dan karamin murmushi Esra ta saki kafin ta ce " kar ka damu cikin apartment di na ka ke " " apartment din ki kuma ? me na ke yi a nan ? ta ya na zo ? " ya fada ya na janye hannunshi da ga saman kan shi ya ware idanunshi slowly ba su sauka ko ina ba sai cikin nata , ta zaune saman sofa ta na kollon shi da murmushi a face din ta kara fadada murmushin ta ta yi kafin ta ce " ya ka ke jin jikin naka ? " " Fine " ya fada a takaice kafin ya mike tsaye da sauri ta ce mishi " ina za ka je ? " " ban san ya a ka yi na zo nan ba , but ya kamata na tafi yanzu , na gode " ya fada ya na shirin takawa da sauri ta mike ta na fadin " no , ka tsaya ka yi breakfast kafin ka tafi " bai ce mata komai ba ya nufi kofar fita ya bude ya fice abun shi ita ma ba ta yi kokarin tsayar da shi ba , sai da ya fita sannan ta koma ta zauna , ta bude laptop din ta da ke ajiye saman table ta fara aikin ta _____________________________________________ ▪BROOKLYN ▪AYDEN zaune ya ke saman chair din bakin pool da ga shi shi short , ya mike kafafun shi ya daga kai sama ya shafa wani abu green a face din shi kamar mask na cream haka , ya lumshe idanunshi lips din shi kawai a ke iya gani pink color da su ma su mugun laushi ya na a haka Adrian ya iso wajen kamar a na kore da shi , kai tsaye Ayden ya nufa ya na fadin " Ayden , please wake up akwai matsala " cikin nitsuwa Ayden ya bude baki a sanyaye ya ce mishi " wace irin matsala early haka ? " " Ayden , ban ga relieve din company ba " Adrian ya fada cikin ko in kula Ayden ya ce mishi " and ? ba ka na da copy ba a cikin laptop ba ? " " no Ayden babu copy din ta ....... " cikin nitsuwa Ayden ya katse shi da cewa " no wonder , ka ban tsoro ni , na ma zata wani abu a ka yi " " Ayden , in ban ga relieve din nan ba ba za mu san kudin da Kevin ya fitar ba last month , duk investigation din mu zai zama kamar banza " wani dogon nunfashi Ayden ya ja ya na gyara zaman shi saman chair din ya ce " don't worry , za mu San abun yi , kai dai kawai ka bi tsarin plan di na " wata yar karamar ajiyar zuciya Adrian ya sauke kafin ya zagayo ya zauna saman chair din geffen ta Ayden kafin ya ce " Bro , tun wuri ya kamata ka san abun yi dangane da Kevin , ko wane month ribar companyn ka kassa ta ke , in a ka ci gaba a haka sai mun yi bankruptcy , hakan na nufin sai ka rufe companyn , na san kuma ba haka ka ke so ba " shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba amma ya jin abun da ya ke cewa , har cikin ran shi ya na jin zafin satar nan da Kevin ke yi , ya na neman ya kashe mishi company shi kuma ba zai iya jure hakan ba saboda companyn amana ce momyn su ta bar mishi , duk abun da ya samu companyn shi ne mai laifi dan bai tsaya ya kula da ita ba yadda ya dace ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya jiyo Muryar Adrian ya na fadin " ya kamata ka koma ka ci gaba da kula da companyn ka , please my Bro " a sanyaye Ayden ya ce mishi " Monday , ka sa a gyara Office di na monday zan koma " wani kyawatencen murmushi Adrian ya saki ya wata yar karamar dariya ya na fadin " Yes , Yes , Yes , da gaske za ka koma ? i'm really happy , finally tsawan shekaru za ka kama business din ka " " amma a tare za mu koma " cike da fara'a Adrian ya ce mishi " no wonder , ni dama a shirye na ke , kai kadai na ke jira , za ka gani yadda business din zai kara habbaka , na san saboda Kevin ba da zuciya daya ya ke kula da shi ba shi ya sa mu ke yin kassa " shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai ba da allamun ya tafi duniyar tunanin shi shi kuwa Adrian sai zuba mishi surutu ya ke bai san da cewa abokin nashi ya yi nisa duniyar tunanin shi ba sai da ya share wajen good ten minutes a haka kafin ya lura abokin nashi ba ya ma sauraron shi hannu ya kai ya buge shi a cinya ya na fadin " kai tunanin me ka ke tun dazu ina yi maka magana ka kyale ni ? " wata boyayyar ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya bude baki a hankali ya ce " Adrian , i think i'm falling in love " dan zaro idanu Adrian ya yi ya na kallon shi , a rude ya bude baki ya ce " love , Ayden ka na jin abun da ka ke cewa ? Love fa ? da wa ? ban taba ganin ka ba da mace ? ta ya z...... " kut maganar ta yanke bai kai karshen ta ba sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " Ayden , ko dai yarinyar da ka taro jiya ka fara so ? " " Esra , sunan ta Esra " Ayden ya fada ba tare da ya bude idanun shi ba A hankali Adrian ya maimaita sunan kassa kassa , Tabbas ya jiyo lokacin da Kevin ya kira sunan Esra , kenan Ayden ya kamu da son ta lokaci guda haka ? in na gane saboda ita ne zai koma companyn Monday ? " Ayden , da gaske ka kamu da son ta " Adrian ya fada murya cen kassan makoshi a hankali Ayden ya gyada mishi kai allamun Eh sannan ya ce " lokacin da idanuna su ka sauka cikin nata , ji na yi kamar na bar wannan duniyar , wani sabon feeling na ji a zuciya ta wanda ban taba jin irin shi ba , for the first time in my life na samu nitsuwa cikin idanun wata macen bayan na momy , Adrian please help me na cire wannan abun da ga cikin zuciya ta dan bai kamace ni ba " a rude Adrian ya ce mishi " why ? kamar ya ka fitar da shi ? " " Adrian , ba na jin zan iya jure rashin wani wanda na ke so cikin rayuwa ta , gwara na cire wannan abun tun ban yi nisa ba " da sauri Adrian ya girgiza mishi kai ya na fadin " No , No Ayden , you too have the right to love, you have the right to happiness if you really love this girl, live your life with her, forget the past, live the present with a thousand and one colors so that your future will be more than perfect, with her , ni fa abokin ka ne tun mu na 4 years , tun bayan rasuwar momy tsawan shekaru yanzu ban taba ganin ka ka yi murmushi ba " cikin nitsuwa Ayden ya sauko da kafafun shi kassa ba tare da ya bude idanun shi ba ya mike tsaye ya fara takawa zai bar wajen ido a rufe dan ba ya tunanin zai ci gaba da wannan hirar da kallo Adrian ya raka shi har sai da ya bar wajen sannan ya saki wani cool murmushi ya ce " in har da gaske ka na son yarinyar nan na yi maka alkawari sai na sa ta zama mallakin ka , Esra ...... Sunan ya hadu haka ita ma ta hadu gaskiya , ban ga laifin ka ba dan ka kamu da son ta " ya na gama fadar haka ya mike a hankali ya bi bayan Ayden ya bar wajen , wannan abun ya ban mamaki gaskiya , ya a ka yi Ayden ya kamu da son Esra haka , Wannan shi ne love at the first sight , yanzu ya za ta kasance in Ayden ya koma companyn 🤣🤣 Ga Kuma Kim shi ma , da alamun Esra ta kamu da son shi ba ta sani ba , ni dai zan ga ya game din zai kasance su uku 🤣🤣🤣 [21/02 à 09:45] 🪷🩷: 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 19 & 20 🕊❤} ________________________________________ ▪ESRA ❤💫 zaune su ke cikin restaurant ita da Cherry da Arthur , Arthur na rike da wata paper ya na karantawa Cherry da Esra sun tsare shi da ido sai da ya share two minutes a haka kafin ya ajiye takardar saman table din su , ya na kallon Esra ya ce " ina ki ka samu paper din nan ? " cikin nitsuwa Esra ta ce mishi " Yesterday na zo restaurant din nan yin breakfast , to wajen fiddo kudin biyan na san na yarda wata paper ta file din da za mu yi meeting a kai har sir Kevin ya yi min magana a kai , to bayan na koma gida Safna ta kawo min paper din ta na fadin restaurant din su na bar paper din " " but wannan ba ita ce paper din ba , ina ki ka samu wannan ? " Cherry ta fada ta na kai hannu ta dauki paper din Esra ba ta ce mata komai ba ta dauki wayarta da ke ajiye a gefe , ta fara latsawa na dan lokaci kafin ta juya ta na nuna musu pic din Adrian da ta dauka jiya ta na ce musu " lokacin da na shigo restaurant din wannan mutun ya shigo , ku na gani da paper a gaban shi ya na aiki , to wannan paper din tashi ce , kuma jiya bayan na baro taron meeting din na hadu da shi cikin hall din Building din tare da Ayden Brian , mamallakin companyn " dan zaro idanu Arthur ya yi ya na fadin " no , da gaske ? Ayden ya zo companyn mu jiya ? " " Eh , ya zo , har ma mu ka yi karo da juna " da sauri Cherry ta katse ta da cewa " wait , kenan shi ne saurayin da a ka ce ya taro ki ? " " yeah , shi ne " Esra ta fada a sanyaye cikin nitsuwa Arthur ya ce " kin ga face din shi ? ki na iya gane shi kenan ? " a hankali Esra ta girgiza mishi kai ta na fadin " no , ban ga face din shi ba saboda ya na sanye da face mask , amma ina iya gane saurayin da ke tare da shi na ji sir Kevin ya kira shi da Adrian " " ta baci , da a ce kin ga face din shi da za mu iya gano inda ya ke har mu yi mishi maganar abun da ke faruwa " fadin Arthur ya na gama rufe bakin shi Esra ta ce " no , yanzu ma ba ta baci ba , wannan paper din za ta yi mana anfani dan kara karfafa hujjojin mu wajen shi , abu guda mu ke bukata kawai file din office din sir Kevin " Cherry : " to yanzu ya za mu yi mu samo file din , kin dai ji uban security din da ke office din Sir Kevin " Arthur : " idea din ku za mu bi , ta shiga ta System of climatisation " Esra : " kai fa ka ce it's not a good idea , za mu iya bacewa ko zafi ya kashe mu " wani dogon nunfashi ya ja kafin ya ce " That's why mu na bukatar ground plan din building din , cikin sa'a ko na samo daya da ga cikin architects din da su ka gina building din , but ya ce zai dauki two or three days kafin ya samo mana ground plan din " a tare Esra da Cherry su ka washe baki su na dan zaro idanu kafin su dago hannu su yi tapi , sannan Esra ta ce " Fine , yanzu plan din mu zai fara , sai mun kawo karshen wannan azzalumin mai fuskar shanu " ta fada cikin bacin rai da allamun har yanzu ta na jin haushin fadan da ya yi mata gaban mutane a tare Cherry da Arthur su ka yi dariya dan sun gane abun da ke cikin zuciyar ta har Cherry ta bude baki za ta yi magana Wayar Arthur ta fara ringing , a hankali ya kai hannu cikin aljihun shi ya fiddo wayar ya na kallon screen din a hankali ya mike tsaye ya na fadin " girls ina ga zan tafi , akwai in da a ke jira na " " okay , see you next time " Esra da Cherry su ka fada a tare bai ce musu komai ba ya fara takawa ya bar wajen ya fice restaurant din ya bar su nan " ya kamata ni ma na tafi " Cherry ta fada a hankali Esra ta kai hannu ta tattare kayan ta , ta dauki bag din ta ta na fadin " mu tafi " ta qarashe maganar ta na mikewa tsaye a hankali ita ma Cherry ta mike su ka baro restaurant din su na fitowa su ka yi hannun riga , Esra ta yi dama , Cherry ta yi hagu a hankali ta ke tafiyar ta cikin nitsuwa har ta karaso greenwich street dan ta na mugun son ganin Kim , dan tun lokacin da ya baro apartments din su ta ke son ganin shi ta ga in ya na cikin koshin lafiya kai tsaye Dan kangon ban da ya ke zama ta nufa ta na sallama a hankali duk da ta san ba za a amsa mata ba cen ta hango shi zaune ya na sanye da wani crazy jeans blue , da t-shirt white color ya saka wasu Thong farare a kafafun shi , yatsun kafar shi sun fito dogaye da su farare kal gwanin burgewa ya tirje wannan gashin kan nashi har ya rufe mishi idanu , ya na rike da sigari da hannu guda , gudan kuma ya na rike da gongwanin maltina ya na sha ya na busa sigarin shi cikin nitsuwa Esra ta karaso gaban shi ta tsaya ta na fadin " Kim , please ba na ce ka daina shan wannan abun ba " ta kai karshen ta na kai hannu ta buge tabar da maltinar a dubu dari ya dago kai , ba karamar razana Esra ta yi ba har wani baya ta yi ta na dafe saitin zuciyar ta bare ko idanun shi sun yi jazir cikin bacin rai ya bude baki ya ce mata " why ? me ma ki ke yi a nan ? wai ba za ki iya ba ni lafiya ba ? me na yi miki ki ke son takurawa rayuwa ta ? " ita dai ta tsaya ta na kallon yadda ya ke yi mata magana cike da bacin rai da allamun a buge ya ke wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke ta matso a sanyaye ta ce mishi " Kim , please calm down " da sauri ya katse ta da cewa " stop ! ba na bukatar kyautatawar ki , please let me , let me , babu abun da ke tsakani na da ke so let me " ya na gama fadar haka ya mike a zafafe zai bar wajen da sauri ta riko hannunshi ta na fadin " please Kim wait , ka manta alkawari da ke tsakanin mu ? " da karfi ya kwace hannun shi ya tura ta baya ya na fadin " forget that , i don't need you in my life , i'm happy without you " ya kai karshen ya na juyawa da sauri Esra ta bi bayan shi ta na fadin " zan saya maka chocolate " cak ya tsaya jin ta ce chocolate , abun da ya fi so fiye da komai a rayuwar shi Esra na ganin ya tsaya ta saki wani cool murmushi ta karaso geffen shi ta tsaya ta na fadin " ko ba ka son chocolate din na tafi ? " shiru ya yi bai ce mata komai ba har cikin zuciyar shi ya na son chocolate a yanzu ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya ga ta yi gaba ta na fadin " shikenan tun da ba ka so na tafi abu na " cikin nitsuwa ya taro ta da cewa " ina so " cak ta tsaya ta na sakin wani dan karamin murmushin geffen fuska , ta samu abun da ta ke so slowly ta juyo ta mika mishi hannu ta na fadin " okay , let's go " a hankali ya tako ya riko hannunta , kamar wani karamin yaro ta fara jan shi su ka bar wajen , ta na sakin wani dan karamin murmushi shi kuma ya sunkuyar da kai ya na kallon kafafun shi kun san yadda yanayin garin US ya ke kowa harkar gaban shi ya ke hakan ya sa ba wanda ya damu su kowa na aikin shi a haka har su ka iso wani market , sai da su ka shiga ta saki hannun shi sannan ta ce ya jira a nan ba musu ya tsaya waje guda ya na kallon ta ta nufi fridge din wajen , ta bude ta kwashi chocolate har wajen goma sannan ta dawo ta nufi wajen biya ta , ta biya kudin a ka saka mata chocolate din cikin leda , sannan ta dawo inda ta bar shi ko motsi bai ba a hankali ta mika mishi hannu allamun su tafi ba musu ya riko hannunta su ka bar wajen sai da su ka dan yi nisa sannan ya ce mata " ban chocolate di ta " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " chocolate din ka ko tawa ? in ka na son chocolate din nan ka bi ni a hankali " shiru ya yi bai ce mata komai ba , ya na biye da ita dan ba ya jin zai iya tafiya ba tare da ya karbi chocolate din nan ba a haka har su ka iso wani kyawatencen garden cike da mutane musaman yara kowa na sha a nin shi su na wassa su na dariya gwanin burgewa sai da su ka karaso wajen wani banci sannan ta saki hannun shi ta zauna ta na fadin " Oya , Sit down " ba musu ya zauna geffen ta ba tare da ya ce komai ba wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta kai hannu ta fiddo chocolate guda ta na fadin " zan yi maka tambaya , duk lokacin da ka ba ni amsar da na ke so zan ba chocolate guda , ka yarda ? " slowly ya gyada mata kai allamun Eh ya yarda " okay , First question , minene cikaken assalin ka ? " kai tsaye ya ce mata " ba ni da " " no , impossible a ce ba ka da assali , minene sunan momyn ka , da Daddyn ka ? " a takaice ya ce mata " gidan marayu na girma " nan take yanayin face din ta ya sauya , kenan maraye ne ? ta tambayi kanta slowly ta mika mishi chocolate din a hankali ya kai hannu ya karba , kafin ya bude ta ya fara ci cikin nitsuwa hannu ta kai ta fiddo ta biyun ta na fadin " tun da gidan marayu ka taso hakan na nufin ba ka da yan uwa ko guda , right ? " a hankali ya gyada mata kai allamun Eh dan lumshe idanu ta yi a hankali kafin ta ajiye mishi chocolate din geffen shi , ta kai hannu ta fiddo ta ukun ta na ce mishi " That's why ka ke shan wine saboda rage kadaicin da ka ke jin kanka , right ? " yanzu ma gyada mata kai ya yi a hankali Allamun Eh ya na ci gaba da cin chocolate din shi a hankali ta ajiye mishi chocolate din sannan ta fiddo ta hudu ta ce mishi " yanzu me ka ke yi da rayuwar ka ? a ina ka ke barci ? a ina ka cin abincin ? na san dai ba ka da aiki , ko kuwa ? " ba tare da ya kalle ta ba ya ce " security a nightclub idan dare ya yi , ta haka na biya kudin apartment din da na ke zama a ciki " cikin sanyin ta katse shi da cewa " ka na da apartment ka ke zuwa ka kwana cikin wannan kangon ? " shiru ya yi bai ce mata komai ba shiru ta yi ta na jiran amsar shi amma bai ce mata komai ba sai da ya gama shan chocolate din ya kai hannu ya dauki guda cikin wadda ta ajiye mishi gefe ya bude ya fara ci ta na ganin ta tuno ashe ba ta ajiye mishi chocolate din ba da sauri ta ajiye chocolate din hannun ta , ta dauko wata ta na fadin " ba ka ban amsar tambaya ta ba " sai da ya hadiye chocolate din bakin shi sannan ya ce mata " saboda na fi jin dadin zama ni kadai , babu wanda zai takura min , amma ga shi yanzu ki na son ki takura min " wani cool murmushi ta saki kafin ta ajiye mishi chocolate din ta dauki wata ta na fadin " ban takura maka ba , kawai ina son na gyara maka rayuwa ne , ba dan ka na maraye ba za ka meda kanka mara gata , tabbas ban san ka ba kuma ba ka san ni ba amma zuciya ta ba za ta lamince ganin ka cikin wannan halin da ka ke jefa kanka , wine da taba babbar illa ce ga rayuwar ka " " akwai ma su shan taba da wine dayawa a garin nan , why sai ni za ki taimakawa ? " murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " ai kai ma ka taba taimaka min lokacin da samarin nan su ka sace min bag di ta , ka ga ko dan hakan zan iya taimaka maka , yanzu fada min minene favorite habit din ka , wanda in ka na yin shi ka na jin duk damuwar ka tafi gushe har ka daina tunanin shan wine ? " sai da ya dauki wajen two minutes bai ce mata komai ba kafin ya bude baki ya ce mata " cooking " wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ajiye mishi chocolate din ta kai hannu ta dauki guda ta ce mishi " Fine , da ga yau duk wajen karfe 8 na dare ka tardo apartment di na , za mu yi girki a tare dan ni ma na iya girki sosai " a hankali ya dago kai ya kalle ta ya ce " specially with chocolate ? " gyada mishi kai ta yi ta na fadin " yeah , with chocolate , za ka dinga zuwa ? " slowly ya gyada mata kai allamun Eh " Fine , ka ga in ka daina tunanin wine , za ka daina shan ta , in kuma ka daina za ka ga komai na rayuwar ka ya sauya " " why ki ka damu da ni haka bayan ba mu hada komai da ke ba ? " wani dan karamin murmushin geffen fuska ta yi mishi kafin ta ce " ni ma ban sani ba , kawai zuciya ta ce ta ke ce min na taimaka maka , kuma ni ina bin duk abun da zuciya ta ke fada min " " a ka je duk abun da na fada miki yanzu karya ne , a ka je yadda ki ke tunani ba haka na ke ba , wannan rayuwar tawa duk basaja ce " a sanyaye ta ce mishi " Idan har duk abun da ka fada min karya ne , ba zan ji komai ba saboda kai abokina ne , kuma tsakanin abokai sai dai wassa da dariya ba fada ba " " abokai ? we are friends ? " gyada mishi kai ta yi ta na fadin " yeah we are friends , ko ba ka son zama abokina ? " " ina so , ko dan ki dinga saya min chocolate " ya kai karshen ya na kai chocolate din shi a baki wata yar karamar dariya Esra ta yi dan maganar shi gaskiya ta ba ta dariya wai zai zama abokin ta ko dan ta dinga saya mishi chocolate [24/02 à 09:13] 🪷🩷: 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 21 & 22 🕊❤} sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce mishi " kenan saboda chocolate din ne za ka zama friend din na ? " cikin ko in kula ya ce mata " yeah , rayuwar yanzu babu wanda ke zaune da kai da zuciya guda sai in ya na son wani abu wajen ka , kowa abun da zai gyara shi ya ke dubawa , ni ban san me ya sa ki ke son zama friend's di ta dan ba ni da komai kuma ba za ki samu komai ba sai problems , amma ni zan zama friend's din ki dan ki dinga saya min chocolate , kin ga advantage di na na ke dubawa " wani dan karamin murmushi geffen fuska Esra ta saki kafin ta ce mishi " abun da ke fada gaskiya , kowa advantage din kan shi ya ke dubawa , but ba zan ga laifin ka ba ko da a ce ka yi anfani da ni dan samun abun da ke so , asali ma zan ji dadin ta sanadiya ta ka samu abun da ka ke har ka yi farinciki , na san ko ba komai wata rana in ka tuno da abun nan za ka tuno da ni " shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na shan chocolate din shi cikin konciyar hankali ya na a haka kawai ya ga wata ball ta buge shi a kafa slowly ya dago kai ya ga wani dan yaro ya nufo shi ya na dariya allamun tashi ce sai da ya karaso gaban Kim ya tsaya ya na fadin " please Sir ko za ka iya ban ball di ta ? " ba musu Kim ya kai hannu a hankali ya dauki ball din kafin ya ce mishi " zan iya yin wassa da kai ? " wani kyawatencen murmushi yaron nan ya saki kafin ya gyada mishi kai da sauri ya kai hannu ya karbi ball din ya na fadin " Oya , let's go and play " ba musu Kim ya tashi ya bi bayan yaron nan , kafin ya iso wajen yaron ya ida chocolate din hannun shi ya tilla leda , ya kai hannu ya meda gashin gaban goshin shi baya ita dai Esra ba ta ce komai ba ta na kallon shi har su ka fara wassa da yaron nan gwanin burgewa kamar uba da yaron shi , ga shi ko yaron sai dariya ya ke ya na biyewa Kim , lokaci guda su ka yi mugun burge ta wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta kai hannu cikin bag din ta , ta fiddo wayar ta , ta yi musu wata yar karamar video ta yi musu pics har uku kafin ta meda wayar cikin bag din ta ta dauki chocolate din da ta ajiye wa Kim ta meda su cikin ledar sannan ta ajiye ta mike a hankali ba tare da ta ce komai ba ta fara takawa ta nufi hanyar fita garden din ta na sakin murmushi Kim kuwa bai ma san abun da ke faruwa ba ya na wassan shi kamar wani karamin yaro sai da iyayen yaron su ka kira shi za su bar wajen sannan su ka daina , Ya na juyawa ya ga babu kowa saman bancin su sai ledar chocolate din da ta ajiye mishi a hankali ya tako ya dauki ledar kafin ya fice Garden din shi ma _________________________________________________________ ▪BROOKLYN ▪DISTRICT OF WILLIAMSBURG wani kyawatencen parlour ne mai mugun girma , ya kyawatu iya kyawatuwa komai na cikin shi White and black colors ne , duk walls din wajen na zallar glass ne , ka na iya hangen garin , da allamun samun building ne dan ka na ganin garin da wasu buildings ta ko ina a bangaran dama , parlourn kyawace ya ke da wata doguwar sofa White color irin wannan ma su disign din L , sai wasu kananan pillow a saman ta white colors suma a dayan geffen ta akwai wasu Sofas one seater biyu duk black color da ga tsakiya kuma an shinfida wani kyawatencen carpet round , Black color mai ratsin white , an daura wata kyakyawar table ta zallar glass white color da ga sama da ga saman ta kuma akwai wasu magazine wajen uku ko hudu haka ajiye , geffen su kuma remote ne biyu sai dan decoration na flowers ma su kyau wall din da ke fuskantar Sofar ya na rufe da wasu curtains farare kal , an rufe wall din da su da ga gaban wall din akwai wata yar table an daura wata makekiyar Tv plasma a sama wall din da ke fuskantar wadanan sofas one seaters guda biyu kuma , da ga gaban shi kadan akwai wata doguwar dining table ta zallar glass black color zagaye da wasu slipcover chair guda goma sha biyu su ma duk black colors ne , saman table din gaban ko wace chair akwai wani dan karamin tablecloth white color kamar handkerchief haka da ga saman shi akwai wani plate white color a juye , sai spoon da fork da eating knife a geffen dama geffen hagu kuma glass ne guda biyu kamar irin na shan wine haka , guda babban guda karami dan nesa da dining table din na hango wata kyawatenciyar kitchen cike da kayan girki na zamani , kuma duk abun da ke ciki white color ne a nan ba a saka black ba a bangaran hagu kuma na hango wani dan madaidaicin office , da wani closet cike de books kamar library da ga gaban Closet din akwai wani carpet white color mai dan girma , ya fi na parlour girma da ga saman shi an daura wasu Armchair guda biyu white color su na fuskantar junan su da ga tsakiya kuma wata yar table kamar ta ice haka bayan wannan closet din kuma na hango wani Stair na zallar glass , sai abun ya yi kamar saman closet din nan stair din ya ke takaitaciyar description din wajen kenan amma a zahari abun ya fi haka dan in na ce na ci gaba da description din sai mun kammala book din ma ba page din nan ba , abun dai Masha Allah kawai za a ce dan ka na ganin wajen nan ka san ba na kananan mutane ba ne , amma bari mu koma cikin labarin mu a zaune na hango Kevin saman chair a dining table da allamun diner ya ke yi ya na sanye da wasu pajama farare kal fuskar nan tashi a daure kamar hadari a geffen daman shi na hango wani kyakyawan bature fari kal da shi , ya na kama da Kevin , sai dai ya tsufa sosai dan zai kai 55 years , kun san yadda farar fata ta ke ba ka da resistance , da ka fara Tsufa ta ke jemewa , ga shi kuma duk gashin kan shi fari ne , amma ba shi da gemu ko kadan ya na sanye da wasu Suit navy blue ma su kyau tsadadu da ga gani da allamun wannan shi ne mahaifin su Ayden wato Brian a haka na hango wata kyakyawar budurwa ta na fuskantar Kevin , fara kal da ita kamar ka taba jini ya fito , cikakiyar baturiya a shekaru ba za ta wuce 20 to 21 years ba ta na kama tak tak da Kevin kamar an tsaga kara sai dai color din idanun ta Hazel ne mai mugun kyau ta na da gashi sosai har tsakiyar bayan ta kuma mai laushi russet color da shi mai daukar hankali ta na sanye da wani mini skert pink ko ida rufe mata guyiwa bai yi ba , da wata yar karamar T-shirt dai'dai cibi Red color , amma gaskiya ba ta da shape kun san turawan ban ba wani shape ne da su ba , dama dama breast din ta ya dan tasso kuma ba ramamiya ba ce sosai kowane ya na cin abincin shi cikin konciyar hankali babu me cewa ufan a hankali Kevin ya kai hannu ya dauki glass din ruwan da ke geffen shi na hagu ya kai a baki ya surbi kadan kafin ya ajiye ya juyo ya kalli Brian ya ce " Daddy , gaskiya ya kamata ka yi wa Ayden magana , na daina wannan shiriritar da ya ke , ya dawo mu kula da companyn mu , mu na samun matsala kwana biyun nan , a na yi mana satar makudan kudade Daddy , ba zan iya kula da komai ba ni kadai " a hankali shi ma Brian ya kai hannu ya dauki glass din ruwa ya kai bakin shi ya surbi kadan kafin ya ajiye ya kalli Kevin ya ce mishi " kai ma ka sani , bayan restaurant din shi ba abun da ke cikin zuciyar shi , ko ya dawo ba zai maida hankali ya kula da companyn kamar yadda ya ke kula da restaurant din shi ba " " but Daddy , i've my own life , ba iya ci gaba da kula da companyn nan ba , ni ma ina dreams , ina da aikin da na ke so na yi , please ku yi mishi magana mana , duk abun da ya ke ku/ku ke goya mishi baya ya na yi , da tun farko kun bar shi ya kula da companyn da ba za mu fuskanci wannan matsalar ba , ni ban ma san abun da ya sa momy ta bar mishi companyn ta ba " ba tare da ta dago kai ba budurwar nan ta ce " Saboda ya fi ka kaifin basira , ya fi ka ilimi , ya fi ka tunani , ya fi ka sanin ya kamata , ya fi ka sanin harkar kasuwanci , ya fi ka zuciya , ya fi ka kula da tattali , na ci gaba ko ya isa haka ? " gaskiya maganar ta ba karamin batawa Kevin rai ta yi , cikin bacin rai ya dago hannu zai wanka mata mari cak Brian ya taro hannun ya na fadin " Kevin , are you mad ? marin ta za ka yi ? " da karfi Kevin ya kauce hannun shi kafin ya koma ya zauna ita ko ko a jikin ta dan ko dago kai ba ta yi da allamun ta san Brian ba zai bari ya mare ta ba cike da bacin rai Kevin ya ce " Daddy ka na fa jin abun da ta ke fada " dawo da kallon shi Brian ya yi kan budurwar nan ya ce " Emilie , why za ki fada mishi hakan ? " " ai gaskiya ce na fada " ta fada ta na kai abincin ta a baki " da ke da wancen sakaren zan yi maganin ku , sannan Daddy ka ce mishi ya shirya ya koma companyn in ya wuce one week gaskiya ni bari zan yi , i'm tired " Fadin Kevin slowly Emilie ta dago kai ta kalle shi a sanyaye ta ce mishi " don't worry , na ji ya ce monday zai koma " a tare Kevin da Brian da su ka zaro idanu har su na hada baki su na cewa " da gaske ki ke ? " a hankali ta gyada musu kai ta na fadin " i'm serious , na ji shi ya na waya da Adrian ya ce wai ya sa a gyara office din shi , monday zai kama aikin shi " wani kyawatencen murmushi Brian ya saki ya na fadin " to ka gani , ka na nan ka cika mu da surutu , ka ji monday zai karbi companyn shi , idan ka so za ka iya tafiyar ka " shiru Kevin ya yi bai ce mishi komai ba sai ma hannu da ya kai ya dauki ruwan shi ya kai a baki ya sha kadan kafin ya sauko ya ci gaba da cin abincin shi da allamun ya yi sumar zaune ko kuma wani makamancin hakan su na zaune a haka Ayden ya fara sauko stair a tare duk su ka kai kallon su wajen stair din sanye ya ke cikin wasu Tracksuit farare kal kamar madara , ya saka wasu sneakers farare kal su ma a kafafun shi ba na iya ganin face din shi saboda ya saka hular rigar ya kuma saka face mask baki , ya na takowa Hannayanshi cikin aljihun rigar shi , kai a sunkuye a haka ya gama sauko stair din ya nufi hanyar fita gidan da sauri Brian ya taro shi da cewa " Ayden ba za ka yi diner ba ? " a hankali ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " No , ni da Adrian za mu fita may be idan na dawo zan yi " bai gama rufe bakinshi ba Kevin ya ce " kullum ka fita , kullum ka fita , wai ina ka ke tafiya ? , a sani na ba kai ke dahuwa cikin Restaurant din ka ba , ba kuma company ka ke zuwa ba , kawai ku na cikin gari kai da wancen sakaran ku na yawo " maganar shi ta so ta sosawa Ayden rai gaskiya , duk duniya ba abun da ya tsana kamar a ci mutuncin wani na kusa da shi , wannan abun ya na bata mishi sosai wani dogon nunfashi ya ja kafin ya daga kafa a hankali ya taka ya fice gidan ya na fita Brian ya ce ma Kevin " kai dai ba ka iya fadin al'heri da bakin nan naka , ga shi yanzu ka bata mishi rai " " ai gaskiya ce na fada , tun baya kai ne da ba ka tsawatar mishi , ni ban ma san abun da ya ke cikin familyn mu ba " da sauri Emilie ta dago kai ta ce mishi " no , our family , shi ma ya na cikin familyn mu , ka daina mayar da shi bare , little brother din ka ne " cike da bacin rai Kevin ya ce " no , ni ba brother di na ne ba , kawai yaron da momy ne ta samu wajen cin amanar Daddy da ta yi " " Kevin ! " Brian ya fada da dan karfi ya na zaro idanu dan maganar Kevin ta bata mishi rai shi kuwa Kevin ko a jikin sa sai ma cewa ya yi " why za ka daga min murya ? ai ba karya na yi ba , ba banza ta mallaka mishi duk companyn ta ba saboda na uban shi ne , da a ce ba ta ci amanar ka ba da ba zai zo duniyar nan ba " a hankali Brian ya kai hannu ya dafe saitin zuciya shi ya na yamutse fuska ya na kallon Kevin cike da takaici Emilie na ganin haka ta zaro idanu ta na fadin " Daddy , are you okay ? " murya a disashe ya ce mata " ban ruwa " ba musu ta dauki ruwa ta mike ta kai mishi a baki ya sha sannan ta sauko shi ta koma ta zauna wani dan karamin tsaki Kevin ya yi kafin ya ce " I'm sorry maganar ce ta fito haka kawai , amma ba haka na ke tunani ba , i'm so sorry " MY BOOK IS ₦500 VIA 8081129487 Khadija Sabi'u Monie point bank 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 23 & 24 🕊❤} Da Brian da Emilie duk babu wanda ya ce mishi ufan , amma har cikin zuciyoyinsu sun ji zafin maganar shi duk abun nan da Kevin ya fada a kunnen Ayden , dan ya na tsaye bakin kofar da ga baya , bai tafi ba , abun da Kevin ya fada ya kara tabbatar mishi da abun zuciyar shi ke fada mishi na Kevin ya tsane shi , kawai ya na nuna mishi soyayya ne a fili , abun nan ba karamin zafi ya yi mishi ba dan har hawaye sai da ya zubar amma da ido guda a hankali ya kai hannu ya goge sannan ya bar wajen ya yi tafiya shi 🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼🕊🌼 ▪MISALIN KARFE 8 NA DARE ▪ESRA ❤🕊 Zaune ta ke cikin parlourn apartment din su ta na sanye da wasu kananan kaya blue ma su mugun kyau , sun yi mugun kama ta ko kamar a jikin ta a ka yi su ta na zaune ta na latsa laptop din ta cikin konciyar hankali , Safna kuma ta na cikin bedroom din ta ta na barci dan tun safe ta ke jin jikin ta ba dadi ta na a haka ta ji an bubuga musu kofa a sanyaye slowly Esra ta dago kai ta kalli saitin kofar , kafin ta rufe laptop din ta , ta ajiye saman table ta mike a hankali ta nufi kofar ,l ko tsoro babu ta bude kofar ta na budewa idanun ta su ka sauka saman Kim tsaye bakin kofar fuska a marairaice , ya na sanye da kayan shi na safe idanun shi na sauka saman ta ya ji zuciyar shi ta yi wata muguwar bugawa ya rasa dalili , har wani dan zaro idanu ya yi kadan ya na kallon ta kamar bai san ta ba ita kuma ta na ganin shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta na fadin " na zata ba za ka zo ba " shiru ya yi bai ce mata komai ba ya na kallon ta babu ko kiftawa ta na ganin haka ta juya ta na fadin " tun da ba za ka ce komai ba shigo , na shirya maka duk abun da za ka bukata a kitchen " ba musu ya biyo bayan ta ya shigo gidan kafin ya tura kofar ya rufe ya na ida shigowa ya gan ta zaune saman sofa ta na rike da laptop din ta kawai sai ya yi tsaye ya tsare ta da ido babu ko kiftawa ita kuwa duk hankalin ta na kan aikin ta , ta ma manta da shi lokaci guda kawai ta ji duk ta tsargu kamar a na kallon ta wani cool murmushi ta saki kafin ta dago kai ta kalle shi , cikin zolaya ta ce " Ba ni za ka girka ba , ga kitchen din cen , akwai aikin da na ke yanzu idan na ida zan zo na taya ka " a hankali ya gyada mata kai kafin ya juya ya nufi Kitchen da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta juya ta ci gaba da aikin ta Kim kuwa ya na shiga kitchen din ya tsaya ya na kallon ingredients din da ta jera mishi saman counter a hankali ya juya ya nufi fridge ya bude ya fara bin abun da ke ciki da kallo cen ya hango fish , Potato , carrot , peas , cikin irin ledodin nan na deep freeze bai tsaya bata lokaci ba ya kai hannu ya dauki Fish , potato da carrot , ya dawo ya ajiye saman counter , sannan ya juya ya dauki green pepper , da chilli pepper sannan ya rufe fridge din a hankali ya nufi Oven ya bude ya fiddo tray din ciki ya ajiye saman counter , kafin ya juya ya fara bude closet na sama daya bayan daya da allamun ya na neman wani abu sai da ya bude closet na biyu sannan ya ga wasu kwalaben spices , hannu ya kai ya dauki thyme , rosemary , garlic powder , onion powder ya juyo ya ajiye geffen tray din oven sannan juya ya bude closet na gaba ya fiddo Aluminum, ya juya ya ciro ya shinfida saman tray din oven bayan ya shinfida ya juya ya nufi mixer din da ya hango dayan geffen , ya bude ya fiddo bowl din , ya zuba green pepper , chilli pepper Thyme, rosemary garlic da onion , ya zuba salt da black pepper , ya zuba oil ya koma ya yi mixing din su ya yi marinade sannan ya fiddo bowl din ya dawo ya wajen counter din ya ajiye ya kai hannu ya dauki fish da potato da carrot ya Zube su saman tray din oven ya dauki marinade din na ya zuba a sama ya juya ta shiga cikin kowane , sannan ya dauki tray din ya juya ya saka cikin oven din ya riga ya kunna ya yi zafi sannan ya rufe ya dawo ya tattare ledodin ya zubar a trash ya wanke bowl din mixer din ya mayar ya na juyowa ya ga Esra tsaye bayan shi ta na sakin wani kyawatencen murmushi ba karamar razana ya yi ba dan har wani dan baya ya yi wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " me za mu yi yanzu ? " a hankali ya karaso gaban counter din ya tsaya ya na fadin " oven nawa gare ku ? " " biyu ne " ta fada ta na karasowa geffen shi ta tsaya " okay , ki na da puff pastry ? Apple , cinnamon , cane sugar , lemon " cikin rudu ta ce mishi " me kuma za ka yi da su ? " sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " Apple pie , ko ba ki so ? " dan zaro idanu ta yi ta na fadin " no , da gaske , shi ne favorite dessert di na " slowly ya juyo ya kalle ta sai sakin murmushi ta ke , shi kan shi bai san lokacin da ya saki wani dan karamin murmushin geffen fuska ya na ce mata " ni ma haka " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta juya ta nufi fridge ta fiddo mishi duk abubuwan da ya zano mata ta dawo ta ajiye gaban shi ta na fadin " amma fa ban da mold din yi pie " " no wonder , wadda za mu yi ba ta bukatar mold , it's simple and delicious , cikin 30 minutes za ki iya yin ta " gyada mishi kai ta yi a hankali kafin ta ce " okay prof , bismillah ina kallon ka " wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " yawwa student , yanzu kawo min tray din gudan oven din , sannan ki kunna shi saman 180° " " Yes Chef " ta fada cikin zolaya kafin ta juya ta nufi dayan oven din maganar ta gaskiya ta ba ta shi dariya har wani murmushi ya ke saki shi kadai fiddo tray din ta yi ta kunna oven din kafin ta juya ta ajiye mishi gaban shi ta na ajiye wa ya juya ya nufi gas cooker dama pan din na ajiye a sama , kawai sai ya kunna , ya dawo ya dauki Apples din ya yanka su kana kana sannan ya zuba cikin pan din da ta riga ta yi zafi , ya zuba cane Sugar din da cinnamon da juice din lemon kadan , ya jujuya su , su ka shiga cikin juna har apples din su ka fara yin laushi ya na ganin hakan ya kashe ya dauko pan din ya juyo da ita ya ajiye saman counter sannan ya juyo ya kalli Esra ya ce " ina fatan ki na ganin abun da na ke ? " " ni fa kaina 10000GB ne , duk na yi recording abun da ka ke yi " wani dan karamin murmushi ya yi kafin ya juya ya dauki puff pastry din nan , ya shinfida saman tray din oven , sannan ya dauki knife ya raba shi gida 8 da ga haka ya dauki spoon ya fara debo apples din ya zuba saman parts 4 , sannan ya dauko wadancen da bai zuba ba a kai ya rufe su da su , ya dauki fork ya danne bakunan su daya bayan daya dan kar su bude ya na gamawa ya matsa gefe ya kalli Esra ya ce " za ki iya sakawa a oven " dan zaro idanu ta yi ta na fadin " ban gane ba , har mun ida ? " gyada mata kai ya yi a hankali ba tare da ya ce komai ba " mun yi sauri fa " ta fada ta na daukar tray din ta saka a oven ta rufe kafin ta dawo geffen shi ta tsaya ta na fadin " minti nawa zai yi a ciki ? " " juste 20 minutes " ya fada ya na kai hannu ya dauki spoon ya debo apples ya kawo saitin bakin Esra allamun ta ci wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta bude baki a hankali ta karba ta na kallon shi gaskiya ba karamin dadi abun ya yi mata ba har wani dan lumshe idanu ta ke yi sai da ta gama cinyewa sannan ta kalle shi ta ce " gaskiya ya yi dadi , har na matsu ya gama " wani cool murmushi ya sakin mata kafin ya ce " ke ce mutum ta farko da ta ci abun da na girka kuma ya ce ya yi dadi " " hmmmm , yanzu mintina nawa za mu jira ? " " just 20 minutes " ya fada a takaice wani dogon nunfashi ta ja ta na saukewa a hankali kafin ta ce " Yanzu me za mu yi ? " sai da ya dan jinkirta kafin ya ce mata " Watch cartoon " dan zaro idanu ta yi a hankali ta na fadin " cartoon ? da wannan shekarun naka ? " " yeah , har yanzu ni baby ne " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kai hannu ta ja mishi kumatun shi na dama ta na fadin " yeah , you are a big baby " shi kan shi maganar ta sai da ta ba shi dariya , har sai da wadanan fararen hakwaren nashi su ka fito a hankali ta janye hannunta ta na kallon face din shi gwanin burgewa tun da ta ke ba ta taba ganin murmushi mai kyau irin nashi ba wani cool murmushi ta saki kafin ta juya ta na fadin " mu je na saka maka , Big baby kawai " ba musu ya bi bayanta su ka koma parlourn , su ka zauna sannan ta kunna mishi Tv , ta ba shi remote din sannan ta dauki laptop din ta ta ci gaba da aikin ta cikin nitsuwa Kim ya fara sauya chanel din har ya samu chanel din da su ka saka cartoon kamar wani karamin yaro ya tsaya ya na kallo amma ta wutsiyar ido Esra ya ke kallo ya na a haka kawai ya fara jiyo Muryar ta sama sama kamar ta rero waka shi ko karatun Qur'ani ne ta , ta na karanto suratul Mariam cike da nitsuwa ga Muryar a sanyaye mai dadin sauraro duk da bai san abun da ta ke fada ba amma ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi , irin sanyin da bai taba ji ba a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juyo ya kalle ta da kyau ya ce mata " wace waka ce wannan ki ke ? " wani cool murmushi ta saki kafin ta dasa Aya ta dago kai ta kalle shi ta ce " ba waka ba ce " " to minene ? ni ban taba jin wannan abun ba " " dama ta ya za a yi ka ji shi , kai da ba musulmi ba kuma babu musulmai a kusa da kai , ka san minene religion ko ? " " Eh na sani , amma ban taba yarda da su ba saboda duk makaryata ne , sai su yi ta maganar abubuwa da ba gaskiya ba su na karbar kudaden mutane " " wannan church ne su ke yin hakan , akwai mosque a garin nan zan so ka je ko so guda ne , za ka gane abun da ya ke gaskiya da abun da ya ke karya , amma zan so ka san addini na ba karya ba ne , sai wanda Allah ya so ke samun damar kasancewa musulmi " cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " wanene wannan Allah , kenan in bai so mutun ba ba zai iya zama musulmi ba ? , kenan ni ba ya so na ? " " Allah shi ne ubangijin da mu ke bautawa , shi shi kadai ya ke , babu wani abun bautawa bayan shi , shi ya hallice samai da kassai sannan ya hallice mu dan mu bauta mishi , cikin addini na shan wine haramun ne , shi ya sa na ke son ka daina , bayan hakan babbar illa ce ga rayuwar ka ma " bai ce mata komai ba ya mike a hankali ya nufi kitchen Esra kuwa tambayar shi ba karamin dadi su ka yi mata ba tun da har zai iya tambaya wanene Allah hakan na nufin ta fara jan hankalin shi zuwa ga musulumci , in har Kim ya koma musulmi to tabbas abun alfahari ne wajen ta ta na kallon shi har ya shiga kitchen din ya bude oven kai tsaye kawai ya kai hannu zai dauki tray din a dubu dari ya janye hannun ya na ja da baya shi duk ya mance da zafi abun gare shi da sauri Esra ta ajiye laptop din ta ta tasso ta nufe shi ta na fadin " Oh my God , Kim kai ma ina hankalinka za ka sa hannu kai tsaye babu mitten " " mantawa na yi " ya fada ya na matsowa wajen washbasin ya kunna fanfon ya zuba ma hannun shi ruwan sanyi kafin ya janye cike da kula Esra ta ce mishi " mu je na shafawa maka pommade kar wajen ya ja ruwa ya zame maka matsala " potholder ya dauka ba tare da ya ce mata komai ba ya saka , sannan ya fiddo tray din ya ajiye saman counter ya na ajiye wa wani qamshi mai dadi ya fara tashi a wajen ko ni sai da na hadiye yawu a hankali ya juya ya nufi gudan oven din ya bude ya fiddo tray din ya ajiye geffen dayan sannan ya fidda gloves din ya ajiye gefe ita dai Esra ta zama yar kallo a nan ta na hadiyar yawu shi kuma plates biyu ya dauko , dan madaidaita , ya dauki spoon da fork ya fara dauke Apple pie din nan daya bayan daya ya jera saman dayan plate sannan ya fara kwassar fish din nan da potato da carrot ya Zube duk saman dayan plate , sannan ya dauki tray din ya kai wajen washbasin ya ajiye MY BOOK IS ₦500 VIA 8081129487 Khadija Sabi'u Monie point bank 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 __________________ 💞🔥 TRUE LOVE 🔥💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 25 & 26 🕊❤} bayan ya ajiye ya dawo ya tsaya geffen ta ya ce " here is , ga shi na kammala " da murmushi a face din ta ta ce " gaskiya da ga gani zai yi dadi , Yanzu ka iya girki haka ka ke neman bata wa kan ka lokaci wajen yin security a nightclub , why ba za ka nemi aiki ba a wani restaurant ba ? " " na nema , amma duk restaurant din da na je sai su ce na gwada musu takardun karatu na ko certificate din kwarewa ta a girki , ni kuma ko primary school ban yi ba , shi ya sa na hakura na daina nema " har cikin zuciyar ta ta rasa dalilin da ya sa ta ke mugun jin tausayin Kim , he look so innocent , amma rayuwar shi ta na neman ta ruguje haka , gaskiya ya kamata ta gyara mishi rayuwa ko da shi ne abu na karshe da za ta yi a ta/ta rayuwar wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce kai hannu ta dauki plate din Apple pie ta na fadin " okay , let's go and eat " ta kai karshen ta na fara takawa ta nufi parlour ba musu ya dauki dayan plate din ya bi bayan ta su ka nufi yar dining table din su ta ajiye a sama sannan ta zauna saman chair guda ta na ce mishi ya zauna ajiye plate din kawai ya yi kafin ya dan ja da baya ya na ce mata " no , lokacin hawa aikina ta kusa , tafiya zan yi " marairaice fuska ta yi ta na mikewa tsaye har ta bude baki kawai ta ga ya juya ya fara takawa zai fice da sauri ta ce mishi " Kim , ka tsaya na zuba maka cikin box kar ka tafi da yunwa " ko juyowa bai yi ba ya sa kafa ya fice ya janyo mata kofar ita dai da kallo ta raka shi har sai da fita sannan ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta koma zauna ta so ya tsaya su ci abincin tare ko da pie din ce tun da ita ce favorite dessert din shi , amma yanzu ya tafi a hankali ta kai hannu kai tsaye ko spoon ba ta saka ba ta dauki Apple pie din nan guda ta kai a baki ta na bismillah sannan ta fara ci a hankali ta sauke wata boyayyar ajiyar zuciya kafin ta lumshe idanunta a hankali , gaskiya taste din da yi mata mugun dadi , ita ba ta ma taba cin Pie din da ta yi mata dadi irin wannan ba , ga shi abun so easy amma taste din duniya ne guda , gaskiya Kim ya iya girki cikin kankanan lokaci ya shirya wannan abun ina ga an ba shi isashen lokaci abun da zai yi sai ya fi hakan sai da ta gama cinye sannan ta tashi a hankali ta nufi corridor ta shiga a hankali ta kai hannu ta tura kofar bedroom din Safna ta na sallama kassa kassa a konce Safna ta ke saman bed din ta , ta na rufe da duvet ta na ganin Esra ta dago kai a hankali ta na amsa mata sallamar ta a hankali Esra ta karaso cikin dakin ta zauna bakin gadon ta na fadin " ya jikin naki ? " wata yar karamar ajiyar zuciya Safna ta sauke kafin ta ce " da sauki , amma yunwa na ke ji , tun dazu na ke jin wani qamshi na tashi ban san da ga ina ya ke ba , please gyara min wani abu na ci " wani dan karamin murmushi Esra ta saki kafin ta ce " tashi mu je ki ci , shi ya sa ma na zo na kira mu je mu ci abinci " ta na gama fadar haka ta mike ta nufi kofar fita a hankali Safna ta janye duvet din jikin ta , ta mike zaune ta sauko da kafafun ta kassa ta mike tsaye ta fara takawa a sanyaye ta fito dakin ta na fitowa ta isko Esra zaune saman yar dining table din su dan zaro idanu ta yi ta na kallon abincin da ke sama ta karaso wajen ta janyo dayan chair din ta zauna ta na fadin " Esra , ina ki ka samo wannan abincin ? " wani dan karamin murmushin geffen fuska Esra ta yi kafin ta ce " kamar ya ? ni na shirya " a hankali Safna ta girgiza mata kai ta na fadin " fadi gaskiya , na san kin iya girki amma ba ki taba girka irin wannan abincin ba , asali ma ban taba ganin ki gyara fish ba , ko dai sayo wa ki ka yi ? " wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta ce " kin yi gaskiya , ina saurayin nan da mu ka taimaka a garden ranar nan ? " a hankali Safna ta gyada mata kai allamun ta gane shi " To shi ne ya zo ya girka mana , kuma da yay duk karfe 8 zai zo mu yi girki tare " dan tabe baki Safna ta yi ta na kai fork din da ta debo fish da potato a ciki ta kai baki sai da ta gama ta hadiye sannan ta kalli Esra ta ce " Yanzu saurayin nan ya yi wannan girkin ? " gyada mata kai Esra ta yi ta na fadin " ni kaina na yi mamakin yadda a ka yi ya iya girki haka , kuma wlh ko one hour bai yi ba " " gaskiya ya fi shirmen da ki ke girka mana " ta qarashe maganar ta na wata yar karamar dariya , kamar ba ita ba ce dunkule kamar an aiko mata mutuwa ita ma Esra wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mata " wannan karan zan yarda da ba ki yi karya ba , amma ai koya min zai yi nan gaba kadan sai na fi shi kwarewa " ita dai Safna ba ta ce mata komai ba ta na cin abincin kawai ba karamin dadi ya yi mata ba Esra na ganin ta yi shiru ta gane ta tafi , hakan ya sa ta ja bakin ta ta yi shiru ta ci gaba da cin abincin sai da su ka cinye komai har Apple pie din ba su rage ba sannan su ka tashi su ka gyara wajen Safna kuwa har ta dan ji karfin jikin ta bayan sun gyara table din su ka wanke plates din a tare sannan Esra ta dawo parlour ta zauna Safna kuma ta koma bedroom din ta , ciki ya cika sai barci _________________________________________ ▪AYDEN 🦋 💙 konce ya ke saman wata doguwar sofa fara kal , ya daura hannun shi guda saman cikin shi , gudan kuma saman idanun shi , wa ya sani ya na farke ko barci ya ke ya na a haka Adrian ya shigo parlourn da ga shi sai short da singlet fuskar shi da damuwa a kai ya nufi wajen kafafun Ayden ha na zauna murya a sanyaye ya ce " Ayden , ba ka ce komai ba dangane da paper din nan ba ? " shiru Ayden ya yi bai ce mishi komai amma ya na jin shi dan ba barci ya ke ba a hankali Adrian ya kai hannu ya buge shi a cinya ya na fadin " bro , da kai na ke magana please ka ce wani abu mana " wata boyayyar ajiyar zuciya Ayden ya sauke kafin ya ce " Please ka bar ni da abun da ke damu na " cike da kula Adrian ya ce " Oh my God , damuwa kuma ? wace irin damuwa kuma Ayden ? please tell me , mi ke damun ka ? " dan jinkirtawa Ayden ya yi kafin ya ce " Adrian , son yarinyar nan ya na neman ya min illa , ban san ya a ka yi na kamu da son ta ba , wai ko na haukace ne ban sani ba ? " wani kyawatencen murmushi Adrian ya yi kafin ya ce mishi " no , ba ka haukace ba , amma nan gaba za ka haukace in har ka ci gaba da rejecting abun da ke cikin zuciyar ka , ka san minene love at first sight , shi ne kawai ya kama ka , yanzu kuma sai ka yi kokarin ka bawa zuciyar ka abun da ta ke so " cikin zuciyar shi kuma ya ce " ko da ba ka yi kokarin bawa zuciyar ka abun da ta ke so ba ka tabbata ni sai na mallaka maka ita " shi dai Ayden bai ce mishi komai ba da allamun ya tafi duniyar tunanin shi wata yar karamar dariya Adrian ya yi ganin yadda abokin shi ya damu kawai saboda mace , abun da bai taba gani ba hannu ya kai ya bugi cinyar shi ya na fadin " yanzu tashi ka gyara mana wani abu mu ci dan ni yunwa na ke ji " wani dan karamin tsaki Ayden ya yi ya na fadin " ba ka san hanyar kitchen ba ? " " na sani amma ka san ni ban iya girki ba kamar kai , please tashi ka gyara min wani abu , tun safe ban ci komai ba , please bro " ya kai qarshen a sanyaye wani dogon tsaki Ayden ya ja kafin ya juya ya shige cikin sofar ya na fadin " in dai ni zan girka maka ka mutu da yunwa " hannu Adrian ya kai ya buge shi a baya kafin ya mike ya bar wajen da gudu kamar wani karamin yaro ko motsi Ayden bai yi ba amma ya na jin shi , kawai ba ya da karfin tashi ne ya na tunanin Esra , ya rasa yaya ya kamu da son ta lokaci guda haka , shi dai ya san lokacin da su ka yi karo ne ya taro ta kar ta fadi har su ka kalli juna cikin ido , a lokacin ne Cupid ya samu damar harba mishi kibiyar son ta a cikin zuciya , kuma ya saita dai-dai dan bai taba jin ya so abu kamar irin son da ya ke yi wa Esra ba a yanzu To ya za ta kasance Ayden fa ya kamu da son Esra har cikin zuciyar shi , ita kuma musulma ce , ya za ta kare ga kuma Kim a gefe dan ga dukkan allamu Esra ta fara kamawu da son shi yanzu dai bari mu ci gaba da labarin za mu ga in da ya dosa _______________________________________________ ▪AFTER ONE DAY ( MONDAY , misalin karfe 8 ) ▪ONE WORLD TRADE CENTER ▪ESRA ❤🔥 da sauri sauri ta shigo building din , dan yau da ga gani ta yi late ta na sanye da wata gown white color har kassa mai mugun kyau ta yi Rowling veil din black color , ta na rike da bag din ta , amma sam hankalin ta ba ya tare da ita ta na tsaka da tafiyar ta kawai ta ji ta bugi mutun har ta fadi kassa ta na sakin wata yar karamar kara nan take duk takardun hannun shi su ka zube a kassa wani dan karamin tsaki Ayden ya ja ya na kai hannu ya dafe kan shi da ke mugun sara mishi dalilin da ya sa ma bai zauna ba zai koma gida ya huta Esra kuwa ta na ganin kafafun shi cikin wasu bakaken sneakers ma su mugun kyau tsadadu ga kuma trouser din suit da ta gani nan take ta ji zuciyar ta ta buga dan a tunanin ta Kevin ne da sauri ta fara tattare takardun kamar ta yi kuka ta na fadin " i'm so so sorry sir " Ayden bai ce mata komai ba ya raba ta geffen ta ya wuce ya bar ta nan har da takardun tsab Esra ta gama tattare takardun ta na dago kai za ta mika mishi ta ga babu kowa a wajen da sauri ta kalli damar ta ta kalli hagun ta ba ta ga kowa ba ta na juyowa ta ga hannun mutum a gaban ta slowly ta dago kai ta ga Adrian ya na miko mata hannu da wani dan karamin murmushi a face din shi allamun zai taimaka mata ta tashi ita kuwa kawai sai ta daura mishi takardun ta na fadin " i'm sorry " bai ce mata komai ba ya meda takardun dayan hannun kafin ya sake mika mata hannu kallon hannun ta yi da kyau sai a lokacin ta tuno ashe a kassa ta ke slowly ta dago ta daura hannunta saman nashi , sannan ya taimaka mata ta mike tsaye ta na yi mishi godiya da murmushi a face din shi ya ce mata " Miss Esra , ya kamata ki dinga kallon gaban ki , sau biyu yanzu ki na yin karo da shi , please kar a yi na ukun " dan sunkuyar da kai ta yi ta na fadin " i'm so sorry , in sha Allah zan kiyaye , i'm sorry " " okay , sannan a rage wannan late , gobe akwai meeting din da mu ka shirya tare da duk ma'aikatan One world trade center , a cikin amphitheater ina fatan za ki kasance a lokaci " " in sha Allah Sir , zan kiyaye " ta fada a sanyaye wani dan karamin murmushi Adrian ya yi kafin ya raba ta geffen ta ya wuce ya bi bayan Ayden ya na jin ya fara takawa ta dago kai ta na sauke wata nanauyar ajiyar har da kai hannu saitin zuciyar ta ta dafe kafin ta ci gaba da tafiyar ta amma wannan karan cikin nitsuwa har ta isa office din ta duk abun nan da ha faru a kan idon Kevin dan ya na tsaye ya jiyo bayan Ayden amma kawai sai ya ga Esra ta kai mishi karo har ya taho zai yi mata magana Adrian ya tare shi bai san dalilin ba , amma ya yanke shawarar kawo karshen wannan shirmen na Esra tun ba ta shiga hanyar shi ba dan in ta shiga hanyar shi zai samu matsala babba [28/02 à 08:18] 🪷🩷: 💞 🔥 TRUE LOVE 🔥 💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 27 & 28 🕊❤} bangaran Esra kuwa kai tsaye Office din ta ta nufa , ta na shiga ta ajiye bag din ta ta fara aikin ta ko ten minutes ba ta yi ba da zama Cherry ta turo kofar office din ta shigo ta na sanye da wani mini skert pink color da shirt white color mai dogayen hannu da murmushi a face din ta ta karaso cikin office din ta na fadin " you're late Miss Esra " wani dan karamin murmushi Esra ta yi kafin ta ce " wlh , akwai in da na biya ne , but i'm here now " " okay , amma kin yi late sosai fa dan yau na fada miki abu guda ya hana mu haduwa da Ayden Brian " slowly Esra ta dago kai ta kalle ta ta ce mata " ban gane ? " " Ya dawo bakin aikin shi , but yanzu ya koma gida wai kan shi ke ciwo , amma an shirya Meeting gobe duk ma'aikatan wajen sai sun hallata , si kar ki zo late gobe " shiru dai Esra ta yi ba ta ce mata komai ba kamar mai tunanin wani abu ta na a haka kawai ta ga Cherry ta mike cikin sanyin murya Esra ta ce mata " ina kuma za ki je ? " " zan koma aiki na mana , tun da mai wajen ya zo dole mu kama jiki , see you later " ta qarashe maganar ta na nufar kofar fita ta fice da kallo Esra ta raka ta har sai da ta fita sannan ta saki wani cool murmushi ta sunkuyar da kai ta ci gaba da aikin ta ta share wajen good one hour a haka kafin ta ji an turo kofar office din ta wani dan karamin murmushi ta saki a tunanin ta Cherry ce ta dawo kawai sai ta ce " Ba kin ce za ki kama jiki ba ? me ya...... " ba ta kai karshen maganar ta ba sakamakon dago kan ta da ta yi ta ga Kevin tsaye bakin kofar office din ta Dum ta ji Zuciyar ta ta buga dan Kevin kamar tarmamuwa mai wutsiya ya ke , ganin shi a office din ta ta san ba al'heri ba ne a razane ta mike tsaye ta na dan zaro idanu ta ce " Good morning Sir , ku na..... " ba ta qarashe maganar ta ba ya daga mata hannu ya katse ta ya na fadin " ina jiran letter din barin ki aiki gobe a office di na , Miss Esra you're fired " ko amsar ta bai jira ba ya juya ya na taku cike da nitsuwa ya fice office din ko motsin kirki Esra ta kassa ta yi kawai ta tsaya ta kurawa kofar ido hawaye na zubo mata bibiyu , a hankali ta yi kassa ta zauna saman chair din ta na sakin kuka kamar wata karamar yarinya ta na fadin " yanzu tsakani da Allah ya zan yi ? ya sallame ni da ga aiki ? me na yi mishi zai sallame ni ? " ta ke fada ta na kukan ta ta na a haka kawai ta ga wani security ya turo kofar office din ya shigo fuska a daure tamau a hankali ya karaso tsakiyar office din ya riko hannayanshi a baya ya ce mata " Sir Kevin ya ce na raka ki waje , please don't waste my time let's go ! " ya fada ya na nuna mata kofar office din ba musu ta tashi ta rufe laptop din ta ta saka cikin jakar ta sannan ta dauki handkerchief ta goge face din ta sannan ta fara takawa jiki a mace ta nufi kofar office din amma kafin ta fice sai da ta juyo ta kalli office din nata kallo na karshe sannan ta fita ta na hawaye Security din nan na biye da bayan ta kai tsaye Lift ta nufa ta shiga ta baro building din baki daya , sai da security din nan ya rakata wajen building din sannan ya koma cikin building a hankali ta ke tafiya idanun ta cike da hawaye ta na kuka kassa kassa , yanzu ya za ta yi ? aikin nan shi kadai ne ya zaunar da ita US , in har a cen gidan su su ka ji labarin ta rasa aikin ta , da kan shi mahaifin ta zai zo US ya meda ta Nigeria yanzu ya za ta yi , ita kuma gaskiya ba ta jin za ta iya komawa Nigeria bayan ta sama sosai US tsawan shekaru biyar yanzu , dan a nan ta yi karatun ta har a ka dauke ta aiki a one world trade Center gaskiya Kevin bai kyauta mata ba ba ta ji ba ba ta gani ba ya raba ta da aikin ta kawai saboda son zuciya irin nashi ta yi nisa cikin tafiyar ta kawai ta jiyo Muryar Kim a bayan ta ya na fadin " Miss chocolate , Miss Chocolate " ta na jin shi amma ba ta tsaya ba dan yanzu zuciyarta sam ba ta yi mata dadi ta na a haka kawai ta ji ya kwace mata bag din ta ta baya yanzu ma ba ta ce mishi komai ba ta ci gaba da tafiyar ta a sanyaye a hankali ya matso geffen ta su ka jera ya na fara duba abun da ke cikin bag din ta ya na fadin " Miss Chocolate , yau kuma da wuri ki ka sauko ? yau ba monday ba ? " shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba amma ta na jin shi sai da ya gama lalube bag din ta sannan ya dago kai ya kalle ta nan ya ga ruwan hawayen da ta ke yi a dan razane ya ce " la , Miss Chocolate , lafiya ki ke kuka ? ko dan na karbi jakar ki ne ? ki yi hakuri ba dauka kin sayo min chocolate ne , I'm sorry ki daina kukan nan ni ba na son ganin mutum na kuka , ni ma kuka ya ke saka ni " ya na gama rufe bakin shi ko ta saki kukan kassa kassa ta datse idanunta cak ya tsaya ya riko hannunta ya juyo ta su na fuskantar juna ya na kallon yadda ta ke kuka ido a rufe hawaye na zubo mata bibiyu duk da babu wani abu a tsakanin su amma gaskiya ba ya jin dadin ganin ta ta na wannan kukan , ko dan chocolate din da ta ke saya mishi ya kamata ya yi wani abu cikin sanyin murya ya ce mata " Miss chocolate , please stop crying , ki fada min kukan me ki ke ? wani ya ci zarafin ki ? ki fada min zan je na rama miki " a hankali ta girgiza mishi kai ba tare da ta bude idanun ta ba " to minene ki na kuka ? ko ciwo ki ke ? " a hankali ta girgiza mishi kai ba tare da ta bude idanunta ba ta ce " sun sallame ni da ga wajen aikina , ban yi mishi komai ba kawai ya ce gobe na kai mishi letter din barin aiki na wai ya kore ni " ta kai karshen ta na kara sautin kukan ta cikin ko in kula Kim ya ce mata " to sai me , ki kai mishi letter din , ya je ya rike aikin shi in ya na so ya cinye shi ba " a dubu dari ta ware idanunta ta na kallon shi ta ce " ka na jin abun da ka ke fada kuwa ? tun da ba ni da aiki hakan na nufin babu kudin da dinga saya maka chocolate , in kuma gidan mu su ka ji labarin na rasa aiki na ce min za su yi na koma ni kuma gaskiya ba na jin zan iya komawa gida " ta kai karshen ta na sakin kuka shiru ya yi ya na kallon ta , jin ta ce babu kudin sayan chocolate , a hankali shi ma ya fara kuka kassa kassa kamar wani karamin yaro ai ba shiri Esra ta yi shiru jin sautin kukan shi sai da ta nemi kukan nata ta rasa a rude ta ce mishi " Kim , lafiya ka ke kuka ? " " yanzu wa zai saya min Chocolate ? ni gaskiya ban yarda ba " ya fada ya na kuka Wata yar karamar dariya ta yi ta na kallon shi yadda ya ke kuka kamar wani karamin yaro har da lumshe idanunshi ya na jin ta yi dariya ya bude idon shi guda ya ga Eh da gaske dariyar ta ke a hankali ya bude idanun shi ya yi shiru ya na fadin " tun da kin yi shiru yanzu mu je park " dama ba kukan ne ya ke ba kawai dan ya sa ta dariya ne ya yi hakan " park kuma ? " ta fada ta na kai hannu ta goge hawayenta gyada mata kai ya yi kafin ya fara takawa ya yi gaba , a hankali ta juya ta bi bayan shi su ka fara takawa a tare ▪PROSPECT PARK 🌲🌲🌲 park din cike ya ke da mutane specially couples kowane ya na sha-anin gaban shi , sai wassa su ke su na dariya , ga wajen da mugun girma cike da ciyayi da itace , ga kukan tsintsaye da ke tashi , abun dai gwanin burgewa tun da su ka shigo wajen Esra ke jin zuciyarta ta yi mata sauki , saboda yanayin wajen , Kim na ganin ta fara sakin face din ta , ya sauke wata yar karamar ajiyar zuciya a hankali ya riko hannunta ya ja ta da gudu a razane ta saki wata yar karamar kara ta bi bayan shi su na gudun ta na fadin " Lafiya ? me ya faru ka ke gudu ? " ba tare da ya tsaya ba ya ce mata " wani abu zan gwada miki " ba ta ce mishi komai ba ta bi bayan shi su na gudun ta na wata yar karamar dariya , a haka har su ka karaso tsakiyar park din wajen katuwar fountain ta na zubar da ruwa gwanin burgewa su na isowa wajen ya saki hannunta ya tsaya ya na kallon fountain din a hankali ita ma ta tsaya ta na haki , ta na kallon fountain din ta ce mishi " Kim , wai me mu ke yi a nan ? " bai ce mata komai ya ajiye bag din ta bakin fountain din , ya kai hannu ya tattare kafafun wandon shi har zuwa guyiwa nan ta ga farare kafafun shi cike da gashi baki kirin ya konta mishi luf gwanin burgewa ya cire sneakers din shi sannan ya shiga cikin fountain din kamar wani karamin yaro ya fara watsa ruwan da kafafun shi wata yar karamar dariya Esra ta yi kafin ta fidda flat shoes din ta , ta shiga cikin fountain din ita ma ta sa sannu ta watsa mishi ruwa da sauri shi ma ya sa kafa ya watsa mata ruwan a fuska wata yar karamar dariya ta yi kawai ta biye mishi su ka shiga wassa kamar wasu kananan yara su cikin wannan yanayin mai dadi su ka jiyo Muryar wani security ya na fadin " kai , ba a shiga cikin ruwan nan , maza ku fita ! " ya fada da dan karfi a tare Esra da Kim da su ka zaro idanu su na kallon juna kafin su juya a hankali su ka kalli saitin da su ka jiyo Muryar security din nan su ka ga ya na takowa ya nufo su fuska a daure kawai sai ganin ta Yi Security din ya tsaya ya na kallon Kim , ya na dan zaro idanu da sauri Kim ya riko hannunta ya na fadin " Run , Run , Run ! " ya fada su na fitowa da ga cikin fountain din da sauri ya dauki sneakers din shi da takalmin ta da bag din ta da hannu guda dukka ya na rike nata hannun da gudan su ka fara gud da sauri su ka bar wajen Esra kuwa sai dariya ta ke Security na ganin sun bar wajen da gudu ya juya a hankali ya koma bakin aikin shi sai da su ka yi nisa sosai da Fountain din sannan Ya tsaya ya saki hannunta ya zube a kassa ya na haki ya saki kayan hannun shi ita ma zaunawa ta yi a kassa ta na sauke nunfashi sama sama ta na dariya ta na kallon shi sai da nunfashin shi ya dawo dai'dai sannan ya dauki sneakers din shi ya saka sannan ya mika mata shoes din ta ya na fadin " tashi mu bar wajen nan tun kafin ya kamo mu " ba musu ta karbi takalmin ta ta saka sannan ta mike tsaye a hankali shi ma ya mike tsaye ya na rike da bag din ta ya fara takawa cak ya ji an riko hannun shi a hankali ya juya ya na kallon ta sai sakin murmushi ta ke cikin sanyin murya ta ce mishi " na gode , bayan kai babu wanda ya taba saka ni annashuwa haka " slowly ya juyo ya riko hannunta da kyau cikin nashi ya saki wani cool murmushi ya ce mata " ni ma na gode , rabon da na saka mutum cikin farin ciki har na manta , na san ni da ke ba mu dace ba , kuma na san babu wata alaka tsakanin mu amma duk lokacin da na ke tare da ke ina rage kewa sosai , na gode ko ba komai kin saka ni cikin farincikin da na jima ban ji kaina a ciki ba " wani kyawatencen murmushi ta saki ta na fadin " it means we're friend's now ? " murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " kin yi kokari , amma har yanzu ba ki ci makin zama friend's di ta ba , amma ki ci gaba kin kusa yin nassara " ya na gama fadar haka ya juya ya fara takawa ya na rike da hannunta ba musu ta bi bayan shi ta na murmushi cikin zuciyar ta ta na fadin " za ka gani , in sha Allah sai ka bude baki ka roke ni na zama abokiyar ka " a hankali su ke tafiyar su cikin park din kamar wasu masoya a haka su ka fara hango wasu samari guda uku zaune saman wani bancin , biyu na rike guitar dayan kuma ya na rike da saxophone su na kidan su cikin konciyar hankali , kuma gaskiya sun iya [28/02 à 08:19] 🪷🩷: 💞 🔥 TRUE LOVE 🔥 💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMENTS SECTION https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 29 & 30 💙💦} a hankali ya juya ya ce mata " mu tafi ko gani " ba musu ta bi bayan shi su ka iso wajen musician din nan , su ka tsaya kawai su na kallon su haka su ma samarin ba su daina kidin nasu ba , har sai da su ka kammala su na kammala wa ko Kim ya shiga yi musu tapi , da sauri ita ma Esra ta shiga yi musu tapi ta na wata yar karamar dariya da ga haka Kim ya ba su hannu daya bayan daya su ka gaisa sannan Kim ya ce musu " gaskiya , song don nan ya yi min dadi sosai " a tare su uku su ka yi dariya kafin su yi mishi godiya " please , ko za ka ara min guitar din ka ? ina so na gwada ni ma " " why not " wanda ke rike da guitar guda ya fada ya na mika mishi guitar din hannun shi wani kyawatencen murmushi ya saki kafin ya kai hannu ya karbi guitar din , sannan ya zauna geffen shi da sauri Esra ta ce mishi " Kim , ka ga ka ba shi abun shi , yaushe ka iya wassan guitar ? " bai ce mata komai ba ya fara buga guitar din sai da ta dan zaro idanu jin yadda ya ke buga ta cike da kwarewa , har su kan su musician din sai da kidin ya burge su shi kuma sai ya dan yi nisa da kidin sannan ya bude baki cike da nitsuwa ya fara rera waka ya na fadin " LOOKING ME LIKE I'M CRAZY , WHEN I SHOT MY FEELINGS OUT LOOKING ME LIKE I'M DIFFERENT , STILL YOU STAY CAUSE YOU FEEL SOMETHING REAL IT'S SO LOST IN MY MOMENT , DOESN'T MEAN I DON'T NEED YOU , I , I........ FELL IN LOVE WITH THE COLORS , THEY KINDA TELL ME WHAT I'M THINKING FELL IN LOVE WITH THE WAY WE ARE , AND THE WAY WE LOSE IT SOMETHING DIFFERENT ABOUT US , AND THE REASON WHY WE STAY , STAY...... WE FLY AROUND LIKE PAPER PLANES THEY NEVER KNOW WHERE WE WILL FALL NOBODY CAN SEE US STILL THEY WANNA TEAR US APART , THERE'S SOMETHING DIFFERENT ABOUT THE WAY WE ARE , ARE , ARE......... OOHHHHHH , OOH , OOH......... THERE'S SOMETHING DIFFERENT ABOUT US OOHHHH , OOH , OOHHH........ THERE'S SOMETHING DIFFERENT ABOUT US " Ita dai Esra ta tsaya cak ta na kallon shi , ta na sauraron zazzakar Muryar shi ya na wakar shi cike da nitsuwa ba ita ba har su musician din sai da ya burge su slowly ya daina kidan bayan ya gama rera wakar shi , har ya daina kafin ya dago kai slowly , idanun shi ba su sauka ko ina ba sai cikin na Esra ta na ganin ya tsaya ta saki wani cool murmushi ta na yi mishi tapi a tare su ma samarin nan uku su ka shiga yi mishi tapi kafin wanda ya ba shi guitar din ya ce " guy , wakar nan ta hadu gaskiya " wani dan karamin murmushi Kim ya yi kafin ya mika mishi guitar din shi ya na fadin " na gode " a hankali ya kai hannu ya karba , mikewa tsaye Kim ya yi kafin ya koma geffen Esra ya tsaya ya riko hannunta , ya na kallon musician din nan ya ce musu " mun gode sosai " wanda ke rike da Saxophone din ne ya amsa mishi da cewa " ba komai , we are HAPPY to see mun saka couple din ku farin ciki " dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon shi jin ya ce wai couple har ya bude baki zai yi magana Esra ta riga shi cewa " Thanks a lot " ta na gama fadar haka ta juya ta kalli Kim ta ce mishi " let's go now " ba musu ya bi bayan ta su ka bar wajen ya na tunanin abun da saurayin nan ya ce wai couple , yanzu a haka sun yi kama da couple ? shi ko bai san tun lokacin da su ka shigo park din kowa kallon couple ya ke yi musu musaman hannun ta da ya ke rike da sai da su ka yi dan nisa sannan ta ce mishi " Kim , babu toilet a cikin park din nan ? " ba tare da ya juyo ba ya ce mata " akwai , ki na son shiga ne ? " " Eh " ta fada a takaice bai ce mata komai ba su ka ci gaba da takawa har su ka karaso wajen toilet sai da su ka iso sannan ya saki hannunta ya na nuna mata kofar wata toilet ya ce " cen ne toilet din Mata " okay kawai ta fada mishi kafin ta taka ta shiga toilet din ya na ganin ta shiga ya juya ya nufi wata katuwar bishiya da ya hango ta na fuskantar toilets din , ya jingina bayan shi jikin bishiyar ya lumshe idanunshi , ya tafi duniyar tunanin shi ya na a haka ya jiyo Muryar Esra ta na fadin " Kim , na ga jakata please " slowly ya bude idanun shi kafin ya juyo ya kalle ta ya mika mata bag din hannu ta kai ta karba ta na yi mishi godiya , bai ce mata komai ya juya ya lumshe idanunshi hannu ta kai cikin bag din ta fiddo wata yar karamar leda , sannan ta ajiye bag din gaban ta bude ledar ta yi ta fiddo wata ledar amma kamar sallaya ta ke a hankali ta daga kai ta kalli sama , kafin ta juya ta shinfida Sallayar , ta na fuskantar gabas , ta haye sama ta juyawa Kim baya sannan ta kai hannu ta warware veil din ta , nan take jelar gashin ta , ta warware ta zubo mata har tsakiyar baya slowly Kim ya bude idanun shi wai ya ga me ta ke yi , nan idanun shi su ka sauko saman gadon bayan ta da jelar gashin ta ita kuma bude veil din ta ta yi nan ga ashe babba ne sosai kawai ta na ninke shi ne meda ta yi ta yi Rowling din shi a kai , ya zubo mata har wajen guiwa cikin nitsuwa ta tada sallar ta shi dai Kim ya tsaya ya tsare ta da ido ya na kallon yadda ta ke sallar sai da ta yi sujada ta farko sannan ya ce mata " minene ki ke yi haka ? " kawai sai ya ga ko juyowa ba ta yi bare ta amsa mishi , hakan ya sa ya ja bakin shi ya yi shiru , ya zauna a kassan bishiyar ya na kallon ta kawai sai ya ji wani bakon yanayi cikin zuciyarshi , ya ji wata nitsuwa ta shigo lokaci guda ita kuma cikin nitsuwa ta yi sallar ta , bayan ta gama ta zauna ta na addu'o'in ta ta shafa kafin ta juyo a hankali ta shafa mishi shi ma ya na ganin haka ya ce mata " wai me ki ke yi tun dazu na miki magana kin kyale ni " wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Sallat ce na yi " cikin rudu ya ce " Sallat ? minene sallat ? " " ta na daya da ga cikin kinshigin addini na , sallat ita ce abu me mahimanci ciki addinina , ta ita ce kawai a ke iya gane musulmi " " kamar dai irin sallar da a ke yi church ? " girgiza mishi kai ta yi a hankali ta na fadin " a'a , ka na dai gani yadda na yi yanzu , haka nan su ke yi a church ? " slowly ya girgiza mata kai allamun a'a sai da ta saki murmushi sannan ta ce " to ka gani , ka ga ko na fada maka ba ganewa za ka yi ba dan haka tashi mu tafi " cikin nitsuwa ya ce mata " wata rana za ki fada min ? dan ina son na san yadda addininki ya ke " wani kyawatencen murmushi ta saki abun da ta ke so ya samu , cikin sanyin murya ta ce mishi " yau daddare idan ka je , zan yi maka bayani " okay kawai ya fada mata kafin ya mike tsaye , ya na fadin su tashi su koma gida ba musu ta tashi ta nade sallayar ta , su ka bar wajen a tare su ka baro park din sai da ya raka ta har building din su , sannan su ka yi sallama , shi ya juya ya bar wajen ita kuma ta shiga ciki , da allamun ta mance da sallamar ta da kevin ya yi ko da ta koma apartment din su bayan ta ajiye bag din ta , kai tsaye toilet ta wuce ta yi wanka , ta fito ta shirya cikin kananan kaya kawai ta haye gado ko two minutes ba ta yi ba barci ya yi gaba da ita _________________________________________________________ ▪BROOKLYN ▪DISTRICT OF WILLIAMSBURG A zaune duk mutanan gidan su ke a saman dining table su na cin abincin su cikin konciyar hankali , amma Ayden ya na zaune ya na rike da wata jarida ya na karantawa , ya rufe fuskar shi da ita ba na iya ganin komai sai hannayan shi da ke rike da jaridar cen sai Brian ya ce mishi " Ayden , ka ajiye jaridar nan ka ci abincinka tun bai yi sanyi ba " ya fada cike da kula ba tare da ya ajiye jaridar ba Ayden ya ce mishi " i'm full Dad , mun biya restaurant ni da Adrian kafin ya sauke ni " " okay , " Brian ta fada a takaice kafin ya juya ya ci gaba da cin abincin shi su na a haka su ka jiyo Muryar Ayden ya na fadin " Kevin , na ji an ce ka sallami wata da ga cikin ma-aikatan mu na one world trade center " ba tare da ya kalle shi ba Kevin ya ce mishi " Yes , haka ne " " zan iya sannin dalilin ka na sallamar ta ? ko wani laifi ta yi maka ? " cikin ko in kula Kevin ya ce mishi " no , kawai na gaji da aikin ta ne , kullum late ta ke zuwa shi ya sa na sauwake mata aikin " dan jinkirtawa Ayden ya yi kafin ya ce " dan ta na zuwa late kawai sai ka sallame ta , ba ka san abun da ke tsayar da ita ba , kuma ai ni ban ba ka izinin sallamar ta ba " shiru Kevin ya yi bai ce mishi komai ba ko dago kai ma bai yi ba ya na cin abincin shi a hankali Ayden ya mike tsaye ya na rike da jaridar ya ce " next time idan za ka sallami wani ma-aikacin ka fara ba ni hujjojin sallamar tashi kafin ka sallame shi , ba zan lamunci ka na sallamar ma-aikatana ba haka kawai babu dalili , kar ka manta kai ma zan iya sallamar ka idan har na ga dama " ya na gama fadar haka ya juya ya nufi stair ya haye gaskiya maganar shi ta yi matukar sosawa Kevin rai , sai da ya ji ya fara takawa sannan ya dago kai a hankali ya bi shi da kallo har sai da ya haye stair sannan ya kai hannu ya dauki glass din ruwan geffen shi ya juya ya tilla shi a glass din bayan shi ya na huci kamar zaki cikin sanyin murya Brian ya ce mishi " Kevin , ai ba karya ya yi ba , why za ka dinga sallamar ma su yi mishi aiki ? at least ka fara sanar mishi , ka yanzu ya karbi kayan shi , zan so ka hakura ka bar mishi ya kula da abu ne " Cikin bacin rai Kevin ya juyo ya wurga ma Brian wani mugun kallo kamar ba shi ne mahaifin shi ba " dama na sani ka fi son shi fiye da mu , mu ne fa yaran ka ba shi " Kevin ya fadawa Brian da sauri Emilie ta ce mishi " Kevin , wannan zancen bai tasso ba na Daddy ya fi son shi fiye da mu , na sani tun ya na karami ka ke mugun kishin shi har zuwa yanzu , please ka danne zuciyarka , tsawan shekaru 20 ya na tare da mu amma har yanzu ka kassa kabar shi a matsayin dan uwanka " ta karashe maganar cikin dan rauni wata boyayyar ajiyar zuciya Kevin ya sauke kafin ya ce mata " ranar da ya bar duniyar nan a ranar zan karbe shi a matsayin dan uwana " ya na gama fadar haka ya mike ya nufi stair ya haye da kallo Brian da Emilie su ka raka shi har sai da ya Haye sannan Emilie ta kalli Brian , ta na marairaice fuska ta ce " Daddy , why Kevin ba ya son Ayden ? brother din mu ne fa , amma duk duniya shi ya tsana " " na sani Emilie , Ba ba ya son shi ba ne kawai hanyar da ya shigo ahalin mu ne ba ya so , tabbas na san abun da momyn ki ta yi bai dace ba , kuma har yanzu ina jin zafin hakan , amma ba laifin Ayden ba ne abun da ta yi , shi kan shi na san ba zai so ya shigo duniya ta hanyar cin amana , amma babu yadda mu ka iya " " yanzu kennan Daddy kai ma ba ka son Ayden ? " ta fada idanun ta na cikowa da ruwa wani dan karamin murmushin geffen fuska ya sakin mata kafin ya kai hannun saman face din , murya a sanyaye ya ce mata " ko kusa , yadda na ke son ku haka na ke son shi har cikin zuciyata " wani dan karamin murmushi Emilie ta sakin mishi ba tare da ta ce komai ba su na a haka Ayden ya fara sauko stair , ya na sanye da wasu Tracksuit purple , da sneakers farare , ya saka wata face mask white ita ma , da wata coat black color sam ba na iya ganin face din shi bai bi ta kan su ba ya nufi kofar fita gidan ya fice abun shi [28/02 à 10:12] 🪷🩷: 💞 🔥 TRUE LOVE 🔥 💞 __________________ 💞 SOYAYYAR GASKIYA 💞 ( A HEART TOUCHING LOVE STORY ) STORY & WRITING BY : MEERAH 💋 GA DUK ME BUKATAR YIN MAGANA DA NI KAI TSAYE ZAI IYA TABO NI TA WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL 👇👇👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i ربي أزح الألم الذي يعتصر قلبي! حرر لساني وخلصه من كل غموض، حتى يفهم الناس ما أقول! BISMILLAHIRRAHMANIRAHIM {P A G E 31 & 32 💫💛} da kallo Emilie da Brian su ka raka shi har sai da ya fice sannan Brain ya yi wata yar karamar dariya ya ce " ke dai wannan dan uwan naki ya na son face mask " ita ma dariya ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba 💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛💫💛 ▪ESRA ❤🌼 zaune ta ke cikin parlourn apartment din su , ta yi zugum waje guda ta na tunanin yanzu ya za ta yi tunda ba ta da aiki ta ya za ta ci gaba da zama a New York , ba za ta iya daurawa Safna nauyin ta ba , in ba ta koma Nigeria ba , to dole ta nemi aiki ko da na server ne ta na cikin duniyar tunaninta ta ji a na yi musu knocking a hankali ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya kafin ta mike jiki a sanyaye ta nufi kofar ko tambaya ba ta yi ba kawai ta bude kofar ta na budewa idanunta su ka sauka saman Kim tsaye bakin kofar sanye da wani wandon jeans dai'dai guyiwa white color da wata shirt white , gashin nan nashi a gyare yau ya yi wani smooth a konce gefe guda ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta na shirin magana ta jito wayar ta ta na ringing a hankali ta juya ta na fadin " bismillah , come in " ba musu ya shigo ya meda kofar ya rufe Esra kuma ta nufi wayar ta ta dauka ta na kallon Screen din wayar ta ga sabuwar number ce kuma ta New York ce cikin rudu ta dago ta kalli Kim da ke tsaye ya na kallon ta kamar shi ne ya kira ta a hankali ta dawo da kallon kan wayar kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ba tare da ta ce komai ba kawai sai ya jiyo Muryar Adrian ya na fadin " please ina son magana da Miss Esra Yahaya " " ita ce " ta fada a sanyaye murya cike da tsoro cike da fara'a ta jiyo Muryar Adrian na ce mata " Good , Miss Esra my name is Adrian Manager of Ayden Brian , PDG of ONE WORLD TRADE CENTER , na san dazu da safe sir Kevin ya je ya ce miki ya sallame ki haka ne ? " a hankali ta zauna saman sofar kamar za ta yi kuka ta ce " Eh haka ne , please sir ku yi hakuri , in sha Allah zan gyara ko ma minene matsa...... " da sauri Adrian ya katse ta da cewa " I'm sorry Miss Esra Sir Kevin bai isar da sakon ba yadda ya dace , ba sallamar ki a ka yi ba , Sir Ayden ne ya ba ki promotion na zama P.A din shi " cikin rudu ta ce " P.A ? " " Yeah P.A , hakan na nufin za ki samu karin Albashi , sannan kuma promotion din ta na tare da gida da mota duk na P.A din shi , in har kin amince ki zo company karfe 7 da rabi dai'dai dan sa hannu a cikin sabon contract din , da ga nan ki fara aikin ki , Hope za ki zo , Na gode " ya na gama fadar haka ya katse kiran slowly Esra ta sauko da wayar ta na kurawa gaban ta kallon ta kassa wani motsi ganin ba ta ce komai ba ya sa Kim matsowa ya na fadin " Miss Chocolate , what happened ? " ya na rufe bakin shi ya ji ta saki wata yar karamar kara ta tashi da sauri ta na tsale ta na kara kamar wata yar karamar yarinya dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon ta cike da rudu ya ke fadin " Miss Chocolate are you okay ? what happened ? " ba ta ba shi amsar tambayar shi kawai ta nufe shi ta riko hannayanshi ta fara jujuwa da shi ta na dariya shi dai kawai ya biye mata sai tambayar ta ya ke amma ta ki amsa mishi kawai ya ja bakin shi ya yi shiru sai da ta gama juyin nata sannan ta shiga yi wa Allah godiya ta na karanto addu'a ta na shafawa kafin ta kalli Kim ta ce " ka san wani abu ? " " ta ya zan sani bayan tun dazu ina tambayar ki kin kyale ki ne " ya kai karshen ya na kauda kai wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " i'm sorry , farin ciki ne ya hana na ji ka , yanzu Manager din shugaban companyn mu ya kira ni , ya ce an ba ni promotion din zama P.A din Shugaban mu , hakan na nufin za su min karin Albashi " dan zaro idanu Kim ya yi ya na kallon ta baki sake ya ce mata " P.A fa ? " da sauri ta gyada mishi kai ta na murmushi ta ce " hakan na nufin za mu samu kudin sayan Chocolate ko yaushe , kuma har gida su ka ba ni da Mota " shiru ya yi bai ce mata komai ba , ya ma rasa me zai ce mata ganin bai ce komai ba kawai sai ta daina murmushin , a sanyaye ta ce mishi " Kim , da allamun ba ka ji dadin abun da na fada maka " wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yi wani dan karamin murmushin geffen fuska ya ce " Ta ya za ki ban ji dadi ba ? ni da za a dinga saya ma chocolate kullum , congratulations I'm really happy for you " ya qarashe maganar ya na mika mata hannu ba musu ta riko hannunshi su ka gaisa ta na sakin wani kyawatencen murmushi da ga haka ta ce mishi " okay , yau me za mu girka kuma ? " dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " ina ga kamata ya yi mu fita mu yi celebrated wannan news , ko ya ki ka gani ? " ya kai karshen ya na daga mata gera guda da sauri ta nufi Corridor ta na fadin " give me ten minutes yanzu na dawo " da kallo ya rakata har sai da ta shiga sannan ya nufi sofa ya zauna ya na jiran ta sai da ya yi ten minutes cib ko zaune a haka kafin ya jiyo wani dadaden qamshi ya fara tashi cikin parlourn har wani dan lumshe idanu ya yi dan bai taba jin qamshi mai dadi irin wannan ba slowly ya juyo da kallon shi saitin corridor nan ya gan ta ta na tafiya a hankali cike da nitsuwa , ta na sanye da wata Abaya navy blue mai mugun kyau , ta sha ruwan stone launin gold ma su mugun kyau , ta gyara gashin ta , ya zubo mata har saman shoulder ta yafa veil din abayar white color ta na rike da wata yar karamar bag a hannunta , fuskar ta cike da annashuwa tun da ta fito ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , wannan shi ne first time da ya gan ta cikin Abaya kuma gaskiya ta yi mugun kamata a haka har ta karaso gaban shi ta na yi mishi magana amma sam bai ji ta ba tuni ya tafi duniyar shi murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta kai hannun ta saitin face din shi ta kyasta mishi yatsu a dan razane ya dawo cikin hayacinsa ya na fadin " me ya faru ? " cikin zolaya ta ce mishi " irin wannan kallon haka ai sai ka saka min evil eye " bai ce mata komai ba ya mike tsaye ya na fadin " i'm sorry , ban taba ganin ki ba ne cikin irin wannan kayan " daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " sun yi min kyau ? " slowly ya gyada mata kai allamun Eh wata yar karamar dariya ta yi kafin ta yi mishi godiya ta na fadin " yanzu ina za mu je ? " a takaice ya ce mata " shan ice cream , amma ke a ki biya " ba ta ce mishi komai ba ta kai hannu ta dauki wayar ta , ta bude bag din ta ta saka kafin ta juya ta fara takawa ta na fadin " let's go ! " ba musu ya bi bayanta su ka fito , kai tsaye building din su ka baro , su na tafe ta na zuba mishi hira , shi dai kawai ya na kallon ta ya na jin abun da ta ke fada mishi , yau bakin nata ya ki rufuwa kamar parrot a haka har su ka karaso chop din , su ka sayi ice cream din , ta sayowa Safna ita ma , amma dan jaraba shi Kim biyu ya ce ya na so daya ta chocolate daya kuma vanilla babu yadda Esra ta iya haka ta saya mishi biyun , ta biya kudin kafin su juya su nufi hanyar gida tafiyar su ke yi su na shan ice cream din su har su ka iso greenwich street ba tare da ta lura ba , shi kuma a ganin shi ta nan zai fi sauri su koma gida ne shi ya sa ya biyo ta nan hanyar babu kowa , ko lamps ma daya daya ne ke kunne , kamar an yi busa a wajen su na tsaka da tafiyar su kawai su ka ga wasu samari uku sun sha gaban su , da ga ganin su ka San ba mutanan kirki ba ne , har wani warin taba su ke yi dum Esra ta ji zuciyarta ta buga har ta saki bowl din ice cream din ta ba shiri , da sauri ta yi bayan Kim ta buya cikin nitsuwa Kim ya ce musu " Guys , what are you doing here ? " wanda ke tsakiya ne ya ce mishi " ni ke tambaya a nan , where is my money ? ka ce min two weeks , yau har one month shi ne ka sauya wajen zama dan kar na kama ka , yau sai ka ban kudi na " cikin sigar rarrashi Kim ya ce mishi " I'm sorry Pablo , i don't have money now , ka ba ni one week wlh zan kai maka kudin ka har gida " ko sannu Pablo bai ce mishi ba ya juya ya kalli saurayin da ke daman shi , da kai ya yi mishi allamun ya caje shi ba musu ya karaso ya kai hannu ya fara caje Kim da sauri Esra ta dan ja da baya ta na sakin kara da sauri Kim ya juya ce mata " please calm down " kafin ya juya ya kalli Pablo ya ce mishi " please , ka ba ni one week zan ba ka kudin ka " ya na gama fadar haka kawai ya ji saurayin nan ya kai hannu saman dick din shi a dubu dari Kim ya sa hannu ya ture shi ya na dan zaro idanu kallon Pablo saurayin nan ya yi ya na fadin " Boss , babu ko sisin kwabo a tare da shi " cike da bacin Pablo ya kai dunkule hannu ya kai wa Kim bugu a face har sai da Kim ya dan rinsina kamar zai fadi amma ya dago ya na dan ja da baya ya ce " please Pablo , i promise zan biya ka kudin ka , ka ban one week , in na wuce ka kashe ni in ka na so " ko sannu Pablo bai ce mishi ba ya kai hannu ya damko kwalar rigar shi , ya daga hannu a dunkule zai sake kai mishi wani bugun da sauri Esra ta shiga tsakiyar su ta datse idanun ta da karfi ta na jiran saukar naushin a face din ta Pablo na ganin ta ya tsaya Cak , wani makirin murmushi ya saki ya na kallon ta Kim na ganin irin kallon da ya ke yi wa Esra ya san ba al'heri ba ne , da sauri ya sa hannu ya buge hannun da ya rike kwalar shi da shi , ya riko hannun Esra ya meda ta bayan shi ya na kallon Pablo cikin ido Wani dan karamin murmushi Pablo ya saki kafin ya ce " ai ga kudina nan a bayan ka , ka ban ita kawai mu tafi " Dum Esra ta ji gaban ta ya fadi , nan take idanunta su ka ciko da ruwa , kawai sai kara kankame Kim ta yi ta baya ta na girgiza kanta a hankali a sanyaye Kim ya ce mishi " No Pablo , please and please na ce zan biya ka kudin ka " murya kassa kassa Esra ta ce mishi " nawa ne kudin zan biya shi " murya kassa kassa shi ma ya ce " ki na ji ? zan kirga zuwa uku , ki juya ki bar wajen nan da gudu " da sauri ta ce mishi " No , ba zan iya tafiya na barka ba , ka fada m....... " ba ta kai karshen maganar ta ba Pablo ya katse ta da cewa " kai , wai maganar me ku ke yi kassa kassa haka ? " Kim bai amsa mishi tambayar shi ba kawai ya shiga girkawa da ga uku , a rube su Pablo su ka tsaya su na kallon shi sai da ya ida girkon shi kawai ya ji Esra ba ta motsa ba , cikin rada ya ce mata " ki bar wajen nan na ce miki ! " ya na gama rufe bakinshi ta sake shi ta juya ta kwassa da gudu Pablo na ganin ta fara gudu ya dan zaro idanu kafin ya kwassa da gudu shi ma ya yi bayan ta da sauri Kim ya bi bayan shi ya na fadin " No Pablo , please ka kyale ta ! " ya na haka kawai ya ji an riko hannayanshi ta baya an tsayar da shi dai'dai lokacin da Pablo ya cin ma Esra ya damko ta ta kugu wata razananiyar kara ta saki ta na neman kwatar kan ta har sai da ta saki bag din hannun ta [28/02 à 10:22] 🪷🩷: Assalamu alaykum Barkanmu da warhaka yakk Allah ya sadamu da alkhairin dake cikin wannan ranar Ta Juma'a yamana kariya daga dukkan sharri 😊😊😊 In sha Allah gobe za mu shiga watan Azumi mai Albarka 😊 zan so na nemi gafarar baki daya , wanda na batawa ba tare da sani na ba ku yahe min 😊 yau dai kun gani har pages 3 na yi posting 😂 na bankwana ne , da ga yau zan tsayar da posting sai bayan sallat , 😂 da ga nan kuma sai dai na ce mu hadu a paid group d'ina , 🥱🥱🥱🥱 da farko na saka kudin littafin a kan 500 ne , so saboda abun da ke faruwa kwana biyun nan na ce zan sauko da shi kan 400 ko kuma 300 har yanzu ban yanke shawara ba 🥱🥱🥱 😂😂😂😂 sai mun hadu a paid group din , ni da ga nan na yi tafiyata amma in sha Allah bayan sallat zan fara posting din Free book d'ina , ma su jiran RETURN OF EXILED PRINCE 😂😂😂 a ci gaba da jira to 😊😊😊 Na gode sosai da irin kulawar da ke samu da ga gare ku Sisters , Allah ya bar zumunci duk me son yin magana da ni ga number ta nan +22798999753 I LOVE YOU SO MUCHHHHH 🩷🩷🩷 sign : MEERAH 🪻💜 .......... Downloaded from GNOVELS.COM.NG This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG For feedback and support Facebook : https://facebook.com/gnovels Twitter : https://twitter.com/gnovels Telegram : https://t.me/gnovels